Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 23 of 52
Chapter 127
Washe gari sunday, sai wajen karfe sha biyu ta Tashi da wani matsanancin ciwon kai, dakyar ta samu ta Tashi daga kan gado ta wuce toilet ta watsa ruwa kafin ta fito, bin dakin nata tayi da kallo, packaging din kayan da haifa ta saya ajere a kasan wajen, mikewa tayi ta kwaso su ta wuce dasu cikin closet ta ajesu, Riga da wando ta jawo daga cikin closet ta saka, rigar takai Har gwuiwarta, wandon ma yanada fadi sosai don bai kamata ba saidai ya zauna daidai a jikinta,fitowa tayi ta wuce kasa wajen Nadine.
Gaba daya gidan is so boring, tunda ta zauna a parlor ta kunna tv ta rasa abunda zatayi,kamar wadda aka tsugula janyo wayarta ta shiga camera ta daidaici fiskanta dauke da murmushi har attractive dimple dinta na futowa ta dauki hoton kanta, murmushi tayi tana kallon kanta, ta chanza sosai tayi kyau, hutu ya zauna a jikinta, cikin Instagram ta shiga tayi posting iyakacin fuskanta don babu hula akanta, tayi mugun kyau sosai, dukda bata da followers da yawa a account din nata, fita tayi daga app din ta shiga whatapp nan taga hotunan da sukayi haifa ta turo mata, ita kanta mamakin yanda ta chanza tayi don ta saje da larabawa,murmushi kawai tayi ta daura hotonsu da sukayi ita da haifa rungume da juna a profile dinta, Harda Instagram.
Nigeria…
Alamarin daddy dai sai gaba suke yi,don kullum threat daban daban yake yima Amar ta bayan fage, karshe dai amar yayi deciding ya dauke su daga gidan, dukda yana tsoron tambayar dalilin hakan da ammah zatayi, bayan wannan ma baya son tasan komai dukda dole saiya fada mata wata rana but not now, baya jin zai iya tunkararta da maganar yanxu cause her heart is weak gashi tana da ciwon zuciya, abu qalilin ne zai saka mata heart attack, don doctor yayi warning akan damuwan da take sama kanta shike affecting din zuciyarta.
Ba tare da wani bata lokaci ba yasa ayi masu visa, su salima ma da kanshi ya dauke su ya kaisu akayi masu passport cikin mintuna, komai was moving smoothly kamar yanda ya tsara don baya son kowa yasan zai daukesu daga gidan,tunda suka dawo ammah taso tambayanshi inda suka je, saidai yana saukesu ya wuce office din asad, su salima na shiga gidan a kitchen suka samu ammah, da sauri salima ta karaso inda yake ta karbi plate din hannunta tace “ammahh please ki daina shugowa kitchen, nida anty lantana ma mun isa muyi komai, kinga doctor yace ki dunga hutawa saboda health dinki”
Murmushi ammah tayi tace “Toh Ay naga yau kun fuce yawon ku kuda ya Muhammad din naku shiyasa na shigo don na taimaka wa lantana”
Cikin zumudi alima tayi tace “laa ba yawo mukaje ba fah ammah,wani waje ne mukaje akayi mana hoto”
Shuru ammah tayi tana dan nazari kafin tace “hoto kuma?wani irin hoto?”
Saukar da kai salima tayi tace “eh, ni bansan wajen ba amma naga an rubuta Nigerian immigration service”
Nazari ammah ta soma yi don tasan me hakan ke nufi, Toh kodai maida yaran zaiyi wajen mahaifinsu, ta tambayi kanta, ganin babu wanda zai bata amsa yasa tabar zancen kawai saiya dawo taji bayani daga bakinshi.
Bangaren amar bayan ya sauke su salima office din asad ya wuce direct, yana zuwa ya mashi bayanin plan din yake shirin shi, kallonshi asad yayi yace “oga Ay saida na fada maka tun wuri kasan yanda zakayi saboda safety dinsu,mu kuma saimuji dashi daga baya, yanxu ina zaka tura su?”
Kai tsaye Amar yace “dubai, yau za ah tura min visa dinsu zuwa gobe nasan passport din yaran will ready”
“Okay Allah ya kaimu”
“Ameen, yanxu menene on the ground? Ya bunciken ku?” Amar ya tambaya
“Kamar yanda na fada maka ya toshe Duk wata kofa da za a zargesa ko a kama shi da wani laifi, Duk inda muka saka kai bama samun komai. Don Har accounts dinshi mun bincike Duk wani transactions dinshi na kamfanin ne, komai under taura yake,abunda mafi zargi shine yana amfani da 2identity wanda daya musanshi dayan kuma babu damar sani, but trust us oga, Insha Allah something will definitely come out”
Shuru kawai Amar yayi don yasan hakan ne zata kasance, Yanxu idan ya biye masu haka za aita surutu babu wani progress shiyasa yake Ganin komai na Nigeria yana baya, babu cigaba kwata kwata, yanxu inda achan dubai ne da tuni an rufe shafin sa kamar yanda aka rufe na alif dukda cikin sirri ne saidai hakan bazai yuwu ba don ba a kasar bane dole saida sojojin nigeria da maaikanta dake karkashin ta.
