Best Hausa Novels

Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx

Chapter 34 of 52

Chapter 138

UPDATE

Unedited page

Ba tareda ya saurare ta ba ya janyo table din da chef din ya ajiye abuncin kafin ya fuce yace ‘’bana son gardama eat’’

Kauda kanta gefe tayi jiki amace tace ‘’toilet nake son shiga’’

Mikewa yayi ya sungumeta gaba dayanta, arazane ta juyo ta kalleshi, gaba daya bata da wani kuzari ajikinta don hka ta lafe a jikinshi har ya shige da ita bathroom din, yana shiga ya sauketa akan wc ya fuce daga bathroom,

Bayan fitarshi ta soma tube kayan jikinta tayi wanka da ruwan zafi sosai kozaji dadin jikin nata, tana gamawa ta dauro alwala  jiki amace dukda tana jin jiri sosai.

Tana gamawa ta maida kayan asibitin ta fito anaste,lokacin dta fito yana zaune kan kujeran dake gefen gadon asibiti, ya dafe kanshi dake sara mashi, baiji alamun fitowanta ba saida ta rufo kofar bathroom din, dago kanshi yayi ganinta tsaye tana shirin takowa harta karaso baking ado kanta akasa, tana zuwa bakin gadon ta janyo jallabiyanta datazo asibitin da ita ajikinta, kokarin komawa bathroom tayi ganin haka yasa yayi saurin ‘’let me excuse you’’

Yana kaiwa nan ya juya ya fuce, da mamaki ta bishi da idanu kamar bashi ba,gaba daya yayi laushi sosai, tausayinshi ta soma ji lokacin data maida idanunta kan abuncin day ace taci, yanxu haka shima baici ba ta fada aranta,jiki a mace ta sauya kayan jikinta zuwa abayar nata kafin ta zauna a kan carpet ta tada sallah.

Tan idarwa ta koma kan gado ta lafe jikin gadon ko kallon abuncin batayi ba don bakinta ma daci yake mata sosai.

 

Wajen karfe daya tana nan zaune kafin ta miqe ta gyara mayafin abayarta ta fuce daga dakin, direct emergency ward ta wuce zuwa inda aka kwantar da ammah, anatse take tafiya kamar zata fadi harta karaso wajen, batama lura dashi ba, yana zaune daga gefen kujerun reception din ya dafe kanshi dake sara mashi sosai,

Gaban dakin da ammah ke ciki ta tsaya, ta jikin glass din kofar dankin take hangota hancinta maqale da oxygen dake taimaka mata waje fidda nunfashi, ba karamin tausayinta taji ba, ta kasa gane dalilin da zaisa lantana ta cutar da wannan baiwar allah, dan zaman datayi da ammah ta karanci halayyanta, macece mai tausayi da kaunar kowa, bata da ha’inci kwata kwata ga son mutane ga hakuri uwa uba ga kyauta, batada matsala kwatakwata kowa nata ne, idan kowa bai shaide ammah ba toh tabbas ita da kannenta zasuyi mata sheda mai kyau don tayi masu komai a duniya, ammah uwace ta gari a gurin kowa.

Fashewa amra tayi da matsanancin kuka sosai tana wannan tunanin aranta harya dago kanshi don kwata kwata baijin motsin ta ba data karaso wajen ba sai yanxu, samun kanshi yayi da kallonta ba tare da tasan yana yi bama, kuka sosai takeyi kamar ranta tana tausayin ammah sosai, ayau koda ance ta bata zuciyarta zata iya, ba karamin tashin hankali ta shiga ba lokacin data ga lantana tana saa mata abu acikin drink, don bashine frist time da hakan ya faru ba, dukda bata kawo komai aranta daga farko ba saidai dole yanda lanata tayi acting kamar mara gaskia lokacin data shiga kitchen dinnan ya tabbatar matar mata da something is fishy, tana nan tsaye wani irin karar na’ura ta soma tashi daga dakin, ammah dake kwace ta soma jijiga, zaro idanu amra tayi kan kace me saiga nurses gaba daya sun taho hanyar dakin harda likitoci guda biyu, hankali atashe amar ya miqe yazo gaban dakin inda amra ke tsaye, nurses na ganinsu bakin kofar suka ce ‘’sir ku bamu waje,’’

Hankali atashe amar yace ‘’waaa…waaas…whats going on? Meke faruwa, you guys should fucking explain whats going on’’

Ba tareda sun bashi amsa ba suka wuce cikin dakin gaba dayansu harda doctors din, nurse day ace kawai ta tsaya bakin kofar tana kokarin yi masu explaining,’’sir dan allah ku kwantar da hankalinku, zamuyi iya kokarinmu akanta please’’

Tana kaiwa nan ta koma cikin dakin suka dukufa akan ammah da likitoci, amra dai kasa tsayuwa tayi saida ta dafe bango, amar kuwa tunda ya kafama kofar idanu yana hango yanda suke fidda wasu na’urori agaban ammah hankalinshi ya tashi, yanda likitocin ke zarya akan ammah suna kokari cetota, babu abunda amar ke fadi sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sun dauka kusan minti ashirin a gaban ammah suna kokarin daidaita bugun ziciyarta saidai kasha bun yaci tura, kafa masu idanu amar yayi ganin sun tsaya gaba dayansu, nan take gabanshi ya fadi dammm, bude kofar doctor yayi jiki a mace kanshi a kasa ya karaso inda amar ke tsaye yace ‘’im so sor….’’

