Best Hausa Novels

Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx

Chapter 25 of 52

Chapter 129

Update 

Unedited

Karasowa tsakiyan parlor ammah tayi,cikin mamaki tace “salima???what’s going on here”

Muryar ammah ne ta dawo dasu daga koke koken da suke, cikin sauri salima ta janye jikinta daga na amra tare da komawa gefen ammah tana hawaye, Ganin yanda take kuka yasa hankalin ammah Tashi tace “whats going on speak up?” 

Kasa magana dukansu sukayi, amra dai tunda ta tsaya a tsaye babu abunda take sai kukan zuci dana fili kanta a kasa jikinta na bari don bata ma Lura da ammah ba, Salim dake gefenta shima matsawa yayi daga jikinta ya koma wajen ammah.

Ganin haka yasa ammah kallon amra don kwata kwata bataga kamannin sani a tattare da ita ba,

Cikin natsuwa ammah ta kalleta sounding calmly tace “baiwar Allah daga wurin wa kika zo?”

Dan dagowa amra tayi ta kalli ammah, kafin ta sauke kanta kasa, don tana ganinta ta gane cewa mahaifiyarshi ce don kamanni su daya fito sosai, gaba daya kanta ya gama qullewa, meya kawo su salima gidan nan? How? Waye ya kawo su? Maysa ya kawota nan gidan? Wadannan sune tambayoyin da ta fara yima kanta, jiri ne ya fara dibanta tayi baya kamar zata fadi, da sauri ammah ta karaso kusa da ita ta rike hannunta cikin kulawa tace “are you okay?”

Kanta a kasa ta girgiza kai, kallon inda salima ke tsaye ammah tayi tace “dear jeki kawo glass of water”

Juyawa salima tayi ta wuce kitchen kafin ta fito da glass cup a hannu, gaban ammah ta tsaya ta miqa mata kafin ta koma gefe ta tsaya,mikama amra ruwan ammah tayi, saida taga ta samu natsuwa kafin ta kalleta tace “sannu, wurin wa kikazo?”

Ammah tayi tambayar tana kallonta don itama Duk a tunaninta maybe cikin Yan matan aman ne da suke zuwa,saidai tayi mamakin Ganin yanda ta rungume su salima tana kuka, itama salima dalilin da yasa ta kasa cewa komi kuwa shine saboda Duk zamansu da ammah bata taba zancen amra, and Duk sanda akayi masu tambaya a school ne cewa take Salim ne kawai sibling dinta, don ta cire amra daga rayuwar su gaba daya.

Kallonsu ammah tayi Ganin Duk sunyi shuru kafin tadan murmusa tace “salima come and seat” ta fada tana nuni da kujeran dake gefenta, karasowa salima tayi ta zauna ta kalleta, hannunta ammah ta rike tace “dear kin Santa ne?”

Sunquyar dakai salima tayi don kunyar fada ma ammah ma take ji don bata taba fada mata cewa suna da babbar ya ba.

 

Sallamar Amar ce ta katse su su duka, dawowa yayi don saida ya kawo hakan zai faru aranshi, “wa alaikum salam” ammah ta fada tana kallon hanyar da yake karasowa, sanye yake da suit din daxu, yayi kyau sosai, kwarjini da qimarshi ta futo fili sosai.

Kauda kai gefe ammah tayi tunawa da abunda ya faru jiyan, kallon su yayi duka Har ammah da yanayin ya chanza da ya shigo,samun waje yayi dan nesa dasu ya zauna akan 1seater dake facing dinsu su duka,salima ce ta dago tace “Ina wuni ya Muhammad”

Ta fada kanta a qasa, amra dai bata daga ba saidai kamshinsa ya tabbatar mata da shi dinne ya shugo sai kuma sallamarsa data doki kunnenta.

Kallon gefen ammah yayi yace “ina wuni ammah na”

Ba tare da ta kalleshi ba tace “lafiya!!”

Shuru ne ya biyo baya, ganin Duk sunyi gum yasa ammah kallonsu su gaba daya, idanunta ne ya sauka kan amar dake kallon amra shima ya kasa cewa komai, ganin haka ya tabbatar mata da sun san juna gaba daya su, rai Adan bace tace “cikin ku babu wanda zaiyi min explanation ne?”

Dan dagowa amar yayi ya kalli fuskanta yanda yaga ranta yadan baci yasa yayi gyaran murya ya kalli salima yace “kun san wannan?”

Dan waigowa salima tayi ta kalli inda yake masu nuni da amra kafin ta sunkuyar da kanta qasa tace “eh”

Nunfasawa yayi yace “who’s she?”

Kanta a kasa tace “addan mu ce, she’s our elder sister”

Da idanu ammah ta bisu su duka tana buqatar bayani, katse mata tunani yayi ta hanyar cewa “ammah,kwanakin baya banyi maki bayani akan yarannan ba saboda rana irin ta yau,“

Nuna salima da Salim yayi yace “waennan yaran ba yaran aboki na bane,marayu ne hasalima ban sansu ba kwata kwata saita dalilin yar uwarsu”

Ya karashe yana kallon amra, gaba daya suka juyo suka kalli amra da kanta ke kasa, tana hawaye,kafin su maida kallonsu kanshi, salima was so surprised da jin zancen nasa,Nunfasawa yayi ya cigaba “ranar da aka kawo su gidannan nina saka private investigator dina dayake min buncike akan su ya kawosu daga kano ,saboda……. ” nan ya kwashe duk yanda akayi da buncike a daya saka akayi akansu Har kawosu gidan da akayi, saidai bai fadi dalilin kawosu da yayi ba kwata kwata”

