Best Hausa Novels

Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx

Chapter 49 of 52

Chapter 151

Update 

Unedited page

Daga nesa daddy ya hango baban su amra dake tsaye yana kallon daddy, kallonshi daddy yayi da kyau kafin ya zabura ya mike zaune, shida baya Tashi da kanshi saidai a daga shi saiga shi ya zauna jiki na bari ya fara furta “wa inaahu suleimanu wa innahu….ku kuke Ganin mu bamu muke Ganin ku ba, na shiga uku kareema na fara gane gane, innalillahi wa inna ilaihi rajiuna kumin agaji, kodai na mutu ne nima”

Kareema dai dake zaune a gefenshi itama wata irin naquda ce ta kusan zuwan mata daga nan zaune don Harda futsarin zaune tayi bata ma tasan yi ba, daman zanin dake daure a jikinta ba wani zanin arziki bane, hankali atashe take kallonsu daya bayan daya, tabbas idanunta sun hango mata badaru, badaru dai, gefenshi kuwa wasu mutane ne da bata gane su bama kwata kwata don itama badaru ta hango, khady ce Tayi wulli da kullin nata tace “amra?????? Salima kune??”

Yanda take kallonsu ta zaro idanu cike da mamaki haka suma suke kallonsu kamar sunga tv dukda hancinsu a toshe yake, asma ce ta fito daga  cikin uwar dakan su da ledar arziki ma babu da yar sandarta tana dogarawa, 

Kiff kiff da idanu kareema tayi tana kallon inda khady ke nuni da ikirarin sunan su amra, gabanta ne ya bada dam tana kokarin mikewa zaune tana kakkbe zanin nata jiki na bari don tabbatar da abunda idanunta ke gane mata, amra dai hannun salima ta kankanme itama hannun nata ta rike tana kallonsu su duka,

Lokaci guda kareema ta burkice ta Dora hannu aka “na shiga uku ni kareema, Wallahi su ne, kadai wata masifar kuka kwaso yayannan kuka dawo nan don wallahil azeem babu abunda zaku tsinta anan, wannan kuma daga Ina kuka kwaso shi kamar ubanku?”

“Kinga sunyi maki kama da matsiyata ne?” Ammah ta fada tana murmushi ta karaso inda suke, “babu abunda suke tafe dashi sai alkhairi,wannan kuma mahaifinsu ne dai da kuke tantanma akanshi bai mutu ba yana nan da ranshi”

“Karya ne Wallahi karya ne, akan idanuna motar ta kone karya ne Wallahi,“ daddy ya fada yana rawar jiki kamar mahaukaci 

“Ka daina rantse wa Mustapha, ban mutu ba saboda lokaci na baiyi ba,”

“Wallahi fatalwa ne, akan idona nasa a kashe shi, karya ne “

Yanda yake magana ma kwata kwata ba a cikin hayyacinshi yake ba.

Kallon inda kareema ammah tayi tace “ko zaki bamu wajen zama sai muyi magana?”

Katseta labaran yayi yace “hajiya karna yo hanzarin katse maki magana, ammah ba zama mukazo ba, babu wata magana data rage da zamuyi, mu wuce sasan inna kawai”

Sai alokacin kareema ta tabbatar da gaske ne don haka ta fara kokarin dukawa tace “dan Allah ku tsaya hajiya,”

Kallonshi ammah tayi tace “baban amra kayi hakuri mu zauna ayi magana”

Runtse idanu kawai labaran yayi baya son jayayya da ammah don haka yayi shuru kawai, kallon inda asmaa ke tsaye da sandarta kareema tayi tace “ke chogala jeki dauko tabarma a uwar daka”

“Wace tabarmar zata dauko? Daman Akwai wata tabarmar ne bayan wannan wadda kuke zaune?” Khady ta fada babu alamu respect kwata kwata a kalamanta, 

A burkice karima tace 

“Auu laa haka ne, kuyi hakuri bari mu Tashi sai ku zauna akan tabarmar, 

Amar ne yayi saurin katsesu don bayajin zai bari amra ta Kara taku daya  da yaranshi zuwa wajen nan, gaba daya Kuda ya gama bade wajen ga wani ruwan yauqi na ciwo dake fita daga jikin daddy,”kuyi zamanku anan babu damuwa zamu tsaya daga nan”

Ya karashe ranshi abace don gaba daya haushinsu yake ji idan ya tuna da sune suka wulaqanta mashi matar shi, yanxu ko ba a fada masu ba su san cewa rayuwa ta juya masu baya babu arziki babu takamar balle ayi wulaqancin, daman ance inka Shuka alkairi zakaga alkairi inka shuka sharri kuwa shi zaka girba bayan wannan ma ga hakki, hakkima ba daya ba hakkin mutane Har hudu, na marayu dana ubansu da sukayi kokarin kashewa.

Saukar dakai kasa kareema tayi don gaba manta yanxu basuda matsayin da zasu wani saukar da baki a waje mai kyau, don koda Amar yace mata basai sun zauna ba tasan abunda hakan ke nufi, 

Ammah dai kasa cewa komai tayi don mai duka yayi magana batada jayyayya don itama kanta bazata so jikokinta suzo wajen ba, daga nan tsaye ta soma magana “nasan kinsan waennan ko?”

“Eh na sansu, yayana ne don yayan suke a wajen kanin mijina  gashi nan” ta karashe tana nuni da daddy, 

Wata irin bazawarar dariya khady tayi tace “chap ikon Allah, yau kikasan yayanki ne ? Kai mummy jin shiga uku,hmm”

Wani irin kallon Amar ya wurga mata don ta juyo tana kallonshi aranta tana yaba kyawun d a yake dashi Har tana jin ina yace yana sonta.

“To tabbas wannan mahaifinsu ne kuma bai rasu ba yana nan raye,” ammah ta fada

“Toh ya akayi hakan ta faru? Hajiya Kar nayi katsalandan menene alaqarku da su?”