Janyo rigarshi amar yayi yace ‘’what do you mean by that?, why are you sorry’’

‘’yallabai sai hakuri, zuciyanta ya tsaya chak bata nunfashi babu abunda zamu iyayi  im sor….’ Doctor bai gama fadaba amar ya katseshi ya soma cewa

‘’innalillahi wa inna ilaihi rajiun, innalillahi wa inna ilahi rajiun’’, nan take yayi baya yuuu zai fadi, cikin sauri doctor ya taroshi, mikewa amra tayi aguje ta karaso inda amar ke yashe a kasa babu numfashi yayi passing out, saurin kamo hannunshi tayi ‘’yaya yaya dan allah ka tashi na shiga uku’’

Gaba daya ta gama susucewa kamar wadda tayi karamin hauka babu abunda take cewa sai ‘’yaya dan allah ka tashi, ammah bata mutu ba bazata mutu yanxu ba insha allah’’ 

 

doctor ne ya kira nurses sukada janyo gado aka saka amar akai don yayi passing out gaba daya, amra  dake tsaye itama kunnuwanta zun gama jiyo mata abunda doctor fada ga amar a kwance shima kamar babu rai hankalinta ya gama tashi sosai har wani dishi dishi take gani, haka aka gangara da gadon da aka kwantar da amar har zuwa wani daki amra na biye dasu duk ta gama susucewa, har aka kwantar dashi aka mashi allura don ya samu shock ne, amra dai babu abunda take sai maimaita innalillahi a zuciyanta, shikenan ammah ta mutu, innalillahi wa inna ialihi rajiun, kallon amar tayi kawai saita fashe da wani matsanan cin kuka, haka ta duga sintirya agaban gadonshi tana hawaye ga jiri na dibanta, hankalinta y agama tashi don bata san mezai faru dashi ba shima,gabanshi ta karaso ta tsaya tana kuka ta rike hannunshi da kyau ‘’yaya…’’ tana fadin sunan shi ta sake fashewa da wani matsanancin kukan sosai, ta dauka tsawan minti talatin a kusa dashi har ya soma motsa hannunshi, da sauri ta dago ta kalleshi lokacin harya bude idanunshi da sukayi jaa sosai, zumbur ya miqe ya dafe kirjinshi dake bugu fat fat fat, amra na ganin haka ta soma toshe bakinta ta kalleshi, shi baima kalleta bay a soma juya kanshi yana cewa ‘’no nooo nooo innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan wani irin mafarki ne haka’’ ya fada yana confusing kanshi, shuru amra tayi tana kallonshi ta kasa cewa komai har nurse ta shigo  don ta duba koya tashi don alluran da akayi mashi relaxing mind takeyi idan mutun ya samu shock, after 30mins kuma zai farka, don haka tana shigowa ta kaarso gabanshi zata duba yanayin bugun zuciyarshi tana karasowa ya daka mata uwar tsawa ‘’don’t fucking touch me, get outtttttt!!!’’ yanda ya fada saida ya razanar da nurse din harda amra, aguje nurse din ta fuce don idanunshi sunyi jaa sosai jijiyoyin wuyanshi duk sun mike, amra dai bata motsa ba dukda ta tsorata sosai baya ji baya gani haka ya sauko da kafafunshi kasan gadon yana kokarin fucewa daga dakin ‘’karya kuke wallahi, ammah na tana raye’’

yana miqewa ya fara tangal tangal zai fadi, da sauri amra ta taroshi, nauyinshi ne ya rinjayeta nan take suka fadi gaba dayansu a kasa, da sauri yafusge jikin shi ya juyo da jajayen idanunshi ya kalleta, kafin ya yunkura zai sake tashi, bai kaiga daga kafarba ya sake faduwa kasa,yana ganin haka ya dafe kanshi kawai, amra na kuka matso kusa dashi da kyar ta karaso hannunta na rawa ta fara kokarin dafashi ya daka mata tsawa ‘’leave me alone, ki fitaaaaa’’

muryanta na rawa ta dafa ‘’ya…ya’’

‘’ki futa nace, bana son ganinki’’ ya fada yana sunkuyar da kanshi, idanunshi sunyi jaaa sun tara ruwa, kwata kwata hawaye suqi futa daga idanunshi, abunda yakeji kadai ya fi kuka ciwo, yau ta kasance rana mafi baqanta a cikin rayuwarshi, har lokacin ya kasa believing abunda kunenshi suka jiyo mashi, yana nan zaune ya dunqule hannunshi ya fara bugun tiles din dakin,amra na ganin haka tayi baya tana hawaye ta fara girgiza kanta ta toshe bakinta da hannunta tana, gaba daya ya sauya kamar bashi ba, babu abunda ke shimfide afuskanshi sai pain,he’s in so much pain, bugun hannunshi yake akan tiles din yana ‘’noo noo nooo ammah noooo’’

Yanda yake bugun nan saida tiles din ya fashe, hannunshi ya soma fidda jini, arazane amra ta karaso gabanshi jikinta na bari fara kokari rike hannunshi nashi, kasa hanashi tayi don kamar ta rike rock har jini ya fara Malala akasan dakin, tana kuka haka ta miqe ta rungumoshi gaba daya zuwa jikinshi ta kankameshi, ‘’yaya dan allah ka bari, zaka jima kanka ciwo’’

Baya jinta ma kwata kwata don y adage sai bugun hannunshi yake yana ‘’nooooo ammah na nooooo’’

Rukoshi tayi da kyau ta soma karanto mashi addua a kunenshi, tana jin yanda kirjinshi ke bugu kamar zuciyarshi zata futo, har razana saida tayi saidai hakan baisa ta sake shi ba saima dagewa datayi tana mashi addua a kunneshi,ta dauka kusan minti goma tana yi har ya daina bugun hannunshi nashi ya fara sauke ajiyar zuciya, ‘’shikenan, ammah kin tafi abu ya tafi,kun barni ni kadai, innalillahi wa inna ilaihi rajiun,’’ ya fada yana kankame amra sosai, kwata kwata ya kasa fidda hawayen dake cikin idanunshi, zuciyarshi is so tough, when it comes to ammah hes so weak, itace weakness dinshi, lokaci guda yaji kamar an toshe mashi farin cikin rayuwarsa gaba daya.

Yanda yake maganganu ba karamin karya zuciyar amra yayi ba,fadin irin tausayinsa da take ji a lokacin ma bata lokaci ne, she can feel his pain don ta shiga irin yanayi daya shiga lokacin da nasu iyayen suka mutu, tana kuka shabe shabe ta soma mashi Magana anatse cikin kunnenshi ‘’yaya, youre not alone, you have us you have me, allah yana tare dakai yaya, dan allah ka sauke hawayen dake cikin idanunka ko zaka samu sauki,’’

Gaba daya ya gama sandarewa ya zama kamar dutse, zuciyarshi ta dashe gaba daya ta sauya daga haske zuwa baki.

