Best Hausa Novels

Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx

Chapter 3 of 52

Chapter 107

Update……

Washe gari ya kusa makara sallan asuba don Sai wajen karfe bakwai ya tashi, toilet ya wuce direct ya watsa hot bath da body wash dinshi masu shegen tsada da kyau, cikin natsuwa da kamewa ya futo, bai tsaya wani shafe shafe ba ya shingida sallaya ya fada kabbarar sallah yana idarwa ya fara shirin tafiya, normally yana aje travel box dinshi da Duk abubuwan buqatanshi daya Tashi tafiya kaya kawai zai deba wanda zasu ishesa tsawon kwanakin da zaiyi, wani lokacin kuma pablo ke hada mashi sanin yawanci kayan daga jallabiya sai kananun kaya karasa nauyi wanda yawanci yafi buqatansu musamman idan zaiyi tafiya Kasashen da ake yawan zafi sosai, yana gama hada box din nashi ya fidda kayanda zai saka, farrar Riga ya jawo ta brand din Ralph Lauren wanda ke cikin manyan collection din kayansa, sanin yanayi weather na nigeria a lokaci yasa ya dauko dogon wandon army ya saka, kafin ya feshe jikinshi da hadaddun turarukanshi masu da yin kamshi da tsada, laptop bag dinshi kawai ya jawo da wayoyinshi kafin ya sauka kasa, bai tsaya ko Ina ba Sai dining area, bai wani tsaya cin abunci da yawa ba, coffee kawai ya buqaci pablo yayi serving dinshi da english breakfast, cikin natsuwa ya gama cin breakfast daidai nan m5 ya shigo, saida ya gaishesa ya shaida mashi komai is ready kafin su fito tare m5 na gaba ya bude mashi bayan katuwar jeep dinshi da tasha zanen army a jiki kana ganin motar kasan ta manya ce, Pablo ne ya fito dauke da baggage dinshi, da mugun speed suka fuce daga penthouse dinshi, tafiyan 20 mins sukayi suka iso uae international airport, lokacin da suka iso kusan sauran 30mins suyi taking off, yana zaune hakimce kamar bazai fito daga motar ba idanunshi a lumshe yana tunanin abubuwa da dama wanda suke mashi yawo, saida ya dauka kusan minti goma kafin m5 ya bude mashi kofar ya sanyo kyakyawar fatar kafafunshi waje, wayanshi kawai ya rike a hannunshi yayi gaba m5 ya rufe kofan tare da janyi baggage dinshi ya bi sahunsa, bai tsaya ko Ina ba sai first class lounge, ya hakimce tareda daura kafanshi daya kan daya, turarenshi ne yayi ma mutanen dake zazzaune akan kujerun wajen sallama,nan kallo ya koma kanshi, wayanshi ya soma latsa wa ba tare da ya kalli kowa dake wajen ba don basuda wani yawa Ma a wajen don Sai yayan wane da wane ne a wajen.

M5 ne ya mashi Duk wani necessary arrangements, ya karba boarding pass dinshi, kafin ya wuce lounge din, cikin girmamawa ya aje mashi laptop bag dinshi gefen shi tare da su boarding pass dinshi da passport dinshi kafin ya mashi sallama ya fuce daga cikin airport din.

“Meeda kinga wani Hadadden guy kuwa, ya Allah ya hadu harta gaji da haduwa”

Wadda aka kira da meeda ce ta dago ta kalli inda ta gefenta ke nuna mata, wani irin maybe kallo ta Bishi dashi kamar zata hadu ya shi, nan take taji wata Kibiyar sonshi ta daki zuciyarta, da sauri ta hadiye wani irin Miyau ta juya tareda kallon kawar Tata tace “kam bala’i, zabgi wallahil azeem gayen nan ya hadu, kura bata ganin nama ta kauce” 

Dariya wadda aka kira da baby akay kafin ta juya ganin inda kawar Tata take tunkarowa, gaban shi ta isa lokacin ya mike don lokacin tashin jirgi yayi, kamar an wullota ya hanya gabanshi, dago idanunshi yayi da suka kusan saka ta suman tsaye dukda babu alamun dariya ko annuri a fuskanshi hakan bai hanata hango 

Sirrin kyau da yake dashi ba, gaba daya saida ta karaso gabanshi ya tafi da imanin ta, cikin yanga da iyayi irin na Yan mata da sukaji duniya, ta soma magana “assalam handsome”

Tsayuwanta a gabanshiya bashi daman yi mata kallo daya don ya fita tsayi sosai, kananun kaya ne a jikinta wanda ya fidda surar ta sosai, batada wani kyawun jiki don komai ya gama yin lanqwasa nan take ya soma jin kyankyamin ta, kauda sexy eyes dinshi yayi gefe ba tareda ya sake mata kallo daya ba ta sake magana “sunana hameeda idan babu damuwa inason na san sunanka harma dakai din gaba daya” ta karashe tare da juya idanuwanta wanda shi baida lura da hakan ba, wani irin disgusting kallo ya mata tare da giftawa gefenta ya wuce, kamshinsa ne ya daki hancinta nan take ta lumshe idanu ba tare da ta damu da dizgata da kallon da yayi mata ba, kawar ya kuwa dake zaune ne zatayi Banda dariya harta juyo ta dawo inda suke zaune, “ke meeda daman wannan Ay yafi karfinki nesa ba kusa ba, kidai lallaba da sugar daddies dinki dake baki kudi suna biya maki jirgi kina zuwa hutawa”

“ hmm baby bazaki gane ba, wallahil azeem ban taba ganin hadadden gaye wanda kina ganin shi kinsan ya juqu da kudi ba kamar wannan,”

Kallonta baby tayi yanda ta lumshe idanu tana smiling hakan ya tabbatar mata da abunda ta hango a idanunwan kawar tata 

“ Toh mayya, kedai ako Ina Sai kin nuna zalama, irin wannan Mazan dai kinsan basa daukan raini,don mugun wulaqanci ne dasu,”

Ganin kamar bata sauraronta yasa tace “malama saiki Tashi kamu tafi ay tunda kinaji an kira flight din namu”

Kallonta meeda tayi tareda daukan wayanta tace “Toh tsaya muyi hotunan posting mana”

Karban Wayar baby tayi tace “ aikin banza, dama dai rayuwar karyarki da kika saba kika bawa himma da zalama ba irin wadannan Samarin ba”

Hotuna zafafa suka dauka, kafin su wuce cikin jirgi, suna shiga kuwa direct first class area suka wuce, tattara idanuwa meeda ta soma yi ko zata ganshi saidai bata samu damar hakan ba akayi announcing take off, daman seat dinsu ba roll daya bane da baby don haka bata damu da wanda ke gefenta ba da yake a rufe ba, baka ganin wanda ke ciki ta zauna, wayanta ta fidda ta soma zafafan hotuna Harda tsaida wata crew ta sakata yi mata hotuna, cikin qanqanin lokaci jirginsu ya daga.

Saida tafiyan tayi nisa har aka fara zuwa rabon  wine da juice harda starter ga masu buqatan Ana zuwa wajensu kuwa matar ta tambayeta abunda yake buqata, ba tare da bata lokaci ba tace red wine, nan take matar ta zuba mata, kallon gefenshi matar tayi tare da zagayowa gefenshi tace “sir would you like to have anything, juice,water,wine”

Cikin dakakkiyar muryarshi kamar na zaiyi magana ba yace “no thanks”

Jin daddadar muryarshi yasa hameeda sako kanta don ganin mai maganar, nan take idanunta suka sauka akanshi, cikin sauri ta koma ta zauna tana wani murmushi mai ma’anoni daban daban, kallon matar tayi tace “can I get something else please”

Sauya wine din tayi zuwa juice, tunda ta tabbatar shine ta Kasa sukuni, fatan ganinshi kawai takeyi don gaba daya bangarenshi a rufe yake, goga kuwa bai Ma san tanayi ba don tunda tazo gabanshi dazu kallo daya ya mata yaji kyankyamin ta a gabanshi yasa manta da ita nan take, don bashi da time din irin wannan matan.

