Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 37 of 52
Chapter 141
Update!!!
Unedited…
Tunda ya kunna motar yayi reverse ya bar harabar compound din ya dau hanyar zuwa gida, motar tayi tsit sai karar ac, motar su salima na gaban tasu inda salima ke zaune agaban motar sai Salim a baya har suka karaso gida.
Tunda sukayi parking kowa ya fito ya nufi inda ammah ke zaune a bayan motar Amar na shirin fitowa da keken da za a sakata, da taimakon nurse Amar ya fito da ita, kafin su wuce cikin gidan gaba daya,babu wanda yakai su salima jin dadin dawowarta,suna biye da ita har suka shiga parlor, bin parlor ammah tayi da kallo kafin ta fara hamdala, salima ce Tayi saurin cewa “welcome back ammah, gidan was so empty bakya nan, yanxu ya zama complete Alhamdulillah!”
Dariya Duk sukayi ammah dake zaune kan wheelchair ta fuskanceta tace “Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kaddarar hakan zai faru, Ina rokon Allah ya tsare mu daga Duk wani sharri na fili dana badi’ni”
Gaba daya suka amsa da Ameen, sama Amar ya wuce da ita tare da nurse, saida ya tabbatar she’s comfortable kuma babu abunda zasu buqata ita da nurse din.
“Son kaje Ka huta, hidiman ya isa haka, tunda ga nurse nan zata taimaka min” ammah ta fada tana kallonshi bayan ya taimaka mata ta zauna bakin gado, murmushi kawai yayi ya kalleta cikin kulawa “Akwai abunda zaki buqata a sayo?”
Hannunshi ammah ta rike don yana tsaye bakin gadon “no son, kaje Ka huta you look stressed”
Murmushi kawai yayi mata kafin yayi mata sallama ya futo daga dakin, da amra yaci karo dake shirin shugowa, batayi expecting mutun zai bude kofar ba don haka yana bude tayi baya saboda ta ciki aka budo, saurin rike hannunta yayi don yayi tunanin faduwa zatayi “careful!!!!”
Ya fada ahankali kamar ba Amar ba, saurin cire hannunta tayi daga nashi tace “thank you”, bai tsaya ba ya bar wajen, ya dauka kasa, yana wucewa ta shige cikin part din ammah, dakinta ta wuce direct ta bude kofar da sallama, kallonta sukayi gaba daya daga nurse din Har ammah fuskanta dauke da murmushi ta karaso bakin gadon ammah ta zauna tace “ammah kina buqatan wani abu? Me kikeso na daga maki?”
Kallonta ammah takeyi tana murmushi fadin irin dadin da take ji idan ta kalli amra ma mai wuya ne, Nunfasawa ammah tayi fuskanta duaie da murmushin bata daina ba tace “daughter daga dawowa ko hutawa bakiyi ba, gashi alamu sun nuna jin fara nauyi, karki damu kinji, bana buqatar komai yanxu kije ki kwanta ki huta, Kisha barcinki kinji ko?”
Sauke kai amra tayi dukda bata gane akalar zancen ammah ba sai kawai ta tsinci kanta da jin kunyar ammah lokaci guda, kallonsu nurse din tayi fuskanta dauke da murmushin tace “gaskia kam, barci nada amfani a wannan stage din da drinking lots of water”
Shuru amra tayi don bata gane kan zancen ba,gaba daya sun gama confusing dinta, ammah na Ganin haka Tayi saurin cewa “kije ki huta daughter dake da son bansan waye yafi wani damuwa akaina ba, I will be fine”
Mikewa amra tayi jiki a mace tace “Toh shikenan ammah, Zan dawo anjima”
“Toh daughter Allah ya kaimu” ammah ta fada tana godiya ga Allah a cikin zuciyarta
Futa amra tayi zuwa dakin ta don agajiye yake sosai dukda batayi wani abun gajiyan ba, abun yanxu ya daina bata mamaki kwata kwata, yawan barci, da mood swings ga changes da yake gani a jikinta, bata kawo komai aranta ba sai maybe stress din jigilar asibiti da suka dunga yi wanda tana tunanin idan ta samu ta tsaida natsuwarta guri daya komai zai daidata.
Tana shiga daki ta rage kayan jikinta ta shige bathroom ta watso ruwa mai dumi kafin ta fito daure da towel, gaban dresser ta tsaya tana son shafa mai saboda skin dinta dake zama dry sosai cikin kwanakin saidai kuma qiwar yin hakan na cinta sosai, lumshe idanunta tayi jin barcin na neman fuskaganta “wannan wani irin yawan barci ne haka nake yi”
Ta fada tana Mirza idanunta da hannu, kallon kanta tayi a jikin mirror, yau kusan sati biyu kenan rabon da ta kalli kanta a mirror haka, ta dan kara qiba kadan don cukowar tafi futowa akan fuskanta fuskanta ma yadan kumbura kadan, shafa face din nata tayi kafin ta juya ta nufi kan gadon, zama ta fara yin tana tunanin abubuwa da dama, sauke idanunta tayi akan feet dinta Ganin kamar sun dan kumburo kadan, bata kawo komai aranta ba ta basar da komai tabi lafiyar gado cikin mintina kadan barci ya fusgeta.
Bayan futarta ammah ta kalli nurse fuskanta dauke da murmushi tace “is it obvious?”
Kallonta nurse din tayi tana kokari balle magungunan da ya kamata ta sha yanxu kafin yamma tayi, “yea ma”
Nurse ta amsa ta tana murmushi, murmusawa itama ammah tayi tana kara godiya ga Allah.
