Best Hausa Novels

Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx

Chapter 13 of 52

Chapter 117

Update!!!

17/5/2023

Unedited

Yanda yake zugar motar a guje kamar zai Tashi sama, tunanin shi ya tsaye chak wuri daya, hankalin shi ya gama Tashi saidai bazaka taba tantance hakan ba daga fuskanshi, daman yana shiga irin wannan yanayi na fushi da zafin zuciya yake peaceful waje yayi addua Har yaji sanyi a cikin ranshi, ahankali ya gangara da motar shi gefen titi inda babu mutane sosai , bai kashe motar ba saima Kara karfin ac da yayi ya kwantar da kanshi baya tare da rufe idanunshi yana karanto adduar da zata sanya zuciyarshi tayi sanyi babu abunda yake ayyanawa a ranshi sai rashin hankali irin na yarinyar nan, babu macen da ta taba bashi ciwon kai sai gashi wannan tana neman saka mashi ciwon kai, saida yadan dawo daidai kafin ya bude idanunshi ya sauke kan titin dake gabanshi, badan yana da dalilin shi ba akanta daya barta ta tafi, saidai bazai ita ba, na farko saiya tabbatar Idan Akwai cikinshi a jikinta na biyu kuma yasan she will be broken Idan Har tace zata koma wannnan gidan don abunda zata tarar zai tada mata hankali, bayan wannan he has so much plan da shi kadai yake yinshi, bawai rabuwar ne bayanson yayi da itaba, saidai shi komai a lissafe yake a wajenshi kuma komai da lokacin shi. Shi mutunne mai magana daya, idan yace gaba da za ayi Toh nan za ayi babu abunda zai sa ba za ayi yanda yake so ba,he’s nan of his words, aure sukayi na yarjejeniya, kuma ya cika nashi alqawarin don Har ya gama proceeding card din citizenship dinta na nan uae,ta bangarenshi shima dole sai ta cika nata alqawarin, dukda yana mamakin yanda qiri qiri ta nuna bata san shi nashi buqatun ba akan yarjejeniyar da abunda yake so gurinta while he made a very clear statement akan abunda yake so a cikin yarjejeniyar su.

Dan tsuka yayi tare da furzar da nunfashi yace “I will deal with you later on” mtewww ya Kara buga wani tsakin kafin ya bude wayanshi, number asad yayi dialing, yana picking ya danyi shuru yace “I need your men, Akwai wani aiki da zasuyi min, will send a picture of a lady, inason a bincika min duka garin nan, most importantly car parks, I need all the information of transportation na yau,”

Ba tare da tunanin komai ba asad yace “okay sir”

Yana kashe wayan ya tura Ma asad picture dinta kafin ya shiga line dinta da baiyi saving ba saidai ya haddace digit din gaba daya, tsaida hannunshi yayi ya kasa dialing, chan kuma ya Danna call tare da saka speaker, “the number you’re trying to call is not avai….”

Yana jin haka yayi saurin katse wayan ya shiga wani application masu na sojoji da suke tracking ya saka number nata, babu duban da baiyi ba don kokarin yin tracking dinta saidai hakan bai yuwu ba sakamakon rashin network daga wajenta don Sai app din ya fara nuna mashi inda take Sai ya bace, but it’s looks like zai dawo anytime, tunda ya hakimce anan cikin motar ya bada other bai sake magana ba, kusan minti ashirin kafin asad ya kirashi, saida wayan ya kusan katse kafin ya dauka “any update” ya fada chan kasan maqoshi, magana akayi daga chan bangaren kafin yace “okay”

Yana kashe wayan ya fige motar hankali kwance.