Saidai yayi mamakin jin bahaushiya dake kusa dashi wanda ta buqaci a bata giya saidai shiga hurumin da ba nashi ba baya cikin tsarinsa don bai fiye bama mutane attention ba.

Tana nan zaune aka soma kawo abunci nan take ya bada order abunda take so still tana fatan ya zuge nash bangarenshi saidai bata samu daman hakan ba, kofa suka tambayi abunda yake buqata, juice kawai yake su kawo mashi nan take kuwa aka kawo mashi hadadden juice tare da glass cup, matar na kokarin zuba mashi takalmin kafar ta yayi slippering ta zuba mashi juice din akan jacket din daya daura kan farar rigarshi, Allah ya taimaka bai zuba a jikin white Riganshi ba, hankalin matar ne ya Tashi ta soma bashi hakuri, kai kawai ya girgiza mata ya miqe zuwa toilet ba tare da kallon gefenshi ba, gyaran wajen data bata mashi crew din tayi karfin ta koma don kawo mashi sabon juice din,yana shiga toilet din ya Gyara jikinshi kafin ya futo, meeda kuwa da taga wucewanshi toilet cikin sauri ta bi bayanshi, yana bude kofar kuwa zai fito ta kame hanyar ta zuba mashi idanu kamar mayya tace “do you need any help?”

This time around tsayawa yayi ya mata kallo tsab take ya gano itace ta buqaci wine, mamakin yanda yayan musulmai suka lalace yakeyi qira qira yasan tayin wani abun yake mashi daban saidai bata san cewa shi ba irin mazan nan bane ba, Karon farko ya bude bakinshi dake kamshin mint yace “you’re so disgusting,get the hell out my way”

Ya fada idanunshi sun nuna babu wasa a cikin zancen nasa, a burkice ta matsa mashi baya dinta tsorata da yanayinshi tana nan tsaye wata crew tazo wucewa yace “get me head of Crew staffs now!!!!”

Wucewa yayi nan kuwa meeda ta tsaya kyam don Duk ihun nan dayayi akan idanun mutanen dake zaune kusa da toilet dinne, kunya yasa ta komawa cikin toilet din ta rufe kanta a ciki.

Goga kuwa ya shaka sosai, don haka head of staff na zuwa babu bata lokaci ya buqaci roll guda ba tare da kowa ba, Allah yaso kuwa Akwai roll din da babu passengers nan take ya sauya zuwa chan don baya buqatan hayaniya dukda Sai ya biya kudin roll din gaba daya wannan ba damuwa shi bane don kudi kam Akwai su.

Ganin zaman cikin toilet bazai amfane ta da komai ba sum sum ta fitowa wuce wajen mazauninta, baby kuwa da take Yan gaba gaba me zatayi Banda dariya don akan idanunta akayi drama din. Kwafa tayi tace “shegiya kai taurin kai da zalama, maganinki kenan, nan gaba bakya kara tunkarar irin wadannan yan girman kan ba”

Meeda kuwa tana komawa seat dinta ta kame, ganin baya wajen yasa ta jin wani iri, saidai tayi alkawarin koma waye shi saita nemo shi kuma ta nema abunda take buqata.

Karfe takwas daidai jirgi su na emirate ya sauka ah Nnamdi azikiwe international airport abuja, saida kowa ya tsaya  akayi clearing ko ina kafin ya sauko cikin isa da kasaita, nan fa kowa ya soma kallon isa da harkar manya cikin Yan kallo kuwa Harda meeda wadda yanxu kam ta cire rai don taga fin karfi nesa ba kusa ba, gaban jirgin motoci manya manya kusan guda biyar a jere hade da sojoji suka zo tarbanshi, dan wannan official zuwa ne ba normal zuwa da yake yi ba na visiting Ammahn shi,Sara mashi aka soma hi kafin a bude mashi katuwar lexus baqa tinted, sauko wa yayi hannunshi rike da jacket dinshi Dayan kuma ya zuba cikin aljihun wandonshi, direct gaban Lexus din mai plate number hade da sunan TAURA a kasan da manyan harufa ya tsaya sojojin suka soma Sara mashi irin gaisuwar su ta sojoji, kamewa yayi bayan motar kafin a rufe mashi suka juya harsuka fuce gaba daya da tawagar datazo tarbanshi.

Ranar kuwa abuja ta shaida babban sojan uae ya iso nigeria, wanda basu san da zaman shi bama su san da zamanshi ba sun sani saidai kuma babu wanda yasan fuskanshi.

Bude laptop bag dinshi yayi ya fidda da wallet dinshi da yake zuba Duk wasu sims dinshi na kasashe daban daban, Ciro din din Nigeria yayi na mtn ya bude wayanshi ya musansa ya aje na uae, yana kunna wayan ya soma dialing wata number ya kara kunanshi Ana dagawa daga chan akace “oga harka iso kenan” 

“Wannan mutanen fa daka hadoni dasu, kasan fa bana son hayaniya, infact bana son Adam na shigo kasar nan Ma sbd aiki ne zamuyi cikin sirri”

“Toh ka fa dawo kenan, anyway na turo su ne sbd bazan samu zuwa tarbanka ba”

“ please call them, bana buqata su”

“Okay, anyway gida zaka wuce yanxu? Zan shigo anjima daman nasan ni mai laifi rabona da Ammah tun bayan rasuwar dada,”

“No karka damu ba gida Zan wuce ba, heading somewhere else, zamu hadu gobe kawai”

“Yes ranka ya dade sir”

Ya fada yana dariya kafin ya aje wayan.

General asad Abdullah kenan da ga abokin Alhaji taura kuma babban aminin sa tun tasowarsu, shima mahaifin sa ya rasu saidai zumuncinsu bai dauke ba tsakanin yayansu dukda ba wani kusanci suke dashi sosai ba, asad shima soja ne mai rike da babban mukami na chief of army staff anan Nigeria(lieutenant asad Abdullah) ya girmi Amar sosai saidai yanda Amar keda kwarjini zaka dauka zai fishi ma.

Kallon sojan driver yayi bayan ya gama wayan yace “to larrics estate”

“Yea sir” yayi saurin amsawa

Maida kanshi yyi bayan kujeran ya lumshe idanunshi Har wani bacci baccin gajiya ne ke neman fuzganshi.

Horn din da driver yayi ne ya tabbatar mashi da sun iso, drivern yana parking yayi saurin bude mashi bayan motar futo cikin kamewar shi, tunda ya sanya kafafunshi kasa yake jin wani irin niima na saukar mashi, kamshin kasa da bushiyoyi tare da sanyin dake kadawa ne ya bade ko’ina, lumshe idanunshi yayi kafin ya soma takawa gaban entrance din, cikin sauri driver ya karaso gabanshi ya Danna door bell din tare da janyi baggage dinshi, bude kofar da akayi ne ya sashi dago kanshi, Nadine data bude kofar saida tadanyi baya, sauke kanta Kasa tayi kafin tace “welcome sir”

Don Duk kwarjininshiya cika ko’ina, ba tare da ya kalleta ba ya raba gefenta ya wuce ciki, saida ya karema ko’ina kallo kafin ya juya ya kalli Nadine data karaso da akwatinshi da laptop bag dinshi, sama ya wuce tabu baya shi da akwatinnashi,karema gidan kallo yayi tsab babu abunda ya sauya Sai furnitures da yasa aka sauya zuwa sabbi, gidan yana daya daga cikin properties dinshi daya gina da kudinsa saidai bai banbantashi da saura gidajenshi ba da yake hadawa da inkiyar sunan familynsu wato TAURA

