Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 74 of 79

Episode 76: Truth in the shadows

Bayan Sadeeq ya bar conference room ɗin cikin ɓacin rai, ya wuce kai tsaye zuwa office ɗinsa ya ɗauki car key da sauri, kamar wanda zai tashi sama haka ya fito cikin sauri, parking space ya wuce tun kafin ya karasa ya buɗe motar, bayan ya shiga motar, ya zauna yana kallon steering, zuciyarsa cike da ruɗani,

"Even her number I don't have… not to talk of knowing where she lives" ya furta a hankali, yana jin wani iri bakin ciki a zuciyarsa

Ya dafe kansa da hannayensa, yana sauke numfashi a hankali. Sai kuma ya tada motar, amma tunanin ta ina ma zai fara kawai sai ya kashe ya sauka. Cikin sanyin jiki ya koma office dinsa

Yana shiga ya kalli Sagir na zaune, É—aga kai yayi ya ce

"Man me kake tunani akan wannan case É—in? Is like naga kamar baka so da aka kira sunanta ba?" Sadeeq bai amsa ba ya karasa wajen zamansa ya zauna, Sagir ya ce

"Magana fah nake maka?" Wani dirty look ya basa ya ce

"Toh me zance tunda kun gama yarda?" Sagir ya sake baki ya ce

"Wait... Don't tell me you have feelings for her now? Shiyasa kake son kare ta?" Wani dariyan da bai shirya bane Sadeeq ya fara sai kuma lokaci guda ya koma ainahin Sadeeq dinsa ya ce

"I have feelings for her ka ce???"" Sagir ya ce

"Of course yes, naga sai kare ta kake yi?" Wani dogon tsaki Sadeeq yaja ya ce

"You are not serious, Kai ma kasan bana bin bayan karya, duk tsanar dana ma mutum ba zan taɓa ganin an zalunce sa ba, that's all, Amma idan kana ganin hakan ne, It's Okay duk yadda kace daidai ne" daga haka Sadeeq ya cigaba da abin da yake yi ya bar Sagir baki buɗe...

Azrah na zaune tana kallon Umma da ta sata gaba tace sai ya cinye abinci, Azrah ta marairaice ta ce

"Umma kema kin san bana iya cin abinci fah, ai kuma na sha tea" Umma ta ce

"Tea dama abinci ne? Kuma Ni ban san baki ci ba sai dai acan India kika koyo" Zahra ta ce

"Umma toh ki kyaleta anjima sai ta ci" Azrah ta gyada kai ta ce

"Please Umma" Umma ta ce

"Kin kira kin faÉ—a musu kuwa? Kar suga baki zo ba?" Azrah ta ce

"Bari na kira" ta É—auki wayanta, tunanin babu wanda take da numbern sa a wajen yasa tayi shiru, numbern Sadeeq da Sarah ta turo mata not long ago bata ji zata kira ba, sai kuma kawai ta dake ta kira, yana fara ringing taji zuciyar na bugawa, ji tayi kamar ta kashe amma ya hakura, har ya katse bai É—auka ba, haka ta kara kira shima har ya yanke bai É—auka ba

Tana ajiye kiran zata faÉ—a wa Umma bai dauki wayan ba sai ga wayanta ya fara ringing, tana É—auka taga Smaira ne, dama tana expecting É—inta, Umma ta ce

"Su ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a, Samira ce" Umma ta miƙe ta fita daga ɗakin

Azrah ta kai wayan kunnenta bayan taÉ—aga ta ce

"Ke gani a gidan ku wannan masifaffiyar stepmom É—in naku ta fara balbaleni da masifa, wai kun bar unguwar?" Azrah tayi murmushi ta ce

"Ki tsaya wajen, ga Zahra zata zo É—aukan ki" daga haka ta katse kiran, tun kafin tayi magana Zahra ta ce

"Kila can ta tafi ko?" Azrah ta gyaÉ—a mata kai ta ce

"Yanzu dai ki dauko ta"

Zahra na fita taga motar dake parke ashe ma a kofar gidan nasu yake, ta karasa jikin motar, Samira na mata murmushi, Zahra ta leka ta gaishe da Saif sannan ta mayar da kallonta ga Samira ta ce