Bangaren amra, kwana tayi idanunta biyu, Har safiya karfe takwas daidai ta fito da hijab dinta kasa, tun bayan sallar asuba take monitoring mutanen gidan gaba daya don neman chance din guduwa, kamar da wasa tana fitowa kuwa securities basa zaune Sai mutun daya wanda ke monitoring cctv shima barcinsa yake hankali kwance, tana zuwa bakin gate kusa ta Danna button din dataga suna dannawa, nan take kofar ta bude bata tsaya rufewa bama ta fara tafiya cikin sassarfa, saida ta fuce daga cikin estate don gaba daya hankalinta ya dawo jikinta don ba karamin dogon tafiya tayi ba don estate din yanada girma sosai, hankalinta bai gama Tashi ba saida ta tuna ko sisi bata dashi a jikinta, take taji jikinta yayi sanyi, tunanin tafiyar ta farayi, yanxu ina zataje, kallon wayar hannunta tayi, ba kowa ta sani ba balle tace zata kira wani don ya taimaka mata, ta dade tana nazari kafin wani mai drop ya tsaya gabanta don kamar bayarbe ne, kallonta yayi yace “madam where are you heading too”

Bata tsaye tunanin komi ba don hankalinta yayi gaba, so take kawai ta tafi don haka tace “motor park sir”

“How much you go pay”

Taurus tayi da idanu don bata da kudi a jikinta “uhm I don’t have money sir”

Kallonta yayi daga sama Har qasa don gani yake kamar ta raina mashi hankali don ga alamun hutu nan a jikinta, wayar hannunta ya hango cikin asaka yace “you get money na, your phone too na money, you wan go o should I just move?”

Jiki a sake tace I will pay with my phone but please sir will You give me something so that I can use it to travel”

Dariya kawai yayi yace “oya naw “

Bude bayan motar tayi ta shige kafin ya ja motar.

Daidai jabi park ya sauketa ya nuna mata inda line din abuja to kano yake, godiya tayi mashi sosai kafin ta miqa mashi wayar nata gaba daya harda sim din, washe baki yayi don yasan zai samu kudi Idan ya sayar, zaro dubu goma yayi chif ya bata yace “thank you madam”

Godiya tayi mashi taja baya ya wucewarshi, da sauri drivers sukayo kanta yuuu saida gabanta ya fadi, da sauri tayi baya Duk ta gama tsorata, don gaba Dayan su kamar Yan kwaya, “madam where you wan go”

Daya daga cikin su ya tambayeta, saurin tashe hancinta tayi don abuga yake, kauda kanta tayi gefe ta wuce wajen wasu drivers musulmai ta masu sallama tare da tambayar su motar zuwa kano, “hajiya Sai karfe Tara motar kano zata Tashi, saidai Idan zaki dan jira”

Shuru ta danyi tace to”

Samun waje tayi wajen wani bench ta zauna, kallon ko ina take, kazanta dai Akwai ta a wajen kamar mutun yayi amai, ga satin maza, hakan nan ta daure don wani amai amai take ji,tana nan zaune motar kano ta soma diban passengers, saida motar ta cika maqil kafin driver yace hajia “shugo bismilla”

Hankali tashe take duban kwarbabbiyar motar karshe seat aka bata kuma namiji a kusa da ita, nan take taji kamar karta shiga saidai tunawa da abunda ke gabanta yasa tayi addua ta shige.

Nan take suka fuce daga park din sai kano….

Daidai ajuwele road yayi parking motar shi ya fito cikin qasaita ya Taka Har inda asad yake da mutanenenshi, gabansu wani mutumine yayi kneel down hannunshi aka yana roko, “oga I take god beg una, please I swear to god I no steal the phone, I collect tam from someone”

Gabansu Amar ya karaso Har lokacin idanunshi sunyi jaa saidai fuskarshi tana nan yanda take bazaka gane a wani yanayi yake ciki ba, tunda ya karaso wajen mutane aka Kara cika wajen, daman rundunar asad ne suka kama yaruba driver din don an samu anyi tracking wayar Tata anan aka kamashi tare da wayar, an sun fara lugudar shi amar yace su jira yazo wajen.

Hannunshi na cikin aljihunsa ya kafa masu idanu baya son rana sosai gashi ranar ta fara fitowa don wajen karfe goma da rabi na safiyar ne.