Suna nan zaune saiga doctor ya shgo dakin……

 

Update

Unedited

Suna nan zaune saiga doctors sun shigo, dagowa amra ta ‘[taimaka mashi ya zauna bakin gadon, tunda ya zauna ya dafe kanshi bai dago ba amra na gefenshi ta rike hannunshi, har lokacin bata barkuka ba idanunta sunyi jaa sosai, kallonsu su duka doctors din sukayi kafin daya daga ciki ya soma bayani, ‘’ alhamdulillah sir, shes still alive’’

Saurin runtse idanu amar yayi kafin ya dago ya miqe tsaye don wani irin kuzari ne yazo mashi lokaci guda ya bude baki ya kasa cewa komai, babu abunda yake fada a zuciyarshi sai hamdala, baima tsaya ya saurari bayanin da suke shirin yi mashi ba ya juya ya fuce zuwa dakin da aka kwantar da ammah, suma bin bayanshi sukayi harda amra gaba daya zuwa inda aka kwantar da ammah, har lokacin ba a ganinta don tana kwance an kafa mata na’urar dake supporting heart dinta don ya dunga beating on a normal rate, tunda ya kaarso wajen bakin kofar ya kafa mata idanu, he cant believe idanunshi, ammah is alive bata mutu ba, doctors na karasow da amra ya juyo ya kallesu, ran shi adan bace yace ‘’wani irin useless facilities kuke dashi ko ince wani irin aiki kukeyi da bakwa tantance idan mutun yam utu ko be mutu ba, im going to sue duka ma’aikatan asibitin nan’’ ya karashe a fadace

Kallonshi wani magidancin doctor yayi kafin ya soma Magana cikin kamewa ‘’we’re very sorry sir, mutuwa bata zuwa sai lokacin mutun yayi, sai dai wannan zamuce it’s a miracle,ko zamuje office sai muyi maka bayanin komai’’

Tamke fuska yayi sosai, ganin girman mutumin yasa yace ‘’no need for that, I just need explanation’’

Gyara tsayuwa doctor yayi don daman shine yake Magana don dayan ya kasa cewa komai don shine ya fada masu ay ta rasu lokacin da zuciyarta da nunfashin ta ya tsaya

‘’theres a condition whereby someones heart stops and then it starts again which is called heart palpitation, idan har mutun ya wuce 10mins babu heart response after cpr anan ne muke declaring time of death, abunda ya faru da hajiya Kenan muna kiranshi da lazarus syndrome wanda hakan yasa mukayi declaring time of death don nunfashinta ya tsaya tare da zuciyarta lokaci guda’’

Ba tare da ya kallesu ba idanunshi nakan ammah yace ‘’whats her condition now? Is she stable’’

Doctor ne ya gyara tsayuwanshi ya kalli amar yace ‘’yes shes stable hajiya is very brave, she’s a fighter, alhamdullahi, shes out of coma, zata iya tashi anytime, muna rokon allah ya bata lafiya ‘’

Amra ce kawai ta amsa da ameen kafin suyi masu sallama su

Takowa amra tayi har gabanshi, farin ciki y agama lulubeta bata ma san lokacin data rungumoshi ta bay aba tana hawayen farin ciki, tunda ta frungumeshi yayi shuru ya kasa motsawa, don he needed it sosai, ta zaman mashi kamar wani source of confort, sun dade sosai a tsaye suna kallon ammah babu wanda yace qala tsakaninsu, kiran sallar asuba ne ya fargar dasu su duka, kallonta amar yayi yace ‘’kije kiyi sallah, zanje masallaci aynxu’’

Kallonshi tayi itama kafin ta sauke kanta kasa tace ‘’ah ah yaya, kaje ka fara yi, zan tsaya anan idan ka idar sainaje nayi nima’’

Saurin runtse idanunshi yayi muryanshi baya futa sosai don harta dishe yace ‘’okay, wait for me here karkije ko’ina’’

Bata kalleshi ba kanta akasa tana gyara mayafinta dake neman sulalowa kasa ‘’tohm yaya saika dawo’’

Wuceta yayi ya fita daga emergrncy ward, yana fucewa ta samu waje anan ta zauna emergency ward din wajen waiting, minti kadan zata miqe ta leka wajen ammah kafin ta koma ta zauna, idanunta har wani rurufewa suke yi tsabar kasalar data dabaibayeta,

Mikewa ta sakeyi ta leka dakin, ta dan dade a tsaye jiri na neman dibanta, ahankali ta sake takowa ta koma ta zauna tana sauke nauyayyan ijiyar zuciya, tundaga nesa amar ya hangota da yanda take tafiya, ba karamin tausayi ta bashi ba, he never thought haka take, bait aba tsammanin haka take da jajircewa da dauriya ba, kana ganinta kasan shes not okay, but she’s acting as if she is, dan tsayawa yayi yana kallonta yana nazarin abunda ya faru daga cikin daren.

Daga kafarshi yayi ya tako har inda take ya tsaya ya kalleta ganin yanda ta lafe jikin kujerar fuskanta tayi paling, bakinta duk ya bushe idanunta a lumshe.

‘’aishaaa!!’’

Bude idanunta tayi ahankali ta sauke akanshi, bakinta na karkarwa tace ‘’ya..yaa.. har ka dawo’’

‘’jekiyi sallah’’ ya fada ahankali yana zama gefen kujerar fuskanshi na nan yanda yake babu yabo ba fallasa

Mikewa ta soma yi kafarta ta rike kafin ta sulale ta zauna, kallonta yayi cikin tausayin yanayinta adan kausashe yace ‘’whats wrong?’’ ya fada yana lumshe idanu, hawaye ne ya soma zuba a fuskanta ‘’yaya im weak’’

Ta fada ahankali kamar bakinta bazai furta ba, ganin haka yasa shi mikewa ya sungumeta gaba dayanta ya daga ya wuce dakin da aka kwantar dashi, da hannu daya ya bude kofar ya shige dakin da ita, bai tsaya ko’ina ba sai bathroom ya sauketa ba tareda ya kalleta ba yace ‘’kiyi alwala, zan tsaya idan kin gama just call me’’

‘’no yaya ka koma wajen ammah, zan iya’’ amra ta fada tana wasa da yastunta

‘’bana son gardama, just do as I say’’ ya fada akausashe kamar bashi ke Magana calmly ba daxun.

Yana kaiwa nan ya futa ya rufe mata bathroom din, bin bayanshi tayi da idanu har ya rufo kofar, ta dade a zaune abubuwa da dama suna yawo a qwaqwalwarta kafin ta fara gyara jikinta jiki a mace.

