Azaad Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: AZAAD.txt
Chapter 17 of 35
page 20
Ta zauna gaban mirror ta shafa mai ta buɗe humra ta mulke jikinta da ita ta shafa powder ta gyara girarta ta ɗauki lip liner pencil brown ta ja ta kawo lipgloss ta shafa ta miƙe ta ɗauki tufafin da ta fitar ta saka ta kawo daurin nan na zarah buhari ta yi ta koma wajen mirror ta ja kujerar mirron ta zauna ta buɗe drawer ta ɗauko wata ƙaramar akwatin ƙarfe inda sark'ok'inta suke ta ciro wata had'ad'd'iyar sark'a ta saka tare da yan kunne da abun hannu ta mayar ta kalli kanta ta cikin madubi, ita kanta sai da tayi murmushi ganin irin kyawon da tayi, atamfar tayi mata kyau ga ɗinkin da aka yi mata wanda ya ƙara fito da ita ta miƙe ta ɗauki turare ta ƙara feshe jikinta ta ɗauki wayarta ta koma gefen gado ta zauna ta lalubo number Mamma ta fara kira
Wayar bata jima da fara ringing ba Mamma ta É—aga suka gaisa, Tana cikin wayar Ummie ta shigo da fara'arta idanunta suka sauka kan Alesha sai da cikinta ya murd'a ganin irin kyawon da Alesha tayi ta yi cass abunta kamar wacce zata je wani Babban taro na manyan mutane nan take ta haÉ—e fuska wallahi Alesha tafi Ummie da komai nesa ba kusa ba domin duk wanda yake da mata irin Alesha aka ce zai tsaya kula irin Ummie to ko kai kanka abun zai baka mamaki amman saboda So da ya rufe mata ido yasa ita bata ganin haka sai take ganin ta fita
Kasa zama d'akin ma tayi saboda har wani abu take jin yana taso mata ta fito ta dawo falo
Sun jima suna waya da Mamma sannan suka yi sallama tana kashewa kiran Yaya Imran na shigowa ( Ɗan Mamma wanda ya siya mata waya) Murmushi ɗauke a kan fuskarta ta ɗauki wayar suka gaisa shi ma sun ɗan taɓa fira sannan suka yi sallama ta tada Noor ganin lokaci ya ƙarato ta kaita bayi ta wanke mata baki, ta sa tayi alwala suka fito ta saka mata uniform ɗin islamiyya tasa hijab suka yi sallah tare bayan sun gama ta ɗauko mata jakarta suka fito falo, Ummie na kwance tana charting ta kalleta tace "Ummie lokacin sallah fa yayi"Ban tashi yi ba " ta faɗa ko ɗago kanta bata yi ba, bata sake cewa komai ba ta wuce dining ta zubama Noor abinci ta zaunar da ita ta bata, suna gamawa driver na isowa har harabar gida ta rako Noor sai da suka wuce ta tsaya tana kallon yadda gidan yake, tunda aka kawota tsawon wata huɗu yanzu ko bakin k'ofar falo ƙafar ta bata taɓa lek'awa ba sai yau da ta fito tayi tsaye tana kallan gidan da fulawowin da ke wajen
ta juya ta fara tafiya kenan aka buɗe masa gate, tun da ya danno motorsa ciki idanunsa suka sauka a kanta ta juya tana tafiya, wani abu yaji ya tsaya masa a mak'ogaro yana tunanin meya fito da ita wajen nan, koda ya isa parking space yayi parking ya fito har ta shige ciki, ran nan nasa a ɓace ya wuce ciki
Koda ya shiga bai ganta ba tayi kitchen, Ummie da ta lula duniyar charting tana kwance bata tashi taje tayi sallah ba k'amshin turarensa ya ziyarci hancinta ta ɗago da sauri ta zuba masa na mujiya ta tashi zaune Azaad ko kallan wajen da take baiyi ba tace "Sannu da zuwa yaya Azaad"Sannu "ya faɗa tare da ƙara haɗe fuska, ta miƙe tsaye ta nufi wajen da yake tace"Yaya Azaad tun d'azu nake ta zaman jiran ka kasan fa zamu yi magana amman shi ne kaje kayi zamanka " Okay kar na je gun aiki kenan ko?" Ni ba haka nake nufi ba " Mtwwssssssssssssss dallah matsa min can" ya faɗa tare da ra'bawa gefen ta ya wuce ya zauna cikin falo
