Auren Katin Kasa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Katin Kasa Book 3.docx
Chapter 1 of 52
***AUREN KATIN KASA BOOK3***
Romatic love story
Written by QUEENMARH
GARGADI!!! KARKI KARANTA LITTAFIN NAN INKINSAN BAKI BIYA KUDIN LITTAFIN BA, IDAN KIKAYI KO KAYI HAKAN NA BARKU DA ALLAH.
Chapter 105
Update….
Yau Monday kamar koda yaushe tun karfe bakwai ya gama shirinsa tsaf cikin kaki yayi matuqa amsar jikinsa sosai, saida ya feshe jikinsa da nora mens black perfume, yayi matukar kyau sosai, duban gefen wajen couch yayi ganin tana baccinta hankali kwance idanunsta a lumshe zara zaran eye lashes dinta sun kwanta lub fuskanta tayi fayau so cute hijab dinta ne maqale a wuyanta kamar kullum har mamaki yake ko gajiya batayi da sakawa saidai tunawa da shi ya haneta da zama babu hijab din ya sahi yin kwafa ya kauda kanshi gefe, mamakin yanda hes into her yake dukda yaqi believing hakan yanxu ta daina kwanan sitting room don tun bayan lokacin da investigators dinnan suka zo ta daina kwana achan shima bai hanata kwanan dakin ba saidai baiyi yunkurin yi mata tayin kwanciya akan gadon shi ba don bashida plans akan wannan, zazzabinshi kam yanxu yana dan sauqi sosai ba kamar da ba dukda doc yayi warning dinshi kan idan ya bari har zazzabin ya rinjayi kwayoyin lafiyar jikinshi zaizo ya daina saidai hakan yana da risk sosai don side effect din unfreezing din da akayi mashi ne
Tunda ya mata kalo daya bai sake kallonta ba, har y agama duk abinda zaiyi kafin ya janyo wayanshi ya tako har inda take, ganin wayanta a gefenta ya sahi sanya hannu ya dauka ya fuce daga dakin, fucewa yayi cikin natsuwa har gaban inda m5 yayi parking, shigewa ciki yayi bayan m5 ya mashi gaisuwa irin tasu na sojoji, aje wayoyin yayi a gefensh kafin m5 yaja motar suka wuce, relaxing kanshi yayi a jikin kujeran motar ya rufe idanunshi kamar maijin bacci abubuwa da dama suna yawo a kanshi, abunda yafi bashi mamaki shine ya duk sanda yake zaune shi kadai sai yarinyar nan ta fado mashi arai saidai yana danganta hakan da tausayinta da yakeji da kanneta da yanxu sun saba dashi sosai don duk a tunaninsu shine abokin ya muhammd daya zama gatansu a yanxu, shima sarai ya gane cewa suna mashi kallon abokin yayansu saidai basusan cewa shine ma ya daukesu harya kawosu gidansu don yayi protecting dinsu, duk zamannnan da sabon da yayi da yaran bait aba hadata dasu ba kuma baiyi tunanin hakan ba sbd nashi kudirin, saidai yayi alqawarin watara zaiyyi reuniting dinsu lokacin daya dace.
Gaban headquarters m5 yayi parking motar oga general kafin ya bude mashi, ahankali ya sanyo kafafunshi waje ya fito cikin kamewa da isa, gaa daya y agama bade compound din da kamshinsa mai dadin gaske, takowa ya soma yi harya wuce first security entrance anata sara mashi gwanin burgewa, daga masu hannu ya dungayi kafin ya wuce kowa na yabawa da kwarjini da isa irin nashi, yana shiga reception ya wuce lift zuwa last floor na bulding din m5 biye lift din na budewa ya tako gaban wajen helicopter din da ke jere kusan guda biyar a fadin wajen, kallon freshers din yayi basuda wani yawa daman basufi su ashirin ba, sai yan medicals suma su biyar, kallonsu yayi cikin saurin m5 ya rada mashi cewa mss amra bata zo ba, girgiza kai kawai ya basu go ahead kan cewa su wuce daman yana sane da ita don dalilin dauke wayanta da yayi Kenan don yasan saida wayanta zatayi komai ciki kuwa harda requesting ride harda payment,nan take kowa ya kame aka sara mashi ganin general gaba daya, kallonsu yayi kafin ya bada umarni kowa ya shiga cikin helicopter din, guda daya ne basu shiga ba wanda ta fita daban daga sauran guda hudu, shima shigewa yayi kafin m5 ya sara mashi don bandashi za ayi tafiyan ba daman ya barshi ne ya lura da wasu abubuwan da sukeyi cikin sirri, kafin ya wuce ya kalli m5 yace ‘’get her a new phone and a sim I will send her passport information,’’
Kamewa m5 yayi yace ‘’yes sir’’ kafin suma nasu helicopter din ya tashi sama.