“Oga gashi nan ga wayar Ma”

Karba amar yayi take ya shiada wayan nata ne, kallon driver din yayi yace “let’s make things very easy for all of us, just answer me where did you get this from”? 

Ya fada yana nuna wayar, driver dai kamar munafuki ya soma bayani daga inda ya dauko ta Har zuwa inda ya sauketa, kwade kanshi asad yayi yace “you’re a thief, you agree on collecting phone that’s worth hundreds of money”

Dago da rinannun idanunshi yayi ya kalli asad ya mashi alamun ya kyale shi da hannu daya, sun card dinta ya cire mata ya jefama driver wayar ya kalli asad yace “let’s move to the park”

Da sauri asad ya shige motarshi suma sojojin kusan su ashirin suka shige tasu nan take ko ina ya shiga jiniya wiwi wiwi, mikewa driver yayi yana ayyana masifar da yaso jefa kanshi.

Koda suka iso park nan take Yan shaye shaye suka dunga watsewa aguje don Duk tunanin su su akazo kamawa, asad ne ya jagoranceshi shiga park din saidai bai sauko ba yana cikin motarshi hankali kwance,futa asad yayi ya baza mutane shi aka fara tambaya, basu wani kuma ba suka samu bayanin da suke nema, bayan motar amar ya bude ya shiga yace “Sir Mun samu motar da ta shiga da number driver din, and sun dade da tafiya don Ina kyautata zaton sun fita daga abuja heading to kaduna by now”

Dan waigowa yayi ganin yanayin fuskanshi, kamar bai damu ba kwata kwata haka zalika yanda yake yi da fuska zaka dauka kamar Baiji abunda asad din ke fada ba, yar tsuka yayi yana tunanin irin hukuncin da zai mata for stepping on his words, saurin runtse idanunshi yayi aranshi yace “babu yarinyar data isa tayi stressing dina, I will surely deal with you”

Bude jajayen idanunshi yayi kan asad yace “I want her in abuja in d next 30mins, just do whatever you can do, ko helicopter ne ka nema, I don’t fucking care just bring her here”

“Yes sir kawai asad yace ya fuce daga motar, shima juya akalar motarshi yayi ya fuce daga park din, tafiya ya dunga yi batare da sanin inda yake zuwa ba, don ya kusa zagaye abuja gaba daya,ganin stressing kanshi bashida wani amfani yasa ya juya zuwa gida, yana gab da shiga taura estate wayar asad ya shigo,saida ya kusa tsinke wa kafin ya dauka tare da sakawa a speaker ya danyi shuru,”oga!! Akwai matsala”

Dan jin yayi yace “what’s the problem”

Yanxu haka Mun samu report Akwai attack anan abuja to kaduna road”

Yanda ya Taka burki zaka dauka motar zatayi tumble ta juya, kokarin daidaita kanshi yayi kafin yace “what attack?”

Da sauri asad yace “kidnapping”

Runtse idanunshi yayi ya budesu ya dauka kusan minti biyar baice qala ba saida asad yace hello kafin ya dawo daidai yace “get the helicopters ready I’m coming now”

Aguje ya fuzge motar ya juya ya hau titi kamar zai Tashi sama, babu abunda yake fada aranshi Sai innalillahi, bayason ya zama selfish amma nan take ya ayyana wani abu ya faru da ita while cikinshi na jikinta? Saurin runtse idanu yayi ya maida hankali kan tuqin, cikin mintuna biyar ya iso headquarters din sojoji, baima kaiga rufe motar tashi ba ya fito ya wuce inda ake aje helicopters, already su asad na jira shi don haka ya shige ciki shima, billet protection suka miqa mashi, da sauri ya masu wani mugun kallo yace “do I look like I need one”

Yanda yake fada yasa kowa yin baya asad ne yayi ta maza yace “oga you have to…”

Saurin tsaida shi yayi ta hanyar nuna mashi yatsanshi, babu wanda ya sake cewa qala, wayar driver din asad ya cigaba da kira Har lokaci baya shiga,gashi babu damar yin tracking line din don babu network, yanda helicopters ke yawo a sararin samaniya kusan guda goma ajere zaka dauka yaqi za a tafi.

