Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 26 of 52
Chapter 130
Update
Unedited page
Bai dawo gidan ba saida ya tsaya akayi sallar isha’I dashi kafin ya shugo gidan, lokacin daya shigo main sitting room babu kowa a kasan don haka ya wuce bedroom dinshi direct don hes not in a good mood.
Bangaren amra tun bayan fitar ammah wani irin zazzabi ya rufeta, babu wanda yasan da situation din da take ciki, don ko sallar magrib kasa tashi tayi don ta samu tayi, tana nan kudundine cikin blanket akayi knocking kafin a shugo, lantana ce ta shigo hannunta dauke da tray da ammah ta zubama amra abinci, da sallama ta karaso dakin ta aje a kasan carpet, ganin amra a duqunqune tana rawar sanyi yasa ta karaso gaban gadon tace ‘’anty baki da lafiya ne?’’ kasa Magana amra tayi don gaba daya ta zama very weak, sai karkarwa da jikinta keyi, ganin haka yasa lantana fucewa daga dakin zuwa part din ammah, da sallama ta shiga sitting room din ammah don bata shiga cikin bedroom dinta kai tsaye, tundaga bedroom ammah taji sallamanta don haka tace ‘’shugo’’
Ahankali lantana ta bude bedroom din ta shugo daga bakin kofa ta tsaya tace ‘’hajiya nakaima bakuwar abunci saidai na ga kamar bata jin dadi,’’
Ammah dake zaune gaban dresser ta juyo ta kalli lantana tace ‘’subhanallah, bari nazo dakin’’
Futa lantana tayi ammah ma ta miqe tabi bayanta, amar dake shirin hawowa part din yana ganin ammah da yanda ta rude yayi saurin kallon inda take shirin shiga,ammah ma bata lura dashi ba don yana tsaye wajen stairs, dakin amra ta shige direct cikin sassarfa, lanatana na biye da ita,kai tsaye gaban gadon ammah ta tsaya ganin yanda amra take rawar sanyi, idanunta na neman rufewa, hankali atashe tace ‘’daughter meke damunki subhanallah’’ tallafota ammah tayi ta janye duvet din data qanqame a jikinta kallon lantana ammah tayi tace ‘’jeki dubamin ko Muhammad ya dawo akaita asibiti’’
Lanatana na juyawa don kiranshi sai gashi ya shugo dakin shima kai tsaye, sanye yake da doguwan jellabiya fara har kasa, hannunshi cikin aljihun rigar ya zuba masu idanu, juyowa ammah tayi ganin shi tsaye tace ‘’yaka tsaya anan, shugo mana ka dauketa Mukai ta asibiti’’
Kasa daga kafafunshi yayi, ranshi ya a dagule, ganin ya tsaya kyam ya qi motsawa yasa ammah juyowa ta kalleshi tace ‘’muhammad? Kana jina kuwa’’
Anatse ya bude baki yace ‘’I will call doctor yazo ya dubata’’ yana kaiwa nan ya janyo wayarshi yayi dialing contact din family doctor dinsu, doctor na daga ya fuce daga dakin.
Kauda kai kawai ammah tayi tana mamakin hali irin nashi, me Kenan yake nufi? Badai yana kan bakarshi na sakin yarinyar ba, tasan shi da kafewa akan abu saidai wannan karan zata nuna mashi ta isa dashi don ita ta haife shi bashi ya haifeta ba, kallon lanatana ammah ta sakeyi hannunta rike dana amra dake karkarwa ‘’shiga bathroom ki kawo min luke warm water da towel’’
‘’toh hajiya’’ lanatana ta fada tare da shigewa bathroom din dakin, agurguje ta debo ruwa a cikin bowl da towel ta karaso gaban ammah tare da dukawa, karwan towel din ammah tayi ta jiqashi kafin ta fara gogama amra a fuskanta da wuyanta,ta dae sosai akan amra tana shafa mata ruwan don taji dadin jikinta saidai kamar ma kara mata zazzabin akeyi don jikin yayi zumm sosai, nunfashinta ma kanshi da zafi yake futa daga bakinta, ganin haka yasa ammah tace ‘’wannan wani irin zazzabi ne oh ni Maryam, yarinya daga dawowa’’ kallon lanata ammah tayi tace ‘’ke rage min ac nan’’
Mikewa lanatana tayi don itama a furgice take ta kashe ac, suna nan zaune after like 20mins saiga doctor, amar ne ya shigo dashi har cikin dakin, ammah na ganin haka ta bashi waje ya fara dubata, futa lanatana tayi don ta basu waje shima gogan bai tsaya bay a fuce ganin irin kallon da ammah take jefanshi.
Cikin gaggawa doctor ya dubata harda drip ya saka mata ganin ta zama weak, kafin ya mata allurai da zai saukar da zazzabin, saida ya tabbatar shes stable kafin ya kalli ammah yace ‘’hajiya bamu gaisa bama ina wuni’’
Murmushi ammah tayi don tana zaune daga bakin gadon tace ‘’lafiya kalua doctor, ya jikin nata?’’
‘’alhamdullah its just a fever, nayi mata allurai da zai saukar dashi sannan ga drip nan na saka mata zuwa anjima idan yak are sai a cire mata’’
Godiya sosai ammah tayi mashi kafin ya ta rakoshi har kasa, doctor na tafiya ta wuce dakin amar kai tsaye, tana knocking kofar tace ‘’muhammd’’
Amar dake kwance daga shi sai shorts yayi saurin miqewa ya janyo jallabiyanshi ya saka ya bude kofar bedroom din, ganin ammah tsaye fuskanta babu walwala yasa ya sauke kanshi kasa, kallonshi tayi cikin fada tace ‘’muhammad lafiyanka kuwa?matarka na chan kwance babu lafiya kai kana nan zaune hankalinka kwance? Waye zai kula maka da ita ni? ‘’
‘’im sorry ammah ba haka bane’’ ya fada kanshi a kasa
‘’okay menene then? Don’t tell me kana kan bakar ka saika saki yarinyar nan? Look bari kaji, Muhammad baka isa ka saki yarinyar nan ba saina baka umarnin haka, don sainaji daga bakinta idan tana raayin haka’’ ta karashe rai abace
Dan dagowa yayi ya kalli ammah zuciyanshi na mashi zafi sosai yace ‘’but ammah….’’
Katse shi tayi ta hanyar cewa ‘’but what?’’
Sunkuyar dakanshi yayi don bazai iya kallon cikin idanunta a wannan yanayi ba, ganin haka yasa ammah fucewa daga bedroom din nashi gaba daya, tana fucewa ya cije lower lips dinshi, saida wajen yayi jaa sosai amar zai fashe, dakin ya koma ya zauna bakin gadonshi ya dafe kanshi, ahanakli ya soma Magana ‘’ya allah, ammah please karki hanani abunda nayi niya, babu wani amfani aje mace arayuwana, bana buqata’’
Ranshi a dagule haka ya kwanta, abubuwa sunyi mashi yawa.