Bai dade a office din asad ba ya wuce forensic lab don ko asad bai fada ma komai akan plans dinshi ba, akwanakin baya da aka kama saurayin daya so smuggling drug din, an kamashi da kwayar wadda dakyar amar ya samu ya dauka sample dinta daga chan headquarters don Har an kai maajiya mai karfi,haka ya taho da ita Nigeria,da farko baiyi tunanin bincike akan kwayar ba anan Nigeria sai daga baya private investigator dinshi ya buqaci any little hint akan bunciken da sukeyi nan amar ya tuna da kwayar, take suka kai forensic lab don su duba abubuwan dake cikin kwayar don suyi tracking drugs manufactories na nan Nigeria, buncike ne mai karfi don kamar yanda private investigator dinshi ya shaida mashi dole sai sunyi abubuwan da are illegal don su samu amsan da suke buqata.
Lokacin daya karasa lab din yaga result hankalinshi yayi mugun Tashi, don sinadarin abubuwan da akayi amfani dashi wajen production din kwayar masu illa ne sosai,don masu karfi ne sosai da suke illah, musamman idan akayi over dosing, result din kawai ya karba yayi saurin tura ma investigator dinshi kafin ya koma gida.
Tun akan hanya ya lura da Ana binshi abaya, bai wani damu ba ya cigaba da tafiya harya karasa gida hankali kwance.
Alhaji kabiru…..
Zaune yake wayar da yake expecting ya shigo, hankali kwance yayi sipping drink din dake cikin cup dinshi kafin ya daga wayar, magana akayi chan kafin ya sauke wayar ya na murmushi, aranshi yace “alif you’re useless to me now, bana buqatar ka,”
Dariya kawai ya kece dashi kamar wani zautacce, kallonshi Aman dake gefenta anan guest house dinshi yayi yace “dad what’s your plan now? Ka rigada ka gano yaron nan na buncike akanka, ya zakayi dashi kenan?”
Kallon dan nashi Alhaji kabiru yayi yace “kasan ance idan kana son kama karamin kwaro saikayi amfani da abunda zai kasheshi directly”
Wata irin dariya yayi ya sake kallon Aman yace “weakness!!!!!, I’m going to use him, atafin hannuna yake,idan kaga an kama hero toh an tabo weakness dinshi”
Kallonshi kawai Aman yayi yana dan murmushi yaqe shi yasan abunda hakan ke nufi. Tunani ya soma yi yanda zai yi stopping din baban nashi don kiri kiri yanason ya salwantar da rayukan da basu jina basu gani ba.
Ganin ya fada tunani yasa kabiru cewa “kai dan ubanka fatan Ka rarraba wa mutanenka wanda na baka kwanaki?”
Firgigi Aman ya dawo daidai yace “eh, Ina buqatan more badge, kudin suna nan cikin gida yanda kace a ajiye su”
Juice Alhaji kabiru ya sake kurba ya kalleshi da kyau yace “why do I feel like you’re changing? Yau kai da kanka Ka aje min kudi na? Ka daina kashewa kenan?”
“No dad, kawai I’m being serious ne,when it comes to business it’s strictly business”
“Now that’s what I’m talking about, I’m proud of you,go and spend it, kudinka ne tunda na ubanka ne babu wanda zai hanaka” Alhaji kabiru ya fada yana wani shu’umin murmushi
Wani tunani aman yayi take yaji wani irin dadi aranshi yace “Zan iya diba yanda nake so?”
“Yes son,” Alhaji kabiru ya fada don yaji dadin yanda Aman yake nuna interest dinshi akan business din, daman burinshi kenan,yanxu yana jin zai iya yarda da danshi sosai.
Wani card ya aje agefen Aman yace “spend as much as you want, bazan sake hanaka ba”
Kallon card din Aman yayi cike da tambaya don card din baiyi kama da card din zarar kudi ba,kamar Alhaji yasan abunda ke cikin ranshi don haka yace “entrance key”
Godiya sosai Aman yayi mashi kafin ya fuce daga gidan jikinshi na rawa, daddy dai dadi yake ji sosai Ganin Aman na bashi hadin kai ayanxu.
Wani call dinne ya sake shugowa wayar alhaji kabiru bayan fitar Aman, yana dagawa yace “kuma bibiyarshi?”
