Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 24 of 52
Chapter 128
Arana irin ta yau duniya ta dauka kafar yada labarai da social media,kan video din Alhaji kabiru Taura,ceo na kamfanin taura oils, na miyagun business din da yake gudanarwa a boye, mutanen alhaji kabiru da ma karrabanshi sun shiga tashin hankali sosai don lokaci guda abun yayi blowing a social media ba tare da sun ankare ba, Alhaji kabiru ma abun yazo mashi a bazata saidai a koda yaushe a shirye yake don Duk tashin hankalin da zai shiga yana da mabiya bayanshi, wato Yan siyasa da yake bama maqudan kudaden musamman lokacin campaign don haka yasan ko an kamashi dole za a sakeshi saboda connection na mutane da yake dashi da suke mara mashi baya,cikin qanqanin lokaci maganar arresting din Alhaji kabiru ta gama karade Duk duniya wanda hakan yasa suka Kansu Yan siyasar da suke mara mashi baya suka fara kokari janye hannayensu don babban alamari ne da Duk wanda hannunshi ya shiga cikin alamarin zai iya affecting dinshi shima.
Aman da ya koma daki zuciyarshi na bugawa, hawaye na gangarowa a fuskanshi, saurin janyo remote din tv dake jikin bangon bedroom dinshi yayi ya kunna news, inda timeline din ke nuna cewa “ayau ne aka kama babban attajirin shugaban kamfanin da yayi suna a duniya gaba daya wato TauraCom bisa ga zargin shige da fuce na miyagun kwayoyin da safarar mutane acikin video da ya yadu a duniya a Safiya yau litinin goma ga watan April, acikin video an shaida shi a matsayin shugaban kungiyar daya kafata shekaru a shirin da suka wuce, baya wannan yana hada hannu da manya manyan kasa inda jami’an tsaro da kula da hakkin dan Adam suke buncike akan wannan, Alhaji taura dai dan asalin jihar Adamawa ne inda ya samu muqamin ceo na kamfanin taura yayin da dan uwanshi Alhaji Yunus taura wanda aka sani da Taura ya kafa kamfanin Har ya mutu Alhaji kabiru ya karbi ragamar companying, acikin video an shaida wasu maqudan kudi a maajiyar Alhaji kabiru da yanda suke safarar kwayoyin da production din kwayar”
Gaba daya jikin Aman saki yayi ya kasa motsawa, hawaye da yake hana kanshi yi suna sulalo, samun kanshi yayi da zama bakin gadonsa ya kura ma tv din idanu, nan aka hasko video din daya dauka yana zagaye dakin daddy lokacin daya shiga, dafe kanshi yayi yana kuka yace” ya Allah ka dubeni, I’m I doing the right thin?” Ya tambayi kanshi yana kuka,tunawa da shine ya tona asirin mahaifinshi da kanshi yana mashi ciwo a zuciya saidai hakan shine abun da ya kamata yayi tun farko,tunda ya dafe kanshi yake kuka wiwi kamar karamin yaro.
Yau dai gidan kowa yana cikin tashin hankali, waya kam babu irin wadda ba a ayi masu, kofar gida ya cika makil da reporters,Amar dai tunda ya fito daga dakin ammah yake zarya a cikin nashi dakin, babban tashin hankalin da bai taba shiga ba yau ya shigeshi, ammah ta zubda precious hawayenta akanshi wannan wace irin masifa ce ya fada aranshi, babu abunda yake sai innalillahi a zuciyarshi, gaba daya matsalar da take tunkaro shi musamman kamfanin taura da yanxu image din company din yayi tarninshing ba problem dinshi bane, shi ammah ce damuwarshi, because he can see how shock she is da taji yayi aure, yanxu inaga taji cewa daddy ne ya kashe dada kenan? She will be miserable qilama ta samu heart attack, abun saiya fi mata ciwo sosai saboda itake auren daddy ita ta zauna dashi ba tare da sanin cewa shine makashin mijinta ba.
Da sauri ya girgiza kanshi dake Sara mashi yace “no I can’t let that happen, no matter what bazan bari wannan zancen ya fito ba”
Zama yayi seating room din part dinshi ya dafe kanshi, shima news din ya kunna don bai gane bayanin da asad ya soma yi mashi ba akan abun daya yadu a social media, nan take aka hasko video din komai, ga daddy a zaune Harda alif shuraim da wasu mutane suna yin meeting, next video kuma dakin sirrin shi ne da yake aje kudade da kwayoyin, idanu Amar ya kurama tv din yana karantar environment din da kyau, idanu ya zaro ya furta “what???? Acikin gidan nan”
Bai gama tunanin ba salima tayi knocking kafin ta shigo tana baki tace “ya Muhammad wasu mutane sun…zo”
Kallonta yayi ya miqe ya wuce tabi bayanshi, yana karasowa parlor din yaga dandazon maza kusan su goma a tsaye da suit sun Dora wata rigar akan kayansu da tambarin efcc a jikin, kallonsu yayi fuskanshi a hade ya kallesu daya bayan daya yace “who gave you the permission to enter my house?”