Ammah na fitowa daga bedroom dinshi ta nufi hanyar stairs, salima dake zaune a dining tana cin abunci ta hango ta, da sauri ta karasa cin abuncin don daman kadan ya rage a plate din,kafin ta miqe zuwa wajen ammah ‘’ammah naaa tun daxu nake zuwa dakinki ban ganki ba’’
Murmushi ammah tayi mata tace ‘’ina dakin daughter ne bata jin dadi’’
Shuru salima tayi kafin ta dan tabe baki, kallonta ammah tayi tana karantar ta, kafin tace ‘’ina salim?yayi dinner?’’
‘’eh yayi tun daxu, har yayi bacci mah,’’ ta bata amsa fuskanta dauke da murmushi
‘’ammah kinci abunci?’’ salima ta tambaye ta cikin kulawa
Murmushi amma tayi mata kafin tace ‘’nayi dinner tun daxu, kune dai da kuke son cin dinner late’’
Dariya salima tayi suka hau sama atare har daki salima ta rakata kafin tayi mata sallama ta fito, tunda ta fito daga part din ammah ta kafa ma kofar dake chan gefen dakin su kallo, tunani kala kala na yawo aranta, tana son shiga saidai wata zuciyar na hana ta yunqurin shiga.
Jiki a mace ta taka zuwa bedroom din tayi knocking, jin shuru babu response yasa ta dan bude kofar ta shiga, a kwance ta tadda amra hannunta da drip, kasa daga kafa salima tayi, hawaye ne ya soma bin kuncinta take tausayin amra ya fara dabaibaye ta, takowa tayi har bakin gadon ta tsaya ta kafe fuskar amra da kallo, ta chanza mata sosai, tayi kiba da cika, ta zama wat babbar mace a fuskanta, kallon yanda take barcin wahala salima tayi, tana jin qaunar yar uwar tata na ninkuwa hade da tausayinta lokaci guda, nan take ta fara tunanin da bata son yi,ganin amra na kokarin juyi da hannunta dake dauke da canula zata danne hannun yasa tayi saurin rike hannun nata don har yadan kumbura kadan, ahankali salima ta taimaka mata ta gyara mata kwanciyar kafin ta janyo mata duvet ta lulluba mata ta juya gaban switch ta rage mata haske kafin ta fuce..
The next morning…
Wajen karfe takwas amra ta bude idanunta da sukayi mata nauyi sosai,kallon dakin ta fara yi daga kwance, kafin ta miqe zaune dakyar, cije lebenta tayi jin yanda bayanta ya rike,tace ‘’arshhh’’ da muryarta da baya fita sosai,kallon rail din dake dauke da drip tayi kafin ta maida kallonta ga hannnuta dake mata zugi dauke da canula,anatse ta cire canula din ta kafin ta sauke kafafunta kasa ta wuce bathroom, wanka ta farayi da ruwa mai dumi sosai don jikinta yayi tsami sosai kafin ta wanke bakinta ta dauro alwala, dakin ta dawo ta maida kayan data cire kafin ta shimfida sallaya don gabatar da sallolin da ake binta, tana idarwa ta jingine da bangaon dakin tana tunani, da sallama ammah ta shigo dakin, da sauri amra ta miqe muryarta chan ciki ciki tace ‘’ina kwana’’
Takowa har inda take ammah tayi ta riko hannunta zuwa gefen gadon ta zaunar da iat kfin ta zauna gefenta tace ‘’morning daughter kin tashi lafiya? Ya jikin ki?’’
Anatse amra ta sunkuyar da kanta tace ‘’alhamdullah da sauqi,’’
Murmushi amma tayi mata tace ‘’bari akawo maki breakfast ko akwai abunda kike so adafa maki’’
kasa cewa amra tayi kanta a kasa jiki a mace tace ‘’ah ah!!’’
nunfasawa ammah tayi ganin har yanxu taqi sakewa yasa tace ‘’toh bari akawo maki saiki samu ki karya,babu abunda ke maki ciwo ko?’’
‘’ah ah babu nagode ammah’’ amra ta fada tana dan murmusawa
Wani irin dadi ammah taji kafin ta fuce daga bedroom din, cikin yan mintuna kalilan lanatana ta shigo da lafiyayyan breakfast ta aje mata bayan sun gaisa, lanatana na fita ta tako har inda ta aje mata breakfast din, zama tayi ta deba yanda zai zauna a cikin ta.
Nan zaune lantana ta sake dawowa hannunta dauke da kaya doguwar riga mai mayafi mai kyau cuttons,gabanta ta karaso tace ‘’gashi hajiya tace akawo’’
Karba amra tayi tare da yin godiya, kafin ta juya.
Anatse ta gama cin abuncin ta mikew ta sauya kaya, rigar ta zauna mata ciff ciff don bubu ce, mai hade da mayafi, tana gama shiri ta dan fesa turaren dake kan dresser, cikin nastsuwa ta kwashe plates din data gama cin abunci da tray din ta futo daga dakin, waige ta fara yi don parts din dake saman suna na da yawa, chan gefe ta hango stairs, cikin natsuwa ta bi hanyar ta fara saukowa, babu kowa a kasan don haka ta fara waigen hanyar kitchen, gashi bata san ko’’ina a gidan ba, tana cikin waige waige ta hango hango wani dan sako da sautin cokula, takowa ta farayi don duk tunaninta nan ne hanyar kitchen din, shiga wajen tayi kai tsaye bakinta dauke da sallama, duk atare suka waigo suka zuba mata idanu banda amar dake facing hanyar shugowa dining din, dago tayi idanunta ya suaka akanshi, nan take hannunta ya soma karkarwa don kirish ya rage plate din ya fadi, saurin sauke kanta kasa tayi, kallonta amma tayi tace ‘’daughter kin sauko?kina buqatan wani abun ne?’’ tayi tambayar fuskanta dauke da murumshi, anatse amra ta dubi bangarenta don tana daga gefen amar tace ‘’daman kitchen nake nema zan aje wannn’’
‘’ay da kin barshi kin kwanta kin huta lanatana zata kwashe,lantana lantana’’ ammah ta fada tana kallon hanyar kitchen, daga chan kitchen lantana ta amsa
Aman dai kasa tauna abuncin dake bakinshi yayi don yana ganinta yaga kammaninta da su salima sosai,don badan yaga tana da kiba bama zaice wannan ay salima ce, amar kuwa ta wutsiyar ido ya kalli inda take tsaye kafin ya kauda kanshi gefe, maida hankali da yayi wajen cin abuncin sa cikin kamewa, ba tare da yace tak ba, amra dai kamar ruwa ya cita ta kasa cewa komai saida lanatana ta karaso ta karbi plate din kafin ammah tace ‘’daughter kije ki huta ko’’
Sunkuyar dakai amra tayi kafin ta juya, har zata tafi ta dawo tace ‘’ina kwanan ku’’ Aman ne kawai ya amsa ta fuskanshi dauke da surpise,
Batare da ta tsaya sanin wanda ya amsa ba ta juya ta wuce sama gabanta na faduwa don wani irin kunyar amar take ji sosai.