 

Shima yana futa ya dan tsaya nesa da bathroom din, yana son futa yaje ya duba ammah saidai yana tunanin maybe idan ya futa kafin ya dawo zata buqace shi, juyawa kawai yayi ya fuce daga dakin zuwa emergency ward, yana zuwa yadan tsaya wajen ammah ganin da nurse a gefenta yasa ya juya zuwa dakin da yabar amra, yana shiga tana kokarin fitowa tana tangadi ruwa na diga daga fuskanta, tana hangoshi tadan daidata natsuwarta.

Takowa ya soma yi cikin kamewa ya karaso inda take fuskanshi adan murtuke yace ‘’youre so stubborn’’ yana kaiwa nan ya sungumeta gaba daya ya dorata kan gadon marasa lafiya yace ‘’zansa a aiko da abunci yanxu, idan kin idar kici abunci ki kwanta bana son gardama’’

Yana kaiwa nan ya juya yana shirin futa tayi saurin tsaidashi tace

‘’yaya kaifa? Bakaci komai ba fa’’

Dan tsayawa yayi bai juyo bay ace ‘’I’m okay’’

‘’toh yaya ka huta ni zan tsaya wajen ammah’’ amra ta fada in a concerning way

Sai alokacin ya juyo ya kalleta adan harzuke yace ‘’bana son gardama, nace maki ki kwanta ki huta kici abunci why are you being stubborn, do you want to fall sick ne?  just do as I say’’

‘’tohm yaya’’ ta fada ashagwabe tana sunkuyar da kanta kasa harya fuce daga dakin.

 

Yana fucewa ta gyara mayafin abayrta ta fuskanshi qibla ta tada sallah anan zaune saboda jirin datake ji, tana idarwa ta fara azkar tana yima ammah addua sosai har chef ya shigo da tray a hannu na abunci daga kitchen, gaisheta ya fara yi kafin ya janyo mata table din da ake ajema marasa lafiya abunci, yana aje wa ya juya ya fuce daga dakin, yana futa ta daidata zamanta ta janyo table din inda take zaune ta soma bude food cover din, chips ne da egg sauce sai custard a gefe cikin wani bowl an zuba madara sosai a ciki, kallon abuncin tayi tana tunanin shi, shi baici komai ba tun bayan breakfast din safe wanda lantana ta katse masu, batajin zata iya cin abuncinnan tunda shi ma baici ba, saidai tunawa da maganrshi yasa hakanan ta soma cin abunci ba don tana soba, baifi spoon biyar tayi ba ta ture gefe ta koma bakin gado ta lafe, har barci ya soma fusgarta dukda tana kokarin hana kanta yin baccin,

 

Tun bayan futarshi daga dakin amra ya koma wajen ammah, nan ya tadda nurses na kokarin futowa da ita daga ward din zuwa dakin marasa lafiya, cikin sauri ya kaarso inda suke, likita ne daya biyo bayansu yana ganinshi yace ‘’good morning sir’’

‘’morning’’ ya amsa mashi ataqaice

‘’sir zamuyi shifting dinta zuwa ga recovery room, alhamdullah jikinta yana recovering sosai’. Doctor ya fada yana mika mashi mashi hannu

‘’thank you so much’’ amar ya fada fuskanshi na nan yanda take saidai kana ganinshi kasan yana cikin farin cikin wannan news din.

Atare suka wuce dakin da aka kwantar da ammah tare da doctor din, sai alokacin ya samu damar zuwa har gaban ammah ya rike hannunta yana jin kaunarta da tausayinta na yawo a jinin shi, sallama doctor yayi mashi ya fuce daga dakin while nurse ta tsaya tana gyara mata drip din jinin da ake kara mata.

Nurse na futa ya zauna gefen ammah ya soma ya zuba mata idanu,addu’a ya soma yi mata akanta na neman lafiya da kariya daga duk wani sharri, ya dade sosai yana mata addua kafin ya ruko hannunta ya soma Magana kamar tana jinshi ‘’ammah na, allah ya baki lafiya ya tashi kafadunki, im so sorry for not protecting you,’’

Hannunta ya dago yayi kissing tana mai jin tausayinta da kaunarta da tausayinta, tunanin halin daya shiga daxu yayi lokacin da doctor yace mashi zuciyanta ya tsaya ta daina nunfashi, ya shiga mummunan tashin hankali sosai, tashin hankalin da bai taba tunanin zai shiga ba. Shuru ya danyi yana nazari gaba daya rayuwarshi baitaba tsintar kanshi a wannan yanayin ba sai yanxu, tsoro da fargaba da baitaba jiba arana irin ta yau yaji, ada chan baya yana ganin babu abunda zai furgitashi koya bashi tsoro anan duniya ko yayi breaking heart dinshi, saidai yau halin da ammah ta shiga yasa ya gane cewa itace weak point dinshi wanda bai sani ba, fadin irin tsoron dayaji daga wunin jiya zuwa safiyar yau ma bata lokaci ne,donma shi jarumine kuma yana da jarumta sosai.

Ya dauka kusan awa guda yana zaune wajen ammah kafin ya mike ya wuce wajen amra, ahankali yake tafiya harya shiga dakin nata, yana shiga dakin tun bai gama rufe kofar ba idanunshi ya sauka akanta, tana rakkube bakin gado tana barcin wahala, rufe kofar yayi ahankali ya karso bakin gadon ya zuba mata idanu, knocking kofar dakin akayi kafin a shugo, su salima ne da aman sai salim, gaba dayansu sunyi zuru zuru don daga wajen emergrncy ward suke inda aka kwantar da ammah, ganin bata wajen yasa hankalin su ya tashi sosai suka taho dakin, da sallama suka shugo suka zuba mashi idanu, takowa aman yayi su salima suna biye dashi, ‘’ina kwana yaya’’

Juyowa yayi ya kalli salima dake gaishesa ita da salim yace ‘’lafiya’’ ataqaice, aman ne yayi jarumtar tambayarshi jikin ammah, nan amar ya shaida masu an fiddata daga emergrncy ward an maidata recovery room, hamdala sukayi gaba dayansu, nan amra ta bude idanunta ganin su a tsaye, don barcin mai nisa ne ya dauketa bata maji shugowansu bag aba daya, ganin su chirko chirko tayi saurin mikewa tsaye ta kalli amar tace ‘’yaya jikin nata ne?’’

