Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 71 of 79

Episode 72 & 73 The Return of Azrah

Gida ne mai ciki da parlor sai kitchen wanda ke É—auke da cabinet, sai toilet na zamani, dake kitchen É—in ne a fakon ya sa suka fara tsaya dubawa, sabbin warmers guda hudu, É—an karamin gas, sai robibin aiki, da wasu kayan aikin da zasu bukata a kitchen É—in, Umma ta ce

"Ayyah Azrah kudin ba zasu kare ba?" Azrah tayi dariya ta ce

"Duk yawansu kuma sai su kare yanzu?"  Suna shiga parlor dai ga center carpet da ɗan deep freezer sai curtains, Zahra dai banda murmushi babu abinda take yi, musamman ganin gidan tiles ne, ɗayan dakin suka shiga nan

Azrah ta ce "wannan naki ne Umma, É—ayan kuma na Ni da Zahra ne, a weekend za'a kawo gado da wasu abubuwan" Zahra tayi hugging É—inta ta ce

"Alhamdulillah, Allah mun gode maka" kafin nan duk kayansu da yara suka taya su shigowa da su wanda ke compound suka fara shigowa da su ciki, kafin dare duk sun gama aiki.

Mama tayi tagumi ta ce

"Ohh toh ina suka shiga kenan?" Siyama ta ce

"Ke Mama ya akayi kika san cewa basu nan?" Ta ce

"Ki kalli kofar nasu mana, rabi a buÉ—e yake kuma babu labule, na leka kuwa naga wayam, dama babu wani abun arzikin a dakin nasu ai" Habibah ta ce

"Toh ina suka tafi?" Mama tace

"Ki tambaye Ni na tambaye wa?, naga kusan tare muka dawo gidan"

Bappah dake ɗakinsa sai juyi yake akan gadonsa, tun safe ya rasa meke masa daɗi, haka kawai yake share hawayen dake zuba masa wanda shi kansa bai san dalili ba, ya miƙe ya zauna yana dafe da kansa, buɗe idanunsa da suka yi ja yayi, ya kurawa kofar ɗakin ido yana jin maganganun su Mama dake sakar gidan, a hankali ya miƙe ya isa zuwa kofar ya saka mata sakata yadda ko mutum ya tura ta waje ba zai buɗu ba, ya koma ya zauna sai kuma ya kwanta yana kara jin abin da yake ji na jikinsa na tsananta....

Kafin Isha'i kaff layin unguwar nasu ya gama karaɗewa da cewa su Azrah ne ke wannan gidan, dama karamar unguwa ce hakan yasa duk maganar ya bazu, mutanen da suke shiri har sun fara shigowa suna musu murna, ɗayan ɓangaren kuma banda zagin Mama da Allah wadaranta ba abinda suke faɗi, dan duk gidan da suke shiri da su Umma haka suka dinga Maganar ta da kuma mugayen halayyarta...

Mama dake zaune suna fantayawa da Yaranta sai ga Maman Asabe kamar an jefo ta haka ta faÉ—o musu gida, Mama na kallon ta ta ce

"Lafiya Maman Asabe da Daddaren nan?"

Maman Asabe ta samu waje ta zauna ta ce

"Mu fah dama mun saba da fitar dare kawai bana zuwa miki ne, wannan halin tun na kauye ne ya bi mu har nan" Mama ta ce

"E, ko" Mama Asabe ta É—an kalli kofar É—akin Bappah sai kuma tayi kasa da muryanta ta ce

"Ke Nikam me naji yake yawo a unguwar nanene?" Mama ta ce

"Kar de kinji labarin sun gudu ne?" Maman Asabe ta wani kalle ta ta ce

"Kamar ya kuma? Bayan ga gidan da suka koma kuma, shine ai nazo naji ta bakin ki" Mama ta zaro ido ta ce

"Ni fah ban san maganar ba, kawai dawowa muka yi naga bata nan, dama kin san inda ta koma ne?"

