Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 47 of 52
Chapter 149
Update
Unedited page
Cikin sauri ammah ta miqe tsaye tana tunkarar inda Salim ke kwance a sume tana fadin “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”
Dagawa salima tayi don Ganin abunda ke faruwa, kwata kwata batama Lura da labaran dake zaune ba shima hankali a tashe ya miqe, arazane tayi baya kiris ya rage bata fadi ba ta dafe gefen kujera, nunfashinta ne ya soma yin sama sama ta qame kamar gunki, she can’t believe abunda yake gani agabanta, amra dai kamar kurma haka ta dawo jikinta na bari kamar mazari, hannunta ma dake rike da Hamad da Hamid ma karkarwa yake, cikin sauri Amar ya karbe yaranshi don kwata kwata bai ganema abunda take ma rawar jiki ba.
Malam labaran shima daya kafesu da idanu ya kasa cewa komai, yanda suke Binshi da ido haka shima yake binsu da idanu gabanshi na faduwa kamar zuciyar shi zata buga, at the same time kanshi yana sarawa kamar an buga mashi guduma.
Waigowa ammah tayi bayan ta tsugunna inda Salim ke kwance a sume ta tallaboshi zuwa jikinta tace “ku bani ruwa”
Kyam ko wannen su ya tsaya babu wanda ya motsa, Amar dai kasa daina kallon amra yake Ganin tana kuka, sheshekar kukan salima ne yasa ya maida kallonshi gareta itama, gaba Dayan su waje daya suka kurama ma idanu jikinsu na bari kamar sunga dodo “babu wanda zai iya bani ruwa ne?” ammah ta daka masu tsawa hankalinta a tashe, jiki na bari salima ta miqe ta miqa ma amra angel har lokacin idanunta na kan labaran kwakwalwarta ta kasa aiki kwata kwata, wucewa kitchen din tayi ta dauka ruwan bottle ta dawo kitchen din, Har lokacin jikinta na Rawa tana kallon inda labaran yake tsaye kikam ya kasa motsawa shima, yana jin kamar ya sansu a wani wajen ko kuma suna da alaqa da past rayuwanshi, don yanda kirjinshi ke bugu ya gane tabbas yana da wani babban attachment’ da yaran, saidai abu daga ne bai gane ba, kwata kwata babu wani memory dunsu akanshi.
Salima na miqa ma ammah ruwa ta tsaya daga gefe, ruwan ammah ta yayyafa ma Salim Har sau biyu kafun ya ja nunfashi, yana Jan nunfashi ya kankameta sosai jikinshi na bari sosai.
Abunda ya razanar dasu su duka Har hankalinsu ya dawo garesu shine first furucin da Salim yayi tsawon shekarun nan, “un…cle ne Wallahi un..cle ne ya kashesu, ammah kice ma ghost din abba ya tafi Wallahi uncle ne”
Rike shi sosai ammah tayi Ganin kamar yana neman zaucewa kafin ta fara karanto mashi addua, malam labaran ne ya mike tsaye yana kokarin takowa inda suke salima ma tayi baya Har tana neman faduwa kansu ammah jikinta na bari tace “innalillahi,Wallahi fatalwan abba ne”
Kallon ta ammah tayi Ganin tana nuni da labaran gashi itama tana shirin neman zaucewa yasa ammah cewa “Ina fatalwan yake?”