Tana fucewa aman ya kalli amma yace ‘’ammah whos she?’’
Murmushi amma tayi ta cigaba da cin abuncinta tace ‘’your sister inlaw ga mijinta nan a gefenka’’
Da sauri amar ya dago ya kalli ammah, itama shi take kallo don ganin reaction dinshi, saurin kauda kanshi gefe yayi ya miqe yabar dinin din, aman kuwa da tambayoyi suka mashi yawa ya sake cewa ‘’itace matar shi da yayi aure?’’
‘’yes itace’’ ammah ta bashi amsa kai tsaye, jinjina kai kawai yayi
Amra na wucewa sama ta shige daki ta zauna gefen gado ta doka wani uban tagumi, gaba daya jikinta yayi sanyi, tunawa da yanda ko kallon inda take baiyi ba, ahankali wani hawaye mai dumi ke xubowa a fuskanta, tana regretting abubuwa sosai akan shi, yayi mata abunda duk duniya bazata taba ganin laifinshi ba, takaicin kanta takeyi akan yanda ta dunga judding dinshi, ashe gata yake mata, she can clearly recall lokacin data gudu daga gidanshi, ashe all this while shike protecting kannenta shine ya taimake su shine ya inganta rayuwarsu, saurin runtse idanunta tayi tana jin takaicin kanta da yanda ta dunga behaving.
Yana shiga daki bathroom ya shige after few minutes ya fito daure da towel,agaggauce y agama shiryawa cikin kananun kaya, saida ya feshe jikinshi da turarukanshi masu sanyin kamshi kafin ya fuce daga dakin, yana fitowa sama ya wuce zuwa dakin ammah, yana shiga bai jima ba ya fito ya sauka kasa ya fuce daga gidan gaba daya.
Haka amra ta wuni a daki ita kadai, time to time ammah ke shigowa dakin tana dubata, su salima kuwa daman sun tafi school, karfe biyu daidai suka dawo ita da salim, daki suka wuce direct suka sauya kaya, salim ne ya fara fitowa yabar salima a daki, direct dakin amra ya wuce yayi knocking kafin ya bude kofar, amra na ganin shi tayi saurin miqewa tsaya, kallonshi ta soma yi tana mamakin yanda ya kara girma, miqewa tayi da saurin ganinshi tsaye shima ya kafa mata idanu, har gabanshi ta tsaya ta mashi murmushi tace ‘’salim kaima kana fushi dani ko?’’
Hannunshi ta janyo fuskanta gwanin ban tausayi tace ‘’forgive me kaji salim, bazan taba abandoning dinku ba kaida salima’’
Saurin rungumeshi tayi tana hawaye shima rungumeta yayi yana hawayen kewar ta, yanxu wannan addar su ce, yana jin abun kamar a mafarki, da kyar amra ta janye jikinta daga na salim, yana ganin haka ya soma goge mata hawyen fuskanta yana mata murmushi, itama murmushin take mashi, kallonshi tayi tana nazari don tunda ya shigo baice mata kala ba don haka tace ‘’bazaka kulani ba ko salim? Kana fushi dani har yanxu?’’ ta fada tana marairaicewa , kallonta yayi ya girgiza mata kai alamun ah ah, daga chan bakin kofa salima data fito daga dakinsu ta hango su tayi saurin karasowa inda suke, kallon yanda amra ta kafe salim da idanu tayi, cikin sauri salima ta karaso dakin ta janyo hannunshi waje ranta a bace tace ‘’meka tsaya yi anan, wuce mu sauka’’ juyawa tayi tare da salim, amra na ganin haka tayi saurin cewa ‘’salima…’
Tsayawa salima tayi ba tare da ta waigo ba, amra na ganin haka tace ‘’salima dan allah….’
Katseta salima tayi ta hanyar cewa ‘’don allah ki rabu damu adda, na fada maki bama buqatar ki yanxu, alokacin da muka buqace ki ay baki waigo mu ba’’
Tana kaiwa nan ta jaa hannun salim suka bar wajen,ammah dake jinsu daga kasa tayi mamakin yanda salima ke Magana da amra, tasan dole suji zafi saboda ta tafi ta dauka shekaru acahn wata kasa ba tare da ta waiwaye su ba saidai sanin cewa basu san halin data shiga sanadinsu bane yasa suke jin haushin ta,
Suna saukowa kasa salima ta kalli salim tace ‘’duk sanda na kara ganinka a dakin nan saina mareka wallahi’’
Kallonsu ammah dake zaune a sitting room tayi kafin tace ‘’salima zo nan’’
Karasowa salima tayi don bata lura da ita bama a sitting room, bin bayan salim yayi shima yana gunguni har suka karaso gaban ammah.
Zama salima tayi a gefen ammah kanta a kasa, kallonta ammah tayi in a calming tone tace ‘’why zaki hanashi zuwa wajen yar uwarshi?, nasan kuna jin haushinta but that doesn’t give you the audacity kiyi ma addan ki Magana haka,kin tsaya kin saurari dalilinta na qin dawowa da tayi?’’
Jiki a mace salima ta girgiza kanta, nunfasawa ammah tayi ta shafa kanta cikin dabara ta manya tace ‘’haba dearest, bai kamata kina mata Magana ahaka ba kinji ko, kamata yayi ki sameta kuyi Magana ta fahimta, babu yanda za ayi dan uwanka na jini yayi abandoning dinka, listen to her with open ears kinji ko?’’
Hawaye ne ya zuboma salima tayi saurin sharewa tace ‘’toh ammah’’
‘’yauwa ko kefa, kuje kuci abunci kafin lokacin islamiyya yayi’’
‘’tohm ammah’’ salima ta fada tare da miqewa, dining suka wuce ta zuba masu abunci ita da salim.