Wani irin kuka amra ta fashe dashi jin irin ukubar rayuwar da qannenta suka shiga, babu abunda take sai sheshekar kuka jin yanda uncle ya wulaqanta rayuwarsu,salima da Salim ma kukan sukeyi sosai don sai Yanxu suka gane komai.jikin su duk yayi sanyi,musamman salima da Duk a tunaninta amra ta manta dasu gaba daya ashe ta dalilinta suke zaune a gidan,

Kallon su salima ya sakeyi yace “kuje dakinku keda salim”

Mikewa sukayi suka wuce sama, suna wucewa amar ya kalli ammah ta gefen ido Ganin tana mashi kallon neman Karin bayani, cikin natsuwa yace  “she’s the one ammah”

Binshi da kallo ammah tayi sosai don kwata kwata bata dago zancen nashi ba saidai,

Ganin haka ya sashi Sunkuyar da kanshi don kunyar abunda ke shirin futowa daga bakinshi yake “she’s the lady that I got married to”

 Cike da mamaki ammah ke kallon bakinshi, sai a lokacin ta dago zancen, amra dai babu abun da takeyi sai hawaye ta rasa tunanin da zatayi a ranta.

Kasa magana ammah tayi saidai idanunta na kanshi don jin Karin bayani, nan take ya labarta mata tundaga lokacin da sukayi yarjejeniyar aure inda ya amince da aurendon ta samu katin kasar don ta kawo kannenta kasar saidai baice komai game da nashi dalilin auren ba wanda ya hasala ammah sosai,saida ya gama labarta mata kaff kafin yace “wannan ne dalilin da yasa ban fada maki ba, ki gafarce ni ammah, wannan auren ba komai bane, it’s just a contract marriage, daman na bari ta karasa karatunta Saina sallameta don na hadata da Yan uwanta”

Yana kaiwa nan ya kalli amra kafin ya kauda kanshi gefe,amra dai bata dago ba Har ya gama bayin nashi, saida ya gama ta fara processing komai a kwakwalwarta, she can’t believe abunda kunnenta ke jiyo mata, hawayen ma neman qafe mata suka fara yi,kwata kwata ta kasa dago ido ta kallesu don wani irin kunyan hada idanu take dasu musamman amar.

 

Shuru ammah tayi tana nazarin bayanin nashi, bata ce qala ba ta kwala ma lantana kira, lantana na shugowa tace” ki kai baquwa sama ta huta”

Kallon amra ammah tayi tace “dear go and freshen up nasan jin kwaso gajiyan jirgi”

Tunda amma ta fara magana ta kasa dagowa kamar ruwa ya cita, gaba daya tunaninta yabar jikinta, Har saida lantana tace muje, kamar munafuka haka ta miqe tabi bayan lantana kamar Ana ingizata, don idan zaka tsaga zuciyata zaka ga yanda tayi laushi,har ta wuce ta gabanshi bai kalli gefenta ba.

 

Suna wucewa sama ammah ta kalleshi fuskanta babu wasa tace “go and freshen up and meet me in my room”

Tana kaiwa nan ta wuce sama zuwa dakinta,tabar nan zaune, jikinshi ne yayi sanyi don kwata kwata baiga alamun walwala a fuskan ammah ba dukda yayi mata bayanin da take nema, mikewa yayi jiki a mace ya bedroom dinshi, gaba daya haushin kansa yake ji,meysa bai sake ta tun da wuri? Maysa tun bayan daya gani she’s not pregnant bai saketa ba? Da tuni yanxu Duk haka bata faru ba, cire suit sun jikinshi yayi ya aje a bakin gado tare da wayanshi dake ta faman ruri tunda ya shigo gidan, yasan yan jarida ne don haka baima bi takansu ba, kayan jikin ya soma tube wa ya rage daga shi sai shorts kafin ya wuce bathroom don sakarma kanshi ruwa mai dumi,yana fitowa ya shirya cikin jallabiya ya feshe jiki shi da turare kafin ya fuce zuwa masallaci don an kira sallar azahar.

Amra dai tunda lanatan ta shigar da ita guest room dake nan sama ta kasa sukuni, bin dakin tayi da kallo, dakine babba da yasha Turkish beddings, katon gado ne a tsakiyan dakin sai dressing mirror, dakin yayi kyau sosai don kana Ganin kayan dake ciki kasan foreign ne.

 

Karasawa tayi bakin gadon ta Raqube a gefe ta kasa motsawa sai hawaye, da sauri ta dafe kanta dake Sara mata sosai, take ta fara tariyo bayanin daya yi masu dasu da, saurin runtse idanunta tayi tana jin haushi kanta sosai, wato wannan ne dalilin da yasa ya hanata zuwa kano Har ta gudu aka kusa kidnapping dinta, tunawa da inda yake basu labarin yanda aka wulaqantar dasu salima akan titi tayi da inda yace saboda ita ne ya taimakesu,badan ita baba bazai sansu ba, so all this while shike kula da Yan uwanta, shine ya kubutar dasu daga ukubar da suka shiga? Shiya haskaka rayuwar su yayi protecting dinsu ya kawo su gidanshi ya maidasu mutane, she can’t believe it, she has been seeing him wrongly,take hankalinta ya Tashi ya soma innalillahi a zuciyarta don Har dishi dishi ta fara gani,tana nan zaune tana kukan takaici aka budo kofar, bata dago ba taji muryar matar dazu da taji suna kira da ammah, Har gabanta ammah ta karaso da zauna gefenta fuskanta dauke da murmushin, wani irin dadi ne ya dabaibaye zuciyarta lokaci guda datayi setting idanunta akan amra,