Jan ido ne yayi saurin cewa “yea oga, da alamu bai karaya ba, don kamarma cikin sirri yake wasu abubuwan,“
“Ina da Ina yaje yau” Alhaji kabiru ya tambaya
“Forensic lab,munyi kokarin sanin abunda yaje yi achan bamu samu ba, saboda wajen Akwai security sosai”
Dariya Alhaji kabiru yayi yace “ay daka fada min da baku wahalar da kanku ba, ni nasan me yaje yi chan”
Yana kaiwa nan ya kashe wayar, ahanakli ya soma cewa “you’re not ready to give up, Saina koya maka karamin hankali”
Ya karashe yana jefar da glass cup din hannunshi, gaba daya ya fashe anan kasan.
Aman na karasawa gida kamar zautacce ya wuce cikin tsohon part dinsu inda nan ne secret ma’ajiyar alhaji kabiru da yake aje Duk kudadenshi harda stock drugs din, ahankali ya bude kofar yabi gidan da kallo, komai taaftsaf babu datti Yan nan yanda yake, wani irin hawaye ne ya soma zubo mashi lokaci guda tunawa da rayuwar da sukayi a cikin gidan tare da mahaifiyarshi kallon kujerar data zauna lokacin daya kawo mata juice din da ya daddy ya saka mata drug aciki yayi, I can clearly recall ranar,ya dade sosai a tsaye kafin ya daga kafanshi ya fuskanshi dakunan, normally idan zai aje ma dadi kudin a cikin daya daga cikin dakunan yake aje mashi, dukda yasan ba anan daddy ke ajewa ba bai taba tunanin son shiga inda yake aje kudin ba, wato dakin daya banbanta da sauran dakunan, gaban dakin ya tako ya tsaya, kofar is smart don idan akayi attempting shiga tana warning din Alhaji kabiru,
Card din daya bashi ya dauka ya saka a kofar, ahankali kofar tayi verifying ya bude,ahankali yasa kai ya shige, da farko babu komai a cikin dakin don empty room ne sai shelves dake tsagaye da dakin saida ya saka kafanshi yayi taku daya nan take shelves din suka fara budewa, ba karamin furgici ya shiga a wannan lokaci ba, duban dakin yayi da kyau Ganin ko’ina is surrounded with cameras, maido da idanunshi yayi kan shelves din dake shaqe da different currency na kudi, daga kan dollars, euros, naira, dirhams babu wanda babu a ciki,Dayan gefen shelves din kuwa different types of drugs ne ashake,ahankali ya dunga zagaye dakin, daidai wajen wani safe ya tsaya aranshi yace “I’m sure anan yake ajiya molly”
Dan taba wajen yayi safe din na sensing finger prints dinshi ta fara Kara, mai gama tunani ba daddy ya kirashi yace “kaida Nace Ka dauka kudi Ka tsaya kana shirme daban”
Gaban Aman ne ya fadi damm, wato daddy na kallonshi kenan, saurin tsaida nutsiwarshi yayi yace “sorry dad, dan Allah daddy Ka nuna min wannan molly dinne”
“Why kake so Ka gani?” Daddy ya tambayeshi
“Kawai inason naga yanda take”
Kashe wayar Alhaji kabiru yayi ba tare da ya bashi amsa ba, juyawa Aman yayi jiki a mace, dan tsayawa yayi jin safe din ya bude da kanshi, juyowa yayi don he was amazed, dady nada control akan komai kenan, lallai yau ya sake tabbatar da how dangerous he is, karasa bude safe din yayi nan take yaga molly din a cikin safe din, hayaki na fita daga safe din, hannunshi ya saka a ciki nan take yaji wani irin sanyi kamar cikin safe din freezer ne,wayarshi ne yayi kara Ganin number daddy yasa ya dauka “don’t touch, inba so kake a yanke hannun naka ba, kasan how strong and effective wannan drug din yake? Ba a tabawa da bare skin”
Saurin cire hannu Aman yayi dukda yana cikin furgice yace “wow daddy you’re genius”
Dariya kawai dady yayi ya kashe wayar, sai Aman ya kalli wajen da kyau kafin ya rufe safe din ya koma wajen kudi ya deba bundle biyu na dollars kafin ya fuce daga dakin, koda ya fito da Amar yaci karo yana shirin parking, da sauri ya shige cikin gida, ammah na Ganin shugowa shi tayi welcoming dinshi baima taaya ya amsa ta ba ya wuce dakinshi yana sauke wani wahalallen nunfashi,he can’t believe what he just did, gaba daya ataorace yace ahanakli ya furta “ya Allah ka bani karfin gwiwar abunda nake shirin yi” rigar jikinshi ya soma un buttoning saida ya zo na tsakiya ya finciko camera daya maqala a wajen, da sauri ya samu gefen gado ya zauna ya jawo wayarshi ya shiga app din mini unnoticeable camera din yayi connecting nan take Duk inda yaje d conversation dinshi da dady ya bayyana akan screen dinshi, Har cikin safe din saida camera ya dauko, wani irin sanyi da daci yaji a zuciyarshi, “I have to do this,I’m doing what I’m supposed to do years back, ya Allah ka karfafa min” ya fada ahankali.
