Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 46 of 52
Chapter 148
Update
Unedited page
Hannunta biyu ta daga ta Dora mashi su duka akan laps dinshi, ahankali ya waigo ya sauke idanunshi akan kyawawan babies din guda biyu da suke kama dashi kamar an tsaga kara, shuru yayi ya kafa masu idanu kwakwalwanshi ta kasa processing, babu abun da ammah keyi sai murmushi taba hawayen farin ciki, salima na Ganin haka ta ajiye baby no3 a gefen Yan uwansa,kafin ta fuce daga dakin, yanda yaran suke a jere a kan laps dinshi ya kafa ma idanu ya kasa dauke idanun nashi, baby girl na tsakiya an nade ta da pink towel, sauran mazan ma an daure su da blue towel.
“Ammah Ina kuka samu babies haka” ya tambayeta yana kallon yaron har lokacin ya kasa dauke idanunshi akan su,
“Dawa suke yi maka kama?” Ta jefa mashi tambaya, Har lokacin idanunshi na kan yaran bai dauke ba,kanshi ya gama kullewa don yaron kamar cabon copy dinshi, kamannin sun baci sosai, babu zato babu tsammani yaji furucin ammah“yayanka ne”
Da mamaki ya dago yana kallon ammah, fuskanshi dauke son jin qarin bayani, Har lokacin ita yake kallo fuskantarta “son Allah ya azurtaka da matarka da triplet, yayan Ka ne, kuma jininka”
Bin Bakinta ya dunga yi da idanu don lokaci guda yaji kamar an toshe mashi qwaqwalwa,
“Yes son yayanka ne jininka, Ka tafi Ka bar Aisha da cikinka na tsawon wata shida a jikinta, kaga ikon Allah ko? Duk wannan futar da kaga munayi Har kake complain asibiti muke zuwa,”
Dip taga kamar baya fidda nunfashi, saida ta dan dafashi tana hawaye, “son Allah ya nuna mana ikon sa, Allah ya rubuta zaka ga jininka anan duniya, babu ruwan allah da wani zancen likitoci idan har ya kaddara kana da rabo a duniya to zai baka alokacin da baka taba tsammani ba”
Duk wannan maganganun da ammah keyi kasa cewa komai yayi har jikinshi ya soma bari, abun mamaki saiga hawaye na saukowa akan fuskanshi, general guda yana hawaye, ammah na hawaye shima yana hawaye yana kallonta yana kallon babies din.
Kallon hannunshi ammah tayi dake karkarwa yana son taba su ya kasa gaba daya shock din daya shiga bai taba shiga irin shi, kanshi ya kasa daukan abunda ammah ke fada mashi, waennan yayanshi ne? Tabbas ko ba a fada mashi yaga kammaninshi a fuskokinsu, kamar an dauki fuskanshi an saka masu dukda suna jarirai, wani ikon Allah kenan, don gaba dayansu replica dinshi ne,
Yau ne tana ta biyu a duniya da ammah ta ga hawayen shi, don ya kasance mutun mai taurin zuciya, saidai wannan ya taba shi sosai,abunda baka taba expecting ba, abunda Ka cire rai dashi sai gashi allah ya baka lokaci guda babu zato babu tsammani.
Bude bakinshi tayi da kyar voice dinshi na cracking ya soma magana kamar zai shine “Am…mah am…””
Kasa karasa abunda yake don fada yayi hawaye na zarya a fuskanshi, hannunshi na karkarwa kamar mazari, ammah na Ganin haka ta mike tsaye ta dauka baby number 1 da idanunshi ke bude tarr yana lasar baki alamun yana son abunci, sauran biyun kuwa barcin su suke yi.
Tana daukan babyn ta Dora mashi babyn a hannunshi, saida ta taimaka mashi ta talla be babyn don Har lokacin hannunshi karkarwa yake, he can’t believe it abun kamar a mafarki, saida ammah ta daura mashi babyn a hannunshi ya tabbatar da gaske ne kuma jaririne a hannunshi,
Kallon jaririn ya dunga yi yana hawaye har lokacin bazaka taba tantance yanayin da yake ciki ba da facial expressions dinshi, hannunshi daya ammah ta dago ta Dora akan kirjin babyn, yana jin heart beat din yaron yayi saurin runtse idanunshi sai a lokacin ya samu kuzarin bude baki ya soma magana “Allahu akbar, Allahu akbar Allahu akbar,”
Yana hawaye yana kabbara, yana Kiran Allah, “ammah I’m I dreaming? Please don’t wake me up,”
“Ba mafarki kake ba son,” ammah ta fada tana hawaye tana mashi murmushi, kallon babyn yayi ya dagoshi zuwa kirjinshi, ya kwantar dashi, yana kwantar dashi wasu hawayen na sauka a fuskanshi, “Alhamdulillah!!!! Allah na gode maka Allah na gode maka”
Haka ya dunga furtawa, kallons inda ammah ke tsaye yayi, “ammah gashi rikemin haka inason nayi sujudu shukr,”
Karban babyn ammah tayi ta kwantar dashi gefe kafin ta dauke sauran suka ta kwantar dasu, tana kwantar dasu yayi saurin mikewa ya sauko kasa ya fuskanshi kibla, ya dade a kanshi a kasa yana godiya ga Allah kafun ya dago ya daga hannunshi yana hawaye, jikinshi na bari kamar wanda ke jin zazzabi,kana ganinshi kasan yana cikin wani emotional moment.