Bangaren amar direct headqauters ya wuce inda suka hadu hardasu m5 da sojojin da suka karso suka shiga helicopters kusan guda uku, tafiyar awa hudu ta fiddasu daga Nigeria, daidai inda bunciken su ya tabbatar da nan ne factory din alhaji kabiru suka tsaya, wajen gaba daya daji ne gaba da, suna landing duk suka fifito harda asad da mukarrabban shi,gaba daya kowannensu hannunsu dauke da bindigu, tun daga bakin gate suka fara harbi, agurgije suka shiga cikin factory din, nan take yaran alhaji kabiru suma suka fara don zuwan bazata sukayi masu, nan take wajen ya kacame da karar harbi, an kama kusan mutane talatin da suke cikin factory din, waenda sukayi yunkurin guduwa ma saida aka kamosu, daga bayan factory din kuwa katon gida ne da dakuna inda maaikatan ke kwana, nan take suka farabinciken ko ina, akallah sun samu kudi a cikin factory din akallah kusan billion goma, bayan wannan harda kwayoyin da sukayi sealing, abunda yafi bama su amar mamaki shine suna yin production din drugs din professionally harda batch number da seal din nafdac alamun shaidar drug din an tantance su, nan take suka fara fidda drugs din daya bayan daya, da chemicals din da suke amfani dasu wajen hadawa, harda waste din drugs din komais aida suka dauka saboda evidence, asad dai tsayawa yayi yana kallon yanda ake ainihin bincike, ba kmar yanda sukeyi baa nan Nigeria, don nan idan an kama mutun kotu kawai ake kaishi a yanke mashi hukunci, suko su amar da sauran sojojin dake karkashinsa daga uae aiki sukeyi tukuru wajen tattara komai babu abunda suka bari, saida suka gama komai suka tattara komai kafin su rufe wajen gaba daya.
Basu suka dawo ba sai wajen karfe sha biyu na dare, daga headquarters gida ya wuce direct, yana shugowa ya wuce dakinshi direct.
Washe gari da sasafe ma haka ya shirya ya fuce daga gidan tun kafin kowa ya tashi.
Bangaren Aman ya natsu sosai, ya daina shaye shaye ya zama natsatse sosai da taimakon salima, wanda yanxu sun fara jonewa dukda har yanxu bata karbi tayin soyayyar shi shiko kullum nuna mata yake yanda yake qaunarta, yanxu ya maida hankali sosi wajen aiki a company don gayara abunda mahaifin ya lalata, relationship dinshi da amar ya gyaru sosai don yanxu baya mashi irin kallon da yake mashi a baya, don ya gano da taimakon aman aka gano duk wani ayyukan da alhaji kabiru yayi.
Salima ma tun bayan Magana da ammah tayi mata akan amra, tayi kokarin danne abunda ke zuciyarta, saidai har yanxu ta kasa daina fushi da ita, don ko hanyar da take bata bi,salim dai kullum yana zuwa wajen amra don hanashi da salima keyi yanxu ta daina.
Bangare amra har yanxu ta kasa sakewa da gidan,yau kwanan ta hudu da suwa gidan kullum tana kunshe a daki,zuwan da salim keyi ne ke debe mata kewa, abunda yake tayar mata da hankali shine yanda kwata kwata salim baya Magana, gashi salima taki bata dama zuyi Magana don tsoron tambayarta ma take yi, haka zaizo idan tayi Magana yayi shuru sai ta fashe da kuka.
Saturday morning….
Tunda ta tashi take fama da ciwon kai,tun bayan datayi wanka ta zauna bakin gado ta doka uban tagumi, tan nan zaune lanatana ta kawo mata breakfast, tana futa salim ya shugo, kallonshiamra tayi harya karaso inda take ya zauna agefenta,kallonshi amra tayi tace ‘’salim ka tashi?’’ girgiza mata kai kawai yayi yana murmushi
Tana ganin haka tace ‘’salim baka Magana ne?’’
Nan ma girgiza mata kai yayi, jiknta ne yayi sanyi ta kara tambayrshi ‘’meysa baka Magana?’’
Sunkuyar da kanshi yayi kasa tana ganin haka tace ‘’kaci abunci?’’
Girgiza mata kai ya sakeyi alamun baici komai ba tana ganin haka tace ‘’zo muci tare’’
Da murnarshi ya zauna gefenta ta jawo masu abunci sukaci atare, tana kallonshi tana jin dadi aranta.
Suna gamawa ta kafa mashi idanu tana kallonshi babu uhm babu uhm uhm.
Baibar dakin amra ba saida lokacin islmiyya yayi ya koma dakinsu don ya shirya, yna shigowa salima ta waigo ta kalleshi kafin ta kauda kanta tace ‘’kaidai wallahi kana da naci, harka manta wahalar da muka sha a gidan uncle, shine kake..’’
Juyowa tayi ganin ya wuce bathroom baima tsaya ya saurareyta ba yana fitowa ta kalleshi tace ‘’banza kurma kawai’’
Juyowa yayi ya galla mata harara, banza tayi dashi ta saka hijab dinta tace ‘’inkaga dama ka sauko mu tafi’’ tana kaiwa nan ta fuce daga dakin.
Dakin ammah ta fara zuwa tayi mata sallama kafin ta sauka kasa wajen driver.
Driver dake zaune da maigadi suna hira ya hangota daga nesa kallon ta yayi kafin yace ‘’baba mai gadi yarinyarnan gaba daya zubinta na Fulani ne, yanda kasan gari daya suka fito da mlm labaran,’’ juyowa baba mai gadi yayi yace ‘’naji ance yayan kanin hajiya ne, kasan itama bafullatana ce saidai basa kama da yan gidan kwata kwata’’
Miqewa driver yayi yace bari naje na saukesu a islamiyya’’
Yana kaiwa nan ya karasa ya bude motar, tana ganinshi ta gaishesa ta shige motar, cikin yan mintuna salim ya fito shima suka fuce daga gidan.
Bayan fitarsu ammah ta fito cikin shigarta da kamala,riga da zani na atamfa, dakin amra ta wuce direct tana shiga ta hangota gefen gado ta doka uban tagumi, murmsuhi amma tayi ta karso har bakin gadon ganin gaba daya tunaninta yayi nisa, ‘’daughter, lafiya dai tunanin me kikeyi’’
Da sauri amra ta kalleta kafin ta sunkuyar da kanta kasa tace ‘’ina wuni ammah’’
‘’alafiya lau daughter’’ ammah ta masa ta fuskanta dauke da murmushi
Shuru ne yadan ratsa tsakaninsu kafin ammah ta nunfasa tace
‘’menene asalin sunanki?’’
Atsanake amra tace ‘’Aisha’’
‘’masha allah’’ ammah ta fada tana murmusawa kafin ta cigaba
‘’’’aisha ina son ki daukeni a matsayin uwa kamar yanda su salima suka daukeni, inason ki cire kunya ki saki jikinki anan gidan kinji ko?,’’
‘’insha allah’’ amra ta fada tana sunkuyar da kanta fuskanta dauke da dan murmushi
‘’masha allah, yanxu inason naji ta bakinki, ki fada gaskia karki boye min komai, wani irin zama kukayi keda Muhammad achan dubai’’
Gaban amra ne ya fadi dammm,samun kanta tayi da kasa cewa komai har saida ammah tace ‘’karkiji tsoro kinji ki fada min komai, shin zamanku da Muhammad bayan yarjejeniya da kukayi babu komai tsakanin ku?’’
‘girgiza kai kawai amra tayi ta kasa cewa komai saida ammah ta sake cewa ‘’yace kin buqaci ya sakeki?,har yanxu kina son ya sakeki ne?koda kuwa shi baya son yin haka?’’
