Best Hausa Novels

Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx

Chapter 16 of 52

Chapter 120

Update!!!

20/05/2023

Unedited

Ranar haka suka wuni suka tufka da warwara,inda sabo ya shiga tsakanin su sosai kamar kawaye, Nadine na mamakin yanda suka sake da ita dukda ita ba kowa bace face yar aiki,Sai wajen karfe takwas haifa tayi masu sallama ta shiga motan ta wuce gida.

Bangaren Amar kuwa tunda doctor ya kirashi ya shiga tashin hankali da abunda ya shaida mashi, don haka ya yanke shawarar zuwa dan dole yazo ya tabbatar da kanshi, ranar dai haka yayi ta babu walwala kwata kwata,koda ammah taga yanayinshi ta tambayeshi abunda ke damunshi nan take ya shaida mata baya jin dadi ne.

The next day…

Da wurwuri ta shirya cikin Kamala ta sauko kasa, Nadine na ganinta tayi saurin zuwa gabanta tace “good morning ma”

Murmushi kawai tayi ma Nadine kafin su wuce wajen dining,Nadine ce tayi serving dinta special English breakfast da pablo ya dafa, bata ci da wani yawa ba ta mike tayi Ma Nadine sallama ta fuce daga parlor zuwa inda m5 ke parking? Yau ya chanza mota zuwa wata Bakar benz,Tana karasowa yayi saurin fitowa ya bude mata bayan motar ta shiga kafin shima ya shiga ya jasu, “good morning ma’am”

Bata kalleshi ba tace “morning”

tafiyar minti ashirin suka iso headquarters, yana parking ta fito rike da wayar ta da laptop dinta ta shige ciki a tsanake.

Tun daga bakin reception haifa ta hangota, da sauri ta karaso gabanta tace “kinyi latti fah”

Dariya amra tayi tace “lattin 10mins ko”

Dariya sukayi gaba daya kafin haifa tace “let’s go in, yau Akwai aiki da yawa inaso muyi mu gama da wuri Akwai inda zamuje”

Kallonta amra tayi feeling so excited tace “daman na gaji da zaman gidan nan, Ina zamuje”

“It’s a secret” haifa ta bata amsa 

Ciki suka wuce ta aje laptop ta saka lab coat  dinta kafin su fito tare gwanin ban sha’wa, saida saida suka fara first round medical check wanda ya dauke su kusan awa guda son Akwai patients da yawa don Akwai manyan officers da sukaje operations, wasu sun raunata wasu cikinsu kuma sun samu minor injury, da yake aikin nada yawa yasa suka raba, don yawanci daman chanza dressing ne Sai nada magunguna da duba pulse din patients, abunda yake burge amra shine Duk wannan aiki da sukeyi wanda yawanci duba maza ne basa samun matsala dazu, don wasu saikaga har flirting mutane suke yi saidai banda larabawa, kwata kwata basa flirting da mata musamman waenda ba al’adar su daya ba ko Yan wata kasar,dama dama haifa, ita yar kasar ce saidai hakan baisa suna shiga sabgar su ba.

Ahankali ta janye labulen dake rufe da gadon patients don yawanci Ana janyo shi ne Idan za ayi Ma mutun allura, ko idan patients zai kwanta, wani saurayi ne Akwance ya juya ma labulen baya, kafanshi na daure da igiya dake rike da gadon da alamu ya samu karaya ne ko ya buge akafan, dogo ne sosai bashi da qiba dan daidai jikinshi, kanshi kwance da gashi irin na larabawa, saurin kauda kanta tayi tace “salam” duban file din hannunta tayi tana karanta maganin da ya kamata yasha da safiyan, bai waigoba sarai kuma yajita idanunshi a lumshe saidai muryarta yasa ya bude idanunshi tare da dan waigowa dan ganin me zaqin murya irin wannan, kyakyawan saurayi ne balarabe sak, yana da kyau daidai musali don fuskanshi yar siririya ce, wannan yana da gashi daya rufe kusan duka goshin sa, tunda ya kafa mata idanu yaqi saukewa don bai taba ganinta anan dukda shi bangaren department din da yake basa zama a headquarters, yawanci operation suke, batasan kallonta yake ba don idanunta nakan file din saida ta gama ta dago, murmushi ne dauke a fuskanshi kafin yayi saurin dauke idanunshi don lowering gaze, murmushi kawai tayi tace “good morning sir”

Dan dagowa yayi yace “morning”

Matsowa tayi da hannunta sanye da glove ta fara kokarin duba kafan nashi, tana tabawa ya danyi Kara “ouch”

Da sauri ta dago tace “so sorry, futa tayi kafin ta dawo da tray a hannunta dake dauke maganin sai wani disposable cup, Miqa mashi maganin tayi da ruwan, karba yayi ya sha kafin yace “thank you”

Tana shirin juyawa yace “you’re beautiful!”

Chak ta tsaya kafin ta juyo,ba kallonta yake ba fuskanshi a kasa yayi maganar, wani kayataccen murmushi ne ya Kubce mata tace “thank you!” Kafin ta fuce.

Tana futowa ta hango haifa dake shirin wucewa office, cikin yar sassarfa ta karaso kusa da ita tace “you!!” Da dan karfi da yasa haifa razana tace “ya Allah! Babe qin bani tsoro”

Dariya amra tayi Har set of hakoranta na futowa sosai, kallonta haifa ta tsaya yi tace “you look so happy today, is there anything that I need to know?”

Jan hannunta amra tayi tace “nothing let’s go”

Office suka wuce kafin lokacin sallah,

Karfe daya da rabi suka fito daga masjid suka wuce cafe, ice tea suka karba da snacks kafin su koma office.