Tun bayan yabar dakin ammah dakinshi ya wuce direct, gaba daya agajiye yake don kana Ganin fuskanshi kasan he’s stressed, gajiya ne sosai a tattare dashi, yana shugowa dakinshi ya wuce bakin gadonshi ya aje keys dinshi kafin ya fara kokari cire wrist watch din hannunshi, yana cire ya ajiye gefen gado tare da wayarshi kafin ya wuce closet room, cikin natsuwa ya bude kofar ya shige ciki ya soma rage kayan jikinshi saida ya rage daga shi Sai shorts dinshi kafun ya futo, yana fitowa toilet ya shige hannunshi sanye cikin gashinta yana hautsina Ganin nasa,cikin shower ya tsaya ya sauke shorts din nashi kasa ya kunna tab din ya rike kugunshi, ruwa na sauka akanshi yana tunanin maganganun ammah,bazai taba take zancen ta ba don haka dole yayi abunda yake so don ya faranta mata,na farko yanxu zai fara settling case din daddy ya cireshi daga hannunsa yabarma su asad don daman niyarshi ya tafi dashi chan dubai don ya hukunta shi achan don anan bazai iya hukuntashi ba saboda bashida wannan right din don ba Nigeria yake ma aiki, chan dubai kuwa babu wanda zai hanashi hukuntashi, shiyasa ya nemi asad ya karba mashi approval ko kuma ya karba da kanshi hannun president don abu ne mai sauki a wajen shi, kira daya zaiyi mr president zai sa abashi approval saidai baya son bin wannan hanyar don kamar ya karba ne ta inda dole abashi ba saida approval din military din Nigeria ba don case din na hannun su shiyasa asad ya dage akan ya bari ya karba mashi da kanshi idan sunyi approving.
Shampoo dinshi ya dauka ya latsa a hannunshi ya goga a gashinsa dake sheki, ya dauka kusan awa guda yana gida chan yana wanke chan,Har shaving gashin bakinsa saida yayi yana gamawa ya futo feeling refreshed, don kwata kwata tun bayan admitting ammah da akayi a asibiti bai samu time din yin komai ba musamman kula da kanshi daya saba yi koda yaushe, anatse ya fito qugunshi daure da towel harya karaso gaban dresser dinshi, Yan shafe shafen shi yayi ya feshe ko’ina na jikinsa da body mist dinshi kafin ya wuce cikin closet room.
Cikin Yan mintuna kalilan sai gashi ya futo a shirye cikin kananun kaya da sukayi mashi kyau, Riga da wando, rigar ta kamashi sosai musamman wajen damtsen hannunshi gashi tabi lafiyar fatar jikinshi don six packs dinshi sun fito ta cikin rigar, agurguje ya janyon wrist watch dinshi ya saka kafin ya janyo wayarshi da car keys dinshi.
Anatse ya futo daga part dinshi ya tsaya ya karema gidan kallo, gidan is so big yanxu tunanin yanda zaiyi da help din da zata dunga taimakawa wajen Gyaran gidan yake don Yan matan gidan kadai bazasu iya ba,gashi dalilin abunda ya faru yasa baya jin zai iya trusting wata house help ayanxu, harma da professionals helps dukkansu baya jin zai iya yarda da kowannensu ayanxu.
Kauda kanshi gefe kawai yayi ya fuce daga cikin parlor zuwa motarshi, yana shiga motarshi ya kunnata yayi reversing kafin ya fuce daga gidan gaba daya.
Salima dake tsaye a kitchen tana kiciniyar dora lunch a kitchen ita kadai don kafin ta sauko saida ta Leqa dakin amra Ganin tana barci yasa ta sauko kasa kawai don bata son tashinta don alamu sun nuna agajiye take yanda take yin barcin a wahale,
Sanye take da simple doguwar riga mata nauyi hannun rigar ma karami ne sosai,gaba daya kana ganinta kasan tana cikin walwala saboda ammah, Bude freezer tayi ta fiddo Jan mama da kayan miya, naman ta fara sarrafawa kafin ta bude fridge ta fiddo veggies ta fara yankawa anatse cikin kwarewa, jin alamun shugowa mutun cikin kitchen din yasa ta dan juyo, idanun su ne ya sarke dana juna, kallon kallo suka fara na kusan minti biyu don Har wukar hannunta na neman gifcewa daga hannunta harta gives ya fadi kan kafarta, “ahhh wayyo Allah na “
Ta danyi Kara tana duban kafarta, da sauri ya karaso inda take tsaye tana kokarin dukawa, da sauri ya duka ya fara duban kafar nata yana dan fada “why are you careless sai jin jika kanki ciwo jin tsaya kina kallo na kamar zaki cinyeni”
Saurin fusge kafarta tayi ta kalleshi “yaushe na kalleka?”
Dagowa yayi tsaye ya mata kallon ko in kula yace “yanxu mana,”
“Saidai in kaine ke kallo na” ta bashi amsa tana kauda kanta gefe, matsawa baya shima yayi ya tabe baki yace “why are you denying bayan na kama ki?”
