Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 26 of 35

page 33

Tana tura ƙofa sai ga Noor tsaye tana murza ido tace" Baby kin tashi?" Noor ta gyad'a mata kai tare da faɗin " Mommy zan yi fitsari" Okay mu je " ta faɗa tare da kama hannunta duk da saurin da take son tayi amman ta kasa a hankali take takawa har suka isa toilet ta saka ta fitsarin bayan ta gama tayi mata tsarki tasa tayi alwala suka fito ta bata hijab ta shimfid'a mata sallaya ta tace" Princess magrib raka'a nawa ce?" Uku " ta faɗa tare da nuna mata yatsunta uku tace" Yawwa good girl oya do it "Okay mommy "

Alesha ta wuce ta kwanta Noor ta fara sallah, koda ya shigo ya ga Noor na sallah yayi murmushin jin daɗi as her age abu ne mai matuk'ar wahala a samu yaro ko yarinya iyayenta na saka ta yin sallah har ta san raka'oin da zata yi, wucewa yayi wajen Alesha dake kwance idanunta a rufe kamar mai bacci al halin kuma ba baccin take yi ba da ta ji k'amshin turarensa sai ta ƙara lafewa
Zama yayi kusa gareta yace "Kin yi bacci ne?" Ya faɗa tare da kai hannu ya shafi fuskarta take yaji zafin jikinta yace "Subhanallah fevern ya dawo meyasa baki sanar min ba ko na kira likita ne?" A hankali ta buɗe idanunta har ta sauke su a kan sa ganin yadda ya riki ce yana ƙoƙarin kiran likita har ya lalubo number sa zai kira ta riƙo hannunsa ya juyo ya kalleta ya aje wayar gefe ya riƙo hannun cikin nasa har tafin hannun ta akwai zafi

Yace "Mene ne?" Yaya ba sai ka kira likita ba da na sha magani zai sauka " Beb ki bari kawai na kira ta kinga ko ɗazu kinyi fama da zazzaɓin nan yanzu ma gashi ya sake dawowa" Yaya ko ɗazu da na sha magani ya tafi yanzun ma da ya dawo saboda k............."Sai tayi shuru ta ƙasa ƙarasawa yace"Ina jin ki saboda me?" Ta turo baki tace"Please ni dai ba sai ta zo ba da na sha magani zai tafi "Hakan ki ke so?" Ya tambeta ta gyad'a masa kai yace " Shikenan amman idan naga bai sauka ba zan kirata kin amince?" Eh"

"Mommy! Mommy na miki addu'a"Noor ta faɗa tare da hawa gadon tayi wajen Mommynta Azaad yace "Ni kuma fa?" Mommy nayi ma "Ikon Allah gaskiya gidan nan ana nuna min son kai ba komai nima na kusa na rama wannan wulak'ancin da ake min da kin haihu" Alesha tayi dariya tare da faɗin "Yaya wulak'ancin me aka maka"Wa yasan iyaka idan nace miki abu sai ki ce y'ar ki ita kuma Mommynta komai Mommynta nima dai Allah ya nuna min kin haihu komai zamuyi daga ni sai ɗana don ma ku ji " Hhhhhh yi hak'uri"Ku zan bama hak'uri bama wannan ba me kika roƙa mata ne?" Wannan sirri ne fa tsakanin y'ar da uwa" Hmmmmmm sirri ba" ya faɗa tare da tashi yaje ya ɗauko mata magani ta sha cikin ikon Allah ba da jimawa ba maganin ya yi mata aiki zazzaɓin ya sauka

Sha É—aya da arba'in yana zaune a É—aki yana ta dubin shigowarta amman shuru hakan yasa ya tashi ya zura takalminsa ya fito ya nufi É—akin ta ya tura ya shiga, É—akin ba haske ya laluba ya kunna glub kwance ya hango su suna baccin su hankali kwance " Matar nan me take nufi ne?" Ya faÉ—a tare da nufar gadon yayi tsaye addu'a ya yi ya tofa ma Noor yasa hannuwa kawai ya tallabo Alesha ta buÉ—e idanunta da sauri ta fara mutsuniya tana zillo tana son ta sauka ya fito da ita yayi É—akin sa suna shiga ya sauke ta saman gado "Yaya dan Allah ka barni na kwana a can"Saboda me?" Yaya ita kaÉ—ai ce fa dan Allah ka barni na kwana tare da ita" Saboda Ita kaÉ—ai ce me zai cita ba inda zaki je a nan zaki kwana " ya faÉ—a tare da cire jallabiyarsa tayi saurin É—auke idanunta daga shi sai gajeren wando ya wuce ya kashe wuta

Ya hayo gado ya kwanta taji gabanta ya bada É—asssss, ganin yayi kwancinsa yasa ta gyara ta kwanta tana kwanciya ya matso kusa gareta ya janyota jikinsa "D......dan Allah y......a.....ya ky......... Kayi hak'uri" Ta faÉ—a bakinta na rawa"Mu yi bacci " ya faÉ—a ita dai duk a tsorace take da shi sai da taji numfashin sa ya sauya alamun yayi bacci sannan ta sauke ajiyar zuciya ta rufe idanunta da tunanin Noor bacci yayi awon gaba da ita

Ummie tun da ta koma ta shige ɗaki banda kuka ba abunda take yi mommy ta kasa gane kanta tambayar duniya ta yi mata amman taƙi faɗa mata abunda ke damunta, washe gari rufi ta zo ta kawo mata maganin da malamin ya bayar wanda zasu karya sihirin tana kawo mata tayi hayak'in ta kira sunan musa mai gadi sau uku tare da faɗin "Na sake ka na sake ka na sake ka "

Tsawon wata biyu Ummie duk ta rame tayi baƙi har da abincin kirki bata ci tunanin Azaad ya addabi ruhi da gangar jikinta tana gida ko ina bata zuwa mommy tun tana tambayarta har ta zuba mata ido 'bangeren su Alesha kuwa soyayyar su suke sha bilhak'k'i Azaad na nuna mata tsantsar soyayya da kulawa abun sai wanda ya gani............

🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.