Mikewa yayi cikin sauri ya tsaya bakin gado ya dan rankwafo ya zuba masu idanu, kamar wani zautacce haka ya soma dariya yana kallonsu,
Hannunshi daya ya sanya ya fara taba cute hannayensu daya bayan daya, ammah dai na daga tsaye a gefe ta rike Bakinta tana hawaye,
Juyowa yayi a zafafe ya kalli inda ammah ke tsaye yace “ammah yarana? Yarana ne? Yayana ne ya Allah” ya karashe yana kama kanshi, fadin irin farin cikin da yake ciki bata lokaci ne,this is the best day of his entire life, abunda bai taba tsammani ba kwata kwata, yanxu waennan jininshi ne yayanshi ne? Allah daya tashi bashi saiya bashi uku lokaci guda lokacin daya cire rai gaba daya ya fidda ran samu Har karshen nunfashinsa,
“Yes son yayanka ne su duka naka ne”
Daga kanshi yayi sama kamar zaiyi ihu yace “ya Allah I’m a father, ammah I’m a father nine babansu, ya Allah…”
Haka ya dunga maimaitawa yana kallonsu yana daga hannunshi sama, gaba daya ya gama zaucewa kamar ba Amar ba,
Ganin haka yasa ammah dake ta faman murmushi ta janyo hannunshi ta zauna dashi tace “wannan farin cikin karyasa Ka fadi fah,”
“Ammah bazan fadi ba, I’m a hero”
“Yea you are my son, and I’m so proud of you son, kayi tawakkali saiga shi Allah ya dubeka”
“Ammah Zan iya daukansu” Amar ya tambayeta kamar wani yaro yana murmushin da nan taba ganin irinshi ba akan fuskanshi,
“Kaida yayanka saika tambayeni son?” Ammah ta fada tana kokarin daukan yar jaririyar, tana dauka ta ya mike tsaye, “ka zauna son”
“Toh Tohm bari na zauna,” ya karashe yana zama cikin zumudi at the same time yana kallon sauran yaran.
Yana zama ammah ta ajiye mashi jaririyar a hannunshi, tana daurata kuwa ta bude idanunta tarr, “ammah wannan ma baby na ce?”
“Yes son Duk naka ne, baby girl ce wannan”
Maido da idanunshi yayi kanta, yana kallonta hawaye na sauka akan idanunshi baima san yanayi ba,
Saurin rungume babyn yayi a kirjinshi, wani irin sanyi na zagaye gaba daya sassan jikinsa.
Ammah na murmushi tana kallonshi tana godiya ga Allah.
Zama dai Amar kasa zama yayi haka ya mike yana zagaye dakin da babyn a hannunshi, saida ammah ta dauki gaba dayansu ta dunga bashi daya bayan daya, yanda yake karban yaran daga hannunta ma with so much affection saida yasa ammah hawaye, da kyar ammah ta samu ya zauna Har lokacin babies din na hannunshi mazan while macen na hannun ammah, sun dauk awa guda suna abu daya shida ammah, minti kadan zai dago yace “ammah yara ne? Jin I’m a father”
Haka zata amsa shi itama “yes son you’re a father, and you’ll be the best father to them”
Tana kaiwa karshe zai girgiza kai ya soma kissing dinsu ta ko’ina Har lokacin yana hawaye,
Shuru ya danyi yana nazari kafun ya ajiye babies din kan gadonshi a hankali, yana ajiyesu ya sake karban na hannun ammah, ammah dai yau taga ikon Allah don ko minti biyu batayi da daukansu zai amshe, yanxu ma haka ma cewa yayi “ammah kawo ta,”
Ammah na murmushi ta miqa mashi babyn “careful ammah,” ya fada yana murmushi.
Zama ammah tayi gefenshi bayan ta bashi jaririyar,tana zama ta kamo hannunshi daya ta rike tana kukan murna “I’m so sorry ban fada maganar pregnancy din ba son, nayi hakan ne saboda Ina son nayi surprising dinka daga baya kuma naga yanda kake treating mahaifiyarsu wanda yasa nayi tunanin gwara na bari sai kunyi settling kanku kafin na shaida maka” tana kaiwa nan ta girgiza mashi kai tana hawaye,
Saurin kallon inda take yayi ya cire hannunshi daga nata ya maidashi kan fuskanta ya soma goge mata hawayen kan fuskanta, “ammah na, today is the most beautiful and amazing day of my life, this is the best gift of my life, bansan da wani irin baki Zan gode maki ba yanda kika kawo mun su, thank you ammah na thank you!!!”
“No son bani zaka yima godiya ba, aisha zaka yi ma godiya, ita ta haifa maka waennan angels din” Nunfasawa ammah tayi tana hawaye ta cigaba “Aisha ta gama yi mana komai a duniyar nan, having her in your life shine the best thing that has ever happen to you Muhammad, itace ta baka wannan farin cikin da babu wanda zai taba baka irin shi”
Sunkuyar da kanshi yayi yana jin takaicin kanshi da yanda yayi treating dinta, yanxu da wani ido zai kalleta kenan, ashe abubuwan da ya dunga yi mata tana shanyewa a wannan lokacin da cikin shi a jikinta, wani irin haushi da takaicin kanshi yake ji sosai, a zuciyarshi babu abunda yake nanatawa sai “I’ve messed up”
“Son” ammah ta kirashi, ahanakli ya soma dago kanshi idanunshi tayi jaa sosai, “kaga abunda nake fada maka ko? Daka rabu da ita da shikenan Ka rasa kenan gaba daya, what you’re feeling now is nothing compare to how you will feel idan da Ka sake ta kuma Ka gano tana da cikinka, shiyasa nake na haneka da sakinta kuma na dunga nanata maka karka zo kayi dana sani, you keep on pushing her kamar ba matarka ta sunna ba, now kalla” ta karashe tana pointing triplets, “kalla abunda ta haifa maka”
Sauke kanshi ya sakeyi kasa, jikinshi yayi sanyi sosai, inda za a bude zuciyarshi a take babu abunda za a gani sai sunan aisha.
