Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 27 of 52
Chapter 131
UPDATE
Uendited…
The next morning…
Amra ce ta fara tashi, agurguce ta shege bathroom dinsu salima ta dauro alwala don gari ya soma yin haske, tana fito ta karaso gaban gado ta kurama su salima idanu tana jin dadin reuninting da qannenta, shagala tayi da kallon su, dukkansu sun chanza sosai sunyi kyau, fatarsu fresh hutu ya zauna ajikinsu, bin daki nasu ta soma yi da kallo, babu abunda babu a cikin dakin na yayan gatan,wani irin dadi ne ya ziyarce ta lokaci guda,acikin ranta babu abunda take sai godiya ga allah daya saka su hannun mutane na gari.
Zama amra tayi gefen gadon ta soma tashin su, ‘’salima…salim.. ku tashi lokacin sallah yayi karmu makara’’ amra ta fada tana kokarin tashin su, salima ce ta fara bude idanunta kafin tayi miqa tace ‘’adda harkin tashi,?’’ murmushi amra tayi mata tace ‘’yanxu nima na tashi, mun Makara sallan asuba’’
Mikewa amra tayi tace ‘’zoki bani sallaya da hijab’’
Gaban closet salima ta bude, juyowa amra tayi ta karema closet din nasu kallo, kaya ne shake aciki tamm, murmushi kawai amra tayi don lokacin da suke hannun uncle basu samu wannan gatan ba kwata kwata.
Mika mata hijab din salima tayi tare da shumfida mata sallaya tace ‘’bari nima nayi alwala, wanchan shemamman nayin barcin nan nasa bazai say a tashi ba’’ tana kaiwa nan ta wuce bathroom, amra kuwa murmushi kawai tayi ta zura hijab din ta tada sallah, tana idarwa salima ta fito daga bathroom, itama shimfida sallaya tayi gefen amra ta zura hijab ta tada kabbara, sun dade sosai azaune suna addu’a, musamman amra data daga hannunta sama tana yima ammah da amar addua’a sosai, hr salima ta mike tana nan zaune tana addua hawaye na yawo akan fusknata, gaban lafiyayyan gadon su salima ta tsaya ta karema salim kallo tare da bugun hannunshi tace ‘’kaiii, tashi da allah, kai wallahi wannan barcin naka saikace na mutuwa’’
Anatse ya bude idanu ya galla mata harra kafin ya miqe, shima bathroom din ya wuce ya dauro alwala kafin ya fito, kusa da amra inda salima ta shimfida nata sallayan ya tsaya ya tada kabbara yana idarwa ya kafama amra idanu, kallonshi itama tayi tace ‘’salima ta takura maka ko?’’ girgiza mata kai yayi ya watsa ma salima harara, tana ganin haka kuwa tace ‘’mara kunya, gwara da bakinka ya tsuke dan allah kadai yasan irin kunyar da zakayi ma mutane’’, dariya amra ta soma yi tana jin dadin ganin kannen nata.
Kallon salima amra tayi tace ‘’yau zakuje school?’’
‘’yes akwai, yau zamu gama mid term test ma, zasu bamu hutun 2 weeks,’’ salima ta fada tana shirin shiga bathroom, bata dade ba ta fito salim ma ya shige bathroom din yayi wanka, agaggauce suka gama shirin school duk akan idanun amra, babu abunda take sai murmushi har suka gama, atare suka fito sukayi mata sallama kafin ta wuce dakin ta, tana shiga daki ttabi lafiyar gado don barcin bai gama sakinta ba.
Ba ita ta farka ba sai wajen karfe goma, agurguje ta shiga bathroom tayi wanka kafin ta fito daure da towel, anatse ta shirya cikin kayan da ammah ta kawo mata, material ne na bubu milk color, kayan sunyi mata kyau don sun haska fuskanta, anaste ta gama saka kayan ta feshe jikinta da turare mai sanyin kamshi kafin ta fuce daga dakin, part din ammah ta fara zuwa, daga sitting ta fara sallama, jin shuru yasa ta fuce daga part din, kasa ta fara sauko wa nan taci karo da lanatana dake shirin haurowa saman, tana ganinta tace ‘’ina kwana anty’’
Kunya amra taji datace mata anty saboda lantana ta girmeta sosai, kanta akasa tace ‘’ina kwana, mun tashi lafiya?’’ ta maida mata fuskanta dauke da murmushi, lanatana ma murmushi tayi mata tana yaba kyawu irin nata kafin tace ‘’daman hajiya ce tace nazo na duba ko kin tashi’’
‘’oh!! Ayya na tashi ina ammah in? amra ta fada tana kallon lanatana,
‘’tana kasa’’ tana kaiwa nan ta sauka kasan amra na biye da ita,
Nuni da hanyar dining lanatana tayi mata tace ‘’tana cikin dining’’
Murmushi amra tayi ta karasa wajen dining din, da sallama ta karasa kafin ta tsaya chak, idanunta ne suka sauka akan shi, lokaci guda suka hada idanu, samun kanta tayi da kasa dauke idanunta akanshi saida ya kauda nash kafin ta sauke nata wani irin kunya na lullubeta, ammah dai murmushi kawai take don taga yanda suka kafe juna da idanu, wani irin dadi takeji aranta sosai, miqewa ammah tayi ta tako har inda take ta janyo hannunta zuwa dining din tace ‘’daughter kin tashi ashe’’
Da sauri amra ta danyi kasa tace ‘’ina kwana ammah’’
Da murmushi ammah ta tarota tace ‘’no bendings dear, how was your night’’ ammah ta fada fuskanta dauke da fara’a, dan dagowa amar yayi ya zuba masu idanu, don ammah na ganinta t aaje serving dinshi da takeyi ta wuce wajen amra, tabe baki kawai yayi yana mamakin yanda ammah ke nuna kulawa agareta sosai, hannunta ammah taja har kusa da seat din ammah kafin ta zaunar da ita
Da sallama aman shima ya shugo dining din ya karaso inda suke zaune yace ‘’good morning’’ ammah ne ta dago fuskanta dauke da murmushin daya qi barin fuskanta don murna tace ‘’morning son how was your night’’
‘’alhamdulillah’’ ya bata amsa kafin ya maida kallonshi kan amra yace ‘’good morning sister inlaw’’ sunkuyar dakai amra tayi don kunya tace ‘’ina kwana’’
Ataqaice ya amsa kafin ya maida kanshi kana mar daya turnpike fuska kamar hadarin kaji, ammah ce ta juya ta kalleshi gannin yanda ya hade rai tace ‘’sorry son, what where yous saying me za’a zuba maka’’
Ba tare da ya dago kanshi ba murya a kasa ayce ‘’anything’’