Nuni ammah tayi mata da amra tace “wannan diyata ce matar dana Muhammad kuma marikin qannenta”

Ammah ta fada tana nuni dasu, hannu aka kareema ta daura tace “na shiga uku ni kareema, don Allah ku yafe min yayan nan ashe zubar daku danasa ayi sautin rayuwa ya kawo maku”

Yanda kareema ke magana ba karamin qular da Amar Yayi ba harma da ammah, don kwata kwata babu wani sign of nadama a tattare da ita saima wasu surutai da takeyi marasa kan gado,

“Hajiya dan Allah kiyi min afuwa Zan wuce ciki bazan iya tsayuwa anan ba” labaran ya fada yana kaiwa nan ya nufi hanyar bangaren innarsa “baba badaru Ay inna ta rasu” asma ta fada tana daga tsaye don Har lokacin basu yarda shi mutun bane kallon kamar fatalwa suke yi mashi, chak ya tsaya ya juyo yana kallonta kafin ya runtse idanunshi, amra ce Tayi karfin halin cewa “inna ta rasu? Yaushe ta rasu?” Ta karashe hawaye na yawo akan fuskanta,

“Tun watan bara lokacin da muka dawo nan da zama ma bamu taddata ba” asma ta amsa mata fuskanta gwanin ban tausayi,

Gaba daya wajen dauka yayi da innalillahi wa inna ilaihi rajiun, juyowa babansu amra yayi ya nufi hanyar futa nan take daddy ya tsaidashi “Wai da gaske ne daman baka mutu ba? Wannan wace irin masifa ce?na shiga uku ni mustapha,”

Juyowa labaran yayi rai abace yace “Ada banso nayi magana ba saidai yanxu bazan iya jurewa ba, allah ya isa tsakanina dakai, Ka cuceni Ka cuci yayana na barka da allah, ahaka ma kaga yanda karshen Ka ya kasance”

Labaran na kaiwa nan ya juya ya fuce daddy na faman kiranshi “laa da gaske bai mutuba, kai badaru baka mutu ba ashe”

Yanda yake magana da yanda zugin azabar jinyar da yake fama dashi ke rudashi yasa yake sambatu baima san yanayi ba, labaran na fuce wa Amar yace “muje ko ammah”

Khady ce Tayi saurin cewa “anty amra don Allah ku tafi dani Wallahi bama cin abuncin kirki, kullum wahala muke sha kinga wannan ma gwanjo ne nake saidawa nake dan rufa mana asiri Wallahi dani suka dogara ni kadaice gatansu saboda su bakiga yanda na koma ba”

Kallon yanda take abun tausayi salima tayi harta asma ma saida tayi mamakin furucin nata, aranta tace “munafuka annamimiya Wallahi Saina tona ki”

Kareema ma mamakin khady take da yanda take wani kwallar makirci, 

   “karya take Wallahi, muguwa azzaluma, babu abunda takeyi mana a gidannnan saidai taje ta sayar da gwanjonta ta dawo da ledar tsire ta cinye abunta ita kadai, munfi shekara bamu ci nama ba” asma ta fada tana kallon khady tana hararta, dizguwa dai khady ta dizgu don dama lankwasar da kai datayi tayishi ne don ta samu ta gudu tabar wannan jarababbiyar rayuwar ko zata samu wannan kyakyawan yace yana sonta.

Wani irin ashariya khady ta kwararo mata wanda yasa salima doka auziya tace “chapp Allah mai iko, haka kuka koma? lallai Allah baya barci,”

Kallonta kareema tayi har lokacin tana kan gwiwarta “don Allah ku yafe mana aisha, don Allah ku tausaya mana”

“Dame zamu taimaka mukun? Ay Wallahi bazan taba yafe maku abunda kukayi mana ba,” salima ta karashe rai abace 

Kallonta amra tayi tace “mey haka salima? Ina kika bar hankalinki?”

Kuka ne ya kubce mata tace “Wallahi bazan taba yafe wa adda, bakisan irin wahalar da suka bamu ba, ko ahaka aka barki Wallahi tallahi alhakinmu ke binko” tana kaiwa nan ta fuce tabi bayan babanta ya rage daga ammah sai Amar da amra.

“Hajiya don Allah ki taimaka ki taya mu basu hkuri su yafe mana,” wani irin tausayinshi ne ya durar mata, gaba dayansu kamar wasu mahaukata, amra ma dai jikinta ya gama yin sanyi sosai, tana shirin takawa inda suke Amar ya matso ammah tace “Aisha bashi yaran ya su jira mu a waje”

Karban su Hamid Amar yayi ya fuce daga gidan ya rage daga ammah sai amra, daddy dai gaba daya ya zauce don surutai kawai yakeyi kamar tababbe.

Amra ce ta karaso inda Haj kareema take ta dagota da hannunta ba tare da ta kyamaceta ba, Haj kareema na Ganin haka ta fara hawaye nadama, takaici, da dana sani, “dan Allah ku yafe mana aisha, Wallahi Wallahi alhakinku ke  binmu, kinga gaba daya yarnnan su tagaiyyara, bakuda cin yau balle na gobe,ga babansu nan kullum a kwance baya….”

Saurin katseta khady tayi tace “Kun manta baki fada mata cikin shegen jikinki ba”

Saurin runtse ido amra tayi ammah dai girgiza kai kawai tayi, wannan wace irin masifa ce ta aika masu haka,

“Kema Ay iskancin kikayi Har kika samu aids,” asma ta fada tana kallonta, 

Khady dai ji tayi kamar ta makure asma don takaici, babu kunya ta cigaba da taunar cingum dinta ta dauki gwanjonta ta kalli inda asma take tace “ke ay ba iskancin kukaje yi club ba Har kika shawu keda dan iskan saurayinki kukayi accident Har kika rasa kafa daya, futsararriya”

Tana kaiwa nan ta fuce daga gidan, amra dai kasa cewa tayi komai haka zalika ammah ma don bankadar da sukeyi ma junansu Har taso tayi yawa.

 Khady na fucewa asma ta karaso inda amra ke tsaye tare da Haj kareema Duk gaba Dayan su babu abunda suke sai kuka,

Kallon asma amra tayi tana hawaye tace “haba asma meysa kika lalata rayuwarki?”

Sauke kanta kasa tayi ta kasa cewa komai, ammah ce Tayi breaking silence din nasu tace , “baku da yayyu ne?”

“Muna dasu, ya Wahab yana prison, shi kuka ya Ibrahim Har yanxu ba a san inda yake ba, ya muhammd kuma yau shekara daya kenan namiji daga gareshi ba, daman shike tura mana kudin da zamu saya abunci dana makarantar su jalal”

Shuru ammah tayi tana dan nazari kafin tace “toh Allah ya rufa asiri, shi maisa baku kaishi asibiti ba?”

Ta karashe tana nuni da daddy daya kafe amra da idanu yana sambatu, 

Hajiya kareema ce ta iya cewa “hajiya babu kudin zuwa asibitin ne,”

Juyowa amra tayi ta kalli ammah ta dan girgiza mata kai, Nunfasawa ammah tayi tace “Allah ya rufa asiri” 

Bude handbag ammah tayi ta zaro bundle din dubu gida biyu ta miqa ma amra tana miqa mata tayi mata murmushi ta kalli kareema tace “Toh sai anjima ku”

Tana kaiwa nan ta juya ta fuce daga gidan, daddy daya kyallarawa kudin nan idanu ya kasa rufe bakinshi.

