Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 44 of 52
Chapter 147
Update
Unedited page
Suna tafiya Aman ya kalli salima dake tsaye dan nesa dashi kadan tana daukan hotuna ita da kawayen ta, daya daga cikin kawayen nata ne ta dan tabota tace “kaii sal wannan yayan naki Akwai kyau Wallahi, dama…”
“Shut up Malama, shi Zan aura fah kike maganan banzan nan”
Aman dake gefensu yana jinta ya soma dariya, yanda tayi maganan is so funny, ahanakli ya karasa inda take fuskanshi dauke da murmushi, tun kafin ya karaso inda yake ma Tayi saurin tunkararsa tana Galla mashi harara, “muje chan mu zauna, waennan Yan sa’idon har sun fara kai maka hari”
Tana kaiwa nan ta ja hannunshi suka wuce wajen chairs don garden sun school.
Suna zama ya zaro jakar da yake boyewa a bayanshi ya Mika mata, kallon hannunshi tayi kafin ta karba jakar tana murmushi, “yaya ashe zaka bani gift”
“Yea love Nina isa naqi bada gift, yaufa is one of our special day, now open it”
Ahankali ta soma bude jakar, tana budewa taga kwali anyi amshi wrapping, dagowa tayi ta dan kalleshi, kifta mata idanu yayi don haka ta maida idanunta kan kwalin, ahankali ta soma bude wrap din, tana budewa taga kwalin waya iPhone 14 pro max sabuwa dal, cikin sauri ta dago da idanunta ta kalleshi kafin Tayi saurin rungumeshi, “laaa iphone, iPhone 14 yaya thank you so so much love”
Ba karamin dadi yaji ba yanda ta nuna farin cikinta sosai “thank you yaya Allah ya azurtaka ya saka da alkairi I love you so much” ta karashe tana kai mashi peck a kumatu, tsabar murna batama san tayi ba.
Saida ta dago ta maida idanu ta kan kwali tana jujuyawa, shiko kasa motsawa yayi,fadin irin farin cikin da yake ciki bata lokaci ne, finally ta furta mashi abida he has been longing for tun last time data fada,“ baby say it again”
Dagowa ta kifta mashi idanu alamu bata gane ba, “you mean I love you?” Ta tambayeshi saurin runtse idanunshi yayi ya sumbaci hannunta “I love you too so so much, I can’t wait to make you my wife, zaki haifa jin babies ko?”
Saurin rufe idanunta tayi kafin ta mike ta shige hall, shiko da idanu ya bita yana godiya ga Allah don sai yanxu yasan rayuwarshi ta sauya ba kamar ta da ba.
Bangaren Amar tunda suka fito daga school dinsu salima yake kakin calls,Cikin Yan mintuna qalilan suka iso gidan,yana parking bai ma tsaya sun gama fitowa daga motar ba ya wuce cikin gidan yana receiving emergency call.
Atare ammah da amra da Salim suka fito daga cikin motar, ammah ce ma ta tsaya ta rufe mashi motar ta zare key din motar kafin su wuce cikin gidan, suna shiga amra ta wuce sama zuwa dakinta don agajiye take, ammah ma part dinta ta wuce ta sauya kaya.
Bayan ya shiga dakinsa, a gaggauce ya zaro traveling bag dinshi da laptop dinshi saida ya gama shirya Duk wani abu dayasan zai buqata kafin ya wuce bathroom ya sakarma kanshi ruwan dumi, ya dan dade tsaye a tsakiyan shower ruwa na sauka akanshi, yanda ya dafe gaban shower nitch da hannayenshi babu abunda yake tunani sai amra, haka kawai ya tsinci kanshi da tunanin ta wannan lokaci kafin ya fito daga bathroom din waist dinshi nade da towel, a gaggauce ya fara shirinsa,cikin Yan mintuna qalilan ya gama shirin nasa kafin ya janyo baggage dinshi da laptop bag dinshi ya fuce daga dakin.
Koda ya fito sitting room saida na kalleshi na sake kallonshi, fadin irin kyau da yayi ma bata lokaci ne, kakin sa ne a jikinsa da five stars dinshi maqale a gefen right shoulder dinshi, kafanshi kuwa sanye yake da boot dinshi same color da kakin sa, cikin kamewa yake tafiya harya karaso sitting room, ganin babu kowa yasa ya ajiye baggage da laptop bag dinshi anan sitting room din kafin ya wuce sama cikin natsuwa,
Da sallama ya bude dakin ammah, a zaune ya taddata tana latsa waya, idanunta sanye da farin glass na karfin idanu, karaso yayi inda take zaune bakin gado ya dan duka ya kamo hannunta cikin nashi, fuskanshi gwanin nan tausayi ya soma magana “ammah na, Har yanxu kina fushi dani ko? Ina rokon ki yafemin, I’m so sorry bazan iya tafiya da fushinki akaina ba,”
Da farko daya durkuso gabanta kauda kanta tayi don Har lokacin fushi take dashi kuka tana son ta nuna mashi kuskuren sa sosai,kallonshi ammah tayi nan take taji wani irin tausayin da kaunar sa a zuciyarta, Muhammad is her world shine komai nata, shine farin cikinta don shi kadai Allah ya bata, bazata so ya tafi da tunanin tana fushi dashi ba.