“Hmm da wani idon kasan Ina kallonka in kaima ba kallo na kake ba” ta bashi amsa tana kokarin dora carrot daya akan chopping board ta fara yankawa aqule, don maganar shi ta kona mata rai sosai, bai sake kulata ba ya bude fridge ya janyo hallandia yogurt, duban kitchen din ya soma yi yana neman glass cup don baisan inda suke ajiye wa, tana Lura dashi don jefi jefi take kallon side dinshi kafin ta kauda idanunta don karya kamata, ganin duban nashi yaqi karewa gashi cups din na drawer da yake tsaye, runtse idanunta tayi kafin ta bude su ta ajiye knife din ta karaso gabanshi, yana Ganin yanda ta taho ya danyi baya ya jingina da gefen cupboard din drawers din, matsawa tayi daf dashi sosai don nunfashinsa na gogan juna ba tare da ta kalli fuskanshi ba ta zura hannayenta ttsakanin shi ta janyo drawer ta fidda glass cup kafin ta rufe drawer ta danyi baya, kallonshi tayi ta miqa mashi cup din ba tare da tace mashi qala ba, kallonta yayi kafin ya maida idanunshi kan cup din, karba yayi atsanake ya hada da hannunta, wani irin shock tayi saidai bata nuna hakan ba saima zame hannunta datayi ta danyi baya ta koma inda take tsaye tana yankan veggies don, “thank you!” Ya fada ahankali yana kokarin bude cover din pack din, saida yasha ya koshi ya maida sauran kafin ya koma Inda take tsaye daga gefenta “meysa kike gaba dani, is it because…”
Saurin ajiye knife din salima tayi ta kalleshi “baba gaba dakai, babu dalilin da zaisa nayi gaba dakai,”
Katseta yayi saurin yi yana matsawa kusa da ita “then why are you ignoring me?nine ya kamata nayi ignoring dinki saboda ni kika yima breaking heart tho I’ve moved on” ya karashe yana daga mata kira, kallonshi tayi kafun ta kauda kanta gefe “ni bana gaba dakai kaine de…” ta fada tana jin yanda zuciyarta ke pounding,
Murmushi kawai yayi ya miqa mata hannu fuskanshi dauke da murmushi “friends”
Kallon hannun nashi tayi hawaye na shirin zubo mata Tayi saurin dannewa tace “no”
“Please!!!!!” Ya fada yana Jan word din kamar mai riko
Kauda kanta gefe tayi tana jin zafin shi sosai Wai friends may yake nufi da ita kenan,
“Kinyi shuru friend” ya sake magana
Wani irin maqoqon bakin ciki ne ya turniketa yana ganin haka, wata irin dariya ce ke ciyo bai Ganin yanda yake take reacting ba tare da saninta
A harzuke tace “okay but don’t call me frind call
Me with the name you usually call me”
“You mean baby sal? Or sal? Or salima”
Y tambayeta yana kallon cikin idanunta, saurin kauda nata idanun tayi da suka kawo ruwa “anyone” ta bashi amsa tana kokarin slicing green pepper, maganar da yayi ne ya Dakar mata zuciya “okay but banda baby sal, sabod ayanxu baby daya gareni kinga bai kamata na dunga hadata da kowa ba ko sal?”
Rai abace ta dago ta kalleshi “just call me with salima, and please kaje kana distracting dina idan Ka gama abunda kakeyi” tana kaiwa nan ta juya mashi baya ta wuce wajen sink ta fara wanke veggies sun hawaye na sauka akan idanunta tana gogewa, sarai yaga yanda yake goge hawayen tana basar wa, baice komai ba ya danyi dariya ta gefen baki kafin ya tabe baki “au harda korata salima?“ yanda ya karashe maganar da suna ta kamar an buga mata mashi a zuciya, saurin runtse idanunta tayi ba tare da da tace mashi Tak ba, “daman Zan taimaka maki da wasu ayyukan ne but tunda an koreni bari nayi tafiya na”
Yana shirin juyawa call ya shugo wayanshi, saurin muting call din yayi ya kai wayar kunnenshi kamar ya amsa yace “hello baby na how are you today?Kinci abunci kuwa?”
Ya fada yana fucewa daga kitchen din, wani maqoqon bakin ciki ne ya turnike salima ta juyo ta bishi da harara “Allah ya isa Wallahi, shegiya koma wacece bazaki taba samunshi ba”
Ta fada ahankali tana goge hawaye kafin ta maida hankalinta wajen girkinta, Aman da ya dan labe a hanyar kitchen din sarai yaji abunda tace don Har darawa saida yayi “zanyi maganin ki ne” ya fada yana dariya shi kadai kamar wani zautacce, wayar hannunshi ce ta sake yin ruri, kallon wayar yayi ganin Amar na kira don shine ya kira dazu ma, saurin dagawa yayi ya kafa wayan a kunnenshi, magana Amar yayi daga chan bangaren kafin ya soma amsawashi “Bari na duba dakin nata, yanxu nake shirin haura wa saman ma”
“Okay thanka, idan kaje Ka kirani zanyi amra magana” Amar ya fada yana kokarin kashe wayar
“Okay” Aman ya amsashi kafin ya wuce sama.
Dakin ammah ya wuce direct, da sallama ya bude kofar,budurwar nurse din dake kula da ammah ce a tsaye hannunta rike da wayanta, kallonshi tayi fiskanta duake da murmushi, shima kallonta yayi, black beauty ce ga ido ga diri saidai gajeriya ce sosai don sai ya zamana dirin nata ya dunkufe, kallonta Aman yayi yana karasowa inda ammah ke kwance tana barci saboda maganin da aka bata wanda kesa barci sosai sannan yana hana jin yunwa sosai, “welcome sir” nurse din ta fada anatse tana kallonshi tana lankwashe murya don tunda ta shugo gidan tasan gidan masu hannu da shuri ne, don haka taci alwashin cusa kanta itama, kallon gefenta yayi fuskanshi duake da murmushi yace “thanks, tasha magani ne?”
“Yes sir, maganin yana aka barci but zata Tashi in 2hours” ta bashi amsa tana kallonshi da manya manyan idanunta kamar na mujiya, juyawa kawai tayi ba tare da yace mata komai ba ya fuce daga dakin ya sauko kasa, dialing number Amar ya fara yi ya shiada mashi tana barci don daman ya kirata ne bai sameta ba don yanason yaji ya lafiyar jikinta sannan yana son ya shaida mata ya futa sai yamma zai dawo “na shiga yanxu tana barci saboda magani data sha, she will be up in the next 2 hours, will call you zuwa lokacin”daga chan bangaren Amar yace “thanks, please let me know idan wani abun ya faru”
“Don’t worry I will watch over” Aman ya bashi amsa kafin ya dauke wayan daga kunnenshi ya wuce dakin shi.