Amra ne ta kalli Haj kareema tace “mummy ga wannan ku saya kayan abuncin dashi”

Kallon kudin kareema tayi nan take ta duka kasa tana hawaye, babu yanda amra batayi ba akan karta duka mata amma taqi, asma ma ajiye sandar Tata tayi ta rungume amra tana hawaye, “dan Allah kuyi hkuri ki yafe mana, Wallahi alhakin ne yake binmu, mun wulaqantaku, mun zalinceku”

Zame wa amra tayi daga jikinta ta share mata hawaye “na yafe maku duniya da lahira, Allah ya bawa daddy lafiya,”

Tana kaiwa nan ta juya ta fuce, harta fuce hajiya kareema na hawaye haka zalika asma ma, daddy kuwa babu abunda yake cewa sai “kudi kudii miqo min nan kiga”

Wani irin banzan kallo kareema tayi mashi kafin ta miqe ta wuce daki tana zubar hawaye.

Amra na fitowa ta wuce wajen da sukayi parking lokacin kowa ya zauna Duk sunyi jugum jugum, tana shiga motar amar yaja sukabar wajen.

Tunda suka shiga mota babu wanda yace da wani uffan Har suka iso airport, nan cikin airport din Amar yayi masu wani booking sun don daman flight sun yamma yayi masu.

Tun a cikin motar malam labaran ya yanke shawarar zama anan katsina don tund ayaji ance inna ta rasu kuma ba a gidan ta rasu ba Toh tabbas tana wajen Yan uwanta da suke Yan uba don hakan ya yanke shawarar zama don ya samu yaje chan kauyen don daman chan kauyen katsina suke, don haka sukayi sallama su kuma suk wuce abuja….

Tun bayan zuwansu katsina komai ya sauya, labaran ya samu yaje kauyen dangin inna, sunyi mamakin ganinshi sosai don kowa yasan ya rasu shekaru da suka wuce sai gashi kwatsam, bai tsaya yin wani dogon baya ni ba ya shaida masu bata yayi daga baya kuma Allah ya dawo dashi.

Har labarin inna saida dan uwanta ya kaishi, ya dade sosai yana mata addua yana hawaye kafin yayi masu sallama bayan ya danyi masu sha Tara ta arziki.

Bangaren Yan abuja komai ya sauya, zaman lafiya sukeyi mai tattare da farin ciki da kwanciyar hankali, Har lokacin babu abunda ya sauya tsakanin amra da general wanda ammah ta zuba masu idanu kawai,

Kullum triplet kuwa na wajen ammah, don wataran ma a dakinta suke kwana tare da ita, basuda rigima kwata kwata, don idan kaji kukansu Toh suna son madara ne, yara dai girma sukeyi sosai suna kyau, kamannin su da iyayensu na fitowa sosai kamar Ka sace su Ka gudu.

Amar dai ya dauka son duniya ya daura masu, idan har yana gidan dashi ake rainon su  wani sa”in ma a dakinsa suke wuni saidai a buyosu da madara, gwanin ban sha awa, gidan kuwa daga shugo babu abunda zakaci karo dashi sai kayan wasan yara tun basu kai lokacin wasan bama, gata dai babu wanda basa sha wajen amar da ammah.

Har lokacin shima yana sane da amra yana timing dinta yana kokarin karantarta da abubuwan da take so daga nesa, kwata kwata ya daina shiga sabgarta, wani sa’in saisuyi kwana biyu ma bai ganta ba don koda yaushe tana zaman daki sai Yan kwanakin nan ne take yawan futowa ta shiga kitchen.

Bangaren Aman gaba daya ya maida kanshi busy man, gaba daya ya maida hankali wajen ci gaban company saboda yanda Amar ya bashi babban mukami wanda haka ke nuni da ya bashi yardarsa da amanarsa wanda hakan yasa yake son ya nuna mashi how hardworking he is,

Ta wani bangaren kuma ya danyi baya baya da salima wanda Intayi complain saidai yace aiki ne yayi mashi yawa  don yanda suke yin waya suna soyewa suna raba dare yanxu sun daina, wayar ma itama ce ke kokarin Kiran sa, daga kira kuwa saidai su dan gaisa yayi shuru idan ta fara janshi da hira sai yace mata Ay he’s busy, abun na damunta sosai haka zalika shima, shi a bangarenshi dalilin da yasa yake mata haka ba komai bane sai guilt din abunda yayi ma mahaifunsu dake cinshi sosai, yana jin kunyar tasan abubuwan da yayi mashi, wanda hakan yasa yake danyi baya baya dukda abun na damunshi sosai.

After few months….

Yau wata biyu kenan da tafiyar Amar dubai don yanzu yana zuwa ne yayi wata daya ko biyu idan ya koma kafin ya dawo Nigeria saboda tarin responsibility daya hau kanshi, acikin watannin nan ya samu Karin girma, don yanxu yana matsayin overall major general.

Hanyoyin alkhairi ta bude masa sosai don indai yasa hannu a cikin abu to fa sai abun ya zama alkairi, ayanxu babu abunda suka wuce family dinshi, he is a complete man, abu daya ne yake lacking which is love and care from a partner wanda a yanxun yasan da hakan ba kamar ada chan baya ba.

Ayanxu ya tabbatar namiji baya taba zama complete idan babu mace a kusa dashi,a Lissafin da yake yi kusan shekara daya da watanni kenan rabon shi da mace, wata irin matsuwa ce ke  damunshi na buqatar mace dukda yana dannewa don yayi alkawarin bazai sake takura ma uwar yayan shi ba, his heart wato “Aisha!!!” He’s loving her from far, aisha ta gama da kwakwalwarshi da zuciyarshi gaba daya lokacin da baima ankare da hakan ba, Duk sanda ya koma dubai baya samun sukuni, yana son jin muryarta yana son Ganin ta yana son kasan cewa da ita saidai hakan bazai samu ba saboda Har lokacin yasan bata sauko ba, and baya Ganin laifin ta don ya zauna yayi reversing Duk abubuwa da yayi mata da irin pain din dayayi causing mata a zuciya, idan ya tuna da abubuwan nan yana jin haushin kansa sosai, tabbas maganar ammah ta tabbata don sai yanxu yake regretting komai, don aisha is one in a million, ada chan bai ga worth dinta ba sai yanxu datayi mashi nisa, babu abunda yake gani a idanunta sai kiyayyarsa da haushinsa, sometimes idan yana zaune a penthouse dinshi saidai ya bude laptop dinshi yana scrolling recorded videos dinta na cctv lokacin da suke a apartment dinshi, baya gajiya kwata kwata da Ganin videos din, sometimes haka zai zauna ya dauka hours yana kallon videos din yana murmushi kamar bashi ba, bayan wannan countless of times haka zai dauka wayanshi yana kallon contact dinta, yana son kiranta wata zuciyar Tashi tana hanashi yin hakan.