Yana nan zaune ya kasa motsawa Har aka kira sallar magrib, mikewa yayi ya dauro alwala kafin ya sauya kaya zuwa jallabiya ya fito zuwa masallaci, yana futa Amar shima ya fito, ammah dake zaune babu abunda yake sai murmushi Ganin aman ya fara natsuwa, Aman ne ya karaso inda take yace “ammah na seems like you’re in a good mood today”
Murmushi tayi ta kalleshi tace “yea son I am, by d way kaje masallaci Ka dawo inason magana dakai”
Sunkuyar da kanshi yayi don yasa me hakan ke nufi don haka yace “okay, nima inason zamuyi wata muhimmiyar magana”
Mikewa yayi tace “adawo lpy”
“Ameen” ya amsa mata
Amar bai fito daga masallaci ba saida akayi sallar isha’I, yana idarwa yadanyi adduoi kafin ya futo, dake masallacin cikin estate ne few steps zai kaika cikin apartment dinsu, tundaga nesa ya hango aman a bankin gate, kauda kai aman yayi har ya karaso inda yake, kamar bazai ce komai ba ya kalleshi yace “excuse”
Dan dagowa aman yayi yana wani nazari kafin yace “inason zanyi maka wata magana”
Tsayawa aman yayi ya hade hannunshi a kirjinshi alamun yana sauraron sa
“I don’t have to say much, Ka aje Duk wani buncike da kake yi,”
“Why?” Amar ya tambayeshi ba tare da yaji tsoron abunda yake fada ba
“Because you’re going to hurt people around, I’m just advising you” Amar ya fada kafin ya wuce ciki ya bar aman tsaye da mamakin shi, bai gama tunanin ba ya jiyo muryar aman yace “be careful”
Murmushin gefen baki amar yayi kafin ya shige cikin gidan, dakin ammah ya wuce direct, yana zuwa ya taddata kan sallaya, zama yayi kan couch din dakin saida ta idan ta shafa kafin ta karaso can couch din, kallonshi tayi da kyau kafin tace “baka fada min zaka kai yarannan ayi masu passport ba, is there something that I need to know?”
Shuru ya danyi kanshi a kasa kafin ya kamo hannunta ya dago yace “ammah na, nasan you trust Duk wani decision dina, nasan u understand me better, gobe da karfe goma zaku wuce dubai,”
Bude baki tayi zatayi magana yace “no please ammah, dan Allah karki ce komai, you trust me right?”
Girgiza mashi kai tayi kanta Duk ya gama kullewa, maisa yake don su tafi dubai cikin gaggawa haka,
“Son, I trust you and your decision, shiyasa I never question you on that, but hakan bazai hana zuciyarta tunani da kokonto ba,”
“Ammah I promise I will explain everything daga baya, don Allah kiyi min alfarmar hana zuciyarki tunanin komai, kinga yanda health dinki yake yanxu,I don’t want to say anything for now”
Murmushi kawai tayi ta shafa kanshi tace “I owe you thousands of explanation son, Allah ya kaimu goben”
“Ameen” ya amsa mata shima fuskanshi dauke da murmushi
Bai wani dade ba a dakin ammah ya fuce zuwa dakin su salima, da sallama ya shiga dakin, a zaune yake daga ita sai yar shigo da dogon wando, karasowa yayi cikin dakin, da sauri ta janyo hijab dinta ta saka tace “Ina wuni ya Muhammad”
“Lafiya” ya amsa mata atakaice
“Get your ready you’ll be traveling with ammah tomorrow Insha Allah” ya fada yana juyawa
“Okay ya Muhammad Allah ya kaimu”
Chan kasan maqoshi ya amsa da Ameen, yana shirin fita lanatana na kokarin shugowa, hannunta rike da bowl din fruit, gaishesa tayi kafin ta shige ciki, kallon salima tayi daga sauke hijab din data saka tace “yarinya mai kyawu ga fruit din”
Da sauri ta tako Har inda lantana take ta karba bowl din tace “thank you anty lanatana”
Kallonta lantana tayi tace “naga ya Muhammad din naku yanxu daga nan ya futo?”