Shuru ne ya biyo bya kafun ammah tace “naka tuna munyi fushi dakai, bani jikoki na” tana kaiwa nan ta amshe baby girl, tana karban ta ta dauki baby boy, kafin ta nufi hanyar futa “ammah please ki bar min su anan”
“Inna bar maka su zaka basu Nono ne?” Ammah ta tambayeshi, saurin girgiza kanshi yayi alamun ah ah, “Zan turo salima ta daukan min mijina yanxu”
Tana kaiwa nan ta fuce, tana futa ya mike ya hau kan gado ya zauna gefen Dayan babyn daketa barci abunshi, yar mici micin hannun babyn ya dauka yana kallon fuskan babyn “ my look alike, open your and I’m your daddy”
Haka ya dunga ma babyn sambatu shi kadai Har salima tayi sallama, tana shugowa ta kafa mashi idanu tana kallonshi tana murmushi,shi baima san ta shigo ba saida tace “ya Muhammad ammah tace a kawo baby”
Kallonta Amar yayi kafin yace “kin iya dauka ne?”
“Laa na iya mana yaya” ta bashi amsa
“No jeki kawai Zan kawo shi da kaina “yana kaiwa nan ya maida kallonshi ga babyn yana sumbatar kumatu shi, salima dai yau taga sabon ya muhammd don wannan dai ba ya muhammad din data sani bane, tana shirin futa ya katseta “bude bedside drawer nan ki dauka abunda ke ciki duka wannan tukwicin ki ne”
Cikin sauri salima ta karasa inda yace taje, tana zuwa ta bude bedside drawer, 100 dollars ne wrapped biyu, saurin zaro idanu tayi waje tace “yaya dolars ne fah”
“Yes duka naki ne, tukwaicin kawomin baby da kikayi”
“Yaya sunyi yawa….”
Bata gama fada ba ya daga mata hannu don haka ta dauki wrapper daya ta juya ta nufi hanyar futa “Nagode yaya Allah ya Raya mana triplet,”
Juyowa yayi ya mata murmushi kamar bashi ba yace “thank you”
Jinjina kai kawai salima tayi ta fito daga dakin ta wuce sama tana mamaki, tana haura wa sama dakin ammah ta wuce, tana shiga ammah tace “Ina babyn kuma?”
“Ya Muhammad yace ban iya rikewa ba shi zai kawo”
Tabe baki ammah tayi kafin ta dan murmusa, bataga laifinshi ba,tsananin farin cikin da yake ciki ne.
Kallon inda amra ke kwance tayi da babies din data kwantar mata daga gefe don ta basu zamzam sunsha saboda ruwan Nono bai zoba tukunna Har suka koma barci abunsu.
Fitowa ammah tayi daga dakin don zuwa kitchen saboda ta Dora mata pepper soup din kayan ciki da kanta da kunun gyada saboda su zatafi buqata ayanxu.
Tana fitowa corridor saiga Aman shima yana hauro wa, “ah ah kaga su second daddy”
Dariya aman yayi ya kalli ammah yace “Wallahi ammah Bakiji yanda nake ji ba, kamar ni akayi ma haihuwar nan,gidan namu yau Har ya Kara haske “
“Son ba dole ba, Ay dole gida ya Kara haske an haifo min mazaje Har biyu”
Kyal kya cewa sukayi da dariya, waigowa sukayi gaba Dayan su don jin kukan baby, amar ne rike da baby number 2 jikinshi har Rawa yake fuskanshi kamar zaiyi kuka, ammah na Ganin haka Tayi sauri karasowa ta amshi babyn don ya karaso saman, “ammah meysa yake kuka? Ko mu koma asibiti”
“Kawoshi kaga, yunwa yake ji ne shiyasa” ammah ta karashe tana jijiga babyn, “Toh ina abincin a bashi”
Wani irin kallo ammah tayi mashi yayi saurin sauke kanshi kasa yana murmushi, “yauwa Aman, prescription din na hannuna ko? Kaje ka amso sauran magungunan daga nan Ka taho da peak din new borns saboda asamu a basu” ammah ta fada tana kallon aman,
Amar ne yayi saurin katseta “Bari naje na sayo madaran”
Girgiza kai kawai ammah tayi Ganin yanda yake rawar jiki, abunda ya dan tsaya mata arai shine tambayar amra da baiyi ba, itama bata ce mashi komai ba don zuba mashi idanu tayi taga yanda zaiyi.
“No kaida Ka dawo jiya, ga gajiya a tattare dakai, Ka bari ya sayo tunda Harda magungunan da bath karba ba a pharmacy din asibitin zai sayo”
Shugowa Aman yayi ya kalleshi kafin ya miqa mashi hannu for the first time yace “congratulations bro, Allah ya Raya mana yasa su zama mahaddatan alqurani”
Cikin sauri Amar ya amshe hannunshi bakinsa yaqi rufuwa yace “thank you so much brother, thank thank you”
Murmushi ammah tayi tana jin dadin ganinsu a haka “Ay dole kayi amshi godiya kuwa don dashi akayi labour, shi ya dunga dawainiyar kai kawo a cikin asibitin”
Wani irin dadi Amar yaji dayasashi cewa “jibi monday ko? you’ll resume as managing director”
Gwalo idanu Aman yayi, cikin mamaki “wow muma hardamu kenan, mun ci albarkacin angels ammah a tayani godiya”
Dariya Duk sukayi gaba Dayan su kafin aman ya sauka kasa.