Maman Asabe dai ta hangame baki tana kallonta Mama ta ce

"Haba Maman Abdul, gaki ga kishiyarki gida na kallon juna shine ai nazo jin ba'a si" Mama ta wangale idanu tana kallon Maman Asabe kamar idon zasu fado kasa ta ce

"A'a.. ban.. ban gane gida na kallon gida ba?" Maman Asabe ta ce

"Gidan da 'yan Borno suka ta shi nan suka koma fah!" Mama tayi saurin dafe bishiyar wajen jin kamar jiri ne ke son É—ibarta ta ce

"Wai wannan gidan mai tayils kike magana? Da pilawa ta waje dai?" Mama Asabe ta ce

"Kwarai kuwa, shine dai gidan da suka koma, magana kuma har ya gama karaɗa unguwar nan, shine Nima na zo jin ya aka yi kuma?" Mama dai har sannan bata gama fita a mugun shock da ta shiga ba, da sauri tayi wajen kofar, ta tura kofar gidan nasu don sake tabbatar gidan 'yan Borno ne ke kallon nasu, ai kuwa ta kalli gate ɗin gidan na kallon kofar nasu, ta juyo tana haɗa zufa, ta zauna kan tabarma, Siyama ta miƙe ta fita sai kuma ta dawo ta ce

"Tabbas Umma gidan ne suka koma, kinsan ya akayi na gane?" Maman Asabe ta ce

"Yaya?" Ta ce

"Ai gidan ba'a kunna wutan sakar gidan saboda ba kowa amma yau wutan a kunne yake, sannan kuma jikin gidan ga kwalaye da alama ma ina ga har Tv suke da shi" Mama ta ce

"Dan ubanki rufe min wannan mugun bakin naki, wani irin Tv kuma? Ai sai dai su kalla a lahira ba nan ba" sai kuma ta kalli Maman Asabe ta ce

"Ina ga kuwa Mazan da Azrah ke bi su suka kama musu hayar gidan, ai kuwa idan haka ne ba zan damu ba, su suka sani" a ranta ta fara gyaÉ—a kai cike da bawa kanta cewa aikinta ya fara ci, kila har Azrah ta fara yawo kamar yadda ta bukaci ayi mata asirin, wani dariya ta yi tunawa da Dada har sannan bata ga kafarta ba hakan ya tabbatar mata duk cikin aikin ne, sauke ajiyar zuciya ta yi, Mama Asabe ta mike ta ce

"Toh Nikam sai da safe" daga haka ta fita, Siyama ta fashe da kuka ta ce

"Shikenan Mama duk sanda aka musu Mugunta sai ya koma Alkhairi, ki kalla gidan da suka koma wannan ai mugun ci gaba ne" Habibah kam na bakin baranda tama gagara cewa komai, Mama ta ce

"Dama fah mutumin ya ce zata fara yawo ne, kuma ina ga Mazan da ta fara bine suka biyo ta kuma suka kama musu haya" Siyama ta sake fashewa da kuka ta ce

"Toh ko muma ai namu Mazan bama su kuÉ—i bane, amma ace dole ko Mazan banzan ne ma sai masu kuÉ—i?" Habibah ta ce

"Toh sannu ko?" Siyama ta kalle ta sai kuma tayi saurin share hawayenta, Mama dake kallonta ta ce

"Toh ai naku na arziki ne ba Mazan banza bane" ta gyaÉ—a mata kai kawai amma tana jin kishin Azrah, sai kuma ta ce

"Kila ma wancan saurayin nata É—an kasan waje ne ko?" Mama ta zaro ido tunawa da Khalil da tayi sai kuma ta ce

"A'a ba shi bane, dan an raba su da wannan, an shafe ta a kwakwalwarsa ma" daga haka Siyama ta miƙe zuwa ciki ba tare data ko sake bi ta kan Mama ba.

Suna zaune suna cin abincin da Azrah ta taho musu da shi, Umma na kallon yaran nata ta ce

"Bana so ko da wasa ace wani abun zai haÉ—a ku da Mama ko yaranta wani ya ce zai tanka, ko a hanya ne ta zage ku bana kaunar ku tanka, sannan Zahra ke baki jin magana kwatakwata ba'a isa da ke ba, toh this should be the last time da zan miki warning akan su" Zahra ta ce

"Yanzu kamma aina zasu ganmu Umma? Ai sai dai hange daga nesa" Umma ta girgiza kai dan lamarin Zahra na bata tsoro.