Haka zuciyarshi zata dunga mashi wasi wasi idan ya gaji saidai ya kira ammah kawai a video call don ta nuna mashi babies dinshi.

Bangaren amra, a cikin watannin nan ta Kara kyau sosai tayi murmur, shape dinta ya dawo kamar wadda bata taba haihuwa ba, ta Kara kyau da cika idanu Har wani sihirtaccen kyau ta kara saboda yanda ammah ta saka ta agaba take yi mata gyara sosai kamar wata Amarya, musamman ammah ta kira yar chad wadda ta taba yi mata wankan Amarya tazo ta fara gyara ta sosai, don saida suka dauka wajen sati biyu tana gyara ta ciki da waje nonstop,

Karshe ma dai ammah ta dage akan Duk end of the month yar chad zata dunga zuwa tana gyara ta, kudi sosai ammah ke kashe wa akan amra wadda ita batama wani damu da Gyaran ba don wanda tasan danshi akeyi bata ra’ayin shi kwata kwata.

 

    kyauta ta musamman ammah ta bama yar chad saboda yanda ta gyara amra sai san barka, Duk inda ta gifta kamshi ke fita daga jikinta,

 Dukda haka bata barta ba haka Tayi mata ordern kayan mata daga Sudan masu kyau sosai ta bata, babu wani kunyar surkunta ammah ta zaunar da ita ta nuna mata mahummacin Gyaran jiki a wajen mace, yanda ammah keyi ma amra ko uwar data tsugunna ta haifeta sai haka, shakuwa sosai ta shiga tsakaninsu, inda kwata kwata ammah bata mata maganar Amar ko zancen rayuwar aurensu wanda hakan kesa amra jin dadi don ko babu komai tana Ganin ammah na supporting dinta,

Duk wata zata ga alert a cikin wayarta na kimanin dubu dari biyar daga wajen dadyn  princess, oga kwata kwata kenan, batama san ya bude mata account ba ta karkashinsa sai aranar ta gani, abunda ya fara bata mata rai was sunanta datagani da nashi daga bank din “Aisha Muhammad taura” dataga alert din tabe baki kawai tayi batace komai ba, the second time daya sake tura mata same amount still bata wani damu ba don ta gama fiddashi daga ranta don haka bata buqatan wani abu daga gareshi kuma babu abunda zaiyi mata da zai girgizata ko ya sauya yanda ya Gina tsanarshi a zuciyarta

Yanxu in kunga Amra ta kile sosai don yanzu she’s socialise ba kamar da ba ta kara zama yar gayu sosai irin manyan classy matan nan, idan kuka ganta kamar bata haifa triplets ba, Har lokacin bata da wata kawa a duniya data wuce haifa da anty Madina wadda ayanxu ta zama abokiyar shawarar ta kuma itake bata shawarwari sosai idan sunyi waya don ita ta koma uk da yayanta saboda offer data samu achan, 

Duk wani sirrin amra a wajen Madina zaka jishi, don ta maida Madina kamar babbar yayarta, Duk wani abunda ya shige mata duhu gurunta  take zuwa ta bata shawarwari sosai, Har lokacin kuwa idan Madina tayi mata maganar Amar bata cewa komai saidai ta sauya hirar kota nuna bata ra’ayin maganar shi, tun Madina na yin shuru tana kauda zancen don ta nuna kiri kiri bata son zancen Har tazo ta fara mata fada don yanxu takaiga idan tayi mata maganar shi kiri kiri zata ce ita bata son zancen shi, auren ma bata so tunda ta haifa mashi yaya bata son zama dashi, abun yana damun Madina sosai don fada sosai takeyi mata akan wannan zancen, saboda ayanxu ne ya kamata ta jaa mijinta ta rikeshi ta tarairaye shi don ya gama saukowa sosai kowa ya shida hakan don itama ta shaida hakan musamman ranar sunan triplet, da idanu ta taga yanda yake kallon amra da yanda yake haba haba da ita amma take waskewa tana basarwa, Har lokacin da yaso suyi hoto dashi da ita da yayansu amma ta wucewan ta sama, aranar ma Madina tayi mata fada sosai akan wannan.

Amra nada taurin kai sosai, wanda hakan yasa Madina ta soma binta da lallami tana nuna mata  cewa yanxu batada wanda ya wuce shi a duniya don shine uban yayanta, babu laifi yanxu idan tana mata fada ko tana nuna mata mahimmacinsa tana dan tsayawa ta saurareta, don Har waazi tana tura mata akan mahimmacin da darajar miji a wajen mace da rights dinshi akan mace, bayan wannan Har sirrikan yanda mace zata rike miji yanda zai mace yaji Duk duniya babu wadda yake so sai ita take tura mata, wasu haka zata bude ta karanta wasu kuma haka zata barsu taqi karantawa saidai idan taji boredom, Akwai ranar da Madina ta tura mata wasu zafafan erotic ideas wanda yasa ta dauke wuta sosai, tana fara karantawa ta ajiye tana turo baki kamar yarinya, haka ranar ta wuni da wani alamari daya shigeta dalilin tunawa da tayi na intimacy dinsu ita dashi, dukda tana kokarin deceiving kanta saidai gangar jikinta bai lamunce da hakan ba, sai a lokacin ta tabbatar da tana cikin jerin mata mabuqata sosai don tanada muguwar sha’awa.

Bangaren babansu kuwa komai yanxu ya sauya mashi shima, ya zama babban mutun don jari babba Amar ya bashi dukda da kyar ya karba, bayan wannan ma da farko yayi mashi tayin aiki a company’s taura ltd nan babansu amra ya nuna mashi abubuwa da sukayi mashi na alkairi  yayi yawa sosai don haka yake jin kunyar karban wannan offer din bayan wannan ma yanxu yana son yayi rebuilding kanshi don Har yanxu talent dinshi na nan.

Dukda haka amar bai barshi ba saida ya samo mashi wani project mai tsoka sosai a wani babban company, da farko company hankalinsu bai kwanta dashi ba don gani suke kamar bashida qualification sai daga baya suka fara testing dinshi, outcome din abunda suka bashi yayi blowing mind dinsu sosai don komai daki daki yayi da tsari, nan take suka daukeshi suka bashi wani babban mukami wajen yin project din Har ya zama project leader.