Aman na kashe waya shima ya aje wayarshi ya maida hankalinshi kan tukin da yakeyi anatse, tafiyar minti goma ta maqoshi Nigerian military headquarters, anatse ya shige da motarshi kamar koda yaushe, yana parking ya dauki wayarshi dake kan dashboard ya futo daga motar kafin ya rufe ta ya nufi hanyar shiga cikin headquarters din, bai tsaya ko’ina ba sai office din asad, da sallama ya bude office din yasa kai ya shige ciki.
Asad ne zaune kan kujeran office dinshi, sanye yake da kakin sojoji, saurin miqewa yayi, nan Amar ya tako inda yake ya miqa mashi hannu, musabaha sukayi kafin amar ya zauna, shin zama yayi fuskanshi dauke da murmushi yace “ya jikin hajiya? Allah yasa kaffara ne”
“Alhamdulillah,taji sauqi mun dawo gida ma”
Amar ya bashi amsa yana kokarin duban wayarshi
Kallonshi asad yayi ya tura mashi file din gabanshi yace “Masha Allah Zan shugo yau da daddare, Allah ya bata lafiya”
“Ameen” Amar ya amsa shi a taqaice
Kallon file din yayi kafin ya soma budewa, “oga ga approval ta iso, you have the right to take him zuwa uae,“
Kallon file din Amar yayi saida ya gama karantawa gaba daya ya rufe file din ya tura gaban asad, kallonshi asad tayi tana neman Karin bayani,
“No need for that anymore, Zan barshi anan kuyi mashi hukunci daidai da abunda yayi,”
Da mamaki asad ya dago ya kalleshi don yasan saboda wannan abun ne ya kasa komawa bakin aikin sa acahn uae saboda yana son ya tafi dashi don a hukuntashi achan, “but oga..”
“No but, lieutenant asad, saidai Ina rokonka don Allah karka bani kunya,”
Amar ya fada yana kallonshi fuskanshi a hade tauuu kamar baiso hakan ta kasance ba,
“Yes sir, justice will served”
Asad ya fada yana Sara mashi, fuskanshi a hade ya cigaba “suma ku hukuntasu gaba dayansu, nabar komai a hannunta nasan bazaka bani kunya ba?”
“Insha Allah sir,but oga…why did you suddenly change your mind” asad ya tambaya yana kallonshi don gaba daya he’s confused, yayi mamaki sosai don yasan idan Amar yace zaiyi abu sai yayi babu wanda zai hanashi haka zalika daya nemi abashi kabiru koda military ta hanashi zaiyi using power shi ya karbeshi ta karfi da yaji, saidai yanxu dayaga akasin haka yayi mamaki.
Bai amsashi ba ya mike tare da miqa mashi hannun “thank you so much for your help”
Jinjina kai asad yayi “nine da godiya oga fir trusting me on this case”
Fucewa sukayi atare daga office sun suka wuce criminal room inda aka aje Alhaji kabiru, gaba daya nan bangaren babu wuta kwata kwata don cikin duhu ake ajiye criminals Ana Kiran wajen ma da dark room don azabar da ake gamawa a ciki, asad ne ya bata umarnin aka kunna wutar wajen nan take haske ya hade ko”ina, dakunan ne aqalla zasu kai kusan goma sha biyar Kowanne da manya manyan criminals a ciki gefen su kuma na kananun criminal ne da ake kamawa suma Ana ajiye su, cikin dakin da aka ajiye Alhaji kabiru suka shiga
Kallon inda Alhaji kabiru ke maqure amar yayi, an kulle hannayenshi da karafuna gaba daya ya sauya fasali ya yanqwane ya zama kamar tsumma, ahaka ma in aka barshi ya gama lalacewa gaba daya, takowa Har gabanshi amar yayi ya tsugunna ya kalleshi “yanxu menene ribarka na abubuwan da kayi? Ka cuci kanka kuma muka Ka cucemu”
Dagawa kabiru yayi ya kalleshi dakyar don idanunshi a kumbure suke, yana gane amar ne ya babbake da dariya, kamar mahaukaci “finally!!!! Burina ya cika yanxu, you’re miserable, yanxu saika kashe ni ko?”
Alhaji kabiru ya fada yana dariya, murmushi amar yayi sai yanxu ya gane abunda ammah ta fada mashi jiya, ganin yana murmushi yasa Alhaji kabiru tsagaita dariyar shi ya kafa mashi idanu kamar mahaukaci, kallonshi amar yayi kallon ina tausaya maka “in kashe Ka saboda na zama kamar kai ko? Haka kake so?” Nunfasawa amar yayi ya cigaba “bazan taba zama kamar kai ba, kuma bazan kashe ka ba, Zan barka kasha azabar duniya da hakkin waenda ka salwantar da rayuwarsu, shi kadai ma ya isheka, “
Mikewa Amar yayi bai sake kallonshi ba ya juya ya fuce daga cikin dakin, Alhaji kabiru dai ba haka yaso ba, don haka ya dunga ihu yana surfa ashariya, “ Wallahi saika kashe ku kasheni dan Allah na gaji da wannan masifar na shiga uku”
Kallonshi asad yayi don shima sai alokacin ya gano dalili da yasa amar ya fasa tafiya dashi chan “ay mutuwa ba yanzu zakayita ba sai lokacin Ka yayi bayan munci ubanka”
Asad ya karashe yana Kiran yaranshi don zuci ubansa.