Miƙewa Azrah tayi tana kallon su ta ce

"Ni kam sai da safe" Umma ma ta mike ta ce

"Yama ka mata ace mun kwanta yanzu, tunda gobe ina zaku je wajen cika Jamb É—in Zahran ko?" Azrah ta ce

"In shaa Allah" daga haka suka yi sallama. Azrah na zaune bakin katifarta tana replying message É—in Khalil wanda ya wuni kira bata É—auka ba saboda struggling, Zahra ta zauna gefenta ta ce

"Sannu Yaya kinyi kokari, amma gobe zaki tsiyamin wayan? Naga kin ce zanyi registration É—in Jamb" Azrah na kallonta ta ce

"Mantawa yau É—in ma nayi, da na zo miki da shi amma Kinga ai ba wannan nutsuwar" Zahra na murna ta ce

"Amma kuma ai zan iya tafiya Ni kaÉ—ai ko kuma na bi ta gidansu Layla saboda kar kiyi missing wajen aiki" Azrah taji gabanta ya fadi tana kallon Zahra sai kuma a hankali ta ce

"Ai na bar wannan aikin Zahra" Zahra ta fara salati, Azrah ta ce

"Dan Allah kada ki faÉ—awa Umma for now idan ba haka ba zata hana mu gyaran gidan nan yanda ya kamata, in shaa Allah zan nema wani wajen, ko service dina na gama a can ne Kinga kafin na gama kuma sai na fara neman aiki idan ban samu ba ko Honorable zanma magana" Zahra ta yi shiru ta ce amma meya faru?", Azrah tayi mata narrating komai ta ce

"Toh Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" daga haka suka kwanta.

A bangaren Mr. Alhassan kuma, yadda kasan yayi disowning É—in Sadeeq ne da Sagir, ko a masallaci da suka haÉ—u a Magrib haka ya share su kamar bai san su ba, haka da suka yi Isha'i ma wanda yanzu hakan kuma ya fara damun Sadeeq, shiga parlon su yayi da sallama, ya karasa ciki kansa a kasa bayan ya gaisa da mahaifiyarsa yana kallon Mahaifin nasa ya ce

"Barka da warhaka, sir" ba tare da ya Kallesa ba ya amsa, Sadeeq ya yi ta zaune yana jiran jin mai Babansa zai ce masa amma yaji shiru, shi wannan silent ɗin Mahaifinsa ne baya so, ganin sun kusan shafa 30mins bai ce masa komai ba sai ma news daya maida hankali yana kallo kawai ya miƙe ya ce

"Sai da safe, sir" still ba tare da ya kalle sa ba ya ce

"Allah tashe mu lafiya" daga haka ya nufi kofa ya fita jiki ba kwari..

Yau tunda suka tashi suka bar gida ita da Zahra basu dawo ba, wajen sha É—aya saura yayi parking a kofar gidan nasu, wanda ke driving É—in ya sauka yana kallon wani yaro ya kira sa, yaron na zuwa ya ce

"Gani" ya ce

"Ka shiga gidan nan ka ce ana sallama da Azrah a waje" yaron ya gyaÉ—a kai ya tafi da gudu ya shiga gidansu Azrah, Mama dake aiki a sakar gidan ta É—ago jin sallamar yaron ta ce

"Ya ne?" Ya ce

"Wani ne ke sallama da azrah a waje" Mama ta ajiye abin hannunta ta ce

"Wani kuma kamar Yaya?" Ya ce

"Eh Nima ban san su ba, a mota suka zo" Mama ta zaro ido ta ce

"A mota kuma?" Ya ce

"Eh, a mota suka zo" Mama ta ce

"Na shiga uku Ni Uwani" yaron na kallon ta sai kuma ya ce

"Amma mutanen fah Babba sosai ne" kamar ma polis ne saboda sun sa bakin wando da rigar sama shima baki" sai kuma ta sauke ajiyar zuciya bayan wani tunani ya fado mata a rai ta ce