Wannan aiki ba karamin arziki ya kawo ma babansu amra ba sosai don he work so hard for it dukda da taimakon Amar ya samu aiki, 

Har alokacin he’s leaving a lowkey life anan abuja haka zalika Har lokacin bai fasa aiki a gidan gonar ammah ba karshe ma Har expanding gurin yayi sosai ya kawo wasu ma’aikata suna taimaka mashi don yasan how ammah value gidan gona sosai.

Duk bayan sati yakan zuwa gidan ya duba yayan nashi sannan ya gaida ammah, wani irin tsaftattacen relationship sukayi buliding cikin wayewa inda Har alokacin yakan zuwa Har cikin gidan ya zauna su gaisa da ammah sannan ya bata Duk wani update akan gidan gonar harma shawararta yana zuwa ya nema akan wasu abubuwan.

Acikin watannin nan baban amra ya lura da rayuwar auren da amra da amar ba kamar kowanne aure bane, dukda bai taba tambayarta yanda auren nasu ya faro ba don hakan bashida wani amfani ayanxu saidai yanayin yanda komai ke tafiya yasa yake jin Akwai wata a kasa.

Ranar dayazo gidan dubasu kuwa aranar ya samu ya zauna da amra don suyi magana, koda ya fara yi mata tambaya akan Amar nan ya gane kwata kwata kamar ma bata damu da Amar dinba don babu wani corner corner tace “bata sani ba”

Anan take ya tambayeta kodai Akwai wata matsala ne, abunda ta fada mashi ya girgiza shi inda ranshi ya baci sosai, babu abunda yake maimaitawa a zuciyarshi sai kalamanta “abba ni bana son shi inason araba auren mu” 

Aranar dai amra taga fushin baban nata wanda zata iya rantsewa bai taba fushi da ita haka ba tun suna kananu kafin su rabu, baima tsaya ya tambayi dalilinta ba ko ya saurari bayanin nata ba ya dakatar da ita akan karta sake gangancin fadin irin wannan furucin, idan har ta sake irin haka kuwa ya tabbatar mata ta zama butulu.

Aranar dai hankalin amra ya gama Tashi, don harga Allah ita da da gaske take,kodata fada ma baban nasu ma batayi tsammanin zaiyi fushi ba dukda tasan daman bazaibi bayanta, saidai kalaman daya fada mata ya razana ta sosai inda ya shiada mata idan har tayi tunanin rabuwa da Muhammad to babu shi babu ita don akan Amar da ammah zai iyayin komai ciki kuwa Harda fushi da ita sosai,

Taurin kan amra bai sa ta saduda ba don tana kan bakarta,

Ranar wata juma’a tana zaune a daki ta kira Madina a waya don ta bata shawara akan abunda take shirin yi.

wani abun takaici da tayi wanda yasa ran Madina ma ya baci sosai shine inda ta shaida mata yanda sukayi da baban su sannan ta shaida mata zata tunkari ammah da zancen don ita kadaice ke supprting dinta.

Saida Madina ta gama sauraronta kafun ta sille ta tass ta mata fada sannan ta tunatar da ita wacece ammah a wajenta kuma a wajen amar din shi kanshi, 

“Amma yau na gama tabbatar da bakida hankali amra, yanxu ke ko kunyar fadin wannan zancen Bakiji ba? Ammah zaki tunkara da wannan maganar? na farko dai Kun manta lokacin da kike fada min yanda suka rike qannenki

Amana? Sannan Kin manta yanda matar nan ta nuna maki so da qauna ta kula dake kamar ita ta tsugunna ta haife ki har yanxu ma tana kula

Dake tana kaunarki kamar daga cikinta kika fito Har kina tunanin fada mata cewa bakya son auren danta kina son a raba ku? Wai bayan wannan ma ke wace irin uwace? Bakya tunanin yayan dake tsakanin ku?  Haka kike da taurin zuciya daman? Kin bani kunya amra 

Ban taba expecting haka daga gareki ba Ay na dauka Duk surutan da kikeyi a baki ne ashe da gaske kike? Toh Wallahi Zan baki shawara tun wuri kafin kiyi regretting ki sauya wannan banzan tunanin naki don wannan stubbornness din naki zai kaiki ya baro ki”

Madina ta karshe ranta ya baci sosai, gyara zaman wayar amra tayi jikinta Duk ya mutu kwata kwata Duk ta manta da komai babu abunda ke ranta sai abunda yayi mata wanda yasa ta manta alkhairin da sukayi mata ita da kannenta shi da ammah,

Murya ta na Rawa tace “innalillahi wa inna ilaihi rajiun, anty Madina dan Allah ki bani shawara Wallahi bansan maysa nake waennan abubuwan ba Wallahi Ina sane da abubuwan da ammah tayi min, Wallahi sharrin shedan ne yasa nake kokarin tafka babban kuskure, ni Wallahi dalilin da yasa na fadi hakan shine gaba daya ya futa akaina, idan na tuna shi babu abunda nake tunawa sai abubuwan da yayi min”

Banza Madina tayi mata don Har lokacin haushinta  take ji

“Anty Madina kuyi hkuri don Allah karkiyi fushi, ki bani shawara Wallahi Zan dauka Allah,”

Gyaran murya Madina tayi kafin ta soma magana anatse “Ay dole nayi fushi amra, fushi da taurin zuciya zai kaiki ga yin aikin dana sani, wanda zakiyi regretting daga baya, my dear Allah y baki komai, kinada kyau kinada ilimi Kn addini dana Boko, Allah ya azurtaka da family da suke sonki, Allah ya Baki suruka ta gari wadda ta duake ki kamar ya, Allah ya Baki miji na gari san kowa qin wanda ya rasa don Wallahi mijin is one in a million, ga arziki ga komai, Allah kadai yasan irin matan dake rububunsa laifi sa daya na abunda yayi maki wanda na yarda bai kyauta maki ba a matsayinki na matarsa but da

Bakinki kince yayi apologising kuma yace he wants to makeup for everything right?”

“Yes anty Madina but still ni Wallahi…”

Katseta Madina tayi tace “kimin shuru ban gama ba, kona kashe wayarta ne idan gardama zakiyi?”

