Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 10 of 35

page 11 & 12

Mamma ta daure zuciyarta ta hana kanta kuka ta kama Alesha ita da kanta ta saka ta mota suka wuce, har suka isa gidan Alesha na kuka sai dai yanzu kukan nata ba mai sauti ba ne, gidan an cika har anyi shirin walima an kafa baranda ga kujerun zama duk an aza, mutane a ka yi taro suna san suga fuskar amarya Aunty binta 'yar uwar su mamman taƙi yadda da a buɗe mata fuska suka yi cikin gida

Ammie ta tarbesu hannu biyu biyu ta kai Alesha har ɗakin su Rukayya dan ta samu ta zauna ta huta, Ammie ta hana kowa shigowa ɗakin daga ita sai Aunty binta sai amaryar, Ammie ta zauna kusa da Alesha tasa hannu ta yaye mayafin da ke kanta fuskarta ɗauke da murmushi lokacin da tayi arba da face ɗin Alesha ita kanta bata san lokacin da kalmar "Ma sha Allah tabarakallah" ta fito mata ba saboda ko kaɗan bata yi tunanin Alesha ta kai kyawon haka ba bugu da k'ari amincewa da tayi da wannan auren duk da bata taɓa ganin yaron ba wannan ya tabbatar ma da Ammie yarinyar na da tarbiya ta samu raino mai kyau ga kuma alamun kunya a tare da ita ko kallan Ammie ta kasa kanta na ƙasa lokaci ɗaya Ammie taji Alesha ta shiga ranta tana farin ciki na ganin ɗanta ya samu matar kirki

"Daughter ki saki jikin ki daga yau kema kin zama y'arta kamar yadda na haifi Azaad yake kira na da Ammie kema yanzu duk matsayin ku É—aya a waje na Ina rok'on Ubangiji Allah yasa wannan auren ya zama sanadiyar farin cikin mu baki daya" Amin ya Allah "Aunty binta ta faÉ—a
Ammie tace" Bara na baki ɗan tak'aitaccen bayani y'ar yan mu huɗu maza biyu mata biyu Aminu Azaad Rukayya Husnah, Azaad shi ne yaron mu na biyu a gidan nan ban sani ba ko an faɗa miki ya taɓa aure matarsa ta rasu wajen haihuwa yana da yarinya ɗaya sunanta Amina ana kiranta da Noor yayansa kuma yana da mata ɗaya da yara biyu sai k'annensa Rukayya da husnah dake karatu yanzu ma sun fita ne suna tare da k'awayensu zasu haɗa dan biki a gidan gwaggwan su na kin gan su, abunda zan faɗa miki nasan kafin ki zo gidan nan an faɗa miki shi zan dai ƙara tunasar da ke ne kawai Daughter Shi aure da kike gani ɗan hak'uri ne yau da daɗi gobe ba daɗi sannan duk wanda yace zo mu zauna to yace zo mu saɓa saboda dole wata rana sai an samu rashin fahimta a tsakani daughter bazan 'boye miki ba wallahi sai kin yi hak'uri sosai da Azaad ni na haifesa cikin halayyarsa ba wanda ban sani ba sai kin jure kin zage damtse kafin ku fahimci juna mutum ne shi mai wuyar sha'ani amman idan kin fahimce shi kuma mutum ne mai sauƙin kai muddin kika fahimci abubuwan da yake so da wanda baya so kika fahimce su kuma kika kiyaye wallahi zaki ji daɗin zama da shi abu ɗaya nake muku fata Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba Allah ya kwauda duk wata fitina da tashin hankali a zamantakewar ku kar na cika ki da surutu bara na baki waje ki huta nan da awa ɗaya dan Allah ki samu ki shirya dan a fara da wuri a gama" Alesha ta gyad'a kai Aunty binta ta yaba sosai da Ammie

Ammie ta fito ta basu waje ta koma wajen baƙi, da wuri ko aka fara walima biyar da rabi aka gama Amarya ta sake wanka aka jera motoci ta shiga suka wuce gidan ta

Ba k'arya wallahi gidan ya haɗu over, tun daga bakin gate zuwa harabar cikin gidan sai gaf da ƙofar shiga ciki motar amarya ta tsaya suka fito, kana tura kanta cikin falon wani sanyayyen sanyi mai haɗe da ni'imantaccen k'amshi zai kai ma hancinka ziyara, wasu dangararrun kujeru ne masu kyau aka zuba a falon ga k'atuwar tv bango mai tsawo da faɗi duk da ba'a wani sa kayan kyale k'yale sosai ɗin nan ba amman falon yayi mugun kyau kai abun sai wanda ya gani