Suna wucewa m5 ya soma buga calls ‘’the plan is going smothly’’
Fucewa yayi daga cikin headquarters ya sayo sabuwar bugaggiyar iphone 14 pro max deep purple tare da sim card ya saka mata a ciki, yana gamawa yayi setting wayan ya tura ma ogan shi number ta kafin ya wuce apartment domin ya kai mata, koda ya karasa yayi knocking kamar jira take tayi saurin budewa idanunta yayi tsurtsuru don tsoron abunda zai biyo baya takeyi na qin zuwa private training da aka saka ta aciki, tana ganin m5 yayi saurin gaysheta sanin matsayinta a wajen oga kafin ya miqa mata sabuwan wayan yace ‘’oga yace a kawo, sannan yace zan dunga zuwa kaiki aiki from tomorrow’’
Shuru ta danyi kafin ta kalli ledan da yake bata, godiya ta mashi kafin ta rufe kofar ta koma ciki, zama tayi a sitting room din tana mamaki me Kenan, saurin budewa ledan tayi ganin kwalin iphone 14 promax irin tashi saidai nashi black color ne ya sata gwalo idanunta sosai sai alokacin ta gane komai, ashe shine ya dauke yar iphone x mas dinta da take riritawa, juya wayan ta soma yi, take wani irin farin ciki ya lullubeta sosai kafin ta kunna ganin an mata setting komai yasata shiga cikin wayan tana dube dube, ganin bbu contacts dinta ya sa hankalinta tashi, number daya ne a ciki shima na kasar ne kuma tasan ba number haifa bane, aje wayan tayi a gefe ta raftaka uban tagumi tama rasa wani tunani zatayi.
Chan bangare amar kuwa suna isa suka far training babu zama, sun dauka kusan kwana biyu suna tsattauran training, mamaki yake sosai yanda suk sanda za ayi training shida hammam sukeyi saidai this time araound babu hammam babu labarinshi karshe ma dai samun leave report dinshi yay akan cewa zaije india tare da babanshi health check up, share alamarin shi yayi ya maida hankalinshi kan abunda yazo yi.
Kwana biyun da sukayi sun samu wahalan network don gaba daya babu network a inda suke sai a kwana na uku ne suka samu network ya dawo, sai a lokacin ne ya samu damar yin wasu ayyukan ciki kuwa harda sakon m5 wanda ya shaida mashi komai yana tafiya daidai saidai sakon karshen ne ya bashi mamaki sosai ya sanya shi cikin zulummi, nan take ya samu kebatccen waje yazaune tare da bude laptop dinshi ya soma research, hoton susupect dinsu ne ya bazu a labaran naigeria da duniya gaba daya akan cewa babban drug dealer from nigeria, mamaki ne karara a fuskanshi da tsoron abunda zai biyo baya tunda gashi yanxu dai komai ya soma bayyana saidai duk sanda siriin empire dinan ya soma tonuwa idan ana gab da kamasu komai ke rugujewa saidai yayi alqawari wannan karon komai zai faru saiya ganosu nan take ya umarci m5 daya tura mashi gaba daya backround check da mutumin, shuru yayi ya soma karanta background din yaron ciki kuwa abubuwa dadama sun bashi mamaki nan take tunani da yawa ya fara wanzuwa akanshi background check dinma dakyar m5 ya samu don koina akayi bincike akanshi ba a samun komai, a rude ya bude wayanshi ya shiga emails dinda private investigator dinshi ya tura mashi ganin address da profile din yaron iri daya ya sashi dogon nazari, tunawa da wani abu ya sashi bude report file din suspect din nan komai ya futo daga kan time din da aka kamashi da hospital report dinshi da kalar kwayar da yake safarar ta da aka samu a cikinshi, nan take ya soma comparinsing sai kawai ya kece dariya kawai chan kuma ya tsuke fuska yana mamaki sosai, menene alakar yarannan da kwayarnan, idan bai tuna ba lokacin da kannenta ke asibiti daya daga cikinsu an gano kwayar taso ta mashi lla saidai abunda ya kasa ganewa shine ashe dama chan kwayar daga Nigeria ake yenta ne kokuwa suma zuwa tayi nan kasar ganin ya rasa amsoshinsa yasa ya dukufa da nashi binciken, bayason wani tunani daban don haka ya soma bin komai a sannu a hankali.