“Ah ah nayi shuru anty Madina” amra ta amsata tana gyaran zaman wayar a kunnenta

“Yauwa, as I was saying ba laifi bane don kinji zafin abunda yayi maki and kinada right din hukuntashi idan kina tunanin hakan ne zaisa zuciyarki taji sauqin abunda yayi maki ammah maganar rabuwar aure ki cireta a lissafi mu mata Allah yayi mana wata baiwa da ba ko wacce mace tasan da haka ba, zaki iya rama abunda yayi maki cikin ruwan sanyi ta yanda da kanshi zai dunga binki yana baki hkuri yana lallaba ki Har sai zuciyarki tayi sanyi, bari kiji na fada maki gaskia wallahil azeem bazanyi kaffara ba kinason mijinki sosai, son da kike mashi ko ke kanki kin kasa Ganin haka saboda wani banzan fushinki da taurin zuciyanki,”

Turo baki amra tayi waje ta soma magana yanda bazata jita ba “ni babu wani son shi da nake yi”

“Kince wani abu ne?” Madina ta tambayeta 

“Ah ah bance komi ba inajinki” amra ta amsata 

“Yanzu shawara daya Zan baki, ban hanaki ja mashi aji ba wannan yana da kyau saidai ki jawo mijinki a jiki ki bashi kulawa ki tarairayeshi, ki sanya ya mutu a sonki yaji dukduniya bai wata mace sai ke wannan shine abunda ya kamata ki dunga tunani akai bawai ki dunga tunanin rabuwa da uban yayanki ba.”

“Toh anty Madina na dauki shwarar ki bazan Kara maganar rabuwan ba saidai gaskia Saina Rama abunda yayi mun don bazai dameni ta sauqin ba after all he has done to me”

“Kyaji dashi wannan ya rage naki, saidai kuma anan ma zanyi maki gyara, adaiyi saffa saffa don Wallahi idan kikace zaki jaa ajin nan sosai to Wallahi zaiso ya tsinke ne kizo nan ma kina dana sani, I’ve said my own yanxu komai ya rage naki”

Madina ta karashe tana sauke ajiyar zuciya

Nunfasawa amra tayi kafin ta soma magana 

“Toh Yanxu anty Madina meya kamata nayi?”

“Ban sani ba, abunda ya kamata kiyi ma Saina fada maki? Kije kibi Duk videos da abubuwan dana tura maki ki karanta, saiki dawo muyi magana”

Sauke kai amra tayi kamar tana kusa d auta tace “tohm zanyi Insha Allah”

Sallama Madina tayi mata ta kashe wayar.

Tun bayan wayar da sukayi da Madina amra ta dan chanza, tundaga ranar bata kuma gangacin maganar rabuwarta dashi ba don sai daga baya ta gane cewa badan Madina tayi saurin hanata shirmen dataso yi ba da tazo tana dana sani, don duba ga Duk abubuwan da ammah keyi mata da yanda take kula da ita da son da take nuna mata dasu triplet yasa take jin takaicin kanta, what was she thinking? Maysa ta zama so stupid for thinking of that? Haka zata dunga tambayar kanta tare da jin haushin kanta gaba daya.

A cikin kwanakin ne ta sake Kiran Madina, sun dade suna waya sosai Inda ta bata wasu shawarwarin masu mahimmanci sannan ta buqace ta data kirashi a waya ko ta dunga mashi dan morning message tana jin yanda yake, da farko dai taso tayi halin nata saidaga baya Ganin ran Madina ya soma baci tace zatayi, haka dai ranar Madina ta dunga fama da ita kamar wata Mara wayo ko irin wata local dinnan, idan tace kaza saitace ita bazata iya ba Ay saiya samu damar Kara rainata ahaka dai ta dunga nusar da ita amfanin duk abubuwan da take fada mata don babu abunda zasu Kara mata a idanunshi face darajarta da zai dunga gani kuma hakan zaisa ta shiga ranshi sosai don da haka zata saye zuciyarshi.

Duk wannan abubuwan da Madina ta fada mata baisa ta kirashin ba don ita a ganinta inshi baiyi mata message ba maisa ita zatayi mashi, don haka ta watsar da zancen ma gaba daya.

Washe gari haka ta shirya ta fada ma ammah zata je saloon ita da salima nan ammah ta bata atm card din da Amar ya bari idan zatayi buqatun gabanta, da mamaki amra ta karba card din kafin tayi ma ammah godiya suka fuce ita da salima don driver ne zai kaisu,tunda suka shiga mota take kallon card din sai alokacin ta ga sunanta hade da nashi a jikin card din nan ta tuna lokacin da alert din kudi ke shigowa cikin wayarta, Nunfasawa kawai tayi tana danyi wani nazari Har suka iso saloon, basu wani jima ba don wanKi kai kawai akayi mata akayi blow drying sai stretching, suna gamawa suka fito, nan ta umarci driver ya wuce dasu mall,

Tunda suka shiga ta fara yima kanta sayyayyah  sosai, salima dai kallonta kawai takeyi tana mamakin ta don ita ba ma’abociyar saye saye bace hasalima in taga anayi sosai cewa take Ana almabazaranci, batace mata qala ba haka dai ta dunga binta Har saida ta gaji suka dawo gida.

Amar…..

Yau watanshi biyu kenan da komawa dubai tun last tafiyar da yayi bai dawo ba saboda ayyuka da sukayi mashi yawa, tun ammah na expecting dinshi harta hakura,

Kwatsam sai gashi ya dawo ranar da triplets suka cika 6months, babu wanda yayi expecting dinshi don ko ammah bai fada Nawa ba.

Karfe uku daidai na rana ya shigo gidan da sallama cikin kamewa, su amra dake zaune dasu salima Duk sunsha kwalliya sai ammah da Salim, amra na rike da princess data kara girma tayi wayo sosai tayi bulbul don Har zama tanayi, tasha wata pink gown an saka mata crown pink tayi kyau sosai kumatu ta sun fito, gefe ammah ce zaune da Hamad da Hamid a hannunta sunsha riga da wando sunyi wayo sosai sunyi bul bul bakinsu an maqala masu pacifier, ammah ma itama tayi kyau sosai don jigaggaen lace ne a jikinta wanda ya amsheta sosai, gabansu cake ne manya manya guda uku akan Center table inda aka rubuta kowannen happy 6 month, cake dinma kana gani kasan yasha kudi sosai, don kowanne da sunan triplet a jiki, salima na tsaye tana kokarin daukan hoton ammah da amra da triplets sai jin sallamar shi sukayi,

Waigowa sukayi gaba dayansu suka zuba mashi idanu, yayi kyau sosai yayi kiba har wata qasumba ya Tara sosai ba kamar yanda yake barin ta ba a fuskanshi, sanye yake da kananun kaya as usual wandon jikinshi na army sai white Riga mai gajeran hannu sai jacket dinshi a hannu da briefcase, yayi masifar kyau sosai, tun daga nesa kuwa kamshinsa ya gama bade parlorn, murmushi ammah tayi “maraba lale, saukan yaushe son? Sannu da zuwa baka shaida mana zaka zo ba”

Wani kayataccen murmushi ya sauke ma ammah kafin ya karaso cikin parlorn amra dai kasa dauke idanuta tayi akanshi, she can’t lie ya gama captivating dinta, shiko baima kalli inda take ba don yana kallonta dan tsimin dayake dannewa zai taso mashi, karasowa yayi ya ajiye briefcase din hannunshi da jacket din yana murmushi “thank you ammah na, my babies haka suka Kara girma ammah”

Ya fada yana karasowa gaban ammah ya duka Hamid yayi pecking dinshi yana gamawa ya yi amshi hamad ma yayi pecking dinshi, nan take yaran suka fara mashi dariya, gaba daya mamaki ma ya hanashi magana, “I missed you my boys,” yana karashe wa ya kalli bangaren amra, saurin ajiye Hamid da Hamad yayi kan ci yar ammah kafin ya tako inda amra take ya dan duka ya kama hannun princess yayi pecking yace “my little princess, I missed you daddy girl, how are you???”