Direct bedroom aka wuce da ita nan ma an gyara mata shi sosai, mutane suka musu fatan alheri suka wuce gidan ya rage daga ita sai Aunty binta, sai da aka yi sallahr isha'i Aunty binta ta wuce aiko Alesha taci kuka kamar ranta zai fita idanunta sun yi jajirrr ta dawo falo ta zauna saman kujera tayi tagumi har goma ta buga tana wajen ta ƙara gyara zamanta daga haka bacci yayi awon gaba da ita ba ita ta farka ba sai ƙarfe huɗu na dare ta miƙe ta wuce bedroom kai tsaye toilet ta wuce tayi alwala ta fito tayi tsaye tana dubin inda zata ga sallaya ganin bata gansa ba ta wuce wajen wardrobe ta buɗe nan ta hangota sama ta ɗauko tare da hijab ɗin da ke wajen ta shimfida sallaya ta saka hijab ta kabarta sallah, sai da aka fara sallar asuba sannan ta dakata tayi sallahr asuba ta cire hijab ta nad'e sallaya ta mayar ta faɗa toilet tayi wanka ta fito ɗaure da towel ta shafa mai ta fesa turare ta buɗe akwati ta fito da wata riga marar nauyi ta saka ta faɗa gado ta kwanta ta janyo wayarta ta lalubo number Mamma kiranta taso yi sai kuma ta fasa ganin safiya bata ko ida wayewa ba ta aje wayar ta kwanta bacci ya sake ɗaukarta

Ammie tun da ta tashi sallah bata koma bacci ba ta sauko ta shiga haÉ—a ma amarya breakfast da kanta koda takwas tayi ta haÉ—a komai har su yau ita tayi musu breakfast ta shirya na amarya ta haÉ—a komai ta saka cikin basket, ta wuce É—aki dan ta shirya

Zuwa ƙarfe goma kowa ya shirya ya fito dan yin break, har sun fara cin abinci sai kawai suka ga Azaad yana saukowa Ammie da Dad suka kalli juna kusan gaba ki ɗayan su abun ya basu mamaki ganinsa gida kuma ga dukkan alamu gidan ya kwana, hankalin sa kwance ya ƙara so wajen su ya ja kujera zai zauna Dad ya haɗe rai yace " Kai kuma daga ina? Me ka ke min a gida da wannan sanyin safiyar Azaad? Kar dai abunda nake tunani haka ne? A gidan nan ka kwana?" Azaad yayi shuru alamun rashin gaskiya ya bayyana a fuskarsa

"Azaad kana nufin yarinyar nan ita kaɗai ta kwana a gidan nan? Innalillahi wa inna ilaihiraji'un wai dan Allah wane irin mutum ne kai" Ammie ta faɗa tare da dafe kanta tana jin wani irin k'una a cikin zuciyarta "Yanzu a ganin ka kayi ma yarinyar nan adalci? muma iyayenka ka muna adalci kenan? " Bar ni da shi kawai wallahi yanzun nan tun kafin raina ya ƙara 'baci ka fice min a gida ka wuce gidan ka kai bari ma kaji yau yau nake san ka kwashe duk wani tarkace da ya zamo naka a gidan nan ka kai gidan ka ai kaji ni?" Azaad bai ce uffanba Dad ransa ya 'baci yace"Zaka fice min a gida ko sai na taso?" Sumi sumi ya kama hanya Ammie tace"Dakata " ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko basket ta wuce gabansa ta aje tace"Abinci ne ka ɗauke sa kaje ka kai mata " abincin ya kalla da sauri ya kalli Ammie yace" Haba Ammie kina nufin ni zan kai mata abinci?" Ko kafi ƙarfin ka kai ne? Eh idan kafi ƙarfin kaje aikin da nayi ma ne sai na ji" ba dan ransa yaso ba ya ɗauka har ya kama hanya Noor dake zaune a wajen tace" Papah zan bika " wani mugun kallo ya yi mata zai ɗauke kai suka haɗa ido da Dad yace " Sai kaje da ita wallahi sai ta bika tashi ki bisa ki je kiga mommyn ki" Noor ta miƙe da sauri tana farin ciki

"Yaro sai taurin kai da bak'ar zuciya sai dai ka mutu sai ta bika" Dad ya faÉ—a

Azaad yayi gaba abusa Noor ta bi bayansa da sauri har ya fita, ya buÉ—e mata gaba ta shiga ya saka kwando ya shiga ya ja motar tsiyace

Alesha sai goma saura ta tashi ta shiga tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani material maroon mai haɗe da mayafinsa sai k'amshi take zubawa ta fito falo ta zauna sai kallon falon take yi ya mata kyau sosai, ko kaɗan bata ji alamun buɗe gate ba saboda daga wajen gate ɗin su zuwa nan akwai yar tazara kuma gate ɗin ba mai ƙara ba ne bare idan aka buɗe ka sani sai kawai jin tayi ana faɗin " Mommy! Mommy" ta juya ta kalli ƙofar daidai ita ma Noor na kallan wajen da take cike da farin ciki tace " Mommyyyyyy" ta shek'a a guje wajenta Alesha farin ciki ya mamayeta sosai ta buɗe ma Noor hannu tana zuwa ta ɗagata sama ta rungume........................

🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.