First stair ma ya fara hawa saida ya tsaya ya karema ko’ina kallo kafin ya hau sama da yake na master bedroom a ciki Sai tapkeken sitting area Harda dining, bude kofan bedroom din yayi direct ya saka kanshi ciki, yana nan yanda yake saidai kayan alatu shima da aka chanza, Nadine kuwa tana karasowa daidai gaban dakin ta aje akwatin tareda Rossi awara gaishesa, bai kalleta ba ya amsa da “uhm” bai sake cewa komai ba saima kafama babban frame din dake gefen bedside dinshi idanu yayi, hotone shida dadan shi lokacin da yana school yazo mashi surprise visit, muryar Nadine ne ta katse shi don yana dauka ta fuce “sir do you need anything”

“no thanks ya amsa”

Yana son tambayarta inda yarinyar nan take saidai kuma ya basar yace “you are excuse”

Tana shirin futa yace “just coffee in the next 1hr”

“Yes sir tayi saurin amsawa “

Sauko wa tayi ta wuce dakin amra, wadda tunda ta zo kwana biyu kenan bata lekowa ko’ina, abincin Ma daki Nadine ke kawo mata shi, bude dakin Nadine tayi ganin an rage hasken dakin Saina bedside yasa ta kallon fuskanta mamakin yanda ta dage da kuka kullum wanda ya sanya idanunta yin ciki ciki Nadine keyi saidai bata taba tambayarta dalilin hakan ba don ba huruminta bane, gani ko taba abuncin ta saya kawo mata batayi ba yasa ta jawo mata kofar ta rufe ahankali, Kasa ta sauka ta fara diban time gudu min karya wuce lokacin daya buqaci coffee.

Wanka ya farayi kafin ya futo daure da towel, closet dinshi ya bude ganin komai nashi yana nan yanda ya barshi yasaashi yabawa da company daya bama maintainance din gidan hatta sabulun shi da abubuwan buqatanshi Duk an zuba mashi a ciki, jallabiya ya zura ya tada kabbarar sallah, saida ya Rama Salomon da ake binshi kafin ya miqe ya sauya zuwa kayan baccinsa farare don kusan karfe 10 na dare kenan, knocking akayi ya bada umarnin shigo, aje mashi coffee din tayi kan table kafin tace “sir here’s the coffee” bai kalleta ba haka zalika bai amsa ba, ganin kamar bai Jita bane yasa ta maimaitawa

Gyaran murya kawai yayi yace “you’re excuse”

Sum sum ta fuce ganin yanayinshi na rashin magana,

Saida yasha coffee don ya janyi laptop dinshi ya soma wasu Yan ayyuka, Sai kusan karfe 1 ya aje laptop din ya rage hasken dakin ya kwanta.

Washe gari kuwa a kunnanshi aka kira sallah asuba, dadin gida kenan, muke wa yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa mai zafi kafin ya futo Sai zuba kamshi baths dinshi yake, gajeran wandonshi ya saka kamar koda yaushe  kafin ya  zura jallabiyanshi ya fuce daga dakin, benne farko ya fara sauko wa ganin ko’ina dim ya sashi sauka kasa, nanba dai dim dim babu hasken kirki saina censor light din daua tsaya a wajen, fucewa yayi daga gidan ya wuce massallacin dake cikin estate din, masllacinma haduwanshi ma yakai a fada, ko’ina kamshi da sanyin ac ya gama bade cikin massalaci tsaf tsaf very clean, very few mutane ne a cikin masallacin hakan yasa Ana idar da sallah mutane suka soma ficewa, zama yayi saida yayi azkar Sai wajen karfe bakwai ya fito daga masallacin, direct gidanshi ya wuce Nadine dake goge goge tana gani shi ta rissina tace “good morning sir”

Daga mata kai kawai yayi ya wuce sama direct dakinshi, jallabiya shi kawai ya tube ya fuce daga dakin, second floor ya sauka ya wuce Dayan dakin dake gefe inda yake gyming dinshi don baya sake da physical health dinshi, ya dauka kusan awa daya da rabi kusan karfe 8:30,futowa yayi ya wuce sama ba tareda kallo side din Dayan dakinba da yake kyautata satin anan take kwana, wanka ya shiga nan ma saida ya shafe kusan 30mins ya fito, shirinsa yayi kamar na jiya saidai na yau din yafi na jiya kyau, yauma wa don army ne a jiki shi hade da rigarsa saidai ya daura had dadi yar jacket dinshi a sama, briefcase dinshi ya jawo tare da wayanshi ya sauko Kasa Sai baza kamshi yake, yana sauko wa Nadine na futowa daga cikin kitchen, da sauri tace “ breakfast is ready sir”

Baibi ta kanta ba ya wuce dining tayi serving dinshi chips da beef sauce da soyayyan plantain, da coffee, kadan ya tsakura yaci kafin ya kira driver yazo, kika mashi briefcase dinshi yayi yace “get the car ready now”

A Gurguje ya gama shan coffee din ya fuce daga gidan, gaba daya, Nadine na ganin fitar shi ta tattara dining din ta deba na amra ta wuce sama don kai mata nata.

Lokaci data shiga dakin babu kowa a ciki, jin alamun saukan ruwa ya tabbatar mata tana wanka, Ajiye tray din abunci tayi gefen ottoman din dake hade da gadon kafin juya ta rufe mata kofar dakin, futowa amra tayi daure da towel dinta, gaba daya fuskanta ya dan kumbura alamun damuwa da kukan da take,ganin tray agefe ya tabbatar mata da nadine ce ta aje mata, agurguje ta shirya cikin kayan zaman gida masu kyau, doguwan rigace mai Dan hannu,kayan ya amsheta sosai, zama tayi ta tsakuri abunci ta soma ci badon ranta naso ba saidan yunwa dake nuqurqusar ta, wayanta ta jawo ta soma kiran haifa saidai kwata kwata wayan baya shiga, gaba daya ta rasa abunyi, babu irin tunanin da batayi ba, da farko ta yanke shawarar gudu kano saidai kuma bata san daga inda zata fara ba ga tsoron abunda zata tarar achan, saidai kuma tunanin qannenta ya bata karfin gwaiwar komawa don sanin halin da suke ciki gashi ba wani kudin kirki yake dashi ba gashi batama kawo zancen ragowar kudinda yake dashi cikin account dinta na chan ba don indai anyi banning dinta daga shiga kasar account dinta shima dole za ayi banning.

Tagumi ta doka don gaba na daya abun duniya ya isheta.

Wunin ranar kamar kullum a daki tayi shi bata leko koda parlor ba haka zalika nadine ma batace mata komai ba akan zuwan shi.

Karfe goma sha daya ya shugo gidan, nadine ce ta bude mashi tare da mashi barka da zuwa, baibi ga kanta ba ya wuce sama, saida ta tabbatar ya huta kafin ta Kwankwasa mashi

Kofa, tana shugowa tace “ what would you like to have sir”

“ just coffee”

Ya amsa mata,

Futa tayi ta Hado mashi coffee din kafin ta fuce, coffee din yasha kafin ya wanke bakinshi kafin ya fito yabi lafiyan gado don yasha aiki sosai.

Washe gari Ma haka ya Tashi da wuri ya fuce bai Ma tsaya yin breakfast ba, don ya samu Kiran gaggawa daga wajen asad inda yake shaida mashi sun samu clue akan wani member na empire saidai tracing dinshi ne ya basu wahala sosai don sun Kasa samun hanyar da zasu Farke mashi, sunma Kasa gane waye saidai ta wani account da akayi transacting wasu kudade in dollars wanda yanda suka gano hakan shine sun bibiyi account din suspect din da aka kama achan uae tana suka gane inda yake transacting kudin,bai samu dawowa da wuri ba Sai wajen karfe sha daya.

