Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 53 of 79
Episode 53: A Day to Remember
Daga nan suka nufi eatery mai kyau. Suna shiga suka zauna a corner mai dan soft lighting. Azrah ta zaɓi pasta da grilled chicken, shi kuma ya ɗauki burger da fries. Bayan an kawo musu suka fara ci a hankali without saying uffan
Can Khalil yana murmushi ya ce "Do you remember your first semester?"
Â
Azrah ta dan sosa kai tana dariya ta ce
"Don't remind me… I was too lost wallahi"
Khalil ya ce "And now… you shine. You didn't just survive, you bloomed"
Azrah ta zuba masa ido, zuciyarta cike da soyayyar sa. Tana ji kamar zuciyarta tana karanta ƙaunarsa har cikin numfashinta.
Ta É—auki ice cream da aka aje mata, banana flavor, ta fara sha kamar bata son sha shi kuma ya zuba mata ido. Bayan sun gama yayi clearing Bill sannan suka fito, inda yayi parking suka karasa, suna shiga ya tada motar straight schl dinsu ya wuce. A kofar hostel É—in yayi parking. Ta buÉ—e kofar motar, ta juyo tana kallon sa da murmushi a fuskarta ta ce
"Thank you... I don't even know what to...."
Yayi saurin matsowa kusa da ita, ya daura yatsansa a bakinta ya ce
"Shhhh... no thanks. Just shine tomorrow. That's all I want"
Ta ɗan lumshe ido, jikinta yayi sanyi. Sai kuma ta karasa sauka a motar, ta dauki laidan sayayyan, ta shige cikin hostel
Tana shiga dakinsu babu kowa As expected, Samira bata nan. Ta ajiye designer bag a gefen gadon ta wuce toilet ta watsa ruwa. Bayan ta fito, ta saka soft pajamas, ta kwanta akan gadonta.
Ta jawo wayarta. Ta rubuta masa sako
"Thank you for everything. For believing in me. For seeing the light I didn't even know I had. I'll shine tomorrow, for us..." tana turawa ta kashe wayanta nan da nan bacci ya kwashe ta
Yau ta kasance itace ranan da duk wani mai karatu a makarantar yake burinta, Da asuba Azrah ta farka, kamar yadda ta saba, miÆ™ewa tayi a hankali bayan tayi addu'ar tashi daga bacci, ta wuce toilet tayi alwala ta fito, cikin nutsuwa ta gabatar da nafilfilo sannan sai sallar Asuba. Bayan ta gama, ta zauna tayi Azkar, zuciyarta cike da godiya da farin ciki. A hankali ta É—auki wayarta ta shiga video call wa su Umma.Â
Duk da dare ne a Nigeria, suna cikin annashuwa da fara'a suka amsa kiran.Â
"Kin tashi lafiya 'yar albarka?" Umma ta faÉ—a da murmushi.Â
Azrah ta amsa da dariya, "Lafiya lau Umma, Umma yau ne fah"
Zahra ta É—ora kanta a kafaÉ—ar Umma ta fito ta cikin waya, tana kallon Azrah kamar zata yi kuka ta ce
"Yaya da ace da hali da na zo, sai dai kawai ki ganni" dariya ta yiÂ
Suka yi hira cikin nishaÉ—i, suna tayata murna. Bayan ta kashe kiran, Samira ta juyo daga gado tana kallonta.Â
"Jiya na dawo kina bacci kuma Naga... waÉ—annan kayan masu tsada fa... kar dai saurayin ki Khalil ne ya siyo miki?"
Azrah ta Æ™yalÆ™yale da dariya, sannan ta gyada kai cikin kunya.Â
Samira ta ware ido tace "Lallai wannan Khalil É—in yana so ki fito as Queen fa!"