Kallonshi ammah tayi kafin ta maida dubanta ga amra tace ‘’daughter bismillah, kiyi serving dinshi’’
Dago da idanunshi yayi ya kalli ammah kafin ya maida dubanshi ga amra dake shirin miqewa, wani irin kallo ya watsa mata mai wuyar fassara daya sata tsorasata sosai kafin ta kauda kanta gefe, duk wannan kallon da yake mata akan idanun ammah, batace komai ba ta zuba msu idanu tana karantar relation din tsakanin su da yanda suke treating juna, cikin ranta tace ‘’waiii akwai gyara,’’
Jiki amace amra ta miqe ta soma serving din ammah, saida ta zuba mata kafin ta matso wajen da yake, tunda ta karaso kusa dashi kamshinta ya shige hancinsa, hade rai ya sake ya kauda kanshi gefe hart agama serving dinshi, tana gamawa ta karaso kusa da aman tace ‘’mey za a saka maka?’’ dagowa amar yayi ya bita da idanu da wanda take ma Magana, take ranshi ya baci jin ta tambayi wani chan daban shi dake ta rainashi bata tambayi abunda yake buqata ba,lallai zai gyara mata zama, wani irin tsaki ya buga wanda yasa duk suka juyo suka kafa mashi idanu harda ammah, amra dai wani iri tashi don tasan saboda ita yake wannan abun, aman kuwa girgiza kai kawai yayi yace ‘’thank you sister zanyi serving kaina’’ yana kaiwa nan ya janyo plate ya deba yanda zai isheshi, tana ganin haka ta koma seat dinta ta janyo plate ta deba kadan kafin ta fara ci anatse, duk ta zama so unconfortable gaba daya, ta chan kasa ta soma jin kafarta na kaikayi, da sauri ta zura hannunta kasa don tabo wajen, da sauri amar ya dago jin saurkar hannunta kan kafanshi, kasa hadiye abuncin bakinshi yayi ya kalleta akausashe yace ‘’whats the meaning of that?’’ dagowa duka sukayi daga ammah har aman suka zuba mashi idanu don sanin abunda ya sashi Magana,da sauri amra kuwa ta cire hannun don bata san kan kafanshi hannun nata zai sauka ba, tsaki kawai yayi ya miqe tsaye ya fuce daga dining din, amra dai jikinta har bari ya soma yi don tsoro, yana fuce wa ammah tace ‘’daughte is everything okay?’’ kasa dagowa amra tayi sai girgiza ai da tayi, abuncin ma baifi loma uku kawai ta iya kaiwa bakinta ba har suka gama ta soma kwashe plates din zuwa kitchen, da sallama ta shiga ganin lantana a tsaye, bin kitchen din ta soma yi da idanu, kitchen din ya hadu sosai don babba ne kamar daki, babu abunda babu acikin kitchen din na amfani, lanatana na hangota tayi saurin juyowa tana gyrara zaninta adan fugice tace ‘’laa ay da kin barshi yanxu zan zo na kwashe’’ kallonta amra tayi bata kawo komai aranta ba don haka tace ‘’ba komai zan iya ay’’ tana kawai nan ta karasa gaban sink ta ajiye, kafin ta koma dining din, ammah dake shirin fucewa daga dining din ta kalleta tace ‘’daughter barshi lanatana will take care of that, zo muje sitting room muyi fira’’
Yanda ammah keyi mata kamar ba surukarta ba, janta take kokarin yi sosai a jikinta don kwata kwata bata dauke ta amatsayin surkulle ba saidai ya kamar yanda ta dauki amar a matsayin da.
Sitting room suka zauna ammah ta janyo mata album dake cikin kasan tv unit, karasowa ammah tayi kusa da ita ta zauna tace ‘’zo daughter na nuna maki hotunan tarihi’’ cikin zumudi amra ta matso kusa da ita ta zauna, album din ammah ta bude ta soma mata bayani, kallon cute picture din amar ammah tayi don hoton ne a farkon album din kafin tace ‘’wannan mijinki ne, bazan manta ba ranar da aka dauki hoton nan, awanshi biyu a duniya, he was a very calm baby baya kuka kwata kwata, but idan ya fara kukan yunwa saikinyi mamaki, baya jurar yunwa’’ dariya amra tayi ammahma dariya tayi sosai kafin ta cigaba,’’shiyasa yanxu nake mamakinsa sosai yanda baya son cin abunci yanxu, dear saikin dage sosai fah’’
Kasa dakai amra tay I don taji kunyar maganar ammah, wuce hoton ammh tayi kafin tace ‘’wannan shine mahaifin muhammd, kinga kammanin su ko? Mutane suna cewa wai sunfi kama’’
Dariya amma tayi ta kurama hoton idanu kafin tace ‘’ammah yafi kama dake gaskia’’
Murmusawa ammah tayi ganin ta dan fara sake yi kafin tace ‘’ahh toh nima dai haka nace, ni kwashe min kyawu na ma yayi’’
Dariya sosai amra tayi don shes enjoying the conversation sosai, gashi daman yanxu ta samu experience din laraba na saurin sakewa da mutane, haka ammah ta dunga bude album din tana mata bayani, duk wajen da ya bata dariya kuwa haka zata kyakyace da dariya, suna nan zaune amar ya fito, basu ma ji tsayuwanshi ba a bayansu ya kafa masu idanu, yanda suke hira suna daiya sosai sai abun ya bashi mamaki sosai, daga dan nesa chan yace ‘’ehmm’’
Waigowa sukayi gaba daya su suka zuba mashi idanu, ‘’son harka fito’’ ammah ta fada tana kallonshi, anatse ya soma Magana ‘’eh, ammah please kisa agyara min bedroom dina’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’okay son, kwana biyu nina hana lantana shiga dakin naka saboda youre now a married man’’ ta karashe tana kallonshi tana murmushi, hade rai kawai yayi yace ‘’saina dawo’’
Kafin ya fuce, nunfasawa ammah kafin ta maida dubanta ga amra tace ‘’daughter jiya na tambayeki abu baki bani amsa ba,inason ki cire kunya ki fada min komai kinji’’
Sunkuyar dakai amra tayi don ta tuno da tambayar da ammahn tayi matan akan wani irin zama sukayi ita dashi, bat agama tunanin ba ammah ta kasa ta ta hanyar cewa ‘’daga jiya zuwa yau na fuskanshi yanda kuke treating juna, karki boye min komai ki fada min kinji?’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’tohm’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’kina tsoronshi ne?’’