Kusa da ita amma ta zauna cikin kamala da dattako irin na manyan mata ta kalleta cikin kulawa “daughter bamuyi proper gaisuwa ba”

Kasa dagowa amra tayi sai a lokacin ta tuna basu gaisa ba kwata kwata, ahankali ta soma zamo da jikinta kasa harta tsugunna tana kokarin hana kanta kukan da yake ciyota na takaicin kanta don kunyar hada ido ma

Take da ammah, aduuniya babu matar da take Ganin qimarta ayanxu kamar ammah, ta dauki kannenta ta rikesu na tsawon watanni ba tare da sanin ko su waye ba kuma ta rike su da amana hannu bibbiyu, hawayen dake shirin zubo mata ne Tayi saurin hadiyewa arrarabe ta soma magana “Ina…wuni..Haj…ya”

Saurin tallabota amma tayi fuskanta dauke da murmushi ta dagata sama tace “please karki duqa min daughter” maido ta kan gadon ammah tayi kafin ta fuskanceta fuskanta dauke da murmushi “ki daina wannan kukan kinji, is not good for your health,ki saki jikinki, you’re part of us now”

Wani irin sanyi amra taji a ranta jin kalaman ammah,kanta a kasa ta kasa hada idanu da ammah, miqewa ammah fuskanta dauke da murmushi jin dadin Ganin yanda amra keda kunya tace “Bari na turo maki lanatana ta hada maki hot bath inkin gama saiki ci abunci ki huta ko?”

Anatse amra ta bude Bakinta da yayi mata nauyi tace “tohm, Nagode”

“Babu godiya okay???” Ammah ta fada tana kallonta 

Girgiza kai kawai amra tayi tana jin wani irin nauyin ammah, don kallo daya ma tayi mata tun kasa bata kara bari sun sake hada idanu ba.

Bayan fitar ammah da Yan mintuna saiga lanatana ta shigo, toilet ta shiga ta hada mata hot bath kafin ta fito ta kallieta tace “bismillah”

Dan dagowa amra tayi ta kalli lanata kafin ta kauda kanta gefe tace “na..go..de”

Murmushi lantana tayi ta juya ta fuce tare da rufo mata kofar

 

Bayan fitar lantana da yan mintuna ta miqe tsaye, inda taga lantana ta fito ta wuce, jikinta gaba daya ya gama mutuwa, ahankali ta bude kofar toilet din ta shiga tare da karo kofar, bin toilet din tayi da kallo, ya hadu sosai kamar ba a Nigeria ba, mamakin irin kudin da aka zuba a gidan take don tunda ta shigo tasan gidan manyan mutane ne, tube kayan jikinta ta soma yi don gaba daya bata jin dadin jikinta, cikin bath tube ta shiga ta gatsa jikinta, ta dauka kusan 30min a cikin bath tube din tana tunani irin iri, shes feeling so guilty, tana regretting abubuwa da dama wanda bata son tunasu gaba daya, tana gamawa ta janyo sabon towel dake jere anyi hangin dinsu ta daura kafin ta fito daga bath tube din, gaban toilet sink ta tsaya ta janyo sabon brush ta wanke bakinta kafin ta dauro alwala don ko sallar asuba bata samu tayi ba saboda tafiyar da sukayi.

Agurguje ta fito daga cikin toilet din, saida ta karaso tsakiyan dakin ta fara tunanin kayanda zata saka,samun waje tayi ta zauna ta doka uban tagumi ta fada tunani, nan take ta tuna da yanda su salima suka matsa daga jikinta kamar suna kyamarta, don kiri kiri taga zallan tsanarta da fushin su agareta, wasu irin hawaye ne suka zubo mata don kwata kwata bataga laifin su ko jin haushin su don dole suji kamar tayi neglecting dinsu, tana nan zaune akayi knocking, kafin a shigo, salima ce hannunta rike da kaya ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, dan tsaywa tayi daga nesa fusknta babu walwala ta kalli amra, kukan dake ciyota take kokarin hana kanta, yanxu wannan addar su, ta chanza gaba daya, hutu a kwanciyar hankali ya zauna a jikinta, badan akwai soyayya da shakuwa tsakanin su ba bazata taba yarda wannan addan su ce ba, don ta chanza gaba daya, su suna nan suna jimamin rashinta ita kuma tana chan tana rayuwarta, tunawa da abunda ya Muhammad ya fada yasa tayi saurin korar shedan din dake mata gangar zuga a ranta tayi kafin ta tako inda amra take zaune lost in her thoughts dan ko sallamar da tayi ma bata san tayi ta ba,tsayawa dan nesa da ita salima tayi kamar wata bakuwa tace ‘’gashi amah tace akawo maki’’

Dan dagowa amra tayi jin muryar salima, da sauri ta miqe tsaye tana hawaye tace ‘’salima!!’’