Futowa yayi ya tadda amar a tsaye kafin su wuce dakin mata da aka ajiye lantana, bude dakin asad yayi kafin amar yabi bayanshi, a zaune take a kasa kan cement don ko leda babu a cikin dakin, dago da idanunta da sukayi jaa tayi, da sauri tayi baya Ganin Amar a tsaye, gaba daya furgicewa tayi kamar mahaukaciya don bazata taba mantawa da dukan da yayi mata ba din taji kamshin lahira, kallonta Amar yayi daga nesa, ta rame sosai ta koma kamar wata mai kanjamau saboda rashin abuncin kirki, hawaye ta soma yi jikinta na bari “dan darajar Allah ku yafe min, dan Allah yallabai Wallahi sharrin shaidan ne”
Takowa Inda take Amar yayi idanunshi sunyi jaa, aduniya babu wadda ya tsana kamar lantana dukda yana kokarin dannewa saboda itace ta kusa sanadin rabashi da farin cikin sa wato mahaifiyarsa, “dan Allah yallabai ku yafemin l, hajiya ta yafemin Wallahi sharrin shaidan ne”
“Ba sharrin shaidan bane, da saninki cewa abunda aka baki kiyi ba daidai bane kika karba kikayi, kinci albarkacinta don saboda ita ne kike nunfashi Har yanxu,”
Yana kaiwa nan ya fuce fah dakin asad na biye dashi, ganin yana shirin sauka kasa yasa asad saurin cewa “ oga Dayan doctor fah?”
“No need, Zan wuce gida yanxu saikazo” ya fada yana mikama asad hannu, sallama sukayi kafin ya fuce daga cikin headquarters din ya nufi inda tayi parking motarshi.
Yana shiga motarshi ya sauke nauyayyanijiyar zuciya yana jin zafi aranshi sosai, saidai yanda ya saki komai a hannun asad sai yaji kamar ya sauke wani nauyi ne daya rataya akanshi, ya dauka kusan minti goma a zaune kafin ya kunna motar shi ya fuce daga headquarters din.
Gidan gona…
Futowa malam labaran yayi daga cikin gidan gonar ammah bayan ya gama ban ruwa saboda cikin kwanakin Ana rana sosai,gidan gonar nada girma sosai don babu abunda baya shukawa a ciki Harda kiwon kaji Duk yana yi, fitowa yayi hannunshi rike da buta, sanye yake da triga da wando da yadi fari, ya rame sosai ba kamar yanda yake abaya ba saboda rashin lafiya da yayi ta tsawon sati uku, don hakan ne ma bai samu yaje ya kaima ammah abunda ya fidda na cikin nima wanda ya gyara, don Duk shekara saiya fara kai mata gida idan ta diba sauran sai akai kasuwa idan an sayar sai ya maido mata da kudin dukda kusan Rabin kudin take bashi a matsayin ladan shi wani sa’in ma haka zata ce ya rike gaba daya kudin, ammah wadda yake kira da hajiya ta gama yi mashi komai sosai, don yanda take kyautata mashi, bata sanshi ba bata san asalin shi ba hasalima tsintarshi tayi ta bashi ci ta bashi sha da sutura da yanda ta damka mashi amanar gonarta ba tare da ta waiwayeshi ba hakan na sashi jin Duk duniya babu abunda zata nema a wajen shi da bazai yi mata ba, fatanshi kullum Allah ya kawo ranar da zai saka mata da alkairin datayi mashi.
Zama yayi bakin bishiyar dake gefen gonar yayi ya daura alwala, yana gamawa ya shimfida abun sallah ya tafa kabbara yana idarwa ya zauna yana lazimi yana bin tsirarrun mutane dake yawo,
Mikewa yayi ya tattare abun da yake sallah dashi tare da butarsa ya shige cikin gidan gonar, bin ko’ina ya soma yi da kallo yau sati shi guda kenan rabon da yazo gona sai yau saboda rashin lafiyar da yayi na zazzabi da matsanancin ciwon kai dake hanashi yin komai don Har dishi dishi yake gani idan ya Tashi da safe don haka ya zauna a gida ba tare da ya futa ba Har saida ya danji dama dama.
Gaban buhunhunan shinkafa kusan guda talatin ya tsaya ya bude yana duba su sosai, shinkafar tayi kyau sosai daman ya bari sai ya tara bugu talatin kafin ya kaima hajiya don ta gani, saida ya duba duka kafin ya zaro wayarshi dake cikin aljihun wandonshi, yar Nokia ce karama da ya saya cikin Albashin da ammah ke bashi dukda yana da kudin da zai saya babba hakan baida ya saya ba saboda babu wani amfani, he’s leaving a lowkey life.
Kira ya fara yi ana daga ya kafa wayar a kunnenshi “iruu ya aiki, Ina buqatar akori kura karama wadda zata diba buhu talatin gobe”
Shuru ya danyi yana sauraron shi daga chan kafin yace “yauwa Nagode sosai.
Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya futo daga gonar ya rufe inda yake Adana shi kafar kafin ya wuce bakin titi, tunda ya taaya bakin titin ya dafe kanshi dake Sara mashi sosai, wani irin dishi dishi yake gani, kwata kwata baiyi tunanin tsaywan shi kan titi ke kawo mashi ciwon kai ba sai yanxu, da kyar ya samu ya tsallaka ya tari mai machine don ya kaishi GRA.
Tafiyar minti a shirin ta kawosu high way dake hade da titin taura estate don mashin baya wucewa ta wajen,saukowa yayi ya zaro dari biyar ya bama mai napep, godiya yayi mashi ya fara takowa zuwa eatate din, tafiyar minti goma ta kawoshi taura estate, bai wani sha wahalar shiga ba don an sanshi, yana shugowa ya wuce babban apartment din estate din kai tsaye, da sallama ya karaso inda securities suke dukda ba musulmai bane hakan baisa basa amsawa ba, gaisawa sukayi kafin su bude mashi ya shige ciki, da baba mai gadi yaci karo a compound din gidan yana zuba ma flower ruwa, yana ganinshi labaran yayi saurin karasowa inda yake suka gaisa tare da yaushe gamo.