Kallonta Amar tayi kafin ya maida kallonshi ga babyn da Har yayi barci abunsa, yana son tambayarta abu ammah yana jin kunya, da kyar ya tattara courage dinshi yace “Zan ita ganin ta?”
Kanshi a kasa ya karashe magana, kallonshi ammah tayi kafin ta dan tabe baki tace “no, tana hutawa yanxu saidai anjima”
Ya dauka ko haushinsa taji daya tambaya don haka yace “Ammah please…..”
“Sai yanxu Ka tuna da uwar tasu? Dazu da kake zumudi ba mantawa kayi da ita ba, kaje sai zuwa anjima saikazo ka ganta “
Jiki a mace ya amsata da “tohm” yana kaiwa nan ya juya ya sauka kasa yana waigowa gaba kallon babyn.
Yana wucewa ammah ta dan murmusa kafin ta wuce daki ta ajiye baby no 3 kusa da maman shi shima.
Koda ya koma daki shima kasa yin komi yayi yama manta ko wanka baiyi ba balle brush don pjs dinshi ne a jikinshi, cikin zumudi ya shige bathroom Har yana Yan wake yayi wanka agurguje ya fito yana waqa “I’m a father, father of triplets”
Haka ya dunga waka shi kadai yana juyi, fuskanshi Har lokacin dauke da murmushi, saida ya gama wakarshi kafin ya shirya.
Yana gama shiri ya janyo key dinshi tare da wayarshi ya fuce daga dakin.
Koda ya fito daga sitting room babu kowa anan kasa don haka ya wuce sama direct don bazai iya jiraba soyake ya ganta kawai.
Yana karasowa saman ya tsaya bakin kofar bedroom din, ahankali ya soma bude kofar, yana bude wa ya rufe ahanakli, salima ya gani a zaune ta dauka jaririn a hannu tana jijiga shi saboda ya Tashi, tana ganinshi kuwa tace “ya muha…”
Saurin maqale maganar Tata tayi Ganin yanda ya mata alamu datayi shuru.
Ahankali ya soma takowa ya karaso bakin gado, tunda ya fara takowa gabanshi ke faduwa Har lokacin daya tsaya bakin gadon, kwance take ta juya ma kofa baya don baya Ganin fuskanta, sanye take da doguwar Riga ta Shan iska tana barci, gefenta baby 1 da little princess dinshi daya lakaba mata ne, wani irin murmushi ne ya kufce mashi daya sa kumatunshi lobawa, salima dai kasa dauke idanunta tayi akanshi tana nanata wato ya Muhammad yana murmushi daman aranta.
Ya dade a tsaye yana kallon bayan amra kafin ya dan Rankwafo daidai kunnenta ya soma mata magana yanda babu wanda zaiji don ko salima dake zaune gefen gadon bataji me yake cewa ba.
Yana gamawa ya miqe tsaye ya kalli salima ya soma mata magana ahankali “take care of my little okay?”
Girgiza mashi kai salima tayi kafin ya fuce daga dakin.
Yana futowa ya sauka kasa direct wajen motarshi ya shige ciki, yana kokarin tada motarshi baba mai gadi ya taho yana mashi barka, yanda baba me gadi ke zuzutashi yana ce mashi “Allah ya Raya Yan uku baban yan uku” abun ya mashi dadi sosai don Har wrapper guda ya zaro ta Yan dubu dubu daga cikin darsh board dinshi ya bashi.
Amra bata Tashi ba sai wajen karfe hudu na yamma, tana Tashi ammah jata zuwa bathroom ta gasa ta sosai saboda danyen jikinta, tana gamawa ta futo ta bata wuri don ta samu tayi wanka, tana fitowa kuwa ta tadda already ammah ta ajiye mata kayan da zata saka.
Kallon kayan tayi don akan gado ta ajiye mata su gefe guda kuma jariran ne a kwance an chanza masu kaya da alamu har ammah tayi masu wani wankan, wani irin lausassan murmushi ta sauke don sai yanxu ta samu kuzarin kallonsu da kyau, agurguje ta shirya ta feshe jikinta da turare mai kamshi na ammah kafin ta koma kan gadon ta zauna, tana zama tayi bismillah ta dauka baby number one ta shafa kanshi, barci yakeyi hankali kwance sai kuma yan matsu mutsu da yakeyi, fatar hannunshi ta shafa tana kallon fuskanshi sai irin ta ubanshi, mamaki takeyi sosai yanxu waennan duka yayanta ne kuma daga cikinta suka futo, idan ta tuna wannan wani irin dadi yake ji mata misaltuwa, gaba daya kamar rayuwar ta ta masu gida biyu don gaba daya ayanxu hankalinta da tunanin ta ya koma ga yayan.
Bata taba tsammanin Allah zai bata yaya har uku ba lokaci guda dukda tasha wahalar labour dinsu don haihuwar su tazo mata da sauqi da wahala at the same time don lokaci guda suka dinga fitowa after 2 mins,
Sumbatar kumatun babyn tayi kafin ta fara karanto mashi addua a kunnenshi, haka ta dunga yi masu daya bayan daga tana yi tan ajiyesu, saida tazo kan jaririyar ne ta kaga mata idanu, wasu irin hawaye ne suka fara zubo mata don tana Ganin jaririyar ta tuni da mahaifiyarta, wato haka iyaye ke jin da zarar sun haihu, farin cikin wannan yanayin Mara misaltuna ne.