Karfe hudu daidai suka fito,cikin shiri, haifa ce ta kalli amra tace “ga wanchan bodyguard din naku yana jiranki, ya zamuyi da fitan namu”

Kallon inda haifa ke nuna mata tayi kafin tace “muje”

Suna zuwa daidai inda m5 yake Har yana shirin bude kofa ta tsaya tace “hey!

Mamaki ne karara afuskanshi kafin yayi saurin kauda kai yace”good evening ma’am “

Banza tayi dashi tace “kaje Zan taho daga baya”

Bai kalleta ba yace “I have to inform s..” saurin katseshi tayi ta hanyar cewa “I messaged it him”

Tana kaiwa nan ta wuce motar haifa da ke jiranta, bude gaban motar tayi ta zauna haifa taja motar suka tafi, ganin haka yasa m5 shiga motar shima yabi bayansu.

 Gaban wani pink spa and haifa tayi parking, kafin su fito atare gwanin nan sha’awa, suna shiga ciki haifa tayi clearing bookings dinsu kafin attendee dinsu ta masu jagora, saida suka sauya kaya zuwa bathtub kafin a fara masu spa da massage, same room aka basu kowa da massage bed dinshi, hira suka sha Ana masu spa, nan haifa tasa akayi Ma amra waxing dukda fatarta babu wani gashi sosai, girly gyra akayi masu sosai inda suka sha hira sosai tsakaninsu, amra Ma ta sake sosai don Sai taji rabin damuwarta ya ragu saboda peaceful conversation da suka yi ita da haifa, shuru ta danyi aranta tana godema Allah daya bata aminiya kamar haifa.

Karfe shida daidai suka fito daga spa din, kafin su fito, saida haifa ta Kara masu booking wani session din don tana son su amra ta gyaru sosai, 

Gaban wani pink lush restaurant suka taaya haifa ta karbo masu take away na Italian food da grilled kafin su wuce, suna isa gida haifa tayi parking Har cikin penthouse din, sallama sukayi da amra kafin ta juya abunta, m5 dake biye dasu shima don tunda suka wuce spa yake binsu a baya ganin sun wuce hanyar gida yasa ya wuce inda zaije shima.

Baiyi gangancin kiran Amar ba don haka yabar alamarin tunda yasan wacece haifa a wajenta bayan wannan kuma yanda general ya bashi order akan safety dinta dole ya bi Duk wani sahu nata.

Washe gari haka m5 ya kaita asibiti lokacin Tashi nayi tace mashi ya tafi zata biyo bayanshi, this time around bai mata maganar tambayar oga ba ya taaya saida suka fita kafin ya hi bayansu,wannan Karan ba spa din da sukaje suka koma ba wani peacefully vally suka je mai hade da park, ciye ciye babu wanda basu yi ba, they had so much fun sosai kafin su koma gida.

Cikin kwana biyun nan amra ta nemi damuwarta ta rasa, don wannan treat din da haifa ke bata ba karamin kwantar mata da hankali yayi ba, gashi ta dafe da bata shawarwari akan ta kwantar da hankalinta tayi kokari ta karasa housemanship Dinta ta karbi certificate dinta, don yanxu anzo yabar da ta yanke shawarar gwara ta koma kawai Duk abunda ta tarar achan zata rungume shi ita da kannenta ba kamar lokacin da taci burin kawosu ba don zaman nan yafi na chan din, kuma anan zata dogara da aiki mai kyau don suna gama housemanship yawanci asibitocin nan uae Idan ka samu certificate mai kyau Har competition akeyi wajen daukan sabbin upcoming doctors ko nurses because they belief the younger ones are better.

Kano state Nigeria….