Bangaren amra tun bayan ya tafi ta samu sakewa sosai a gidan, kullum kuwa m5 ke zuwa ya kaita headquarters sannan lokacin tashi ma da kanshi yake daukanta cikin daya daga cikin motocin general dake penthouse dinshi, sannu a hankali zancen aurenta da general ya soma fitowa, dalilin kawota da m5 keyi a motar oga kwata kwata wato general saidai sanin girman general din yasa babu wanda ya tunkareta da maganar saidai gossip dake yaduwa kamar ruwa.
Cikin kwanakin haifa ta dawo aiki, ba karamin dadi amra taji ba saboda tayi kewanta sosai, saidai ganin yanda haifa ta chanza sosai ta rame yasa hankalinta ya tashi, saida sukayi round medical check kafin suka wuce office din haifa, zama sukayi cikin hira amra ta jefo mata tambayan dalilin chanzawanta, nan take ta mata bayanin abubuwan da suka faru tsakaninta da hammam, ba karamin tausayinta amra taji ba don ita kadai tasan yanda kawarta ke sanshi saidai abunda yafi bata mamaki shine dalilin daya rabu da ita, shawarwari amra ta bata tare da tausasa ta harta warware tayi alkawarin mantawa dashi har abada.
Hira suka sha sosai inda amra ke tambayanta jikin abuh wanda ya ji sauqi sosai, karfe hudu daidai suka fito, kamar koda yaushe suna fitowa m5 yayi parking motar shi gaban entrance na shiga asibiti, nan take mutane dake wucewa tsakanin headquarters da asibiti kowa yay a zuba masu idanu,kallon amra haifa tayi don tayi mamaki sosai, murmushi haifa tayi kafin tace ‘’mrs general, har anyi nisa ne ban sani ba’’
Kauda kai amra tayi takai zata dan bugeta tace ‘’hmm so much has happen, shiyasa nayi ta kewarki sosai,’’
Bude jakanta tayi ta dauko wayar daya bata ta kalli haifa tace ‘’I lost my other phone, bani contact dinki’’
Kallon wayar haifa tayi batace komi ba ta saka mata contact dinta kafin suyi sallama ta wuce cikin motar m5 ya zagaya ya bude mata ta shige.
Tana isa gida ta aje jakanta da laptop dinta ta wuce dakinshi soma tube kayanta don a gajiye take, saida ta rage komai daga jikinta ya rage daga ita sai dogon tight da bra daman abayace kamar kullum,
Wucewa tayi cikin toilet din ta watso ruwa kafin ta fito daure da towel dinta, gaban clost dinshi ta bude ta dauko kaya marasa nauyi doguwan riga kafin ta wuce kitchen tasha cereal, ganin lokacin sallah yayi ta koma toilet ta dauro alwala tayi sallah,
Kan couch ta koma ta janyo wayar, number haifa tayi dialing, ringing daya biyu ta dauka, hira sukaasha sosai kafin haifa ta soma tambayanta bayanin abunda idanunta suka gani dazu, shuru amra tayi kafin ta soma bata labarin komai da zaman da sukayi a kwanakin da batanan, wani irin ihun murna haifa tayi tace ‘’babe you guys are in love inba haka ba meysa zaisa a dunga private bodyguard din general gaba daya zai dunga hidima dake haka ’’
‘’babe nifa bansan dalilin shi nayin hakan ba’’
‘’Okay now tell you are you in love with him’’ haifa ta jefo mata tambayar
Shuru amra tayi gabanta na bugu sosai tace ‘’babe noo, ke kinsan wannan yafi karfina, infact nima hes not my…typ…’’
bata bari ta karasaba tace ‘’uhmmmm, yanxu ki fadamin, did anything happen between you guyss’’
Da sauri amra tace ‘’kamar me kenan’’
‘’babe you know what im talking about’’
Banza amra tayi da ita tace ‘’babe kinga wannan general din yanada wni irin hali da baka gane mashi, ina tausayin matar da will end up with him,talking of wani abu haif kokin manta ba auren gaske bane wannan, auren yarjejeniya ne fa, how can I just give him my body bayan nasan ina samun abunda nake buqata shima ya samu abunda yake buqata shikenan kowa zaiyi hanyanshi and beside kinga na kusa gama housemanship dina’’
‘’hmmm babe kedai kawai abar maganar’’
Dariya haifa tayi kafin ta cigaba ‘’talking of yarjejeniya, shi ya fada maki me yake buqata ne?’’
