Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 9 of 35

page 10

Koda ya shiga cikin falo ya tarar da mata sai surutu suke yi wasu na cin abinci ya kaÉ—a kai ya wuce yayi sama bakin sa É—auke da tambayoyi shi dai ban san da wani biki a gidan su ba da wannan tunanin ya wuce É—akin Ammie

Sallama yayi ya tura ƙofar ya shiga aunty suwaiba matar yayansa da su Rukayya sune a cikin ɗakin ya haɗe fuska ya dudduba bai ga Ammie a ɗakin ba ya juya zai fita sai gata ta shigo "Son kai ne? Mu je ciki" ya juya Ammie ta ƙara sa shigowa suka yi ciki, su Rukayya suka gaidasa ko alamun amsawa bai yi ba Ammie tace "Please ku ɗan bamu waje" Duk suka tashi har aunty suwaiba, ya wuce ya kwanta saman gado sai yanzu ya lura da Noor dake kwance saman gadon tana bacci

"Wai taron me ake ne a gidan? Me yake faruwa?" Ya faɗa yana lumshe idanu " Hidimar auren ka muke yi" Kamar wanda bai ji abunda tace ba can ya zabura ya miƙe ya kalli Ammie yace " Me kika ce Ammie ?Kamar kunne na ya jimin ba daidai ba" Ammie tayi murmushi tace" Hidimar auren ka yau aka ɗaura ma aure " ta faɗa tare da wucewa wajen fridge

Azaad ya nuna k'irjinsa da hannu yace " Ni aka ɗaura ma aure" Yayi wani murmushi wanda yafi kuka ciwo, Ammie ta miƙa masa lemon da ta ɗauko masa yace " Ammie wai gaske kike ko wasa?" Mun taɓa irin wannan da kai Azaad baka ji ba yadda daddynku bai yi ba akan ka fito da mata har lokaci ya sa maka amman kayi bulus nima ban so hakan ta kasance ba amman ka kai sa ƙarshe naso ka fitar da wacce ka ke so yanzu komai ya ƙare dan har an ɗaura aure nan da sati uku zata tare ya ma ce na sanar maka kasa a gyara gidan nan a zuba duk abunda babu kayan abinci a kai komai da ake buƙata wajen girki saboda ya sanar da iyayen yarinyar ba'a buƙatar komai " Azaad kasa magana ma yayi idanunsa sun yi jajirrr tashi kawai yayi ya fita

Kwana biyar da aure aka kawo lefe akwati dozin biyu komai an saka mata cikin lefe babu ne kawai babu a ciki, Mommy da ka kalleta zaga ka baƙin ciki ƙarara a fuskarta bata taɓa tunanin arzikin su yakai haka ba sai yanzu da aka kawo lefe da kayan sa ruwa kuka zahiri ne kawai bata yi ba amman tayi na zuci dan tayi nadamar k'in amincer da tayi tun farko da yanzu y'arta ce da wannan kayan sai yadda suka so amman yanzu Mamma ta hakimce komai sai yadda tace ayi haka ake yi, tsawon sati biyu Mamma na bama Alesha maganin sanyi sannan ana mata dilka ta gyara jiki sai da akayi sati biyu ciff sannan ta fara bata wani hatsabibin maganin mata mai kyau da inganci tsumi mai kyau ga gumba kala kala ko wace da lokacin da zata sha ta

'Bangaren ango ba wani shiri da ake yi ango auren nan ko a jikinsa walima kawai za'a yi ranar da amarya zata tare, An yi ma amarya lalle mai kyau ya zanu a fatarta washe gari aka yi kitso k'ananu sosai Alesha tayi kyau haskenta ya ƙara fitowa fatar ta tayi clear tun da aka ɗaura aure har zuwa yau da amarya zata tare ango bai taɓa zuwa ba bata san sa ba shima bai san ta ba babban abunda ya ƙara tayar ma da Alesha hankali kenan ƙarfe goma na safe aka fara walima saboda ƙarfe biyu gidan miji zasu turo a ɗauke ta za'a je da ita ƙarfe huɗu suma suyi walima ƙarshe shida akai amarya ɗakin ta

Sha biyu daidai aka gama walima Mamma ta ja ta suka wuce ɗaki sai kuka take, Mamma ta sa ta rage kayan jikinta ta shiga toilet tayi wanka koda ta fito daga wanka ta fitar mata da kayan da zata saka, ta shirya cikin wani material mai shegen kyau da tsada ga awarwaron hannunta masu kyau tasa sark'a mai haɗe da yan kunne da abun hannu ta yafa mayafi Mamma ta miƙa mata jakarda sai gashi an faɗa musu gidan miji sun turo motoci Alesha kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi ta rirrik'e Mamma.....................

🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*

Wannan shafin sadaukarwa ne a gareku masoyana masoyan asali 🥀❤️❤️❤️ina matuƙar k'aunar ku Ubangiji Allah ya faranta muku ya shiga lamuran ku Allah ya barmu tare, ina son ku matuƙa🧡🧡🧡💛🩶♠️❤️❤️❤️❤️🥀🌷

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.