Ogan ciki ne ya karaso gabanshi ya miqa mashi hannu sanin koshi waye yace “we’re very sorry sir but this is strictly official, we have to search the whole house”
Ba tare da wani bata lokaci ba ya jawo wayarshi yayi connecting line dinshi dake da rank dinsa na uae ya kira head of financial crimes wato executive chairman of the efcc, call din na shigowa chairman din Ganin international rank code yayi saurin dagawa cikin respect suka fara magana, baima tsaya introducing kanshi ba don mukamin shi ya wuce yayi introduction nan yace “kana da masaniya akan buncike da ake shirin yi a cikin gidana?” Nan take cikin girmamawa yace “sorry sir, I think it’s a mistake saboda nayi mamakin Ganin call din, ayau buncike guda daya muka tura shine na gidan alhaji kabiru taura…”
Katseshi Amar yayi yace “withdraw the investigation,”
Ba tare da wani jin ba asi ba yace “yes sir”
Ko kallon inda suke Amar baiyi ba ya juya, nan take call suma ya shigo masu.
Harya shiga daki ya fito lokacin har sun fita suna shirin fucewa daga gidan, karasowa Har inda suke yayi ya kira ogan yace “check that part”
Ya fada yana nuna tsohon part din su aman, agurguje suka shiga part din, bin bayansu Amar yayi ya tsaya daga chan gefe, saida sukayi buncike dakunan kaf Har suka zo kan dakin sirri ajiyar, dakyar suka samu suka bude kofar dukda suna da wata na’ura ta scanner da ke detecting abubuwa da suke amfani wajen scanning da bude komai dayake digital, gaba daya suka shiga cikin dakin, masu daukan hotuna sunayin job dinsu masu scanning suma haka suka fara, daya bayan daya saida suka fito da komai saikace masu operation, Amar dai yana tsaye daga baya baice komai ba, ya kyalesu ne suyi nasu job din don yanason duniya ta shaida hakan kafin ya karbe case din, agabanshi suka bude safe dinnan basuyi yinqurin tabawa ba Har ya futa bayan yayi observing wajen shima, sake Kiran head chairman din efcc din yayi, saida suka danyi magana kafin ya kashe,bangaren ma’aikatan kuwa kowa mamakin waye wannan da yake hanasu yin aykinsu daya kamata sukeyi saidai tunda sukaji order ne daga chairman gaba daya yasa basuyi yunkurin taba komai ba saidai sun dauka hotuna da za aje a record, Amar dai abunda baya so saida ya fito fili wato identiti dinshi as the only son of taura kuma general uae armed force, da farko baiso hakan ta faru ba saidaga baya ya gane dole saiya fito ya wanke company mahaifinshi daya gina da guminshi don duniya ta shiada cewa babu hannun company a cikin mugayen ayyukan daddy saima amfani da companying da yake yi don kariyar kansa wanda yaci galaba akan hakan don yanzu duniya kowa ya dauka kan cewa da company Alhaji kabiru yake amfani wajen boye Duk wasu miyagun ayyukan shi, lokaci guda sales din kamfanin yayi kasa, shareholders kowa na neman janye hannu, abubuwa da yawa sun ma Amar yawa, dole haka ya jajirce ya tsaida natsuwarshi waje daya wajen gyara alamuran daya shafi family name dinshi, dukda dole yayi alkawari sai ya gurfanar da daddy no matter what, he will make sure justice has been served, a ranar m5 da soldiers dake karkashin amar suka hau private jet suka taho kasar suma.
Ammah…
Tana shiga toilet ta dafe kirjinta dake mata zafi da nauyi at the same time, wasu irin hawaye tausayin danta ke silalo wa afiskanta,she can’t believe cewa Amar yayi inheriting oligospermia from mahaifinshi, dan she can clearly recall lokacin da suka dauka shekaru basu samu haihuwa ba Har saida suka asibiti a Germany nan aka gano mahaifinshi nada oligospermia, tun samartakar shi,a lokacin har sun cire hope don babu abunda yayi masu saura, sai cikin ikon Allah, Allah ya azurtasu da Muhammad wanda yawanci dada ke kiranshi da kyautar Allah don lokacin da sukaji asibitin an shiada masu bazai taba haihuwa ba don stage din chance din samu ya wuce sai gashi allah ya basu, saurin goge hawayen da takeyi tayi ta dauro alwala ta fito,sallaya ta shimfida ta fara jero salloli tana kai kukanta wajen Allah, harta idar tana kuka tana rokon Allah ya kawo masu sauqi, wani irin tausayi da qaunar dan nata na ninkuwa a zuciyarta, kwata kwata gama manta da alamarin wani daddy gaba daya, tana nan zaune salima ta shigo dakin sanye da hijab, karasowa Har inda ammah yake tayi ta zauna gefenta kamar zatayi kuka tace “ammah jikin ne? Are you feeling sick”
Saurin share hawaye dake kan fiskanta tayi tace “no dear, kunci abunci?”