Shuru amra tayi don all this time bata taba tambayanshi mey yake buqata ba daga wajenta da har ya amince ya aureta, gyara zaman wayanta tayi a kunnenta kafin tace ‘’ban tambayeshi ba, and baice komai ba,but babe me kike tunanin zai buqata daga wajena sbd im very sure ba haka kawai ya amince ya aureni ba don na samu citizenship ta karkashinsa’’
‘’babe time is not on our side, ina ganin ki tambayeshi kiji mey yake buqata daga wajenki kinga yanxu yanda kuka fara zama topic of discussion a cikin headquarters saidai ina tsoron kinsan yanda zance zaita yawo’’
‘’haif nibazan tambayeshi ba tunda baice komi ba,’’
Basu wani dade da hiran nasu ba ta sukayi sallama.
Tana aje wayan ta lumshe idanunta tana tunani kalaman haifa, tunanishi ne ya fado mata da moment dinsu tare, tabe baki tayi kafin tace ‘’ina tausayin matarda zatayi rayuwa da wannan mutumin da baka gane mashi’’
Shanye tunanin tayi har bacci ya kwasheta, bata wani dade da baccin ba wayanta ya soma ruri, da sauri ta janyo wayan don baccin nata baiyi nisa sosai,tayi picking, cikin muryan bacci tace ‘’allo’’ tare da sauke nunfashinda ya sashi runtse idanunshi sosai don ya jishi ne har cikin tsakiyan kanshi
Shuru taji daga chan bangare saida ta sake maimatawa kafin ya sauke ijjiyan zuciya da nunfashi a tare wanda ta jishi har kwakwalwarta, bude idanunta tayi sosai ta zare wayan daga kunnenta ganin unknown number yasa ta maida wayan kunnenta ta sake tambaya ‘’hellowww’’
Jin anyi shuru ya sata tsaki don bata kaunar abunda zai katse mata baccin ta, bata kaiga kashe wayanba yace ‘’did you just hiss ’’
Gabanta ne ya fadi don bata taba tsammanin kira daga wajenshi ba kwata kwata, mikewa tayi zaune kamar yana gabanta ta sauke kanta kasa tace ‘’ím so sorry bansan kaine ba’’
Shuru yayi chan kasan maqoshi yace ‘’baki iya….’’
Bai karasa ba ta tari nunfashinsa ‘’ina wuni ya aiki’’
murmushi yayi sosai don yanda ta fada saiya bashi dariya, guntse dariyan yayi yace ‘’is everything okay over there, do you need anything’’
bata gama mamakin daya bata ba da tambayoyinshi ya sake jefo mata wata ‘’is there anything suspicious around you’’
tsintar kanta tayi da murmushin da bata san dalilinshi ba tace ‘’alhamdullilah, everthing is okay’’
jin shurun yayi yawa yasa itama tace ‘’hows your health?’’
baiyi tsammanin tambayn nata ba saidai kuma yaji dadin tambayar ‘’alhamdullah’’ ya amsa mata ataqaice kafin ya kashe wayan, jin alamun ending call din da yayi ya sata tabe baki tace ‘’ikon allah’’
aje wayan tayi gefenta ta cigaba da baccinta.