Ranar an kwana da bala’i a cikin gidan alhaji mustapha,rasuwar hilma ba karamin tayar da hankali hajiya labiba tayi ba don mutuwa ce tayi sanadiyar cikin da aka sameshi ta haramtacciyar hanya, abun kunyar da suke rufewa sai gashi duniya ta shida hakan, gashi yanxu komai ya tsaya ma alhaji Mustapha daman Duk kudaden da yake samu haramtattu ne kuma akan yayanshi suke salwanta kamar gadon su amra wanda ya kwace shi kirikir, karshe dai bayan ya sanya HAYA gidan yazo ya sayar dashi inda ko rabin kudin filin gidan kafin a gine shi bai samu ba, karshe kudin Ma ya tafi a banza, kasuwan ci sun tsaya mashi chak,babu gaba babu baya, yaya Duk sun tagayyara, ahankali ahankali asirin kowa yake futowa, da farko babu irin cin mugunci da Haj labiba bata sha ba wajen shi alhajin da Haj kareema harma da duniya don ko futa ta gagaresu ita da diyarta lokacin da ciki ya bullo wanda dukda yarinya tace ga wanda ya mata babu wanda ya yarda harma da daddy din wato mahaifinta,Haj kareema dai cewa tayi za ayi Ma danta Sharri, kowa dai da kashinsa a mazaunanta sa inji labiba don har lokacin babu labarin Ibrahim din, dukda suna boyewa sai daga baya haj labiba ta dau alkwarin daukan fansa, mutuwar hilma kuwa ta Kara hargitsa labiba wanda yasa ta daura damarar yanda zatayi ta rama,da taimakon Rita ta gano khady bugaggiyar yar kwaya ce, don harya soma taba kanta sannan zubda ciki babu wanda batayi ba, Haj kareema kuwa tasan halin da harta ke cikin na shaye shayen da take yi saidai boyewa takeyi da cewa shedanu ne suka shigeta, alokacin ne cikin hilma ya ya futo kafin ta rasu, babu irin cin mutunci da kareema batayi Ma labiba ba akan wannan dukda tasan itama yarta hamshakiyar kanta ce, sannu a hankali ta tsaya akan  khady harta samu natsuwa ta daina shaye shaye, cikin shekarar wani hamshakin mai kudi da suna ya futo neman aurenta wannan abun yayi ma kareema dadi ganin inda yarta zata tafi, Duk wannan abubuwan akan idanun labiba da tayi sanyi agaban su saidai basu san tarko take nada masu ba, ana sauran sati biki labiba ta tarwatsa auren ta hanyar fidda hotunan khady da tsiraicinta tana maye, wanda ta samu hakan ne ta hannun Rita, take wanda zai aure ta yace ya fasa, don bazai auro wadda ta gama lalace wa ba, ya barsu da Allah da sukayi mashi karyar cewa kamilalliya ce Har yayi niyar aurenta,sanadiyar wannan yasa aka koma gidan jiya, khady ta dawo da shaye shaye ta har yakaiga an kaita dawanau don ya taba kanta, Haj kareema tayi kuka kamar ranta saidai bata kawo cewa Duk wannan sharrin labiba ne ba, akwana a Tashi case din asma shima ya futo wanda ita kuma taje club da take satar hanya tana zuwa da saurayinta, aranar Ma haka ta fito wajen karfe goma ta saci hanya ta futa tare da saurayinta saida sukaje club suka shawu kafin su fito a make wajen karfe biyar na Safiya don su koma gida,haka suka hau hanya ita abuge shima saurayin abuge, suna hawa banban titi saurayin ya dauke wuta,don steering kubce mashi yayi nan take motar ta fara juyawa har ta gangara ta buge wata katuwar bushiya, Allah ya taimaka Akwai tsirarrun mutane da suka fito daga masallaci, nan take mutane suka fara ta ruwa don Har motar ta fara hayaki, dakyar aka futo dasu don saurayi Ma ya rigada ya mutu cikin maye wa’iyazubillah, itama Har an fidda rai aka hango yatsunta na motsi kafin aka ita asibiti, Ana kaita asibiti aka kai cigiya gidan radio, Harda police station don asibitin Ma anki attending dinta Sai taimakon gaggawa da aka bata, koda ta farka azaba ta sata kwala ihu agigice don ta samu karaya a duka kafafunta biyu, baba me gadi dake zaune yaji tahoton a gidan radio bai kawo itace ba dukda yasan tana satar hanya ta futa wani lokacin Idan ya fadama hajiya ko alhaji saisuce sharri ake Ma yayansu don haka ya daina hanata Duk sanda taga dama saita sashi hanya ta fucewanta bada sanin kowa ba, daddy dake zaune ya doka uban tagumi abun duniya yayi mashi yawa don kasuwanci ya tsaya chak, shugowar kareema a furgice yasashi saurin dagowa tare da tambayarta ko shun lafiya, wayar hannunta kawai ta nuna mashi, da sauri yayi baya zai zube, “Alhaji asma ce innalillahi na shiga uku, nidai wannan wace irin masifa ce”

Duban kasan rubutun yayi akan shafin wani blog da suka sako rahoton “an samu wata yarinya mai kimanin shekaru goma sha takwas tare da saurayinta wanda ya rigamu gidan gaskia mai kimanin shekaru ashirin da baakwai a maye akan hanyar titin beirut, daga club Duk wanda yasan iyayenta yayi gaggawar zuwa asibitin murtala”

Zama dady yayi dabas idanunshi sunyi jaa, wurgar da wayar yayi ya dafe kanshi, kareema na ganin haka tace “meyasa ma nazo wajenka bayan nasan baka da wani amfani yanxu”

Tana kaiwa nan ta Dauki wayarta ta wuce asibiti, koda ta isa taga tashin hankali don kafar asma dole sai an yanke duka,ga kudin aiki ya kai kusan miliyan shida don ba anan kano za ayi ba Sai an kaita wani babban asibiti anan abuja na kashi.

A haukace kareema ta soma kiraye kiraye don neman taimkon kudaden, don gaba daya utama business din ya tsaya don gaba daya ta tattara kadarar ta ta sayar akan case din Ibrahim, hankali tashe ta dawo gida ta harhada gwala gwalanta ta wuce dakin dady dake zaune don yanxu kullum yana gida “aikin banza aikin wifi, harka nachan rai hannun Allah mana zaune har kana iya kai abunci bakinka, ribar mai na samu a aurenka iye?”

Kallonta yayi yace “ribar me kika samu?, ke aurenki me ya amfane ni dashi, Duk wata masifa daga yayanki yake futowa saboda halayyanki na banza da ya hanaki bawa yayanki tarbiyya mai kyau, idan banci ba kashe kaina zanyi?,ke nifa na gaji dake da matsalolinki gaba daya”

Hankali a tashe kareema tace “Akwai asararre mugu azzalumi sama dakai, harka manta marainun yayan da ka wulaqanta?, karka laqabawa yayana hakki ne ke bunka shiyasa komai Naka Yake lalacewa, Wallahi hakkin yarannnan ma bazai barka ba”

Tana kaiwa nan ta fuce fuuu

Hankali atashe dady ya ture abunci sai a lokacin ma ya tuna da yayan badaru tsawon shekarun nan, tambayar kanshi ya soma yi shin ko wace duniyar suke don tun lokacin da yayi wata doguwar tafiya ya dawo nan kareema ta shaida mashi sun gudu tundaga nan bai sake waiwayon su ba.

Shi yanxu bama sune damuwar shi ba, wani irin dadi yaji don yanxu koba komai zai samu wasu Yan kudade, da sauri ya lalubo wayanshi ya soma Kiran layin amra, wayar kwata kwata baya shiga sake kira yayi shima bai shiga ba don haka ya tura mata message kan cewa yarjejeniyar da sukayi lokaci yayi da zata biyashi, idan tana son ganin Yan uwanta cikin koshin lafiya yana turawa ya saki wani irin murmushi kafin ya cigaba da cin abuncin shi da Haj labiba ta zuba mashi.