Washe gari kam bai Tashi da wuri ba Sai wajen karfe sha daya, wanka kawai yayi don weekends ne bashida plans din futa, sitting room ya sauko ya zauna bayan ya gama karin kumallo, wayanshi ne rike hannunshi yana receiving wasu calls masu amfani, yana gamawa ya danyi jin yanason kiran ammah ya shaida mata yana Nigeria saidai kuma yasan zata fara expecting dinshi shikuma bayason zuwa gidan saiya gama Ayyukan da yake, bayaga wannan bayason taji ya na nigeria a wani wajen, dialing number yayi, tana picking kuwa suna gaisuwa ta soma tambayanshi yaushe zai zo Nigeria ta matsu ta ganshi, 

“Ammah zanzo very soon Insha Allah”

“ babana, na Kasa gane dalilinka na qin zuwa kasarka inda aka haifeka,”

“Ammah please calm down shikenan zanzo next week Insha Allah”

Sanin baya mata magana biyu ya sata saurin cewa “da gaske son”

“In sha Allah ammah”

“Alhamdulillah Allah ya kawo ka lpy, yarannan ma are so excited to see you”

“Uhm suna zuwa school din kuwa”

“Sun fara zuwa fah, saidai Muhammad baka min bayani ba yanda Zan fahimta,”

“Amma ki bari idan nazo Zan maki bayani dallah dallah”

“Toh Allah ya kawo ka lpy”

Sallama sukayi kafin ya kashe wayan ya fuskanci katuwar tv dake aiki babu sauti sosai

Bude kofar dakin tayi ta fito, sanye take da doguwar rigar abaya sky blue tasha stones,fuskanta fayau babu walwala, idanunta sunyi ciki ciki da alamu ta danyi kukan da ta saba ne,babu komai a kanta Sai ribbom data nade jelar gashinta dashi duban parlorn ta soma yi kafin ta wuce stairs cikin nutsuwa kanta a Kasa take takawa harta kai karshe stairs din, bata tsaya dube dube ba ta gifta parlor da yake zaune ta wuce kitchen direct,alamun saukowanta hade da takun ta cikin natsuwa ya ankarar dashi,zuba mata kyawawan idanunshi yayi har ta shige kitchen, yana nan zaune idanuwanshi kan hanyar kitchen din ta fito hannunta dauke da bottle water mai sanyi tasha kusan rabi hannunta dafe a goshinta,harta sanya kafarta kan stairs ta tsaya chak, wasi wasi ne ya shiga ranta na kamshin sa dataji lokaci guda ya shiga hancinta, kalle kallen hanyar shugowa ta soma yi har lokaci. Idanunta bai sauka ga sitting room din da yake zaune ba runtse idanunta tayi ta bude jin jira na neman Zubar da ita lokacin da idanunta suka Sarqe cikin nashi, kamar a mafarki take ganin komai, rufe idanunta tayi ta sake budewa akansu, Har lokacin shima idanunshi nakanta, kafin ya kauda kanshi gefe kamar bai ganta ba, kafafunta ne suka Gaza daukanta saida ta dafe handle din stairs din,miqewa yayi ya soma takowa, Duk takun shi daya jinshi take a kirjinta, saida yazo dan da ita hannunshi sanye cikin aljihun Riga da gajeran wandon dake jikinshi ya zuba mata idanunshi kamar zai cinyeta, Kasa dauke nata idanuwan tayi daga kanshi itama Sai wasu siraran hawaye da suka soma ambaliya a fuskanta, baya ta soma yi kamar zata fadi hannu daya yasa ya tsaidata ta hanyar janyo nata, fuskanshi babu alamun annuri akanta, kallonta yayi tsaf kafin ya kauda kanshi gefe hade da tabe bakinshi ya gifta gefenta ya wuce sama, haka kawai taji kamar kallon tsana yake mata tsabar ta rude,ganin yana neman kauracema ganin ta yasa ta saurin bin bayanshi lokacin harya wuce daki, ya rufe kofa, tana karasawa gaban dakin batayi wata wata ba ta bude kofar dakin ta shige, lokacin har yakai bakin gado jin alamun an bude kofa yasashi juyowa ya kalleta kafin ya kauda idanunshi daga kanta 

Bakinta take motsawa alamun don furta abu saidai ta rasa da wani kalamai zata tunkareshi, tsinkayar daddadar muryarta yayi a kunnenshi “I’m so sorry” ta fashe da kuka sosai mai sanya ya zuciya, runtse idanu yayi don baya Kaunar jin kuka kwata kwata 

Bai kula ta ba saida ta tako Har gabanshi ta sake maimaita kalaminta hawaye na zubowa daga kan fuskanta “ I’m so sorry”

“ what are you sorry for”

Ya mata tambayar babu alamun fara a a tattare dashi,

Kasa cewa komai tayi saima wasa da yatsunta da take kanta a Kasa, Kasa hada idanu tayi dashi, sarai yasan daman zatayi blaming kanta tunda bata samu bayanin komai a wanda ya haba m5 fada mata sbd Bayason kowa yasan plan dinsu don haka ya gyara tsayuwanshi don yagane taqamaiman abunda ke ranta

“Get out of my room”

Ya fada Adan zafafe 

Saurin dago rinannun idanunta tayi, tama rasa abunda ke mata dadi, cikin Rudu tace “it’s my fault, Duk laifina ne, nina nemi taimakon ka badan ka taimake ni ba bazan jefaka cikin wannan halin ba”

“I’m so sorry, I’m so sorry, da na san wannan kaddararren auren zai jawo Ma kowa matsala da ban nemi yin shi ba me zanyi don ka yafemin dan Allah ,”

Zuba mata idanunshi yayi yana karantarta sosai

Tamke fuskanshi ya sake yace “I don’t want to repeat my self get out of my room now”

Yana kaiwa nan ya wuce toilet, kafafunta ne suka soma sare mata don gaba daya tunaninta ya tsaya chak, ya tabbata kenan, ya rasa aikinshi ta dalilinta innalillahi wa inna ilaihi rajiun ta furta a tsorace, 

General kuwa yana shiga toilet yadan saki murmushin gefen bakin kafin ya tsuke fuska yana jin yanda take sauke ajjiyan zuciya da sauri da sauri da alamun kuma ta da yake tsananta, saurin bude kofar yayi Ay kuwa Harda dan gudunta ta fuce daga dakin ya bita da mayun idanunshi ahankali ya furta “ cute” tare da dan murmushin da bai san yana yinshi bama.

Amra kuwa tana futa daga dakinshi Kasa ta wuce dakin da take kwana, ta kwanta kan gado hawaye nabin kuncin,gaba daya tsanarta take hango wa a cikin idanunshi, runtse idanunta tayi wani irin zazzabi na zuwan mata.

Tana nan kwancewa galabaice aka kira sallar azahar, muke wa tayi ta wuce toilet ta dauro alwala ta fito ta tada sallah tana idarwa ta miqa kukanta gurin Allah. Tana shafawa ta fito tama rasa abunda zatayi, parlor ta sauko ganin Nadine na jera abunci ya sata tsayawa gefe guda, sosai Nadine tayi mamakin saukowanta don haka tace “Ma kina buqatan wani abu ne”?

“No thank you”

Rasa abun cewa tayi don haka ta hau sama, cire hijab dinta ta fara yi kafin ta zaune gefen gado ta doka uban tagumi. Tana nan zaune Nadine ta shugo dakin tace “Ma na gama lunch akawo abinci yanxu Ko zakici a kasa”

Da sauri amra tace “barshi zanzo kasan”

Nadine na fita kuwa ta mike zumbur ta sauko kasa don dama neman damar sauka take, tana sauka kuwa ta zauna a dining Nadine tayi serving dinta, raraba idanuwa tayi tana kallon stairs saidai ganin babu alamun saukowanshi yasa ta maida hankalinta kan abunci dake gabanta don ko cokali daya bata kai baki ta ba,

Haka nan ta dunga tura abuncin badon tanaso ba don daci Ma abuncin yake mata, tana gamawa ta wuce parlor ta zauna idanunta kan stairs din shuru shuru saida aka kira sallah asr ta mike ta wuce sama.

Amar kuwa tun bayan fitar ta ya chanza kaya ya fuce daga gidan sai wajen karfe 10 ya dawo gidan yana shigowa yazo giftawa ta sitting room ya hangota shingide kanta yadan karka ce alamun barci ya kwashe ta a wajen, kauda kanshi yayi ya kalli Nadine data bude mashi kofa yace “ wake her up taje ta kwanta, and bring me just coffee”

Yana kaiwa nan ya wuce sama, amra dake jin maganganunshi da Nadine sama sama cikin bacci, Tashi ta nadine ta soma yi tace “Ma kije ki kwanta”

Cikin bacci amra tace “ya dawo ne?”