Kwanan su amar goma cip wajen training ya samu kiran gaggawa daga highest attained rank na army gaba daya, cikin kwanaki goman nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda wanda yayi preparing kanshi, ranar da zai dawo ya riski abubuwan da suka bashi mamaki sosai don baiyi tunanin hakan ba, ciki kuwa shine ya gano da hannun hammam dumu dumu cikin waenda keson rufe zancen suspect din da aka kama, yanda ya gano hakan kuwa shine, tun bayan tafiyarsa training hankali alif shuraim wato baban hammam ya tashi wanda yasa hammam amfani da duk karfin da yake dashi a cikin headquters don ya toshe maganar saidai abun ya faskara sosai, daman already an karbo shi susupect din daga hannun officials din da suka kamashi, lokacin da zancen yazo kunnen alif cewa yaron yana hannun army hankalinshi ya tashi sosai sanin waye general a yanxu da sun kasa samun abunda zasuyi using don suyi amfani dashi yanda suka saba akan sauran da suka karbi mukamin har sukayi retire ko suka bar aikin gaba daya,ganin basuda wani option dole sukayi amfani da abubuwan da suke dashi don ganin sun ci nasara akanshi, abunda yafi bama amar mamaki shine yanda kiri kiri babu wani kwana kwana amininshi wato abokinsa ya futo ya nuna asalin shi waye, a day before ranar da za ayi mashi kiran gaggawan kiran hammam ya shugo wayanshi, baiyi expecting call dinshi a wannan lokacin ba.
Gaysawa sukayi kamar yanda suka saba kafin ya soma Magana ‘’dude, weve been friends for over 8years now, and don’t be surprised with what I will be asking you now, inason ka cire hannunka daga research din da kake nasan ka gane me nake nufi’’
Murmushi amar yayi don baiyi mamakin hakan ba kwata kwata,
‘’dude why, why are you doing this, koka manta abubuwan da kake kowa zaiyi considering din wannan as betraying army gaba daya why’’
Dariyan yaqe hammam yayi yace ‘’oh so ka san komai Kenan, then why did you pretend’’
‘’yes na gane komai tun ba yanxu ba tun last general da kukayi threating ta hanyar using wani wrong doing dayayi achan baya,’’
‘’So why did you pretend’’ hammam yayi saurin tabayan shi
‘’ saboda na baka wani chance da benefit of doubt hammam why? Tell me why are you doing this tun chan baya kaike protecting dinsu kaida mutanenka, ka zama mai liken asiri, shin kayi tunanin outcome din hakan idan har gaskiyan cewa daga cikin the most secretive and hardworking officer kamar kai, mai kake tunani za ayi tunani idan aka gano cewa daga cikin masu kokarin protecting kasar gaba daya cikinsu akwai corrupted ones , im so disappointed dude ’’,
Idanunun amar ne sukayi jaaa, yanda yake magana zaka gane hes hurt sosai,
‘’waye ke saka ka hammam, who are the empires, dude you need to wake up before its too late, this people are dangerous, they kill, they manipulate, they detroy a lot of family, shin kasan irin mutane nawa muke rawasa duk a shekara ta dalilinsu ta hanyar trafficking yara da kwayar da suke producing, kana da damar kawo karshen su,’’
‘’I didn’t call you to listen to all of that, just do as I say, stop the investigation if you don’t you’ll regret it’’ hammam ya fada ba tareda ya wani damu da abunda amar ke fadaba
Nunfasawa amar yayi kafin yace ‘’do your worst’’ yana kaiwa nan ya kashe wayan, zuciyanshi zafi take mshi sosai, bai taba tunanin idan har yayi confronting hammam abunzai mashi zafi haka ba, ko lokacin daya gano komai game da sa hannun hammam wajen rufe duk wani hanyar samun evidence na kama kungiyar ba saidai yasan cewa akwai mastermind behind hammam din shima yana kyauta zaton manipulating dinshi akeyi wanda dalilin hakan yasa baita ba nuna mashi ya san komai ba don tun lokacin da yaje wani secret operation tare da m5 don kamo su ya gano cewa da hannun hammam.
Washe gari kuwa sakon gaggawa ya iso mashi wanda ya katse masu training din da ya kamata su gama cikin kwana hudu, koda helicopter ya iso daukan gaba daya freshers hardashi yayi mamakin ganin yanda security dinshi ya karu sosai, saiya zamana kamar criminal akazo dauka, bai kawo komai a ranshi ba don yasa ko baibada umarni ba dole yana da nashi security din, suna isa headquarters kuwa ya wuce direct inda ake emergency meeting security dinshi biye dashi a baya, tunda aka bude kofan shiga ya shige ba tare a wani tunani bay a zaune a kujeran dake tsakiyan wajen, daman yayi expecting hakan, saida ya sara masu don manyanshi ne sosai kafin ya zauna.