Aje mata kayan salima tayi a gefe gado kafin ta juya don ko Magana bata son tayi mata, da sauri amra ta riko hannunta, ciki kuka tace ‘’salima please wait,’’

Kasa juyowa salima tayi itama tana danne kukan dake cinta,zagayowa gabanta amra tayi ta fuskanceta ‘’salima nayi kewar ku, nayi kewarku sosai,life was so hard babu ku ate dani, tunda nabar kasar nan ban samu kwanciyar hankali ba, kullum da tunaninku nake kwana nake ta…’’

Ani irin kallo salima tayi mata tare da cire hannunta daga nata cikin zafin rai tace ‘’kinyi kewar mu adda? Ah ina Kenan?, adda pleas im not ready to talk to you now”

Kallonta amra tayi cikin kunci ta fara kokarin kama hannunta tace ‘salima please believe me….”

‘’no adda,how do you expect me to believe that?, wallahi baki damu da halin da muka shiga ba da kin damu da alokacin da aka kusa kashemu na kira a waya zakiyi gagawar dawowa, kinsan irin wahalar da muka sha kuwa’’ salima ta fada tana kallonta hawaye na zarya a fuskanta, kafin ta cigaba ‘’mun sha azabar da ko a lahira sai haka, we spend months cikin daki babu haske, munyi wanka babu sabulu, mun kwana cikin dauda,abunci ma gagarar mu yake, zauciyar salim ta kusa bugawa, ya Ibrahim ya kusa raping dina, daddy yayi min dukanda saida nunfashina ya kusa daukewa, babu cima mai kyau, hatta ruwan sha gagarar mu yayi, kullum cikin kuka da fargabar abunda zai faru da salim nake, shin kinsan irin masifar dana shiga sanadiyar amfani da wayar da nayi wajen kiranki?kullum da kukan rashinki muke wuni har allah ya akwo mana ya Muhammad, our life saviour, sai yanxu daga baya zaki dawo rayuwar mu kice kinyi kewar mu and you think I will believe that?, wallahi bazan taba yarda da maganar ki ba adda, you neglect us bayan kinsan bamuda kowa sai ke’’

Ínnalillahi amra ta fara maimiata a zuciyarta, hawayen dake zarya a fuskanta na kara gudu kamar race, kalaman saima sun daketa sosai, shes regretting komai, shes regretting kaaratunma dataje tayi, duk zaman datayi achan bata taba kawo zasu shiga worst rayuwa kamar haka ba, kwata kwata bata taba imaging haka ba, and ahaka ta zauna kusan shekara uku da rabi, kannenta suna cikin azabar rayuwa da kuncin rayuwa, while ita tana chan tana cima mai kyau,

Dariyar takaici salima tayi ganin amra ta kasa cewa komai

‘’im so disappointed, as I expect, adda baki da explanation din da zaki yi min da zan yarda’tana kaiwa nan ta fuce daga dakin tabar amra a tsaye tsayuwar ma data gagareta sulalewa tayi kasa tana kuka sosai a fili, ta dade anan tsugunne ta kasa rarrashin kanta,ta dauka kusan rabin awa kafin ta lallaba kanta ta miqe don wani irin jiri jiri takeji sosai, baking ado ta koma ta zauna tana kukan zuci don hawayen ma kafewa yayi, ganin kukan bashi da wani amfani yasa ta janyo doguwar rigar mai hade da mayafi cutton da salima ta aje mata,ta saka, saida ta gama sawa aka sakeyin knoking, lanatana ce ta  shigo hannunta dauke da tray na abunci, a tsakiyan dakin t aje mata tray din tace ‘’bismillah ga abunci’’

Mikewa amra tayi fuskanta babu walwala ta kalleta tace ‘’dan allah ina ne gabas’’…nuna mata alkibla lantana tayi kafin tace ‘’bari na kawo maki abun sallah’’

Gaban wardrop lantana ta tsaya ta bude tare da zaro sallaya, tana daukowa ta tako gaban amra ta shimfida, kallonta amra tayi tace ‘’nagode’’, murmushi kawai lanata tayi kafin ta fuce daga dakin, tana fita amra ta fara gaba tar da sallah, tana idarwa ta doka uban tagumi,kalaman saliama suna tsaya mata arai sosai, data tuna da abunda ta fada sai hawaye shar har saida ta gala baita, kanta ne ya soma sara mata sosai ga yunwa dake ciyota don bata ci komai ba throughout the flight,jiki a mace ta mike ta nannade sallayan tare da zama gefen gadon, kallon haddaen tray din da lanatana ta aje mata tayi, kwata kwata yanxu ma tsoron cin abunci takeyi, don gani take she doesn’t deserve to eat, kiri kiri ta hana kanta cin abunci saida taji yunwar na neman nakasa ta, kafin ta sauko kasa, bude warmers din ta fara yi, fried rice ne sai gizzard sauce harda pepper chicken daga gefe, yawunta ne ya tsinke don abuncin yayi kyau a ido ga kamshin abuncin dake bugarta, anatse ta janyo plate ta danyi serving kanta kadan ta soma ci, loma daya biyu tayi ta aje don jin kamar zatayi amai, tunawa da hours din data dauka babu komi a cikinta yasa ta aje abunci ta hakura kawai don normally idan bataci abunci ba takanyi amai idan taci mai nauyi yunwar bazai sa abuncin ya zauna ba saidai ruwan tea, aje abunci tayi ta koma bakin gado ta zauna tana tunanin rayuwa.