Ammah ne ta shigo dakin da sallama hannunta rike da flask sai salima dake biye da ita da katon tray da aka Dora kayan tea akai, suna shugowa saiga maids ma sun shugo da warmers, anan tsakiyan dakin ammah tasa suka ajiye, amra na dagowa ta kallesu su duka tace “sannu da aiki ammah, sannunku duka”
Maid dinne sukayi saurin amsawa tare da congratulating dinta kafin su fuce.
Zama ammah tayi gefenta while salima ta wuce wajen little princesss ta dauketa don bata gajiya da daukanta
“Sannu daughter ya jiki? Hope yanxu bakyajin kasalan ko?”
Sauke kanta kasa tayi tace “Alhamdulillah ammah babu kasalan saidai abunda baza a rasa ba”
“Sannu allah ya biyaki da gidan aljanna”
Salima ne Tayi saurin amsawa “Ameen grandma ammah”
Dariya dukkansu sukayi gaba daya kafin ammah tace “kwarai kuwa fadi ki kara, na zama grandma”
Dariya suka sakeyi Harda amra, nan baby boy ya fara tsala kuka, kallon inda yake ammah tayi tace “oh ni maryama, wannan miji Nawa Akwai kukan yunwa dazun nan fa na baka madara”
“Laa ammah ya akai kike ganesu?” Salima ta tambaya tana jijiga little princess
“Ya za ayi bazan gane su ba, kinga wannan” tayi nuni da wanda yake tsala kukan
“Shine mijina na farko don shine ya fara zuwa duniya haka doctor yace. Kuma inkin lura zakiga ya danfi dan uwansa chubbiness kamar mamanshi”
Dariya sukayi gaba dayansu, amra dai kasa daukan babyn tayi dake tsala kuka wai ita kunya, ammah na Ganin haka ta daukeshi ta fara jijigashi “salima ajiye princess ki zubama daughter pepper soup dinnan da kunu ta sha, da zafi zafin shi”
“Tohm ammah” salima ta amsa tana ajiye little princess.
Karfe takwas da rabi daidai yayi parking, yana gama parking ya futo daga motar, fuskanshi tarr sai annuri take, kiran securities yayi gaba dayansu, suna zuwa ya bude bayan motarshi,cike motar take maqilda manya manyan ledoji da kwalaye gaba da baya, haka yasa suka dunga jidar kayannnan suna shiga dashi cikin gida suna gamawa ya rufe motar ya shige gidan, ammah dake saukowa daga sama salima na biye da ita da princess a baya suna saukowa suka ga uban tulin kaya a parlor, sallamarshi ce ta katse su, “barka da dare ammah”
Ya fada fuskanshi wa sai kamar mai yallabai Maclean
“Son kaine kayi wannan uban sayyayan?”
Girgiza mata kai kawai yayi kafin ya kalli inda salima take, bai Lura da princess dake bayanta ba saida ammah tace “jeki dauko min flask sun a kitchen”
Tana juyawa ya hango princess “heyy!!! What’s that? Wannan abun bazaiyi suffocating little princess ba?”
Kallonshi ammah tayi aranta tace “oh basa banba kenan”
Kafin ta maida idanunta kan salima da yake nuni da bayanta.
“Wuce ke abunki” ammah ta fada mata kafin ta maido da kanta gareshi
“Banson iyayi fah, wani irin suffocating, you muhammd tun daga yanxu har Ka fara suaucewa akan yaya? Toh Wallahi idanuna idonka Ka kiyayeni “
Sauke kanshi yayi kasa baice komai ba, “meke sayo ne haka kuka cika mana parlor”
Cikin zumudi ya kalli ammah yace “kaya ne for my littles”
“Ahh Masha Allah Toh Allah ya kara budi, Ay daka fada min zakayi sayyaya dana ce Ka bari saboda mun saya komai saidai kawai basusan triplet zata haifa bane”
Zama sukayi anan parlor ammah ta soma duduba kayan daya sayo, ganin kayan suna da yawa don shima kanshi baisan aradun abubuwan da ya sayo ba yasa yace ma ammah “let me fresh up ammah”
“Okay son” ta amsa shi
Yana shige wa dakin Aman ya dawo shima da nashi ledojin.
Karfe Tara da rabi ya fito daga bedroom, yayi wanka ya sauya kaya, fuskanshi Har lokacin dauke da murmushi gaba daya gajiyar daya kwaso ta operation tabi jiki don haka manta da wani operation.
Lokacin daya futo babu kowa a kasa don haka ya wuce sama direct, part din ammah ya shige da sallama, yana shiga sitting room dinta ya tadda salima kwance akan couch tana waya baima bi ta kanta ba ya wuce cikin bedroom din anatse.
Ahanakli ya soma bude kofar dakin bakinsa dauke da sallama cikin kamewa, ammah ne kawai a zaune bakin gado tana petting angel don yan uwanta sunyi barci, duban dakin ya soma yi ganin amra bata nan yasa ya karaso cikin dakin ya zauna gefen gadon inda ammah ke zaune.
“Barka da dare ammah”
“Barka dai son,”
Kallon boys dinshi ya fara yi da suke ta barci abunsu acikin wani haddaden baby net sunsha kayan gayu, kallonsu kawai da yayi kara sanya ya mashi zuciya yayi.
Kallon inda yake kallo ammah tayi kafin ta maida kallonta gareshi, “oh Anya Muhammad zaka barmu mu sarara kuwa”
Sauke kanshi yayi kasa yana dan murmusa baice komai ba kafin ya maida idanunshi kan kofar bathroom jin alamun Ana shirin fitowa daga ciki.