“Yes ma”

Shuru amra tayi takaici barcin daya kwasheta ne ya turniketa donta dade a zaune tana jiran zuwanshi, bata gama tunanin nata ba nadine ta fito hannunta dauke da mug da saucer, ganin tana nufa hanyar stairs yasa amra saurin cewa “ya buqaci coffee ne”

Kallonta Nadine tayi tace “eh”

Takowa amra tayi gabanta tace “kawo Zan kai mashi”

Mika mata nadine tayi kafin ta mata sallama ya wuce nata dakin, saita natsuwarta tayi kafin ta tunkari hanyar sitting room din saman, Sai a lokacin ta karema parlor saman kallo, kayan alatun parlor yafi na kasa kyau sosai, gashi da girma sosai, an kawata shi da kayan zamani masu tsada, hanyar dazai sadaka da dakin tabi saidai tana zuwa daidai kofar gabanta ya soma faduwa, runtse idanunta tayi tare da cije lebbanta ta kwankwasa, saida ya dauka mintuna kusan biyar kafin yace “yea come in”

Anatse ta soma bude kofar harta wangale ta shugo tare da rufe kofar ta tsaya daga bakin kofar kamar mai neman gafara tunda ta dago ta mashi kallo daya yana sanye da kayan barcinsa masu santsi, Riga da wando, wandon Ma bai Halle boturanba dan tana hango kwantaccen gashin kirjinsa, jin shuru yasashi dagowa, karar idanunshi suka sauka akanta, sanye take da kayan daya ganta da gamma dog uwar Riga saidai yanxu ta saka hula ta nade gashin nata saidai yana iya hango edges din sumar gaban gashinta, kauda idanunshi yayi gefe ba tareda ya sake kallonta ba ya tsuke fuska tam ya zauna kan gado ya wulla mata idanunshi da take jinsu suna yawo a jikinta.

Dagowa tayi charaf idanunta suka sauka a nashi, da sauri ta janye nata, yanda ya tsura mata idanu ya sata jin tsayuwar na neman gagarar ta, dakyar ta tartaro sauran jarumtarta ta soma magana cikin sanyi “uhm, ga coffee din”

Jin Shuru yasata dago kanta saidai this time around idanunshi a lumshe suke ya nade hannayenshi a kirjinsa, ganin yana shirin dago nasa idanuwan yasata saurin sauke nata kasa 

“Nace maki Ina buqatar wani abu daga wajen Ki ne?”

Da sauri ta dago jin tambayar da yayi mata, idanunta ne ya soma taro ruwa

Bakinta na karkarwa tace “daa…man..naga zata kawo ne shine Nace ta bani na kaw…..” 

wani irin mugun kallo ya Willa mata tare da tarar nunfashinta yace 

“Bana buqatan abu daga wajenki, now get out with that trash”

Ya karashe yana nuna mata coffee dake hannunta

Hawayen ta dai basu daina ambaliya ba haka zalika bata fitanba saida ya daka mata tsawa arude Har tana harde kafafu ta fuce, tare da rufo mashi kofar, kukane sosai ya kufce mata, ta rasa wani tunani zatayi, ganin batada wani mafita yasa ta wuce kitchen, aje coffee din tayi ta sulale kasan tiles din ta fara kuka sosai mai ratsa zuciya 

Goga kuwa tana futa yayi kwanciyar sa hankali kwance.

Update!!!!!!

Yau kusan kwana biyu kenan rabonta da dashi,haka zata wuni a parlor bata saka shi a idanunta ba haka zalika idan dare yayi haka nadine zata tasheta dan barci ya kwasheta anan zauna a parlor, idan ta tambayi Nadine ko ya dawo cikin rashin sa a zata shaida mata ya wuce daki.

Tun bayan kai masa coffee datayi tya korota bata kara yunqurin shiga dakinsa ba don tsoron ma ya ninku akan wanda yake mashi a baya, goga kuwa yana sane da ita bayaga wannan Ma ayyuka sun mashi yawa don abubuwan dayazo yi sunma nunku akan wanda ya tarar.

Yau weekend bai samu fita ko ina ba saidai yana  kunshe daki kamar koda yaushe yana aiki, baici wani breakfast ba Sai coffee daya buqata nadine ta kawo mashi wanda yasha kusan sau uku, dayake shiba ma’abocin cin abunci bane sosai, farar jallabiya ne a jikinshi sai zabga kamshi yake yi, zura bedroom slippers dinshi yayi wanda suka fidda da asalinsa kyawun yatsunshi kamar na mace wanda suna nan kamar na jariri babu tabo ko daya, kallon agogon hannunshi yayi ganin karfe 3 na yamma ya sashi tunkarar kofar dakin nasa ya bude ya fito saida ya tsaya a sitting room din daman kafin  cikin kamewa ya nufi hanyar stairs, yana sauka stairs din farko ya dan tsaya tare da kallon dakin nata, wani tunani ne yazo mashi harya tunkari kofar dakin nata sai kuma ya juya ya nufi stair din kasa, amra wadda ta kurama tv idanu hankalinta sam baya jikinta, idanunta sundan fada, doguwan rigar shan iska ne ajikinta as’ual kanta yar hula ce data danyi baya kadan don kusan Rabin sumar kanta a bayyane yake, bataji motsin saukowan shiba don hankalinta yayi nisa sosai saidai kamshin turarensq dake shiga hancinta kadan wanda take alakanta shi da kama gidan da yayi gaba daya, zura hannayenshi yayi cikin aljihun jallabiyan nashi, saida ya mata kallo daya tsaf kafun ya kauda kanshi gefe ya fara takowa zuwa sitting room din, saida yazo daf da ita don tana zaune a kan 3 seater dake facing tv station, nan take taji turarenshi ya shiga cikin hancinta sosai, runtse idanunta tayi kafin cikin hanzari ta soma bin parlorn da kallo, karaf idanunta suka sauka cikin nashi, mikewa tayi zumbur da sauri tare da sauke kanta kasa, tunkarar inda yake  yayi cikin sauri tayi baya, zama yayi inda ta tashi tare da daura kafanshi daya kan daya, maida idanunshi yayi zuwa ga tv , bai cemata kala ba haka zalika itama batace komi ba  Sai wasa da yatsunta datake, kamar wadda aka tsungula tayi saurin dago idanunta ta mashi kallo daya ganin fuskan nan babu yabi ba fallasa tayi sauri kauda nata gefe tace “barka da fitowa”

Shuru babu amsa daman batayi tsammanin amsawan nashi ba, bata ida tunanin ba yace “call that lady”

Cikin sauri Harda dan gudunta ta nufi hanyar kitchen, bayanta yabi da kallo yanda mazaunanta suke muskutawa dalilin gudu da take, saida ta daukema ganinshi kafin ya maida idanunshi kan tv, fitowa tayi Nadine biye da ita a baya, chan gefe ta samu ta tsaya kafin nadine ta soma magana “gani sir”

Bai kallesu ba su duka idanunshi kan tv yace “what do you cook for lunch”

“Sir mac and cheese ne sai pepper soup”

Shuru ya danyi kafin yace “prepare tuwo against dinner”

Shiru Nadine tayi hankali tashe tace “I’m sorry sir but ban iya tuwo ba,”

Mugun kallo ya watsa mata kafin yace “daga wani company aka kawoki”

“Cameroon sir”

Shuru ya danyi na Yan mintuna bai sake cewa komi ba, amra dake tsaye kamar munafuka ta dan dago ta kalleshi da gefen ido kafin ya sauke wata dog uwar ijiyar zuciya tace “in ba damuwa na iya Zan dafa”

Karo na biyu daya dago kenan ya kare mata kallo harna da bakin nata daya karshe zancen, jin yanda yayi shuru yasata dagowa idanunta suka shige cikin nashi, da sauri ta sauke nata kasa, tabe bakinsa yayi ya fuzge ganin Nadine na wajen ya sashi hana kanshi abunda yake shirin fada yace “okay”

Da sauri ta dago fuskanta dauke da dan murmushi tayi saurin cewa “miyan me kake so”

Bai kalleta ba yace “anything”

Cikin jin dadi ta kalli Nadine tace “muje”

Wucewa kitchen sukayi kitchen yana jin yanda she’s so excited, maida kanshi yayi baya yayi relaxing tare da shafa suman kanshi data taru kafin ya dan runtse idanunshi shi kadai yasan me yake ji.

