Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 42 of 52
Chapter 146
Update
Unedited page
Hade rai amra tayi tadan tabe baki kafin tace ‘’eh munga fucewarshi lokacin muna dawowa’’
Shuru ne ya biyo baya bayan dawowar salim da ruwan data buqata, tunda tayi resting bayanta ta soma jin barci barci sama sama, ammah na dake duban ta jefi jefi tana ganin yanayinta tace ‘’dear kije ki kwanta kafin anjima da yamma saiku sake futa ko?’’
Kamar daman jira take ta mike tsaye tana dan yin nishi sama sama ‘’toh ammah,’’
Tana kaiwa nan ta wuce hanyar stairs zuwa dakinta, datayi dan taku daya biyu saita huta kafin ta cigaba, ammah na kallontta daga zaune, fadin irin farin cikin da take ji idan ta kalli amra dake dauke da cikin Muhammad mara misaltuwa ne, shes so happy, kusan kullum sai tayi sadaka, duk dare kuwa bata barcin daya wuce awa biyu, haka zata tashi ta kafa goshinta akan sallaya tana godiya ga Allah daya basu wannan kyauta ta musamman, she’s just waiting for the perfect time ta fada ma Muhammad, dalilin dayasa ta boye mashi kuwa shine, yanda ta lura yana qaunar amra sosai amma yaqi futowa fili ya nuna yana son ta, bayan wannan tafison sai ya nuna yana buqatar matarshi da kanshi kuma yayi accepting dinta da kanshi kafin ta fada mashi. Ayanxu ta zuba masu idanu tana karantarsu sosai, daya daga cikin abunda ta lura dashi shine, yanda yake pushing amra don duk hidimar datakeyi mashi akan idanunta ne shi kuma yana basarwa saboda ego dinshi daya kasa barinshi ya saukar da kanshi kasa, da farko taso ta barsu a yanda suke ko zasu dawo dan kansu saidai kuma amaimakon komai ya falling into places sai akasin haka, don yanda yake pushing din amra yasa take baya baya dashi, don da gayya ammah take aikata dakinshi don ta lura ta daina kwana anan dinma, bata takura mat aba haka ta kyaleta tana kwana inda takeso saboda yanayin ta.
Nunfasawa ammah tayi tana tunanin, harga allah tana son tagansu kamar kowanne mata da miji, saidai hakan kamar bazai samu ba saboda kafiya irin ta amar, tunanin yanda zatayi dasu ta fara kafin takai kan decision dinta.
Tana nan zaune salim na gefenta yana barcin daya saba a doguwar kujera akayi sallama, kallon inda yake shugowa ammah tayi fuskanta dauke da fara’a da bata barin fuskanta, ‘’malam labara maraba lale’’
Har inda take zaune ya karaso ya zauna a kasa ya fara gaisheta ‘’nace ka daina zama a asa malam labaran, ga kujera nan manene amfaninta kenan’’
Cikin girmama way ace ‘’hajiya nan ma yayi, ina wuni ya iyali?’’
‘’lafiya kalua alhamdullahi ya aykin gona?,ya kuma jiki’’
‘’da sauqi hajiya alhamdullahi, ‘’ ya bata amsa
‘’toh madallah allah ya taimaka’’ amma ta amsa shi tana kokarin kallon tv.
Hannunshi ya zaro cikin aljihun shi yace ‘’hajiya ga wannan, kudin wannan shekarar ne, shine nace bari na akawo’’
Kudin ya ajiye mata da paper a gefe ‘’wannan list din komai ne na rubuta a ciki, murmusawa ammah tayi ta kalli kudin daya nade a leda kafin ta maida idanunta kanshi, ‘’masha allah, ka rike a hannunka, duk wani abunda za a buqata a gonar saika saya dashi sai kuma amfaninka kaima’’
Kanshi a kasa yace ‘’hajiya akwai duk wani abunda za a buqata, wannan…’’
‘’Toh ka rike kaja jari’’ ammah ta kkasteshi, wasu ahwaye ne suka fara zarya akan fuskanshi, kafin ya dan dago ya soma jero mata adduo sosai.
‘’babu komai malam labaran ka daina min godiya? Yauwa daman inata so na tambayeka, ya maganra memories dinka kuwa, akwai improvement?’’ nunfasawa ya danyi yana murmushi yace ‘’alhamdullahi, gaskia akwai, saboda yanxu idan na kalli wasu abubuwan wani shafi daga cikin rayuwata yana zuwanmin’’
‘’toh alhamdullah allah ya kawo sauqi cikin lamarin’’ ammah ta fada tana murmusawa
‘’ameen hajiya, bari na wuce,’’ ya fada yana mikewa, ‘’toh madallah malm labaran nagode sosai.’’ Dan waigawa yayi ya kallli inda salim ke kwance ya juyamasu baya don baya fuskanta inda suke zaune, murmushi kawai malam labaran yayi ya fuce daga gidan yana jin yanda hajiyar take kara qima da daraja a idanunshi, ‘’oh ashe waennan ne yaran da ta rikesu, allah sarki samun mutane irin hajiya sai an tona, baka sansu ba basu sanka ba ka rike su amana kamar naka allahu akbar’’ malam labaran ya fada yana tafiya shi kadai har yazo bakin wajen mai gadi, don shima maganar yara da hajiya take rikewa daga wajen baba mai gadi yaji zancen.