Hannunta daya ta sanya ta dago da fuskanshi kafin ta sauke mashi murmushi, shafa sajenshi ta danyi kafin ta soma magana “Allah ubangiji ya kiyaye ya tsareka ya dawo mana dakai lafiya, bakayi min komai ba, na yafe maka”
Wani irin dadi ne yaji ya ziyarce shi, cikin sauri ya mike ya rungumeta tsam kamar za a kwace mashi ita, “thank you ammah na, I love so so much, please take care of your self, da yaran”
Dan bubuga bayanshi ammah tayi har lokacin fuskanta dauke da murmushi “Insha Allah, take care of your self as well,”
“Insha Allah ammah na” ya fada yana sakinta fuskanshi dauke da murmushin jin dadi, “yaushe zaka dawo?” Ammah ta sake tambayarshi
Nunfasawa yayi kafin ya dan dago ya kalleta, “Wallahi I don’t know ammah, amma Muna gamawa Zan dawo”
“Toh Allah ya kiyaye ya tsareka”
“Ameen ya rabb bye ammah” yana kaiwa nan yayi mata sallama, idanunshi Har sun danyi jaa sosai saboda kewarta daya farayi, yana futa daga dakin ammah ta zauna bakin gado gabanta na faduwa kamar this is the last time da zata ganshi, ahankali hawaye ya soma sauka akan fuskanta, wannan hawaye ya kasance kamar routine a wajen Duk sanda yazo niger idan zai koma saita zuba da hawaye, hankalinta yafi kwanciya idan tana tare da dashi koda yaushe saidai bazata hanashi yin abunda yake so ba, abu daya ne yanxu take tunawa saitaji sanyi aranta.
Amar na futowa daga dakin ammah ya dan tsaya a corridor tsakanin dakunan nan saman,kasa daga kafafunshi yayi idanunshi na kan kofar dakin ta, da kyar ya tattara kuzarinshi ya soma takowa zuwa dakin nata, dan tsayawa yayi jim kamar mai wani tunani kafin ya danyi knocking, amra dake zaune, tun bayan futowanta daga toilet bayan tayi wanka ta kasa motsawa saboda wani azababban ciwon kai daya kawo mata ziyara a tsakiyan kanta sai bayanta daya dan rike saboda tsayuwan da sukayi wajen daukar hoton graduation din Salima, tana nan zauna ta dafe kanta ko kaya bata saka ba tana zaune da pink towel dinta don Har lokacin bata son saka kaya saboda yana takura ta, knocking din da akayi ne yasa ta dan dago kanta don Duk a tunaninta ammah ne “yea come in” ta fada ahankali muryanta chan kasa tana kokarin rike dafe bayanta da hannu daya tana “washh”
Ahanakli ya bude kofar ya shugo anatse kafin ya rufe kofar ya tsaya yana binta da idanu.
Jin shuru yasa ta dan dago da kanta, nan idanunta ya sauka a nashi, sai kamshinsa daya bade dakin gaba daya lokaci guda,
Saurin kauda kanta tayi gefe ta mike tsaye ta nufi hanyar bathroom yana Ganin haka yayi saurin takowa zuwa inda take, cikin sauri ya kama hannunta “Aisha!!!”
Chak ta tsaya ta kasa motsawa don gab take da shigewa bathroom din gashi ya rike hannunta, ahanakli ya Kara matsawa inda take ya tsaya a bayanta “Aisha please!!!”
Gabanta ne ya dan fadi yanda yake mata magana da yanda ya kira suna ta calming kamar bashi ba sai taji kamar wani Amar dinne a tsaye a bayanta bashi general din data sani ba, kokarin kwace hannunta ta fara yi, yana Ganin haka ya rike hannun nata sosai kafin ya dan juyo da juyo da ita tana fuskantarshi, kasa dagowa tayi ta kalleshi kanta a kasa, fuskanta a hade babu annuri ko kadan, “Aisha please look up” ya fada in a calming tone, Har voice dinshi na cracking
Samun kanta tayi da dagowa ta kafe shi da idanu Har lokacin bata sakin fuskanta ba,
Bakinsa ya soma budewa yana son ya fada mata abu ya kasa, haka ya dunga mimicking ya gaza Tara courage dinshi, ganin haka yasa Tayi saurin kauda idanunta akanshi “Zan shiga bathroom” tana kaiwa nan ta zame hannunta daga nashi ta juya mashi baya ta nufi hanyar bathroom
Taku daya yayi ya cinmmata tare da rungumeta, ya hade bayanta da kirjinshi, Lumshe idanu yayi yana jin wani irin natsuwa na zuwan mashi, itako tunda ya rungumeta taji ranta ya baci sosai, kokarin kwacewa ta soma yi ya qi bata damar haka don kwakwaran rungume yayi mata, ahankali ya sauke kanshi daidai kafadarta, ahanakli yake sauke mata nunfashi anan wajen kafin ya matso da fuskanshi daidai wuyanta, yana sauke fuskanshi a wajen ta lankwasar da wuyanta,
Daidai bakinshi yayi wajen kunnenta kafin ya soma magana ahankali kamar mai rada “I’m sorry ayeeeshhh….I’m sorry for what I did the other time”
Yana kaiwa nan ya saketa tare da juyo da ita sautin fuskanshi ya saqalo hannunshi a kugunta kafin ya matso da fuskanshi saurin fuskanta nunafshinsu na gugan na juna, “I…I….”