Amra…. 

Tun bayan da suka fara tafiya gabanta ya soma faduwa, gaba daya tunaninta ya tsaya chak,addu’oi ta fara a cikin ranta Har barci ya kwasheta, babu mace ko daya a cikin motar sai ita kadai gashi ta maqure sosai gefe guda jikin kofa saboda gefenta namiji ne, ga tafiyar a takure ake yin ta saboda yanayin motar, tunda ta janyo gaban wuyan hijab din ta ta rufe fiskanta bata bude ba Har suka fita daga garin abuja, ahankali ta fara jin faduwar gaban na sauka, runtse idanunta tayi Har barshi ya soma fusgarta don batayi wani barcin kirki ba kwata kwata,tafiya ce sukayi ta kusan awa daya dukda hanyar bata da kyau, ahaka driver nan ya dunga bin titin inda babu wasu mutane dake yawo Sai daji Sai kuma motoci dake wucewa.

Dammm taji gabanta ya fadi lokacin da mutanen cikin motar suka fara doka salati, babu abunda kake ji Sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, afurgice ta bude idanunta da sukayi jaa gabanta na faduwa don ganin abunda ke faruwa, tun daga nesa driver ya hango dandazon mutane a kwance amma dake dan tasha ne hakan bai da shi ya tsaya ba, tun kafin su kaiga karasawa daya daga cikin mutanen gaban motar yace “innalillahi jama’a Mun shiga uku Yan kidnapping”

Tassss sukayi karar bindiga nan take motar su ta fara juyi Har saida ta tsaya sakamakon tayar motar tasu data bayansu da aka harba, mutane ne gandama gandama hannayensu dauke da bindigu manya manya ak 47, ga mutane a gabansu kwance wasu cikin jini wasu kuma sun kwanta, yanda motarsu ta lula yasa ta buge kanta sosai harya dan soma jini, saida motar ta tsaya chak dan nesa da mutanen kafin mutane biyar daga cikin kidnapers su su karaso biyu suka tsaya wajen motar su amra uku suka wuce motar baya, mutane biyun nan na karasowa suka fara bude motar ta bangaren driver da amra dake gefenshi, tunda uwarta ta kawo ta duniya bata taba ganin tashin hankali irin na yau ba, “Ku fito” wata irin murya mata dadin jii ta karade wajen, haka suka dunga futowa suna layi daya bayan daya amra dai suma ne kawai batayi ba don Har wani jiri jiri ke dibanta, haka aka taso su gaba, driver ne a gaban line din kafin ita abayanshi Sai mutumin dake gefenta, suna zuwa inda mutane ke kwance tsoro da furgici yasa ta kwala uwar kara, da sauri ogan cikin kidnappers din yazo gaban wajen su idanunshi jaa kamar garwashi fuskarshi ba kyan gani, yana zuwa baiyi wata wata ba ya fasa kan driver dake gabanta, wanwas driver din yayi baya kan jikinta, jini na malala sosai har kan fuskanta, da sauri ogan ya kalli kowa dake wajen yace “Duk wanda yayi yunkurin dogon nunfashi mai sauti wannan ne sakamakon shi”

Haba wa da sauri amra ta damke Bakinta yanda driver dinnan ya zube haka ta zube wanwas kamar matacciya, ko motsin kirki bata yi, tsabar furgicin data shiga zuciyar ta ta kusa bugawa don kwata kwata nunfashin Ma dauke wa yayi gaba daya, tun bayan wannan abun daya faru bata kara sanin inda take ba don na bayanta Ma ya dauka itama mutuwar tayi.