Nuni tayi mata da labaran tace “Wallahi fatalwan Abban mu ne,“
Chak labaran ya tsaya yana mamaki, saida ya zo dan dasu ne yaji wata hajijiya akanshi, nan take ya runtse idanunshi yana dafe kanshi yayi baya zai fadi shima, cikin sauri amra ta miqe tsaye ta nufeshi, tana karasowa gabanshi ta tsugunna kasa sai hawaye, “abba kaine? Daman kana raye baka mutu ba? Kodai idanuna ne ke min gizau, yaya dan Allah duba min kina Ganin mutun a wajen nan ko fatalwar ne nima nake gani”
Hannunta ta sanya ta rike na labaran nan take ta razana tayi baya,sai hawaye, Amar dai kasa motsawa yayi yana kallon ikon Allah sai a yanxu komai ke dawo mashi, bazai manta ba ranar da yasa akayi mashi investigation akan amra da iyayenta tabbas ba ayi declaring mutuwar baban su ba saboda gawa daya ce ta kone a cikin motar, da farko yaso yayi buncike akan haka saidai kuma daga baya ya bar binciken saboda da Bakinta tace baban su ya rasu, bayan wannan he can recal first time daya ga labaran, tabbas yaga kamannin shi da yaran gaba dayansu, don turawa na cewa blood is thicker than water, tabbas jini baya karya ko a Ina ne, bayan wannan ma yasan ta yanda ammah ta kawo labaran gidan don ta kanta ta bashi labarin yanda suka tsinceshi akan hanya,harta taimakeshi da memory dinshi dayayi loosing, nan take ya gama harharda puzzle din gaba daya, shi kadai ne ya samu courage din daga kafafunshi ya karaso sitting room din ya kwantar da baby Hamad da baby Hamid akan kujera kafun ya karaso inda malam labaran ke zaune, anatse ya maatso ya taimaka mashi ya mike tsaye suka wuce wajen kujrar ya zauna, kallon inda ammah take Amar yayi yace “ammah ku dawo nan sitting room”
Mikewa ammah tayi Salim na maqale da ita kamar za a kwaceshi daga wajen ta kafin su karaso cikin sitting room din suka zauna nan ma saida ya kankameta, suna zama Amar ya kalli inda amra ke zaune tayi zaman dirshen ta hade jikin ta waje daya sai salima dake gefe itama tayi Tsuru tana hawaye “ku taso kuzo nan”
Dan dagoda jajayen idanunta tayi ta dawo ta mike tsaye a hankali Har lokacin jikinta na mazari salima na biye da ita kamar munafukai suka zaunaa kasa kowannen su kana ganinsu kasa a furgice suke.
Suna zama shima Amar ya samu waje ya zauna kafin ya soma magana, kallon inda malam labaran yake zaune yayi, cikin kamewa yace “malam labaran kasan su ne?” Ya tambayeshi don son jin daga gareshi
Dan dagowa labaran yayi ya kalli inda amra take, yana yi mata kallo daya ya runtse idanunshi kanshi na Sara mashi kafin ya maida kallonshi ga Amar bayan ya dafe kanshi yace “yallabai ban sansu ba saidai….”
Kasa karasawa yayi saboda wani moment da yayi mashi flashing akanshi , gashi ga amra a a zaune a wani garden tana nuna mashi assignment dinta na school suna dariya.
Saida memory din ya bace mashi yayi saurin dagowa ya kalleta, ga kamannin nan sosai da yarinyar da memory dinta yayi mashi flashing saidai ita waccar bata kai haka girma ba, kura mata idanu ya dungayi har saida Amar ya sake mashi tambaya, nan ma shuru yayi ya kasa cewa komai, “ya Muhammad don Allah waye wannan mai kama da baban mu?” Salima ta fada tana karkarwa, kallon inda take labaran yayi nan take wani memory din ya sake mahai flashing, gaba daya ya zama so confused, kamar daga sama sukaji yace “sunanki aisha? “ ya fada yana kallon amra, cikin sauri ta girgiza mashi kai tana hawaye, maida kallonshi yayi ga salima bakinshi na karkarwa yana son yin hawaye ammah ya danne yace “sunanki salima?,”
Itama girgiza mashi kai tayi tana hawaye, “kuna da qani Salim ?”
Atare suka girgiza mashi kai nan take salima ta miqe tayi kanshi ta rungumeshi a jikinta , “Wallahi abba ne wannan Abban mu ne wannan”
Gaba daya baki suka bude galala musamman ammah daga zama speechless, ya za ayi ace labaran ne babansu? How ya tambayi kanta, tana nazari, Amar ne yayi saurin breaking silence din yace “yes I think mahaifinku ne wannan, kuma bai mutu ba”
Ammah ce Tayi saurin katsesu tace “ku min bayani dalla dalla karku barni a duhu mana”
Shuru gaba daya sukayi kafin amra ta tattaro courage dinta ta soma bayani.