Saurin katseshi tayi ta hanyar yin baya ta nunfashinta na fita sama sama, hawaye na gangarowa daga fuskanta, amaimakon kalamanshi su mata dadi sai suka bakanta mata zuciya, ya kaita maqura sosai inda take jin bata kaunar ganinshi ko kadan saboda abunda yaso yi kata shekaran jiyan, she begged him, but bai damu ba he’s selfish kanshi kawai ya sani, bayan abunda ya mata sai Yanxu kuma yazo yace sorry? Me yake nufi kenan? Ta hakura daga just saying sorry,
Saurin girgiza kanta tayi tana tunanin tana hawaye “no no,“
Ta dunga furtawa a zuciyarta, ya kaita bango sosai bazata iyaba, sorry dinshi is nothing to her compare to abunda ya mata all this while, Yan a Ganin haka ya soma matsawa inda take “stop please karka matso inda nake”
Chak ya tsaya jiki shi ya mutu sosai, harga Allah so yake yayi reconciling da ita Kodan saboda ammah don yasan tabbas bata huce dashi ba, dazun ma ta kulashi ne saboda zai tafi badan haka ba bazai ga murmushi ta bama.
“Why?” Ya tambayeta kai tsaye
Dan dago da jajayen idanunta tayi ta mashi kallo daya kafin ta sauke idanun nata ta kauda kanta gefe, yana Ganin haka yasa ya juya ba tare da yace mata komai ba,saida yazo daidai kofar futa daga dakin ya dan jinkirta “take care of your self and your siblings”
Yan kaiwa nan ya fuce daga cikin dakin, yana futa ta shige bathroom sai hawaye,haka nan ta dunga kuka ita kanta bata san dalilin kukan nata ba, ta dade sosai a cikin bathroom din tana hawaye kafin ta wanke fuskanta ta dawo cikin bedroom din.
Amar kuwa yana futa daga dakin amra ya sauko kasa, kai tsaye ya nufi Inda yabar jakanshi.
Saida ya karaso ma ya Lura da ammah dake zaune a sitting room din, sanye take da hijab tundaga sama Har kasa, kallonshi tayi fuskanta dauke da murmushi kafin ta mike ta tako Har Ind a yake ta karba laptop bag dinshi, yana Ganin haka ya rike hannunta suka fuce zuwa inda driver yayi parking, suna karasowa shida ammah ya saki hannunta ya dan rungumeta yace “bye ammah take care of your self for me pls”
“I will son, kaima Ka kula da kanka, don’t forget to call us idan kaje chan”
“ I will Insha Allah ammah na” yana kaiwa nan ya shige bayan motar driver yaja motar suka fuce daga gidan,
Jiki a mace ammah ta juya ta koma cikin gidan tana mai yi mashi addauar kariya da tsari.
Wunin ranar dai ammah da amra sunyi shi ne cikin rashin jin dadi,kowannen su na zaune a daki, karshe dai amra barci tayi wanda ya fusge ta batare da ta sani ba, while ammah kuwa tunda ta zauna kan sallaya bata mike ba tun bayan sallan dhuru datayi.
Amar kuwa suna fita da motar airport suka wuce direct, suna isa airport management suka shaida zuwanshi don haka takanas Aka saka mutun daya daga cikin officials yayi masu jagora zuwa wajen jets departures, bai fito daga cikin motarshi ba Har suka iso babban cikin da jet ke sauka, daga dan nesa jirgin driver yayi parking, ahankali amar ya futo anatse hannunshi cikin wandon kakin sa,kwarjinin sa ya gama cika wajen gaba daya, ahankali ya soma takowa cikin kamewa while wasu officials biyu na rike da baggage dinshi da laptop bag dinshi, direct gaban jirgin uae armed force ya tsaya, saida ya dan tsaya ya suke nauyayyiyar ajiyar zuciya kafin yayi addua yana gama wa fara hawa matattakalar jirgin, tundaga kan steps din jirgin yaranshi dake tsaye sunsha uniform dinsu kowannen hannunsa rike da manya manyan bindigu kamar zasuje yaqi, fuskokinsu a rufe da wani black helmet, sai inner bullet prove Riga da Kowannen su ya daura akan kakin, haka suka dunga Sara mashi Har ya shige cikin jirgin kafin su bi bayanshi, su kansu zasu kai akalla su talatin, wani special waje aka bashi nan ya zauna ya daura kafa daya kan daya, cikin sauri m5 y a karaso inda yake shi baima saka helmet dinba don Ana Ganin fuskanshi, “welcoming sir” m5 ya fada yana kamewa, kallonshi Amar yyi kafin yace “drop the formalities, seat”
Zama m5 yayi ind a yake mashi nuni nan opposite kujeran da yake zaune, nan ya buqaci da yayi mashi bayani akan operation din da komai daya kamata ya sani.
Cikin Yan mintuna qalilan jirgin su ya daga sararin samaniya…..