Hawaye ne ya soma gangarowa a fuskan salima Ganin yanda ammah ta sauya lokaci guda gashi tana Ganin hawaye kwance a fuskanta “ammah dan Allah ki daina kuka, mu roki Allah ya kawo mana sauqi, bana son wani abu ya sameki dan Allah ki bar zubarda hawayenki”
Kauda kai amma tayi gefe tace “dear kije ku daura abuncin dare, nasan bakuci komai ba ko”
Shuru salima tayi don ta gane space take nema don haka ta mike ta nufi kofar,
Amar dake shirin shugowa dakin ya jiyo su suna magana, daman yazo ne don ya duba ko ammah is okay, don ya damu da lafiyarta sosai samun kanshi yayi da kasa bude kofar yana sauraron maganganunsu, ragewa ta gefenshi salima tayi tace “Ina wuni yaya”
“Lafiya” ya amsa ataqaice shima Har wata yar Rama yayi,
Dakyar ya samu ya tattara natsuwarshi cikin kamewa ya shiga dakin, juyowa ammah tayi Ganin shi a tsaye yasa ta kauda idanunta gefe, takowa yayi har Inda take idanunshi sunyi jaa ya karaso Har inda take ya zauna agefen ta kanshi a kasa ya kamo hannunta cikin nashi muryarshi a sanyaye yace “ammah!!!”
Banza tayi dashi ta kauda kanta gefe don ba karamin bata mata rai yayi ba na boye mata da yayi,
“Ammah na please ki diana fushi dani,“ banza ta sake mashi, haka ya dunga rokon ta bata ce qala ba karshe ma miqewa tayi ta koma bakin gado ta zauna, ba tare da ta kalleshi ba tace “ina ce na fada maka karka sake yunqurin explaining komai saika kawo yarinyar da kaje Ka aura ba tare da sani ba? Now get out my room”
Dago da jajayen idanunshi yayi sai a lokacin ya tabbatar ranta ya baci sosai, don bata taba bashi silent treatment ba sai yanxu, dole ya bata space, don haka ya juya ya fuce daga dakin jiki a mace kamar maraya, bin bayanshi tayi da kallo tana tausaya mashi sosai saidai dole ta nuna mashi fushinta akan abunda yayi.
Fucewa yayi gaba daya ma daga gidan don ji yayi gidan yayi mashi fadi sosai, ga kanshi dake blowing saboda abubuwa da sukayi mashi chaaa akai.
Saukowa salima tayi sanye da hijab ta wuce kitchen suka daura abuncin dare ita da lantana, koda suka gama Har wajen karfe takwas babu wanda ya sauko, sanin yanayin da ammah ke ciki yasa ta deba mata a cikin flask ta wuce mata dashi sama, tana zuwa ta taddata akwance tana haki, cikin sauri salima ta aje abuncin a gefe ta karasa inda take, magani ta ta dauko mata ta bata kafin hakin ya lafa, gefen gadon salima ta zauna tace “ammah na please ki kwantar da hankalinki dan Allah”
Murmushi kawai ammah tayi mata tana yaba kyawun haki irin na salima, kallon abunci data aje mata tayi tace “yarinyar kirki yau me aka dafa”
Murmushi salima tayi mata tace “tuwo da miyan ganye da kika fi so Harda fish”
Ahankali ammah tace “thank you dear”
Miqewa salima tayi tace “Bari na barki ki huta ammah na”
Futa tayi ta sauko kasa tana nazari, dakin Amar ta wuce Ganin ko Ina akashe alamun baya nan yasa ta fito, tunanin shiga dakin Aman ta soma yi,ahankali ta Taka Har zuwa dakin ya bude,babu kowa a sitting room din sai tv dake aiki don haka ta wuce hanyar bedroom din tayi knocking, ta dauka kusan minti biyar a tsaye shuru, ganin haka yasa ta dan bude kofar kadan, dakin is dim babu haske sosai sai na inner lights, ganin haka yasa tayi tunanin baya nan don haka ta soma kokarin janyo kofar, karaf kunnenta ya jiyo mata sheshekar kukan shi, hankali a tashe ta shiga dakin a daddare ta kunna light din daki, a zaune ta ganshi ya hada kai da gwiwa yana kuka, gefen shi kwalbar giya ne Ganin bai bude giyar ba yasa tayi hamdala ta karaso inda yake ta tsugunna a gabanshi tace “ya aman!!!”