Ahankali ta bude kofar bathroom din ta shugo kanta a kasa tana dan dingisawa, sanye take da wasu kayan daban ba na dazun ba saboda sukayi wankan dare inda ammah ta taimaka mata, batama kura dashi ba kwata kwata daya kafeta da idanu sai muryar ammah dataji
“Toh Ka Tashi Ka bata waje ta zauna ko?” Ammah ta fada tana kallon Amar dake zaune bakin gado ya kafe amra da idanu ko kiftawa bayayi, he missed her a lot, her stubbornness da komai ma, don lokacin da ya tafi operation nan ya tabbatar da feelings dinshi akanta, sai gashi kuka abunda ya dawo ya tarar na haifa mashi triplet da tayi, mukamin data samu a cikin zuciyarshi babba ne sosai wanda baya jin zai iya kallon mace bayan ita,yana jin kamar Duk futar nunfashinsa da sunan amra yake fita, ayanxu ya gama deciding bazai sake danne what he has for her ba, to hell with the ego, haka yake fada ma kanshi kullum don idan yace baya son ta yayi karya.
Saurin dagowa tayi nan idanunta ya sauka cikin nashi, kwata kwata bata san ya dawo ba sai yanxu da take Ganin shi bazata, saurin kauda kanta tayi gefe fuskanta a hade harya karaso, tana karasowa ya mike tsaye ya bata waje, koda ya matsa saida ta dan dago ta kalleshi kafin ta kauda kanta, mamaki ne ya gama cikata, Anya wannan general data sani ne, wanda ta sani murmushi ma wuya yake balle dariya,
Tana zama ammah ta mike don yanda ya kafe amra da idanu tasan idan har ba waje ta bashi ba zai iya yin rashin kunya ma agabanta wanda batada kuzarin Ganin hakan, don yanda yake kallon amra kamar zai cinyeta anan tsaye.
Mikewa ammah tayi ta ajiye mata princess a kan cinyanta ta fuce daga dakin don ta basu waje.
Ammah na futa kamar jira yake ya karaso kusa da ita ya dan rankwafo daidai fuskanta idanunshi na kan princess, Ganin tana barci yasa yayi pecking kumatun ta yana murmushi, amra dai mutuwar zaune tayi don gaba daya ya gama cikata da mamaki, bata gama tunani ba saida taji ya dauke princess ya kwantar da ita gefen gado kusa da Yan uwanta, yana kwantar da ita ya dawo inda amra ke zaune gaba daya mamaki ya gama cikata don Har sakin bakinta tayi batama san tayi ba,
Sanyin lausassan hannunshi dataji akan fatar hannunta ne yasa ta dago da idanunta ta sauke akanshi, baiyi wata wata ba ya matso ya rungumeta a jikinshi ya saqalo da kanshi tsakanin wuyanta, sun dauka kusan minti biyar a haka, itakam tunda ya rungumeta ta kasa motsawa, abunda yafi bata mamaki shine yanda taji saukan wani abu kamar ruwa akan wuyanta, bata san mene ne saidai tana jin saukan abun akan skin dinta,
Ahanakli ya soma magana cikin wata irin murya kamar ba Tashi ba “Aisha, aisha Allah yayi maki albarka, Allah ya faranta maki yanda kika faranta min, Allah yayi maki albarka, bansan da wani irin words zanyi using ba wajen gode maki, kin gama yimin komai a duniya, thank you so so much,”
Yana kaiwa nan ya saketa ya dago da fiskanta, abunda ya daure nata kai shine Ganin ruwa ruwa kamar hawaye akan fuskanshi, kwata kwata bata kawo hawaye bane don tasan that’s impossible don haka ta kauda kanta ta hade rai don daman tasan hakan zai kasance, Duk wannan abunda yakeyi akan yayanshi ne, ba akanta ba saboda ta haifa mashi yaya,
“Now tell me , me kike so a duniyar nan fada min Duk abunda kike so zanyi maki shi”
Babu tsoro ko fargaba ta dago ta kalleshi “ka sake ni,”
Da mamaki yake kallonta son bai gane me yake nufi ba din haka ya saki shoulder dinta daya rike, ganin kamar bai gane abunda yake nufi ba yasa ta sake cewa “I mean divorce me, ban son aurenka akaina”
Saurin mikewa yayi tsaye idanunshi sun danyi jaa ya kalleta “what do you mean?”
“I mean Ka bani takardata, bana so…”
“Shut the fuck up..” ya daka mata tsawa
“Karki sake wannan maganar, babu saki a tsakaninmu never, musamman yanxu da zuria ta shiga tsakanin mu”
Rai abace amra ta dago ta kalleshi “wow, finally Ka nuna komai basai nayi tunani ba, saboda yayanka ko”
Da sauri ya koma ya zauna kusa da ita “no aisha Karkiyi wannan tunanin please, I want you by my side ba yaranmu kadai ba, I want us to clear the air between us komai ya wuce”
Fashe wa amra tayi da kuka tana jin wani takaicin zancenshi
“Just like that? So it’s easy for you to say that Komai ya wuce? Ka manta abubuwan da Ka dunga yimin? Ay Wallahi babu abunda zaka fada min da Zan yarda yanxu, ni kaje kaina yana ciwo”
“Aisha please!!!” Ya fada yana kallonta fuskanshi harta sauya
Da sauri ta dago ta kalleshi har wani sauke murya yake.
Tabe baki kawai tayi bata sake kallon Ind a yake ba, ammah ce ta shugo dakin don taji ihun nasu daga parlor,
Yana ganin ammah kuwa ya mike ya wuce wajen yayanshi yayi kissing dinsu daya bayan daya kafin ya dawo gaban amra, babu zato babu tsammani taji lebenshi a kumatunta agaban ammah, wani irin haushi da takaicin shi ne ya turniketa, ga kunyan ammah data turniketa.