Buga buga kareema tayi ta samu kudin don Harda bashin banki ta ci da sunan mijin nata wanda saida basaja ta samu yayi signing ba tare da saninshi ba, ranar monday aka wuce da asma abuja anan cedar crest aka yanke kafafun don Har sun fara wani irin wato da doyi, haka nan bayan sati guda suka dawo gida, aranar dai labiba tayi dariya kamar ranta, daddy ma baiji dadin dawowar tasu ba don ya gane zaman kareema ke kawo mashi masifa, haka ya dunga cin duniya da tsinke shida Haj labiba da ta zama yanxu itace star a wajen shi don makuden kudade take bashi dukda bai taba tambayar inda take samu ba, kowa da abunda ke ranshi, bayan wata guda aka kawo notice na gidan, hankali tashe alhaji ke kallon takardun, zama yayi dabas yana kallo paper din inda yaga sunan labiba baro baro a jiki as wanda ta sayar sannan ga signing dinshi a jiki as wanda ya mallaka mata gidan, nan take ya fashe da kuka, ganin kukan baida amfani ya wuce sama zuwa dakinta, yana zuwa yaga wayam, babu ita babu kayanta babu sauran yayanta maza jalal da jabir, daman weekends ne, aguje alhaji ya soma surfa ashariya wanda yasa kareema futowa da asma dake rike da sandar dake taimaka mata wajen takawa, Sai sauran kannenta maza, hajiya ce tayi saurin cewa “lafiya dai alhaji”

“Inada lafiya, na shiga uku, Allah ya isa tsakanina dake labiba, Allah ya isa tsakanina dake daman saida inna ta gargade akanki ashe kece gubar da zata kashe ni”

Wiwi ya dunga kuka wanda yasa yayan Ma suka fara kuka take kuwa ya mike don kowa Ma

Haushi yake bashi ya zaro waya ya fara jibgarsu, kareema da taga karshe tashin hankali ta dunga surfa masifa da magiya akan ya kyale mata yayanta saidai fir yaqi karshe Ma Harda ita ya hada ya jibga, Allah ya taimaka aranar Muhammad ya diro kasar, wanda abunda ya tadda ya tayar mashi da hankali sosai, dakyar ya samu gidan ya dan dawo daidai inda kareema ta rantse gidan iyayenta zata kwana, haka ta ja yayanta kananun Harda asma suka Har gidan, nan gidan ya rage daga daddy sai Muhammad wanda yayi takaici da zuria irin tasu,ya dawo da tunanin su salima sai ya tadda masifar datafi tasu.

Gida dai haka ya tafi abanza don dole su Tashi don babu wanda zai iya fidda miliyan Hamsin don amaida gidan, daman Muhammad ne mai dan hali don shi ne ke aiki yanxu toh shima he’s just a start up gaba daya kudin da yake dashi na saving dinshi ko kwatan kudin bai kai ba, ishaq dai Allah ya taimake shi karatun harya gama aka biya mashi, bangaren wahab kuma achan england  yayi raping wata yarinya yar shekara sha bakwai ya hauke mata wanda yasa aka Kore shi a wajen aikinshi, yarinyar kuwa saida ya biya kudin diyya kusan duka kudinshi ya bada don in bai biya ba kalleshi za ayi anan, haka ya tarkato ya dawo ba tare da sanin iyayenshi ba, sauran dan abunda yake dashi ya fara juyawa kamar abun arziki kafin ya koma gidan jiya, rape dai ya zame mashi kamar cuta don zaman da yayi a lagos cikin wani apartment da ya samu saida yayi raping yar neighbour din dake kusa da apartment dinshi,  karshe dai guduwa ya sakeyi inda ya yanke shawarar dawowa gida, nan asad ya samu nasarar chapkarshi. Lokacin da aka kamashi ya shiga tashin hankali sosai, don mai laifi Idan yayi garkuwa da sojoji ba a magana.

Haj labiba dai tunda ta gudu ko garin su bata waiwaya ba don tasan tabbas zai je niger nemanta don haka tayi shiri na musamman tabar kasar gaba daya ita da yayanta da kudin nashi don kudin zasu isheta rayuwa ita da yayanta.

Haj kareema dai taga masifa, don komai ya gama chakude mata, matsaloli daban daban, iyayenta Ma sunyi laushi da pension mahaifinta suke managing rayuwa.

Karshe dai haka ta hakura ta dawo gidan alhaji Mustapha wanda dan dole da kuma yayanta ta dawo, gidane dan daidai Muhammad ya kama masu haya, zama dai baya dadi tsakanin daddy da Haj kareema, har kudin haya ya kare, Haj kareema dai tayi ruwa tayi tsaki ta dage akan danta bazai Kara biyan haya ba shima yaji da kanshi saboda baza su dogara dashi ba su karar mashi da nashi dunkiyar dan haka ta tayarma da daddy hankali sosai wanda yasa suka tattara suka koma katsina family house inda suka tare a bangaren inna wato mahaifiyar daddy, don shi kadaine inda zai ishesu don bangaren kakarsu amra bashida wani girman kirki gashi yana buqatan gyara sosai don har roof din ya fara banbarowa dukda gidan babu kowa don tayi rashin lafiya cikin yan uwanta da suke Yan uba suka dauketa suka maidata kauye don neman magani don anan gidan saidai ta mutu,a cikin wannan kwanakin da sukayi gaba dayansu sun chanza, ita Haj kareema masifar inna ce bata iya dauka don haka zasu Tashi da zage Zage kamar ba surukarta ba musamman akan abunci don yanxu abuncin Ma ba isarsu yake ba. 