“Kayi wuyar gani labaran, yau kusan wata guda rabonka da gidan nan” mai gadi ya fada yana zuba ma flower ruwa
“Wallahi baba nayi rashin lafiya ne sosai, baba iya futa ma, sai cikin kwanakin nan na samu zuwa gidan gona” labaran ya fada yana dariya
Kallonshi baba mai gadi yayi ya aje tiyo din ruwa yace “Allah sarki shiyasa, Ay hajiya ma an kwantar da ita a asibiti yau sati biyu kenan, jiya aka sallamesu”
“Subhanallahi Allah kasa kaffara ne ay ban sani ba dana zo”
Dan matsawa baba mai gadi yayi labaran na Ganin haka yasan gulma zaiyi don haka ya dan dara kawai baice mashi komai ba yana sauraron sa, “labaran baka da labarin abunda ya samu hajiya?”
Da mamaki labaran yace “ah ah fatan dai ba wani munmunan abu bane”
“Hmm rayuwar nan dai babu tabbas, Ka janyo mutun Ka sashi a inuwa ya jefa Ka a rana, wannan la’ananniyar matsiyaciyar yarinyar nan ya take da suna yar aikin nan”
Da mamaki labaran yace “lantana?”
“Ee ita fa, la’ananniya aje guba ta dunga zubawa hajiya a abun sha, rana daya Allah ya tonu asirinta matar yallabai ta kamata”
Da mamaki labaran ya zaro ido yana innalillahi, “yaushe akayi hakan” labaran ya tambaye da yana kallonsa
“Ay nake fada maka dalilin da yasa hajiya ta fadi kenan an dauka ma bazata rayu ba” baba mai gadi ya fada yana sauke muryarshi kasa
Zaro idanu labaran yayi yana jin tsanar lantana yace “gaskia wannan matar anyi azzaluma,allah ya saka ma hajiya ya tsareta,”
“Ameen fah, Ay badan matar yallabai ba da tuni saidai gawar hajiya” baba mai gadi ya fada yana jimami
Wani irin kallo labaran yayi mashi najin rashin dadin kalamanshi na karshe, saurin katseshi labaran yayi don yasan baba maigadi Akwai surutu haka zai dunga zance babu kan gado don haka yace “godiya ta tabbata ga Allah, Allah ya tsare wannan ahalin gaba daya”
Tabe baki baba mai gadi yayi yana yau at goro baya son zancen yayi ending don haka yace “Ashe shi yallaban aure yayi achan wata kasar, itace matar tasa data taimaki hajiya ay”
Jinjina kai kawai labaran yayi ba tare da yace komi ba kafin yadan nunfasa yace “yanxu ana iya Ganin hajiya?”
“Haba kai kuwa, jiya fa ta dawo Ka bari sai zuwa jibi saikazo” baba mai gadi ya fada yana daukan tiyo yana Jan ruwa,
“Toh shikenan bari na koma baba, sai zuwa goben” sallama sukayi labaran ya juya,
salima ce ta futo daga ciki main entrance hannunta rike da flasks “baba bismillah ga abunci”
Da sauri baba mai gadi ya ajiye tiyo din ya taho da gudu ya karbi Kumar yace “Nagode karantar hajiya Allah ya Baki miji na gari”
Murmushi kawai tayi mashi ta Mika mashi ta juya zuwa ciki.
Malam labaran dayaji muryarta Har tsaki Yan kanshi yayi saurin tsayawa, kanshi ne ya soma juyawa yana falshing wasu memories da bai gane daga inda suke ba, saurin juyowa yayi don Ganin koma wacece, bin bayanta yayi da kallon don harta shige cikin gida, dafe kanshi yayi dake Sara mashi yayi yana jin kamata rawar tasu tsaye akanshi, saida ya dauki kusan minti biyu a tsaye kafin komai ya kafa mashi ya fuce daga gidan.
Katsina…..
Yau kusan wata biyu kenan hankalin hajiya kareema atashe, ga ciki nan sai girma yake dukda bata laulayi saidai kumburi, kana ganinta kasan ciki gareta don yana da girma sosai, komai yanxu ya tabarbare mata, hanyar samun kudinta Duk ya toshe saboda ciki da yayi mata cikas rabonta da talatu tun bayan dawowarsu daga wajen malami , ta daina daukan wayarta koda ta kirata, ga talauci daya fara masu katutu don yanxu makarantar government dinma ta gagari yaran gaba dayansu, khadi dai bata fasa Sana’a ba don harda saida gwanjo yanzu takeyi, ta zama wata bugaggiyar Yan matan tasha babu mutunci, saboda da dan abunda yake samu suke samu au daura sanwa, yanxu muhammad ya rage tura masu kudi sosai saboda yabar Jordan ya koma France, nan kuma yanda zai tura masu kudi ya zama wahala saboda idan ya tura kudin saiya dauki watanni kafin yazo masu wanda ko yazo ma a banza yake tafiya don daddy ke cinyeshi tass ah harkar chacha daya koma da bariki, don yabar harabar dillanci don babu cigaba kwata kwata,daure baki kam anyi mashi don yaga ciki a jikin Haj kareema saidai baice komai ba game da ciki, haka ta dunga rainin cikin nata yau lafiya gobe jinya khady ce kadai tasan cikin shege ne a jikin mummy, tun tana damuwa itama harta watsar ta daina damun kanta akan abun kunyar uwartata ta cigaba da harkokinta na Sana’a, asma is useless batada wani amfani kwata kwata, kullum tana fama da kafa daya a tsakar gida don ko shafa bata iyayi, akan haka kuwa babu irin zagin da bata sha wajen Haj kareema ita da ko dukansu bata yi ada chan baya balle akaiga zagi.