Kanta a kasa ta dan dago ta kalli amah kafin ta girgiza kai, sake tambayarta ammah tayi tace ‘’kinyi mashi laifi ne achan dubai?’’
Samun kanta tayi da cewa ‘’banyi mashi komai ba, bansan meysa yake jin haushi na koda yaushe’’
Dan murmusawa ammah tayi ganin yarinta baro baro a tattare da amra. Shuru amra tayi tana nazarin sus u duka, na farko abunda ta lura dashi shine amar bai karbi auren ba, don kwata kwata babu alamun ya damu da auren ba, lallai akwai gyara sosai ammah ta fada aranta, don babu wani alamun closeness a tsakanin su, don bazaka ce mata da muji bane kwata kwata.
Kallonta ammah tayi tace ‘’daughter kince min kin karbi aurenku hannu bibiyu ko?’’
Ammah ta tambaya tana kallonta, dan dagowa amra tayi ta girgiza mata kai, ‘’kinsan aure a addini basai na maki bayani ba right?’’
Ammah ta tambaya tana kallonta duk don taji daga bakinta ‘’eh amra ta fada kanta a kasa
‘’now you have to do your duty as a wife kinji,kinga muhammd mutunne mai wuyar fassara, ba kowa zai iya karantar shi ba, karkiga kina da kananun shekaru, you have right on him, karkiji tsoron komai, ki cire tsoronshi aranshi’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’insha allah…’’
Kiran lantana ammah tayi tana zuwa tace ‘’ki nuna ma daughter part din muhammd, daga yau zata dunga kula da chan’’
‘’tohm hajiya’’ lantana ta fada tana kara tabbatar da maganar auren amar da bakuwar don ranar da aka kama daddy har yace amar yayi aure ba tare da sanin kowa ba tana wajen saidai sanin cewa ba huruminta bane yasa bata cusa kai ba, kallon amra ammah tayi kafin ta miqe tace ‘’daughter bari na wuce sama, lantana zata nuna maki part dinshi’’
Murmushi amra tayi mata tace ‘’tohm ahuta lafiya’’
Sama ammah ta wuce kafin lantana ta mata jagoraan part din amar,suna zuwa bakin kofa salima tace ‘’nan ne part dinshi, akwai duk wani abun buqata wajen gyara dakin a ciki’’
Girgiza mata kai amra tayi tace ‘’okay’’
Bude kofar part din amra tayi, kafin ta shige ciki, bin parlor nashi tayi da kallo, parlor ne maid an girma babu abunda babu a ciki, set of kujeru farare da suka sha pillows sai center table a tsakiyan parlor da furr carpet shima fari tarr sosai, koina fessfess babu datti ko kadan, idanunta ne ya sauka akan katon frames da aka jea a bango guda uku, wanda duk hotunanshi ne da kayan sojoji sai kuma daya daya dauka da ammah da dada sun sakashi a tsayi suna murmushi, kallon hoton amra tayi tana mamakin fuskanshi a hoton, yayi wani masifar kyau sosai, gashi yayi dariya wanda zatace wannan ne first time data ganshi yayi dariya guineuly, ba karamin tafiya da ita yayi ba don wani irin kyau yayi mata a hoton, ta dauka kusan awa kusan minti biyar tana kallon frames din kafin ta wuce cikin bedroom din, tana shiga sanyi ac ya daketa hade da kamshin turaren shi dake tafiya da ita, lumshe idanunta tayi sosai ta karema dakin kallo, ko’’ina neat babu kazanta ko kadan, kallon bed dinshi tayi da white beddings dinshi da suka dan yamutse saboda kwanciya, babu komai a dakin daya yi datti sai gadon kawai dake buqatan gyara don ko beddings dinma babu datti ko kadan, karasowa tayi gaban gadon kafin ta waiga ganin wani sako daga gefe wanda a alamu nan ne hanyar toilet, takawa tayi har wajen sakon, walk in closet ne babba a ajen sai kofa daga gefe wanda da alamu kofar toilet ne, bin kayan cikin glass clost din tayi, don akwai lightings sosai, komai tsaf neat and clean an jerasu, fadar yawan kayan wajen ma bata lokaci ne harda section din takalma da agogon sa da neck ties harda manyan kaya, murmushi kawai tayi chan kasan maqoshi tace ‘’mr perfect guy’’
Dube kofar toilet tayi shima babban toilet ne sosai kamar daki, very clean an neat, futowa tayi daga toilet din ta wuce bedroom ta fara gyara mashi, tana gamawa ta wuce toilet din ta wanke mashi fess fess kafin ta futo, tana fitowa taci aro da lantana da burner, mika mata lanatana tayi ‘’sorry na manta ban baki burner ba, na saka turaren already a ciki’
Karba amra tayi tace ‘’thank you’’
Komawa tayi ta jona burner din kafin ta fito daga dakin, sama ta wuce, tana shiga ta karasa gefen bedside sai a lokacin ta tuna da wayarta dake a kashe tun bayan data shiga flight ta kashe, nan take tunanin haifa yazo mata, ita da Nadine, yanxu haka suna chan hankalinsu atashe suna tunanin ta, saurin zuge handbag din tayi ta zaro wayar kafin ta zauna gefen gado, kunna wayar ta fara yi kafin ta danyi jimm, tunawa da bata da sim card din Nigeria,jikinta ne yadanyi sanyi, ganin bata da wani option yasa ta jawo charger wayar ta jonata a jikin bedside socket da wayar.