Dan dago da jajayen idanunshi yayi don Har cikin kwanyar kanshi yajiyo sunan shi data kira for the first time kafin ya sauke kanshi
Ba karamin tausayi ya bata ba don dole yayi kuka, agaban idanunshi akayi arresting mahaifinshi, shuru ne ya ratsa tsakaninsu don batasan wani word zatayi using ba wajen comforting dinshi,
Cikin natsuwa ta Dora hannunta kan kafafunshi tace “ya Aman dan Allah kadaina kuka,Duk abunda kaga ya faru da bawa Toh daga Allah ne”
Dagowa yayi ya kalli kyakyawar fuskarta kafin ya kauda kanshi gefe yace “I hate my life, I hate my miserable life…look”
Taba zuciyar shi yayi still idanunshi nakan nata yace “the pain in here is unbearable, I have no one, no one can understand what I’m going through ina maraicin mahaifiyata”
Fashe wa da kuka itama salima tayi Ganin yanda hawaye ke zarya a fuskanshi Tayi saurin toshe bakinsa tace “haba ya Aman, ya zakace you have no one? You have ammah, ammah loves you so much”
Girgiza kai yayi yana hawaye “not as much as she loves Amar, I’m always a sucker, who disobey her, I’m very disrespectful towards her”
Kallonshi salima tayi idanunta cikin nashi cikin natsuwa ta soma magana “ya Aman you have us, ammah loves you so much Duk da abubuwan da kake yi she still care about you so please Ka daina cewa you’re alone”
Yatsunta biyu ta saka ta soma goge hawayen dake zarya a fuskanshi Adan shagwabe ta kalleshi tace “kuka baya maka kyau wallahi”
Dariya ya danyi ya rike hannunta cikin nashi muryarshi chan kasa yace “sal, I’m willing to change for better, I want to be a good god fearing man, saidai inajin kamar Allah bazai yafe min ba”
Dan dago da fuskanshi tayi da hannunta daya tace “ya Aman, you can change for better, Allah mai jiqan bayin shi ne kuma mai yafiya ne, idan har kayi alkawarin bazaka sake saba mashi ba, I will be by your side during this journey in sha Allah”
Wani irin dadi yaji da maganganun nata,take yaji kamar gaba daya damuwarshi ta wanke tass, miqewa tsaye tayi ta mika mashi hannunta daya alamun ya miqe, yana Ganin haka ya rike hannun nata ya miqe tsaye baiyi wata wata ba ya rungumeta tsaf a jikinshi, salima daga jishi a jikinta babu zato babu tsammani Tayi saurin yin baya, hannunshi daya yasa ya saqalo kwakwasonta, sun dauka kusan minti biyu ta kasa motsawa ko kadan don kamar wata yar tsana haka ta jiya a jikinshi,ganin kamar yama manta da yanayin da suke ciki yasa ta dan tureshi baya tace “ya aman Ka sakeni”
Ahankali ya soma tsame jikinshi daga nata kafin ya dan juya mata baya yace “sorry sal”
Bata ce komi ba ta fuce tana dan smiling, after like 5 mins ta dawo hannunta dauke da plate na abuncin ta aje mashi kan side stool Ganin baya dakin kafin ta fuce daga dakin.
The next day….
Gidan is just like yesterday, kowa yana jimami, ammah dai damuwar Amar ta kwana don saida doctor yazo ya dubata ba tare da sanin kowa ba a gidan Har yazo yayi mata prescribing magunguna ya tafi.
Karfe takwas da rabi salima ta sauko sanye cikin atamfa wadda akayi mata dinkin doguwar Riga, rigar tayi mata kyau sosai, bata daura dankwalin atamfar fa sai hula data saka same color da atamfar,gaba daya jikinta ya gama sanyi da alamarin gidan, musamman ammah, don ta shiga dakinta donmin ta gaisheta, a yanayin data tarar da ita hankalinta ya Tashi sosai, Duk a tunanin ta saboda arresting daddy da akayi ne yasa ta tada hankalinta sosai, da wannan tunanin ta sauko kasan jiki amace, da sallama ya shiga cikin kitchen din Ganin lanata tana moping, jiki a mace ta kalli lantana tace “sannu da aiki ina kwanta anty lantana”
Juyowa lantana tayi ta kalleta tace “lpy Lau alhmdlh kin Tashi ashe?”
Anatse salima ta kalleta tace “eh, yau me zamu dafa?”