Yau shekara takwas kenan da rasuwar iyayenmu inda sukayi accident alokacin da suka dawo daga umra, Abban mu da mami, a ranar ne uncle ya shaida mana sun mutu kuma sun kone don ko gawarsu bamu gani ba, Salim ne kawai ya gani saboda tare sukace da daddy inda abun ya faru.
Fashe wa Salim ya farayi da kuka kamar ranshi zai fita yana shesheka, hankalin ammah ya gama Tashi gaba daya ganin Duk sun burkice.
“A kwai lokacin dana saka ayi min investigation akan aisha, a buncikenn danayi na gani cewa ba ayi declaring mutuwar iyayensu ba, saidai an rubuta sun kone saboda accident da sukayi shekaru takwas da suka wuce kenan”Amar ya fada yana kallon inda ammah ke zaune
Kallon shi ammah tayi tana son Karin bayani kafin ta maida duban ta ga labaran “yau shekara takwas kenan muka tsinci labaran a hanyarmu ta zuwa katsina daga abuja, does that mean…”?
Kasa karashe kalamanta tayi saboda jin furucin Salim for the first time, Har lokacin yana maqale a jikinta, yana rawar sanyi kamar mai zazzabi, don dazu gaba daya basu Lura ma da maganar da yayi ba sai yanxu suka tabbatar da bakinshi ya bude.
“Da..ddy…ne ya sa a kashe su, daddy ne naji lokacin, kullum sainayi mafarki, daddy ne….” Yana kaiwa nan ya fashe da kuka yana stammering muryanshi na breaking kamar dan koyo, kallonshi Amar yayi ya soma mashi magana cikin natsuwa “dama kana magana? Meysa Ka rufe bakinka?”
Sauke kanshi kasa yayi yana hawaye “ban…san..ina..iya..mag..na ..ba”
Shuru Amar yayi yana nazari kafin yace “zaka iya tuna abunda ya faru?”
“Yace zai kasheni idan na fada…” Salim ya fada yana stammering
“Waye yace hakan?” Amar ya sake tambayarshi
“Dad…ddy ne” Salim ya amsa shi
Kallon amra Amar yayi yace “waye daddy?”
“Uncle dinmu ne kuma marikin mu wan Abban mu” ta amsa shi kanta a kasa.
Hannu Amar ya miqa mashi ya tako inda yake ya zauna gefenshi “karkiji tsoro, babu abunda zaiyi maka I will protect you, now fada min abunda Ka sani”
Shuru Salim kanshi a kasa kamar mai tsoron magana yace “ranar ne daddy zaije airport zai dauko su abba, Ina son naje Amma Ina tsoro kar a hanani shine na shiga bayan motarshi na boye a kasan motar bai sani ba, Muna cikin tafiya ya tsayar da motar yana waya, na manta abunda ya faru but na…naji lokacin da yake cewa su kashe abba da mami,”
Yana kaiwa nan ya fashe da kuka saida Amar ya bubbuga bayanshi kafin ya cigaba, “inajin haka shine na fito daga bayan motar, nan naga ya fito daga motar tashi, a gabana ina kallo wata trailer tazo ta hau kan wata mota, bansan su waye a cikin motar ba don saida motar ta kama da wuta na hango abba da mami acikin motar…”
Shuru ya sake yi yana nazari kafin ya cigaba “shine daddy ya dawo motar nan ya kamani, yana ganina ya gane naga abunda ya faru don naga Yana bama mai trailer din daya buge motar wani envelop bayan ya buge motar harta kama da wuta kafin ya gudu don kan titin express ne babu mutane sosai, shine daga nan yace min nima zai kasheni, nan ya buga min… wani abu bansan menene ba ya bugamin…uhm na manta daga nan me ya faru don adda tace min nakai wata biyu a kwance ban Tashi ba, amma shine ya kashe abba na gani da idona”
