Azaad Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: AZAAD.txt
Chapter 15 of 35
page 18
Kwanan Rukayya huɗu a gidan, Alesha ta sake mata fuska sosai su zauna suyi fira su yi wasa da dariya idan ka tarar suna fira kamar yaya da ƙanwa,
Ƙafarta kuwa sauran kaɗan wajen ya haɗe yanzu tana iya takawa ko ina hannu tuni ya warke daman ba sosai ta ji ciwo a hannun ba, tsakanin ta da Azaad kuwa wata maganar kirki ma ba haɗa su take yi ba amman idan Rukayya ko Noor na wajen yayi mata magana lafiya lau take amsawa idan kuma daga ita sai shi ne yayi mata magana ciki ciki take basa amsa abun har mamaki yake basa
Yau ta kama Saturday tun da tayi sallahr asuba bacci ya ƙaurace ma idanunta ta kalli Rukayya da Noor sai baccin su suke yi miƙewa tayi ta fito dan shirya musu breakfast, har zata shiga kitchen ta hango Azaad kwance saman kujera wuyansa ya ɗan juye ta nufi wajensa tayi tsaye ta turo baki tare da faɗin "Mutum da girmansa yana irin wannan kwanciyar" ta faɗa tare da sa hannunta biyu ta tallafo kansa ta gyara ta juya zata wuce ba zato ba tsammani kawai taji ya janyota ta faɗa jikinsa ta wani zaro ido, daman ba bacci yake yi ba ya rufe idanunsa ne kawai ya wani rirrik'eta yana kallan ta, hannuwanta na saman k'irjinsa, ta ɗago ta kallesa tayi ƙasa da idanunta
"Ina girman yake?" Ta ji ya faÉ—a, a zuci tace "Ohhh daman ba bacci yake yi ba" kiciniyar k'watar kanta take amman ta kasa shi kuwa ya zuba mata ido yaga yadda zata karb'i kanta
"Zaki wahal da kan ki ne kawai"Kitchen zan shiga "Ba ƙarfi gareki ba?" Ya faɗa Alesha ta gyad'a masa kai alamun eh yace "Good k'waci kan ki to" ta ci gaba da kiciniyar k'watar kanta ganin ta kasa kuma wallahi duk da gaji ta kwantar da kanta a k'irjinsa tace "Yaya please ka caka ni ka ji" Har kin saduda ke fa mai ƙarfi ce bai dace ki saduda tun yanzu ba " Ya faɗa tare da sakinta ta miƙe kamar wacce tayi dambe sai haki ta ke, tayi tsaye tana gyara rigarta tace"Ai saboda ka ga ban shirya ba ne shiyasa amman ni mai ƙarfi ce " Hannu ya kai zai janyota tayi saurin ja da baya tayi masa gwallo"Ni ko?" Ya faɗa, Ta ɗaga masa gira tana murmushi dimple ɗinta sai lutsawa suke yi, tayi hanyar kitchen "Zan kama ki ne" ya faɗa yana dariya yana jin wani farin ciki a ƙasan zuciyarsa
Kitchen É—in ta shiga tayi tsaye tana tunanin abunda zata shirya mu su kawai ta yanke shawarar yin YAMARITA ta fitar da duk abubuwan da zata yi amfani da su, cikin k'ank'anin lokaci ta kammala ta dafa Black tea, Ga yadda ake haÉ—a YAMARITA
Ingredients
yam
-4 eggs
-1 cup flour
-2 tbsp corn flour
-1 seasoning cube
-1 tsp dry celery
-½ tsp tumeric
-1 tsp curry
-salt
-oil for drying
METHOD
Peel and cut yams into rectangular shapes
*wash and add them into a pot,sprinkles some salt and add water
*place the pot on a stove and cook the yam under medium heat till soft
*drain in a colander and allow it to cool
*in a plate, combine flour, corn flour, dry celery and turmeric, mix well
*crack in the eggs in a bowl,add seasoning cube and curry ,whisk well
*dip each yam in the beaten eggs then coat with flour mixture
Black Tea
-ginger
-Lipton
-cloves
-cinnamon
-sugar
*method*;
*place ginger,cloves,cinnamon in a pot of water and bring to boil
*strain,add sugar and Lipton.
Azaad ya shigo kitchen ɗin yayi tsaye bakin k'ofa ya lumshe ido yana shaƙar daddad'an k'amshin da ya kewaye ilahirin gidan ya buɗe idon sa yace"Me ake dafa muna ne haka k'amshi duk ya dame ni a falo"ya faɗa yana murmushi Alesha ta juyo ta kallesa ita ma fuskarta ɗauke da murmushi tace "Delicious breakfast ne "Uhmmm let me take shower 🚿 sai na zo naga wannan Delicious food ɗin da ya cika hancina da k'amshi "Okay a fito lafiya" Ya wuce yayi d'akin sa, ta haɗa komai ta kawo dining table kayan da ta ɓata ta wanke ta dawo falo gyara falon kawai tayi ta goge kaya saboda bai yi datti ba ta saka turare ta wuce bedroom ɗin ta
Ta kalli agogo taga ƙarfe tara har da minti uku duk basu tashi ba suna nan suna bacci, ta gyara d'akin ta share ta goge ya rage sauran gado ta wuce toilet ta wanke daga nan tayi wanka ta fito ta ɗauki Noor dake bacci tayi toilet da ita suna shiga ta aje ta tsaye ta ɗibi ruwa ta shafa mata a fuska, Noor ta ɓata fuska tace "Mommy bacci zan yi"Okay bara a yi wanka sai ki ci gaba da baccin "Uhmmm"Ta cire mata kaya tayi mata brush sannan ta sata cikin ruwa Noor tace "Mommy"Na'am"cikin bacci naga kin haifo two baby's masu kyau " ta faɗa tana murmushi Alesha ta zaro ido tace"Mafarki ba gaske ba ne kinji" Eh"tayi mata wanka suka fito ta tada Rukayya su kuma suka shirya, koda Rukayya ta fito har sun shirya sun yi kyau abun su ita ma ta shirya a gurguje suka fito
Suna isowa falo Alesha ta hango Azaad zaune saman dining ya zuba ma kansa abinci yana ci ta saki baki tana kallansa da mamaki Noor ta ruga a guje wajensa tace "Good morning Papah"Morning how was your night?🌃 "Fine Papah "Good " ya faɗa but ko kallanta bai yi ba breakfast ɗin sa kawai yake yi ba ƙaramin daɗi YAMARITAN nan yayi masa ba Rukayya ta gaidasa
Alesha ta kallesa tace "Ina kwana" Ya É—ago ya kalle ta, kayan da ta sa sun mata kyau sosai kamar ba zai yi magana ba can dai sai ya ce "Ban gan sa ba ke kin gansa ne?" Ya faÉ—a tare da tsureta da ido Rukayya ta kumshe dariyarta Alesha ta turo baki tace "Uhm antashi lafiya?" Alhamdulillah" ya buÉ—e baki zai yi magana ko me ya tuna oho naga yayi shuru ya É—auki tea ya kai baki
Alesha ta zuba musu abincin su ta ja kujera zata zauna suka ji ana k'wank'wasa k'ofar falo abun duk ya basu mamaki saboda basa expecting zuwan kowa by this time " Bara na duba waye" Ta faÉ—a tare da wucewa tayi bakin k'ofar tana zuwa ta ce "Waye?" Muryar da taji ne abun ya bata mamaki ta kai hannu ta buÉ—e k'ofar bata gazgataba sai da ta ganta, People Ummie ce janye da k'atuwar akwatin ta.....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.