"Je ka ce musu sun bar unguwar nan" yaron ya juya ya fita ya koma gun mutanen ya ce

"Ance wai na ce maka sun bar unguwar nan"  da sauri suka kalli juna sai kuma suka kalli yaron, dayan dake zaune ya ce

"Inji wa kenan?" Ya ce

"Kishiyar Mamanta" ya ce

"Ko zaka ce musu zan iya shigowa?" Yaron ya rufe bakinsa da hannu bibbiyu ya ce

"Kaiii, matar fah tana da masifa, yadda tace min basu nan idan na koma zata zageni ne koma ta dake Ni" mutumin ya miƙa masa dubu daya ya ce

"Mun gode ko?" Ya karɓa yana murna da gudu ya kama hanyar gidan su

Mr. Alhassan yana kallon PA É—insa ya ce

"Kaji kuma abin daya ce, amma haka kawai sai ace sun tashi? Ina suka koma kuma kenan?" PA ya numfasa ya ce

"Dole tambaya zamu yi, Sir"

Wani keke Napep ne yazo yayi parking a gabansu, Sai ga Azrah ta sauka, Zahra ta biyo bayanta, mai keken ya sauka ya fara sauke musu kayansu dake booth É—in Napep É—in, kana kallonsu kasan ba karamin gajiya suka yi ba, Azrah ta buÉ—e handbag É—inta ta Ciro kuÉ—i ta mika wa mai Keken

Mr Alhassan zai yi magana sai PA ya rigasa ya ce

"Sir, ai sune a gabanmu" Mr Alhassan ya ce

"Ko zaka musu magana kafin nan?" Daga haka ya sauka, Azrah ta kira yaran dake wasa a wajan wanda basu zuwa makaranta ta ce

"Kalli, ku kama ku shigar mana" Zahra ta miƙa mata file ɗin hannunta tana kallon ta , ta ce

"Ke Yaya ki shiga min da file É—ina Ni kuma zan karasa shiga da sauran kayan" Azrah ta ce

"Toh, sannun Babbah" Zahra na dariya ta ce

"Wai taimako ne" duk juyawa suka yi jin ana musu Sallama, Azrah taji gabanta ya faɗi ganin PA ne, sai kuma ta kalli Zahra ta ce

"Zahra ki shigar da kayan ina zuwa, ki sa yaran ma su taimaka miki" Zahra ta gaishe sa sannan ta fara kwasan kayan zuwa cikin gidan nasu, a hankali Azrah ta gaishe sa tana wasa da fingers É—inta, shi kansa ma kunyarta ya ke ji kawai daurewa ne, ya ce

"Miss Azrah ka Mr. Alhassan yana son magana da ke, ko zaki iya karasa wa?" Azrah ta juya da sauri jin wanda ya ambata sai kuma ta kalle sa cike da mamaki, dan gani take kamar mafarki ne, kai kawai ta gÆ´aÉ—a masa sannan ta fara tafiya a hankali zuwa wajen motar, tana karasa wajen, ya buÉ—e kofar motar, Azrah taki kallonsa tana kallon kasa ta ce

"Daddy ina wuni" ya ce

"Miss Azrah kina lafiya?" Ta gyaÉ—a masa kai, ya ce

"Me yasa yau da jiya baki je aiki ba? Kuma shekaran jiya ma baki jira aka tashi ba kika taho abin ki?" Azrah ta sauke kanta ƙasa ta gagara cewa komai, ya ce

"Kin bar aiki da mu ko?" Ta É—an kalle sa amma ta kasa basa amsa, ya ce

"Amma ina son na tambaye ki, Ni na dauke ki aiki ko Sadeeq?" A hankali ta ce

"Kai ne" ya ce

"Toh mayasa duk abin da yayi miki baki yi reporting dinsa ba kawai kika yanke hukunci kuma ba tare da wani consent dina ba?" A hankali ta ce

"I'm sorry, Sir" shiru yayi bai ce mata komai ba, ita kuma jin shirun yayi yawa yasa ta kalle sa taga ita yake kallon, a hankali ya ce

