Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 31 of 79
Chapter 31: Between Books and Breaths
Rayuwa a India ba kamar Nigeria ba ce. Yare, abinci, yanayi, komai daban. Amma Azrah ta yi ƙoƙari wajen blending in da sabuwar rayuwar da ta samu kanta a ciki. A haka har suka gama first semester suka koma second semester wanda kamar wasa yanzu tana neman shekara a India, amma har yanzu dai, karatu ya zama priority dinta, ba ta da wani lokaci sai karatu, ina kika fito karatu, ina zaki karatu
" kuma cikin wannan ƙanƙanin lokaci sunanta ya gama karade department ɗinsu, daga lecturers har zuwa non-academic staff, babu wanda bai san Azrah ba ko da ba da suna ba, da siffa suke ganeta 'yar Nigeria mai natsuwa da hazaka
A bangaren Nigerian Students Association (NSA) ma, sai da suka nemi ta da kansu suka mata rijista da su, wannan kuwa saboda kullum sai sun ji ana ambatonta ko dai daga wani lecturer, ko wani activity inda aka ga irin tsayuwar da take yi. Har wani daga cikinsu ya ce, "Even if she tries to hide, her brain and discipline will always expose her"
Ba wani taro ko activity da ya shafi entrepreneurship, leadership ko creativity da za'a kira dalibai ba, sai an fara da sunan Azrah, ta riga ta zama alamar wakilci ga Nigeria a wuraren da ba ko'ina ba ne ake samun irin hakan, ko a cikin WhatsApp group na department É—insu, in har discussion ya shafi wani abu mai muhimmanci, yawanci sai an ambaci sunanta
Kullum da sassafe tana tashi zata nufa library, daga can ta wuce class, ta dawo tayi assignment, babu wani unnecessary talk babu yawan hira, strict routine kawai. Sai dai idan zata kira gida, musamman su Umma ko Zahra, toh anan ne zaka jita tana magana, ko kuma lokacin da Samira ke lallaba ta ta ci abinci, shine zaka ga ta fara surutu wai tana damunta
A gefe guda kuma, Khalil, wanda ta haÉ—u da shi a cool-down spot, bai tsaya daga kokarin sa ba, ya mayar da ita kamar wata biological sister É—in sa, Kullum sai ya nemo inda take karatu duk da yawan canza wajan karatu da take yi, haka zai tsiya abinci ya kai mata duk da yadda sometimes take ki amma inaa baya hakura, kullum yana zuwa kuwa abinda yake fara faÉ—a shine
"Bari ki huta yauzu pls let ur brain rest, I brought this for you"
Azrah sai dai tayi murmushi wanda ba ya wuce laɓɓanta ta ce
"Na gode, but I have a test next week"
"Wanda kika iya ba guduwa zai yi ba, wanda kuma zaki koya kawai ki fahimta no need ki cigaba da wahalar da kanki" zai faÉ—a yana gyara zamansa kusa da ita sannan ya zuba mata Idanu wanda kallon Granny É—insa yake mata
Azrah har yanzu bata ganin Khalil da wata romantic light, sai dai yadda yake tausayinta yana daɗa birgeta, ba a soyayya ba, amma in silent appreciation, Kamar wani big brother wanda yake tausaya wa ƙanwar sa da take wahala
Amma akwai abu É—aya da ke damunta "Samira" Duk da suna É—aki É—aya, har yanzu ba ta iya gane halin kawarta ba, Yarinya ce mai wayewa sosai, amma kullum cikin hira da samari da kawo su É—akinsu tana cewa ai "friends" ne kawai, amma Azrah tana kallon abin da ke sama da haka dan ita bata saba ganin haka ba, sai tana tunanin wata kila haka rayuwar masu kuÉ—i suke
Wata rana Azrah ta gagara daurewa ta tambaye ta
"Samira, ba kya gajiya da chatting da su ne? Yaushe kike karatu? Kuma bakya jin wani iri ne kawo maza har É—aki ne wai?"
Samira ta yi dariya kawai
"Ai ni in ba nayi socializing ba, I can't even focus, That's how I balance my mind"
Azrah ta girgiza kai
"Allah ya shirya mu baki É—aya"
***
Kiran gida kuwa ya zama wani sashi na ranarta da ba ta sakaci da shi har ya zama yana cikin daily routine É—inta, Zata kira Umma, su gaisa da natsuwa cike da annashuwa su yi hira sosai, sannan idan ita da Zahra ne har wani lokaci sai dariya ta cika dakin, Amma da zarar ta kira Bappah inhar baya É—akin Umma sai ya haÉ—a ta da Mama Wanda ko ta gasheta ma a dakile take amsawa
Wannan disconnect tsakanin Azrah da mahahaifiyarta na daga cikin abubuwan da suka fi daci a ranta sai dai ta saba, ta ɗauki komai a matsayin ƙaddara
*****
A cikin wannan rayuwa, akwai wata rana da Azrah ta ji kamar duniya ta tsaya mata ne, dan duk sanda taji ance zasu tsiya wanu abu hankalinta tashi yake dan kuɗin da gomnati ke basu dashi ta riƙe kanta kuma take turawa su Umma, Khalil ya kawo mata abinci, ya ce
"I hope you try this Egyptian dish, I made it myself"
Azrah ta kalli food container É—in da mamaki
"You cooked this? For me?"