Ba tare da ta kalleta ba lantana tace
“Ki tambayo hajiya”
Kauda kai gefe salima tayi tana kokari daukan wuka tace “bata tashiba tukunna”
Irish salima ta kwaso ta fara ferewa while lantana ta soma yankan veggies,cikin mintuna qalilan suka gama, acikin warmers salima ta zuba soyayyan Irish din da egg sauce da plantains kafin ta fara fita dashi zuwa dining, saida ta kai duka warmers din ta jera kan dining kafin ta wuce sama, dakin ammah ta shiga cikin sallama,babu kowa cikin dakin don haka ta dan jinkirta jin alamun saukan ruwa, Gyaran dakin ammah ta soma yi saida ta gyara mata dakin fess ta saka bakoor mai kamshi a burner kafin ta wuce dakinsu dake nan gefe chan don tashin Salim,tana shiga dakin ta wuce kan gadon Ganin yanda yayi dare dare,zama tayi gefenshi ta dan bubbuga kafadunshi tace “Salim kai wake up, wannan barci naka kamar gawa”
Mutsika idanu Salim ya fara kafin ya miqe zaune ya rungumeta, tana Ganin haka itama ta rungumeshi tsam dan normally idan yayi mata hakan to maybe yayi mafarki ne ko ya tuna da adda, tunawa da adda yasa taji wani irin, bata don ta tuna da ita kwata kwata don haka ta dago kanshi tace “go and shower, you’re stinking hmmm” ta fada tana dariyar mugunta, ashagwabe ya miqe ya wuce toilet domin yin wanka, yana shigowa ta miqe ta fuce daga dakin,dakin ammah ta shige anatse tace “assalam alaikum”
Juyowa ammah tayi sanye cikin hijab, fuskanta tayi fayau Har yar Rama tayi murmushi dauke a fuskanta tace “wa alaikum salam my dear Har an Tashi”
Wani irin dadi Salima taji Ganin yanayin ammah, karasowa tayi da dan gudu ta rungume ta tace “ammah….”
Shafa kanta amma tayi tace “yea daughter”
Dan dagowa salima tayi ta kalleta cikin kulawa tashe “are you okay now ammah? Hope babu abunda ke damunki? Ko muje asibiti”
Hannunta ammah taja Har bakin kofa tace “sorry for worrying you dear, yau ke kikayi girki?”
Kallonta salima tayi cikin so da kaunarta har suka sauko kasan tace “yes ammah, kuma nasan yayi dadi”
“Uhmm sai munyi tasting zamusan idan yayi dadi” ammah ta fada tana kallon ta, kujera salima ta jawo mata fuskanta dauke da murmushi tace “ammah sit, bari nayi serving dinki”
Murmushi ammah tayi ta rike hannunta tace “no dear jeki kira yayyunku sai muyi breakfast gaba daya”
Cikin nishadi salima ta juya zuwa dakin aman, da sallama ta shiga cikin daki kai tsaye ba tare da tunanin komai ba, juyowa Aman yayi jin sallamarta, da sauri ta juya baya ganinshi tsaye da towel a kugunshi, agigice tace “ya aman ammah tace….breakfast”
Tana kaiwa nan ta fuce ba tare da Tashi amsan shi ba, murmushi kawai tayi ya cigaba da shiri aranshi yace “silly girl”
Cikin nishadi ya shirya cikin Riga da gajeran wando saida ya feshe jikinshi da turare kafin ya fito, fuskanshi Har wani annuri take saboda gaba daya daga Daren jiya zuwa yau yaji komai ya ragi a zuciyarshi saboda sallan dare daya kwana yana yi.
Karasowa yayi kanshi a kasa Har gaban ammah kafin yadan duqa yace “good morning ammah”
Da mamaki ammah ta dago ta kalleshi cikin fara a da jin dadin sauyawarshi tace “morning son how was your night?”
“Alhamdlh” ya fada ataqaice kafin ya wuce gefe ya zauna,
Daga Dakin Amar salima ta fito, jiki a mace ta karaso dining din kallonta duka sukayi
“Ammah ya Muhammad baya nan”
Kauda kai ammah tayi tace “Zaki zauna kici mu karya”
Karasowa tayi ta soma serving din kowa saida ta zo kan aman nan ta jawo plate dinshi ta zuba mashi dayawa, kallonta yayi ta gefen idanu ahankali murya chan kasa kasa yace “tare zamuci ne?” Da sauri ta waigo ta kalleshi kafin ta kauda kanta gefe tana murmushi tayi banza dashi,tare da tura mashi gabanshi, wani plate din ta jawo don zubama kanta, bata zubama kanta da yawa ba ta dauka plate din don seat din zaman ta na daga gefen ammah, bata kaiga karasawa ba ta saki plate din a kasa tare da dafe kirjinta, kallonta duka sukayi atare, da sauri aman ya miqe yaa kawota gefe don karta Taka ceramic plate din daya fashe din, hankali atashe ammah tace “dear are you okay?”
Dan dago da kanta tayi tace “yea ammah, gabana ne yadan fadi bansan plate dinma ya subce ba”
“Ayya ki kula next time” ammah ta fada tana kallon Salim dake shirin saukowa fuskanshi babu walwala, karasowa yayi ya zauna gefen ammah yana mata murmushi.
Jan hannun salima Aman yayi ya zauna da ita don kamar ta furgice lokaci guda, playe dinshi ya jawo ya aje mata yace “eat” dan dagowa tayi gabanta na faduwa tace “thank you ya aman”
Wani plate din ya jawo ya diba shima yaci.