Bangare amar bayan ya dawo daga masjid sama ya wuce direct saida karaso yabi lanatan dake fitowa daga cikin daya daga cikin bedrooms din dake nan saman,tabe baki yayi ya wuce part din ammah, da sallama ya bude kofar bedroom dinta, a zaune ya taddata kan royal bed dinta, tunda ya shugo ta bishi da kallo masu ma’anoni daban daban,kafin ta kauda kanta, still yanayinta bai sauya ba game dashi.

Jiki a mace ya karaso ya zauna kan carpet din dake tsakiyan dakin zuwa gadon, kanshi a kasa ya anaste soma magana “barka da rana ammah na’’

Kai tsaye ta bashi amsa ba tare da ta kalleshi ba ‘’barka’’

Dan shuru ne ya ratsa don ya kasa cewa komai, itama dai karantarshi ta fara yi, kafin tayi gyaran murya, ‘’muhammad’’ ta kira sunanshi a kausashe babu wasa, dan dago da jajayen idanunshi yayi ya kalleta yace ‘’naam’’ kafin ya sauke kan kasa, kasa hada idanu yayi da ita, tana ganin haka ta cigaba ‘’ina fatan duk bayanin dakayi min shine abunda nake buqatar ji aka rage ba kuma baka kara ba’’

Bai dagoba ya bata amsa ‘’eh’’

‘’kayi bayanin dalilin auren yarinyar nan dakayi don ka taimaketa kuma saboda yarjejeniya da kukayi tsakaninku saidai baka fahimtar dani naka dalilin auren ta da kayi ba ta bangarenka?, bana son ka boye mun komai, ko dazun da kake bayani banyi tambayar nan ba sabda inason muyi maganar tsakanina dakai’’

Kasa dagowa yayi haka zalika ya kasa cewa komai, tana ganin haka ta gane kunyar ta yake ji ita kuma tana son tasan komai don jin dalilin auren don abunda yafi fado mata arai idan ta tuna da auren da yayi shine maybe ko buqatar mace ne ta sashi yin hakan ba tare da ya shawarceta ba ko ya fada mata, don matse fuska tace ‘’this should be the last time da zanyi maka Magana kayi min shuru Muhammad, im all ears explain’’

Runtse idanunshi yayi gam kafin ya budesu, kanshi har wani sara mashi yake yace ‘’na aureta ne saboda doctor yace I have only one chance, kuma dole na kusanci mace idan banyi ba bazan taba haihuwa ba, I have no other option shiyasa na aureta’’

Wani irin tausayinshi amah tashi, batayi tunanin ospermia nashi yakai last stage ba, zuciyarta ne ya karye sosai, tausayinshi y agama baibaye ta dama tausayin kanta, ashe dalilinshi nayin aure Kenan, allh yaso batayi saurin judging dinshi ba don data biye zancen da daddy yake dole zata yarda kila fasikanci yakeyi da neman matan banza, ashe auren ma da yayi don yak are martabarshi da mutuncinshi yayi don tabbas duk wanda yaji cewa he has last chance of having a child dole kota hanyar fasikanci ne zaiyi abun,

 

Nunfasawa tayi ta danne zuciyarta tace ‘’tun yaushe ka kai ospermia yakai stage 3’’ tambayanshi tayi tana mai kallonshi yanda ya sunkuyar dakai, amar dai yayi mamkin jin tambayar tata don baiyi tunanin tasan ospermia dinba, saidai sanin mahaifiyar tashi wayyayiya ce kuma mai ilimi dole zatayi research yasa yace ‘’stage 3’’

Ahanakli ta soma furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun a cikin zuciyarta bata bari ya dago yaga yanayin ta ba don saida hawaye ya zubo mata, don tasan daga last chance din nan indai ba a samu ba shikenan, ‘’toh yanxu is she pregnant?’’ ta tambayeshi kai tsaye

Shuru ya danyi chan kasan maqoshinsa baka ma jin abunda yake cewa sosai yace ‘’no’’

 

Daidaita natsuwarta tayi cikin tawakkali ta kalleshi ta soma magana

 ‘kayi babban kuskure Muhammad, shiyasa naji zafin yin gaban kanka da kayi ba tare da shawara dani ba, duk abunda babba zai hango yaro bazai iya hangowa ba koda ya hau kan dutse ne,da tunaninka da hankalinka? Na farko dai banga laifinka nayin auren da kayi ba don ka kare martabarka da mutuncinka, na biyu haihuwa ta allah ce basai nayi maka dogon bayani ba tunda gashi allah ya bamu kai because dada also battle with the same ospermia that you had which kayi inheriting’’

Kanshi a kasa feeling so sad yace ‘’im so sorry amah, ban fada maki bane saboda banason ki zama disappointed,saboda you always want me to have a family and naga yanda kikeson jikoki im so sorry’’

Saurin tarar nunfashinsa tayi tace ‘’don’t be sorry son, haihuwa na allah ne, how could you think that I will feel like youre a disappointment to me?im very proud of you, I will always be by your side saidai bakayi daidai ba kuma dole na nuna maka hakan, you made a mistake, tun farko ni mahaifiyarka ni ya kamata ka fada ma damuwarka,yanxu dub aka gani, aure fa baa bun wasa bane, haihuwa idan kana da rabo zaka samu’’

Dan dagowa yayi ya kalleta yace ‘’ammah bawai auren zama dindin din bane, its just a contarct marriage, kuma duk mun samu abunda muke nema, nayi alqawarin sakinta ma ayau daman tun farko that was the plan, idan na saketa saina hadata da yan uwanta, ‘’

