Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 51 of 79
Episode 51: The Becoming of Azrah
Yau kamar kullum, Azrah ta dawo daga lecture gajiya fal tattare da ita, sai ta tarar da Samira ta fito a wanka tana shiryawa, Azrah na cire hijab É—inta ta ce
"Samira lafiya kuwa? Wannan shirin fa kamar tafiya zaki yi" ta karasa maganar ne ganin yadda ta ciro duk kayan wardrobe É—in Azrahn
Samira ta É—an kalli agogo tace,Â
"Kiyi sauri ki shiga ki watsa ruwa, ba zan ce komai ba yanzu sai mun fita tukun nan"
Azrah ta ja dogon tsaki "Ke kuma ai duk lokacin da kike boye min abu haka ake..."Â
"Ki shiga wanka, Azrah!" Samira ta katseta da dariya, tana tura ta cikin ban É—aki wanda ko kaya Azrahn bata cire ba
Azrah ta kwace kanta ta cire kayan jikinta sannan ta shiga toilet É—in
Bayan mintuna ta fito, ta saka kayan da Samira ta ciro mata, shigar modest gown, tana kokarin gyara veil É—inta. Har yanzu ba ta fahimci inda za su ba. Daga haka ta bi Samira kawai
Samira kuwa kai tsaye suka tafi wata eatery wuri mai nutsuwa da kyau, wanda Samira ba ta taÉ“a zuwa da ita ba a baya.Â
Suna shiga, Azrah ta É—an tsaya cak. Idonta na kallon wani mutum da ke zaune ya bada baya, haka kawai taji zuciyarta na bugawa da sauri, ta kalli Samira wanda take murmushi ta ce "mu shiga mana", step É—aya tayi, sai da zuciyarta ta buga ganin wanda ya jiyo....Â
"Khalil"
"Ya Salaam!" ta furta a hankali, zuciyarta na bugawa,
Khalil ya miÆ™e tsaye da murmushin kwance a fuskan sa ya ce "Azrah..."Â
Cikin gasgata shine ko A'a dan ganin komai take a mafarki ta ce "Khalil? Kai ne?"Â
Samira tana dariya ta ce
"Ni zan je can, enjoy yourselves!"
Khalil ya nuna mata kujera, ta zauna still idonta akansa yake dagaske gani take kamar a mafarki.Â
"Kai ne a India? Yaushe kazo? Me yasa ba ka gaya min zaka zo ba?"Â
Khalil ya yi murmushin, reaction É—inta ba kaÉ—an ba ya basa dariya kuma duk abin da zai gani a idanunta kaunar sa ne, ya ce
"Because I needed this moment to be real. Jiya na dawo India a karo na biyu ba da niyyar karatu ba sai dan ke Azrah. Na fada wa Samira ne kawai Sbd nayi surprising É—inki, I wanted to see your face, not through a screen this time, Shiyasa kika ganni anan"
Shiru ya dan ratsa tsakaninsu. Kowa da kalar tunanin daya ke yi, sannan duk zuciyoyinsu yana bugawa ne da shauki da kaunar junansu
Sai Khalil ya ci gaba "Azrah, nayi Æ™oÆ™ari in mantaki tun farkon haÉ—uwar mu da kika nuna baki da ra'ayi na, Nayi Æ™oÆ™ari in daina son ki. Amma ko a cikin duhun yanayi, duk rintsi duk wuya duk wata sassa na jikina yana kiran sunanki a zuciyata. Na dawo... not just for business... but for you, Please karki ce baki So na"Â
Azrah ta rasa inda zata saka ranta da jin wannan kalaman nasa, ta ɗauke kallonta daga gare sa, tana jin yadda zuciyar ke kara tsananta bugu. Hawaye suka gangaro a hankali. ta ce
"Why now, Khalil? Why after all this time?"Â
Khalil ya matso kusa, ya kama hannunta, ta zare hannunta daga nasa, yana kallonta ya ce
"Because now, I'm ready. I'm done running. I want to fight for you. I want to be the man that deserves you"Â
Ta rufe Fuskarta da tafukan hannunta ta fashe da kuka, ba kuka na bakin ciki ba, sai dai na cike da nauyin so da tsoro a lokaci guda. Khalil ya miƙe, ya durkusa a gabanta, yana share mata hawayenta da da handkerchief ɗinsa mai kamshin turare ya girgiza mata kai, dakyar ya ce
"Don't cry, please. Not for me. Not today"Â
Suna cikin wannan halin ne Samira ta dawo da take-away a hannu, tana kallonsu da murmushin jin daÉ—i ta ce
"Yanzu na tabbatar… wannan so ba zaku iya boyewa ba" ta kare maganar tana dariya.....