Yana karasowa ya fashe da kuka, shuru sukayi gaba dayansu kowanne jiki shi ya mutu sosai babu sautin dake Tashi a parlorn sai kukan amra da salima,
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun” amra ta furta tana dagowa tana kallonsu, “Wallahi da gaske ne, bazan mantaba lokacin da abun ya faru, bayan fitar dady zaije airport daukan su abba, ni banma san Salim ya bishi ba don saidaga baya yake ce mana Ay tare suka tafi dashi inda akan idanunshi yaga accident din wanda hakan yasa Salim ya fadi saboda razanar da yayi lokacin da aka futo da gawar su don mu bamu samu munga gawar ba,”
Nunfasawa tayi tana ajiyar zuciya kafin ta cigaba, “daga nan ne mukayi kusan wata biyu a asibiti Salim bai Tashi ba kwata kwata, saidaga baya Allah yasa ya Tashi, koda ya tashi bayan mun koma gida da muka tambayeshi incident din, nan ya nuna mana ya manta bazai iya tunawa ba, bayan mun dawo gidan komai ya dan lafa nan muka fara Ganin sauyi a wajen daddy da Yan gidan ma baki daya, mun zama ware a cikin su, wajen kwanciyar mu daban ne dana Yan gidan don bamu da maraba da Yan aikin gidan, ahankali ahankli salim ya fara samun ciwon zuciya wanda koda mukaje asibiti da daddy nan doctor ya shaida Akwai abunda ke damunshi saboda a shekarun shi bai kamata ace ya samu ciwon zuciya ba da depression dole Akwai abunda ke damun shi, nan doctor ya
bashi magunguna muka dawo gida, bayan mun dawo Duk wata daddy zai kawo mana magani a bashi, a maimakon muga sauyi sai mukaga abun nashi yana gaba sosai, kullum cikin jinya yake Har takaiga muka hakura da bashi maganin ma bayan wasu Yan shekaru harna tafi karatu na barsu a gidan.”
Tana kaiwa nan ta fashe da kuka tana hawaye, kafin salima ta cigaba “bayan tafiyar adda, mu kadai muka rage ma juna, munsha wahala sosai inda Har takaiga bama futa ko Ina kullum Muna daki kamar prisoners, harta school dady yace bazamu yiba saboda…. Saboda na bugama ya Ibrahim kwalba akai saboda yayi kokarin raping dina, shine ya kashe mana zuwa school sannan yace karmu sake mu dunga fitowa daga dakin mu saboda baya son Ganin mu, sau daya suke bamu abunci, babu sabulun wanka, babu kayan kirki ruwan wanka ma gagarar mu yake saboda fanfon toilet din daya lalace ba a gyara ba, babu wanda ke zuwa dubamu kullum Muna zaune a daki, babu hasken fitila saboda globe din ya mutu, Har na fara loosing sight dina na tsawon shekara biyu , karshe dai Har muka fara rashin lafiya, inda Salim baya iya ko motsawa, jikinshi Duk ya shanye, Duk dare sainayi kuka don ban saka ran zai wayi gari da nunfashi ba, ranar da hakan ta faru kuwa da safe bayan mun Tashi naga baya nunfashi, hankalina ya Tashi sosai nan na futo parlor hankali na atashe, koda nazo parlorn ma kallon mahaukaciya sukayi min don gaba daya na futa gayyaci na, allah yaso ya muhammd ya dawo gidan don dana rokesu akan su taimake ni salim zai mutu babu wanda ya kalleni, sai ya Muhammad ne kawai ya iya shugowa dakin mu, shine ma ya kaimu asibiti, daga nan ne bansan inda kaina yake ba saida na Tashi, inda ya Muhammad ya shaida mun aiki da akayi mana nida Salim, kullum shike kula damu Har na tsawon sati biyu, kwatsam sai kuma tafiyar gaggawa tazo mashi inda ya tafi bayan ya shiada min driver zaizo ya maidamu katsina wajen kaka don