Ammah Dia kauda kanta tayi gefe tace “saida safe ko”
Juyawa yayi ya fuce “saida safe”
Washe gari da asuba ma haka ya shigo dakin kafin ya wuce masjid, a zaune ya tadda amra tana bama little madara feeder, da sallama ya shigo, tana mashi kallo daya ta dauka idanunta, karasowa yayi har bakin gado ya kalleta ita da little yace “morning our mommy, and good morning to my little princess” ya fada yana kaima little peck, yana gamawa ya daga yayi pecking go shin amra, da mamaki amra ta dago ta kalleshi “mey hakan kuma”
Sauke muryarshi yayi kasa Ganin ammah na shirin fitowa daga bathroom “it’s a morning kiss for my little and my wifey”
Tabe baki amra tayi ta mashi wani irin mugun kallo tace “sabon salo, that’s not going to work on me”
Murmusawa ya danyi ya shafa fuskanta anan tsaye da yake “we shall see mummny triplet”
Wani irin mugun kallo ta mashi tana jin haushinsa da takaicinsa tana son ture hannunshi babu damar hakan saboda duka hannayenta tana amfani dasu wajen bama little kulawa.
Saida ammah ta futo ya gaisheta ya fuce daga dakin.
Girgiza kai kawai ammah tayi ta hau kan sallaya saidai deep down tana jin wani irin dadi sosai.
Bayan ya dawo daga masjid ma saida ya shiga dakin lokacin sun shiga wankan safe don haka ya tsaya yayi kissing babies dinsa ya dunga masu magana shi kadai kafin su ammah su futo daga bathroom, ammah ce ta fara futowa don ta barta tayi wankan sabulu, ammah na futowa kuwa ya fara mita “ammah adaina barinsu su kadai please, Zan turo salima ta zauna dasu kafin ku gama”
Tana kaiwa nan ya fuce zuwa dakin salima, haka ya taso ta ya tura dakin bayan yayi mata kashaidin kula mashi da triplets dinshi kafin ya wuce dakinshi.
A cikin kwana abubuwa da dama sun faru, inda ta bangaren daddy triplet da mummy triplet sai babu sauyi don gasa mashi aya take a hannu, kwata kwata taqi sake mashi shikuwa babu abunda yake sai chusa akanshi don idan har taci galaba akanshi to tabbas yasan za a samu matsala don ammah zatabi bayanta ne, ayanxu in kukaga general kamar bashi ba, ya sauke wannan ego din yayi laushi, yanda yake nan nan da amra kuwa abun Har mamaki yake bata kuma yayi mata wani banbarakwai cos ba haka ta sanshi ba a sanin da tayi mashi he’s so tough., donko dariyanshi wahalar gani take mata achan baya saidai yanxu yanda ya suke kanshi abun Har daure mata kai yakeyi sosai.
Gata kuwa babu irin wanda triplet basa sha a wajen mahaifinsu da ammmah, kullum cikin order kayan wasa kayan jarirai da abubuwan amfaninsu dana mahaifiyarsu suke kamar basa jin zafin kudi.
After 6days…..
Gobe suna don haka yayi kokarin bin yanda sunna ta gindaya, da kanshi yake ya sayo shanaye guda uku da raguna uku da kayan abuncin da za ayi sadaka a raba saboda babu wani shagali da zasuyi don yace bayason wani taro, dukda ammah taso ayi saboda saidai yaqi yarda da hakan , tunda ya fita sai dare ya dawo agajiye, yana shugowa sitting room ya tadda ammah a zaune da Salim a gefenta yana kallon little princess dake kuka, da sallama ya shigo ya zauna kusa da ammah, yana gaisheta ya amshi diyarshi, ammah dai babu abunda yake sai murmushi saida ya gana yi mata kisses din daya saba kafin ya mika ma ammah ita ya wuce part dinshi.
Yana shiga ya wuce bathroom yayi wanka ya futo ya sauya kaya, yana gama shiri ya futo sitting room, kusan karfe Tara Ganin basa nan yasa ya wuce sama direct don yanzu hawa chan baya mashi wahala.
Da sallama ya shige bedroom din, amra ne zaune sai ammah a gefenta tana mika mata wani hadin kunu na musamman don har yanxu ruwan Nono bai zoba.
Da idanu yabi amra da kallo, kanta babu dankwali gashinta ya sauko Har kasa saboda a jike yake sai sheki takeyi abunta.
Sanye take da wata Riga mai sirin hannu, tunda ta mashi kallo daya ta duake kanta Har yazo ya zauna, yana zama ammah ta mike ta fuce don ta basu waje.
Ammah na fita ya hade rai ya daura kafa daya kan daya, ya soma magana cikin kame wa, “ajiye wannan abun”
yanda yayi mata magana sounding very serious yasa ta ajiye ta hade rai, nuni yayi mata da baby number one yace “kawo shi nan”
Mikewa amra tayi ta duaka babyn ta tako Har Inda yake nan ya dunga binta da idanu harta karaso kafin ta ajiye amshi babyn a hannunshi.