Zaune suke akan tabarma a tsakar gida gaba dayansu, khady na arranging gwajunan data saro while haj kareema na zaune tana jefa gyada a baki asma na yi mata tausa a kafa, su jalal ma na gefenta suna cin gyada, sallama akayi daga waje, kallon jalal hajiya kareema tayi “kai jeka ga da wa ake sallama”
Mikewa yayi tsaye ya fuce, da gudu ya dawo yana haki, “daddy ne daddy ne”
Mikewa haj kareema tayi ta janyo mayafinta khady ma mikewa tayi don Ganin yau wace irin masifar ya kwaso, futa sukayi gaba daya kafin su tsaya chak a bakin soro, daddy ne kwance jini na bin jikinshi yana wayyo Allah na Zan mutu, hannu aka kareema ta dora tana kallon yanda kafarshi ta karkace ta juya baya, kallon dandazon mutanen dake bakin kofar shugowa tayi da waenda ke gabanshi hankali atashe “na shiga uku meya sameshi yau wace irin masifa ce wannan Ka kwaso mana”
Kallonta mutanen sukayi suna Allah wa dai da halin mata irin wannan, wani daga cikin mazan ne yace “accident yayi a bakin titin, munyi munyi yabari akaishi asibiti shine yace akawo shi gida shine muka kawoshi nan”
Cije yatsa hajiya kareema tayi don yasan dalilin dayasa yace akawo gida saboda baya son fidda kudi, “Toh Ay shikenan kuje ku barshi anan tunda hakan ya tsaba”
Mikew Duk sukayi suka barshi anan kwance, alamajirai biyu manya tasa suka shigo dashi cikin gida suka kwantar shi anan kan tabarma, zagaye shi duka sukayi yaran harma da kareema “Yanxu kai fisabillilahi kayi mana adalci kenan? Kullum cikin masifa muke daga wannan sai wannan ni Wallahi ba gaji”
Yana jin azaba haka ya dunga surfa mata masifa yana kwashe mata albarka, “kinsan Allah kareema ki fita a idona, nine Ruffin asirinki don haka mu taru mu rufama juna asiri kawai”
Yana kaiwa nan ya kwala uwar kara, wani irin murmushin takaici kareema tayi ta kalli khady “ki tashi kije gidan malam mai Gyaran hannu ki rokesa kozaizo ya duba”
Tsaki khady tayi ta kalleta “nifa kinga Wallahi yau ban fita siyarda gwanjon nan ba saboda jin rikeni Saina yi shara da wanke wanke, ko tura wannan mara amfanin taje ta kirashi”
Tana kaiwa nan ta mike ta kwashi kullin gwanjonta ta fuce daga gidan, shuru kareema tayi tana debe mata albarka a zuciya don bata tankwabarta ko musa mata saboda ita kadai tasan sirrin ta, kallon asma kareema tayi tace “Toh mara amfani ay gaskiar ta ne bazaki zauna ba bakya amfanuwa, mike kije gidan malam ki kirawoshi”
Sauke kanta kasa tayi tana hawayen cin mutuncin da ake mata kafin ta zari mayafi ta fuce tana dogara sandarta.
After like 20 mins saigata da mai Gyaran targade, da sallama suka shugo nan kareema ta bashi waje don ya duba daddy, kallon hannunshi yayi da kafarta daya yace “karayar hannu ce sai targade a kafa”
Tun kafin ya kaiga fara wa kareema tace “kuma Nawa za a baka”
“Dubu daya” ya amsata
“Haba malam ina laifin dari uku” kareema ta fada,
Mikewa yayi yace “ku nemi wani yayi maku”
Da sauri daddy yace “kutmaa kareema Allah ya tsine maki yanxu dari biyar ce bazaki iya badawa ba don jaraba ayi min gyara”
Gyaran murya mai Gyaran yayi yace “dubu daya nace ba Dari biyar ba”
Wani irin banzan kallo tayi ma daddy, yana Ganin haka yace “toh ki bada Dari biyar Zan bada Dari biyar nima”
“Ay Wallahi baka isa ba, dari uku nayi niyar bayarwa idan bazaiyi ahaka ba Ka zauna Ka rube ma”
“Ke wai wace irin Mara imani ce” daddy ya fada yana hawayen azaba
“Akwai nada imani sama dakai azzalumi” kareema itama ta maida mashi martani, tsaye a mai Gyaran yayi yana kallon ikon Allah yanda suke zagin juna agaban yayan su, tsaki kawai yayi yace “ni kunga tafiya ta”
Da sauri dady ya tsaidashi “ki bada Dari ikon Zan cika sauran”
Zama mai Gyaran yayi ya gyara mashi hannu da kafa kafin ya daure ko Ina “a dunga gasashi da ruwan zafi kullum sannan Zan dawo jibi na duba hannun” mai Gyaran ya fada yana mikewa
Karema ce ta katse shi “Ay basai Ka dawo ba don sisi na bazan sake bayarwa ba”
Maida kallonta tayi ga dady tana kokarin zaro dari uku daga gashinta datake kullewa tace
“Aikin banza asararre ashe da kudin Ka ajikinka amma bazaka fidda sai na bada a nawa ” ta fada tana kallonshi bayan ta mika ma mai gyara dari uku, saida ya tabbatar ta bada kudin ya zaro nashi daga aljihu da hannu daya kafun ya kalleta yace “Ay babu asarriya kamar ke, keda y kikayi cikin shege da auranki Ay kece asarrariya”
Idanun mummy ne sukayi jaa sosai, batayi expecting hakan ba daga wajen shi, ashe yasan komai, shiko mai Gyaran hannu saida ya taaya ya sake kare masu kallo yaqi fucewa don jin abunda zata ce
“An fada maki ban sani bane? An fada maki bansan ta yanda kike samun kudin da kike kashewa a cikin gidan nan bane? Tun Ranar da kuke maganar da diyarki na san komai? Saboda haka ki kama kanki wallahi”
Tsit kareema tayi bata Kara ce mashi Kala ba karshe ma dai daki ta wuce tana hawayen bakin ciki da dana sani.