Adawo lpy sir general😭
Yau kwana biyu kenan bayan tafiyar Amar, gidan yayi shuru kamar an dauke masu annurin gidan, ammah kullum tana daki, abu daya ke fiddata daga daki shine dubo amra don sanin yanda ta Tashi, aranar da Amar ya tafi wahee gari ya chanza masu securities na gidan gaba daya, Banda baba mai gadi, sannan ya sanya asad yayi mashi inspecting wani babban company da suke kawo helps daga wata kasar, nan yasa asad yayi mashi kwakwaran buncike akansu kafin a kawosu gidan, ya mata ne guda biyu akalla zasukai shekaru talatin talatin, dukkansu Yan phillipines ne, bai yarda ya kawo Yan Nigeria ba,
Salima ne tayi kokarin training dinsu akan ayyukan gidan don kusan a tare suke yin komai, daya danganci abunci don basu iya abuncin mu na nan Nigeria ba,yanxu ayyukan gidan Duk ya koma hannunsu.
Yau sati guda kenan da graduation din salima, don haka amra tayi deciding fada mata komai, don daman dalilin dayasa ta ki fada mata was saboda Karta fada ma Aman don idan ta fada mashi zai ita fada ma Amar shiyasa ta qi fada mata a wanchan lokacin, yanxu kuwa inka ga yanda suke ma junansu kamar zasu cinye juna.
Zaune take akan gado hankali kwance tana chan mango da salima ta yanka mata,ayanxu bata da wata damuwa kwata kwata, don daman Amar ne ke bata ciwon kai, tun bayan tafiyarshi kuwa hankalinta ya dan kwanta, bata wani damu ba da alamarinshi don harta ma manta dashi saboda basu da wani memories mai dadi da zaisa ta tuna dashi saidai sometimes yakan dan fado mata arai.
Sallama salima tayi hannunta rike da wani plate din ta sake yanko mata saboda ta buqaci hakan, tana zuwa gaban gadon ta ajiye mata akan gado tana turo baki don hira take da habibinta a sabuwar wayar daya bata don yaje office shine ammah ta tado akan tazo ta yanka ma amra mango.
“Gashi nan, dan Allah abarni na huta haka nan, Wallahi adda lamarinki gaba yakeyi kamar wata mai ciki” tana kaiwa nan ta juya, amra kuwa mai zatayi Banda dariya din haka Tayi saurin katseta “ba laifina bane laifin danki ne ay”
Da sauri salima ta juyo don bata gane inda ta Dosa ba, shafa belly bump dinta tayi kafin ta maida kallonta kan salima “kingani ba? Shike damunki bani ba”
Da sauri salima ta tako inda take idanunta a waje Bakinta ya kasa rufuwa ta shafa cikin amra “adda baby ne anan?”
Salima ta fada tana shafa cikin amra, girgiza mata kai amra tayi tace “yes… “
Fadin irin farin cikin da salima ta shiga a wannan rana bata lokaci ne don kowa saida ya shaida hakan a gidan, she’s so happy Harda dan kukanta.
After one months….
A kwana a Tashi babu wuya yau wata guda kenan da tafiyar Amar, ayanxu hankalin ammah ya gama Tashi, wata guda kenan tun bayan tafiyarshi da sukayi waya sau daya lokacin daya shaida mata sun isa wajen operation inda bai fada mata ba saboda basa fadin work related to anyone hatta family wannan dokar sojoji ce.
Fadin irin tashin hankalin da ammah ke ciki bata lokaci ne ta rame sosai saboda tunanin Amar, this is the first time hankalinta ya Tashi da tafiyar da yayi don this is not the first time yake tafiya operations, don Duk sanda zaije koda yana chan dubai saiya fada mata kuma haka zasuyi kusan wata biyu basuyi magana ba idan yana chan Duk bata damuwa saidai akasin na wannan Karan abun ya dameta sosai, Wai irin unnecessary tunani take yi aranta wanda ada bata yinsu kwata kwata, “what if wani abu ya sameshi? What if something is wrong?” Kullum tambayar da take ma kanta kenan, abunda yafi damunta shine sai yanxu take dana samun fada mashi maganar cikin amra.
Tana nan zaune amra ta shugo dakin, kallonta nayi sama Har kasa sanye take da doguwar rigar atamfa bubu anyi nata free gown da ita, tayi wani irin bulbul skin dinta yayi haske sosai kamar jini zai fita, fuskanta tayi fayau, ga dan baby bump dinta daya futo ba laifi don yanxu kana ganinta kasan tana da ciki, yanxu cikinta watan shi bakwai da sati guda.
Shugowa tayi dakin atsanake ta karaso Ind ammah ke zaune Har zata zauna a kasa ammah ta kalleta jiki a mace kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai “haba daughter, baba hanaki zaman kasa ba yanda kika fara nauyin nan”
Murmushi amra ta danyi kafin ta zauna gefen gado ta gaisheta, cikin fara a ammah ta amsa mata. Shuru ne ya buyo baya kafin amra ta soma magana “ammah, Akwai abund ake damunki ne?”
Shuru ammah tayi kafin ta nunfasa “babu komi daughter,kinci abunci?”
“Eh naci tuwo” amra ta bata amsa
“Ammah please Ki fada min abunda ke damun ki, bakya cikin walwala kwanakin nan”
Kallonta ammah ta danyi baya son ta saka mata damuwa don haka tace “daughter yau wata guda kenan rabon da na samu son a waya, wayarshi baya shiga kwata kwata, Ina jin kamar wani abu ya faru”
Hannunta amra ta kama kafin ta soma magana in a calming tone “ammah ki kwantar da hankalin ki, nasan he’s perfectly fine Insha Allah, maybe Har yanxu basu gama operation sun bane shiyasa bakya samunshi a waya”
Haka amra ta dunga tausasa ta da kalamai masu kwantar da hankali harta danji nauyin da zuciyarta keyi ya ragu, hira suka danyi don yanxu inka gansu kamar uwa da ya babu wani kunya, amra ta sake sosai da ita.