Karfe uku su salima suka dawo daga school, lokacin da suka shugo babu kowa a sitting room don haka suka wuce sama, part din ammah suka fara shiga suka gaisheta kafin su wuce na amra cikin zumudi, a kwance suka taddata, da sauri salima ta karasa bakin gadon tace ‘’adda, kina zaune ke kadai’’’, miqewa amra tayi zaune da sauri salim ya karaso kusa da ita ya zauna fukanshi dauke da murmushi, tana ganin haka tace ‘’duk dadin hutun da aka baku ne ya saka murna haka’’ ta fada tana kallon salim, bude handabag dinshi yayi ya zaro mata result report dinshi na mid term, tana gani ta karba tace ‘’ wow, kayi kokari’’
Dariya yayi kafin ya miqe yayi ma salima gwalo ya fuce, hararashi tayi tace ‘’mara kunya’’
Yana fucewa salima ta kalleta tace ‘’adda, nayi missing dinki’’ ta fada tana rungume amra, dariya amra tayi itama ta rungumeta tace ‘’ay gani nan saikin gaji da gani na ma’’
Mikewa salima tayi tace ‘’bari nayi wanka na chanza kaya saimu sauka kasa tare’’
‘’okay’amra ta amsa ta harta fuce daga cikin bedroom din.
Kasa suka sauka zuwa parlor, salima ta kunna masu tv, salim dake gefensu yana cin abunci amra ta kalleshi tace ‘’acici ashe har yanxu kana nan da halin naka’’ amra ta fada tana mashi dariya, murmushi kawai yayi mata ganin salima ta dawo itama hannunta dauke da plate na abunci, zama sukayi anan sitting room suna hira suna kallon tv, amra nayima salima tsifar gashi, suna nan zaune ammah ta sauko tana binsu da idanu tana murmushi ganin irin bond din dake tsakanin su, wani irin dadi taji ganin su ahaka, suna hangota kuwa salima tace ‘’barka da hutawa ammah’’
Amra ma kallonta tayi tace ‘’ina wuni ammah’’
Salim dai miqewa yayi ya rungume ammah kafin taja hannunshi suka karaso gaban sitting room din, kallonsu tayi tace ‘’daughter sun cikaki da surutu ko?’’
Dariya duk sukayi salima tace ‘’chapp ammah kodai ta cikamu da surutu ba’’
Dungure mata kai amra tayi tace ‘’kundai sani surutu, nida bana surutu’’
Dariya duk sukayi ammah ta kallesu tace ‘’ay gwara ayi tsifa,daman inata tunanin wannan weekend mu fita saloon’’
Da sauri salima ta dago tace ‘’ammah wannan weakend din banda kitso wallahi zafi kaina kemin idan akayi’’
Kallonta amma tayi tace ‘’haba dear wannan gashi naki saida kitso ay, ga cika ga yawa’’
Tabe baki salima tayi ashagwabe tace ‘’dama irin gashin adda nake dashi wallahi,’’
Dungure mata kai amra tayi tac eke har kina fatan irin gashi na idan ya nannade dinnan wahala yake baki’’
Turo baki salima tayi tace ‘’allah ki godema allah kina a coily gashi, ba kamar nawa ba’’
Dariya ammah tayi ganin conversation din nasu gwanin burgiwa da yanda suke,
Suna nan zaune aman ya shugo lokacin an gama tsifar, salim na kwance gefen amma yana barcin shi daya saba, salima kuwa na zaune a kasa, amraa na gefen single seater sun kafama tv idanu,suna kallon wani series da salima ta dunga zuzutawa akan yana da dadi, sallamar da akayi ne ya dawo dasu daga kallon da sukeyi, anatse aman ya shigo sitting room din idanunshi akan salima, wadda itama ta dauke idanunta kan tv ta maida kanshi, ammah ce ta ankare dasu tace ‘’ehmmm’’ da sauri suka ankare amra kam bata ma lura da kallon da suke ma juna ba sai gyran murya da ammah tayi, wani irin kunya ne ya lullube salima tayi saurin kauda kanta, ‘son har an dawo, sannu da dawowa ya aiki’’
‘’alahamdullahi ‘’ya fada yaana murmushi, kallonshi amr tayi tace ‘’ina wuni’’
Lafiya lau sister inlaw’’ ya fada yana kannema salima idanu wanda akan idanun amra, kallon inda yake ma winking tayi ganin salima na murmushi, mamaki ne karara a fuskanta ganin yanda salima ke blushing, maida idanunta tayi kanshi tana mamakin yanda shi baya kama da ammah da ya amar don kammanin shi daban ne, duk a tunaninta qanin amar ne, sauke kanta tayi tana mamakin irin kallon da yake ma salima wanda tana gani tasan kallon so ne, jin ana kiran sallah yasa ammah cewa ‘’ oh har lokacin sallah yayi allah kasa muyi karshe mai kyau ’’
Da ameen duk suka amsa kafin ammah ta tashi salim ta wuce sama, amra ma mikewa tayi tana kallon salima dake blushing idanunta kan tv tace ‘’small madam ay saiki hakura da kallon haka ko’’, tana kaiwa nan ta wuce sama ta barta zaune aman na zaune shima ya kafeta da idanu, yana ganin duk sun wuce sama ya matso kusa da salima yace ‘’baby sal babu welcome’’
Dan waigowa tayi ta mashi wani fari tace ‘’sorry my yaya, ina jin kunyar ammah ne’’
Dariya yayi yace ‘’ay taga yanda kike blushing’’
Zaro idanu salima tayi tace ‘’toh ay kaine, dana ganka sai naji sanyi araina bana sanin lokacin da nake smiling din ma’’
Dariya yayi sosai harda kyakyatawa yace ‘’sister inlaw ma ta ganki’’
Zaro idanu salima tayi tace ‘’da gaske adda ta ganni’’ jin tace adda yace ‘’yes ta ganki, taga yanda kike kallona cikin so’’
