Azaad Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: AZAAD.txt
Chapter 31 of 35
page 40
"Mamma ka da ki barni wallahi na tuba bazan sake ba ki yafemin" Alesha ta faɗa tana bin Mamma a baya, Mamma ta wuce wajen Noor ta buɗe jakarta ta ɗauko ledar sweet ɗin da ta kawo ma Noor ta miƙa mata cike da jin daɗi Noor ta kar'ba tare da faɗin " Nagode mama kaka" kar ki damu " ta faɗa tare da shafa kanta tana murmushi, Alesha ta share hawayen fuskarta, Mamma ta ɗauki jakarta ta wuce
Alesha tayi zaune tana tunanin maganganun da Mamma tayi mata
Misalin ƙarfe huɗu da rabi ya dawo gida ko da ya dawo a gajiye ga kuma yunwa, bai tarar da su a falo ba ya wuce d'akin sa yayi wanka ya fito sanye da gajeren wando da vest d'akinta ya wuce kwance ta tarar da ita idanunta a rufe kamar mai bacci Noor na kusa gareta tana kallo ya ƙara so yace "Bacci ki ke a wannan lokacin?" Ta buɗe idanunta da suka yi ja- ja- ja alamun zazzaɓi Noor tace "Papah" Baby kallo ake yi?" Eh" To ai zaki takurama Mommynki da wannan kallon je ki falo kiyi kallon gamu nan tafe "Okay papah" ta faɗa tare da sauka saman gadon ta wuce falo
Hannunsa ya kai jikinta yaji jikinta da zafi sosai yace" Bakya jin daɗi? Meyasa baki sanar min ba?"Bana jin komai yaya kawai ƙarfin jikina ne bana ji shiyasa ban sanar maka ba kuma na sha magani amman kayi hak'uri " Ta faɗa tare da tashi zaune ta jingina bayan ta ga kan gado yace "Sannu yanzu ba abunda ki ke ji ko?" Ya faɗa tare da ɗaga rigarta ya ɗora hannunsa a cikinta yana shafawa, sai da taji wani iri a jikinta a hankali tace " Eh babu ba abunda nake ji" Okay kin ci abinci kuwa?" Eh "Yawwa to yanzu me ki ke son ci?" Girgiza masa kai tayi alamun bata son komai yace " Ki kwanta ki huta Bara na je naci abinci yunwa nake ji"Ya miƙe ta riƙo hannunsa tace ita ma zata bisa falo, suka fito falon tare
Yayi yayi akan tayi zamanta ya saka abincin da kansa taƙi amincewa dole ya barta ta saka masa yaci sai da ya k'oshi ta kwashe kaya ta kai kitchen ta dawo ta kwanta tare da ɗora kanta saman ƙafafunsa
Misalin sha ɗaya na dare ta shigo d'akin sa fitowarsa wanka kenan yana tsaye ɗaure da towel a k'ugunsa yana duba sakon da aka turo masa a waya ta nufi wajen da yake ta rungumesa ta baya yayi murmushi ya aje wayar hannunsa ya juyo da ita gabansa ta kasa ɗago kai ta kallesa muryarta na rawa tace "Yaya don Allah ka yafe min" ta faɗa tana ƙoƙarin durk'usawa yayi saurin riƙo ta tare da girgiza kai yace "Miye haka?" Yaya ka yafe min nasan kwanakin nan na yi ta ɓata kama rai a bisa wani dalilina na banza wallahi bazan sake ba ka yafe min nasan na aikata babban kuskure " Alesha kin min babban laifi"Yaya girman laifin da nayi ma yafiyarka ta zarce shi na tuba " ta faɗa tana kuka
"Ki daina wannan kukan bana so " Ka yafe min?" Murmushi yayi ya shafi gefen fuskarta yace "Ban taɓa riƙe ki a rai ba na ɗauki abunda ki ke yi kawai a matsayin tausayin da ki ke ma yarinyar nan shiyasa nayi ta ƙoƙarin na fahimtar da ke amman kin kasa fahimta ta shiyasa naje kawai na samu Mamma na sanar mata komai Alesha nafi kowa sanin ki nasan tsananin zafin kishin da gareki kawai tausayin ta ne ya rufe miki ido ki ke ƙoƙarin salwantar da farin cikin mu amman yanzu tun da kin gane Shikenan komai ya wuce "Yaya dagaske baza ka min kishiya ba?" Ta faɗa tana masa wani shu'umin kallo
"Har abada kuwa in sha Allah " ya faɗa tare da janyota jikinsa ya cire hijabin jikinta, Wata rigar bacci ce a jikinta wacce da ita da babu duk ɗaya saboda rigar bata ɓoye komai ba raga raga take ai kuwa nan take gogan naku ya rikice ya shiga kissing ɗinta ta ko ina yana matsa na shanunta da suka ƙara cikowa irin na mai sabon ciki ita ma ta biye masa suka shiga faranta ran juna har suka samar ma kansu natsuwa
Washe gari sha biyu na rana ya kai su gidan Mamma ƙarfe biyu ya ɗauke su ya kai su gidan abokinsa Abbas da ya dawo ƙasar daga can suka wuce wata plaza suka yi siyayya suka kamo hanyar gida
Tun a wajen plazar da suka tsaya yaga wasu motoci uku na bin bayan su har yanzu kuma da suka doshi hanyar gida motocin na bin su a baya, tuk'insa ya ci gaba da yi har ya iso mai gadi ya buÉ—e masa ya wuce motarsa na shiga da sauri motocin dake bin su a baya suka danno kai cikin gidan.................................
*Ina mai matuÆ™ar baku hak'uri na jin shuru ba update sakamakon rashin jin daÉ—in da bana yi* i know kuna hak'uri dani don Allah ku Æ™ara thank you ðŸ™ðŸ˜ŠðŸ’• Love u all💔â¤ï¸â¤ï¸
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.