"Toh gashi ai naga kina kofar gidan" sauka tayi ta ce

"Wannan shine rashin sanin kuwa, in ba haka ba me ma zai kai Ni can gidan balle stepmom dinku ta min rashin kirki" suna shiga compound Samira ta ce

"Wow, Ma Shaa Allah! Wlh ya fi muku da kuka dawo nan akan can, kai gaskiya na muku murna" Zahra na murmushi ta ce

"Mun gode" tun kafin su karasa idon ta ya faÉ—a kan motar dake parking space ta ce

"SubhanAllah! Don't tell me wannan ne motar Azrah É—in?" Zahra na murmushi ta ce

"Shi ne fah" tuni Samira ta karasa jikin motar tana bi da ido tana kara yaba kyaun motar, a haka suka shiga parlorn

Bayan ta gaishe da Umma ta musu Allah sanya Albarka ta mike suka shiga ciki, Azrah tana murmushi ta ce

"Matar Deen" Samira na dariya ta ce

"Haba Azrah shine baki faÉ—a min abun arziki ba? Da badan nazo kallon motar ba Shikenan Ni ba zan san kun bar gidan can ba" Azrah ta ce

"Toh ai gashi yanzu kin sani" Samira ta ce

"In faÉ—a miki gida kam Ma Shaa Allah, na muku murna wlh kawata" Azrah murmushi kawai tayi, Samira ta ce

"Wait.. ko dai kina cycle É—inki ne naga kina wani abu kamar wata mai laulayi?" tayi maganar tana zare veil É—in jikinta tana haurawa kan gadon

Azrah ta ce "toh ai kema kin san yadda yake galabaitar da Ni" Samira ta ce

"Sannu, shine kike wani yi kamar mai ciki? Toh ai ko Ni ina jin bana yin haka" Azrah bata san sanda ta fashe da dariya ba ta ce

"Samira just tell me kina da ciki ba sai kin kawo wani reference ba" Samira na murmurshi ta ce

"Oho, duk yadda kika É—auka dai dai ne" Azrah ta kura mata ido ta ce

"Ki ce sirrin daya sa kike ta glowing kenan? Ah Ma Shaa Allah, Allah raba lafiya, na kusa zama mother ashe" ta amsa da Amin sai kuma ta ce

"Ke ban baki labari, last week dai mutumin ki sai gashi a gidan mu" Azrah ta taɓe baki sanin halin Sadeeq ɗin da Saif duk ɗaya ne, a ranta ta ce ai dole suyi abota...

Sai can yamma sannan Saif yazo É—aukanta, Azrah ta raka ta bakin gate ta ce

"Toh sai Anjima" Samira ta mata wani kallon ta ce

"Anan zaki tsaya? Kuma ba zaku gaisa da shi bane?" Azrah ta kirkiri murmushin ta ce

"Muje, na É—auka ba zaki so bane" har Azrah suka isa jikin motar Saif bata sake fuska ba, koda zasu gaisa wani wajen take kallo a haka ta koma gida.....

Da yamma bayan duk ma'aikatan sun tafi, Sadeeq ya fito daga office ɗinsa kai tsaye ya nufi wajen masu gadi, suna ganin sa duk suka miƙe suna gaishe sa ya amsa sannan ya ce

"Tambaya nake son muku please" suka amsa da okay sir, ya ce

"Ku tuna, jiya bayan kowa ya tafi, akwai wanda ya dawo cikin building É—in nan ne?"

Daya daga cikin masu gadin ya ce

"Eh ranka ya daÉ—e, Miss Safiyya ce ta dawo, wai ta manta waya" kallonsa Sadeeq yake yi ba kiftawa, sai kuma ya ce

"Kamar da misalin karfe nawa ne?"

"Wajen biyar da da wasu mintinan haka sir" suka amsa

Wani tunani ne ya fado masa a rai, idan bai manta ba jiya da yake cikin Office kafin ya tafi gida kamar yaga Safiyya ta ɗaura story, da sauri ya ciro wayansa ya shiga Whatsapp ya buɗe status ɗin Safiyya yaga da gaske hakan ne, tun around 3:00pm ta yi updating da 'Bad/stressful day' wani murmushi ne ya ƙuɓuce masa ya ce

'Hmm…' sai kuma yana kallon su ya ce "Thank you" daga haka ya wuce

Kallon juna suka yi, sai yanzu suma suka tuna da zuwanta jiya, nan suka fahimci dalilin tambayar nasu da yayi

Yana haurawa sama ya nufi system room, ya kunna CCTV, a hankali ya fara kallo, dai dai time É—in da suka faÉ—a masa ya yi forwarding, har sai daya tabbatar da ganin Safiyya ta shigo building din, ta fita, sannan daga footage na second floor ya kuma ganinta a wajen da leak É—in ya faru.