Tabe baki salima tayi ta miqe tace ‘’ni ba sonka nake ba’’ wata yar bazawarar dariya yayi yace ‘’don’t deceive your self baby na’’ yana kaiwa nan ya miqe shima yayi pecking kumatunta ya wucewarshi ya barta tsaye kamar sanda,da sauri ta wuce sama tana blushing, tana karsawa cikin bedroom dinsu ta tadda amra zaune kan sallaya, wucewa cikin bathroom tayi ta dauro alwala kafin ta shimfida sallya kusa da amra, tana idarwa amra ta kalleta, kamar bazata ce komai bat ace ‘’meysa kike blushing dazu’’
Dan fusgewa salima tayi kamar bata gane inda ta dosa ba tace ‘’blushing kuma? Mey zai sani blushing’’ dan bugu amra takai mata tace ‘’soyayya kike ko’’
Dariya salima tayi tace ‘’kai adda ni babu wani soyayya’’
‘’soyayya kuke mana, naga yanda kike kallonshi shima yana kallonki, wai shi waye ne?kanin ya muhammd ne?’’ amra ta tambayeta tana kallonta, dariya salima tayi,don shes enjoying the conversation tace ‘’chapp yayan ya muhammd ne saidai shi bad an ammah bane, babanshi shine qanin baban ya amar and shi ne mijin ammah ayanxu kafin a….’’ nan take salima ta bata labarin gidan da yanda suka zo suka samesu, ba karamin tausayin aman amra taji ba jin yanda mahaifinshi ya kasance dukda ita kanta salima bata san dalilin kamashi da akayi ba, ‘’back to our discussion, fada min gaskia soyayya kukeyi’’
Dan dukar dakai salima tayi daga zaune ta dan tabe baki tace ‘’yace dai yana sona, ni kuma ban amince ba’’
Idanu amra ta kura mata kafin tace ‘’ke kina sonshi ne’’ shuru salima tayi ta kasa cewa komais aida amra tadan yi dariya tace ‘’ na wa wo, my sister is in love, oh salima har kin girma’’ mikewa salima tayi tana turo baki ta koma baking ado ta jawo book din zanen ta tace ‘’ni adda bance maki ina sonshi ba fa’’
Wani irin dadi amra taji ya ziyarce ta,ba tareda tace mata komai ba ta dawo inda take zaune tace ‘’small madam, bazan hanaki abunda zuciyarki ke so ba, I will always support you, idan har kina sonshi’’
Shuru salima tayi kafin ta dan dago tace ‘’bazaki min fad aba?’’ grigiza mata kai amra tayi ‘’meysa zanyi fada, youre an adult now, kuma kin kusa gama school, duk abunda kike raayi shi nake raayi’’
Rungumeta salima tayi gam hawaye nabin kuncinta tanajin kamar mam ice agabnta, itama amra rungumeta tayi gam a jikinta.
Kasa suka sauko atare zuwa kitchen, nan suka tadda lanatana tana tuka tuwo,da murmushi amra ta karba mata tace ‘’kawo na taya ki’’ mika mata lantana tayi haka suka karasa girkin atare suna hira gwanin burgewa, salima harda cocnut drink tayi, karshe dai lantana barinsu tayi suka karasa miyar ogu daya sha nama da ganda da kifi, sun agamawa salima ta fidda warmers kamar yanda suka saba ita da ammah, anatse suka fara fidda komai zuwa dining, ammah dake saukowa t hangosu suna shirin komawa kitchen, kallonsu tayi yanda suke dariya suna hira, anatse ta karasa cikin kitchen din tace ‘’my daughter wannan kamshi haka ay saiku sakamu jin yunwar dole’’ dariya salima tayi ta karaso kusa da ita tace ‘’wallahi ammah nay au idan kikayi tasting miyar adda sai kunnenki ya kusa cirewa, shes a best cook’’
Kallon inda amra ke tsaye amma tayi tana murmushi hannnunta dauke da warmer da suka zuba miya,
‘’ashe daughter ce tayi mana wannan delica din, shiyasa naji kamshin gidan ya chanza gaba day aba kamar ba da ba’’
Dan tabe baki salima tayi cikin shagwaban tace ‘’ámmah ni nawa girkin bashi da dadi ne?’’
‘haba dear kema naki yana da dadi sosai’’
Dariya duk sukayi gaba daya kafin su fito atare, zama amma tayi a sitting room don sai kowa ya hadu ake cin abunci, su salima kuwa sama suka koma, amra ma dakinta ta wuce tayi wanka ta dauro alwala, sallah ta fara yi tana idarwa ta sauya kaya zuwa marasa nauyi cikin wanda ammah ta kawo mata, doguwar rigace saidai ba bubu bace ba, rigar tabi jikinta ta zauna mata dam, gaban dresser ta karasa ta fesa turare kafin ta futo zuwa dakinsu salima.
Ammah na zaune amar ya shigo gidan da sallama, kallonshi tayi fuskanta dauke da murmushi tace ‘’welcom son’’
Wani irin dadi yaji ganin mood dinta, anatse ya tako har inda take yace ‘’thanks ammah na barka da dare, seems like youre in a good mood’’ dariya ta danyi tace ‘’ba dole ba son, yau zanci girkin matar ka, oh ashe inada rabon ganin wannan rana’’
Take yadan hade rai ya tsuke fuska, ammah na ganin haka tace ‘’go and freshen up’’
Mikewa yayi ya wuce bedroom dinshi,yana shiga ya aje wayanshi ya rage kayan jikinshi ya wuce bathroom, wanka yayi atsanake don already yayi sallah kafin ya shugo, agurguje y agama shirinsa cikin gajeran wando da riga na under armor, rigar ta kamashi sosai ta fidda asalin kyawun surarshi, anyways shi komai ma kyau yake mashi lols..yana gama saka kaya ya feshe jikinshi da turaren shi kafin ya fito, ganin ammah a zaune ya karasa inda take ya zauna, hira suka farayi, nan aman ya fito, kallonshi amar yayi yace ‘’ka dawo ashe ya office din?hope komai na tafiya daidai,’’ aman yayi mamakin Magana da yayi mashi haka me tsayi don haka yace ‘’alhamdulillah, komai yana tafiya daidai,’’ murmushi amar yayi mashi nan suka cigaba da hira harda aman din, sun saka ammah a tsakiya.