Nnamdi ezikewa International airport….
Karfe sha biyu daidai flight dinsu amra ya sauka a babban airport din nnmadi azikiwe dake cikin garin abuja, tunda suka shiga cikin jirgi take barci har suka iso, about 7houra flight, ahanakli ta janyo handbag dinta da passport dinta ta fito daga cikin jirgin, tunda ta fito daga jirgin gabanta ke faduwa wanda kwata kwata last time data dawo Nigeria bata ji wannan fargabar ba sai yanxu, runtse idanunta tayi ta sauko daga stairs din jirgin tabi hanyar arrivals, bata tsaya bin wani layi ba don a first class ta zo, don haka tana shigowa airport din tayi clearing komai ta fito harabar airport din ba tare da bata lokaci ba don batada wani baggage’s da zatayi clearing, hankalinta ne ya soma Tashi don bata san Ina zata bi, kallon gefenta tayi Ganin wani security yasa ta tambayeshi wajen chanza cash nan ya Kun mata wani waje cikin airport din inda ake chanza kudi, gaba daya babu wani kudin arziki a jikinta sai 100 dirhams don haka ta wuce wajen don chanza kudin, tana zuwa ta chanza su zuwa naira, gaba daya subu sha biyar ne, jikin Jakarta ta tura kudin kafin ta sake fucewa daga cikin airport din, dube dube ta soma yi don neman taxi, ta dauka kusan minti biyar a tsaye ta rasa taxi din da zata shiga don masu taxi dinma suna ganinta babu wanda yayi mata tayin shiga motar don kana ganinta batayi kamar wadda zata shiga taxi ba, Fendi bag dinta ta janyo ta lalubo wayarta, gaba daya tama manta bata da sim din nigeria don haka ta aje wayar kawai kamar zatayi kuka ga rana dake dan bugun ta,tana nan tsaye wani mutumi yazo ta gabanta yayi mata sallama, Adan tsorace ta amsa
“Hajiya tun dazu nake jiran isowarki”
Shuru ta danyi tana kallonshi don bata gane abunda yake nufi ba, ganin haka ya bude wayarshi ya nuna mata hotonta yace “oga ne yace azo a daukeki”
Tana jin haka ta matse fuska tace “malam inaga kayi mistake ne”
Kallonta ya sakeyi kafin ya dubi wayarshi yace “hajiya kece, ga hoton daya bayar nan”
Azafafe ta dago tace “Wai waye”
Baice mata komi ba ya Danna ma Amar kira, yana dauka ya miqa mata wayar, karba tayi tasa wayan a kunnenta, muryarshi ne ya daki kunnenta “get in the car,”
Shuru ta danyi kafin ta hade rai yace “Ina zai kaini?”
“I hate repeating my self, just get in the car” cire wayar tayi daga kunenta jin yanda yake magana afadace gashi da alamu kamar yana cikin mutane, itama Adan fada ce tace “no babu inda zani,”
Tana kaiwa nan ta katse wayar, ta miqa mutumin tace “malam kaje kawai”
Kallonta sosai mutumin yayi yan yaba kyawun irin nata kafin ya sake wani tunani amar ya kira wayar, yana dagawa yace “don’t let her move, I’m coming now”
“Okay sir” mutumin ya amsa, juyawa tayi zata tafi yace “hajiya dan Allah kiyi hkuri ki tsaya, ba a samun taxi anan, bari na nemo maki ko nayi maki bolt”
Shuru tayi tadan jingina da motar gefe, ranta a hade don tayi alqawarin wannan Karan bazai sake yi mata wayo ba.
Amar dake meeting da shareholders din taura company wayar driver daya tura ya daukota ya shugo wayarshi, yana Ganin call din yasan cewa tayi gardama kenan,daukan wayar yayi ya saurari abunda driver ya fada mashi kafin ya buqaci ya bashi ita, take ranshi ya baci yanda yana mata magana tana maida mashi kai tsaye, kallon shareholders din yayi da suke ta surutai wasu na cewa saidai a saida company din sbd imaging company din ya rigada ya fadi so babu wani hope,kallonsu yayi daya bayan daya miqe ba tare da yace masu komai ba ya fuce suka bishi da idanu,daya daga cikin mutanen ne yace “mu za a mayar Yan iska”
Juyowa Amar yayi don Har yana gab da kofar ya kalli mutumin yace “Nawa ne share dinka a company dinnan?”
Cikin tsagali mutumin yace “5%”
Wani irin banzan kallo Amar yayi mashi cikin isa yace yace “you’re out of this company, Ka tura account details dinka to the finance, kudinka zai shugo account dinka” nan take kowa yayi tsit sanin me hakan ke nufi, hankali atashe mutun ya miqe cikin borin kunya yace “so what, a biya I hakina bazan zauna ba, companies da yawa suna buqatar shareholders kamar ni basu samu ba”
Kallon Amar ya sakeyi ya danyi murmushi ta gefen baki yace “send your accounts zasu tura maka kudin 10% share, company nan baya buqatar mutane irinka” yana kaiwa nan ya fuce, lift ya shiga zuwa kasa, bai tsaya komai ba ya shige cikin g-wag dinshi ya bama motar wuta.