Tana ajiye babyn ya gyara zamanshi ya dago babyn ya daidiaci kunenshi yayi mashi addua kafin yayi mahai huduba yana gamawa ya mika mata shi, nan taje ta ajiye shi ta dauko babyn number two nan ma hudubar yayi mashi kafin ya mika mata, yana Mika mata ta dauko amshi little, karban ta itama yayi ya mata huduba yana gamawa ya sumbaceta ya mika mata ita, tana karban ta ta wuce kan gadon ta ajiyeta, tana dagowa taji ya rungumeta ta baya yayi kissing bayanta, “Masha Allah wifey, mun samu Yunus(hamad) badaru (hamid)and maryama, bar maki saiki zama mata nickname daya dace da ita”
Dan juyo da ita yayi ya daga hannunta daya tare da nashi yayi nuni da baby number one yace “wannan shine yunus takwaran dada kenan Allah yayi mahai rahama, wannan kuma mahaifinki ne shima Allah yayi mashi rahama, sannan ga little princess dina nan ammi na, Allah ya Raya mana su”
Saurin runtse idanu amra tayi hawaye na saukowa akan fuskanta intace bataji zuciya ta yayi sanyi ba tayi karya, hawaye takeyi sosai Har yana diga akan hannunshi, yana jin haka ya juyo da ita ya share mata hawayen “Allah ya masu rahama, stop crying wifey”
Idanunta a rufe tana jinshi yana ta maganganunshi, babu zato taji lipa dinshi akan Bakinta, wani irin passionate kiss yake mata wanda bai taba yi mata shi ba, idan tace bataji saqin da yake aika mata ba tayi karya, kukan Hamad ne ya dawo dasu daga yanayin da suka shiga don haka Tayi sauri kwace jikinta ya wuce bathroom tana hawaye.
Ammah ne ta shugo dakin jin kukan yayi yawa tana zuwa yayi kata albishir da sunan daya sanya ma yaran, guda sosai ammah tayi tana murna tare da masu addua.
Bai wani dade ba yayi mata sallama ya fuce don Har lokacin amra bata futo ba.
Washe gari yara sukaci sunayensu bayan anyi masu yanka, tunda safe babu wanda ya runtsa a gidan, ammah na tsaye akan abuncin sadaka da akayi na kusan mutane Dari Harda kudi aka dunga rabawa mutane, lowkey suna sukayi anan cikin gida inda ammah ta dage kan dole sai sunyi hotuna, at that minute Aman yayi booking wani mai hoto abunka da harkar kudi nan take sukazo babban company ne inda suke service na komai daga kan makeup zuwa photoshoot, suna zuwa aka zarara ma mai jego kwalliya sosai, hannunta tasha red henna wanda salima ta goga mata asuba a yatsunta sai yayi jaa sosai yayi ma cute fingers dinta kyau aranar kuwa Madina ta dura a nigeria ko zama batayi ba ta taho nan gidan aka fara shagali da ita.
Sunsha hotuna sosai inda baban twins bai shugo bama ya fuce daga gidan tun safe.
Sai wajen yamma ya dawo gidan, yana dawowa kuwa ammah ta jawo shi akayi hotunan dashi inda akayi mashi shida yaranshi, amra dai qin yarda tayi a daukada ita don yana zuwa wajen ta wuce sama abunta.
Agajiya kowa ya kwanta aranar inda amra kuwa ta kwana a zaune don aranar tasan motherhood is not an easy job donma ammah na gefenta tana taimaka mata.
Washe gari sai wajen karfe sha daya kowa ya Tashi a gidan, amra dai na zaune a daki tayi wanka ta shirya zasuje first week immunization na triplets, tana nan zaune salima ta shigo itama a shirye take don tare zasuje saboda ammah zata zauna ta huta saboda bp dinta, tana shugowa ta dauki princess a hannunta “adda ya Muhammad yace ki sauko”
“Gani nan dan Allah” amra ta amsa ta
Fucewa salima tayi tana rike da baby hamra.
Ammah ne ta fara saukowa daga stairs fuskanta dauke da murmushi, harta karaso parlor, malam labaran dake zaune akan kujera Amar na gefe shima a zaune bayan sun gaisa yayi mashi barka.
Karasowa ammah tayi “ah ah malam labaran kaine da Safiya haka”
Har kasa ya duka “hajiya ina kwana ashe an samu karuwa Allah ya Raya”
Zama ammah tayi “lpy Lau malam labaran mun samu Yan uku”
Dariya labaran yayi yace “Masha Allah Allah ubangiji ya Raya su yasa su zama mahaddatan alqur ani”
“Ameen ya Allah” ammah ta amsa
“Basu sauko bane son?” Ammah ta tambayi amar
“Uhm “ kawai yace mata ya cigaba da latsa waya Yana kokarin Kiran bata daukan wayan, ranshi yadan sosu
Kamshin turare ta ne ya fara kawo masu ziyara parlor inda ammah ta dago ta hangosu yana saukowa ita da salima, tana gaba ta rike su Hamad da hamid a hannun ta while salima ta rike hamra a hannunta, karasowa suka farayi inda ammah tace “Masha Allah malam labaran ga mai jegon nan ma saiku gaisa”
Dagawa malam labaran yayi a daidai nan salim dake shugowa cikin gidan don tare suka futa da aman zuwa gyaran handle din game dinshi , yana sauke shi ya wuce office shi kuma ya shugo gidan har ya karaso sitting room din babu wanda ya kura dashi kwata kwata, idanunshi babu inda suka sauka sai akan labaran take ya kwalla kara wanda yasa gaba daya suka dago suka kalli inda yake tsaye, amra ce kadai bata kalli inda yake tsaye ba idanu ta ya sauka akan labaran, wani irin jiri jiri ne ya soma dibanta tayi baya cikin sauri Amar ya mike ya taro ta saboda kiris ya rage ta fadi ga yara a hannunta, Salim dai tunda ya kwala karar nan ya sume a kasa…..
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.