Inka ga daddy saiya baka tausayi sosai, Duk wanna isa da duniya yanxu babu shi, gaba daya ya lalace ya zama wani iri, har lokacin bai kawo cewa alhakin marayun yarannan ne ke bibiyarshi  ba wanda Allah ya nuna mashi akan nashi yayan. Don har yanxu Idan zai samu yanda zaiyi ya cuci wani zai iya don zuciyarshi gaba daya ta gama bushewa, wannan ne ke kara maidashi kasa, yana kaskancewa.

Muhammad dai yana kokari sosai wajen tallafawa sosai don Duk wata yana turo masu da kusan 100k don su rage wani abun har ya koma jordan wajen aikinshi.

Nnamdi azikiwe international airport!!

Ahankali ya fito daga cikin motar da driver yayi parking, sanye yake cikin Riga da wando na kamfanin herms, kayan sunyi matukar karbarshi, gefen hannunshi jacket dinshi ce don saboda wether da zai tadda acahn kasar, wayanshi ne maqale a kunnenshi yana sauraron magan daga chan bangare, fito da akwatinshi driver yayi kafin wani daga cikin airport ya tunkaro inda suke, da sauri ya karba box din tare da briefcase dinshi tayi gaba dasu shi kuma Amar ya daga Ma driver hannun ya wuce cikin Airport din 

Maida hankalinshi yayi kan wayar yace “kayi kokari ka tattara Duk wani evidence daka samu, bazan wuce 5days ba Zan dawo,”

Asad dake sauraronshi a waya yace okay “oga Allah ya kiyaye”

“Thank you” ya bashi amsa bai kaiga kashe wa ba call din ammah ya shigo, kashe na asad yayi ya daga nata tare da yi mata sallama, “har Kun isa airport din ne son”

“Yea ammah,I’m just checking in,I will be back in 5days Insha Allah”

“Allah ya kiyaye hanya, call me Idan ka isa”

“Insha Allah ammah na, take care”

Kit ya kashe wayan.

Cikin airport ya shige wasu official biyu na Taka mashi baya Har ya suka isa wajen private jet dinshi da yake amfani dashi wajen emergency trip, tundaga kan benen hawa crews din jet din nashi sukayi welcoming dinshi, glass ne a fuskanshi baka ganin idanunshi yayi kyau sosai saidai fuskanshi ta dan rame kadan, zama yayi tare da daura kafanshi daya kan daya ba tare da daukan lokaci ba jet din yayi taking off.

Daddy dake gefen ta hannunshi dauke da news papers, idanunshi nakan paper din saidai kunnuwanshi nakan maganar da take yi da Amar, kallon shi tayi tace “yau bazaka je office bane?”

Kallonta yayi tana sanye da atampa mai shegen tsada doguwar Riga, gashinta a kwance Har gadon baya, daman haka ya shigo ya sameta “kin gaji da ganina ne?”

Dariya tayi tace “nina isa. Naga koda yaushe you’re busy, baka kaiwa Har yanxu baka je office ba”

Aje news don yayi ya tako inda take yace “babu maganar office Ay indai zaki dunga wannan shigar da safe babu zuwa office”

Ya karashe yana shafo fuskanta, dariya tayi tare da mikewa tace “Bari na duba Aman, tun jiya bai fito daga dakinshi ba”

Tana kaiwa karshe ta fuce daga dakin, da idanu ya bita aranshi yana ayyana abubuwan da yawa akanta.

Tana fita ya zaro wayarshi ya sake dialing contact din alif still shuru wayar baya shiga haka ya dunga neman mutanen da suke masu aiki tare na chan dubai suma baya samun su, hankali sa ne ya soma Tashi don hakan bai taba faruwa ba tunda suka fara kasuwanci tare.

Ammah na zaune daddy ya sauko cikin shiri kallonshi tayi aranta tace “hmm namiji ba abun yarda bane”

Hade rai yayi yace “Zan fita, Akwai wasu abubuwa da zanje duba achan warehouse”

Murmushi tayi ba tare da kallon inda yake ba tace “adawo lapiya”

Bai amsa ta ba ya fuce daga gidan, 

Yana fitowa driver ya bude mashi motar kafin su fuce daga compound din, kallon driver yayi yace “maitama”

Driver najin haka ya gane inda zasuje, tafiyar minti ashirin ta kawo su maitama,daidai wani gidan bene gida ne dan Madaidaici bashida girma, driver ya tsaya yayi, horn akabude kafin ya shige ciki saida ya yi parking kafin ya bude Ma alhajin ya fito, ya wuce cikin gidan, bai tsaya knocking ba ya saka key ya bude kofar tare da rufowa, tundaga bakin bene ya hangota, yar fincikar Riga ce a jikinta, wadda ko kwankwasonta bata gama rufew ba , da gudu ta taho inda yake ta rungumeshi tare da cewa “my sweet sugar I’ve missed you”

Tunda ta rungume alhaji kabiru ya sandare, wannan yarinya tana bashi wuta, haukatashi takeyi sosai, kallonshi tayi tare da fari tace “ko bakayi missing dina bane na tafi”

Da sauri yace “haba my chakwala dadi, kwana Nawa kenan Ina binki kina wahalar dani”

Kissing din kumatu shi tayi ayangace tace “sorry sugar na, my ruwan madara I have a surprise for you today yau zaka zubamin ruwan bazan hanaka ba.”