A kitchen kuwa da idanu Nadine ta dunga bin madam dinta don wannan ne first time dataganta tana fara’a,nan take Nadine ta shiga taya ta fito da abubuwan da zata buqata don saida yasa aka zuba duk wani kayan abunci da za a buqata a gidan, cikin kwarewa amra ta dora ruwan tuwon shinkafa yanda zai ishesu duka, kadan kadan ta soma hira da nadine wanda tayi mamakin cewa ita ba yar Nigeria bace, aiki ne ke kawo su nigeria, cikin nishadi suka sauke tuwon inda amra ke nuna mata yanda ake mulmula tuwon a cikin leda, abun saiya kayatar da nadine don batasan tuwo ba, suna gamawa nadine ta dauko hadden warmer masu shegen kyau ta aje, nan ma amra ce ta jera tuwon a cikin warmer din, suna gamawa Nadine tace “ma, me zakiyi da wannan duka” ta fada tana nuna alayyahun da amra ta zaro daga cikin fridge da nama da bushahhen kifi Harda ganda.

Yanda tayi maganar yabama amra dariya tace “zanyi amfani dasu ne duka, abunda zanyi we call it miya, dashi ake cin tuwo”

Jinjina kai nadine tayi kafin tace “I want to learn from you ma”

Dariya kawai amra tayi ta bata jajjage tayi mata a cikin chopper, tana gamawa ta wanke mata su naman da Sauran, cikin qanqanin lokaci qanshin abuncin ya bade gidan, tun daga kitchen Har wajen gate, general dake zaune tunda ya jiyo kamshin ya soma hadiye miyau, sun dauka kusan awa biyu kafin su Kamala komai,su amra da kaudi harda su coconut drink ganin Akwai abubuwan hadawa available a cikin fridge, fita Nadine tayi don sanar dashi an kammala komai lokacin an soma kiraye Kirayen sallar magrib,bata sameshi a sitting room dinba don haka ta koma kitchen.

Futowa amra tayi daga kitchen din ganin baya sitting room din yasa ta wuce sama bata kaiga shiga daki ba ya sauko kasan kallo daya ya mata ya dauke kanshi tare da wucewa, tura kofar dakin ta tayi ta shige tare da jinjina kallon da ya mata kai Wayar fassara, dauro alwala tayi kafin ta tada kabbarar sallah, tana idarwa tayi soma addua, tana nan zaune aka kira sallan isha’I,mikewa tayi ta gabatar da sallah isha’I tana idarwa ta ninke sallayan ta soma tube kayan jikinta, ta wuce bathroom wanka tayi da shower baths dinta masu kamshi lavender kafin ta Nado  jikin ta da towel ta fito, zama tayi gaban dresser ta shafo kanta daya nannade sosai alamun yana buqatar gyara, karema kanta kallo tayi tsaf daga fuskanta zuwa kirjinta, fuskanta yayi fayau saidai ya soma dawowa daidai dalilin kukan nata data rage saidai damuwa da baza a rasa ba don tana son ta samu suyi magana dashi don ta nemi gafarar shi akan abubuwan da suke faruwa wanda a ganinta Duk ta dalilinta ne hakan ta faru,bayan wannan Ma tana son ta komawa Yan uwan ta don yanxu auren kuma babu amfani,zamanta dashi Ma babu amfani, saidai tana jin kunya da tsoron tunkararshi don tana ganin hakan kamar tayi mashi butulci ne saidai dubaga ga auren yarjejeniya ne tsakaninsu abu daya ne zai faru wanda saiza ta daina jin zafin kasancewa wanda ta lalata mashi aikinshi shine jin nashi dalilin aure ta da kuma buqatarshi ta auren da ya zama yarjejeniya tsakaninsu bayan wannan Ma tayi Ma kanta alqawari kome ya buqata zatayi mashi indai bai saba addini ba don cika alqawarin yarjejeniyar.

Manta na Orel ta janyo ta shafe jikinta dashi kafin ta bude closet din dakin don ta jera Yan Kayyyakinta a ciki, kayan barci ta janyo riga da wando masu sulbi, rigar ta dan kamata daga sama wandon ka ya zauna dam a jikinta daman ga yanayin jikin nata irin na manyan mata ko ina yaji kaya, Dan turare ta feshe jikinta dashi kafin ta janyo hularta, bata kaiga gama saka hular ba Nadine tayi knocking, ta sako kai, ganinta a dan burkice yasa amra kallonta da kyau 

“Ma sir yace kije yanxu”

Tana kaiwa nan yasa kai ta fuce, amra kuwa ganin yanda Nadine ta shigo yasa ta saurin bin bayan nadine hular Ma bata ida sakawa ba ta bude kofar da sauri ta fuce zuwa Kasa, ganin babu kowa a dining din Sai karar ruwa dake sauka a kitchen yasa ta bin hanyar kitchen din, ganin Nadine a tsaye tana wanke wanke yasata cewa “yana Ina ne”

“Laa Ma baki tafi ba, yana sitting room nashi na sama yana jira”

Juyawa amra tayi da dan sassarfa ta wuce hanyar sama, koda takai kofar dazai kaika ga sitting room din saman saida yadan tsaya ta saita natsuwarta gaba daya ta manta a wani yanayi take ganin yanda Nadine ta rufe zuwa kiranta, knocking  ta fara yi, jin shuru yasa ta sakeyin wani knocking din, ganin kamar babu kowa a sitting room din yasata bude kofar Bakinta  dauka da sallama, babu kowa wayan, takowa tayi Har wajen dining ganin baya nan yasa ta wasi wasi ko ta karasa bedroom din tayi mashi knocking, ganin tsayuwanta ma anan bata lokaci ne wanda baya son hakan yasa ta karasawa gaban kofar kanta a Kasa, bata kaiga knocking dinba ya bude kofar, kamshinsa ne ya daki hancinta wanda shima kusan hakan ne don kamshin turarenta mai sanyi ne ya bugi nashi hancin, idanu suka hada nan take tayi  Kasa da nata wanda ya bashi damar kare mata kallo sosai tun daga sama Har kasa, sanyin baya tayi kadan ta koma gefe don bashi hanyar wucewa, fuskewa yayi ya soma takawa zuwa dining ba tare da yace mata qala ba saidai zuciyar wani irin mugun bugu take yi ganinta da yayi, zama yayi akan kujeran dining din, jin shuru ba ya sashi yin Gyaran murya yace “na kiraki ne don ki tsaya”

Cikin karfin hali ta tattara natsuwarta ta karaso gabanshi ta tsaya kyam, dagowa yayi ya zuba mata idanuwanshi nan da Har wani ruwa ne ke kwance a cikin kwayar idanun, Dan dagowa tayi ganin inda yake kallo yasata saurin kallon kanta, take taji wata irin kunyarsh dukda ba wannnan ne karon farko ba da ya ganta da kayan barci,

Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa “ni zanyi serving kaina ne, I hate it when my time is wasted”

Da sauri ta dunfaroshi har yana iya jin motsin jikinta ta soma bude warmers don, janyo plate tayi daga cikin dinner set din dake jere tayi ta soma zuba mashi tuwon, ganin tana shirin Kara dauko wani tuwon zata zuba yasashi cewa “ke zaki cinye shi kenan”