Suka yi dariya daga haka Samira ta sauko a gadon itama. Can suka fara shirye-shiryensu. Sai ga kiran Sarah ya shigo wayan Azrah
"Yaushe zaki taho?"Sarah ta tambaya
"Da É—an anjima ne" Azrah ta amsa tana saka tooth paste a brush din hannunta
"Toh yanzu zan tafi makeup studio, daga nan sai mu shigo da su Mamana" cewar Sarah
Daga haka suka yi sallama. Bayan sun gama breakfast, sai ga kiran Khalil ya shigo
Bayan Azrah ta É—aga "Ki fito Azrah, ina bakin hostel" muryarsa mai taushi ta karade kunnenta
Azrah ta É—an lumshe ido ta ce "Yanzu kuma?" Ya ce
"Eh mana My shay, ke da Samira"
Ta kashe kiran tana kallon Samira ta ce
"Khalil na waje ne, yace mu fito yanzu"
Samira ta tashi da sauri tana cewa
"Ke muje, tashi muje mana, yanzu haka wani abun alkhairin ne naga guy É—in yana son slaying"
Da suka fita, Khalil ya tsaya yana kallon Azrah kamar zai haÉ—iye ta. Yana murmushi, shi ko É—an keftawa baya son yi
"Assalamu alaikum" ta ce a kunyace.Â
"Good Morning princess" yace da taushin murya. Samira ma gaishe sa tayi, bayan ya amsa gaisuwar Samira
Sai ya kalli Azrah "Ko akwai wani abu da za ku bukata a ciki? Idan babu kuma ku É—auko kayanku da za ku sa da dai duk wani abu da zaiyi completing dress É—inku, zan kai ku wajen makeup ne, daga can zan karasa da ku venue É—in kawai"
Azrah ta daure fuska kamar mai son kuka ta ce "Nifa ba zanyi ba wallahi"
Khalil ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka shi ma, exactly yadda tayi yayi copying ya ce "Ni kuma nace sai Queen tayi"
Wannan ne yasa Azrah ta yi dariya tana ja da baya
Samira na hararan Azrah ta ce "Nikam bari naje na dauko kaya na" sannan ta juya ta shiga cikin hostel. Azrah ma ta bita a baya, daya kai Samira gwara duk rashin son ta tayi kawai
Bayan sun fito daga hostel ɗin, Azrah da Samira kowaccensu na ɗauke da small trolley bag ɗin kayan ta. Khalil ya budewa Azrah ƙofa ta shiga bayan ya karɓi trolley ɗin, yasa a booth tare dana Samira, ya zagayo ya zauna a driver seat ya ja motar cikin nutsuwa da kulawa suka bar makarantar
A hanya babu mai magana sosai, hakan yasa cikin motar shiru... kowa da kalan tunanin da yake yi. Kallon gefensa Khalil ke yi ta gefen ido, yana kallon ta a hankali yanda tayi shiru, yanda idanunta ke kallon titi
Bayan wasu mintuna suka isa shagon makeup. Wurin ya kasance babban waje ne, mai tsabta, cike da kyalli da kwararrun ma'aikata. Da suka shiga ciki aka tarbe su da murmushi cike da girmama customers
"Welcome ma'am, happy convocation day!"
Ɗaya daga cikin makeup artists ta faɗa da fara'a tana kallon Azrah, wacce ta yi simple shigar safe, amma kyau da haske ya gama bayyana tun kafin a taɓa fuskar ta. Daga haka suka shiga ciki
Azrah ta zauna a gaban first mirror , Samira kuma a gefen ta. Wata babban makeup artist ce ta zo da kayan aikin ta tana kallon Azrah da murmushi ta ce
"Wow... you are naturally beautiful. Today you'll shine like a queen dear "
A hankali aka fara mata makeup, suka fara da moisturiser, suka shafe mata a fuska da luf-luf, sannan suka fara da foundation, concealer, powder da eyeshadow mai launin rose gold wanda ya shiga da bag and shoe dinta, Lips dinta aka yi soft nude pink, sannan aka gyara mata gira cikin nutsuwa.
Ana tsaka da yi, wata daga cikin staff din wajen tace
"Lallai mu dai zamu baki card É—inmu dan munsan zamu samu customers ta wajen ki? Wlh irin wannan kyau dole ya jawo mana mutane ne"
Sauran suka amsa da "yesss" wata tana É—aukar hotonta da izini tana cewa tana son zata saka a page É—in Makeup artist É—in su a Instagram.
Samira na gefe tana kallon Azrah tana dariya, tace
"Toh! Dama ai nace miki ki shirya zama amarya amma kika ki"
Azrah ta harare ta cikin madubi tana murmushi.
