Azaad Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: AZAAD.txt
Chapter 1 of 35
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
Alhamdulillah Alhamdulillah, yadda na fara littafin nan lafiya Ubangiji Allah ya nuna min na kammalasa lafiya Allah ya bani ikon rubuta daidai a cikin sa ya hayyu ya qayyum🤲
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Page 1
Kyakkyawar budurwa ce ajin farko fara doguwa farin ta irin mai kyaun nan ne sannan tsayinta daidai a k'allah dai shekarun ta zasu yi twenty something, tana ɗaure da towel a jikinta, Allah ya mata diri mai kyau, tana tsaye gaban mirror ta janyo wata kwalbar mai wanda kwalbar ce kawai ke saman mirror sai wani dan ƙaramin turare da ya kusa ƙarewa
Dubanta ta kai ga agogon dake manne a d'akin taga 7:48 "Ya Allah na kusa makara" ta faÉ—a wanda yasa dimple É—in ta suka bayyana, da sauri ta shiga shafa mai ta gama ta É—auki turare ta shafa a jikinta, ta wuce wajen gado ta É—auki tufafin ta da ta fitar, cikin sauri take yin komai har ta gama sa kayan ta É—auki hijabin ta Nut brown dogo ta saka ta kawo nik'ab ta saka ta É—auki jakarta ta saka takalmi tayi hanyar fita
Tana ƙoƙarin isa bakin k'ofar aka turo k'ofar, Wata matashiyar budurwa ce shekarun ta ba zasu gaza 13 to 14 years ba wani k'ask'antaccen kallo ta tsaya tana yi mata tun daga samanta har ƙasa take mata wannan kallon, Ganin haka yasa ta raɓa ta gefenta zata wuce "Wallahi ki ka kuskura ki ka fita gidan nan yau sai azabar Allah ta same ki " Ta ji Muryar yarinyar ta sauka ta tsaya tare da jiyowa ta zuba mata idanu ta cikin nik'af Yarinyar ta ce "Mommy na kiran ki kuma tace kiyi sauri ki sameta falo yanzun nan " Kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta faɗa cikin damuwa yarinyar tace " Ohh mahaifiyar mu ce shad'an kenan wallahi sai na sanar mata" Ba tare da tace da ita komai ba ta juya ta fito ta nufi falon gabanta na dukan uku uku tana addu'a Allah yasa ba wani aikin ne zata saka ta ba dan tama makara sosai wallahi
Bakinta É—auke da sallama ta isa falon kusan sau uku tana sallama duk da mutanen dake falon hakan bai an samu koda mutum É—aya daga cikin su ya amsa sallamar ba, wanda inda sabo ta saba, tasa hannu ta É—age nik'af É—in ta sama ta nufi wajen da matar take zaune ta gurfana murya na rawa tace "Mommy ga ni" ta faÉ—a yafi sau uku sannan ta juyo da fuskarta wajen ta tace " Kinga dama kin zo?" Wallahi yanzun nan Basmah ta sanar min kina nema na"Lahh lahh lalahh sharri zaki min Allah Mommy na jima da faÉ—a mata sai da ta tsaya ta gama abunda take yi sannan tazo kuma ma da na sanar mata kin san abunda tace?" Basmah ta faÉ—a Mommy ta girgiza mata kai alamun aah sai kin faÉ—a tace" Neman tsarin Ubangiji take daga gareki " Alesha Shaid'an ce ni?"Mommy ta faÉ—a tare da nuna k'irjinta
Muryar Alesha na rawa tace"Wallahi Mommy ba hakan nake nufi ba " To me kike nufi?" Ba komai " Kina nufin kenan Basmah sharri zata miki?"
"Wallahi Mommy duk ke ki ke k'yale ta shiyasa ta raina ki da yawa " Cewar wani saurayi dake wajen, Mommy ta buɗe baki zata yi magana budurwar da ke wajen ta riga ta faɗin" Ai bro sakin fuskar da take mata ne yasa ta rainata haka " Mommy ta yi murmushi tace"Naji yanzu duk ba wannan ba ina indomie da Ummie tace ki dafa mata kin gama ne?" Alesha tayi shuru kanta a ƙasa sai da Mommy ta daka mata tsawa ta ɗago kanta tace" Uhm mmmn daman da naga na kusa makara ne shi ne na barma uwani mai aiki ta dafa mata naje na shirya " Uwani! " Ummie ta faɗa tare da ɗagowa ta aje wayar da ke hannunta tace " Ki ka barma uwani? Uwani nasa ta dafa min ko ke? Ai naga uwanir amman nace ki dafa min wallahi idan ta dafa ta bazan ci ta ba Mommy kina jin ta fa ai wannan rainin wayo ne da wulak'anci" Kwantar da hankalin ki miye na tada jijiyoyin wuya indomie kamar kin canye " Mommy ta faɗa
"Alesha zo nan " Mommy ta faÉ—a tare da yi mata alamun da ta wajenta, ba musu taja k'uiwoyinta sai gaban Mommy, saukar mari kawai taji saman face É—in ta " Dis na makarar da kikayi wajen kiran da na miki" kan ta ankara ta sake jin wani" Dis na aikin da ta saka ki ne kika k'iyi " Alesha hawaye kamar an buÉ—e famfo "That's good " Saurayin ya faÉ—a
"Tashi min a nan ko yanzu na sake baki wasu banza kuma ki wuce kitchen yanzun nan ki dafa mata abunda ta saka ki mansur idan bata tashi ba kazo ka 'ba'b'ballah min ita a nan" Da sauri Alesha ta miƙe ta ɗauki jakarta " Shegiya tana fama da hijabi har ƙasa kamar mai takaba" Mommy ta fada
Alesha hanyar É—aki tayi ta cire hijab ta wuce kitchen har lokacin kuka take koda ta shiga ta tarar da uwani har ta dafa indomie tana juyewa a filet,
Tun da uwani ta ɗora idanunta a fuskarta ta san wani abu ya faru saboda fuskarta tayi ja ga kuma kukan da take yi, Uwani cikin tausayin shugabar tata ta matso wajen ta tace "Hajiya ƙarama meya faru? Me ya samu fuskarki kuma me aka miki kike kuka? Kin fasa zuwa makarantar ne?" Uwani ta jero mata waɗan nan tambayoyin lokaci ɗaya, ba tare da tace da ita komai ba ta wuce wajen pampon dake wajen ta wanke fuskart ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa masu sanyi ta sha ta mayar ta ƙara goge fuskarta ta juyo wajen uwani tace " Har kin kammala? " Eh yanzun nan zan kai mata " Aah ba sai kin kai ba ki ɗauki wannan kawai ki canye" Amman meyasa? Duk fa abunda kika ce a saka na saka " Uwani ki ɗauka kawai" To Hajiya ƙarama amman meya sameki nagan ki cikin wani iri?" Bakomai kiyi aikin ki kawai "Hajiya ƙarama Ubangiji Allah ya sassauta miki ya kawo miki mafita " Alesha tayi murmushi a zuci kuma sai amin take faɗi.......................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943*
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.