"Ki dawo aiki gobe idan na isa da ke a matsayin Mahaifi" ta gyada masa kai ta ce

"In shaa Allah " ya ce

"Good! Ina kuma son duk wani abu da zai faru tsakanin ki da MD just let me know ni zan yi tackling issue É—in In Shaa Allah" ta ce

"Nagode" ya ce

"Toh Allah miki Albarka, ki gaida iyayenki" ta gyada masa kai, daga haka suka yi sallama ta wuce ciki

Tana shiga Zahra tayi saurin cewa "har ki tsiya katin?" Azrah ta fahimci Umma ta tambaye tana ina ne shine Zahra tace hakan, murmushi ta yi ta ce

"Eh na tsiya" Umma ta ce

"Azrah wannan kashe kuÉ—in bai yi yawa ba? Kar fa kice komai sai kin siya, nikam daga haka ya isa" Azrah ta zauna tace

"Umma kin ga Allah ya taimake mu muna zuwa aka fara mata, ta nuna miki Jamb slip É—in?" Umma ta ce

"Eh Nagani, medicine É—in ta cika, Toh Allah bata sa'a" Azrah ta ce

"Amin Amin" Umma ta ce

"Amma nayi faÉ—a gaskiya, ina laifin Umaru Musa Yar'adua amma kawai sai ki kama ki saka mata Alkalam?"

Azrah tayi murmushi ta ce

"Umma kawai addu'a zaki yi Allah ya kawo wasu hanyoyin, kuma ai kuÉ—in dake account dina In Shaa Allah zata gama karatu cikin kwanciyar hankali ba zata yi lacking wani abu ba" Zahra ta rungumeta tana jin hawaye na taruwa mata, wai yau ita ce zata yi Uni kuma ace private, tunawa da hakan ya fashe da kuka...

Umma ta miƙe ita da Yaranta suka sake gyara gidan tass, wunin ranan haka dai 'yan unguwa suka dinga tururuwar shigowa taya su murna wasu ma gulma ce ke kawo su, amma kowa sai Barka yake musu da suka fita ƙangin Mama...

Can Azrah da Zahra suna ciki while Umma na tare da bakinta a nan parlor, Zahra bayan ta gama jin abin da Azrah ta faÉ—a mata ta ce

"Ai tunda mahaifinsa da kansa ya zo har gida yayi honoring É—inki, kawai ki koma aikin Wannan ma ai wani dama ce wanda zaki bakanta masa, hakan zai basa haushi kuma idan kin goma ko da wasa karya ga murmushinki" Azrah ta ce

"Yadda kika san na tsane Saif haka shima, dan ina jin tsana É—aya na musu"....

The following day..

MD Sadeeq ya dinga kallon cikin Office É—in nasa wanda an sake creating wani Office a can gefe, ga Office chair da dai duk wani abu da ma'ailaci zai bukata haka aka yi a edge É—in office É—in, infact yadda nasa yake haka na wannan dinma yake, mamaki ya fara toh wani MD za'a É—auka ko me? Idan ba haka ba baiga amfanin a cikin Office dinsa ayi creating wannan wajen ba, sauke ajiyar zuciya yayi, Sagir ne ya shigo office É—in yana kallonsa ya ce

"Yana ganka haka kuma? Sadeeq ya nuna matsa wajen da hannun sa, Sagir ya kalli wajen sai kuma ya ce

"Ku biyu ne a office É—in yanzu kenan?" Sadeeq ya buÉ—e masa hannu alamar bai sani ba shima daga haka ya karasa ya je ya zauna, Sagir ya dauki abin da zai É—auka ya fita shima yana mamaki..

