Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 33 of 79

Episode 33: The Wait After The Storm

Kwanaki sun shige, sati na biyu kenan da Azrah ta shiga cikakken yanayin exam pressure, Dan har mantawa take da gida idan ba wai ta zo shiga exams hall bane ta kira gida ta ce a mata addu'a. Ba dare, ba rana, babu komai a gabanta sai books da schedule É—inta da ta manna a bango. Kullum dare tana karatu har wayewar gari, idan kuma ta fita da rana toh da kyar take komawa É—aki kafin 11 na dare

A wani yamma, tana zaune a wani kusurwar bayan makaranta, inda take jin iska da nutsuwa duk sanda take karatu a wajan, saboda wajan babu wasu É—alibai, So wajan very quiet place ne, yau ma kamar sauran ranakun ne ta zauna tana karatun ta, ba zato ba tsammani kawai taji an aje mata food flask a gabanta da sauri ta É—aga kai dan ganin wanene, sai ta kalli Khalil ne, ya kafe ta da ido, yana mata murmushi

''You haven't eaten all day'' ya ce a hankali, yana matsawa kusa da ita 'You'll break down if you keep this up''

Azrah ta sunkuyar da kai kawai, sai can ta ce

''I'm fine, I just need to finish these chapters'' mamakin yanda yasan tana wajan ta fara

''Toh ni kuma zanyi reminding É—inki everyday'' ya ce da murmushi sai kuma ya É—aura

"Even if you ignore me''

Can sai ga Samira ta nufo su, tana isa inda suke zaune tayi musu sallama, ganin books a gaban Azrah yasa ta taɓe baki ta ce

''I just came to pick the room key'' And guess what? I'm tired of begging this girl to rest'' ta karasa maganar tana kallon khalil dake zaune gefen Azrah

Khalil ya bawa Samira duk wani attention É—insa yana kallon ta kamar dai ba zai ce komai ba sai kuma yace ''I was just telling her the same thing''

Samira ta girgiza kai

''Wallahi sometimes I feel like I'm talking to a wall, But fine, if she collapses, we'll read the books to her in the hospital.''

Azrah tayi murmushi tana É—auke kanta daga kansu, ta ce

"Thanks for caring, I'll eat, I promise''

Khalil yayi saurin ya ce

''Good, and next time, if you don't eat, I'll drag you myself'' Duk suka yi dariya...

A cikin wani yanayi na zafin rana da gajiyar karatu, ɗalibai ke tafiya a hankali zuwa cikin examination hall. Murmushin nasara da alamar ƙarshe na wani dogon tafiya ya bayyana a fuskokinsu, musamman Azrah da ke tafe da Samira wanda yau venue ɗinsu ɗaya, hannunta ɗauke da biro, exams card da kuma bottle water ɗinta.

''Wallahi Samira idan aka fito da tutorial Questions É—in da nake ta karantawa jiya, sai na miki rawa a cikin hall É—in, dan wlhi calculation É—in da wahala'' Azrah ta faÉ—a tana dariya

Samira ta harare ta ''Ke dai muyi sauri kafin muyi latti a hana mu shiga idan ba haka ba sai kiyi rawan a waje''

Suna isa venue ɗin suka samu already har an shiga, suka shiga cikin hall din, suka zauna a seat da aka riga aka manna sunan su da kuma ID no ɗinsu, silence ya fara ɗaukar hall ɗin, yayin da invigilators suka raba question papers, Azrah ta karɓa, ta kalli page ɗin gaba ɗaya tana bin questions ɗin da kallo, sai murmushi ya bayyana a fuskarta ba tare data ma ankara ba 'Exactly what I revised!' zuciyarta ta furta

Ba tare da ɓata lokaci ba ta fara rubutu da sauri kamar wata ‘yar jarida da ke bi da lokaci, ko kuma judge dake ɗaukan statement Lokaci na tafiya, duk da gajjiyar da tayi amma zuciyarta cike da kwarin gwiwa take, Har aka kaɗa ƙararrawar stop aka karɓi papers ɗin daga hannunsu, Azrah ta dafe kirjinta da hannunta biyu tana fitar da wani hucin gajjiya

''Finally... we made it, In shaa Allah" ta faÉ—a a hankali tana kallon Samira wadda take É—ayan row É—in, suna haÉ—a ido ta sakar mata murmushi

Suna shirin fita sai ga wani non academic staff ya shigo hall É—in nasu, da hannu ya fara musu alamun su zauna suyi shiru ganin yadda suke surutu, ya ce

''Attention please! All students are to remain on campus for seven more days. The final results will be released within this period. Only those without any issues will be cleared to travel afterward''