Khalil ya É—an sosa kai
"Don't be shocked, I know a few things in the kitchen"
Bayan ta ci, sai ya kalleta da nutsuwa ya ce
"You know, I admire how focused you are, But don't let the world pass you by while you read about it in books"
Wannan magana ta taɓa zuciyar Azrah, Bata ce komai ba sai dai ta yi shiru, ta lumshe ido
Maybe... just maybe, akwai darasi a ciki
Wata safiya bayan Azrah ta gama karatunta, ta shiga bathroom domin ta watsa ruwa, Bayan ta fito, tana goge jikinta da towel, ta ji wayarta na kara, da sauri ta É—auka tana tunanin kiran daga gida ne ai kuwa taga video call ne daga Bappah ne dan duk sanda video call zai shigo wayan ta toh shi É—in ne, shi kaÉ—ai
Ta zauna a bakin gado tana receiving call É—in, Zahra ce ta bayyana akan screen da fara'a sosai a fuskarta kamar wacca aka mata albishir
"Zahra ke ce? Masha Allah, sai wani shauki kike kamar an ba ki sabuwar waya!" Azrah ta faÉ—a tana dariya, tana sake hayewa saman gadonta
Zahra ta haɗe girarta da shagwaɓa
"Saboda bani da wata bukata sai ta waya"
Azrah tayi dariya ta ce
"Ai sanin halin ne, ba abinda yanzu kike bukata sai waya, yanzu faÉ—a min menene ya saka min ke farin ciki"
Zahra tayi dariya ta ce
"Ai da gaske ne! A sabuwar makarantar mu Nice dai da aka fitar da result É—in term É—in nan, ni na zo first position!"
Azrah ta tashi zaune ba tare data san tayi hakan ba ma, ta ce
"Subhanallah! Zahraaa! Na miki murna, congratulations! Ni kaina sai na ji kamar ni na ci"
Zahra ta yi ƙara tana dariya jin yadda Azrahn tayi sounding
"Toh ke kuma yaushe za ki dawo? I miss you wallahi"
Azrah ta ce
"Very soon, Muna gama Exams É—in da zamu fara na second semester zan dawo, Nima nayi missing É—inku nayi kuka har na gaji"
Suka ci gaba da hira na Æ´an mintuna kafin suka yi sallama, Azrah tayi tagumi ta faÉ—a duniyar tunani da girman nauyin da ke kanta, Zahra ta dogara gareta fiye da yadda take tunani hakan yake kara bata wani motivation speed
***
Washegarin kamar yadda take daga Library sai class, ana cikin lecture, wani lecturer ne a class ɗin ganin kamar basu fahimta kuma basu wani bada hadi kai yasa ya fara tambayoyi, kamar yadda aka saba, Azrah ce ta miƙe tsaye da kwarin gwiwa ta bada amsa mai gamsarwa, har lecturern ya gamsu da murmushi ya ce
"Excellent response as always, Miss Azrah"
A nan É—alibai suka kalle ta da girmamawa kamar wata scholar
Sai dai kafin lecture ya ƙare, wani lecturer ya shiga cikin hall ɗin da sauri yana daftari a hannu, ya ce
"Hey, Everyone! Please note, new exam timetable has just been pasted outside the department. Check it immediately"
Da sauri É—alibai suka fara fita da damuwa, zuciyoyinsu na duka uku uku, Azrah kuwa, da ke son ta duba da kanta kafin a saka a WhatsApp group, ta É—auki littafinta da nutsuwa ta nufi inda aka manna timetable É—in dake bakin department É—insu
Tana cikin tafiya a corridor mai cike da É—alibai, ta hangi Khalil na tahowa daga nesa, kamar wanda ya shigo da nufin ganinta sai kuma take ayyana cewa dan ita É—inne ma ya shigo dan shi baya wani damuwa da nasa karatun kamar yadda ya damu da nata karatun
Bayan ya iso inda take da murmushi a fuskarta kafin ta ce uffan, ya miƙa mata folded paper
"Your timetable, I figured you'd want it early"
Azrah ta buÉ—e baki da mamaki
"Khalil? How did you even know it's out?"
Ya É—an harare ta da murmushi
"Don't thank me, I don't like all that unnecessary drama"
Ta yi dariya cikin shauki tana jinjina kanta
"Toh shikenan, Nagode kawai in secret"
Buga mata wani littafin hannunsa yayi a kanta ya ce
"Even in secret, I'll still know"
A wannan rana, Azrah ta ƙara fahimtar cewa a duk inda ka ke, akwai mutane da Allah ke turo maka domin rage maka nauyi ba lallai sai danginka ba
Tana tafiya tana duban timetable ɗin, zuciyarta na bugawa da ƙarfin karatu da fargabar jarabawa.