na rokeshi akan karya maidamu gidan daddy, washe gari kuwa da safe wajen karfe goma saiga galaxy driver yazo, drivern gidan ne, yana zuwa ya daukemu muka kama hanya ta zuwa gida don mu diba kayan mu, Muna kan hanya mummy (hajiya kareema) ta kirashi a waya,bamuyi ne take ce mashi abu saidai naji yana ta rokonta akan zai kawo mu gida kafin ya wuce inda ta umarceshi, karshe dai sai parking yayi yace mu sauka, bayan mun sauka ya shaida mana mu jira shi anan zaije ya dawo karmu taci ko’ina, haka muka zauna muka jirashi na tsawon awa hudu, shuru babu shi babu labarin sa Har yamma tayi, haka muka dunga yawo akan titi Muna kuka babu inda zamuje, cikin ikon Allah Muna zaune wani mutumi yazo yace mana ya muhammd ne ya turo shi akan ya tafi damu, da farko naji tsoro sai daga baya da naji bayanin da yayi na yarda dashi nan muka shiga motarshi muka kama hanya harya kawomu nan gidan wajen ammah, saida muka zo nan ne muka samu kwanciyar hankali saboda ammah bata sanmu ba ta karbe mu hannu bibiyu ta bamu ci ta bamu sha ta suturta mu sannan ya muhammd ya saka Muna school muka cigaba da karatu,” tana karashe ta fashe da matsanancin kuka sosai kamar ranta zai futa
Tunda salima ta fara magana amra ta runtse idanu ta tana hawaye bata taba imaging wahalar da suka sha ba sai yanxu, kuka sosai suka dungayi Harda malam labaran saya dafe kanshi shima yana hawaye, dukda memory dinshi bai dawo ba gaba daya, don Har lokacin komai blurry yake zuwan mashi akanshi,tabbas waennan yayanshi ne yana ji a jikinshi ko ba a fada mashi ba, jininshi ne su.
Amar ne ya katse su da nashi bayanin “bayan Allah ya hadani da aisha a uae inda aure ya hadamu na yarjejeniya akan zata samu katin kasa don ta kawo kannenta nan kasar, da farko ban yarda ba wanda hakan yasa nayi kwakwaran buncike akan ta da kannenta, a bunciken da nayi tabbas ba a yi declaring mutuwar iyayen ta ba,saidai an barshi blank inda akace sunyi accident sun kone, da farko naso nayi buncike saidai kuma daga baya na ajiye don ba hurumin a bane saboda da kanta ta shaida mun iyayenta sun mutu, sannan banma san waye muhammd din da suke magana akai ba saidai nayi amfanin dashi don na kubutar dasu daga cikin wahalar da suka shiga inda matar shi alhaji Mustapha tasa a zubar dasu su shiga duniya, wannan dalilin yasa na kawo su nan gurin ammah”
Shuru kowa yayi babu abunda sukeyi sai hawaye Harda ammah ma dake zaune tana jin wannan masifa irin haka,ace Wai dan uwanka jininka yayi maka wannan rashin imanin, koda yake abun bai girgizasu ba ita da Amar saboda kusan similar abunda sukayi facing kenan watannin da suka wuce achan baya,
Dagowa malam labaran yayi yana hawaye sosai yace “tabbas ko ba a fada min ba waennan yaya na ne, kuka jini na ne, ban mutu ba da raina, dukda Allah bai bayyana min komai ba akan rayuwar da nayi a baya ba, kuzo nan”
Ya karashe yana Mika masu hannu yana hawaye,
Mikewa salima tayi daman kamar jira take tare da Salim suka taho inda yake zaune suna zama ya rungumosu gaba dayansu zuwa jikinshi babu abunda yake furtawa sai “Allah na gode maka,”
Amra dai na zaune kanta a kasa Har lokacin bayanin salima na cinta sosai, babu abunda takeyi sai blaming kanta sosai.