Ta karashe tana kashe mashi ido take ya sake susucewa kamar solobiyo ya dunga binta Har suka hau sama yana washe baki yace “me kikeso a duniyar nan baby meeda na , ki fadi Duk abunda kike so” dariya tayi lokacin da suka karaso daki tace “yau harda ruwa zamu kira don ka bani wuta dakyau” ta karashe tana kashe mashi idanu, anan ta fara tube mashi kayan jikinsa saida ta mashi zirr haihuwar isarsa kafin ta soma wasa da jikinshi, take ya hau sama don har ya soma fita hayyacinshi yace “dauko ruwan nan kiga, na koda don na samu karfi dan yau zakisha bulala har saiki kuka”

Biyar data aje mashi anan gefe ta mike tare da rausaya jikinta ta cuko cup dashi ta miqa mashi, karba yayi ya shanye tass kafin ta Kara zubo

Mashi wani, haka ya dunga dinka har saida ya kasa daga hannu don sakin jiki takeyi kafin ta soma aiki, ganin ya shawu ya fara maganganj yasa ta saurin kamashi tace “taho mu hau daga saman gadon karka balla ni anan kasa,” 

haka ta tattaro shi da kyar Harda tumbinsa ta maido shi kan gado ta zaunar dashi sosai ganin yana shirin rufe idanu yasa tayi saurin Danna recording a wayarta tare da saita camera dake jikin Botir din rigarta tace “sugar na”

Dariya yayi ya bude idanunshi da sukayi jaa yace “yea sweet”

“Sugar Wallahi Ina qaunarka ni Idan zaka aure ni ma Zan aureka”

“Da gaske zaki aureni baby?”

“Yes me zai hana”

Dariya yayi kafin ya dan rufe idanunshi yace “ me kike so aduniyar nan ki fada min shi ko

Menene Zan yi maki shi”

Shafa kirjinshi tayi ta danyi murmushi da ita kadai tasan maanar shi tace “ay ka gama yimin komai sugar na, ka saya jin mota ka saya jin gida, ka kaini Haj da umara ka gama min komi”

Dariya yayi yace “ay banyi maki komi ba baby”

Kallonshi tayi ganin maganin yana aiki yasa ta cewa “Toh ay ni kuma Yanxu tsorona kana da mata ni kuma bana son mai mata”

Kai tsaye yace “Zan saketa in kinaso,wannan matar ba dinta nake ba don dukiyarta data danta nake zaune da ita, saboda dukiyar da yayana ya bar masu ni kuma bazan iya zama Ina gani ba su cinye su kadai shiyasa na aureta don na samu riba biyu”

Dariya tayi aranta tace “kai wannan magani bala’I ne, aiki da sojoji abun tsoro ne hmm, kirkir bna tabamye shi abu ba yana sambatu na tabbatar Idan yana hayyacinshi bazai taba fadin haka ba”

Shafashi ta cigaba tace “hmm kace sunada dukiya sosai, sun cika kenan”

“Hahahaha kina wasa dani kenan, dukiyar da nake dashi a kasan kasa zata cutar da duka abuja”

Shuru ta danyi ta sake tambaya “wowww kai sugar ka hadu fah, ashe kaima terror ne, amma kana da wani business ne aside from company da kake running”

Dan shuru yayi yana kokarin fighting kanshi da surutan da yake saidai ya kasa yace “of course, inada Nawa business din”

“Wani irin business kenan sugar na”

Ta fada tana shafa nipple dinshi, wata uwar kara ya buga yace “zakisha mamaki Idan na fada maki”

Maida hannunta tayi kan di”ck dinshi ta dan matsa, wani irin gurnani ya buga, ganin haka yasa tace“kai inason business Wallahi ni ko illegal ne Idan Zan samu zanyi”

“Hahah harda drugs?“

“Yea har abunda yafi haka ma, kai nifa Idan ance na kashe Ma zan kashe saboda kudi”

Kamar zarrare yace “bude drower dinnan zakiga laptop, ki….”

Bata bari ya karasa ba ta dauko,ta aje a gefe 

“Kinga wannan abun ya nuna laptop din yace “wannan ce business dina, komai nawa,I’m the empire itself”

Bata gane me yake nufi ba don haka tace “ menene empire kuma sugar”

“Sunan kamfanina dana gina tun shekaru ashirin chan baya”

Ya bata amsa kamar ba shi ba,

“Wow sugar nima ka bani aiki a kampanin mana tunda kaine oga”

Janyo laptop din tayi ta kunna tare da tura mashi gabanshi tace “ ammah sugar ne kuke sayarwa a kampanin”

Typing wani long encrypted password yayi kafin ya dago idanunshi da suka yi jaa yace “drugs baby, human trafficking, bomb, bullets, gunss, babu abunda bama hadawa, hahaha”

Ya sake dariya, take gabanta ya fadi, daurewa tayi ta sake tambayr shi “wow baby harda drugs, wow irin namu de?”

“Nop wannan namu molly kenan, da kasar bilgaim ake yinta”

“Wow sugar ka sammin mana insha inji”

“Okay sugar Zan baki next time yanxu babu a jikina, ko ki bari Saina koma gida Saina dauko maki a factory”

Shuru ta danyi kafin tace wow sugar baka fada min inda kamfanin yake ba ko video ne ka nuna min na gani”

Yan danne danne yayi ya kunna mata video factory din nasu, ba karamin tashin hankali ta shiga ba don babu irin mugayen abubuwa da babu a cikin factory din, wajen gashi nan kamar dan daki saidai yanada girma sosai Sai mutane dake ciki da baza su wuce goma ba fuskokinsu a rufe”

Saurin Mika mashi wani cup din tayi tace “wow mugani”

Karban laptop din tayi kafin ta kalleshi ta gefen idanu ganin ya rufe idanu yasa tayi saurin bude connecting da wayan ta ta tura ta airdrp don Mac book ce laptop din, tana turawa tayi saurin shiga wasu files din nanma ta tura wasu kam basu shiga ba irin files din kudadeden dake cikin accounts, Harda hotuna saida ta tura duka. Tana gamawa tayi saurin kashe laptop din ta maida cikin drawer din ta dawo kan gadon ta tattara kayan data tube ta maida ta kafin ta zafi wayarta da jakarta, da gudu ta sauko kasa don anytime zai iya Tashi don gaba daya abun baya wuce minti talatin yake sakin mutane.