Maido da idanunshi yayi kanta yace ‘’no shes fine’’

Sauke nauyayyaiyar ajiyar zuciya tayi don sai alokacin ta lura dasu salima atsaye, gyara mayafinta tayi tace ‘’ina kwana yaya’’

‘’lafiya alhamdulillah ya jikin ki’’ aman ya tambayeta yana kallon gefe

‘’alhamdullah naji sauqi’’

Salim ne ya matso kusa da ita tare da salima duk idanunsu yayi jaa sosai alamun basuyi barci ba kwata kwata, salima ce ta dan rungumet tace ‘’adda ya jikin ki’’

‘’da sauqi’’

Juyawa amar yayi yace ‘’muje’’

Bin bayanshi duk sukayi zuwa dakin da aka kwantar da ammah, suna zuwa dakin amar ya bude duk suka shiga gaba daya, karasawa sukayi gaba dayan su suka tsagaye ta, kwance take kamar yanda suka barta saidai ta rame sosai jikin wuni guda, ta sauya kamar ba ammah ba saboda yanda taji jiki sosai, salima ne ta riko hannun ammah ta soma yi mata addua, tana gamawa aman ya kalli amar yace ‘’yu should go  and freshen, mu zamu zauna’’

Amra ce ta dago tace ‘’no zan zauna yaya yaje ya huta bai samu yaci komai ba kuma bai samu runtsawa ba’’

Kallonta salima tayi tace ‘’adda kema kije ki dan huta saiku dawo tare mu zamu zauna da ammah’’

‘’please call me if idan wani abun ya taso’’ amar ya fada yana fuskantar aman, girgiza mashi kai aman yayi alamun gamsuwa.

 

Kallon amar amra tayi shima ita yake kallo kafin ya kauda kanshi gefe, miqa mashi keys din mota aman yayi, karba yayi ya fuce amra tabi bayanshi, ahankali take tafiya har suka zo wajen motar, budewa yayi ya shige itama ta bude ta shiga gaba yaja motar suka bar harabar asibitin.

 

Tunda suka shiga cikin motar babu wanda yace da wani kala, hannunshi nakan steery, gaba daya hankalinshi yayi nisa dukda tuki yake yi hakan baisa tunaninshi ya rabu gida biyu ba, dan waigowa yayi ya kalleta ganin yanda ta kafa ma window idanu jikin ta duk yayi la’asar babu kuzari, ‘’how are you feeling now?’’

Juyowa tayi ta kalleshi tace ‘’naji sauqi’’

Maida hankalinshi yayi kan titi ya cigaba da cewa ‘’baki iya karya ba,’’

Dan waigawa ta sakeyi ta kalleshi alamun bata gane abunda yake nufi ba, bai kalleta ba but yayi sensing kallonshi take, hankalinshi nakan tukin da yakeyi yace ‘’you don’t look okay’’

Sauke kanta tayi kasa, muryanta a kasa tace ‘’yaya kaima you’re not okay, bakaci komai ba, kuma..’’

‘’I’m okay’’ ya katse ta yana kokarin juya akalar motar ya shiga cikin estate.

Securites na bude mashi gate din apartment dinsu ya shige yayi parking motar, yana kashe motar ta bude kofar, shima bude bangareshi yayi ya futo ya rufe motar tabi bayanshi.

Tunda ta shiga gidan gabanta ya fadi dam, gidan ya zama very empty kamar anyi masu mutuwa, part dinshi ya wuce direct ya barta tsaye tana nazari, kamar zata wuce sama ta juya zuwa part dinshi, da sallama ta bude bedroom din nashi, a zaune ta taddashi ya dafe kanshi da hannu biyu don bata hango fuskanshi, takowa tayi dan nesa dashi ta tsaya tace ‘’yaya me zakaci na dafa maka’’

 

Dan dagowa yayi ya zuba mata rinannun idanunshi da sukayi jaa baice mata komai ba,tana ganin haka ta wuce cikin bathroom dinshi ta tara mashi hotbath kafin ta fito ta kalleshi tace ‘’yaya ka shiga na sa maka ruwa’’

Kanshi a kasa yace ‘’thanks’’

Fucewa tayi ta wuce kitchen ta hada mashi white soup sai coffee, ta dauka kusan thirty minutes kafin ta gama ta shirya komai ta wuce dashi bedroom dinshi, tana shiga ta aje mashi a kan side stool ganin kamar bai fito daga wanka ba kafin ta wuce zuwa nata bathroom din, tana shiga daki ta soma tube kayan jikinta ta wuce bathroom. Wanka tayi ta wanke bakinta kafin ta fito, agurguje ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ko dan kwalin atamfar bata daura ba ta sauko kasa zuwa bedroom dinshi, da sallama ta shige cikin bedroom din, akwace ta taddashi daga shi sai towel yayi rub da ciki, ko abuncin ma bai taba ba da alamu daga wanka ya fito ya kwanta don ko bathroom sleepers bai cire ba, tausayin taji sosai don kana ganinshi kasan barcin wahala yayi, karasowa tayi harinda yake kwance ta tsugunna bakin gadon ta zare mashi bathroom sleapers din, ganin kamar kafarshi zata sage don ba a kan gadon kafafun suke ba, don haka ta soma kokarin gyara mashi ta hanyar daga kafar tashi, yana jin motsinta yayi saurin bude idanunshi ya sauke akanta don barcin bai gama fuzgarshi ba, saurin sakin kafar tashi tayi ‘’daman zan gyara maka ne saboda kar afanka ya sage’’

Lumshe idanunshi yayi ya maidasu ya rufe kafin ya sake bude idanun nashi ya kalleta, miqa mata hannunshi yayi, bin hannun nashi ya soma yi da idanu tana son ta gane abunda yake nufi, ‘’come’’ ya katse mata tunani