Anatse su salima suka fara saukowa, salima nag aba amra na bayanta tana zolayarta, ‘’mara kunya, kema wai kin girma ko, ko kin manta lokacin danake tare maki fada a islamiyya’’ amra ta fada tana dariya, dan juyowa salima tayi ta kalleta tace ‘’kai adda, ammah dai kinsan na fiki baki nima ranar nan ay na tare maki fada’’
Tana kaiwa nan ta ruga a guje, amra ma binta tayi da dan gudu ta kamo hannunta tace ‘’ni kika tare ma fada yaushe, ay wallahi saikin fada min’’ ta fada tana kai mata dundu, ‘’wayyooo bayana allah zan fada ma ammah kin bugeni’’ wani dundun takai mata har suka sauko kasan,
Tunda suka sauko ammah da aman suka bisu da idanu suna dariya,amar dai kallo daya ya masu ya kauda kanshi gefe saidai yana jin duk conversation din nasu, kallonsu ammah tayi tace ‘’yau fada sako da sakuwa akeyi kenan’’ sai alokacin suka lura da mutanen dake parlor, da sauri amra ta kame kanta salima ma haka kafin su wuce sitting room, amra dai ji tayi kamar karta karasa parlor, salima na karasowa ta zaune akan carpet kusa da kafan ammah inda aman ke zaune tace ‘’barka da dare ammah, ina wuni ya muhammd, ina wuni ya…yaa’’
Ta fada tana kallon aman da shima kallonta yake, ammah ce kawai ta amsata kafin ta waiga wajen amra data kasa daga kafafunta, saida ammah tace ‘’karaso mana daughter zo ki zauna’’ ta fada tana mata da nuni da gefen amar,tunawa da zancen ammah yasa ta karaso anatse ta zauna gefen da yake zaune a kasa, sai ya zamana kowacce tana gefen nata zabin, ammah dai dadin da takeji baya musaltuwa, amar dai tunda yaga haka ya hakimce a bayan kujera ya janyo wayarshi,
Sauke kanta kasa tayi tace ‘’’barka da dare ammah, ina wuni ya aman’’
‘’barka daughter ya gajiyan girki’’
‘’babu gajiya’’ amra ta amsa mata kanta a kasa
Aman ma kallonta yayi y ace ‘’sister inlaw kin cika mana gida da kamshi’’
Dan murmusawa amra tayi batace komai ba idanunta akan yatsun kafar amar dake gabanta da huge tigh dinshi, ahankali ta dan dago tace ‘’ina wuni ya Muhammad ya aiki?’’
Ba tare da ya kalli inda take ba cikin kamewa yace ‘’lafiya’’
kallon hanyar kitchen ammah tayi ta kira lanatana tana zuwa tace ‘’ki kwaso abuncin anan zamuci’’
Juyawa lanatana tayi ta dauko food mat ta shimfida kafin ta kwaso abunci, da plates duk ta jera a gabansu, nan Salim shima ya sauko hannunshi rike da game pad ya karaso ya zauna.
Ammah ce ta katse shurun tace ‘’ku sauko, daughters ayi serving’’
Saukowa duka sukayi banda amar daya hakimce, salima ce ta fara zubama ammah kafin tace ‘’yaya mey za a saka maka’’
Ta fada tana kallon amar, aman kuwa harara ya galla mata ya tareta da cewa ‘’samin malmala biyu’’ ya fada kamar shi ta tambaya
gwalo idanu tayi tace ‘’ya mu…’’
Dan mintsininta amra tayi alamun tayi shuru, aman kuwa ya danji haushi saidai baya iya fushi da ita don haka yace ‘’malmala uku zaki zuba’’ dariya suka soma yi mashi su duka harda ammah kafin salima tace ‘’kai yaya ina zaka kai har malmala uku’’ galla mata harara yayi itako ta sauke kanta kasa tana murmushi ta soma zuba mashi, amra na ganin haka ta dan dago ta kalli amar daya hade girar sama da kasa ya tsuke fuska, tace ‘’yaya mai zan saka maka’’
Bazan yayi da ita ammah na ganin haka tadan hade rai tace ‘’son bakaji ana Magana bane’’
Dan dagowa yayi yace ‘’anything’’
Wani irin rashin dadi amra taji amma hakan baisa taji haushi ba ta soma zuba mashi tuwon, dan bowl ta dauka ta saka mashi miya tare da namomi sosai tana gamawa tace ‘’bismillah’’
Dan kallonta yayi kafin ya kauda kanshi gefe ya sauko gefen ammah ya zauna, tana ganin haka ta tura mashi abuncin a gabanshi.
Anatse suke cin abunci suna yar hira, wani irin dadi ammah keji don kana ganinsu kaga complet happy family, addaua ta somayi aranta allah yasa su dauwama ahaka, fatanta yanxu allah yasa abunda take zargi tsakanin aman da salima ya tabbata, don babu wanda zai kallesu yace basa son junansu, yanxu damuwarta shine amar da yanda yake nuna halin ko in kula da amra, don kamar ma ya amince ne saboda ammah ta hana ya saketa, tasan shi da kafiya son haka ta daura damarar dagewa akanshi.