Bayan makeup aka ce su shiga VIP changing room. A can kowaccensu ta cire kayan jikinta ta saka kayan da zata je wajen da shi, Azrah ta zaro kwalin gown É—inta da Khalil ya siya mata, tana buÉ—ewa zuciyarta kamar zata fashe. Wannan green velvet gown ne mai É—an É—aukar ido, fitted ne, shoulder É—inta a buÉ—e kadan, sannan ya kama jikinta har kasa ta bayan kamar follow me, kana ganinta kamar queen É—in da za ta hau sarauta.
Ta saka gown É—in, ta saka takalmi da bag É—in da suka haÉ—a da kayan. Wani É—an gold necklace mai kyau da agogo ta saka, sannan ta É—an juya a gaban mirror. Bayan sun fito
"SubhanAllah…"
Wani staff É—in shagon ya faÉ—a yana kallonta, wanda da alama kamar musulmi ne
"Wallahi this is beyond beauty"
Har Azrah ta rasa inda zata sa kanta, ba don girman kai ba, sai don yadda ta ga kanta daban. Wannan ba Azrah É—in da ta fara shekarar karatu ba bace. Wannan wata sabuwa ce, mai kwarjini da nutsuwa, mace mai daraja. Ji tayi kamar ba zata iya shiga cikin mutane da wannan shigar ba.
Samira ta fito itama cikin nata shigar mai kyau. Suka kalli juna suka fashe da dariya.Â
"We're ready for the world" Azrah tace a hankali tana kallon kanta.
Khalil yana tsaye a waje yana danna wayarsa, amma zuciyarsa tun tuni ta gama tafiya cikin shagon. Bayan ya É—auki lokaci yana jiran su, sai yaji kamar ba zai iya jurewa ba, "Let me see for myself"Â ya faÉ—a cikin zuciyarsa.Â
Sauka yayi a motar. Ya bude Æ™ofar salon É—in a hankali, yana shiga ne kamar wanda aka kira sa. Sai idonsa ya sauka a kanta.Â
Azrah na tsaye a gaban mirror tana É—an gyara bracelet É—inta, ita da Samira suna dariya. Da Khalil ya hangota sai ya tsaya cak. Fuskar sa ta cika da wani irin mamaki ne lokaci guda.Â
"Innalillahi... Azrah?"ya furta a hankali kamar mai mamaki.
Salon É—in ya dauki dariya. Wata staff tace
"Calm down, sir? Kar ka cinye mana customer"
Khalil ya karasa a hankali, yana kallonta tun daga ƙafarta har zuwa saman gown ɗinta, yanda tayi shigar, makeup ɗinta da kwarjini da nutsuwa da kyau da yake gani a fuskarta. Ya tsaya gabanta, ya lumshe ido yana jin wani sanyi a zuciyarsa
"Honestly... I've never seen anything more beautiful'' yace da sanyi kamar zai shige jikinta
Azrah ta É—an ja baya tana murmushi, tayi Æ™asa da kai.Â
"Khalil stop… People are watching"
Ya É—an matsa kusa, kamar zai rungume ta, sai ya ja burki da kyar ya tsaya ya ce
"At this point, sai dai in É—auke ki in gudu"
Wata staff ta ce
"Ku tsaya mu É—auki hoto fa kafin ku gudu!"
Azrah da Samira suka tsaya kusa da juna, Khalil kuma ya tsaya a gefen Azrah yana kallonta yadda kasan zai cinyeta ko kuma irin rayuwar sa depends on that. Hakanan suka É—auki hotuna da dama, group pictures, close-up da har da candid É—in Khalil yana kallon Azrah da murmushi.Â
Bayan sun fito, Khalil ya bude musu Æ™ofa suka shiga motar. Yana zagayawa ya zauna a driver's seat ya kunna motar. Har suka bar salon É—in suna dariyan staffs É—inÂ
Yana driving, bai ce komai ba sai da suka kusa shiga makaranta, sannan yace a hankali
"Azrah, yau kin sa ni na sake gaskata cewa mace zata iya haskaka duniya… sai dai na zata.."