Ta zo gabansa ta durk'usa ta marairaice fuska ta kallesa tace "Yaya Azaad dan Allah ka bani lokaci muyi magana wallahi maganar nada matuƙar muhimmanci idan ban sanar maka ba zan iya cutar da rayuwata ka taimakeni ni ko ma nan ne ba matsala sai muyi magana indai zaka saurare ni wallahi ba matsala " Ko da ta ƙarashe faɗa gaba ɗaya hankalin sa baya nan yana kan Alesha wacce ta fito daga d'aki tana tafe tana shan ice cream cikin kwanciyar hankali a natse, Ummie ganin hankalinsa baya kanta yasa ta ɗago ita ma tana kallan sashen da yake kallo, bata san lokacin da taja tsaki ba tana mai kawar da kanta, tsakin da ta yi ne yasa ya juyo ya kalleta
Alesha turuss ta ja ta tsaya lokacin da ta iso cikin falon ganin Ummie durk'ushe a gaban Azaad sai kawai ta yi murmushi ta ƙara so tace "Sannu da zuwa yaya"Yawwa sannu ya kike ya kaɗai ci dan nasan by this time yar' ki ta tafi school " Ai kuwa bata jima da tafiya ba"Okay bara na je na samu na watsa ruwa " ya faɗa tare da miƙewa Ummie ta rafka uban tagumi, Azaad har yayi nisa ya juya ya kalli Alesha yace "Ki dafa min tea ki kawo min"Okay "Kiyi min irin haɗin da kika min jiya" An gama " ya wuce yayi d'aki, ita kuma sai da ta ida shanye ice cream ɗin da take sha sannan ta miƙe ta shiga kitchen
Ummie kamar ta É—ora hannu a kai tace wayyooo Allah tama kasa fahimtar komai tana mamakin yadda aka yi har yanzu bata janyo hankalin Azaad gareta ba duk wannan uban wankan da matsu da rangwad'ar da take masa sai taga duk abunda take yi ma a banza, tana nan zaune a wajen har Alesha ta gama dafa tea ta fito da shi ta nufi d'akin Azaad da ido kawai ta bi bayanta da kallo
Sai da ta k'wank'wasa k'ofar ya bata izinin shigowa ta turo k'ofa ta shiga turuss ta ja ta tsaya ganin sa ɗaure da towel a k'ugu tayi ƙasa da kanta ta cikin mirror yake kallanta "Ƙara so mana" ya faɗa duk da yana shafa mai a jikinsa but still ita yake kallo ta cikin mirror, taka wa tayi a hankali kamar wacce k'wai ya fashema a ciki, wani had'ad'd'en table ta nufa ta daura cup ɗin tea a kai ta janyo table ɗin ta kawo bakin gado ta aje wajen da ta tabbatar da nan zai zauna ta juya zata fita ta tsinkayo muryarsa yana faɗin" Jira ni na gama" Ta wani marairaice fuska ta juyo kallo ɗaya tayi masa tayi saurin yi ƙasa da idanunta saboda ya juyo ya kafeta da ido gashi ba kaya a jikinsa, Alesha jin take kamar ƙasa ta buɗe ta shige wani irin nauyinsa take ji wallahi
'Bangaren Azaad kuwa ya ce ta jira sa ne kawai ba tare da wani dalili ba haka kawai ya tsinci kansa da son ganinta kusa da shi
" Ki zauna mana ko tsayuwa zakiyi kamar wata soja " Yaya dan Allah ka bari na je na dawo" Ina kenan? " Ya faɗa tare da ƙara so wa wajen ta "Akwai abunda zan yi ne" Me za kiyi?" Shi ma ya tambaya" ta wani bubbuga ƙafa a ƙasa tana turo baki "Ina jinki" Uhmmmmm uhmm daman...........uhm daman....hmm." Wallahi duk ta dabulce ta rasa me zata ce, can dai sai tace " Zan je na duba na gani idan lokacin dawowar Noor yayi " ta faɗa ne kawai saboda tana san ya barta ta fita
"Ta da kanki ki duba ga clock nan " ta ɗago kanta ta kalli agogon " Lokacin yayi?" Ya faɗa yana kallanta ta girgiza masa kai, ganin kawai tayi ya ƙara shigowa jikinta kafin tayi wani yunk'uri ta ji ya ɗaga ta sama kamar wata baby ta fara zillo amman ina ya riƙe ta sosai, sai tsakiyar gado ya aje ta
Ummie mafisa kawai take ita kaɗai a falo ganin daga kao tea Alesha ta lak'e, da wani irin sauri ta juyo da taji alamun buɗe ƙofa ta juya ta ga ba ita ba ce, a she k'ofar falo ce ta motsa ta wani ja dogon tsaki kamar bakinta zai fita " Wannan wace irin masifa ce mata daga kai tea sai ki samu guri ki yi zaman ki baya son ki bakya son sa to ba zaku rabu ba kowa ya huta wannan bala'in har ina to wallahi ni dai kam na gaji yau za'a yi ta ta ƙare ki fita ki bar min miji na.....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.