Suna gama cin abunci lanatana ta kwashe komai,nan aman yayi ma salim connecting game a tv, wasa wasa sai gasu su duka suna game ammah na daga gefe tana kallonsu, amar dai ya hakimce yana latsa waya baice, jifa jifa yake dagowa yana kallon yanda salim da salima da aman ne buga game din suna dariya, amra dai kamar mara jini a jika itama tana daga gefe tana kallonsu, idan anyi abun dariya tayi dariya, ammah ma tana daga gefe tana dariya yanda salima ta hade rai saboda an kusa cireta a cikin game din, ‘’yaya wallahi ojoro kakeyi allah’’ ta fada taa kallon aman dake bugunta a game din da gangan, gwalo yayi mata yace ‘’kedai baki iya ba kawai’’
Hade rai tayi sosai tace ‘’nama hakura kawai’’
Amra ce ta sako bakinta tace ‘’why would you give up?, give it all, keep trying zaki iya kema’’
Juyowa amar yayi ya kafa mata idanu jin zazzagar muryarta da yanda tayi maganar, tadan lafe jikin kujera kamar ba ita tayi Magana ba tana lumshe idanu kamar mai jin barci, shagala yayi da kallonta da yanda take Magana, nan take wani abu ya darsu a zuciyarshi ahankali ya soma Magana yanda babu wanda zaiji dagashi sai ita yace ‘’how can ingrateful person like you have the courage of advicing someone ‘’
Sarai taji abunda ya fada wanda ya sata runtse idanunta ta sauke kanta kasa,kauda kanshi yayi shima ya maida kallonshi kan ammah yace ‘’zanje na kwanta, zan fita da wuri gobe, im preparing saboda zan koma’’
Atare duk suka dago suna kallonshi harda ammah datayi mamakin shi, mikewa yayi yace ‘’good night ammah’’
Yana kaiwa nan ya wuce dakinshi cikin kamewa, kallon amra ammah tayi don ta lura dasu tun lokacin da amra tayi ma salima Magana da lokacin daya kafe amra da idanu har zuwa time din da ya yi mata Magana wanda bata jiba, mikewa itama tayi ta wuce part dinshi, tana zuwa sitting room tayi knocking bedroom dinshi, amar dake zaune bakin gado yana jin knocking din yace ‘’yes come in’’
Shugowa ammah tayi ta karaso har bakin gadonshi ta zauna, sauke kanshi kasa yayi don yasa tunda ya ganta har cikin bedroom dinshi to babbar Magana ce,
Anatse ta sauke ajiyar zuciya tace ‘’muhammd,’’
Dan dagowa yayi ya kalleta kafin ya suake kanshi kasa yace ‘’yes ammah’’
‘’muhammad yarinyar nan tana da wani aybu ne da kake qin wannan aure?’’ ta tambayeshi tana kallonshi, dan shuru yayi kafin yace ‘’no ammah..but’’
Katse shi tayi da cewa ‘’ya isa answer da nake nema ka bani,its looks like nika auroma ita ko?, yaushe ka daina jin maganata muhammd?, why cant you accept the marriage now bayan achan baya kaika saka kanka ba wani ya saka ba?’’
Kasa dagowa yayi haka zalika ranshi duk y agama dagulewa yace ‘’ammah, bana sonta, shes too youndg for me, ni bana buqatar mace itama tunda amfaninta ya kare batada wani amfan….’’
‘’shut up…’’ ammah ta fada da dan karfi
‘’muhammad are you sure kana da hankali kuwa?, kasan mace kuwa? To bari kaji na fada maka, ba a yima mace haka, baa raina mace, mata suna da daraja, nima uwarka mace ce ni, ohh wato ta gama maka amfani ko? Bata da amfani yanxu saboda bata dauka cikinka ba?, ka bani mamaki son, toh wallahi bari kaji, babu saki arayuwarka kama cire wannan, wallahi ko bayan raina ka saki yarinyar nan bazan yafe maka ba, kayi imaging ace yanxu kana da kanwa hakan ta faru da ita, yarinya karama zaka maidata bazawara ? saboda ta gama maka amfani?, kayi saurin janye wannan aranka don wallahi youll regret this word muhammd’’ tana kaiwa nan ta miqe ta fuce daga dakin gaba daya.
Washe gari weekends aman ne ya fita dasu gaba daya zuwa saloon, salima na gaban mota ammah da amra na zaune abaya, gaban wani hadadden saloon and spa suka tsaya, ciki suka shiga su uku, ammah nag aba suna biye da ita abaya, dayake ammah special customer ce suna zuwa aka basu wani bangare na manyan baki, anaste matar dake running wajen tazo gaban ammah cikin girmamawa ta gaisheta, bayan sun gaisa ammah tace ‘’ ga daughters dina nan, agyara mun su,’’
Nuni da amra ammah tayi tace ‘’ita special package zakuyi mata’’
Murmushi matar tayi kafin ta fuce, cikin yan mintuna ta dawo tare da workers dinta, gaban su suka jere wasu product na gyaran gashi don daman haka sukeyi sai sun ajiye sunyi comparing gashin client da mayukan da zasuyi masu amfani dashi base on category din gashin kowa, Kallon amra matar tayi tace ‘’maam zamuga gashin naku don mu san wani product zamuyi maku amfani dashi ko’’
Girgiza kai amra tayi tare da cire veil din doguwar rigar bubun dake jikinta, tana cirewa ta zare ribom din kanta ta warware gashin, da idanu ammah ta bita da kallo , aranta tana jin dadin amar ya samu mata wadda ta hada komai,aggauce aka gyara ma amra kai harda pedicure da medicure mutanen wajen sai santin gashin ta sukeyi kamar ba gashin yar Nigeria ba,nan salima tace ‘’were half Nigerian half maroccan’’
Da mamaki ammah ke kallonsu tace ‘’shiyasa gashin ya fita daban da namu nan ba’’
Sun dauka kusan awa uku kafin aka gama, suna fitowa aman na karasowa, don yaje gida, tare ya dawo da salim a gaba, salima na ganin haka ta gallama salim harara, tana jin kunyar ammah gashi babu damar tace mashi ya koma baya don haka ta hakura ta koma baya, direct mall ammah ta umarci aman ya kaisu, daman haka yake so saboda yanason yadan samu ya kebe da yar masoyiyarshi.
Suna zuwa mall ammah tace ‘’daughter ki dauka duka baunda zaki buqata,’’
Kallon salima ammah ta sakeyi tace ‘’ki rakata ku zagaya, bari na shiga wani shop anan baya’’
Ammah na wucewa salima ta janyo trolly, amra dai binta tayi abaya tana kallon ikon allah, haka suka dunga zagaye saida salima ta debo mata duk abunda tasan zata buqata daga kan brass panties, mayukan shafa, turare, babu abunda bata say aba, sauna gamawa ammah ma na shigowa, aman da salim a gefen ta hannunsu niki niki da ledoji da suke shake da manya manyan atamfofi da laces masu shegen tsada, duban abubuwan da suka sayo ammah tayi, ganin sun debo kala uku uku yasa ta kallesu tace ‘’ya haka, kuje ku karo dozen, naga babu night gowns ma,muje na taya ku zaba’’
Ammah is such a classy woman, wadda ilimi ya zauna ajikinta sosai, da kanta ta dunga kwaso ma amra nighties hadaddu da panties da bras, salima na gefe tana taya, babu abunda bata dauko ma amra ba, trolly dinma daya cika saida suka karo wasu, sun dade sosai cikin shop din kafin su gama danan, ammah da card dinta tayi payment din komai kafin su fito su shiga wani shop din,amra dai is speechless ga kunyar ammah data gama dabaibaye ta don koda suka tsaya wajen sayen nighties kasa dago kai tayi ta kalli kayan,har sammah tayi payment suka fito tana mamakin kudin kayan,ganin amra nasan abayasa yasa ammah ta jasu suka shiga wani jamine abaya shop, nan ma ammah ce ta kwaso mata kusan kala sha biyu masu shegen tsada da kyau kafin su fito atare.