Sallama yayi ma baba mai gadi kafun ya fuce daga gidan.
Bangaren amra kuwa tana shiga daki ta soma zame kayan jikinta ta wuce bathroom don jikinta har wani yami yami yake mata saboda dan zufar datayi, a gaggauce ta watsa ruwa ta fito daure da towel tayi kwanciyarta nan take barci ya debeta.
Bangaren amar shima tun bayan ya fusgi motarshi yabar estate din ranshi a bace bai tsaya ba, haka ya dunga zagaye da motar yama rasa ina zaije, ranshi yayi mugun sosuwa da abunda amra tayi mashi, bait aba tunanin zi sauke kanshi to this level ba har ta samu damar fada mashi Magana son ranta and abunda yafi bata mashi rai shine yanda ya kasa ce mata komai, ‘’why why’’ ya fada da karfi yana bugun steering motar shi, gefen titi ya gangara yayi parking don idan rasnhi ya baci baya careless driving, yana parking motar yayi shuru yana dafe kanshi dake sara mashi sosai, shi maganganun ma data fada mashi bai dameshi ba kamar ganinta da yayi zaune wani asararre yana mata Magana ita kuma tana murmushi, abun ya staya mashi arai sosai yanda mutumin ya tsaya yana kallonta har yana kokari taba jikinta, ‘’fuckkk’’ ya fada da karfi yan sake bugun sterring din kamarzai ballah ranshi amugun bace yake ‘’why would she smile’’
Ya fada aranshi, meysa zatayi ma wani murmushi, murmushinta mai tsada ne wanda baya son kowa ya gani bayanshi ya fada aranshi, wata zuciyarshi ce ta tambayeshi ‘’why? Why would you care idan tayi ma wani murmushi?meysa zaka damu’’
Dan jim yayi ranshi a abce kafin ya furta ‘’cause shes my wife, as long as shes my wife no one will ever see that smile’’
Wata zuciyar ce ta sake tambayarshi, ‘’but kace baka buqatarta why now? Why are you acting like that ko dai kana sonta ne? are you ready to accept her?’’
Dafe kanshi yayi ya furzar da wani nunfashi mai zafi kafin yace ‘’no no nooo, bazai taba yuwu hakan ne ba kawai obsession ne da tausayi that’s all, nothing else’’
Wata zuciyarce ta sake tambayarshi ‘’then why would you care, why are you jealous?’’
Haka nan zuciyarshi ta dunga mashi wasi wasi, yama rasa taka maimain, ainihin abunda yake damunshi, he cant lie baya wuni day aba tareda ta fado ranshi ba every seconds, gashi lokaci guda allah ya saka mashi damuwa akanta, don ayanxu sai yayi tunanin sau nawa baima san yana yi ba, hes craving for her, he wants her badly, he cares for her saidai wani bangare na zuciyarshi na ego dinshi bazai barshi ya sauke kanshi ba, infact why would he do that? Haka yake yawan tambayar kanshi daga nan kuma komai saiya sauya, haka zai fara denying feelings din da yake mata,thinking about this kadai yana damunshi sosai, ya dade a cikin motar yana saqa da warwara, sai wajen yamma yabar wajen ya juya akalar motarshi zuwa gida.
Karfe biyar daidai ya shugo gidan bayan ya tsaya a masjid yayi sallan asr, lokacin daya shugo gidan babu kowa don motar ammah bata garage don haka ya gane cewa bata gidan, yana nan tsaye a parlor ya zaro waya shi ya soma dialing number ta, ammah na picking tun kafin ya soma Magana ta katse shi don tasan nagging zai fara ‘’sorry son ka dawo bana nan ko? Naje groceries shopping naga abubuwan fridge sunyi kasa’’
Sauke ajiyar zuciya yayi har tana jin sautin sa ‘’ammah na, maysa baki fada min dana futa ay dana biya na sayo’’
‘’sorry son,nag aka futa ne cikin gaggawa, shiyasa banyi maka maganar ba’’
Saida takai aya ya cigaba ‘’ammah please..bana son kina yawan futa ke kadai, ga aman ne, idan ma bana nan he can go and get it’’
‘’son, calm down, babu abunda zai faru dani cikin ikon allah, besides aman baya nan, zaije daukan salima daga school yau zasu gama exam very late, bazan dade b azan dawo nan kusa ne fah’’
Ahankali ya sauke ajiyar zuciya for the second time yace ‘’okay tohm, allah ya kiyaye’’
‘’ameen yauwa ka shiga ka duba min daughter ko zata buqaci wani abu, na barta tana barci’’
Shuru ya danyi kamar bazaice komaiba har saida tace ‘’hello kana ji?’’
‘’yess ammah’’ yana kaiwa nan ya kasha wayar
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.