Takowa tayi ta rike hannun nashi, baiyi wata wata ba ya fuzgota gaba dayanta zuwa jikinshi ya rungumeta, tunda ta fado jikinshi gabanta na faduwa tayi shuru tana sauraron yanda zuciyarshi ke bugawa ga wani irin zafi da jikinshi ke fiddawa na zazzabi, kankameta yayi gaba daya akan kirjinshi yana sauke nunfashin azaba, sun dauka kusan awa guda ahakan har nunfashinsa ya soma daidaituwa, dan dago da idanunta tayi ta kalleshi, barcin ne ya sake fuzganshi ganin haka yasa ta soma lallabawa donta zare jikinta daga nashi, motsawan datayi yasa ya bude idanunshi kadan ya murginar da ida kan gado ya zamana yana fuskantar bayanta, gyara kwanciyanshi yayi ya rungumota ta baya ya janyo duvet ya lulluba masu, kasa sakewa amra tayi dukda bata hanashi ba saima lumshe idanu datayi har barci ya fusgeta tana jin saukan nunfashinsa a bayanta, wani irin peaceful barci sukayi na kusan awa uku, shine ya fara farkawa ya bude idanunshi, da mamaki yake kallonta saidaga baya kuma ya tuna, ahankali ya soma zare jikinshi daga nata ya gyara mata duvet din ya wuce bathroom, wanka ya sakeyi kafin ya shige cikin closet ya dauko jallabiyanshi ya zura ya wuce masallaci, harya dawo daga masallaci tana kwance tana barcin ta hankali kwance, kallonta yayi kafin ya kauda kanshi gefe ya maida idanunshi kan abuncin data aje mashi dazu dabai samu yaci ba, yana kokarin zama ta bude idanunta bakinta dauke da adduar tashi daga barci tayi miqa, kallo daya ya mata kafin ya dauke kanshi ‘’lokacin sallah ya wuce,go and pray’’

Saukowa tayi daga kan gadon tana dan jin kunya tace ‘’tohm’’, kokarin fucewa takeyi daga dakin nashi yace ‘’you can use that ‘’ yayi mata nuni da bathroom dinshi, juyawa tayi ta wuce bathroom din nashi tana mamakin yanda ya sauya sosai, shigewa tayi ta dauro alwala, tana fitowa ta taddashi zaune yana latsa wayarshi, abuncin data ajiye mashi a gefe, fucewa tayi daga dakin gaba daya ta wuce sama zuwa nata dakin ta zura hijab tayi sallah, tana idarwa ta mike ta sauko ta wuce dakinshi, a zaune data barshi haka ta taddashi don haka ta karaso gabanshi ‘’yaya do you need anything ko nayi maka warming abuncin?’’

Ba tareda ya dago ya kalleta ba hankalinshi nakan wayarshi ‘’yes’’

Ya amsata kai tsaye, daukan tray din tayi ta fuce tayi mashi warming abuncin kafin ta dawo ta aje mashi a gabanshi.

‘’bismillah’’ ta fada tana kallonshi, dan dagowa yayi ya kalleta fuskanshi babu yabo ba fallasa yace ‘’thanks’’

 

Juyawa tayi ta koma kitchen ta dafa simple abunci, coucous da beef sauce, agurguje ta gama ta zuba cikin warmers masu kyau ta saka a basket ta hada dasu plate da serving spoon da bottle water ta fito dashi parlor ta zauna ta doka uban tagumi, after about 30mins sai gashi ya futo daga dakin, ya shirya cikin riga da wando English wears na brand din nike, kayan sunyi mashi kyau sosai, anyways shi komai ma kyauyake mashi, fuskanshi yadan fada kadan, takowa yayi har inda take zaune ba tareda ya kalleta bay ace ‘’muje’’

Mikewa tayi tsaye ta gyara zaman hijab dinta  ta dauki basket din tabi bayanshi don harya fuce daga parlor ya shige cikin motar.

 

Suna isowa asibitin dakin ammah suka wuce, yana gaba amra na biye dashi abaya basu kaiga karasawa bay a dan tsaya, yana duban wayanshi, itama tsayawa tayi daga bayanshi ganin hakan yasashi juyowa yace ‘’go in first’’ yana kaiwa nan ya juya domin picking call din daya shugo wayarshi, shigewa ciki tayi bakinta dauke da sallama, gaba dayansu suna zaune  kan kujeran visitors, salim na gefen aman yana barci while salima na zaune gefen gadon ammah tana kallonta,

Juyowa duka sukayi atare suka kalleta, da sauri salima ta miqe ta karbi basket din hannun nata tace ‘’adda har kun dawo’’

Kaarsowa amra tayi bakin gadon muryanta chan kasa tace ‘’ya jikin ammah’’

‘’Alhamdullah’’ salima ta amsata kafin ta gaisheda aman dake zaune a gefe shima.

Abuncin salima tayi serving aman da salim don basuci komai bag aba dayansu, suna cikin cin abuncin saiga amar ya shugo da sallama, gaishesa su salima sukayi kafin ya wuce gaban gadon ammah, kallonta yayi kafin ya maido da dubanshi kana man yace ‘’any update’’

Aje plate din dake hannunshi yayi ya kalli amar yace ‘’no amma doctor ya shigo dazu ya duba heart rate dinta da pulse dinta yace komai yana daidai tuwa, kuma zata iya tashi anytime’’

Amar baice komai bay a zauna gefen gadon nata  ya kafa mata idanu tare da riko hannunta, kallonshi amra tayi don tana daga dayan gefen gadon tace ‘’yaya a zuba maka abunci’’

Dan dagowa yayi ya mata kallo daya fuskanshi na nan yanda take bazaka taba tantance ta ba kafin ya kauda kasnhi gefe yace ‘’no thanks bana buqata’’

Sauke kanta tayi kasa bata kuma cewa komai ba.

Suna nan zaune har aka kira sallan la’asar, futowa mazan sukayi suka wuce masjid while matan sukayi alwala anan dakin ammah suka yi sallah akan carpet,

Basu dade da idarwa ba saiga su aman sun dawo gaba dayansu,zama sukayi gaba dayansu jugum har doctor ya sake dawowa ya duba ammah.

 

Karfe tara daidai duk suna zaune suna saka ran tashin ammah, kallon amar aman yayi yace ‘’kuje zan zauna da ita yau’’

Dagowa amar yayi zaiyi Magana salima tace ‘’nima zan zauna yaya, ku tafi da adda’’

Shuru amar yayi kafin yace ‘’okay’’

Karfe goma daidai suka fito, amra da aman da salim, cikin mota suka wuce gaba dayansu kafin aman yaja motar.

 

Suna isa gida kowa ya wuce bangarenshi, haka suka kwana sukuku kowa da abunda ke yawo a zuciyarshi.