RAYUWAR AZRAH A INDIA GURGUJE.......
Rayuwa a India ta cigaba da juyawa cikin sauyin lokaci da sauyin hali. Duk da kasancewar Azrah ta saba da sabuwar rayuwa, har yanzu akwai abubuwan da har kullum suke koya mata sabon darasi. Ta shiga Second Semester 200 Level cikin nutsuwa da kwarin gwiwa, sai dai har yanzu tsakanin ta da Sadeeq babu wata jituwa. Duk lokacin da suka haÉ—u a lecture hall, kallo É—aya suke yiwa juna su É—auke kai, wanda har yau ta rasa abin data masa wanda ya tsane ta har haka
Sai dai a gefe guda, dangantakarta da Sarah ta ƙara ƙarfafa. Sun zama kamar 'yan uwa, ba kawai saboda suna classmates ba, A'a saboda sun haɗa zuciya wajen karatu da rayuwa gaba ɗaya. Kowace rana bayan lectures, suna fita karatu, library ko wani quiet spot da za su nutsu su maida hankali. Karatu ya ɗauke musu hankali, sun kaucewa abubuwan da ke ɗaukar lokaci marar amfani. Ba ruwan su da wani social activities na schl, ba yawan yawo. Wannan haɗin kai ne ya ƙara basu ƙarfi a makarantar da ke cike da kalubale sannan yasa kawance su yayi mugun karfi ..
Wata rana, ana tsakiyar semester, iyayen Sarah suka zo daga Pakistan domin duba 'yarsu. Cikin farin ciki Sarah ta gabatar da Azrah a matsayin ƙawarta mafi kusa ma makarantar. Hakan ya sa iyayen nata jin daɗi, musamman mahaifiyarta da lokaci guda taji Azrahn ta kwanta mata a rai... Sun ɗauki hotuna tare da Azrah, sunyi hira sosai har da dariya wanda hakan yasa Azrah sake wa da su. Mahaifin Sarah mai barkwanci ya kalli Azrah yana dariya ya ce "Ke da kyau da hankali ba kamar kawarki ba, lallai Sara ta yi sa'a dai" duk suka yi dariya...
Duk da yadda karatun su yayi zafi, Azrah bata katse waya da gida ba. Ita da su Umma kullum sai sunyi waya. Har sau da dama Umma na cewa, "Azrah, karki manta kina nesa amma zuciyata na tare da ke, hakan ke saka min kamar muna kusa wlh, Ki kula da kanki Allah sa ki gama a sa'a" Wadannan kalmomi ne da ke ba Azrah ƙarfin gwiwan karatu
Khalil kuwa duk da cewa bai fara PhD ɗin ba, yana yawan ziyartar Azrah, musamman every end of 2 months. Amma duk da zuwan nasa, ba lallai su zauna sosai ba, saboda Azrah kullum cikin karatu take. Khalil yakan ce "Azrah, I'm proud of how focused you are" Kuma hakan yana ƙara mata kwarin gwiwa
Lokacin semester ya ja har ta gama 200 Level. Bayan exams, ta tafi gida Nigeria domin hutu. Wannan hutun ne ya zama na ƙarshe da zata koma gida kafin ta kammala degree. Tayi amfani da lokacin sosai, kasancewa da Umma da Zahra, Sake dage wa wajen kara karfin Sana'o'inta, wanda a wannan hutun ma sai data je gidan Dada sbd ba zata sake dawowa ba sai bayan ta kammala
Dawowarta daga hutu ba karamin canzawa tayi ba. tana cikin sabuwar natsuwa, sabuwar kwarin gwiwa. Shigarta 300 Level kamar sabon babi ne a rayuwarta. Wannan lokacin ba kamar da ba ne, dan sake dawowa da kwarin gwiwa sbd ganin har sannan tana first class kuma tayi alkawarin ba zata sauka a wannan class É—in...