Da sauri ammah ta dago ta kalleshi ranta adan bace tace ‘’this is what I’m talking about, ku yaran zamani kun maida aure ba komai ba, kun maidashi kamar wasa, yanxu duk iliminka da wayonka muhammad?allah baya son saki amma ya halasta shi, meysa bakayi tunani ba kafin kuyi auren? Yanxu kace sakinta zakayi ko?shin kasan idan ka saketa ka maidata bazawara? Yau ko ta sake aure bazata taje a matsayin budurwa ba koda kuwa duk duniya babu wanda yasan kunyi aure daga kai har ita, saboda haka yanda kukayi aurennan ba tare da sanin kowa ba haka zaku zauna bazaka saketa ba,tunda nake da mahaifinka saki bait aba shiga zukatanmu ba don haka kaima bazakayi ba, kaida bakinka kace min marayune yarannan, basu da uwa basu da uba, shin ka manta ayanxu kaine gatansu har ita matar taka?’’

Gabanshi ne ya bda dam, daman abun da yake tsro Kenan shiyasa yayi komai cikin sirri yanxu amah zata bata mashi plans din komai, anatse ya soma mata Magana cikin kwantar da murya yace ‘’but amah ita ta buqaci hakan, itama ta buqaci sakin’’

Kai tsaye amah tace ‘’ita tace maka ka saketa?’’

‘’eh’’ ya fada anaste

Kallonshi ta sakeyi tace ‘’wani irin zama kukayi muhammd kaida ita?har ta buqaci ka saketa’’

Dan dagowa yayi idanunshi sunyi jaa yace ‘’ammah please…bana buqatarta a rayuwata, yarjejeniya ce kawai mukayi kuma yanxu komai yazo karshe, just as I promise to freee her anytime I pleased yanxu lokaci yayi wallahi bana buqatarta’’

 

Ran ammah ne yayi mugun baci dajin kalamashi, lokaci guda taji kamar ma ba Muhammad ne ke Magana ba, her only Muhammad, saidai tunawa da halinshi yasa dole tayi buncike akan zaman da sukayi, rai abace tace ‘’wato ta gama yi mata amfani Kenan? You will free her when youre pleased?’’

Dan kasa yayi da kanshi don saida maganar ta gama fita daga bakinshi ya tabbatar da abunda ya fada,’’ammah please, wannan auren ba komai bane yarjejeniyace please’’

Dan daka mashi tsawa tayi tace ‘’shut up Muhammad, ka bani kunya’’

Tana kaiwa nan ta miqe ta barshi nan zaune ta fuce daga dakin.

 

 

Bangaren daddy yau kwananshi daya a headquter na sojoji an kaishi wani dakin buncike na manya manyan criminal, bait aba tsammanin case dinshi yayi girma sosai ba saida aka aje mashi prove da evidence din allegation akanshi, ba tare da tsoron komai ba yaqi accepting charges din don duk laifinshi da aka karanto mashi a wajen cewa yake bai aminta hakan ba sai an aje mashi prove da evidence, asad dake gabanshi dariya akwai yayi ya kalleshi kafin ya kunna mashi video dinshi dayaje viral, daddy dai tunda ya kafama laptop din idanu hankali a tashe ya kasa cewa komai, ya kasa gano waye yayi mashi wannan bankadar, saida video din yakare kafin asad ya mashi playing na meeda wanda ta dauka a cikin flash nan take daddy ya harzuka don baiyi tunanin an gano gaskia ba he cant even believe it, don zuciyarshi ta gama mutuwa to the extent that yasan asirinshi bazai taba tonuwa ba don yana da bokan da yake mashi sirihi akan business dinshi, hankalinshi gaba daya y agama dashi don yasan tashi ta gama karewa, kallonshi asad yayi ganin ya fara zarewa yace ‘’haba ay na dauka kai shege ne, da uban me da kake takama d kake tunanin gaskia bazata fito ba har kana cewa baka yarda da duk abunda ake zarginka dashi ba to ga evidence nan, wannan ma somin tabi ne’’

Takowa asad yayi daidai kunnenshi ya soma rada mashi ‘’ina ji maka tsoron haduwa da general, he will cut you into pieces for killing his father’’ arazane alhaji kabiru ya dago yana kumfar baki ‘’baku is aba, babu wanda ya isa ya kaini kasa’’ saida y agama ciga baki asad ya dago ya kalleshi, fuskanshi babu far a yace ‘’ka cigaba da cika baki, ka roki allah kada ya dauke ka daga nan Nigeria don kila anan kotu bazata yanke maka hukuncin kisa ba chan musammam case dinka da yaje international don wallahi gunduwa gunduwa za suyi dakai, kai anan dinma ni nayi maka alkwari zai kasha azabarda saika gwammace ka mutu kawai’’

Wata irin dariya daddy yayi ya kalli asad yace ‘’kai kana tunanin zan kara kwana guda anan ne? nan da 24 hours bazaka ganni ana ba’’

‘’lallai baka san girman laifinka ba alhaji, nasan yanxu tunaninka mutanenka ko da connection dinka?’’