 

Achan asubiti suna tafiya aman ya kalli salima yace’’maysa baki bisu ba’’

‘’inaso na zauna ne’’ ta bashi amsa, tabe baki kawai yayi ya zauna kan kujera ya lumshe idanunshi, daga nan zaune barci ya daukeshi, mikewa salima tayi ta bude locker na patients da ake blankets da sauran abubuwan amfani, blanket din ta janyo ta rufe closet din kafin ta karaso inda yake zaune, blanke din ta rufa mashi a jikinshi kafin ta kafa mashi idanun ganin yanda yake barci peacefully ba tare da yasan ya dauke shi ba, ‘’I missed you, allah ya bama ammah lafiya mu koma gida cikin farin ciki kamar da, I have so much to tell you,’’

Ba tareda ya bude idanunshi bay ace ‘’you can tell me now’’

Da mamaki ta miqe tsaye donta dauka yayi barci

‘’what o you want to tell me?’’ ya sake tambayarta

Gynguni ta soma yi kafin ta kauda kanta gefe tace ‘’nothing’’

Tana kaiwa nan ta koma bakin gadon ammah ta zauna, yana ganin haka ya maida idanunshi ya rufe.

 

After 2days, haka kullum suke yin switching, yau idan su aman sun kwana gobe su amra su kwana, gaba dayan su sun damu da ammah sosai cikin kwanakin, dukda likita ya shaida masu cewa shes out of coma zata tashi anytime.

Daga 2 days haka kwanaki suka dunga jaa har zuwa sati guda babu abunda ya chanza, a wannan lokacin asad y agama buncike gaba daya akan lantana da abubuwan daya samu daga wajnta don tayi confessing, tunda ya kira amar ya shaida mashi ya kamata yazo yaji komai nan ya fada mashi cewa su riketa kawai kar a shigar da ita kara, saboda bashi da time yanxu, yanxu time dinshi da tunaninshi duk yana wajen ammah, don haka ya tsaida komai akan saita farfado kafin ya ji daga wajen asad akan buncikenan nashi.

Lantana dai tana kulle a wajen headquters din sojoji, bata tsaya yi masu gardama ba lokacin da suka fara interrogating dinta don sun shaida mata zasu ci ubanta idan bata fada masu komai ba, ganin yanda suka hayayyako mata zasu iya kasheta yasa ta yarda ta fara masu bayani.

‘’mene alaqarki da alhaji kabiru’’ asad ya tambayeta

‘’aiki nake yi mashi’’ ta bashi amsa

‘’wani irin aiki kenan’’ ya sake tambayarta

‘’sunana lantana achan kauye, ni haifafiyar kauyen masari ce, neman nakai ne ya kawo ni burni saboda wulaqanci danake fuskanta a kauye saboda cikin shege danayi harna haife dana na barshi a wajen babata achan kauye, lokacin dana dawo nan birni na kama haya na fara sana’ar cigari da goro da safe zuwa rana, da daddare kuma ina saida tuwo a bakin layi, akwai wata rana bazan manta ba na fito kan titi ina kuka saboda kirana da kawuna yayi kan cewa dana da mahiafiyata suna aisbiti basu da lafiya babu kudin magani, inda babata take fama da cutar daji shi kuma dana baya samun ishashe abuncin kirki saboda rayuwar kauye kafarshi ta shanye, ina kuka akan titi ina kokarin na sayar da goro ko zan tattara abunda na tara nakai a masu magani, nan allah ya hadani da alhaji, ya tsaya sayen goro,yana tsayawa ya sayi goron, ganin ina kuka ya tambayeni dalili nan na shaida mashi komi inda nake fada mashi kudinake mena, nan take yace zan iyayin komai don na samu kudi, nan na shaida mashi zan iya, ba tareda da tunani komai ba yace koda kisa ne, nan nashi mashi zanyi saboda bana cikin hayyacina kwata kwata,nan take yace na shiga motarshi, ina shiga kuwa ya kaini har gidanshi, anan cikin motar yace min zan zauna a gidan a matsayin yar aiki, zan dunga fada mashi duk abunda ke faruwa a gidan, in exchange zai biyamin kudin maganin uwata da dana, nan take na amince muka shiga gidan hajiya, nan ya mata bayanin komai, ba tareda hajiya ta musa ba ta amince harna fara mashi aiki, acikin kwanakin kawu nay a kirashi ay shaida min wani alhaji yazo ya biya komai na maganin uwata da dana harda abunci ya saya masu wanda zaikai masu shekara guda, alokacin naji dadi sosai inda na samu alhaji nayi mashi godiya sosai na sake tabbatar mashi da zanyi mashi duk abunda yake so,

Har shekara daya ta wuce banji daga bakin alahaji ba akan abunda zanyi mashi, shekara ta wuce har muka shiga shekara ta biyu inda sabo ya shiga tsakanina da hajiya sosai, hajiya uwar marayu ce, tayi min gata sosai dukda batasan daga inda na fito ba, ta bani ci ta bani sha ta barni na yagi arziki daga jikinta, rana daya alhaji yazo har dakina ya sameni yace aikina ya kusa faraway, nan ya bani wata kwaya yace insan yanda zanyi in dunga sakama hajiya a cikin abunsha, inajin haka nasan so yake ya illatata, da farko daga tambayeshi dalili nan take ya shaken yace idan har nayi mashi gardama ko nayi kokarin bata mashi plans dinshi zai kashe min uwata da kanina harma dani, hankalina ya tashi sosai inda nace mashi zanyi ba tare da gardama ba, nan take ya shaida min duk wata zan dunga ballan kwayar rabi ina saka mata a cikin abunsha, sannan idan yakare zai karo min wasu, haka ya bani na wata biyar kuda shida guda uku Kenan, watan farko babu wata fargaba na samu hanyar saka ma hajiya a cikin abun sha wanda take yawan shansa kusan kullum, haka na dage da hada mata wannan abun ina saka mata duk wata har wata shida ya gifta, abunda na fuskanta a cikin wannan lokacin shine tunda na fara sakama hajiya wannan abun ta fara kananun rashin lafiya ahankali ahankali har shakru suka shude wajen shekara bakwai Kenan da zamana a gidan duk bayan watanni idan maganin yak are haka zai kawo min wasu har takaiga wata rana ta hajiya fadi zuciyarta ta samu heart attack, alokacin hankalina ya tashi sosai nan ya sake tunzurani akan cewa zai kashe min uwata da dana haka na hakura na cigaba da bata, duk wata kuwa haka zai tura min dubu dari a account dina harna mallaki kusan miliyan goma..’’