Ba tare da tunanin komai ma salima tace “eh”
Fita lanatana tayi tace “saida safe”
Daki Amar ya wuce kai tsaye, kayan jikinshi ya sauya zuwa pjs kafin ya zauna kan couch ya janyo laptop dinshi ya soma wasu ayyukan yana nan zaune ya kafa ma laptop dinshi idanu, file din da suka samu a cikin flash drive din nan ya tsaya mashi arai babu yanda baiyi ba ya kasa budewa,Har hiring manyan hackers saida yayi but yaqi budewa kwata kwata don wani irin encrypted password aka saka wanda file din da shi da babu Duk daya ne idan babu password din, kamar ma password din shine video din gaba daya, Har wajen karfe hudu da rabi yana nan zaune barcin ma ya kaurace ma idanunshi, gaba daya, haka ya miqe ya dauro alwala ya wuce masjid yana dawowa ya wuce bathroom
Ya watsa ruwa don yaji dadin jikinshi da yayi mashi tsami, yana fitowa baima tsaya ya saka kaya ba ya bi lafiyar gado nan take barci ya fuzgesa mai nauyi, bai wani jina da barcin ba karar wayarshi ya karade kunnenshi, bude jajayen idanunshi yayi da barci ke kwance akai ya jawo wayar ya ansa ba tare da sanin wanda ke kira ba, da sauri ya bude idanunshi tare da cewa “send it through my email”
Miqewa yayi daga kwance ya zauna, janyo laptop dinshi yayi ya kunna, direct ya shiga cikin email dinshi, nan take email din investigator din yayi popping, ahankali ya soma bin diddigin yanda Alhaji kabiru yake sayar da kwayoyin da yanda yake transferring komai zuwa wata kasar , runtse idanunshi yayi yace “this Isn’t enough,”…kamar zaiyi shutting system din chan kuma ya tsaya Ganin wani email da bai taba budew ba, gaba daya tubda yake bude email dinshi bai taba Lura dashi ba, duban sunan sender yayi nan take hankali shi ya Tashi Har hannunshi na Rawa wajen dannawa, sunan meeda ne baro Baro, bude email Din yayi babu wani bata lokaci, nan take yaci karo da wasu numbers, nazari ya fara gaba daya tunanin babu inda ya tsaya sai password din file din nan, da sauri yayi copying ya shiga cikin file din ya yayi pasting take file ya bude, wata irin Kara ya buga “yesssssss!!!!!”
Kamar zautacce haka ya dunga bin file
Din da kallo Har ya rasa wanne daga cikin video zaiyi playing don kusan guda uku ne ajere, video farko ya soma playing, fadin irin tashin hankalinshi daya shiga a wannan lokaci bata lokaci ne, lokaci guda Allah ya bayyana mashi abunda yake nema shekara da shekaru cikin kankanin lokaci with just a clip, ga Alhaji kabiru nan Baro baro shida mutanen shi su alif suna meeting, da yanda introduction din ya fara Alhaji kabiru’ na zaune don shine head of the empire bayan su wani katon board ne an rubuta empire suna magana akan production din product din da suke developing wato molly, second kuwa gaba daya wurin production dinsu ne wanda bama a cikin nigeria bane achan waje wajen kasar ne inda babu wanda ya taba tsammani, na uku kuwa list of production da sukayi da amount of product da suka sayar da Duk wani illegal transaction da komai ma a rubuce yace, mikewa Amar yayi ya gyara towel dinshi dake neman faduwa kasa yayi sujudul shukr, finally at long last ya gano komai, aggauce ya tura komai zuwa encrypted portal dinshi, barcin ma ya nemeshi ya rasa gaba daya, idanunshi dai na nan sunyi jaa sosai, yanxu ya gano komai yanada strong evidence akan daddy, ayanxu abunda ya rage mashi shine ya dauke ammah daga gidan daga baya sai yaji da komai, don bazai so taji komai ko tasan komai ba don zaiyi shocking dinta ga yanayin zuciyarta.
da sassafe ammah ta Tashi cikin shiri, black abaya ce a jikinta wanda ta amshi jikinta sosai tayi mata masifar kyau, dakin dady ta wuce, tana shiga wayam, daman tasan ba kalli ta sameshi ba son yanxu yawanci baya kwana acikin gidan, already bashi da matsala da Duk inda zataje da wani tafiya da zatayi don haka bata damu ba kawai ta sauko kasa, kitchen ta wuce direct nan ta tadda lantana tana ayyukanta na shirin breakfast tana Ganin ammah ta tsugunna ta gaisheta,
“Lantana zamuyi tafiya yau, jiya nan samu na fada maki da wuri ba, zaki koma gida idan muka dawo saiki dawo ko,”
Kudi amma ta mika mata dubu hamsin tace “ga wannan ki aje zai maki amfani kafin mu dawo”
Murmushin yaqe lantana fuskanta gwanin nan tausayi tace “hajiya yaushe zaki dawo”
“Bazamu wuce sati biyu ba Insha Allah, Muna dawowa Zan kiraki”
“Hajiya gaba daya gidan zaku tafi” lantana ta tambaya
Dariya amma tayi tace “wannan tambaya haka lantana Ay bazamu dade ba Insha Allah zamu dawo”
“Toh hajiya allah ya kiyaye”
Karfe takwas da rabi daidai suka fito gaba daya breakfast suka farayi suna gamawa ammah ta shiga dakin Aman don bai fito break fast ba, a kwance ta taddashi yana barci, karasawa bakin gadonahi tayi ta shafa kanshi, ahanakli ya soma bude idanunshi harya sauke akanta “good morning son”
Murmushi yayi mata yace “good morning ammah na”
Mikewa yayi zaune ya kalleta Ganin ta cikin shiri yace “zakije asibiti ne?”