****
Azrah ta zauna tana fuskantar bangon ɗakin, tana kallon exam timetable da Khalil ya kawo mata jiya, wanda ta manna da tape sosai kamar wani important docx Yadda ta kira masa ido dai ka ɗauka tana son ya mata magana ne, Sai ta sake dauko wani blank paper ta fara rubuta tsarin karatun ta rannan da zata maida hankali akan kowanne course, irin abubuwan da take bukatar maimaitawa, da kuma notes da zata koma duba wa, A hankali ta dora pen a akai ta miƙe, ta manna shi a jikin bangon kusa da timetable ɗin.
Samira da ke kwance akan gadonta tana kallonta cike da mamaki ta ce, "Ohh, Nikam naga ta kaina da ke, Kin dawo kamar irin robot É—in nan ne fah, haba mana ai ko robot ne yana bukatar chargy"
Sai ta kwashe da dariya, ta dafe cikinta tana kallon Azrah, "Just imagine, kina reacting kamar wata mad person! Haba mana Azrah, calm yourself down, yanda kika ci uban karatu yanzu, ko baki sake duba komai ba in exams ya zo, you'll still pass In Shaa Allah"
Azrah ta juyo ta wani harare ta da idonta mai cike da gajiya banda bacci babu abinda kake ganin a idon nata, ta ce da ita,"Ni ki kyale Ni Samira! I can't afford to joke around"
Ta juya zuwa wajan da wayarta ke charging ta cire ta daga charger ta zauna kusa da window, Tana kallon timetable da kuma reading plan É—inta da ta manna a bango, zuciyarta cike da tsoro da fargaba, Ta buÉ—e contact list, ta danna lambar Bappah, A zuciyarta, she just wanted to hear Umma's voice koda kuwa zata ce mata "Allah ya bata sa'a" ne, sannan kuma ta faÉ—a mata already ta tsara schedule É—inta gaba É—aya yau
Zuciyarta na ta bugawa da dan karamin tsoro da kuma anticipation, She wanted to do well, She needed to, bayan ya kusa katsewa sai aka yi picking call É—in, bata san sanda ta sake murmushi ba ganin Umma ce da kanta ta É—aga kiran, cike da farin cikin ganinta
"Hello Umma" ta faÉ—a a hankali cikin lumshewar murya
"Azrah... Azrah 'yata, kina lafiya?" muryar Umma cike da ƙauna da kulawa, kana jin muryar nata kasan tayi missing 'yarta
"Lafiya lau Umma naa, ai yau na ce kiran na musamman ne Umma... timetable ɗinmu ya fito" ta ce tana ɗan lumshe ido, tana ƙoƙarin danne damuwar da ke damunta
"Toh Allah ya taimaka Azrah, Allah ya baki sa'a, ko da yaushe ina muku addu'a kuma za'a kara In Shaa Allah, Kin shirya dai ko?" Umma ta tambaya, tana ƙoƙarin sauraron komai daga muryar nata dan nan take fahimtar komai ko da bata furta ba
Azrah ta ɗan numfasa "Nayi iya ƙoƙarina Umma na, Nayi reading plan na ma, Nakan ɗanyi karatu har dare, sometimes ban ma komawa ɗaki da wuri ba idan na tashi daga lectures"
Umma tayi shiru na dan lokaci sai tace da tausayi 'yarta "Allah ya miki Albarka Azrah, ki tabbatar kina hutawa kaÉ—an-kaÉ—an, kiyi addu'a Kema sosai, sannan kada ki manta da karatun Al-Qur'ani everyday Kuma kar kiyi overwork kanki fa"
Azrah ta dan yi murmushi mai rauni ta ce
"In shaa Allah Umma, Ina missing dinki sosai"
"Ina missing dinki nima, ga Bappahn ku na kusa
Sai taji muryar Bappah ya ce "Azrah sannu da ƙoƙari, ki kula da kanki, Allah baki sa'a"
Azrah ta dariya cike da jin kunya da tace da Umma tana missing É—inta, ta ce
"Amin Bappah, Nagode kwarai"
"Toh Allah ya sa mu dace, ki dinga hutawa dan nasan kinda ɓaci"
"Amin Bappah, Thank you"
Bayan ta kashe wayar, ta sauke ajiyar zuciya, ta dan jingina da gado, tana jin kamar ta samu wani abu da ta daÉ—e tana craving wani nutsuwa ce taji yana shigarta
Samira dake gefe ta ɗago kai, "Anya kuwa wannan kawar tawa ba zata yi distinction ba? You're too focused girl'
Azrah ta juyo da murmushi, ta ce "Distinction kawai fa? In har babu first class, I won't stop'
This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.