Jin hakan ta gane cewa ya mashi yawa, batayi wata wata ba ta maida shi ta bude warmer miyan, koda kanshi ya bugeshi saida ya lumshe idanu kafin ya budesu kan plate don ta da matso dashi kusa dashi, ararrabe ta bude baki tace “bis…millah..” bai dago ba ya kurama abuncin idanu, daukan glass cup tayi ta zuba mashi coconut drink din dayasha madara tayi ta aje a gefenshi cikin natsuwa, saida ya karemata kallo tass yanda take komi cikin kwarewa da natsuwa,

Juyawa tayi zata wuce yace “come back”

Dawowa tayi tadan rabe gefe ta tsaya, dagowa yayi ya runtse idanu ya sake cewa “bana son yawan magana,”

Da idanu ya mata nuni da kujeran dining, janyo wa tayi ta zaune chan nesa dashi, bismillah ya soma yi kafin ya dauka spoon ya saka a cikin plate din ya Debo tuwon hade da miyar allayhun da tasha kaji da kifi da mama Harda ganda, koda yakai bakinshi saida ya runtse idanunshi sosai, harta tauna, dan dagowa tayi don ganin expression dinshi, fuskan nan dai babu mai iya karantar ta don a hade take, tana ganin haka ta sauke idanunta kasa feeling so sad, bangaren general kuwa inba Ammah ba bai taba cin abincin da ya tafi da imani shi ba kamar wannan, yarinya karama with bless hand ya fada a ranshi, saida ya kusa loma biyar ya tsagaita chan kasan maqoshi yace “great cook “

Dan dagowa tayi din bataji me yace ba tace “uhm”

Mugun kallo ya watsa mata ba tare da yace komi ba ya janyo coconut juice din yakai bakinshi, shima saida ya lumshe idanunshi don ya mashi dadi, saidai bai wani sha sosai ba ya goge bakinshi ta tissue ya miqe tareda wuce hanyar dakinsa bai kaiga rufe dakinba yace “zo nan”

Gabanta ne ya bada daranmm dukda bata kawo komai ranta ba, Mikewa  tayi tabi bayanshi harya shige dakin kafin tayi sallama ya shiga itama tsaye ta ganshi yana shirin cire jallabiyan saurin kauda kanta tayi gefe tare da damke hannayenta biyu

“Fix the beddings”

Yana fadin haka ya wuce toilet don harya zare jallabiyan ya aje kan gado ya rage daga shi Sai boxers dinshi tana ganin shigewarsa kuwa tayi saurin takowa gaban gadon ta soma gyara mashi, bata wani dade ba ta gama Gyaran gadon nashi, tare da ninke jallabiyanshi bin dakin tayi da kallo don neman closet dinshi Sai a lokacin ta karema dakin kallo yafi nata girma da haduwa sosai kana gani kasan dakin master bedroom ne, idanunta ne suka sauka kan frame din dake gefen gadon, dauka tayi ta kura masu idanu sir general ne yayi kyau lokacin baikai haka ba Sai wani babban mutun a gefenshi wanda tana kyautata zaton babanshi ne yanda suke rungume da juna suna dariya sai abin ya sata yin murmushi harta sha’afa, general da kusan mintuna biyu da fitowanshi kugunshi nade da towel da karami don bai kaiga qwiwanshi ba Dayan kuma na kan sumarshi yana goge wa ya tsaya tare da rike kugu da hannu daya ya zuba mata idanu, yanda yake murmushi ya sanya dimple dinta da bai taba gani ba ya fito sosai, takowa ya soma yi ya tsaya a bayanta kamar Ana fusganshi, kamshinta na shiga hancinsa don yayi dan da ita sosai, amra kuwa jin sahun mutun a bayanta ya sata firgita frame din yayi kasa saurin saqala hannayenshi yayi wajen kugunta ya zamana tana tsakiyanshi ya taro frame din tare da dan dukawa kasa kadan, saurin juya kanta tayi jin hannunshi dake da danshi wajen kugunta, runtse idanu tayi sosai ta budesu akanshi shima ita ya zubama idanu sun dauka kusan minti daya a wannan yanayin ya kasa cire hannunshi daga kugunta don da hannu biyu ya taro frame din, amra kuwa yanayin daga shiga mata misaltuwa ne, nan take wani baqon yanayi yazo mata jinshi dab da bayanta, tana son kufce mashi saidai babu hanyar kubucewa, shiko oga ya Kasa yin komi ne sbd towel dinshi da ya soma warwarewa dalilin dukowan da yayi, yana son cire hannayenshi daga kugunta saidai yana tsoron yin kwakwaran motsi Kar ayi abun kunga gaban yarinya,wata da bata ce ta fadi mashi ya rankwafo kanshi daidai wuyanta tare da saqalo kanshi wajen ya daidai kunenta ya sauke nunfashi wanda ya sata runtse idanu tare da damke hannayenta sosai ta rufe ido, sauke mata wani nunfashin nashi yayi this time around harda Jan nunfashin yayi alamun yana don yin magana saidai wannan abu ya kawo mata baqon yanayi, ahankali kamar mai rada yace “close your eyes”

Idanun data rufe ta gwalo su waje,ganin kamar bata cikin hayyacinta ya sashi dan fada da karfi “I said close your eyes”

Firgigi ta dawo hayyacinta ta rufe idanun gam don a tsorace take sosai

Yana ganin haka ya dauke kanshi a hankali tare da rike frame din da hannu daya ya riko towel din da Dayan hannun, sauke ijjiyar zuciya yayi don yanda yayi hasashe kuwa towel din na gab da sauka kugunshi ja yayi da baya ya karema bayanta kallo sosai, how curvy she’s is giving him hard hard, sanin yanayinshi ya sashi dauke idanunshi daga kanta gaba daya yace “get out”

Juyowa tayi ahankali idanunta sunyi dan jaaa zata bude baki tayi magana ya tari nunfashinta “out!”

Wani iri taji, hawaye na shirin zubo mata mara dalili don a tunaninta ta dauka fasa mashi frame data kusa yi ne ya sashi haka, hanyar fucewa ta bi saida ta bude kofar har zata futa ta dan daga murya murya tace “dan allah kayi hakuri yaya”

Wani kallo ya wurga mata daya sakata saurin janyo mashi kofar ta wuce daki Harda dan hawayenta.

Tana futa kuwa ya lumshe idanunshi gam yana jin yanda dumin jikinta ke dukan nashi lokacin daya tsaya a bayanta.

Niko Nace anya general bai kamu ba kuwa, lolsss

Tunda ta futa ya kwanta kan gadon tare da janyo bargonshi dake kamshinsa kayanda bai saka ba kenan sbd jin kamar feelings na taso mashi kadan kadan tunanin maganr doctor ne ke yawo a qwaqwalwarshi.

Tana komawa daki ta kwanta tana tunin rayuwarta da lokacin da ya shigo cikin rayuwarta, yunwa ke nuqurqusar ta saidai ta Kasa Tashi don wata kasala ce tazo mata wanda ta Kasa ganin dalilin zuwanta.

 Tana nan cikin tunanin data fada barci ya kwasheta mai dadin gaske.