Driver dake zaune cikin mota ya hango

Fitowa ta a furgice bai ce komai

Ba don oga ya gargade shi akan komi ya gani ya nuna bai gani ba.

Alh Kabiru kuwa tun bayan fitarta bai dawo hayyacinshi ba Sai bayan minti talatin, da kyar ya Tashi don wani irin matsanancin ciwon kai ne ya taso mashi, gaba daya ya manta Duk abunda ya faru, abu daya ne ya iya tunawa shine lokacin data sauko daga bene da maganganun da sukayi anan qasa sai giyar daya bashi yasha bayan wannan ya kasa tuna komai, toilet ya wuce don tunanin maybe tana ciki yana shiga yaga wayam babu ita,shuru ya danyi don ya fara suspecting, kamar wanda ya tuna wani abu ya bude wardrop dinshi nan take yaga babu laptop dinshi da yake aje important documents a ciki, saurin bude dayar drawer yayi nan take yaga laptop din, hankali tashe ya tsaya kyam don tabbas a Dayan side of drower yake aje laptop, me hakan ke nufi kenan? Yar leken asiri ce? Ya bama kanshi ansa, da sauri ya maida kayanshi da wandonshi ya fuce daga dakin, tundaga nesa driver ya hango tashin hankali a fuskan alhaji, don haka yana karasowa ya bude mashi kofa ya shiga ya jasu suka fice suna fita alhaji ya fara balbaleshi “kai dan ubanka kaga sanda yarinyar nan ta fita”

“Eh, minti talatin da suka wuce ta fita”

“Toh dan ubanka shine baka tsaidata ba”

Shuru driver yayi don kamar akanshi ake shirin huce takaici “

Guest house dinshi suka wuce, nan take ya fara kiraye kirayen yaranshi ya baza su don a fara nemanta aduk inda take, nan take ma ya bada umarnin a kwasheta Idan an ganta ma.

Hameeda dai ranar taga tashin hankali don mai gadin gidanta ya kirata ya shida anzo neman ta, kuma daga gani ba mutanen arziki bane nan take ta gane cewa Ana farautar ranta, wanda ta tabbatar alhaji kabiru ne, abunda yafi tayar mata da hankali shine Kiran data dunga yima Amar baya shiga kwata kwata, kuka ne kawai ya kubce mata hankali tace kawarta ta kalleta tace “meeda kukan nan na menene”

“Baby dan Allah ki boyeni sugar faraytar rayuwata yake” da sauri wadda ta kira da baby tace 

“Ban gane ba?”

“Baby bazaki gane ba, nidai Duk wanda zaizo kice baki san inda nake ba please”

“Gaskia bazan iya boyeki ba bansan wace masifar kika kwaso ba karki janyo a hada dani, kinga Tashi ki bar jin gida”

Kuka sosai meeda tayi tace “lallai baby ashe daman ba zaman tsakani da Allah kikeyi dani ba, Toh babu ni babu ke har abada”

Tana kaiwa nan ta zura hijab dinta da niqab data zo dashi ta fuce, tana futa ta wuce tasha, bata dade da futa ba wasu gardama suka zo gidan baby, har duka saida sukayi mata don su ce Idan bata fada masu inda take ba zasu kashe ta karshe dai ta shaida masu bata dade da fita ba, don batafi minti goma ba da fita suka shugo.

Hamieda dai kauye ta nufa don buya don tabbas ta gane Ma kanta masifa akan kudi.

Amar kuwa kamar yasan zata iya nemanshi ya turama asad number dinta yace ya kirata kafin ya dawo.

Amra….

Kwance take kan doguwar kujera tana kallon tv, sanye take da doguwar Riga har kasa pink mai dan gajeran hannu cikin set of maddd kayan da haifa ta sayo mata su jiya, kayan kala goma sha biyu ne, sunyi mugun haduwa sosai don basu da nauyi gashi tana jin dadinsu, kanta yasha gyara sosai yayi coily, har wani shining yake, fatarta ta Kara kyau don tasha gyara a cikin kwanakin wanda haifa ta dage da kaita kusan kullum, fuskarta babu komi Sai dan kohl data goga a kasan idanunta da suka Kara mata kyau, Bakinta Ma ya danyi pink dalilin wani scrub da haifa ta kawo mata tana scrubing lips din dashi,jikinta babu gashi ko daya wanda ya fidda asalin kyawu na fatarta da hutu a bayyane, jikinta wani irin sohirtaccen kamshi ke fitarwa wanda haifa ta amso mata wajen ummi, aranta tana matukar jin dadin yanda mutanen kirki suke around her, duniyar tunani ta fada wanda yasa ta dan lumshe idanunta, gaba daya ta fada wani yanayi Mara misaltuwa don yanxu Duk wani damuwa ta ragu aranta sai karfin gwiwa da take samu wajen haifa da nadine, yanxu babu abunda yake budi face ta gama makaranta ta koma wajen Yan uwanta.