Kamar daga sama suka fara jin karar helicopter na yawo a zarar yin samaniya don kamar an wullosu, da sauri ogan ya kalli gabas kafin ya cije lebenshi yace “an tarfo mu, kowa ya gudu”

Haka suka dunga gudu, dayake mugaye ne haka suka dunga harbin mutane da suka mimmike don neman hanyar guduwa, tun daga sama sojajin suka so su fara Harbi ganin suna neman guduwa saidai babu hali don zasu iya hallaka mutane, haka sukayi landing wasu suka bi hanyar dajin da sukabi sauran kuma suka tsaya,tunda sukayi landing ya Kasa motsawa don tun daga sama ya hango yanda mutane ke kwance, asad ne daya rigada ya fita ya ga situation din wajen kafin yayi saurin tura health team da suke cikin daya daga cikin helicopters din don su duba masu taimakon gaggawa, mutane biyar ne kawai suka rasa rayukansu ciki Harda driver Sai kuma mace daya ta suke tunanin kamar zuciyarta ce ta kusa bugawa, asad baisan wacece amra ba don hotonta ya gani kawai, sannan cikin mutanen wajen bai kura da itaba don Har gaban inda take kwance bayan an daura ta kan emergency bed, dalilin hijab dinta dake kan fuskanta data jawo Har hancinta yasa bai Lura ba, takowa yayi har gaban Amar dake zaune fuskanshi tamm bazaka taba tantance a wani yanayi yake ciki ba, dago da rinannun idanunshi yayi yana kallon asad tare da sauraron bayanan shi “oga mutane biyar ne suka mutu, sauran mutane babu wanda ya samu rauni, Sai mace daya da Muna kyautata zaton kamar zuciyarta taso bugawa don Har yanxu she’s not responding Muna bata taimakon gaggaw….”

Bai tsaya sauraron asad ba ya fito a gaggauce ya fara wucewa, mutane kamar sun san waye shi suka fara bashi hanya Duk tashin hankalin da suke ciki bai hana sun zuba mashi idanu ba ganin yanda yake tafiya cikin izza da qasaita.

Saida ya duba ko ina bai ganta ba, da sauri ya fara bin motocin wajen da kallo daya bayan daya kusan guda goma ajere, nan take idanunshi suka sauka kan motar driver da suka karbi number shi da plate number na motar tashi, dan waigowa yayi wajen mutanen dake zaune yace “waye driver motar nan”

Daya daga cikin mazan da suke cikin motar ne yayi saurin cewa “yallabai gashi nan Akwance shima an kashe sa”

Saurin runtse idanu yayi sosai yace “Duk wanda yake cikin motar ya miqe tsaye”

Nan duka suka mike su kusan shida saidai babu amra a cikin su kuma baiyi tunanin itace matar da asad ke magana akai ba, wani irin zazafan numfashi ya sauke idanunshi sun sake yin wani jaaa sosai, ganin haka yasa asad saurin zuwa gabanshi ahankali cikin rada yace “I think bata cikin motar nan,”

Kwata kwata baya Ma jinMaganar da asad ke mashi, saida ya dauka kusan minti ashirin kafin daya daga cikin health team tace “sir Mun samu pulse din wannan, I think she’s alive”

Dago da idanunshi yayi ya dubai matar kafin ya sauke idanun nashi kan matar da take magana akai, idanunshi ya bude sosai, ya kasa koda motsawa, tabbas hijab din da ya gani ne a jikinta lokacin data fito daga gidan ta cikin cctv camera, kamar zaki haka ya dunfaro wajen ya yaya chak ya kura mata idanu, jini Duk ya bata gaban hijab din nata, cikin sauri ya sa hannu ya zame hijab din daga Bakinta, yana yin arba da fuskar ya runtse idanunshi ya budesu sosai, ya kasa cewa komai ganin haka yasa asad shima matsowa Har inda take ya kafa mata idanu Sai a lokacin ya gane itace suke nema.

“Oga she’s the one”

Shuru asad yayi baice qala ba don kamar tunani yake kafin ya kalli health team din yace “what’s her condition?”

Da sauri wata soja budurwa ta kalleshi tace “she’s stable sir, shock ne ya kamata wanda yasa zuciya ta ya kusa bugawa, she needs somewhere peacefuly da rest zata dawo daidai”

Bai kalli budurwa ba ya sake tambaya “and this blood stain?”