Karfe 2 na dare taji wani irin qululun ciwo ya dunfarota a mararta, zumbur ta miqe zaune, chaf ta manta da period dinta dake hanyar zuwa, mikew tayi cikin sassarfa ta bude Jakarta ta fara buncikar maganin ta saidai duban duniya tayi bata ganshi ba hankali tashe ta tuna ta barshi achan dubai cikin dayar jakarta ta office, rasa abinci tayi don kadan kadan ya soma zuwan mata, samun waje tayi ta zauna a Kasa tare na hade kafafunta don daman haka take yi don samu sauki, wasa wasa Har karfe hudu tana nan tun tana iya miqewa harta galabaita ta natsu waje daya anan kasa, kuka kuwa wiwi kamar an mata mutuwa, tana nan zaune har aka kira sallah lokacin ta soma jin zubowarshi, toilet ta wuce da sassarfa nanma saida ta dauka kusan Rabin awa tana abu daya harta samu ta saka pant da pad, wandon Ma Kasa mai dashi tayi Sai towel ta nada a kugunta , dakyar ta rarrafo ta futo dakin ta ta zauna bakin gado sai hawaye wiwi, fuskanta yayi jaaa alamun jin jiki sosai, ahankali ahankali nunfashinta ya soma neman daukewa kamar mai asma, mikewa tayi don zuwa toilet ta kwata Ma kanta ruwa don intaji irin haka Toh da suka ne kawai zatayi baya iya tsaida kafafunta ba taji sun Kasa daukanta,wata Kara ta kwala da karfi  kafin ta fadi Kasa warr, Amar dake shirin wucewa dakin dake kusa da nata sanye cikin kayan gyming ya jiyo karar tata, kallon dakin nata yayi don tantance ko daga nan ne karar ta fito kamar bazai takaba ya daki handle din dakin da yake shirin shiga ya bude natan, duhu ya soma gani a dakin saidai dan hasken dake lekowa daga window, laluben switch yayi kafin ya Danna, ganinta a yashe kasa ya sashi saurin takowa gabanta yama rasa mai zaiyi, tsugunnawa yayi gabanta yace “ke ke,”

Jin alamun bata motsi yaji gabanshi ya fadi ya sake tabo ta yace “ke ayshaaaa”

Shi kanshi yanda ya furta sunan nata Sai ya sake mashi kamar baqon suna, kamar zai zauce ya sake taba ta, kokarin cicibarta somayi towel dinta ya sake kasa, baima san towel din yayi hanyarshi ba ya kwantar da ita kan gado a natse ya wuce bathroom dinta, ruwa ya deba a cikin bowl yazo gabanta ya soma shafa mata cikin kulawa kamar baya so, doguwan nunfashi taja tare da bude idanunta saidai yake ciki ta ya soma murdawa ta kwala wata karar ta suke, ganin haka ya sashi saurin taba aljihun gajeran wandonshi ya janyo wayanshi ya soma dialing number da ya fara cin karo dashi 

“Morning sir,”

Bai tsaya amsawa ba yace “I need doctors now, it’s emergency”

Hankali tashe asad yace “doctor kuma waye bashi da lpy ko Ammah ne tunda daga ji dai nasan kai lafiyanka kalau”

Cikin dan fada yace “just get me a f**cking doctor now”

“Okay”

Yayi saurin katse wayan.

Ruwan ya sake shafa mata saidai wannan Karin doguwar suma tayi don babu yanda baiyi ba don ya dawo da ita hayyacinta.

Yana nan zaune yaji karar bell da sauri ya fito daga dakin ya tsaya bakin wajen stairs don Ana iya hango wanda ke qasa,bai tsaya sauraran Nadine dake shirin mashi bayani ba yace “let him in”

Cikin sauri ta koma ta shigo da doctor, Nadine ce ta jagoran ce shi har gaban Amar kafin ta juya.

Hannu Amar ya miqa mashi suka yi musabaha kafin ya jagoranceshi gaba, yana bude kofar bai kaiga shiga ba ya hango ya yanda ya barta don sa a lokacin shima ya Lura da yanayi ya don dazun baya cikin hayyacinshi shima, saurin juyawa yayi don doctor na gab da karasowa, daka yar dashi yayi ta hanyar ce mashi “wait a minute” ya bude kofar tare da saurin rufous ya karaso gabanta tunda ya tsaya ya kare mata kallo Har ya kusa shagala da kallon nata kamar wanda aka tsikara yayi saurin janyo duvet dinta ya rufa mata gaba daya ya rage iya fuskanta kafin yace “come in”

Shugowa doctor yayi kai tsaye ya karaso inda yake tsaye kafin ya maida idanunshi kanta. 

Da idanu Amar ya mashi nuni da ita dake kwance hannayenshi nade a kirjinshi dake sanye  da rigar under armor na gym, babbake wajen yayi wanda yasa doctor din zuba mashi idanu shima shi yake kallo fuskannan babu yabi ba fallasa, takowa doc din yyi kusa dashi sosai kafin yadan matsa mashi gefe

 “meke damunta”

“Idan nasan abunda ke damunta Zan kiraka ne”

Ya fada Adan kausashe don yaga lokacin da doc din ya zubama fuskanta idanu wanda hakan baiyi mashi ba sam 

Dan murmushi doc din yayi ganin Duk ji da kanshi da kudi da yake dashi ya hadu da wanda ya fishi 

“Na tambaya ne don na samu damar duba ta yanda ya kamata”

Maida idanunshi doc din yayi kanta ya kai hannunshi wajen fuskanta da duvet yadan rufe sosai sbd yanda ya janyo bargon, Amar na ganin haka ya runtse ido a dan fada yace “don’t…..”

“Just check her”

“I can’t check her just by looking at her face, I have to touch her to feel her pulse tunda naga kamar bata nunfashi”

Tamke fuska ya sake kafin yadan kauda kanshi gefe ya tsaya akansu.

Dan sauke duvet din doc din yayi kafin ya kare mata kallo sosai, shagala yayi da kallonta saida Amar yayi Gyaran murya kafin ya soma taba wuya ta don jin pulse dinta, jin pulse din is so weak yasa shi saurin bude dan box dinshi ya fara mata taimakon gaggawa saida ya kammala komai ya saka mata ruwan nunfashinta ya sauka da karfi alamun ta farfado Sai bacci kuma, dagowa doc din yayi yace “she’s stable now, yanda naga tana nuqurqusar na tabbatar da monthly cramps ne da mata keyi, Banda awa biyu zata ji sauki”

Tattara kayan aikinshi yayi gyara tsayuwar glass dinshi kafin yace “taba da aure ne”

Dan dago idanu Amar yayi ya kalle shi yace “no why”

“Daman yawanci yafi bama yanmata wahala musamman waenda basu taba Sadiya da namiji ba, Akwai magungunan da zata sha harta gama, Zan dawo anjima don na duba ta”

Wani irin kallo mai wuya fasaara Amar ya mashi kafin ya kauda kai gefe yace “thanks, asad will handle your payment”

Cije lebe gayen yayi kafin ya juya ya fuce.

Yana futa ya daga wayanshi ya Danna kira  Ana dagawa cikin dan fada yace “are you sure wannan certified doc ne, send someone I don’t like perverts”

Shuru asad yayi don ya Kasa gane me Amar din ke nufi da inda ya dosa, don wannan Loki tan babban Lokita ne shike kula da family dinshi saidai baya iya jayyay dashi yace “okay sir”

Dakin ya koma ya zauna gefenta ganin lokaci guda ta sauya sosai, kauda kanshi yayi gefe ya dauka kusan awa a zaune kafin ya miqe ya turo Nadine don ta tsaya da ita.

Tunda ya koma dakinshi ya Kasa natsuwa saida ya shigo dakin yafi sau uku cikin awa guda, ta dade bata fara ba don saida ta kai kusan awa hudu don allurar nada karfi sosai, wajen asr ta farka, babu kowa dakin lumshe idanunta tayi ta zauna dakyar,tunawa da yanayin da take ciki yasata dan mikewa don tasan yanda take rushing tsoronta karya bata beddings din, tana mikewa kuwa jiri ya debeta alokacin shi kuma ya sako kai cikin dakin, da Santala santalan cinyoyinta ya soma cin karo bai kaiga sama ba ya runtse idanunshi, itakuwa tama manta da jiran daya debeta tayi saurin janyo towel ta daure kugunta, tana taku daya kuwa ta kwala Kara don kiris ya rage ta zube, da taku biyu ya cimmata kafin Adan fada ce yace “get your head straight tunda kinga bazaki iyaba Ay saiki zauna”

Shuru ta danyi don azabar da take cinta yafi surutanshi zafi, zauna da ita yayi tare da ficewa ya turo nadine, tun daga Safiya zuwa yamma Nadine ke mamakinshi, ashe yanada zuciyar tausayi.

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.