Azrah ta lumshe ido, ta dafe ƙirjinta tana jin zuciyarta yadda yake bugawa. Ta san yau ba kawai graduation day bace, yau rana ce da aka tabbatar da darajarta, taya zata so Khalil less a rayuwarta?
________
Hall ɗin da aka tanada domin Convocation ya sha ado tamkar ana shirin liyafar sarauta. Fitilu masu sheƙi suna haska ko'ina, red carpet ya shimfiɗe tun daga ƙofar shiga har zuwa bakin stage. Kujeru masu furanni sun zagaye hall ɗin, kuma banners masu dauke da sunayen makarantar da "GRADUATION 2025" sun manne ko'ina cikin hall din.
Manyan baki sun fara shigowa tun karfe 8 na safen, minista, shugabannin kamfanoni, sarakuna, iyaye da dangi daga ko'ina, kowa cikin shigar alfarma. Kamshi kuwa ba zaka gane wani kalan kamshin turaren bane kake ji dan kowa kamshi na musamman yake bugawa, babu abin da kake ji sai sautin dariya da gaisuwa daga ko'ina.Â
A wajen makaranta kuwa, cunkoson mutane da motoci ya hade titin. Jami'an tsaro na kai da komowa, da 'yan media suna daukar hoto da bidiyo, wasu kuma na tambayar graduates don jin yadda suke ji a wannan ranan
Duk makarantar ta É—au zafi, har sai da aka saka loudspeakers a wajen hall domin waÉ—anda ba su samu shiga ba su ji abin da ke faruwa ciki.Â
Jerin sunayen students suka fara karantawa cikin tsari. Kowanne department da list É—in students É—in su
Sun iso hall ɗin convocation Khalil yayi parking inda yasan idan zasu bi su shiga rana ba zai taba su ba. Ya kalle Azrah bai san sanda murmushi ya ƙuɓuce masa ba. Sai kuma ya sauka ya zaga ya buɗe mata kofar motar yana murmushi har sannan kuma ya gagara ɗauke idonsa a kanta ya ce
"Ready, Graduation Queen?"
Azrah ta gyada kai, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Tana ji numfashinta kamar na seizing a hankali. Samira data sauka ta karasa gaban motar itama ta rike hannunta, sako kafarta tayi kasa sannan ta fita daga motar a hankali, kayan su kadai abin a juyawa a sake kalla ne
Da suka shiga hall É—in, kallo da murmushi suka fara bibiyar su daga ko'ina da Sautin dariya, wasu ma suna ta hugging dinsu suna gaisuwa, wasu kuwa a hostel suka san fuskan juna, shiyasa sai suyi ta gaisawa at least wannan ranan nasu ne Azrah taji kamar ta koma hostel ta canza kayan barin yadda taga kamar attention É—in mutane ya koma kanta ne
A gefe kuma 'yan department ɗinta ne suke zaune kamar shine spot ɗin nasu, abokai, classmates suna murmushi, ihu, suka karɓe su da farin ciki. Wani yace da da karfi
"Haba! Graduation queen din mu ce! The best of all" duk suka fara dariya. Sarah ta zo da sauri, ta rungumi Azrah, ihu ta fara, mutane na bin su da kallo.Â
"Wow, look at youyyy?" Sarah ta faÉ—i tana bin Azrah da kallo tun daga sama har zuwa kafarta, Azrah ta yi dariya, ta ce "Ke Sarah bana wani son tsokana irin taki".Â
Ceremony begins
Mai jawabi 'Master of Ceremonies' ya fito, ya yi sallama, ya gabatar da manyan baki, Vice Chancellor, Deans, Malamai, parents, dangi. Dukkan hall É—in ya yi shiru, fitilu sai aikin haska ko ina da colors masu kyau
MC ya ce "Barkan mu da wannan rana ta tarihi, ranar da muke taya daktocinmu, sarakunan karatu da graduates masu murna. Yau rana ce da ilimi ya tsaya mana gaba data ke jiran mu!"
Ya fara da kiran sunayen graduates su je stage su karɓi takardun su. Da department na Business Administration ya fara. Kowa na fita zuwa karɓa, amma zuciyar Azrah na bugawa da karfi ta rasa me ke damunta yau ne na bugawan zuciya
Sai MC ya ce......
#Jiddatulkhayr
08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.