Bude kofa akayi kai tsaye, ahankali kunnuwanta suka soma jiyo mata takun tafiya wanda yake jin takun har cikin zuciyarta, kamshinsa ne ya biyo baya wanda yasa ta tuna da shi lokaci guda don gaba daya tunda ta dawo kusan wata guda kenan ta manta da Duk wani alamarinshi wanda ta sanadiyar haifa da taimakon Nadine ta samu karfin gwiwa, sanye yake da kayan da ya taho

Airport dashi Riga da wando na herms sai jacket dinshi daya daura ta akan kafadarshi, takowa yayi har cikin sitting room din hannushi zube cikin wandon nashi, tun daga nesa ya hango tudun ass dinta don rubda ciki tayi ta kwanta, saida ya dan tsaya na Yan mintuna kafin ya tako Har zuwa sitting room din ya tsaya daga can nesa bayan kujeran yana kare mata kallo anan tsaye, take yaji Wani yarr a jikinshi kallonta kawai da yayi, ta Kara kyau da cika sosai a idanunshi, skin dinta Sai kyalli yake yi, ya kwasa kusan minti biyar yana nan tsaye ba tare da saninta ba, gyara tsayuwan shi yayi baice komai ba still bai daina kallonta ba kamar mai tunanin wani abu, nadine data hangoshi tana shirin karasowa hannunta rike da bowl na popcorn tayi saurin karasowa tace “welcome sir”

Gaban amra ne ya bada damm,idanunta alumshe, wato hancinta ba karya ya mata ba shi din ne a tsaye don tunda ya fara takowa taji gabanta na faduwa,

Gaishesa nadine tayi kafin ta aje Mata popcorn din a kasa tadan zunguri kafarta alamu ta miqe kafin ta wuce ciki tana fatan amran tayi abun arziki, don tasan sarai idanunta biyu lokaci data taci kitchen kuma bata wani dade ba ta Juyo zuwa parlor din daman pablo ya daina kwana a gidan sai maid itama tana chan part dinta a baya.

Shi Duk a tunaninshi ma barci take don yasan Idan Har tasan yana tsaye zatayi saurin mikewa, m5 ne ya bude kofar shima hannunshi rike da trolly dinsa da kayan amfaninsa ke ciki, tun kafun ya karaso wajen ya maida idanunshi kan hanyar ya mashi nuni da ya aje ya tafi anan, ajewa kawai m5 yayi ya juya, jin alamun shuru yasa ta dan gyara kwanciyarta da yasa ass dinta dan muskutawa, take ya hadiye wani abu daya tsaya mashi a makogaro, itako tasan yana tsaye tsoronshi ya gama cikata, tana son yin abunda Nadine ta fada mata saidai tana tsoronshi sosai, tunawa da kalaman nadine da take cewa “whenever you feel like you can’t do it, just think about the pain and the lies he cost you”

Take taji wani irin abu ya daki zuciyarta tunawa da abubuwan da yake mata, kamar wanda aka tsugula ta Tashi zaune still Gabanta na faduwa ta daga hannunta sama tare da yin miqa ta buntsuru kirjinta gaba in a calming tone tace “ashhhhh”

Idanunshi Har wani qif qif yakeyi yanda ko kiftawa baya yi, popcorn din ta dauka takai bakinta nan take ya gane ashe ba barci take ba, hade rai yayi sosai don baya son raini, wato tasan da zuwanshi, yana shirin magana kenan kamar wadda tasan zaiyi hakan ta dan juyo ta kalleshi da idanunta da suka qanqance, samun kanshi yayi da Kasa cewa komi Sai binta da yayi da ido yanda danunta suke sheki, saurin kauda nata idanun tayi kafin ta sake maidashi kansa tayi kokarin fidda surprise expression tace “laaa ya…yaa, sannu da dawowa”

Ta fada tana miqewa ta tako Har inda yake jikinta na girgiza, Kasa motsi yayi don ji yayi wani iri yanda tace mashi “yaa…yaa”

To his surprise tana karasowa majestically ta bude hannayenta ta rungumeshi very tight chan beneath her breath tace “sannu da dawowa”

Nan take yaji kamar Ana tsikararshi, he can feel her chest around him, hannayenta na nade da kugunshi ta rike gam ta lumshe idanu, dake ya fita tsayi sosai yana hango tsakiyan kanta da coily gashinta dake fidda wnai kamshin mai dadi, katse mashi tunani tayi tace “Bari na barka ka huta ko,”

Ta karashe tare da zame jikinta ahankali, take yaji kamar karta fita daga jikinshi, saurin runtse idanu yayi yanaso ya bar wajen ya kasa don idanunshi ne sukayi capturing sculpture ass dinta dake cikin rigar tana tafiya kamar me cat walking ahankali harta fara hawa sama, dan juyowa tayi ta kalleshi ta sauke mashi wani lausassan smile da yasa shi jin wani iri, bazaka taba gane shi ba kwata kwata, fuskanshi na nan yanda take saidai ita tayi nasarar hango wani abu a cikin idanunshi, tana karasawa daki ta sauke wani ajiyar zuciya, tace “ya Allah… ashe Zan iya wayyo Allah naaa, meysa nake tsoro shi ne haka kamar naga malaika,” murmushi kawai tayi tace “hmm this is just the beginning, kai amma nayi mamaki, ya kasa cewa komi”

Chan kuma tsoro yadan durar mata tace “what if…” saurin kauda zancen tayi ta karasa cikin dakin ta kwanta tayi rub da ciki, har lokacin tana jin giant kirjinshi dake dauke da kamshinsa a jikinta, saurin runtse idanunta tayi tana jin wani Sabon feeling.

General ko mamaki ya hanashi cewa komai don gani yake kamar ba ita bace, har cikin idanunshi ta kalla, he can’t believe it, Toh kodai shi shock din daya sa zuciya ta ya kusa harbawa ya taba brain dinta, rasa wani tunani ma zaiyi,kamar wanda aka toshe Ma baki karshe Ma dai dakyar ya wuce sama don kamshinta har cikin kwakwalwarsa kamar Ana connecting dinshi zuwa gareta at the same time kamar an rufe mashi baki, tsaki kawai yayi ya wuce daki.

Allah ya tashe mu lafiya guys

Yau amra anyi abun arziki

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.