Matsowa asad yayi ya dafe table din gabansu ya kurama alhaji kabiru idanu yace ‘’kana tunani akwai wanda zai fito don ya kareka ayanxu?babu wanda zaiyi risking kanshi don duk wanda ya shafeka yana hannunmu ayanxu’’ yana kaiwa nan ya fuce yabar alhaji kabriu cikin tsoro,don da za a auna jininshi akalla zaikai dari da saba’in,

After like 2 hour wasu sojoji murdaddu suka zo suka  dauke daddy zuwa wani daki dake jere da karafuna, tunda aka shugo dashi hannayenshi nade da ankwa harda kafarshi hankalinshi ya gama tashi, kallon asad yayi daya zauna agefe guda ya daura kafa daya kan daya yace ‘’bakai kace zakayi mana taurine kai ba, to kuwa zaka ci ubanka dan yau jikinka saiya fada maka cewa kana cikin sojoji’’

Nan take asad ya bada commad ajanyo daddy, alahji kabiru na ihu yana zazzaga masu zagi haka suka janyo shi,asad ne ya kalleshi yace ‘’kana da bakin zagi yanxu Kenan? Uban me kake takama dashi? Youre nothing but a piece of trash,’’ yana kaiwa nan ya miqe da hannunshi da katuwar kaca ta keken hawa ya nannade a hannunshi kafin yace ‘’ku daure min shege’’ haka sojojin nan idanunsu jaja wur babu alamun rahama suka daure dadi, babu irin ihu masifa da cika baki da daddy baiyi ba, saida asad ya mashi jini da majina har bakinshi yamutu, don kusan suma uku yayi suna watsa mashi ruwa, basu barshi ba saida nunfashinsa ya soma daukewa, haka suka kwasheshi suka maidashi dakin da ake aje criminals suka rufeshi.

 

Hankali atashe amar ya fito daga dakin ammah yama rasa tunanin da zaiyi, dole fa saiya saki yarinyar nan don tun tasowarshi babu abunda ya taba shiga tsakaninshi da mahaifiyarshi saita dalilinta, ran shi amugun bace yake, haka ya sauko kasa ya wuce dakinshi yana furzar da huci mai zafi.

Salima dai tunda tabard akin da aka sauke amra ta wuce dakinsu ta kwanta kan gado ta fara kukan da take dannewa, harga allah duk duniya babu wadda suke su sama da amra, don ita kadaice danginsu kuma yar uwarsu ta jini, bazasu taba chanzata ba saidai zuciyarta na yi mata ciwo idan ta tuna da ta barsu sunsha wahala ba tare da ta waiwaye su, fadar irin wahala da suka sha ma bata lokaci ne, sai gashi ta dawo alokacin da basa buqatar ta, shiyasa ko sau daya bata taba maganarta ba a gidan, shi salim daman ba Magana yake ba,

Salim daya shigo dakin ganinta kwance tayi rub da ciki tana kuka yayi saurin karasowa inda take tare da dafe afadarta, dan dagowa salima tayi ganin shi yasa ta miqe zaune ta rungumeshi tana kuka sosai, shima riketa yayi sosai yana hawaye,saida sukayi mai isarsu ta dago ta kalleshi tace ‘’salim kaga adda ko? Sai yanxu zata dawo bayan mun gama shan wahala, ta manta damu ta gina rayuwarta achan sai yanxu zata dawo’’

Girgiza mata kai salim ya fara yi shi babu bakin Magana, yanxu yayi wayo sosai yasan duk abunda take nufi don yanxu yakai shekaru goma sha hudu, goge mata hawayen yayi ya mata alamun tayi smiling, murmushi salima tayi ta dungure kanshi tace ‘’kai wai yaushe zaka fara Magana ne? kodai ka zama kurma?’’ washe hakoranshi yayi ya ja hannunta suka fito daga cikin dakin zuwa qasa, nan suka samu ammah a zaune a sitting room hannunta rike dawayarta, tana ganinsu tace ‘’dear har yanxu kukan dadin haduwa da big sis akeyi’’

Dan murmushin yaqe salima tayi ta karaso gabanta tace ‘’ammah na yunwa nake ji’’

Murmushi ammah tayi mata ganin tayi doging tambayar tata tace ‘’ga abunci nan a dining kuje kuci ku gama a fara shirin islamiyya’’

‘’okay ammah’’

Suna gama cin abunci suka wuce sama domin shiryama islamiyya, karfe uku da rabi daidai suka sauko, kallon su amah tayi tace ‘’toh a dawo lafiya,dear ayi karatu sosai’’

Murmushi sukayi mata atare kafin salima tace ‘’insha allah ammah sai mun dawo’’

Suna fita ammah ta maida kallonta zuwa ga wayarta.

Anatse ya soma fitowa cikin cikin shiri, kananun kaya ne a jikiinsa riga da wando wanda sukayi mashi kyau sosai kafanshi sanye yake da givenshi wanda ya fidda kyawun kafafunshi, cikin isa ya tako har parlorn yace ‘’ammah zan fita’’

Ba tare da ta kalleshi bat ace ‘’adawo lafiya’’

Wani iri yaji don normally idan zai fit aba haka ammah keyi mashi ba, da murmushi take kallonshi ta amsa shi tare da jero mshi addua,jiki a mace ya juya ya fuce daga gidan ranshi duk babu dadi.