Cikin wannan semester ne kuma Deen, Saurayin Samira ya zo India. Da yake ɗakinsu Samira zai sauka, hakan ya sa Azrah ta tattara kayanta ta koma gidan Sarah tun kafin ya iso, Azrah sam bata ji daɗin wannan lamarin ba, dan ko data ma Samira magana akan rashin dacewar haka tunda ba wai an ɗaura musu auren bane da kawai ya kama hotel amma Samira ta nuna A'a babu komai, wanda hakan yasa har ya koma Azrah taki yarda su haɗu ballai su gaisa wanda ba kaɗan ba Samira taji haushin hakan. A bangaren Sarah kuma hakan ya ɗaure musu ƙawance sosai. Sun cigaba da karatun su tare.
Lokacin IT..... Wannan siwes ɗin ne ya daure Azrah sosai. Ko kadan bata samu sauƙi.. kullum cikin aiki saboda ƙwazonta, ga aiki da reports da ake bukata kullum. Takan dawo gida a gajiye, wani lokacin har taji kamar ba zata iya copping ba. Amma haka ta dage da juriya. Wani lokaci Sarah kan ce "Azrah kina bani mamaki wallahi. I wish I had your strength" Azrah kuma sai ta ce "Nima nasan Allah ne ke taimako na amma nima bansa ya ake nake wannan aikin ba"
Cikin wannan semester É—in ne aka saka ranar auren Samira. Ana hutu da sati biyu za a yi. Samira ba kaÉ—an ba tayi murna, wanda tun a lokacin ta fara shirye-shiryenta
A cikin wannan tafiya, rayuwar Azrah ta canza sosai. Ba wai ta canza a fuska bane, amma zuciyarta ta sami sabuwar haske. Ta daina tsoron magana. Ta daina tsoron mutane especially Sadeeq daya sata a gaba, ko kaÉ—an ta daina shakkarsa. Yana yin yadda ta koma akwai wata rana da Sagir ya ce mata "Miss Azrah, you're a silent power"
A ƙarshe semester ya zo ƙarshe. Ta fara shiri don final year. Idan ka ganta yanzu, zaka rantse ba ita ce yarinyar da ta zo India da boyayyen murya da rashin confident ba, Azrah ta girma sosai ta kara hankali, da nutsuwa, da hangen nesa.
Wata rana tana hostel, Samira ta kalleta tana murmushi ta ce
"Azrah do you remember the first day you entered this hostel? You were so quiet and scared. Look at you now you're glowing with confidence"
Azrah ta yi dariya da bata shirya yi ba, ta lumshe ido ta ce
"Wallahi Samira I went through a lot. But I survived. And I've changed... a lot"
Final Semester ya zo kamar ambaliya ya mamaye komai.Â
Deadlines din sun zama kamar ƙaya,
Pressure kuwa? sai ka ce mutum rasa ransa zai yi dan wahala da su project
Amma Azrah ba ta ja da baya ba.Â
Tuni ta saba da wannan yanayin, ta san yadda ake tsallaka wahala da juriya
Yanzu ba ta jin tsoro idan assignments suka taru.Â
Ba ta kuka idan ta kasa gane wani abu.Â
Zata tsaya, ta numfasa, tayi addu'a… sai ta soma aikatawaÂ
Sarah kuwa, ta zama ginshiki gare ta.Â
Su biyu kullum library, dare da rana.Â
Wani lokaci har kwana suke yi a faculty.Â
Ma'aikatan tsabta ma sun saba da fuskar su.