Murmushi ya sake  "Game over..." ya furta, sai ya miƙe ya fita daga room ɗin.

Da daddare... Sadeeq na zaune gaban mahaifinsa Mr Alhassan fuskan nan nasa baka gane ina ya nufa ya ce

"But Dad, why would you expose her name like that in public? You know Azrah better, Amma hakan zai ɓata mata suna" Mr. Alhassan ya ce

"Dokar Majestic Vaults Ltd kenan muka bi, ba'a ɓoye laifi. Ni kuma na fara yarda ne saboda bata zo aiki ba yau, kuma ai ba a shaidar mutum..." Sadeeq yayi murmushin takaici ya ce

"I've left cash, files, and other valuables on my table countless times" sai yayi shiru yana girgiza kai ya É—aura

"But... She never touched anything that wasn't hers"

Mr. Alhassan ya dan yi shiru yana kallon É—an nasa a hankali ya ce

"Kayi gaskiya... Kawai dai nima rai nane ya ɓaci saboda asarar da zanyi"

"Good night, Sir" Sadeeq ya furta yana murmushi takaici daga haka ta miƙe ta bar parlon

Mahaifiyarsa ta ce

"Alhaji, kar kaji haushin sa akan hakan, kasan shi baya son ganin an zalunci wani ko an ɓata ma wani suna ne" ya gyada mata kai ya ce

"Na fahimta"....

Azrah ta farka da safe har sannan akwai ciwon maran, amma hakan bai hana ta shiryawa da wuri ba, ga wani kyau na musamman data yi.

Ta saka doguwar riga Maroon color, an mata É—inki fited gown ya zauna luf a jikinta, ta É—aura Black open Abaya a kai, ta saka simple gold accessories da low heel shoe, ta É—auki Maroon handbag , ba karamin kyau tayi ba, ta fito daga É—akin ta samu Zahra na breakfast already...

Da ta isa Majestic tun daga bakin gate ta kalli yadda gatekeepers suke kallonta sai tayi alaƙanta hakan da maybe ta fuskanta ya kumbura ne tunda idan cycle ɗinta ya zo haka yake mata, tun daga first floor har zuwa can sama, mutane sai magana kasa-kasa suke idan sun ganta, amma sai ta ɗauke kai daga kowa ganin kamar wata baƙuwa haka suke kallona, tazo wucewa a row ɗin office ɗinta kenan, sai ta haɗu da Miss Safiyya wadda ta sha gabanta tana murmushi mai cike da kallom mugunta, ta ce

"In ba a cika kwano ba, ruwa ba zai ɓullo daga gefe ba… Yau ne kwanon naki zai cika kuma dole zai zube Azrah"

Azrah ta tsai da tafiyarta, zuciyarta na bugawa ta juya tana kallon Safiyya da har ta cigaba da tafiya, ta bi bayanta da kallo, haka kawai taji bata fahimci maganarta ba kuma sai ta samu kanta ta da zargin something isn't normal dan yau kallon na daban ake mata ga kuma Safiyya yanzu

Kawai ta juya ta karasa office, tana shiga Sadeeq ya É—ago kansa for the first time in his life ya kalle ta in a very calm and soft voice, ya ce

"Meyasa jiya baki zo ba?"

Azrah ta tsaya cak, tayi shiru, ta juya bayanta tana kallon ko zata ga wani, ganin babu kowa a bayanta hakan yasa ta fahimci da ita yake yi, hakan yasa a hankali ta ce

"Banda lafiya ne"

Sadeeq ya ce

"To me yasa baki sanar ba?"