Wani ''Ahh?'' ya cika gurin kowa ya fara kallon kallo dan wasu already sun shirya tafiya gobe, wasu É—aliban kuma suka ce, ''Gaskiya we need this rest, at least zasu huta a school kafin su tafi gida'' wasu kuma banda hararan sa babu abinda suke masa, Azrah dai bata ce komai ba duk da yadda take craving tafiya gida, sai lumshe idanu da ta yi tana sauke numfashi, ta san cewa kwanaki bakwai kawai ke tsakanin ta da farin cikin ta fiye da komai, she pray hakan shine mafi Alkhairi kuma Allah yasa ta samu sakamako mai kyau, dan bata damu ta tafi da wuri kuma ace sakamakon bai yi yadda take so ba

Washe gari Azrah tayi wani irin bacci mai cike da kwanciyar hankali, da kyar Samira ta tashe ta sallan asuba a hakan ma wai da wari ta kwanta, tana idarwa dakyar dakyar ta samu ta yi azkar dan wani wawan baccin kuma take sake ji, tana idarwa ta miƙe ta faɗa kan gadon ko hijabi bata cire ba nan da nan wani baccin ya sake kwashewa ta, daga karshe Samira ce ta mike ta gyara mata kwanciyarta tana mita

"Ba dole ba, ai dole kiyi irin wannan baccin, wani ma sai ya É—auka ai shaye shaye kika fara" amma ina tuni Azrah tayi nisa

Can wajajen karfe 8am sai ga wayan Azrah na ringing, Samira ta miƙe da niyyar mai da mata wayan silent, idan gida ne kuma ta ɗauka mata, ga mamakinta kawai taga Azrah tasa hannu ta ja wajan daga kasan pillow ɗinta ta yar kasan tile sannan ta cigaba da baccinta, Samira ta kwashe da dariya ta ce

"Da kyau, ai dole ki biya bashin baccin da baki yi"

Ba Azrah ta farka ba sai karfe 12pm itama kanta sai data yi mamakin kanta, wanka ta fara yi sannan ta fito ko kallon Samira dake tsokarta bata yi ba, wayan ta dake ringing yasa ta jawo ta É—auka

Murmushi tayi ta ce

"Umma naa, É—azu kun kira ai bacci nake yi" Umma ta ce

"Just wanna say congratulations ne, Allah yasa kin rubuta a sa'a" bata kai ga amsawa ba sai ga muryan Zahra

"Ya Azrah.. kin taso ne? Ki cemin kawai kina jirgi" dariyar da bata yi niyya bane tayi ta ce

"I'm sorry Zahra sai nan da 6 Days, sun ce sai mun jira result ɗinmu ya fito, wanda basu da matsala ne za'a sake su tafi gida" Zahra ta taɓe baki ta ce

"Ni gaski na gaji da jira" Umma dake gefenta ta ce

"Kuka yi wajan shekara baku tare shine 7 days ba zaki iya kara mata ba, toh sannu Zahra" Azrah ta ce

"Toh ai shine" Umma ta ce

"Toh Allah sa hakan ya zama alkhairi, Allah baki sa'a" ta amsa da Amin sannan ta miƙawa Samiran wayan suka gaisa da Umman.

Tun daga wannan ranan haka Azrah ta mayar da schedule É—inta kamar wata princess, daga bacci sai kuma sallah da cin abinci, ko tashi bata son yi, ita kanta har mamaki take yadda take wannan baccin, duk wani ramar da tayi during exams period duk ta mayar da jikinta harda kara wani kiban, dan ko fita bata yi sai idan Khalil ya zo duba ta ne

Kwanaki bakwai sun wuce kamar mintuna, musamman ga Azrah da zuciyarta ke cikin wani irin tseren murna da fargaba bata da buri kamar ta ganta a gida, A ranar da aka ce za a fitar da sakamakon, tun da safe aka fara jin hayaniyan students a cikin hostels hatta makarantar ma sai data ɗauki wani sauti na musamman duk yawancin students dake offK ma duk sun shigo, kowa da sabuwar shelar sa, wasu na fargaba, wasu na fatan alheri, wasu kuwa ba sa cewa komai duk da dai zuciyarsu a ciƙe take da fargaba

Azrah ta farka da wuri fiye da kullum. Ko data yi sallar asuba bata koma bacci ba kamar yadda ta saba, sai ma wanka da tayi, ta É—aura doguwar rigar cotton mai launin sky blue, ta É—aura light veil, ta zauna bakin window tana jiran lokacin da za a fitar da result, bakinta kuma bai bar ambaton Allah ba

Kamar da misalin 10:35am ne aka fara tura sakamakon ta online platform É—in makarantar. Kamar wani mugun abu ya faru a cikin School É—in, aka fara jin ihun ''I passed!'' daga É—ayan hostel É—in, Samira ta shigo da gudu tana cewa ''Azrah! Azrah! Check your result please! They've started uploading!''