Khalil kuwa yana kiran ta akai-akai.Â
Kamar yana jin lokacin da zuciyarta ke buÆ™atar karin Æ™arfi.Â
Basa daÉ—e wa a wayan dan baya son hanata karatu, amma muryarsa na kawo salama sosai a rayuwarta, yakan ce
"Azrah kin kusa. Kar ki bari haskenki ya mutu, First class din nan dai karki sauka please"
Wannan ya zama kamar zikirinta a zuciya.
Sadeeq?Â
Har yanzu yana nan, yadda yake a farko, sai dai kuma tsanarta a zuciyarsa ya karu ne sakamakon bata tsoron sa ynx, yana ja mata tsaki itama zata yi, idan ko kallon banza ya mata haka zata rama dan tasan bai isa yace zai mata komai ba, da tuni tayi reporting É—insa
Amma duk da rashin jituwa tsakaninta da Sadeeq, Æ™wazon Azrah da hazakarta na ci gaba da ja hankalin sa a sirrance.Â
Yakan ganta tana daurewa da karatu ba kakkautawa,Â
kuma sau da dama sai ya kasa dauke idanuwansa daga kanta ko da kuwa ba zai taɓa yarda da hakan ba.
Sai gashi ranar paper na Æ™arshe ta zo.Â
Azrah bata runtsa ba duka dare tana maimaita notes dinta.Â
Da asuba, jikinta rauni, amma zuciyarta cike da Æ™arfi da shiri.Â
Ta saka hijabinta akan sleepwear É—inta da ko cirewa bata yi ba, ta dauki pen and exams card dinta
ta furta "Bismillah" kafin ta fice.
A cikin hall, zukata na bugawa da tashin hankali.Â
An raba question paper da booklet, Lokaci ya fara.Â
Hannun Azrah bai tsaya ba da rubutu ba, yadda kasan rubutun flowing yake yi haka take rubutu
Bayan awa uku da fara exams É—in… sai aka ce pens down.Â
Farinciki ya barke.Â
"Finally!"Â
Azrah ta kalli kewayenta, fuskoki cike da murmushi, runguma, murna...Â
Ta juya ta kalli Sarah,Â
suka yi dariya mai sa hawaye.Â
Duk suka fita a hall É—in, suka dauki hotuna da abokan su, wasu suka rungumi malamai,Â
har ma daga karshe duk suka tsaya waje ɗaya suka dauki group selfies a ƙarƙashin butterfly
Gaba É—aya abin kamar mafarki.
Bayan exams ance karsu tafi saboda zasu tsaya har result ya fito sannan ayi convocation kafin su tafi, hakan ya zama kamar suna da É—an gajeren Hutu kenan,
Amma Azrah bata samu hutu sosai ba.
A mafi yawan lokacin, tana cikin tunani ne.
"Shikenan kenan? Ina shekarun nan suka tafi?"
Ta tuna da kanta lokacin farko da ta zo yarinyar nan mai kuka.Â
Ta tuna da Umma, Zahra, da Khalil, da rayuwa gaba É—aya.Â
Ta gane cewa ta canza... sosai.
A yanzu dai suna jira sakamako,
sakamakon da zai tabbatar da ta kammala digiri.Â
Gaba kuma shine convocation, ranar da tun shekarunta na farko take mafarkin sa.
Ranar wata Laraba da yamma ne
Bayan sun karÉ“i rigunan graduation É—insu,Â
Wanda ke É—auke da sunan su da tambarin department,Â
Azrah da Sarah suka saka tare da wata Pant, suka fita da fara'a a fuskokin su.Â
Suka tafi zuwa department,Â
Inda suka fara É—aukar hotuna da lecturers É—insu,Â
Kowa cike da murna, dariya da farin ciki.Â
Fuskar su ta bayyana cewa an cimma babban burin rayuwa.Â
Azrah ta ji zuciyarta na tafasa amma na farin ciki,Â
Wannan ne Æ™arshen wata babbar tafiya.Â
#Jiddatulkhayr
08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.