“Ya Muhammad Ay bata fara magana ba” Salim ya fada yana dariya

Murmusa wa gaba daya sukayi kafin ya mike tsaye, nan Duk suka gaishesa amra dai kanta a kasa saida ya gama amsawa tace “sannu da dawowa, ya hanya?”

He never expected that don yayi mamaki sosai, kai tsaye ya amsa ta “lafiya”

Suna nan tsaye driver ya shugo da wani katon packs din jaka guda biyar, yana karasowa Amar yace ma salima taje ta karbo, tana karbo wa ta ta kawo mashi nan ya dauka ya bama kowa nashi, pack uku ya duaka ya ajiye gaban amra yace “wannan for my babies”

Yana ajiye mata ta kalli pack din batace komi ba, waigawa yayi inda su salima suke nan ma ya basu bag daya yace “ga maki keda Salim”

Yana bata ya juya wajen ammah itama ya bata nata sauran dayan pack din daya rage, godiya Duk sukayi mashi babu wanda ya kura bai bama amra ba, ita kuwa ta qulu sosai sai dannewa datayi.

Saida ya tsaya akayi hotuna dashi kafin ya wuce bedroom, yana shiga ya sauke wata ijiyar zuciya yana dafe kirjinshi, tunda ya shugo gidan idanunshi suka sauka akanta yaji yanayinshi ya sauya, “ya Allah…. “ ya fada yana admiring irin kyau data kara, she looks so hot kamar bata haihu ba, daman wata doguwar Riga ce a jikinta dataji shape dinta tayi mata kyau sosai, dukda daga zaune ya ganta but he can imagine yanda zata kasance cikin rigar idan ta mike, da kyar dai ya samu yayi wanka ya sauya kaya yayi sallah kafin ya futo.

Karfe takwas Kow aya sauko kasa, gaba daya sun hallara a dining, abunci suka fara ci gaba dayansu Banda Aman da baya dawowa gidan sai wajen karfe goma, su triplet kowannensu an daura su kan high chair don yanzu an dan fara basu pudding, hira sosai salima yake zagbawa inda Amar ke biye mata, kowa saida yayi mamaki yanda take zuba yana sauraronta shida baya son magana kwata kwata, amra dai takaici da haushinsa take ji sosai for not noticing her, baya yarda ma su hada ido, babu irin saqe saqin da batayi ba aranta, tun ba aje ko Ina ba ya dawo da halinshi ta fada aranta.

Suna gama cin abunci a dining suka wuce sitting room nan suka baza sabon hira Harda ammah, amra dai na daga gefe tana wasa da princess dake hannun ta Har tayi barci.

Karfe goma daidai ta daukesu ta wuce dasu sama ta kwantar dasu, Hamad dake hannunshi dadynshi ne ya rage don haka ta sauko kasan don ta karbeshi, tana zuwa ta tadda sun ammah sun wuce sama sai Amar dake dauke da Hamad don yana shirin shiga bedroom dinshi, yasan zata sauko daukan Hamad don hak yayi saurin wucewa bedroom dinshi.

Tun daga nesa ta hangoshi don haka bataji wani Dardanelles ba ta wuce bedroom dinshi don ta amshi Hamad, tana shiga ta hango ya kwantar da hamad kan gado, dan waigawa ta farayi Ganin bata ganshi a dakin ba yasa tayi hanzarin shigewa dinta dauki hamad, tana karasowa tsakiyan dakin ya damketa, arazane ta fara kokarin juyowa ya hanata dalilin kama kugunta da yayi ya sauke kanshi wajen wuyanta, wani irin nunfashi yake sauke mata mai tafe da saqonnj, 

“Uhm mey haka…”

“Shiiiii,…” ya fada yana mata waiwayi, tsit tayi bata ce mashi komai ba Har saida taji tafiyar hannunshi kan fatar ta, saurin runtse idanu tayi yaqi budewa saida yace “open your eyes”

Bude idanun nata tayi nan ido ta ya sauka akan wata English diamond necklace dake daukan idanu sosai, “sorry wifey ban baki naki tsaraban ba daman nafison sai mun dan kebe and by the way you look so beautifully sexy in this…”

Shuru tayi mashi batace komi ba harya saka mata sarkar a wuyanta kafin yayi kissing bayanta passionately, yanda yake caressing dinta dole ta ji hakan a jikinta, don tayi Lamo kamar  wadda aka zarema laka,

Tunawa da wani abu yasa ta zame jikinta daga nashi ta juya ta dauki Hamad kafin ta maido da kallonta gareshi tace “thanks”

Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin, tana futa ya dan dafe gabanshi da kanshi a d same time yace “Aisha please… meysa kike son wahalar dani”

Su aisha ba a san ma yana yi don daki ta wuce ta kwnatar da Hamad a gadon shi kafin ta fuce zuwa nata dakin don yanxu a dakinsu suke kwana sannan akwai noise machine dake baya idan sun Tashi a barci ko suna kuka.

Washe gari haka sukayi breakfast gaba dayansu, kamar koda yaushe Harda Aman Salim ne kawai ya tafi school abunshi.