Tana kaiwa nan ta sauke kanta kasa tana hawaye hannunta dun an nade da bandage, kallonta asad yayi yace ‘’bayanke akwai wanda kike tuanin yana mashi aiki’’

Shuru ta danyi tana nazari kafin tace ‘’gaskia ban sani ba saidai ranar da aka kama alhaji, wani ya kirashi yayi threatening dina kan cewa idan har ban cigaba da abunda alhaji ya dorani akaiba zasu kashe min dana’’

Zaro wayarta asad yayi ya tura gabanta yace ‘’wannan ne number’’

Kallon wayar tayi ta dago ‘’eh shine number’’

Mikewa asad kawai yayi ya fuce daga dakin bayan y agama recording conversation din nasu, direct ya bude whatapp dinshi ya tura ma amar, kasan video yace ‘’you need to listen to this’’

After like an hour saiga amar ya kirashi, asad na dagawa yayi shuru, nunfasawa asad yayi ya gasihesa ya tambayi jikin ammah kafin ay soma mashi bayani ‘’nasan ka saurari confession din datayi, bayan wannan akwai mutun daya wanda suke aiki tare’’

Akusashe amar yace ‘’waye!!!’’

‘’doctor hafiz, family doctor ku’’

Saurin runtse idanu amar yai ranshi ya mugun baci, shiyasa ya gudu Kenan don ranar da aka kawo ammah asibitin yasan cewa rana irin haka zatazo shiyasa tun kafin a kamashi ya gudu, jikin amar har bari yake, bayaji idan har yayi arba dasu zai iya bari su sake nunfashi a dorar kasa, don sun nemi su hallaka amman shi, mahaifiyarshi, mai share kukanshi, jin wannan zancen kadai ma da asad keyi mashi ya gama bata mashi rai sosai, yana jin wani irin zafi aranshi, a fadace ya miqe yace ‘’duk inda dan iskan nan yake ku nemoshi ku ci ubanshi, I will make sure there suffer’’

Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya wurgar da ita gefe harta fashe tanasauke wani irin huci mai zafi kamar zaki, da sallama amra ta shugo dakin nashi hannunta dauke da coffee ta karaso inda yake tace ‘’ga coff….’’

Juyowa yayi azafafe idanunshi sunyi ya buge coffee din, jijyoyin kanshi duk sun tashi sunyi rudu rudu bai iya fushi ba kwata kwata saboda yana da zafin rai ‘’gettt outtttt’’ ya daka mata tsawa, tsayawa tayi tana kallonshi galala ta kasa motsawa ‘’I said get outtt, do I have to repeat my self kafin kiyi sticking hakan a  dummy kwakwalwarki,’’

Saurin sauke kanta kasa tayi daman mai hali baya taba chanza halinshi, duk a tunaninta yanxu ya sauya saboda yanda yayi sanyi sosai, ba kamar yanda yake ada ba ashe bai sauya ba

Dago da jajayen idanunta tayi tana hawaye ‘’insha allahu rabbi daga yau bazan kara zuwa inda kake ba, basai kayi min korar kare ba, daman nasan banida wani daraja a idanunka, bazaka taba chanza yanda kake kallo na,’’

Tana kaiwa nan ta fuce daga daki fuuu ranta yayi mugun baci tana hawa sama ta afshe da matsanancin kuka sosai.

Tana fita ya zauna bakin gadonshi ya dafe kanshi ya furzar da nunfashi, gaba daya baiyi tunanin zai sauke fushin da yake ba akanta, addua ya soma yi har zuciyanshi ta danyi sanyi, toilet ya shige yayi wanka ya futo ya zauna yana tunani, saida zuciyanshi ta lafa ya tuna da abunda yayi mata dazu, tabe baki kawai yayi ya miqe ya shirya.

 

Ranar ma bata bishi asibiti ba haka ya wuce sukayi switching su aman suka dawo gida, dakinta salima ta shige don taji dalilinta na kin kwana yau, lokacin data zo dakin amra na zaune ta doka uban tagumi tunanin abubuwa na yawo akanta, karasowa salima tayi ta zauna gefenta ta dafa kafadarta tace ‘’adda are you okay’’

Kamar jira amra take nan take ta fashe da matsanancin kuka don yanxu kuka ma baya mata wuya, haka ta dunga kuka salima na patting bayanta saida tayi mai isarta salima tace ‘’adda maisa kike kuka’’

Kallonta amra tayi tana share hawayenta tace ‘’ba komai kaina ke ciwo’’

‘’adda please dan allah ki daina boye min damuwarki, we only have each other now, ki fada min bakida kamarni duk duniya’’

Wani kukan ta sake fashewa dashi tace ‘’salima na gaji da abubuwan da yake min, bansan meysa yake treating dina kamar trash ba, kamar baisan daraja na ba’’

Hannunta salima ta rike saida ta gaam sauraronta tace ‘’adda kiyi hakuri komai mai wucewa ne, watarana sai labara, allah yaga zuciyarki akan lamuranki’’

Ba karamin sauqin abunda takeji ta samu ba da sukayi Magana ita da salima, karshe har suka kare da hira kafin su sauka kasa atare su daura dinner.

Washe gari madina tazo gidan, direct dakin amra ta wuce jin abunda ya faru, da sallama ta shiga, amra na ganinta tayi saurin rungume ta tace ‘’anty madina ina kika shiga kwana biyu ba waya’’

‘’sorry dear wallahi nayi tafiyar gagagwa ne zuwa Singapore munje wani semina’’

Zama sukayi bakin gado madina tace ‘’ya jikin ammah, banje asibitin ba saboda bansan wani asibiti aka kaita ba’’

‘’alahmdulllah da sauqi saidai bata farfado ba, yanxu muke shirin zuwa ma’’ amra ta fada tana kallonta

‘’yauwa shikenan saina biku ma ko , Allah ya bata lafiya ya Tashi kafadun ta ’’ madina ta fada tana kallonta.

 

Karfe sha biyu daidai suka wuce aisbiti a motar aman, amra kuma ta shige motar madina har suka iso asibitin……….

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.