“No son zanyi tafiya ne,”
Shuru ya danyi yana Nazari kafin yace “okay”
Tayi mamakin yanda ya amsa don haka tace “duka gidan zamu tafi Harda yaran, ko saka biyomi daga baya?”
Dan dagowa yayi ya kalleta yace “no ammah Akwai work anan, I have a lot to do sai kun dawo kawai”
Murmushi tayi ta miqe tace “okay son take care please” murmushi kawai yayi yana kallonta harta fuce daga dakin, at least yanxu yaji sauki aranshi tunda zata Har gidan for now kafin komai ya daidaita.
Wayarshi ya zaro ya Danna kira, Ana dagawa ya runtse idanunshi yace “do it now”
Yana kaiwa nan ya aje wayar hawaye na zubowa akan fuskanshi, he’s so sad.
Karfe Tara Amar ya fito daga dakinshi, shima bai samu tayi breakfast dazu ba, karasowa yayi inda suke zaune ammah da salima sai Salim Duk sun shirya tsaf, gaishesa salima tayi kafin ya karasa kusa da ammah ya gaisheta, suna gama gaisuwa tace “son breakfast fa?”
“No ammah Saina dawo zanyi”
Kallon agogon hannunshi yayi yace “let’s move ko,jet din has arrived”
Kallonshi amma tayi don tambaya chan kuma Tayi saurin kauda tambayar Tata ta miqe suka fito gaba daya, shima Aman fitowa yayi daga dakinshi idanunshi kan salima itama kallonshi take kamar yau ne ta fara ganinshi, lanatan ma Harda ita a Yan rakiya, suna fitowa harabar gidan ya fiddo da katuwar Range Rover dinshi, driver ne ya soma shiga da akwatinsu bayan motar kafin ya bude ma ammah gaban mota don already su salima sun shige baya, lantana Harda Yan hawayenta, wani irin horn akayi kamar yaqi, juyowa aukayi gaba dayansu Harda Amman dake shirin shiga motar don Ganin wanda ke shirin shugowa, gate na budewa a mugun speed daddy ya shugo da motarshi cikin gidan, baima kashe motar ba ya fito kamar a maye, idanunshi sunyi jaa sosai gadan gadan ya tunkaro inda suke tsaye ya kece da dariya ya kalli amar yace “dan ubanka Ka tsorata ne zaka dauke uwarka saboda kana tsoron karna kashe maka ita?”
Kallonshi Amar yayi shima Aman dai kalllonshi yake feeling so disappointed, runtse idanu ammah tayi ta kalli amar shima kallonta Hajo ya mata alamu data shige cikin motar kawai karta tambayi komai, bude kofar tayi tana shirin shiga daddy ya sake cewa “kinyi asarar haihuwa maryama, kina tunanin zaki iya guduwa daga wajena?, Har abada!!!!”
Juyowa tayi ta kalleshi irin kallon kodai Ka hauka ce ne, “Alhaji yanxu fisabillahi ya kamata Kana magana haka agaban yaranka? What is the meaning of this? You’ve gone so far this time around”
Wata irin dariya daddy yayi ya kalli amar yace “wow, so she’s your weakness huh?”
Dariya daddy ya sake yi yace “lallai tarihi zai maimaita kansa ubanka ma haka ya ganni kuma ya barni Har daukewar nunfashinsa balle kai karamin kwaro bazaka taba kaini kasa ba,”
Idanun amar ne sukayi jaa sosai, jijiyoyin wuyanshi sun Tashi sosai yace “don’t ever say a word about dada”
“Orrr kana tsoron Kar uwarka ta gano komai?”
Kallon ammah yayi yace “ke kuma dan da kike alfahari dashi shin kinsan sirrikan dayake boye maki?”
Juyowa ammah tayi don kwata kwata sun saka ta cikin duhu,bata gama processing komai a ranta ba daddy ya soma yi masu debar albarka anan tsaye,aman dai ya kasa cewa komai, suna nan tsaye karar jiniya ta karade anguwan gaba daya, ahankali gate ya fara budewa nan take motocin sojoji kusan guda hudu suka shigo cikin harabar gidan ajere, nan take sojojin suka fara durowa daga cikin motar daya bayan daya suka zagaye gidan, amar dai mamaki yake karara haka zalika daddy da bakinshi ya mutu murus, asad ne ya karaso inda sukewsanye cikin maki yace “you’re under arrest” nan take asad ya dago warrant arrest paper ya nuna mashi,sojoji biyu ne suka zo gaban daddy suka dukar dashi kasa, saurin runtse idanu Aman yayi ya kauda kanshi gefe hawaye na zubowa, takowa asad yayi gaban Amar yace “sorry sir we have to do it, naga you looks surprised,Ka duba internet yau kuwa alhamdlh komai yazo da sauqi?”