Washe gari suka shirya da ammah da salima da amra suka wuce asibiti don salima tace Yanxu dole da ita za a dunga hidiman baby, suna zuwa doctor ya duba lafiyar baby Har alokacin ammah taki yarda Suga gender na baby don haka doctor ya bata magungunan Karin jini da wanda zai dunga sakata cin abunci don zatafi buqatan hakan ayanxu don ta kusa shiga wata takwas wanda ya zamana anzo gangara.
Bari mu Yan katsina….
Duniya ta juyama wannan family baya, yanxu taluacin da suke ciki haryaci uwar na da saboda da khady kawai suka dogara da take saida gwanjo itama ribar yanxu tayi kasa saboda hidiman gidan daya dawo hannunta dukda ba wani kudin arziki take fiddawa ba idan zasuyi cefane kullum, dari biyar ce safe da dare don ba a cin abuncin rana a gidan, dady kuwa tun bayan wannan targade da yayi har kayi mashi gyara a hannu da kafa, inda a hannunshi samu karaya while kafar kuwa ya samu targade, Toh da dai gyaran karayan nan baiyi ba kafarcema ya dan samu sauqi saidai hannun ne ya shanye gaba daya baya wani amfanuwa, sai kuma jan ruwa da yakeyi saboda inda ya ciwo wajen hannun ba a yi dressing ba haka gudaje da bad environment din wajen yayi affecting hannun, nan ya dunga Jan ruwa sai wani karshe dai hannun shanyewa tayi babu wani amfani.
Haka kullum zai zauna a gida baya uban komai, tun kareema na jin tsoro shi lokacin daya gano tana da cikin shege har tazo ta daina tsoronsa take gasa mashi aya a hannu, zagi cin mutunci babu wanda basa yima juna agaban yayansu, yaranma Har sun saba da yanda iyayensu keyi ma junansu, ah anguwa kuwa babu wanda baisan kareema matar mustapha mai damfara nada cikin shege ba, tayi cikin shege da aurenta, wannan zance yasa ko fita bata iyayi yaranma idan sun futa da irin zagin da ake jifansu dashi kenan, khady dai ta gama zama yar tasha idan ma an fada bata wani damuwa don Har cewa take “Toh saime idan tayi cikin shegen idan uwar wani ce Tayi ku fada min badai tawa uwar bace to munji tayi ciki”
Yanda ta zama yar daba daba yasa wasu idan sunso goga mata magana suke kyale ta saboda kangararren saurayin ta.
Bangaren wahab yana chan a kurkuku don asad saida ya tabbatar an yanke mashi hukunci daidai da abunda yayi, nan aka kaishi prison na shekara goma,don Akwai diyyar daya kamata ya biya wanda yayi ma yarinyar maqocinshi na chan lagos fyade inda aka tuntubi iyayenshi ko zasu iya biya don in ba a biya ba shekarun da zaiyi a prison zai karu, nan aka tuntubi Alhaji mustapha, lokacin da suka kirashi ma yana gida a zaune babu uban abunda yake sai zaman banza don haka da sukayi mashi bayani nan take yace “ku rufeshi kawai babu abunda zaku samu a waje na”
Yana kaiwa nan ya kashe wayar baima tsaya sauraron su ba, da kareema ta tambayi ko da wa yake waya kai tsaye ya mata bayani, nan take ta dunga kuka tana tsine daddy kan Duk shine ya janyo masu wannan masifa Har yayanta suka wulaqanta gaba daya saboda zalumcin shi da cin amanar dan uwansa da yayi na wulaqanta yayansa.
Nan suka dunga Sarfa ma junan su zagi ta uwa ta uba “kije kiji da shegen ciki wahallaiya asararriyar mata Wallahi nayi dana sanin aurenki kareema kina da kaso mai girma a cikin lalata rayuwata kece ma baqar kafar data lalata kin komai, badan kin sa an zubar da waennan yarannan ba da tuni na samu wani abun a wajen yayarsu”
Kallonshi karima tayi tana takaici ace Wai mutun baiyi nadama ba ko kadan, “shiyasa zaka kare a haka a wulaqance, Har yanxu zuciyarka a mace take”
Nan suka cigaba da cece kucensu dagashi Har ita aka rasa wanda zai jaa baki yayi shuru maqota na jin su.
Bangaren Muhammad kuwa yana chan Australia, yau watanshi biyar kenan, acahn yaqi dawowa don daddy’s ya kirashi ya shaida mashi uwarshi tayi cikin shege don haka ya tura masu da kudi, ranar da yaji wannan baqin labari ya shiga tashin hankali sosai inda ya ko sun kirashi ma kasa daukan wayan yakeyi don yana Allah wadai da iyaye nashi, wannan yasa yaqi dawowa yayi zamansa acahn ya maida hankali wajen aikin shi inda yake taimakawa kaninshi ishaq daya dage yana masters dinshi anan Australia don bayan ya gama karatu ya dawo wajen Muhammad nan ya muyi sponsoring dinshi ya samu schorlaship nan ya fara masters.