Tunda suka zauna salima ke aika ma Aman wani irin kallo, shi kadai yasan maanar kallon, suna gama breakfast kuwa ya zille ya wuce bedroom don ya shirya zuwa office, shine ya fara futa a dining din yana futa salima yabi bayanshi bayan ta faki idanun kowa, kai tsaye ta wuce bedroom dinshi lokacin har yana kokarin saka riganshi, babu sallama ta shigo dakin ta hade hannunta a  kirji tace “ka daina ignoring dina wannan yar boye boye da kake yimin bashi da wani amfani don bazan taba rabuwa dakai ba kai kasani”

Saurin juya mata baya yayi yace “bakiga Ina saka kaya bane excuse me”

“I won’t saboda in fita Ka sulale Ka gudu ko? We have to talk first”

“There’s nothing to talk” ya bata amsa 

“There is” ta fada tana takowa inda yake tana facing dinshi

“Kina matsayin mace bai kamata ki shugo dakina ba Kar wani ya shugo yayi mana wata fasaara”

“And so? Do I look like i care, nifa Bari kaji duba ga Duk wasu abubuwan da zaisa kana ignoring dina nayi observing na kasa gani komai so now tell me menen?” Ta karashe tana kallonshi

“Hmmm” kawai ya iya ce mata  

“Is it because of abba na?” Ta tambayeshi 

Saurin dagowa yayi ya kalleta idanunshi sunyi rau rau

Murmushi ne ya kubce mata tace “Ay nasan saboda shi ne, Toh Ka daina wannan  kauce kaucen, abbana ya yafe maka, don nama fada mashi ni kai nake so” ta karashe tana murmushi

“Da gaske dan Allah?” Amar ya fada with so much happiness akan fuskanshi

“Yes and he understand, Yanxu inason kayi mashi magana da kanka and..”

“I will apologise to me,” yayi saurin katseta

Murmushi tayi mashi tana cin yatsunta tace “yauwa my love yanxu mun dawo daidai ko?”

“Yea my love” ya amsata yana kallonta cikin so da kauna

Juyawa tayi zata futa tace “you’re so…”

Bata karasa ba ta fuce daga dakin nashi tana dariya.

Bangaren amra bayan fitar salima daga dining itama ta wuce sama, daman triplet suna wajen ammah, tana zuwa daki  ta duaka wayarta danna ma madina kira don ta shaida mata abubuwan da suke gudana,

Madina na daga wayar amra ta soma kira mata bayani, babu abunda bata fada mata ba ciki kuwa Harda necklace daya kawo mata, nan Madina ta cigaba da karfafa mata gwiwa sosai Har sukayi sallama ta kashe wayar, tana kashewa sai gashi ya shugo dakinta da sallama, baima jira ta amsa ba ya rufe kofar, gyara tsayuwar, karasowa yayi har inda yake kafin ya zauna bakin gadonta yana kallonta, kallonshi tayi Ganin wannan nuna isa irin Tashi da Har yanxu bata barshi ba, “do you need anything?”

Ta tambayeshi sounding but harshly, “uhmm yes, I need you” ya bata amsa kai tsaye babu wani kwana kwana, wata bazawarar dariya ta danyi kafin ta juya ta wuce gaban dresser tana juya mashi mazaunai yanda zai gani da kyau, tana ajiye wayar ta juyo ta kalleshi tace “you need me for?”

Ta tambayeshi tana zuba mashi idanunta masu kashe mashi jiki, 

“Inason mu koma gidan mu” ya fada mata yana mata wani kallo dake kashe mata jiki,

“Gidan ku kaida wa?” 

“Dawa nake magana yanxu” ya bata amsa don abun nata Harda rainin hankali wanda hakan ke pissing dinshi off, 

“Ohh!!! Wai ni??? Babu inda zanje,” ta fada mashi kai tsaye, 

Yar dariya yayi ya miqe tsaye ya tako gabanta Har tana jin saukan nunfashinsa yace “bazaki jeba?”

Dagowa tayi ta girgiza mashi kai alamun eh, 

Yar dariya yayi yaja kumatunta yace “okay za ayi abun kunya anan kenan?,”

Bata gane me yake nufi ba don haka bata ce mashi komai ba sai kallonshi da ta cigaba tsayi batama san tanayi ba, 

“Why are you acting kamar bakisan abunda nake nufi ba?”

“Mey kake nufi?” Ta tari nunfashinsa da tambayarta 

“Aisha I need you, please ya kamata kiyi hakuri mubar abunda ya faru a baya, mey kikeson nayi don ki hakura uhm? Ki fada min abunda kikeson a duniyar nan wanda zaisa ki gane cewa you mean the world to me zanyi maki shi I promise, I so much l….”

Saurin sanya yatsanta daya tayi akan bakinshi ta sauke wani lausassan murmushi daya sashi melting kafin ta soma magana “shiii please, inyi hkuri? In manta abunda kayi min ? Just like that?“

Riko kugunta yayi ya janyota jiki shi yana dan langwabewa kamar ba Amar ba, he’s doing things da bai taba tunanin zaiyi su a gaban mace ba “yea please wifey for the sake of our children please, Allah I missed you”

Saurin matsawa tayi daga jikinshi bai hanata ba tace “hmm namiji kenan,”

“Nasan me kike tunani, but kinsan I have right akanki ba? Inada hakki na akanki”

Bata juyowa ba ta soma sauke kayan jikinta agabanshi, take idanunshi sukayi jaa sosai ya danyi baya kamar zai fadi, ita kuwa tana sane tayi haka don tayi alqawarin saita goga shi sosai kafin ta sauke kanta gareshi, tana sauke rigar ta juyo ta kalleshi nan ya karema jikinta kallo, ita ko dan stretch marks dinnan ma babu, fatarta tayi luwai luwai, boobs dinta sunyi girma sosai daidai jikinta sun yi wani perky red akan fatarta, “idan Ka gama Ka rufe min kofa na please”

Ta fada tana juyawa tana sending mashi wasu assignments, kasa daga kafanshi yayi saida ta nufi kofar shiga bathroom yayi saurin tsaidata “Aisha please mana…meysa”

Bai gama ba ta banko kofar, haka nan ya tattara kafafunshi ya fuce zuwa dakin ammah, yana zuwa ya fara kame kame, karshe dai saida tace “idan bazaka fadi abunda ke tafe dakai ba Ina da abunyi,”

Ganin haka ya sashi sauke kanshi kasa yace “daman,,uhm daman, inason mu koma ne chan larrics”

Murmushi ammah tayi tana jin dadin furucinshi “ka fada mata ne? Ta amince?”

“Eh ta amince” ya amsa ta

“Toh Masha Allah yaushe kake so su koma? Harda yaran? Nidai da kun barmin su?” Ammah ta fada tana maida kallonta ga wayar dake hannunta 

Kai tsaye ya amsata  “ba damuwa saisu zauna anan din,”

“Okay Friday saita koma chan din Allah ya Baki zaman lafiya, saidai muhammd Ina gargadinka da wannan hali naka don Allah Ka kula da baiwar Allah kaga amana ce a hannuka, karka bani kunya”

“Insha Allah ammah”

Bai wani jima ya fuce daga dakin ammah yana counting sauran kwanakin da suka rage, yau Tuesday nan da kwana uku

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.