Kasa motsi amra tayi balle ta dago ta bata amsa sai , ammah na ganin haka ta gane tana da matsanancin kunya don haka kai tsaye ba tare da wani kwana kwana ba tace ‘’kina sonshi?’’
Shuru amra tayi hawaye na gangarowa akan fuskanta, koda ace bai dauki kannenta bay a kula dasu ba bazata taba iya kallon mahaifiyarshi tace mata bata son zama dashi ba,
Ammah na ganin haka ta sauke ajiyar zuciya tace ‘’bazanyi forcing dinky ki fada min ba aisha, but kiyi tuanni akai kinji, zan dawo anjima zamu sake maganar nan, ‘’
Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin…
Daki ammah ta wuce tayi mata order kayan sawa ready made, dukda bata san size dint aba haka ta bayar ayi mata kafin ta zuwa dan wani lokacin idan komai ya lafa sai suje a dauka size dinta, tana gama waya da designer dinta wato zetatelia fashion house, wayar amar ta soma kira, don tana sane dashi kwana biyu yanda yake doging dinta,ringing daya biyu ya daga wayar yana dagawa tace ‘’kana ina?’’
Magana yayi daga chan bangaren kafin tace ‘’ina son ka dawo da wuri inada Magana dakai’’ tana kaiwa nan ta akshe wayar,mikewa tayi ta shiga dakin closet dinta, abubuwan amfani daga kan sprays, mayukan shafawa masu tsada turarruka, haka ta kwaso ta wuce dakin amra dasu, akwance ta taddata don haka tana shiga tace daughter ga wannan ki fara amfani dashi kafin zuwa nextweek saimuje shopping ko’’
Sunkuyarvdakai amra tayi ta mata godiya kafin ta fuce.
Kallon abubuwan amra tayi, wani irin dadi taji aranta son dama taba buqatar su sosai.
Karfe shida takwas daidai ya shigo cikin gidan saida ya fara tsayawa a masallaci yayi sllah kafin ya wuce cikin gida, direc t dakinshi ya wuce bai tsaya komai bay a watsa ruwa ya sauya kaya kafin ya fuce daga dakin, hawa stair ya fara yi ya tunkari part din ammah, bai kaiga karasawa ya jiyo muryar amra
‘’salima don allah ki kulani, wannan silent treatment din da kike bani is killing me, wallahi azeem bazan taba abandoning dinku ba kiyi hakuri ki yafe min’’
Kallonta salima tayi don daman tazo kiran salim ne don suje suci dinner shine amra ta tare ta da tambayr meysa salim baya Magana, tambayar ta bata mata rai sosai, don idanda tana tare dasu ay zata san dalilin rashin maganar nashi, abunda yafi bata mata rai Kenan, don haka cikin kuka ta soma Magana harshly ‘’wallahi adda bazan taba yarda da maganr ki ba, shekara hudu fah?tunda kika tafi baki waigo mu ba sai yanxu, lokacin da muke buqatarki ay baki zoba sai lokacin da bama buqatarki,yanxu dan allah bakiji kunyar tambayar dalilin rashin Magana da salim keyi ba?are you not feeling ashamed?, tunda tun farko baki damu da sanin halin da muka shiga ba maysa yanxu zaki damu, kibarmu yanda kika ganmu’’ ta karaseh tana kuka wiwi, itama amra kukan takeyi tana jin zafi da kunan rai, amar dai daga nesa yake hangosu don suna bakin kofa, tsaki kawai yayi ya shige dakin ammah, yana shiga ya taddata tana sallah kan sallaya, karassawa yayi cikin dakin ya zauna kan ottoman harta idar ta shafa, kallon inda yake tayi kafin ta miqe tsaye ta karaso inda yake ta zauna bakin gado, cikin nastuwa yace ‘’barka da dare ammah’’
kallonshi tayi a kamilance tace ‘’kaga dam aka dawo gida da wuri yau?, ko ince k agama kauce kaucen naka?’’
shuru yayi ya kasa dagowa,
‘’muhammad’’ ammah ta kirashi
Dan dagowa yayi ya kalleta yace ‘’naam’’
‘’da wayonka da hankalinka basaina fada maka maanar hakki ba, na lura da kana son ka nuna min kai ka girma ko?,’’
Ta fada tana kallonshi, saurin dagowa yayi yace ‘’ammah ba haka bane…’’
Kallonshi ta sakeyi tace ‘’so? Gardama zakayi min Kenan?’’
Sunkuyar da kanshi yayi kasa ya kasa cewa komai, saida tace ‘’maysa kake son sakin ta?’’
Kamar jira ko yake tayi tambayar yace ‘’ammah babu amfanin auren, aside from that wannan auren wallahi ban daukeshi a matsayin komai ba, yarjejeniya ne kuma its over, wallahi ammah bana buqatar mace a rayuwana, I have a lot on my he…’’
Kasa karasawa yayi ganin yanda fushi ya bayyana a fuskanta karara azafafe tace ‘’ta gama maka amfani Kenan muhammad wato bari ka sake ta baka buqatar mace arayuwarka, to bari kaji, wallahi wallahi ka roki allah kada yarinyar nan tace itama batason auren don wallahi youll regret it, kai ina tunaninka, im not trying to be selfish over here don zan tambayeta dakaina idan har tace batason auren zan barku kuyi abunda kukeso but inason ka sani, a zamanin nan babu macen da zata zauna da namijin da baya haihuwa duk kyawunka da arzikinka da mukamun ka da kake takama dashi , maysa bazakayi wannan tunanin ba?’’
Hade rai yayi ranshi adan bace aranshi yana jin zafin abunda ammah tace wai babu macen da zata iya zama dashi Kenan saboda baya haihuwa duk ajin shi da arxikinshi, shi abunda yafi bata mashi rai shine yanda ammah ke mashi fada akan wannan yarinyar’
Dan dagowa yayi idanunshi yayi jaa ya kalli amma muryarshi a kasa yace ‘’ammah please….you have to understand, nine bana buqata, I don’t mind nayi rayuwana a haka, bayan wannan ma ita da kanta ma ta buqaci sakin koda kuwa bata buqata ba ma zan bata dakaina saboda batada wani amfani a wajena, shes not my type, yarinya ce karama ammah, shes just 22,’’
Rai abace ammah ta miqe don kwata kwata kamar ma bai gane maganganun da yakeyi ne suke hasala ta ba ‘’muhammd idan kai ka haifeni zan sani idan kuma nice na tsugunna na haifeka to dole kayi abunda nace, now get out my room,’’
‘’ammah please I don’t mean to upset you, don allah karkiyi fushi’’
Ya fada anatse
‘’muhammd get up, karna kara ganin fuskanka’’ ta fada idanunta a rufe don ranta ya baci, daman ance mai hakuri bai iya fushi ba
Yana ganin haka gabanshi ya fadi hankali atashe ya rike hannunta ya zaunar da ita cikin sanyin murya yace ‘’ammah na, please calm down, don allah kiyi hakuri wallahi zanyi duk abunda kike so dan allah kar kiyi fushi dani please, me kikeso ayi yanxu?bakya son na saketa right? Shikenan zanyi abunda kike so’’
Bata kalleshi ba tace ‘’zan kwanta’’
Yana jin haka ya miqe jiki a mace yayi mat sallama ya fito rai abace, azafafe ya wuce dakin amra yana zuwa ya bude kofar a zafafe, a durkushe ya taddata ta rike ciki tana kuka, rai abace ya karaso dakin ya kalleta yace ‘’keeeee!!!’’