Kallon mamaki Amar ya mashi kafin ya buqaci Ganin warrant arrest din karantawa ya somayi, kafin ya kalli asad yace “why didn’t you consult me? Kasan hakan da kukayi abunda zai jawo?” Ya fada yana kallon bangaren amma da gaba daya shock ya hanata bude baki tayi magana “so sorry sir, I have to do it,”
“Take him away” Amar ya fada kai tsaye kafin ya taka Har inda ammah ke tsaye ya dafa kafadarta, dan dagowa tayi ta kalleshi idanunta na kawo ruwa tace “what’s going on here?” Kasa magana Amar yayi sai rike hannunta da yayi trying to calm her down, daddy da ake shirin tafiya dashi ko ajikinsa ya soma dariya ya juyo ya kalli inda suke tsaye ita da Aman yace “this is just the beginning son,wannan ne babban kuskuren da zakayi a rayuwarka” kallon ammah yayi yace “maryama yanxu zakiyi alfahari da la’anann danki ko?”
Dariya ya kece dashi yace “Ina tausaya maki Maryama,anyways ga danki nan abun alfaharinki”
Kallon Amar yayi yace “ka kula da uwarka sosai kaji, because Ina nan tare da daku ina gaban ku Ina bayanku kai Har Kwanan abuncin ku nan bari ba Ina nan tare daku, and mark my words saina tarwatsa farin cikin ku, you’ll regret this”
Cikin sojojin ne wani ya taliyo kafarshi kasa Har yana kara don ya bugu sosai, dukda haka bakinshi bai mutu ba dukda suna shirin turashi cikin motar, dagowa yayi ya sake kallon inda suke yace “hope Ka fadama uwarka lalatar da kake yi achan wata kasar daban daya hanaka dawowa zama anan? Da auren da kayi achan”
Wata irin dariya ya kece dashi kafin a tura keyarshi cikin motar yace “Saina kawo karshe ku bakusan dawa kuke dealing ba hahahahaha”
Haka nan aka fuce da daddy daga cikin gidan.
Ahankali ammah ta cire hannunta daga cikin na Amar ta kafa mashi idanunta da sukayi jaa fusknata ma tayi jaa sosai, kallonshi disappointment take mashi tare da tuhumarsa, Amar dai tunda ta cire hannunta cikin nashi jikinshi yayi sanyi, bazai iya yi mata karya kuma ba, yanda Duk ta furgice yasa hankalinshi ya Tashi don abunda yake tsoro kenan, kallon mamaki take mashi don ko ba a fada mata ba tasan abunda daddy ya fada haka ne don fuskar Amar ta tabbatar mata da hakan ba tare da tace komai ba ta shige cikin gida kamar zata fadi, su salima ma fitowa sukayi don agaban idanu su akayi komai, cikin suka wuce Harda Aman, Amar dai yana nan tsaye ya kasa motsawa, fuskan amma kawai yake hangowa da yanda take mashi wani kallo mai wayar fasaara, da kyar ya daga kafafunshi ya shiga cikin parlor, babu kowa a cikin parlor don haka ya wuce sama direct jiki a mace, ahankali ya bude kofar, a zaune ya taddata ta dafe kanta, karasowa yayi har inda take, ya dan tsugunnaa gabanta yace “ammah pl….”
Hannu ta daga mashi tace “bana son wani kwana kwana, you have played me for so long so just answer my question”
Gabanshi ne ya bada wani damm, kallonshi ta sakeyi fuskanta a daure kana ganinta kasa tana cikin damuwa tace “wace irin rayuwa kake yi a dubai?” Sunkuyar da kanshi yayi kasa yana jin wani daci aranshi, daka mashi tsawa tayi tace “answer me now!!!!!”
Dan dagowa yayi Ganin yanda hannnunta ke karkarwa yace “ammah na please calm down”
Wani irin kallonta watsa mashi tace “you’re asking me to calm down?, Muhammad answer my question before rabka ya baci anan” ta fada on top of her voice,
Gaba daya ya rasa abunda zaiyi don baya son ta ta da hankalinta, “idan ba zakayi magana ba get out of my room, I don’t want your presence” ta fada tana nuna mashi kofa, hannunta ya sake kamo ta fusge ahankali hawaye ya soma sauka a fuskanta tace “Muhammad fasiqanci kake yi daman? When? Tarbiyar dana baka kenan? Yardar danayi maka kenan? Whyyyy”
Wani irin kuk ne ya kufce mata, nan take hankalinshi ya Tashi, yau mahaifiyarshi ta zubda hawayenta akanshi, innalillahi wa inna iliahi rajiun”
A furgice ya dago yace “ammah please karkiyi judging din komai, I can explain”
Wani irin kallo ta watsa mashi tace “yanxu zakayi explanation kenan?”