Wani solder ne ya matso ya aje mashi wasu papers a gabanshi kafin ya koma ya tsaya kyam,
‘’General Muhammad Taura’’
‘’yes sir’’yayi saurin amsawa
‘’mun samu labarin kana da sa hannu cikin illegal auren da kasan government din uae sun haramta hakan, wanda we believe kasan cewa hakan is not accepted a nan kasar, wannan gaskiya ne’’
Kallon papers din gabanshi yayi ya som karantawa tsaf kafin ya dago yace ‘’yes sir’’
Daga daga cikin manyan ne su uku yace ‘’did you know the consequences of that’’
‘’yes sir’’ ya amsa babu tsror babu fargaba
‘’did you know that this will affect your job with no plead’’
‘’yes sir ya sake amsawa
‘’did you know that this will ban you and your citizenship of the uae’’
‘’yes sir ya kuma amsawa
Shuru wajen ya dauka kafin su cigaba
‘’we hearby declare you under suspension of favourable personnel action, youll be under our supervision for more investigation’’
Mikewa duk sukayi kafin ya sara masu suka fuce, kanshi ne ya soma sara mashi don baiyi tunanin abunzai kaiga haka ba idanunshi kuwa sunyi jaa sosai, sanin abunda suke nufi ya sashi wucewa securities din biye dashi har wajen da floor din da ake investigation daki ne babba wanda shi kadai ne a floor din an zagaye dakin da sound proof glass, saida aka amshi riganshi dake da rank dinsa a jiki ya zamana daga inner white riganshi sai dogon wandon army nashi hatta wayoyin duk sun amshe, zama yayi kan kujeran dake dauke da table din kafin ya dafe kanshi dake sara mashi, bayason tunanin komai hakan yasa ya dafe kanshi don samun sauqin ciwon kan dake damunshi sosai.
M5 ne ya shigo dakin tare da sara ma ogan nashi, dago rinannun idanunshi yayi ya kalli m5 kafin ya gayar zamashi ya fuskanceshi ‘’have you done it’’
Da sauri m5 yace ‘’yes sir everthing is ready, and im sure she has arrived by now’’
Resting bayanshi yayi kafin ya cigaba ‘’in 2 days I will ban from the uae government, just as we planned, I have prep all the evidence through secretive portal,nayi linking dinka to the portal, don’t take any action until you receive my alarm’’
Kamewa m5 yayi kafin yace ‘’yes sir’’ ya sara mashi ya fuce.
Tun baya fitar m5 babu abunda ke mikar dashi sai sallah da zuwa toilet a cikin dakin, koda aka kawo mashi abunci baima bi takan abuncin ba.
Bari mu leka amra…
Tun bayan tashin datayi da asuba ta tashi da fargaba, jikinta gaba daya yayi weak tana jin alamun kamar wani mummunan abu zai faru, wanka tayi hade da sallah kafin ta zauna nan kan sallaya hawaye na zubo mata don idan taji irin wannan halin tana alaqanta shi da qila wani mummunan abu ne ya faru da kannenta, wunin ranar tayi shi ne cikin sanyin jiki hade da ciwon kai mai tsanani karfe bakwai na dare taji karar door bell, mamaki ne ya kamata sosai hade da tsoron daya dirar mata babu zato ba tsammani, miqewa tayi sanye da hijab dinta har kasa ta wuce parlor, jin an sake danna door bell din ya sata saurin budewa, ganin m5 yasata mamakin zuwanshi a daidai wannan lokacin, babu wani bata lokaci ya gaisheta kafin ya mata bayani tafiyanta ‘’maam, you will have to leave the country now’’
Hankalinta ne ya sake tashi dan ta kasa gane me yake nufi dakewa tayi kafin tace ‘’may I know why’’
‘’in 24hour you’ll be arrested for trying to get uae citizenship’’
Hankali a tashe ta kalleshi tace ‘’whatt, please explain to me the way I can understand kamin bayani yanda zan gane?,’’
‘’we don’t have time now, ma’am, your flight is in 30 minutes,’’
Juyawa tayi hankali a tashe ta koma dakin, hawayene ya soma gangaro mata a fuskanta wanda ta kasa gane dalili, meke shirin faruwa Kenan, bude closet tayi ta dauka bakin abaya ta saka kafin ta janyo karamin box dinta tayi ta zuba few kayanta a ciki kafin ta janyo laptop dinta da wayanta, fitowa tayi yanda tabarshi anan ta sameshi tsaye bakin kofar, karban box din nata yayi kafin ya rufe kofa tabi bayanshi, cikin motar yasa mata box dinta kafin ya bude mata ta shiga shima ya shiga suka wuce, abubuwa ne da dama ke yawo a kanta ciki kuwa harda general da makamin karatunta, kukane ya kufce mata mara dalili, wannan wace irin kaddara ce, ta kasa gane inda aka samu matsala, general ne ya fado mata rai yanxu shi wani hali zai shiga kenan, inhar ita kamata za ayi shi kuma aikinsa fa shida yake babban mutun a kasar kuka ne ya kufce mata hankali tashe ta kalli m5 tace ‘’uhm please whats going to happen to him, dan allah ka fada min meke faruwa’’
Cikin airport din yayi parking kafin ya zaro mata wasu takaddu ya bata hade da passport dinta ganin yanda take kuka ya sashi cewa ‘’karki damu, he will be fine,ga passport dinky, ive made an arrangement, akwai motar dazai daukeki idan kun isa, sir will join you soon’’
Innalillahi ta soma furtawa, dakyar m5 ya tausasa ta ya mata sauran abubuwan daya dace ya mata sallama ya tafi.