Yanda ya fada saida dakin ya amsa, da sauri ta miqe tana muzurai gabanta na faduwa,kallon fuskanshi tayi ganin yanda ya karade yayi jaaa kamar bashi ba yasa gabanta faduwa,bata ankare ba ta ganshi gadan gadan yayo kanta, kan kace me nan take ta sulale a sume, dan tsaywa yayi yana kallon ikon allah, yama rasa abunda zaiyi yana huci kamar zaki, juyawa yayi ya doka tsaki yabar dakin, kasa ya wuce zuwa dakinshi wuce ya zame kayan jikinshi ya shige bathroom, cold shiwer ya sakarma kanshi don hot temper dinshi yah au sosai, ya dade sosai saida yaji zuciyarshi ta lafa kafin ya fito anatse kugunshi daure da towel, closet dinshi ya shiga ya zaro kayan barci kafin ya shirya, gadon shi ya hau yayi rub da ciki, ya dauka kusan minti talatin ahaka hanakli ya soma jin yunwa don haka ya miqe ya zura bedroom slippers dinshi ya fuce daga dakin, fitowa yayi daga dakin cikin kamewa yawuce dining, nan ya tadda salima zaune da plate din indomie agabanta, kallonta yayi tana ganinshi itama tayi saurin miqewa tace ‘’ina wuni ya muhammad’’
Ataqaice ya amsa ta ‘’lafiya’’ kafin ya janyo kujera ya zauna, kallon wall clorck din dake gaban dining din yayi ganin kusan goma da rabi yasa yace ‘’why are you eating late’’
Sunkuyar da kanta tayi tace ‘’dazun ne kaina ke ciwo saina kwanta’’
Shuru ya danyi yana wani nazari kafin yace ‘’bring me coffee’’
Da sauri ta miqe ta hado mashi coffee cikin coffee maker tana gamawa ta kawo mashi tace ‘’bismillah ya muhammd’’
Karba yayi yace ‘’thanks’’
Tana ganin haka ta dauke plate din indomie ta wuce kitchen dashi ta karasa tana gamawa ta fito hannunta rike da bottle water,’’good night ya muhammad’’
Dagowa yayi ya kalleta azafafe yac e’’zo nan’’
Anatse ta juyo gabanta na faduwa ta karaso wajen dining din tace ‘’gani’’
Yana sipping coffee din ba tare da ya kalleta bay ace ‘’why where you talking to your elder sister harshly? Ita sa’arki ce?’’
Shuru salima tayi hawaye na zubo mata ta kasa cewa komi saida yace ‘’clean those tears and answer me, ita sa’arki ce?’’
‘’ah ah’’ salima ta fada ahankali tana goge hawayen
‘’who told you tayi abandoning dinku?you better get your head staright, you don’t owe her explation saboda I recall na fada maku cewa saboda ita nasan ku, I don’t have to repeat my self duk halin da kuka shiga ita kinsan wani hali ta shiga ne? kince kunsha wahala tayi abandoning dunku lokacin da kuke buqatarta right? Ita kinsan halin da ta shiga saboda ku day and night? kinsan abunda ta jefa kanta saboda ku?’’ ya karashe a fadace yana kallonta har saida tadan furgita
‘’im sorry ya muhammd’’ salima ta fada tana shesheka, ‘’bani zaki bama hakuri ba, you should be ashamed of your self for being selfish, and this should be the last time da zaki sake mata Magana babu respect understood’’
Da sauri salima ta daga kai jiki na bari tace ‘’insha allah yaya’’
‘’go and sleep’’ ya fada yana aje empty cup din, da sauri kuwa ta juya ta wuce sama.
Tana tafiya shima ya miqe ya wuce dakinshi hankali kwance….
The next morning….
Sai wajen karfe biyar amra ta farfado, bakinta dauke da salati t miqe, duk jikinta ya gam tsami, saida ta zauna ta tuna da abunda ya faru, kamar a mafarki, mikewa tayi ta wuce bathroom tayi wanka ta dauo alwala, tana fitowa ta dora bayarta data zo da ita gida ta saka hija ta tada sallah tana idarwa tayi azkar, sai wajen karfe shida ta miqe ta koma kan gado ta kwanta, bacci ne ya dauketa sai wajen karfe tara ta tashi, tana tashi ta wuce bathroom ta wanko bakinta ta fito, gaban dresser ta tsaya tana karema kanta kallo, ta dan rame, duban kanta tayi dake buqatan gyara sosai don har tsinkewa ykeyi, nannadeshi tayi daga daurewar datayi da ribbom,ahankali ta tura annunta cikin gashi kafin ta fiddashi, hankalinta ne yadan tashi ganin gashi ya biyo hannunta,saurin annnade gashin tayi jin anyi knocking, salima ce ta shigo kanta a kasa tace ‘’good morning adda’’
Da mamki amra ta jyo ta kalleta, murmushi tayi ta tako har inda salima take tace ‘’salima, good morning kin tashi lafiya’’ yanda take Magana kamar itace kanwar salimar, ba tare da ta kalleta ba salima tace ‘’ammah tace ki sauko muyi breakfast’’ tana kaiwa nan ta juya ta fuce daga dakin.
Jikin amra ne yayi sanyi sosai, haka ta jawo veil din abayr tata ta maidashi kanta tayi rolling kafin ta sauko kasan, direct wajen dining ta nufa tana zuwa daidai hanyar gabamta ya soma faduwa, runtse idanu tayi ta karaso cikin dining din tace ‘’sallam alaikum’’ gaba daya juyowa sukayi suka kallet hara mar dake zaune kafin ya hade rai wanda hakan akan idanunta yayi,saurin sunkuyar da kanta tayi ta karaso wajen dining din, ammah na ganinta tace ‘’zoki zauna nan kusa dani daughter’’
Gaban wajen da ammah ke nuna mata ta karaso don dayan side din da mar ke zaune ne sai ya zamana sun sakashi a tsakiya, anatse amra ta zauna kanta kasa tace ‘’ina kwana ammah’’ da sauri ammah tace ‘’lpy lau dota how was your night’’
‘’alhamdulillah amra ta amsa
Murmushi ammah tayi ta kalli salima tace ‘’yan mata na a fara serving dinmu tunda kowa ya zauna’’
Mikewa salima tayi ta fara serving sai alokacin amra ta lura da wanda kekusa da ita, daga chan gefe, ahanakli ta kalli aman tace ‘’ina kwana’’ murmushi yayi mata yace ‘’lafiya kalua sister inlaw’’
Da sauri salima t dago ta kalleshi ta galla mashi harara don duk a tunaninta yaa referring to her ne amatsayin yayar budurwarshi nan ko bata san shi ya fadi hakan ne saboda matsayin amra na matar amar, kallon gefen amar tayi daya hade rai yayi kamar ba a yi ruwanta a wajen ba, kanta a kasa tace ‘’ina kwana’’
Banza yayi da ita kamar baisan dashi take ba wanda hakan akan idanun ammah, ‘’muhammd bakaji ana gaisheka bane?’’ ammah ta fada
Dan waigowa yayi ya mata wani irin mugun kallo ataqaice yace ‘’lafiya’’
Kauda kai amma tayi ta basar, ba tare da tace komi ba.