Kuka sosai suka dungayi a jikin malam labaran, ammah ma na daga zaune tana kallonsu tana hawaye Amar dai sauke kanshi yayi kasa bai ce komai ba jikinshi shima ya mutu, suna maqale a jikin malam labaran ya sauko kasa kan knees dinshi yana shirin dukawa kasa, “hajiya bansan da wani baki Zan gode maki ba keda yallabai, kunyi min komai a duniyar nan, bayan ni da kika taimaka Harda yayana marayu, babu abunda Zan iya saka maki dashi saidai nayi maku fatan Alkhairi keda yallabai, Nagode Nagode Nagode yallabai”
Cikin sauri Amar ya miqe tsaye ya taho gabanshi ya daga shi sama ya maidashi kan kujerar ya zauna dashi “dan Allah Kar Ka duka mana ka daina gode mana,dan Allah”
Ammah ce ta share hawayenta ta kalleshi itama tace “ malam labaran Ka daina gode mana ka godewa Allah shine ya kaddara Duk wani abunda ya faru harya hadamu dakai muka taimakeka kuma shine ya hada aisha da Muhammad Har ta sanadiyar hakan ya taimaki kannenta”
Kanshi a kasa ya kasa kallonsu ammah yace “hajiya bazan fasa gode maku ba, dole na gode maku, Kun yi min abunda bazan taba mancewa ba Har naje ga mahallaccina, Kun gama min komai hajiya,”
Komawa Amar yayi mazauninsa ya dan nunfasa yana kallon inda amra take kafin ya kauda kanshi gefe ya fara magana
“Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya bayyana komai, Allah ubangiji ya kauda Duk wata tsautsayi da masifa, zanyi dogon buncike akan wannan alamarin kuma dole justice must be served ”
“Ah ah yallabai karkiyi buncike, na bar su da Allah Duk wanda ya cucemu, bana fatan past memory na ya dawo saboda babu abunda ke ciki sai baqin ciki, wannan ma kadai ya isheni, na barshi da Allah kawai”
Nunfasawa Duk sukayi Har lokacin kan amra a kasa yake gaba daya ta zama weak, kunyar dagowa ma take ta kalli Abban nasu da su salima,
“Zo aisha” malam labaran ya fada yana kallonta yana hawaye, don yafi jinta sosai aranshi akan sauran yaran, hakan ya tabbatar mashi da yafi kusanci da ita sosai, shuru ta kasa dagowa ta kalleshi saida ammah ta kirata
“Aisha!!! Kije mahaifinki na kiranki”
Dan dagowa tayi idanunta yayi jaa sosai kafin ta sauke kan nata kasa ta mike jiki a mace, tana zuwa gabanshi ta durkusa ta fashe da kuka, saurin kamo hannunta yayi ya rungumeta yana hawaye shima, ya rasa wasu kalamai zaiyi using, tana da wani babban furgice a zuciyarshi, daman soyayyar dan fari dabance a zuciyar uba, sun dade sosai tana hawaye yana hawaye saida sukayi mai isarsu suma su salima suka rungumeshi, gaba Dayan su Ganin abun suke kamar a mafarki, abbansu bai mutu ba yana raye a Doran kasar tsawon shekarun nan ba tare sun sani ba, ashe suna cikin inuwa daya dashi, lallai daddy ya cucesu yayi masu cutarda Allah kadai ne zai saka masu, for the past years ya raba su da iyayen su sannan ya wulaqanta su saboda wani dalili nashi chan da basu sani ba.
Aman daya shigo tun bayan shugowar salim tun bai kaiga karasowa bama bakin kofar kunnenshi suka jiyo mashi Duk bayan nan da suke yi, da farko bai gane wani labaran din suke magana ba saida ammah tayi bayanin yanda suka taimakeshi akan hanyarsu lokacin da sukayi tafiya shida ita, nan take ya gano wani labaran din suke magana, hankalinshi ba karamin Tashi yayi ba don yaci mutuncin malam labaran sosai achan baya, musamman idan yake kai mahai taki chan gona don Akwai lokacin daya zageshi ma ya bishi da kalamai marasa dadi, tunda ya taaya jikinshi ke bari ya kasa takawa ya shugo parlorn kunya ta gama lulubeshi yanxu ya salima zataji idan ta gano irin cin muguncin dayayi ma ubanta don Har wankin mota saida ya saka shi, yana nan tsaye kamar ya Dora hannu aka haka yake ji, bayan wannan bayanin da salima tayi shima ya girgiza shi sosai na wahalar da suka sha, tausayi ya da kaunarta na ninkuwaa zuciyarshi he wish shine ya taimake su ba Amar ba qila da wannan zaisa malam labaran ya yafe mashi akan abunda yayi mashi, dukda yanzu he’s a changed man.
Amra na gefen Abban nasu ya shafa kanta yace “Aisha Allah yayi maki albarka,kin kula da kannenki ki saka su as your top priority, allah yayi maku albarka ku duka”
Gaba daya suka amsa da Ameen..
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.