Da sauri daya daga cikin mutanen yace “Jinin driver ne don shi aka harba maimakon ita lokacin da tayi ihu”

Nan take jini shi ya sake boiling inda Ana measuring zafin zuciya za a gane yanda yayi high sosai babu abunda yake fada aranshi sai “hmmm”

Ya rasa mema zaiyi mata yaji dadi aranshi, zuciyar shi ta hasala sosai, yayi warning dinta bataji magananshi ba.

Kallon asad yayi yace “ka sa akawo available motoci daga kusa su tafi da mutanen nan inda zasuje,let’s move with those that got injured”

Asad najin haka yasan me yake nufi don haka yasa manyan sojoji guda goma su tsaya don kula da lafiyar mutanen wajen sauran waenda suka mutu aka debesu zuwa helicopter din health team, saida akazo tafiya da amra yace su dakata, nuni ya masu da su sakata a helicopter sun da yake, haka suka gurgura emergency bed din zuwa cikin helicopter din suka saka ta tare da likitoci biyu daga cikin health team, shi dai asad bai bisu ba ya tsaya tukunna saboda motocin da zasu zo su dauki mutanen wajen.

Tunda ya suka Tashi sama bai sake kallon ko inda take ba, saboda yanda yake jin wani zafi ganin yanayin da take ciki,tunanin yanda zaiyi dealing da ita yake yanda bazata sake tunanin taka umarnin daya bata ba, kamar wanda aka tsungula ya zaro wayanshi ya soma kira, yana gamawa ya kashe ya kira landline din gidan shi na larrics, Nadine dake zaune hankali tashe tayi picking call din kafin ta saka a kunnenta, “go and bring her few clothes and pack your belongings,” damm gabanta ya fadi da jin abunda yace bata gama tunani ba ya cigaba, “driver will be waiting for you outside, come along with your passport”

Yana kaiwa nan ya kashe wayar, da sauri ta miqe ta tattara kayanta Harda kukanta don tunaninta korar ta yayi saidai tayi mamakin jin yace driver na jiranta a waje, agurguje ta fito da yar jakar kayanta ta shige motar driver ya jasu,

Agaban  headquarters driver ya dire ta, cikin Yan mintuna qalilan helicopter su ya dira a field din headquarters, ahankali ya soma saukowa kafin a sauko da amra wadda Har lokacin bata dawo hayyacinta ba, dan asibitin dake cikin headquarters aka wuce da ita aka cire mata kayan zuwa wasu wanda Nadine ta taho dashi kafin a mata allura don zuciyarta ta samu relive din shock din data shiga.

Takowa Nadine tayi Har gaban gadon da aka kwantar da ita ta kare mata kallo, fuskarta tayi fayau Har wani yar rama tayi, dukda bata san wani hali take ciki ba tausayinta ya gama dabaibaiye zuciyarta take tayi alqawarin koma menene damuwarta zata taimaka mata.

Manyan ambulance ne suka shigo cikin headquarter aciki aka saka ta tare da Nadine, kowa dake cikin headquarters saida ya shaida qila yar governor ce aka ceto ko kuma yar wani minister din, baibi motar ambulance ba ya shige cikin Tashi ya figi motar, wayarshi dake Kara yayi saurin picking yana dauka ya saka a hands free, daga chan baba garen aka soma magana “sir the visa is ready, and the private jet also”

“Okay” kawai yace ya kashe wayan kafin ya Kara ma motarshi speed sosai.

Agurguje dai saiga amra a airport ita da Nadine, dayake ya rigada yayi proceeding komai in less than an hour suna zuwa airports aka wuce dasu wajen private jet Har aka shige da amra wanda ke kwance kamar gawa, kallon Nadine yayi don shi bazai bisu ba tukunna saiya gama abunda ya kawo shi

“When you arrive my personal guard will be there to pick you up,”

Kallon agogon shi yayi ya juya harzai tafi ya dawo yace “take care of her”

Yana kaiwa nan ya fuce suna suka hau jirgin, abun mamaki Nadine na ganin jirgin tana an rubuta Taura baro baro, tasan sir yana bearing sunan saidai bata kawo ko nashi bane ko ba nashi bane saidai taga abunda ake kira da luxury lokacin da ta shiga cikin jet din gashi sak nan nan ake da su.