Lantana ce ta karso dining din ta ajema ammah green juice dinta kafin ta koma kitchen.
Anaste suka fara cin abunci har kowa ya gama amra dai kasa ci tayi sai juya cokali takeyi, ammah na ganin haka tace ‘’daughter ko kina buqatan wani abun ne?’’
Saurin girgiza kai amra tayi tace ‘’ah ah wannan ma yayi’’
Murmushi kawai ammah tayi ta cigaba da cin abuncinta, amar ne ya fara miqewa yace ‘’ammah zan fita’’
‘’ókay adawo lafiya’’ ta bashi amsa yana fucewa aman ma ya wuce office,suna gamawa salima ta mike ta fara kwashewa, amra na ganin haka itama ta mike suka kai plates din kitchen atare, murmushi kawai ammah keyi tana kallonsu su biyu.
Karfe biyu aka kawo kayan da ammah tayima amra order na ready made, da kanta ta shiga dakin don kai mata, tana shiga dakin lokacin amra na toilet, saida ta jira har ta fito.
Da sauri amra ta karaso inda ammah take zaune kanta kasa tace ‘’barka da rana ammah’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’thank you dear, ga kayanan kafin mu samu time mu shiga kasuwa,allah yasa suyi maki daidai,’’
Kallon inda ammah ke nuna mata tayi kafin tace ‘’allah ya saka da alkairi ya kara budi’’
‘’ameen ya allah’’ ammah ta fada tana kallonta kafin tce ‘’zoki zauna nan daughter muyi magana’’
Anatse amra ta tako har inda ammah ke zaune dan nesa da ita bakin gadon ta zauna kanta a kasa, nunfasawa ammah tayi tace’’ daughter fatan kinyi tunani akan abunda na fada maki,’’ anaste amra tace ‘’eh’’
Kallonta amma tayi kafin tadan nunfasa tace ‘’kafin naji daga bakinki ina son nayi wata mahimmiyar Magana dake saboda bana tauyema kowa hakki, muhammd ya fada min auren yarjejeniya da kukayi inda kika buqaci citizenship wato katin kasa ta karkashinsa don ki kawo qannenki kusa dake yanxu dai inason naji daga bakinki shin kinsan dalilin da yasa shi Muhammad ya aureki’’
Shuru amra tayi don bata kwata kwata all this while tunani daya ke zuwan mata akan dalilin aurenta da yayi which is saboda jikinta ya aureta,batayi yunkurin tambayrshi ba ko jin ta bangarenshi dalilin aurenta da yayi, itadai tayi concluding saboda yana shaawar jikinta ne shiyasa ya aureta har ya kaita asibiti aka gwadata don ya tabbatar da bata da ciki don ya saketa, runtse idanunta tayi ta nunfasa tace ‘’ah ah ban sani ba’’
Shuru ammah tayi don tayi tunanin hakan, saida ta danyi wani nazari kafin tace ‘’kinsan oligospermia?’’ Ammah ta tambayeta tana kallonta,
Dagowa amra tayi tadan aklleta kafin ta sauke kanta kasa tace ‘’eh na sani’’
‘’masha allah, Muhammad yana da oligospermia 3rd stage ya aureki ne saboda he has last chance of producing a child’’
Dan nunfasawa ammah tayi muryanta na breaking ta cigaba,’’wannan ne dalili da yasa ya aureki saboda daga wannan last chance din idan bai samu haihuwa ba bazai taba haihuwa ba’’
Da sauri amra ta dago idanunta fal da hawaye, innalillahi ta wa inna ilaihi rajiun ta fara maimaitawa aranta, maganar ammah ce ta katseta ‘’wannan ne dalilin dayasa nace kafin naji daga bangaren inason muyi Magana, duk abunda kika yanke daughter shi za ayi, don anytime muhammd zai iya sakin ki indai kina so,idan kuma bakya ra ayin hakan, ni an tsaya mashi’’
Anatse ammah ta share hawayen fuskanta daya zubo mata tace ‘’my dear babu macen da zata zauna da namijin da baya haihuwa shiyasa bazanyi forcing dinky akan ki zauna dashi ba, idan har bkyaso zai sakeki kinji ko?’’
Kallonta amra tayi hawaye na zarya a fuskanta, tama kasa cewa komai, tausayin ammah y agama dabaibaiye ta sosai, idanunta sunyi jaa sosai wato all this while tayi mashin muguwar fassara, bait aba shaawar jikinta ba ko sau daya, hasalima ya aureta ne saboda that was his lat chance of haihuwa, hawaye ne ya soma yi mata zarya a fuska, sai yanxu take regretting magan ganun data dunga fadamashi, da yanda take cewa ta gode ma allah daya bata dauki cikinshi ba, yanda take jinshi aranta yanxu ya wuce musali, ya samu wani babban gurbi a zuciyarta, dashi da mahaifiyars.
Ammah na ganin haka ta miqe tace ‘’daughter zan barki kiyi shawara kinji ko’’
Tana kaiwa nan ta fuce tana goge hawayen da take boye, salima dake labe bakin kofar su tayi saurin komawa da baya ta boye gefen flower vase, tana ganin ammah ta wuce daki ta fito, idanunta itama ya cika da hawaye she cant believe abunda kunnuwanta suka juyo mata, adda matar ya muhammd ce? Auren yarjejeniya sukayi saboda ta samu katin kasa ta kawosu kusa da ita? Sulale wa tayi anan wajen ta fara hawaye, daman ya Muhammad yace she will regret it idan taji abunda ta jefa kanta a ciki saboda su, kamar wadda aka tsugula ta miqe ta wuce cikin dakin amra, amra dake kukan zuci dana fili bataji kararbude kofar da salima tayi ba sai ganinta da tayi akanta, kura mata idanu amra tayi don tadan tsorata da ganinta tana hawaye,
‘’adda what did I just hear? Auren yarjejeniya kikayi saboda mu?’’