 

Ammah na ganin fitar shi ta wuce sama don an kira sallar laasar, dakin da aka sauke amra ta fara wucewa don jin shuru, da sallama ta bude kofar ta shiga, ganin ta kwance a kasa yasa tayi saurin karasowa tace ‘’subhanallah daughter ya da kwanciya akasa?, bakisan babu kyau mace na kwanciya a kasa ba’’

Amra da tun budewar kofar da amma tayi ta farka tayi saurin miqewa zaune jiki a mace, muryarta dakyar ma take futowa tace ‘’barka da yamma hajiya’’

Saurin kama hannunta amma tayi ta jata bakin gadonta kalleta cikin kulawa  tace ‘’ki daina kirana da hajiya, call me with ammah, kinji ko?yanda na dauki su salima haka na daukeki,’’

Sunkiyar dakai amra tayi cikin jin kunyar ammah tace ‘tohm ammah’’

Murmushi amma tayi tace ‘’yauwa dear, kina buqatan wani abu?’’

Akunyace amra ta amsata da ‘’ah ah’’

Hannunta amma ta kamat cikin kulawa tace ‘’karkiji kunya na don ina matsayin mahaifiyarshi kinji, ki daukeni kamar yanda su salima suka daukeni a matsayin uwa kinji ko daughter’’

Wasu irin siraran hawaye ne suka zubo mata tace ‘’toh’’

Da sauri ta goge su don kar ammah ta gani, ahankali ammah ta dan soma janta da surutu don ta sake saidai hakan bai samu ba sabda gaba daya a tsorace take, ga damuwa shimfide a fuskanta, ganin haka yasa ammah cewa ‘’daughter ki huta kinji ko?idan kina buqatan wani abu don’t hasitate to tell me okay?’’

‘’insha allah’’ amra ta fada cikin sanyi

Fita daga dakin amma tayi ta wuce dakinta, zama tayi tunanin abubuwa da dama, sai alokacin ma ta tuna da wani daddy, wayarta ta janyo ta bude social platform, nan take taga komai, kwat kwat bata wani tada hankalinta ba don ta dade da zargin yana da wata kullaliya, akwai lokuta da dama da take zarginsa akan abubuwa musamman idan wannan baqon nashi wanda ke zuwa duk karshen shekara, wani lokacin bata sanin time din da mutumin ke tafiya bayan wannan ma saidai taji zancen tafiyar baqon a bakin yan aiki, akwai lokacin da ta tambayi lanatana ma nan ta shaida mata ay alhaji kabiru ya saukeshi a dayan part dinshi, shima part din tana zargin akwai abunda yake ajewa a ciki don kwata kwata baya yarda ana shigar mashi part din wanda tun tna damuwa akan sanin menene a part din har ta hakura.

 

Amar na fita masallaci ya fara wucewa domin yin sallar laasar ana idarwa ya shige cikin daya daga cikin motocinshi dake pake a compound, bai tsaya ko ina ba sai nigerian headquarters, yana zuwa asad ya tarbeshi suka wuce investigation room, zama sukayi kafin asad yasa a fito da alhaji kabiru, yanda aka fito dashi ranga ranga zaka dauka kamar matacce ne, ajiye shi sojojin sukayi kan kujerar da ake aje criminals kafin asad yasa a watsa mashi ruwan sanyi, afurgice kuwa ya farka kamar zautacce yana surutai, dakyar ma yake bude idanunshi da suka kumbura suntum, kallonshi amar yayi yana jin wani irin zafi aranshi ace wai kanin mahaifinka ne haka, wani irin zafi yakeji aranshi idan ya tuan shine wanda ya kashe dada,

‘’I hope baka fara regretting rayuwanka bat un yanxu don this is just the beginning, I promise you the pain will be worst than this, wannan somin tabi ne, how could you? Baka tsaya da alhakin mutane akanka ba saika kashe rai? You killed dada? Just because ya gano sirrinka?’’

 Idanuna mara ne sukayi jaa sosai, take yaji kamar ya kashe alhaji kabiru kozaiji dadi aranshi saidai bazaiyi hakan ba don so yake sai yasha azabarda saiya gwammace yam utu, kallonshi alhaji kabiru yayi da idonshi guda da yake iya budewa ya kyallyace da dariya yace ‘’kanason nabaka labarin yanda na kashe ubanka?hahah drug daya na jefa mashi a juice ya karasa’’

Azafafe amar ya miqe idanunshi yayi jaaa kirjinshi har wani irin bugu yake bammbamm ya shakoshi da hannu daya,take kabiru ya hango lahira don saida kullutun idanunshi ya fito, asad na ganin haka yayi saurin kama hannun amar ‘’oga calm down’’ ay inaa amar baya jin abunda yake fada kwata kwata, karshe dai hannu asad yasa don ya janye hannun amar daga wuyan kabiru bai Ankara bay a jishi a kasa duk girmanshi amar ya zubar dashi a kasa, kallon yanda alhaji kabiru ke tarin mutuwa asad yayi kafin yayi saurin kiran sojojinshi don su janye amar, suma dai suna karasowa da hannu daya amar ya zubar dasu duka, saida ya tabbatar alahji kabiru ya shaku da kayau kafin ya turashi baya gaba daya kasa a sume, miqewa asad yayi yana mamakin irin karfi na amar kamar doki, da hannu daya duk a watsar dasu su kusan uku.

Azafafe amar ya fuce daga cikin wajen ya shige motarshi rai abace, wani irin rough driving yakeyi wanda yasa mutane kauce mashi hanya, road safety kuwa da sunga plate number shi basa gigin tareshi ma kwata kwata,

Ikon allah ne kawai ya dawo da amar gidan, koda yayi parking ya dauka kusan awa guda a cikin motar, saida aka kira sallar magrib ya fito daga motar ya wuce masjid kai tsaye.

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.