Azrah ta dan juya kanta, ta ce

"Na kira ka, baka ɗauka ba ai, Ni kuma banda numbern kowa" kallonta yake ba kiftawa, so yake yaji ina ta samu numbern sa sai kuma ya tuna suna group ɗaya na schl sai ya taɓe baki, ya dan lumshe ido, tunawa jiya da gaske yaga missed call from unknown, yayi shiru, bayan wasu some seconds, sai kuma ya ce

"It's okay"

Ta karasa ta zauna, duk da haka tana jin wani iri a jikinta, kamar ta tambaye sa lafiya? Sai kuma ta karasa ta zauna ta fara aikinta

Kamar karfe 9:30am, ta sauka kasa domin siyan light food, tana hanya wani staff ya kira ta gefe, yana kallon gefe da gefe kamar mara gaskiya ganin babu kowa yayi kasa da murya ya ce

"Please Miss Azrah, ba domin cutarwa ba, amma akwai abu da ya dame ni, wannan zancen da ake yi yanzu... cewa ke kika fitar da bayanan company... ba gaskiya bane ko?"

Azrah lokaci guda taji wani irin jiri yana neman kwasarta har sai data kusan missing balance É—inta ta dafe abu tana kallon sa still trying to process me yake nufi ta ce

"Wani bayanan na fitar? Kamin bayani yadda zan gane please? Aihoo shine dalilin daya sa kowa yake min wani kallon yau?"

Staff É—in ya dan yi shiru bai san bata sani ba, ya ce

"Please Miss ki rufamin asiri kar kice daga baki na kika fara ji, za'a yi calling meeting, dole zaki ji, amma yanzu dai ki taimaka min ki kwantar da hankalin ki, duk yadda mutane suke yaÉ—a maganar sosai jiya, sai dai ni dai na yarda da ke, ba zan taba ganin ke zaki cutar da kamfani ba"

Ta gyada kai cikin sanyin murya ta ce

"Na gode sosai"

Abincin data fasa tsiya kenan ta koma sama, taji zuciyarta na ƙuna kamar tayi kuka, kamar ma ta koma gida gaba ɗaya. Sai dai tunawa da halin da ake ciki, da yadda mutane zasu ɗauki hakan a matsayin hujja, yasa ta cigaba da aiki a system ɗinta wanda bata ma fahimci me take yi bama, kawai ta bari ta dafe kanta. A take kuma ta tuna maganar Miss Safiyya

"Yau ne kwanon naki zai zube" kawai tayi murmushin takaici

karfe goma na safe. Aka ga notices na Emergency Meeting at Conference Room by 10:00AM. Attendance is Mandatory

Kowa ya hallara. Staff duka sun cika dakin taron, wasu suna tunani da fargaba, wasu na tsoron abin da zai fito fili. Azrah ma tana daga cikin masu zama a gefe, da idanun jaa da ke bayyanar da baƙin ciki, sai kuma Sadeeq ya shigo cikin fara'a mai cike da natsuwa, ya zauna a gaba. Kallon farko yayi wa duka staff din, sannan ya fara magana da nutsuwa

"Kafin wani yanke hukunci a kan wani, yana da kyau mu samu cikakken bayani. Jiya na karɓi wani file wanda ya kunshi bayanai masu mahimmanci game da companyn nan, da kuma inda aka tura bayanan sirrin, wanda ya turo min, ya yi hakan da niyyar kare martabar kamfanin, sannan kuma a yanke wa mai laifi hukunci. Ina so ya tashi ya faɗi hujjojin sa

Wani staff mai suna Umar ya tashi tsaye ya ce

"Sir, ni ne na turo maka file É—in jiya, na same shi ne daga system na Azrah. Duk evidence É—in na nuno yadda aka fitar da bayanan clients da kuma wasu confidential projects, harda bayanan sirrin"

Sadeeq ya gyara zama, ya É—an kalli gefe inda Manyan Staff suke zaune harda su Mr Alhassan da PA É—insa, sannan ya ce

"Thank you! Now, Mr. Tanimu, please... you're the Head of Cyber Security! Let's hear from you"

Mr. Tanimu wanda tun farko Sadeeq ya sa shi bincike a ɓoye, ya tashi, ya bude laptop dinsa, ya haɗa projector. Duk dakin ya yi shiru, ya fara bayani cikin harshen da kowa zai fahimta ya ce.....

#Jiddatulkhayr

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.