Salima ta fada tana kallonta, kauda kai amra tayi tace ‘’ian kikaji wannan’’
Zama salima tayi gefenta kanta akasa don wani irin nauyin amra ta fara ji tace ‘’adda im so sorry im sorry for blaming you’’
Kuka ne ya kufce mata ta cigaba ‘’wallahi adda ban taba tunani kema kin shiga wani hali ba saboda mu, im so srry addaa’’
Janyota amra tayi a jikinta tana hawaye tace ‘’salima ya za ayi na manta daku, daku nake kwana daku nake tshi, na shiga babban tashin hankali lokacin da kika kirani, don har lokacin nayi niyar dawowa saidai nayi laakari da idan na dawo komai zai iya wargajewa don daddy yace karna sake na dawo ba tare da na biyashi kudinshi ba bayan wannan ma banida wani option daya wuce na san aynda zanyi na kawo ku kusa dani har allah ya hada ni da ya muhammad’’
It was an emotional moment for amra and salima a wannan lokacin, kuka dai har suka gaji babu wanda ya iya hana dan uwanshi suna rungume da juna, saida suka gaji dan kansu suka rarrashi kansu kafin salima tace ‘’adda, ina neman wata alfarma a wajenki, bansan irin zaman da kukayi da ya Muhammad ba but bana jin akwai abunda shida ammah zasu nema a wajen mu muqiyi masu, adda mutanen nan basu san ba sun karbe mu hannubibiyu, ya muhammd yayi mana abunda iyayenmu ne kadai zasu iya yi mana don yayi mana gatan da waenda ya kamat suyi mana basuyi mana ba,shi ya biya mana kudin aikin da akayi mana lokacin da muka kusa mutuwa shine yayi protecting dinmu lokacin da aka watsar damu akan titi, shine wanda dora mu kan ilimin da aka hanamu yi aka tauye mana, shi ya samu a school nida salim ba tareda yasan asalin mu ta sanadiyarki, ke karan kanki bakisan yayi hakan ba,adda babu abunda zasu nema a wajen mu da zamu gagara yi masu shi har karshe nunfashin mu don komai zamuyi masu bazamu taba biyansu da abunda sukayi mana ba’’ hannunta salima ta rike looking very very serious tace ‘’adda rokeki da allah, karki rabu da muhammd don lalurar shi, yau ko bashi da kafa nasan zaki zauna dashi adda, idan har kinason haihuwar ma ni idan nayi aure zan baki duka yayana kyauta, kimin alqawarin bazaki taba barinshi ba adda promise me’’
Amra na hawaye take bin salima da idanu, shes so speechless, wannan yanxu kanwarta ce, salima tayi hankalin da ayau ko bta raye zata kula da kanta da kaninta sannan tasan me ake nufi da halacci,
Murmushi amra tayi danyi tare da yar dariya ta kalleta ‘’basai kin roke ni ba salima, yau koda ace baya iya amfani da jikinshi zan zauna dashi, har abada bazan taba complain ba’’
Saurin rungumeta salima tayi tace ‘’tahnk you adda na, ni zan baki duka yaya na idan nayi aure’’
Kallonta amra tayi tace ‘’soyayya kikeyi ko? Har kinsan wani idan aure zaki bani yaya’’
Dariya salima tayi tace ‘’kaii add aim 19 years fa yanxu’’
Bugu amra takai mata tace ‘’karya kike youre 18 ay a lissafe yake akaina, next month’’
Dariya itama salima tayi tace ‘’wow ni harna manta fah, kuma next month ma graduation dina’’
Hira suka sha sosai ta kewar juna har suka shagala, kiran sallar magrib ne yasa salima fucewa ta barta a daki, murmushi amra tayu sai taji 50% din damuwarta ta raguwa, nauyin da zuciyarta keyi ma duk ya ragu.
Bayan sallar ishai salima tazo ta kirata don suci dinner, tare suka sauko gwanin ban shaawa, anra sanye take da doguwar rigar material da amma tasa akayi mata na bubu, suna karasowa suka tadda ammah da salim akan dining, da murmushi ta tarbesu ganin yanda suka rike hannu suka karso, har kasa amra ta tsugunna tagaishe da amma kafin ta samu waje ta zauna, su hudu kawai sukayi dinner don amar da aman basu dawo ba.
Karfe tara daidai amra ta fito daga dakinta sanye da hijab, cikin natsuwa ta tako zuwa part din da take tunanin na ammah ne don yafita daban a saman, da sallama ta shiga part din, babu kowa a sitting room don haka ta kara kwada sallama, daga ciki ammah tace ‘’bislillah’’ anatse amra ta tako har cikin dakin bakinta dauke da sallama, kanta a kasa ta shigo amma na ganinta tace ‘’daughter shugo mana ya kika tsaya kamar bakuwa daga kofa’’
Anaste amra ta karaso ta tsugunna har kasa ta gaishet kafin ta samu waje ta zauna tsakiyan carpet, ammah na ganin haka tace ‘’haba daughter ki zauna kan gado mana’’
Kai akasa amra tace ‘’nan ma yayi ammah’’
Murmushi amma tayi ta kalleta, kai akasa amra ta soma Magana cikin kunya ‘’uhm daman….’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’kinason ki fada min shawarar da kika yanke ne’’
Kai a kasa amra ta girgiza mata kai tace ‘’ehhh’’
‘’okay inajinki daughter, duk abunda kika yanke haka za ayi’’
Dan nunfasawa amra tayi tace ‘’ammah bana son ya sake ni’’
Runtse idanu ammah tayi cikin farin ciki da jin dadi tace ‘’are you sure daughter, karkiyi deciding kodan abunda yayi maku keda kannenki, inason kibi abunda zuciyarki ta raya maki kinji’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’badan haka bane, babu abunda zan iyayi da zan saka mashi da wannan saidai na roki allah ya biyaku da aljanna, kune gatanmu, duk duniya babu abunda zai chanza wannan’’ ta karashe tana hawaye, kanta ammah ta shafa tace ‘’thank you so much daughter, allah ya maki albarka, allah ya baku zuriyya dayyaba, inda rai akwai rabo, allah mai jin qan bayinshi ne, insha allah zaku dawwama cikin farin ciki har abada’’
Wani irin dadi ne ya ziyarci amra jin kalamin da ammah tayi da adduó ta.
Bata dade ba tayi ma ammah saida safe ta wuce dakin su salima, a zaune ta tadda salima tana zane while salim nab arci, karasowa amra tayi fuskanta dauke da murmushi tace ‘’har yanxu kina zanen’’
Juyowa salima tayi cikin murnar ganinta tace ‘’addaaaaa naa, yau tare zamu kwana ko’’
Kallon book din hannunta amra tayi ta ga zanen nata, kafin tace ‘’kin tuna min da abba, allah ya jikanshi da rahama da mami’’
Hira suka sha sosai kafin su kwanta tare……
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.