Bangaren kakarsu salima kuwa, rana daya Allah ya dauki ranta anan kauye inda take zaune wajen dan uwanta, tayi jinya sosai inda suka dunga bata maganin gargajiya da farko kamar komai ya lafa sai daga baya kuma gadan gadan ciwon nata ya dawo Har Allah ya dauki ranta bata samu damar Ganin marayun jikokinta ba.
Bangaren labaran shima bayan noma haka ya samu yayi renting wani kanti nan kusa da inda yake yake haya, nan yayi amfani da kudin da ammah ta bashi ya zuba provision a cikin shagon don bashi da wani girma sosai, cikin wata biyu wajen ya bun kasa don haka ya hade da shagon dake kusa dan wanda yake haka, cikin ikon Allah Allah ya by kasa mashi, don Allah ya bashi wannan baiwar da zarar ya saka hannu akan abu sai Allah ya bukata mashi, kullum kuwa saiyayi mafarkin yarannan guda uku ada chan baya yana mafarkinsu baya Ganin fuskokoinsu saidai shadow dinsu kuma yana jin saurin kukansu Yanxu kuwa yakan iya ganin su a fili saidai Har yau baiga fuskokinsu ba saidai yaji su suna dariya.
Bayan wannan Har yanxu zane kam yana. Yin shi, don idan ya dauka alakali yana Zane kamar wani pro nan ya gane cewa yayi ilimi don saida ilimi zaka iya zane irin wannan da ake kira da architecture.
Abunda yafi daga mashi hankali kuwa shine Akwai ranar da yazo tsallaka titi bayan ya dawo daga shago, nan take wata mota taso bugeshi Allah ya rufa asiri mutumin ya Taka burki nan take flashback din wani mummunan accident yazo mashi, inda anan ya gane lokacin da yayi accident ne kenan, everything was dark don haka bai gane komai ba.
Alhaji kabiru dai Ana chan prison shima an kaishi gidan yari inda zai gama rayuwar shi acahn gaba daya, irin dukan dasu asad sukayi mashi yasa yayi loosing site dinshi daya, ya rame ya jeme ya zama kamar wani mai kanjamau, talking of kanjamau lokacin da yayi wata irin rashin lafiya anan prison aka kaishi asibiti nan akayi mashi test take kuwa aka gano yana da hiv.
Haka aka sallamoshi bayan ya danji sauqi aka maidashi prison aka rufe shi, Har lokacin he can’t imagine rayuwarshi zata juya ta zama haka ba, ya zama kaskantacce, ya lalace kuma naka sasshe bashida kowa bashida komai, dukiyar daya tara ta hanyar haramci bata amfaneshi da komai ba saima jefa shi cikin mawuyacin hali datayi.
Aman Duk wata yana zuwa nan prison yana dubashi, wani sa’in yakan futo ya ganshi wani sa’in kuwa haka zai Karaci zamanshi daddy yaqi futowa don yanxu blaming dinshi yake yi akan cewa ya cuceshi yana matsayin ubanshi ya fallasa asirin sa.
Su lantaana da doctor ma ana chan ana serving a gidan yari, kowannensu an bashi shekara biyar for attempting murder.
Abuja Nigeria……
After 2 months…
Yau wata biyu kenan da tafiyar Amar, Har ranar dai shuru babu labarinshi, at this point hankalin ammah ya gama Tashi don haka ta fara neman manyan mutane da ta sani acahn dubai en, shuru dai Har lokacin don haka ta fara tunanin zuwa dubai din saidai kuma tunawa da amra tayi nauyi yanxu yasa tayi cancelling tafiyar.
***
Ammah ce zaune a sitting room hannunta rike da charbi tana lazimi gefenta Salim ne dake ta faman yin game a wayar Salima don batama san ya dauko ba tana barci.
Ahankali ta soma saukowa tana dingisawa harta sauko daga stair tana nishi, amra ce sanye da doguwar rigar chan iska wadda ammah ta sayo mata su da yawa saboda ta dunga sakewa a cikin rigar, saurin nishin da takeyi ne yasa ammah ta kalli inda take tsaye bayan ta sauko kasan, murmushi kawai ammah takeyi harta karaso parlor, kallonta ammah tayi da yanda yake tafiya, cikinta ya futo sosai kamar mai wadda zata haihu yau ko gobe, daman doctor ya fada masu cewa da zarar takai wata takwas cikin nata zai bude, yanxu kuwa cikin nata yakai 8months da sati daya, cikin ya futo sosai kuma yayi mata kyau sosai, ta Kara fresh da kyau kamar bamai ciki ba babu wannan kumburu fuska da na hanci, dass dass abunta.
“Wash barka da yamma ammah” ta karashe tana zama gefen kujera mai zaman mutun biyu
“Sannu daughter kina kokari, wannan babyn namu tubarkallah”
Dariya amra ta danyi kafin ta kalli inda Salim yake tace “kai kuma baka daddara ba ko, saita sauko ta mammake zaka daina daukan mata wannan wayar yar gold din”
Dan murmusawa ammah tayi tana kallonsu.