Samun waje tayi a airport din, nan komai ya dawo mata kamar mafarki, tundaga lokacin data iso kasar, allah kadai yasan irin farin cikin da take ciki sai gashi yanxu kuma zata koma kamar mafarki take ganin komai, yanxu ya makomar karatun nata Kenan, me zata cema daddy idan ta koma, mai zata tarar idan taje chan, runtse idanunwata tayi hawaye na kwaranyo mata, gaba daya baifi mata wata uku ta gama housemanship din shima sbd extention data nema ne anan asubiti na haousemanship da takeyi na additional 3 months don ta don samu ta tara kudin da zata biya daddy bayan wannan ma gashi kuma yanxu komai ya juya, cikin yan mintuna akayi announcing jirginsu, mikewa tayi hawaye sharr a fuskanta harta wuce harabar jirgin, koda suka tashi tunani iri iri ne a ranta, yanxu makomar karatunta ma bashine damuwanta ba, sir general ne damuwanta, wani hali ta jefa shi, da career shi, idan har ita arresting dinta za ayi shi kuma fah, a wani hali yake ciki, koma wani hali yake ciki ita ta jefa shi tunda itace ta nemi taimakonshi daya ya aureta dukda sunsan illegal ne a kasar, idanunta ne sukayi jaa sosai, anya ta kyauta kuwa, tanajin kamar tayi butulci, tambayoyi ne burjik a kanta wanda ta rasa wanda zai amsa mata su, na farko ya akayi m5 yasan za ayi arresting dinta, ya akayi asirinsu ya tonu, sannan a wani hali yake ciki yanxu ganin babu mai bata amsosahin ta yasata fashewa da matsanancin kuka sosai har baccin wahala ya dauketa.
Sama sama ta dunga jin Magana akanta, bude rinannun idanuwanta tayi da sukayi jaa sosai kafin saukesu akan crew din dake tashinta, ‘’ma, weve arrived’’
Juyawa tayi ganin bbu kowa cikin flight din har garin ya waye yasata mikewa ta janyo karamin box dinta hade da laptop bag dinta da wayanta, takowa tayi ahankali tare da shaker kamshin kasar najeria, nan take komai ya sake dawo mata, runtse idanunta tayi kafin ta soma takawa gabanta na mugun bugu sosai harta futa daga harabar jirgin,saida ta tsaya ta gama clearing komai don daman daga dubai to Abuja ne booking din da m5 yyi mata,duban wayanta tayi da charge ya sauka kasa, rasa abunyi tayi don babu kudi kwata kwata a jikinta gashi booking daya ne daga dubai to Abuja, gashi bata taba zuwa Abuja ba balle tasan inda zatabi taje car park, futowa tayi daga cikin airport din inda taxis da motoci suke dagowa tayi nan idanunta suka sauka kan wani mutumi daya daga katon board da sunanta a jiki, tunawa da abunda m5 ya fada mata na cewa yayi making arrangement dinda zai kaita gida yasa tayi handala ta daga hannunta da sauri mutumin ya karaso gabanta tare da welcoming dinta, karban box dinta yayi kafin tabi bayanshi, idanunta a kasa yace ‘’bismillah hajiya’’
Dagowa tayi ganin zabgegeiyar motar dake gabanta, ba tareda wani tunani ba ta shiga baya yaja motar suka wuce.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.