Bangaren Amar kuwa wata zuciyar nashi na mashi fadan yin hakan don yasan zai sha wahala idan bata kusa don ya fara sabama kanshi da abubuwan da Allah ya albarkaceta dashi, saidai kuma yana ganin wannan opportunity ne da zai tabbatar idan Har cikinshi ya shiga jikinta ko bai shiga ba bayan wannan plans dinshi da yake akanta na nan yanda ya tsara tun farko kafin ta dawo Nigeria.

Gida ya tafi direct don wani irin ciwon kai ne ya addabeshi sosai, yana zuwa ya wuce dakinshi ya watsa ruwa ya kwanta don ya samu ya danyi barci kozai ji saukin abunda yake ji, saidai kuma barcin gaba daya ya kaurace masa, tunanin da baya son yin ya tsaya mashi arai, zuciyar shi nayi mashi wani irin nauyi ganinta da yayi a wannan yanayi, runtse idanunshi yayi sosai aranshi yace “why won’t you get out my mind”

Tsaki ya danyi ya sake juyawa tare da kure ac din dakin ya janyo duvet Har ya samu barci ya nasarar daukanshi.

Dubai United Arab Emirates Uae …..

Jet dinsu na sauka a uae international airport akayi masu Duk wani arrangement na shiga kasar ba tare da sun motsa ba, Nadine dai tana ganin rayuwar manya, don gaba daya ta gama tsurewa, Duk rayuwar a Cameroon bata taba shiga jet ba, amra dai tana daga chan wani bangare na cikin jet din da masu bata kulawa don Har lokacin bata farfado ba, minti bayar da landing din wata ambulance din ta karaso, m5 ne ya shigo Har cikin jet din ya jagoranci Nadine din suka sauka kasa zuwa motar dake harabar filin jirgin, iska ce mai dadi ke kadawa sosai. Ahankali aka saka amra cikin ambulance din itakuma Nadine ta shiga wata haddaiyar motar daban wanda m5 yazo da ita suka wuce gida tare da special doctor din Amar don shi zai kula da lafiyar amra.

Tafiyar minti talatin suka iso tafkeken penthouse din general Amar,inda tundaga shigarsu Nadine ta soma bama idanunta hakkinsa, tunda take harkar aiki wayo house keeping bata taba ganin gida makamancin wannan ba, Har m5 yayi parking bataji ba don ta Lula tunani, saida ya bude mata kofa kafin ta dawo hayyacinta ta fito daga cikin motar, already motar data shugo da amra tayi parking itama Har an sauko da ita daga cikin motar, m5 ne yayi gaba suka bishi abaya dukkansu, doorbell ya dannan pablo dake expecting dinsu yayi saurin budewa kafin su saka kai cikin main parlor din, Nadine dai ta zama kamar jaka don da kyar ta shiga cikin gidan, direct wurin suka wuce kafin m5 ya Danna floor 2 don nan ne masaukin su, fadar haduwa floor dinnan Ma bata lokaci ne don dakuna ne ajere Sai babban cozy sitting room tamkeke da yasha kayan duniya na gani na fada, babban dakin aka wuce da amra nan Ma ba a cewa komai Sai Masha Allah don an zuba duniya ba kadan ba,  akan wani hadadden English bed aka kwantar da ita da taimakon nurse din dake tare da doctor din kafin su fara dubata don Har lokacin barci take sakamakon allurar da akayi mata.

A Last floor m5 ya nunama Nadine dakinta wanda yaci uwar na wanda aka bata a larrics don itama harda dan coffee table and chairs aka aje mata da tv Sai tamkeken bed dinta..

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.