Dan dago da jajayen idanunshi yayi ya riko hannunta da kyau yace “wallahil azeem nan taba fasiqanci ba, nan taba neman matan banza ba,”
“Okay so??? What are you hiding? You expect me to trust your words now?, son Ka bani mamaki” hawayen dake zubowa a fiskanta yayi sauri share mata yace “please ammah ki diana zubda hawayenki, allow me to explain”
Shuru tayi tana kallonshi, Sunkuyar da kanshi tayi kasa don kunyar kallonta ma yake yace “I got married 8 months ago”
Zumbur ta miqe tsaye ta kalleshi tace “you what?” Dawo da ita yayi ya zauna yace “dan Allah ki kwantar da hankalinki amma”
“How do you expect me na kwantar da hankali na? Muhammad aure fah? Aure kayi ba tare da sanin mahaifiyarka ba? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,”
“Ammah please kiyi hakuri ki yafe min dan Allah, karkiyi fushi dani idan kikayi fushi bansan ya zanyi ba”
Kauda kanta gefe tayi tace “give me one good reason”
Shuru ya danyi kamar bazaiyi magana ba don nauyin maganar ma yake ji sannan yasan she will hurt and disappointed at the same time, runtse idanunshi yayi kanshi a kasa yace
“I’ve been diagnosed with oligospermia “
Da sauri ta dago ta kalleshi, don she couldn’t believe it, wani irin hawaye ne ya sauko akan fuskanta,oligospermia data sani dai? Wanda mahaifinshi yayi battling dashi Har suka fidda rai suka barma Allah cikin ikonsa kuma ya kawo mata cikinshi daga shi kuma shikenan,
Kallonshi tayi tace “oligospermia? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,when did you found out?
“5 years ago” ya bata amsa
Runtse idanunta tayi take taji wani irin nauyi a zuciyarta “meysa baka fada min ba? Why??”
Shuru yayi ya kasa dago idanunshi ya kalleta “you’ll be disappointed kawai kuma nasan zaki saka damuwa aranki”
“Ni ba mahaifiyarka bace? Kana da wanda ya fini ne eh?” Ta fada rai abace
Shuru ne yadan ratsa kafin tace “who did you get married too? Dama chan kana da wadda kake son aura ne?”
Dan dagawa yayi yace “no, yarjejeniya kawai mukayi”
“Bring her this instance,” ta fada babu wasa a fuskanta
“Ka kawota koma wacece inason naji daga bakinta because I can’t trust your words”
Dan dagowa yayi kamar zaiyi kuka yace “Ammah please, everything has come to an end, Ina komawa Zan sake ta, the deal has been done”
Kallonshi ta sake yi tace “ni kake fadama the deal has been done? So Akwai more to this discussion kenan? Na baka dama Ka fada jin komai you wasted that chance now get out of my room na baka nan da awa 24 Ka kawo koma wacece ita”
Tana fada ta mike ta shige cikin bathroom ta barshi nan tsugunne hankali atashe,rasa abunyi yayi don this is the first time yaga fushin mahaifiyarshi, fita yayi daga dakin hankali atashe ya soma dialing contact din m5, yana picking ya bashi umarnin yayi booking flight ticket for amra, ayau yau dinnan.
Monday morning..
Uae
Amra dake cikin school taje submission na report dinta, bata wani dade ba tana gamawa ta fito daman m5 ne ya kawota, she was so excited komai yazo karshe don Har clearance sun gama yi certificates kawai za a basu, tana fitowa harabar makarantar m5 ya bude mata bayan mota kafin su fuce daga compound din, yanda taga yana tuki agaggauce kamar zasu Tashi sama yasa hankalinta tashi, bata ce mashi komai ba Har suka iso airport, dago da idanunta tayi kafin ta kalleshi, ba tare da wani bata lokaci ba ya fito tare da bude mata bayan mota, dinkin ta futo, fitowa tayi tana kallon ikon Allah, me hakan ke nufi kenan? Kallonta yayi yace “ma’am you’ll depart in 10mins from now”
Azafafe ta dago da ta a bace tace “to where?”
Ba tare da wani Kwana kwana ba yace “Nigeria”
Shuru ta danyi tana nazari chan kuma ta dan sake aranta tace “faduwa tazo daidai da zama”
Gaba yayi tabishi abaya suka shiga cikin airport din, babu komi a hannunta daga ita sai handbag dinta, sanye yake da abaya orange wanda ta amshi jikinta sosai tayi mata kyau, aggauce m5 ya gama yi mata komai y bata boarding pass saboda babu wani kaya da zatayi weighing don haka yayi mata sallama ya wuce abun shi….
Kallon boarding pass din tayi Ganin a abuja jirgin zaiyi landing yasa ta tabe baki tace “not this time around”
Karfe uku daidai na yamma flight dinsu ya daya zuwa nigeria….
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.