Cikin minti goma ya isa airport, gaban wajen arrival parking space yayi parking motar shi,kafin ya kira driver din, jikin Yan mintuna kadan saiga driver din tana biye a bayanshi don cemata yayi ya samo mata bolt din da yayi mata order ya iso, kallon motar tayi da kyau kafin ta kalli mutumin, bata kawo komai aranta ba don normally a dubai zaka iya requesting mota irin haka saidai kudinka ne zaiji jiki, a matse take data bar wajen don haka ba tare da wani tunani ba ta bude bayan motar ta kalli driver din tace “nagode malam”
Murmushi kawai mutumin yayi ya rufe mata baya motar, yana rufewa Amar ya figi motar suka bar wajen, kanta a kasa tace “malam dan Allah moto park zaka kaini”
Banza yayi da ita saida ta sake maimaita wa,kiii ya Taka burgi da karfi Har tana buge kanta da seat din gaba, dan dagawa tayi karaf idanunta suka sauka akan na Amar ta cikin mirror, hankali atashe ta gwalo idanunta waje, ranshi a mugun bace don yawanci 70% of abunda ke damunshi Duk akanta ne, rai abace babu wasa afuskanshi yace “get out, waye driver ki?”
Ay kamar jira take ta bude bayan motar ta fito waje, zuge glass din gaba yayi babu wasa a fuskanshi ya kalleta yace “get in” banza tayi dashi ta kauda kanta gefen, Ganin ta tsaya gefe guda ta kame, kuma sarai yasan ta jishi ranshi a mugun bace yake da wannan sabon attitude din nata “Aisha!!!!!!”
Ya daka mata tsawa da yasa Tayi saurin kofar gaba ta shige, bata gama rufe kofar bama ya figi motarshi ba tare da ya kalleta ba Har tana dan buge kafarta da motar,
Shuru ne ya biyo ba sai kawai ta fashe mashi da kuka, quluwa dai ya gama quluwa da attitude dinta sosai don kamar ya buge Bakinta haka yake ji, murya asanyaye don gaba daya yama gaji da hayaniya don tunda yazo Nigeria yake hayani yace “shut up”
Kamar wadda ruwa yaci kuwa tayi tsit batace komi ba,gabanta na faduwa, kauda kanta gefe tayi tana kallon yanayin garin daya hade kamar za ayi ruwa lokaci guda, tunda suka shigo cikin layin gabanta ya soma faduwa, anguwan is so peaceful and serene, kallonshi ta danyi kamar baza tayi magana tace “Ina zaka kaini?”
Banza yayi da ita hankalinshi nakan Yukon da yake saida ta sake fashe mashi da kuka tace “Wai meysa kake min haka ne dan Allah?,ni na gaji da wannan rayuwa, Ka sake ni kaki, Nace maka I’m done bana…”
Juyowa yayi ya kura mata jajayen idanunshi rai abace yace “you don’t have to worry your self, yau yau dinnan Zan sakeyi babu kari, having you in my life was a mistake, mara Konya”
Tunda ya fadi haka ta danji wani dadi aranta, chan kasan zuciyanta kuma tana jin wani iri don yana sakinta shikenan ta zama bazawara, saurin kauda zancen kawai tayi har yayi horn a gaban estate din gidan, bude idanu tayi tana kallon tsarin gidan, ya hadu sosai ba kadan ba don kamar ba a Nigeria ba, komai a tsare tun daga bakin gate, shigarda motar yayi cikin estate din, direct ya wuce hanyar babban apartment din daya fita daban daga sauran gidajen estate din, nan ma saida yayi horn aka bude gate din kafin yasa kai da motar, bin ko’ina ta soma yi har inda yayi parking gaban entrance sun gidan, bai kashe motar ba ya juyo ya kalleta yace “sauka kije ciki”
Juyowa tayi tana buqatan jin karin bayani,ganin ko kallon inda yake baiyi ba yasa ta bude motarshi gabanta na faduwa, hannunta maqale da Jakarta ya juyar da motar ya fuce daga apartment din, ahankali ta soma takowa jiki a mace cikin tsoro ta karaso gaban entrance door din, hannunta Har karkarwa yake ta Danna door bell din,saida ta Danna Sau biyu kafin a bude kofar, kallonta lantana tayi daga sama Har kasa Ganin zankwadediyar budurwa yasa Tayi saurin cewa “bismillah!!”
Matsawa tayi ta bata hanya don tasan daga gani qila cikin yan matan aman ne da yake kawowa Duk sanda yaga dama, Har gaban sitting room lanatan ta rakota kafin ta nuna mata wajen zama “bismillah, wurin wa kika zo?”