Azrah ta fara danna wayarta hannunta na rawa. Password É—in kanta ma sai da ta kusan mantawa, Sai da ta shaki iska sau biyu kafin ta sake shiga portal É—in tana addu'a ta danna result section...

First Class Honors CGPA 4.88/5.00

Best Student of the year Department of Business Administration

Ji tayi kamar wacca aka datsa ta a wajen, zuciyarta ta tsaya na wani dakika, Sai hawaye suka fara tsintiri suna sauka kan fuskanta, ta toshe bakinta da hannayenta biyu, sai kuma ta fashe da kuka sosai, Kukan da ke tattare da shekara guda na wahala, rashin bacci, tashin hankali, da ƙoƙari amma sai yanzu ya mamaye da abinda take buri, burin samu, wato ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na farin ciki ne, Samira ta rungumeta tana cewa, ''Azrah you did it! Wallahi kin ci ubansun! I'm so proud of you!''

Itama tayi wrapping hannunta a bayan Samira tana sake fashewa da kukan kuma meanwhile tana dariya ta ce

"Samira ki ce min ba mafarki bane, please ki faÉ—a min Samira, Ya Allah..... Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!"

Kan kace me har neighbors É—insu sun fara shiga suna mata murna

Bayan ta samu nutsuwa ta kira Umma, tana É—aga wayar muryarta na rawa

''Umma… result ɗinmu is out Umma... na fito da first class... I'm the best in my department...''

Umma was speechless at first sai kuma ta ce

"Alhamdulillah ya Allah, Allah mun gode maka... Ma Shaa Allah Azrah, Congratulations, In Shaa Allah kuma da wannan first class din zaki gama makarantar"

Zahra data shigo daga waje ta tsinci reply É—in Umma hakan yasa ta fahimci me ke faruwa ta saka ihuu ta ce

''Allah ya saka miki Ya Azrah, wallahi baki taɓa bani kunya ba...  Dan Allah ki bari sunanki ya zaga cikin India kamar yadda ya zaga anan, Ni kuma nayi ta bragging da sunanki" ta kare maganar tana dariya da karfi

Azrah tayi dariya ta ce

"Nagode Zahra, yanzu ki kwantar da hankalin ki gobe ko jibi zan dawo amma sai na tafi scholarship unit tukun zan san yaushe zan dawo, a haka suka gama wayan cike da farin cikin

Samira dake kallonta ta ce

"Khalil fah? Ki kirasa"

Azrah ta yi screenshoting ta tura masa, immediately taga ya buÉ—e dan yana online, next thing kawai taga kiran Khalil ya shigo, ta É—aga ta kai kunne ya ce

"Hey Azrah, wlhi I'm very proud of youuuu, Ma Shaa Allah, Congratulations" Azrah tayi murmushi ta ce

"Thank you" Ji tayi ya katse kiran, ba'a wani É—auki time ba sai ya sake kira tana É—auka ya ce ta fito yana bakin hostel, ta É—auki veil É—inta ta rufe kanta sannan ta fita ta same sa, tun kafin tayi magana ya ce

"Ai ba zan iya magana ta waya bane, kai I'm super proud of you Azrah, I told you, babe! I told you all the strees will pay off!''

Azrah ta É—ago kanta, tana murmushi mai haÉ—e da hawaye, ta ce

''I didn't just make it… I conquered''

Khalil ya gyaɗa kai, yana kallon ta kamar bai taɓa ganinta ba, ya ce 

''Azrah, kin zarce duk wata expectation da nake da ita akan ki, I'm genuinely proud of you''

A cikin hour guda kacal, department É—inta ya cika da congratulatory messages, dama su haka suke saboda yadda suke É—aukan karatu da muhimmanci, Lecturers sun kirata har da wasu da bata tsammanin suna ma kula da ita. Ana yi mata kallon 'model student" Hatta school page ta saka ta a official handle É—insu da rubutu ''Student of the Year'' na IG É—insu

A daren ranar, Azrah ta koma dakinta. Ta kwanta a saman gado, tana kallon ceiling da murmushi yana yawo saman fuskarta, sai kawai ta ce a ranta

''Every tear, every pain, every sleepless night… it was all worth it''

Zata rufe idonta kenan tana gyara kwanciyarta kawai taji murya Samira ta ce

''Bari na faÉ—a miki gaskiya wahalan da kika sha? It has paid off completely''

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.