Abuja Nigeria…..
Yau kwanan ammah goma da dawowa daga asibiti, taji sauqi sosai don tana takowa Har kasa tana saukowa, Duk bayan kwana biyu Amar ke kaita asibiti Ana mata general checkup, gaba daya yanxu health dinta shine damuwanshi, baya zaman hour guda koda baya gidan bai kirata a waya ba yaji yanayin jikinta, tun tana hanashi Har tazo ta saba ta hakura don gaba daya yanxu ya zama very strict akan komai, Har yau kuwa baiyi gigin kawo masu house help ba, salima da amra keyin komai dukda salima ce karfin aiki sosai don amra na kwance kullum bata da aiki sai barci sai cin abunci kamar kasa, ammah na kura da ita sosai don yanxu tafi damuwa da ita agidan akan kowa, kowa mamakin hakan yake Harda Amar saidai babu wanda ya taba tambayarta dalilin da yasa take damuwa akan amra da bata so much attention dinta gaba daya don Kowa yanaa Ganin hakan ne a matsayin saboda ta bata jininta ne alokacin da yake buqata, bangaren ammah kuwa ita kadai tasan komai haka zalika bata fada ma kowa ba tayi shuru abunta Harda amra ma.
Bangaren Amar yanxu babu laifi yana dan nuna kulawa ma amra don tun bayan da sukayi wannan maganar da ammah yake dan shiga sabgar amra, haka Duk Safiya idan yaje gaisheda ammah in ya fito zai wuce dakin ta don ya duba lafiyar yanda ta tashi, Duk sanda yake zuwa tana barci don haka yana shiga yake futowa baya zama ko na minti daya, ammah na Lura da hakan da yakeyi kullum kuma ta nuna mashi jin dadinta akan hakan sosai.
Tskanin Aman da salima kuwa yanxu sai fada kamar kaji haka zai biye mata suyi ta fada,Akwai ranar da tana shara a kitchen ya shugo, yana shugowa ya zubarda banana daya ci anan kasa inda ta share, ranar tayi masifa kamar menene haka nan ya tsaya yana kallonta ta rike kugu idanunta a rufe tana masifa “kaje Ka kira budurwar kanta share maka ni ba yar aikin ka bace”
Kallon cute face dinta yayi, ba karamin burgeshi takeyi ba da yanda take masifa abun yana kunnashi sosai “Ay baby na bata shara, yar hutu ce shiyasa nake sonta sosai”
Ya fada yana sake kunnota,
Wullata da tsintsiyar tayi ta wuce sama tana kuka. Tana futa kuwa ya tuntsireda dariya abunshi don ya gama gano ta, ko ba a fada mashi ba shi da kanshi ya shaida irin mahaukacin son da take mashi, shima dai daman ba wani giving up da yayi kawai dai yana son ya tabbatar tana sonshi.
Ammah ne ta fito daga part dinta ta wuce dakin amra, a kwance ta taddata wujiga wujiga daure da towel, da sallama ammmah ta shigo dakin “daughter barcin ne Har yanxu kusan sha biyu ko breakfast bakiyi ba”
Da kyar amra ta dan gyara zaman towel dinta gaba dayanta kana ganinta kasan she’s weak don ta dan zabge sosai tace “barka da rana ammah bismillah”
Karasowa Ind a take ammah tayi ta kalleshi tana murmushi “ya jikinki daughter? Hope baby baya baki wahala sosai?”
Da mamaki amra ta dago ta kalleta tana neman Karin bayani, hannunta ammah ta kama duka biyu tana murmushi tace “nasan baki sani ba,shiyasa nayi deciding na fada maki”
Nunfasawa ammah tayi ta sake kallonta ya cigaba da magana “wannan barcin baby ne ke sakaki daughter” ta karashe tana dariya,
da mamaki amra ke kallonta gaba daya kanta ya kulle Bakinta na karkarwa tace “ammah wani baby kuma? Ina baby yake?”
“Listen to me daughter, kin kusa zama uwa, Allah ya amsa addua ta, you’re pregnant” a furgice amra ta daga ta kalli ammah da mamaki, gaba daga kana ganinta kasan she’s shocked, “yes dear you’re pregnant, tun daga ranar da kika shigo gidanan naga hakan a tare dake saidai ban tabbatar ba na barma Allah komai,”
Kasa motsawa amra tayi sai binta take da idanu haka zalika ta kasa cewa komai, riko hannunta ammah ta sakeyi tace “listen to me dear, karkiji komai kinji ko, wannan kyauta ce daga Allah nasan zaki shiga rudu,Akwai wani abu daban fada maki ba acahn baya, tabbas Muhammad baya haihuwa kamar yanda na fada maki abaya don dalilin aurenki da yayi was his last chance of having his own blood line, nasan kunje asibiti ko? Kuma an gwadaki babu, wannan jarabawa ce daga Allah kuma hakan na Kara tabbatar mana da allah baya barci kuma mai yanda yaso ne kuma yana bayarwa a lokacin daya ga dama kuma ya hana a lokacin daya ga dama, zamuje asibiti gobe don muga how far you’ve gone don naga baby bump din namu mai boye wa ne,saidai bana son Muhammad yasan da wannan zancen kinji ko sai mun Kara tabbatarwa kema dole ne yasa na fada maki don ya kamata ki sani.”
Girgiza mata kai amra tayi kamar wata doluwa, ta kasa daina kallon bakin ammah dake furta mata tana da ciki cikinma na ya muhammad don sai yanxu kwakwalwarta ta fara processing.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.