Salima ce ta sauko rai a bace Har tana grade kafafunta daga stairs, tana karasowa parlorn tayo kan salim, “kai Ka gama rainani ko? Toh Wallahi yau Saina koya maka hankali”
Tana kaiwa nan tayo kanshi, ammah ne Tayi saurin hanata “haba yarinyar kirki, yi hkui bazai sake ba kinji”
“Ki barta ta bugeshi ammah tunda baya ji, haka ya lalata min yawa Yanxu kwata kwata idan an kirani baba jin kara” amra ta fada tana kallonsu
“Ah ah baza ayi haka ba daughter” karban wayar ammah tayi daga hannunshi kafin ta mikama salima “ungo yarinyar kirki yaci albarkaci na”
Dungure kanshi salima tayi kafin ta karbi wayar, alokacin call din Aman ya shigo don haka ta wuce sama abunta tana murmushi.
Kallonta amra tayi da yanda jikinta ya dau zumudin Kira harta wuce sama, shuru ta danyi don sai a lokacin amar ya fado mata, dukda tana kokarin hana zuciyarta tunanin shi saidai hakan ya gagara don yanxu idan babyn cikin ta ya danyi motsi shine yake fadi mata arai.
Suna nan zaune wayar ammah tayi vibrating, dan waigowa ammah tayi, kamar a mafarki idanunta ya sauka akan sunan Amar, cikin sauri ta dauka wayar Har hannunta na karkarwa yau wata biyu kenan rabonta dashi, “hello hello son is that you”
Cikin jin dadi da murna Amar yace “yes ammah nine”
“Subhanallah!! Son in Ka shiga Ka barmu cikin damuwa, wata biyu…”
“So sorry ammah na shiyasa na kira ma yanxu, ko sauka bamuyi daga jirgi ba ayanxu haka maganar da nake dake”
“Ya kake are you okay babu abunda ya sameka? Kana cikin koshin lafiy…”
Saurin katseta yayi “I’m fine ammah, please don be worried I’m perfectly fine okay? Hope kuma kuna nan lafiya?”
“Yes son we’re fine alhamdullah yaushe zaka dawo? I have something very important to tell you”
“I don’t know ammah, saimunyi rounding up komai anan, but inason ki kwantar da hankalinki I’m perfectly fine, Muna gama operation Zan dawo Insha Al….”
Dip wayar ta dauke, amra data gyara zama tana. Kallon ammah data sauke wayar, gaba daya ta maida hankalinta kan ammah haka zalika Salim shima yana daga gefe yana kallon ammah Duk sun zama curious suji ko lafiya,
“Ammah lafiya dai ko?”
Dan Nunfasawa ammah tayi tace “Alhamdulillah, son ne yace yana lafiya Har yanxu basu gama operation bane”
Wata ijiyar zuciya amra ta saki Har yasa ammah ta juyota.
“Har hankalina ya kwanta daughter, yau wata biyu da kenan, alhamdullah ya Allah”
Sauke kanta kawai tayi kasa batace komai ba, saima wasa da Yan yatsunta data fara.
Washe gari wajen karfe biyu suka fito gaba dayansu, da yake weekends ne, sunyi kyau gaba dayansu daga kan amra zuwa salima sai ammah, Duk sunsha native kaya, atare suka fito gaba sayansu suka wuce motar ammah, ammah ne ke jan motar sai salima a bayan motar,
Anatse ammah ke drinving while tana dan duban amra ta jikin mirror, hira suka dan farayi a tsakanin au inda amra dai saidai tace uhm ko ah ah saidai kuma in anyi abun dariya Harda ita ake kyakyatawa.
Gaban wani katon mall suka 360 mall, mall din ya gadu sosai don yana dauke da wani babban bulding mai tsayi sosai, atare suka fito gaba dayansu inda salima ta taimakawa amra ta bata helping hand saboda yanayin ta, ahankali suka shiga cikin mall, fadin irin kyau na wurin ma bata lokaci ne, babu wani hayaniyan mutane dan few mutane ke yawo, ko Ina fess fess sai kamshi, maintainance din wajen sai ba a magana saboda ko Ina clean, cikin lift suka shiga nan ma saida salima ta taimaka mata, suna hawa second floor suka wuce wani katon shop may suna baby shark, tundaga nesa zaka san shop din kayan babies ne, ammah ce agaba suna biye da ita Har suka shige cikin shop din, mutanen wajen ne sukayi welcoming din ammah kafin su fara zagaya wajen,
Katon trolling ammah tasa salima ta janyo nan suka shiga shopping, abun da suka kwasa akalla zaikai wajen miliyan uku, ammah dai sage wa tayi babu abunda bata saya ba a wajen na Abubuwan da mummy and baby zasu magana dashi don suna da kaya designer don kamar ma kayan Duk na kasar waje ne, sun kwashi wajen awa biyu Ana abu daya, amra dai data gaji zama tayi nan mutanen wajen suka kawo mata ruwa da snacks, zamanta kuwa tayi taci snacks din tana cinye wa ta buqaci a kara mata nan ammah tasa su kawo mata da yawa.
Saida su salima da ammah suka gama kwashe kwashe su Duk wani cute kayan baby saida suka dauka Harda unisex babu wanda suka bari, Harda abubuwan da amra zata buqata wajen preparing delivery bag dinta, suna gamawa ammah tayi payment, lokacin da amra taji kudin saida ta kama baki, bazata iya musama ammah ba don haka taja Bakinta tayi shuru saidai bata kam taga abunda ake kira da gata.