Tun da ta iso bakin gate, masu gate suke gaishe da ladabi suna murmushi, alamar dai sunyi murna da zuwanta ne, a haka ta shiga duk wani cleaners da kananun ma'aikata haka suka dinga gaishe ta ita kam kunyar yadda suke gaishe ta take yi, tana hawan 2nd floor ta haÉ—u da Oga Mahmoud, da ladabi ta ce

"Ina kwana, Sir" ɓata rai yayi ya ce

"Kawai sai ki wani tafi, haka ake yi?" Ta ce

"I'm sorry sir" murmushi ya mata ya ce

"It's Okay toh" daga haka yayi gaba, ta wuce office É—in PA tana buÉ—e wa ga kuma Miss Safiyya tana kokarin fitowa, kishi da kyashi clearly written all over her face, Azrah ma ta tamke fuska ganin ba zata bata hanya ba kuma dama tun a gida tayi alkawarin babu wanda zata ragar masa idan zai kawo mata wargi, ta ce

"Idan ban manta ba kamar nan hanya ce ko?" Sake baki Miss Safiyya tayi tana kallon Azrah, Azrah ta raɓa ta gefenta ta shige cikin Office ɗin ba tare da wani izini ba, ganin PA ya fito a main Office ɗin Mr Alhassan ya sa ta gaishe sa ya amsa ta ce

"Sir, amma Daddy na ciki?" Ya ce "Yes, barin masa magana" daga haka ya shige ciki"

Miss Safiyya tayi wani irin humming ta sauka da sauri a ranta tana shirya abin da zata yi wanda zai sa a Kore Azrah, fitowa yayi yace

"Zaki iya shiga" shiga tayi kanta a kasa, ya É—ago yana kallonta da murmushi a fuskan sa ya ce

"Welcome on board Miss" ta ce

"Thank you, Sir " ya miƙe ya ce

"You can follow me, zan nuna miki office É—in ki" ta ce

"Okay" daga haka ta juya ta bisa a baya, Office É—in MD ya shiga, Sadeeq ya É—aga kai ganin mahaifin nasa ya ce

"Sir, kana son wani abu ne?" Kai ya girgiza masa yana jiran Azrah ta shigo, sai gata ta shigo da sallama, da sauri Sadeeq ya Kallesa sai kuma ya sake kallon ta, kamar ya kurma ihuu haka yake ji, Mr Alhassan ya ce

"So, Miss wancan ne spot É—inki, a matsayin PA É—in sa, sannan idan akwai abin da bai gane ba zaki iya taimaka masa" murmushi ne yayi escape a fuskanta ta ce

"Okay sir, zan taimaka masa ai ko sanda muke degree tare da shi naka yi duk waɗannan abubuwan su joint hand din nan, group din mu ɗaya da shi kuma nakanyi guiding ɗinsu, at the end group ɗinmu ne ke winning" Idan akwai abun da ya taɓa ɓata wa Sadeeq rai kuma abun kuka toh shine wannan, Mr Alhassan na dariya ya ce

"Wait.. Tare kuka yi degree" ta ce

"Of course, yes sir! Tare muka yi" ya ce

"Very good, Shiyasa dama ai nace nasan zaki taimaka masa, though kina aiki ne a karkashin sa amma definitely zaki saka sa a hanya, yadda ake yi da abokan saka hannun jari ma duk sai ki koya masa" itama tana dariya ta ce

"Toh shikenan, In Shaa Allah zan koya masa" ya ce

"Very good" daga haka ya juya ya fita, ta ɗan kalli direction ɗinsa wani kallo ɗaya zuba mata har sai data tsorata amma ta dake ta zauna a office chair ɗinta, sai kuma ta miƙe ta ɗauki remove ta rage Acn office ɗin, shi dai Sadeeq ya gama koma wa kamar wani mutum mutumi ne, zuciyar sa kuwa banda tafarfasa babu abin da yake yi...

Miss Safiyya tana share hawayenta ta ce

"Shine kuma har zata sake zuwa? Mu dai mun zama useless a Company, ace har ta fi mu matsayi duk da ihun da tayi wa MD kuma shine za'a barta a Company, kalli any small thing yadda MD ke ihu wa mutane yana sallamar su a aiki duk taka tsantsan muke dashi amma tayi musayar baki da shi shine zasu dawo da ita?" Ita dai Miss Merry ko da wasa bata ma kalle inda take ba, dan yanzu tama fara tsoron Miss Safiyya É—in

#Jiddatulkayr writes

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.