Shuru amra tayi don gaba daya tsoro ma take ji, rasa abun cewa tayi tayi gum da Bakinta, ganin haka yasa lanatana cewa bari na kawo maki abunsha, baya nan ya fita”kallonta amra tayi don bata gane kan zancen ba lantana kuwa Duk a tunaninta cikin yan matan Aman ne dake biyoshi Har gida, tabe baki tayi ta shiga kitchen, kallonta salima tayi tace “ya Muhammad ne ya dawo?”
“Bashi bane ba, wata baqi wa ce inaga cikin Yan matan yallabai ne”
Juyowa salima tayi ta kalleta yace “waye kenan?”
“Wa kika sani Banda wannan bugaggen dan Alhaji”
Hade rai salima tayi ta kauda kai jin abunda lantana ta fada, kafin ta cigaba da yankan carrot ba tare da ta sake tanka mata ba don kalamanta na karshe basu mata dadi ba
Bude fridge lantana tayi ta dauko ruwa da juice ta saka a tray tace “dan Allah kikai mata Zan wanke rice din naga ruwan ya tafasa”
Fuska Adan sake salima ta aje yankan carrot din ta karba plate din ta juya zuwa parlor, kanta a kasa ta soma takowa Har cikin sitting room ba tare da ta kalli inda bakuwar ke zaune ba don tunda lanata tace mata cikin Yan matan aman ne tazo taji wani irin bacin rai.
Amra ma bata Lura da ita ba don kanta a kasa yake ta takure don taji motsin su a kitchen, gashi bata san gidan waye ya kawotaba bayan wannan ma batasan yanda zatayi introducing kanta ba,aje tray din salima tayi agabanta kafin ta dago, jin alamun faduwar abu yasa salima juyowa ga bakin kofar, salim ne a tsaye daga bakin kofa game handle din hannunshi a fashe a kasa, idanunshi kyam akan su, salima na Ganin haka tace “kai lafiyarka kalau kuwa, kalli yanda Ka fada game handle din” takowa tayi har inda yake ta dauki handle din tana dubawa ko ya fasa.
Amra da taji muryar da bazata taba mantawa da ita ba Har karshen nunfashinta Tayi saurin dagowa karaf idanunta ga sauka akan salim daya kara tsayi sosai don Har ya kusa kamo salima, gefenshi kuwa wata budurwa ce ta juya mata baya don bata Ganin fuskanta, mikewa tayi tsaye zumbur Bakinta na karkarwa haka zalika jikinta ya soma kyarma, salim ma cikin tsoro yake kallonta gashi babu bakin magana, dagowa salima tayi tana mashi fada kan ya fasa, Ganin yanda ya kafa ma parlor idanu babu ko kyaftawa saidai mana ganinshi kaga he’s shocked sosai,juyowa salima ta soma yi don Ganin abunda yake kallo, karaf idanunta ya sauka kan amra babu zato babu tsammani, baya ta soma yi kamar zata fadi Salim ya taro ta, idanunta ne ya soma yaro hawaye, saurin goge idanunta tayi don tabbatar da abunda idanunta ke gane mata, ahanakli kamar mai koyon magana tace “addaaaaa!!!!”
Amra dai tuni ta fara tagal tangal kamar zata fadi don ma Allah ya taimaka da kujera a bayanta, hawaye na bin kuncinta tace “salima????? Salim??? Kune kodai mafarki nake? Kodai ido na ne ke mani gizo? Innalillahi wa inna”
Take ta fashe da kuka, amma dake shirin saukowa dan duban girkin da sukeyi ta taaya kyam itama surprisingly take kallonsu duka, musamman amra data taaya chak kamar wadda aka zare ma ruhi,jikinta na rawa, da gudu salim ya tako Har gaban amra ya tsaya bakinshi na rawa ya kasa magana, hannunta ya kama ya fara shafawa dan tabbatar da idanunshi daidai suke Ganin mashi,a furgice ya koma wajen salima ya jawo hannunta Har gaban amra dake hawayen farin jiki na ganinsu, “adda kece?” Salima ta sake tambayarta hawaye na zubowa a fuskanta, ammah dai kallonsu ta fara yi kamar tv don kana gani su kasan Yan uwa ne, don kamaninsu harya baci sosai, cikin saurin amra tace “salima!!! Salima kune??”
Da sauri ta hada su su duka ta rungumesu tana kuka, wani irin kuka suka fashe dashi at the same time, kankankameta sukayi kamar za a kwace masu ita
“Adda daman kina raye? Shine kika barmu muka shiga qangun rayuwa?, why adda why?,”
Babu abunda amra ke cewa sai “I’m sorry ku yafe min, rashinku yamin babbar illa arayuwa”
Kasa sakinta sukayi suna kuka sosai sun dauka kusan minti goma a haka….
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.