Daga nan saida suka tsaya ammah ta saya masu kayan ciye ciye don itama tana son kayan dadi saidai diabetes dinta dake hanata cin wasu abubuwan,
Sai wajen karfe biyar na yamma suka dawo gida da kaya niki niki, daki guda ammah ta fidda anan sama aka zuba kayan a dakin.
Washe gari Kayan da ammah tayi order daga dubai da uk suka iso, suka fadin irin yawan kayan da kudin da aka kashe akansu bata lokaci ne.
Su Aman ne suka dunga shugowa dasu suna hawa dasu sama shida salim, suna hawowa dashi ammah tasa suka wuce dashi dakin data ware, daki ne babba sosai don Har yafi inda amra take, empty room ne saidai yasha frames, nan suka dunga zuba komai a ciki daga kan crop zuwa strollers da baby swings. Suna gama ajiyewa ammah ta shugo dakin tare da salima sai maida din gidan, nan suka fara shirya komai suna jerawa inda nan Aman shima yazo ya tayasu harhada crip da sauran abubuwan da dole sai anyi assembling, amra dai bata shugo dakin ba don kwana biyu tana dan fama da ciwon baya ga kumburin kafa da yake fama dashi.
After 1 week…
A cikin sati daya ammah ta gama komai na sayayyan baby, babu abunda bata saya ba Har wanda bazasu buqata ayanxu bama Duk ta siya.
Yau last appointment din amra before delivery don haka suka wuce asibiti, a cikin satitikan nan cikin amra girma yake kullum abun Har mamaki yake bama ammah, don cikin yayi girma sosai lokaci guda babu zato, Duk wasu kayanta yanxu basa shiga ta kwata kwata, sai doguwar riga mai bubu, wadda ammah ta karo mata su da yawa tana sakawa yanxu ma rigar ce a jikinta sai mayafin rigar, ahankali take sauko tana rike bayanta, tana saukowa ta dan tsaya tasa maid ta kawo mata ice water, tana nan tsaye ammah ta sauko kasan “sorry daughter na barki tsaye ko, muje”
Suna sauka saiga salima ta taho da sauri itama daga sama, “Laa ammah shine zaku tafi babu ni, dan Allah Zan biku “
“Toh muje” ammah ta fada tana wucewa gaba harta karasa gaban mota, tana karasawa ta bude gidan gaba kafin ta bude ma amra baya don ta daina zaman gaba, suna shigewa gaba dayansu suka bar cikin gidan.
Suna karasowa asibiti ammah tayi parking, fitowa sukayi gaba dayansu inda salima ke rike da hannun amra tana bata helping hand, anatse suke tafiya Har suka shiga cikin asibitin, suna zuwa kuwa time din appointment dinsu na cika cif. Basu tsaya komai ba suka wuce office din doctor.
Da sallama suka shiga cikin office din ammah ce a gaba sai amra dake biye da ita tare da salima.
Zama sukayi gaba dayansu baya sun gaisa da doctor din.
“Sannu madam ya nauyi? Hope baby is kicking”
Doctor ya fada yana kallon amra
Murmusawa kawai tayi batace komai ba, maida kallonshi yayi kan ammah yace “Bari mu fara scan ko? Saimug ko edd dinta yayi gaba ko ya dawo baya”
Mikewa amra tayi ta wuce inda doctor kw dubata, hawa tayi kan gadon kafin ya soma dubata, yana gamawa yayi printing scan din.
Mikamaa ammah paper yayi kafin ya soma magana “alhamdullah hajiya, ta shiga wata Tara ciff and edd dinta yana nuna in the next 7 days baby will be ready to come to the world, yanxu form now ya kamata ta dage da exercise sosai zai taimaka mata sosai”
“Alhamdullah I Alhamdulillah thank you doctor
Ammah ta fada tana murmushi.
***
Suna fitowa daga office din doctor motar suka shige, suna shiga ammah ta kunna motar suka bar cikin asibitin, kowannen su fuskanshi dauke da murmushin jin dadi, musamman ammah, amra dai mamaki ma ya hanata tunanin komai, she can’t believe itace zata haihu, allah mai ko kenan.
Suna isowa gida amra ta wuce daki saboda wani irin ciwon baya daya riketa sosai, yau kwana biyar kenan tana fama dashi yazo ya dawo haka yake mata, abunda yasa bata fada ma doctor ba kuwa shine normallly tana yin haka tun kafin cikin ta ya tsufa so yanxu daya fara mata hakan sai tayi tunanin it’s normal.
Karfe Tara nayi ammah ta shugo dakinta da sallama, a zaune ta taddata tana rike bayanta, “daughter Yadai”
Ammah ta fada tana zama gefenta don yanxu bata wuce minti talatin bata leko ta ba, “ba komai ammah, na gaji ne kawai da zaman”
“Toh ki miek ki zagaya gidan zai saki Insha Allah”
“Tohm ammah”
Tana kaiwa nan ta mike ta nufi hanyar futa daga dakin, kasa ta sauka ta zagaye parlor kafin ta hau sama, tana haurowa ammah na fitowa daga dakinta, “daughter Ina zuwa, Ay kin gama kwanan dakinki yanxu, wuce muje part dina”
Kanta a kasa tace “Toh ammah”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.