Basu suka dawo gida ba sai wajen karfe biyar na yamma agajiya, sama duk suka wuce gaba dayan su, saida sukayi sallah suka huta kafin su fito zuwa kitchen, yauma amra ce ta dora abuncin, salima da lanatana suna daga gefe suna tayata yanke yanke har suka gama.
The next day basu tashi da wuri ba saboda gajiyar fitan jiya, sai wajen karfe sha biyu su salima suka fito,a kasa suka tadda ammah da baquwar datayi, har kasa suka duka suka gaisheta tare da baquwarta kafin su wuce dining, anatse suka fara cin abunci har suka gama, suna gamawa ammah ta kira amra, salima kuma ta tsaya kwashe kwanukan da suka bata, karaso amra tayi cikin natsuwa ta zauna gefen kujera, kallon baquwar ammah tayi tace ‘’ta chadi, gata nan, inason ayi mata wankan amarya package wanda kika taba yimin kwanaki’’
Dariya matar tayi tace ‘’wai hajiya da alamu kinji dadin wankan amaryar nan, ay kuwa zaiyi mata kyau sosai idan akayi mata,na kwana daya ma ya isa, nan gaba idan lokacin yayi sai ayi na sati guda a jere’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’toh shiknan,bari na kira lantana ta taimaka maki ku kwaso kayan amfanin naki ko’’
Kallon amra amma tayi tace ‘’dughter kuje dakinki zatayi maki bayani’’
Kai akasa amra tace toh ammah
Sama suka wuce lantana biye dasu har zuwa dakin, matar tace ‘’an taaba maki waxing?’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’éh’’
Murmushi matar tayi mata tace ‘’okay baru mu fara’’
Anatse matar ta fiddo da kayayyakin gyran jiki wanda take kawowa daga chad, daukan wata robar madara matar tayi ta wuce bathroom ta tara ruwa a bthtub ta zuba ruwan a ciki tare da cika bath din, tana fitowa tace ‘’ki rage kayan jikinki zamuyi waxing yanxu,
Anatse matar ta fara mata gyaran jikin, abubuwan tada shafama amra ajiki kamar za asauya mata fata, ta dirjeta tass, kafin ta jata har bath tube,ciki ta umarceta data shiga, ruwan wani irin kamshi yake fidda wa kamar ruwan madara, ta dauka kusan rabin awa aciki kafin ta bata wani hadin sabulu tace ‘’kiyi wanka kizo’’
Futa tayi ta bar amra donta tayi wanka, tunda amra ta soma goga salulun nan tajii fatarta kamar audiga, luwai luwai gwanin burgewa, ga wani irin sheki da fatar keyi, tana gamawa ta nado towel ta fito, kallonta matar tayi ta sake kallonta tace ‘’masha allah, kinada kyau’’
Murmushi amra tayi mata don wannan kalma ta saba jinta sosai,wasu hadin ruwan madaran ta bata tace ‘’shafa wannan’’ karba amra tayi ta shafa, kafin matar ta sake bata wani nasha, babu gardama amra ta karba tana mamakin wannnan abubuwan da ammah tasa ayi mata,tasan kayan mata ne saidai bata kawo komai aranta ba don haka ta zauna tana kallon ikon allah ana gamawa matar ta kunna turaren wuta akan kujeran zama ta saka mata tare da luluba mata, saida ta kasu sosai kafin tamtar ta bata wasu turarruka na chad tace ‘’ki dunga sahsafawa da safe inkin tsahi sai kuma da ddare idan zaki shiga turaka, wanna special hadi ne daga chad, zaiji dadinki sosai’’ amra bata kawo komai aranta bat ace ‘’nagode’’
Kallon wata roba dake dauke da waist beads amra tayi cikin zumudi tace ‘’wannan sayar dashi kikeyi?’’ dariya matar tayi tace ‘’kina son irinsu ne’’
Nan amra tace ‘’eh’’ ganin haka yasa matar ta fiddo mata su tace ‘’zabi wanda kike so’’ nan amra ta zabi haddade, matar na gani tace ‘’wannan ma yana da kyau, yana daukan hankali’’ godiya amra tayi mata sosai.
Sun dade sosai don sun dauka kusan awa uku, har lalle chad saida tayi mata a damtsen hannayenta, wanda sukayi mata kua sosai, matar na gamawa ammah ta shigo daki, kallon amra data sauya lokaci guda tayi tace ‘’masha allah daughter, youre beautiful’’
Sunkuyar dakai amra tayi cikin jin kunya, godiya sosai ammah tayi ma matar harda kyautar zoben gold, ba karamin dadi kuwa matar taji ba sosai kafin tayi masu sallama.
Matar na fita ammah ta zauna gefen amra ta rike hannunta tace ‘’haka ya kamata ki dunga yi koda yaushe kinji, koda bana nan ki zama mace mai gyaran jikinta’’
Kai a kasa amra tace ‘’insha allah ammah’’
‘’daughter, yau inason ki koma part din mijinki’’ dammm amra taji gabanta ya fadi bata dago ba haka zalka batace komai ba saida ammah tace ‘’karki ji tsoro kinji ko’’…girgiza mata kai kawia amra tayi kafin ammah ta fuce.
Ammah na fuce ta mike tsaye gabanta na bugu, part dinshi?, nan take taji tsoronshi ya durar mata, harga allah shes not ready to face him saidai bazata iya cema ammah bazatayi abunda tace ba don haka jikinta yayi sanyi…………..
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.