Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 2 of 35

Page 2

Cikin k'ank'anin lokaci Allah ya taimaketa ta kammala ta juye indomie saman filet da É—auka ta nufo falo, har yanzu duk suna nan zaune kowa da abunda yake yi banda Mansur da ya tashi ya fita

Har gaban Ummie ta isa ta aje indomie, tace "Gashi nan" Wani yatsina fuska Ummie tayi tace "Ya banga egg 🥚ba bayan kin san idan ba shi bana iya cin indomie" Na manta ne wallahi dan Allah kiyi hak'uri kinga na makara idan yaso anjima idan zan dafa miki sai na saka " Wallahi baki isa ba dole ne kije ki dafomin k'wai ki kawo yanzun nan" Amm.........." Alesha" Mommy ta kira sunanta kana tace " Ba na hanaki yin jayayya da ita ba ne? Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da kunnuwana zasu ƙara jiye min ina fatan kin jini?" Eh" Good kuma ki wuce kije ki kawo mata abunda take buƙata" To Mommy "

Ta juya ta koma kitchen jiki ba k'wari sai da ta dafa k'wain ta kai mata sannan ta fara cin indomie, Bayan ta gama da sauri ta ɗauki hijabin ta ta saka ta mayar da nik'af ɗin ta a fuska ta ɗauki jaka ta fito taje ta sanar musu ta tafi, tana ƙoƙarin fita sai ga daddy ya fito da shirinsa da alama fita zai yi shima tayi masa ina kwana ta wuce, Da sauri ta fito, motoci uku ne a compound ɗin gidan amman ga mamaki na sai naga ta nufi bakin gate ƙasa bata yi wajen motocin ba buɗe k'ofar gate ɗin tayi ta fita, mai gadi dake cikin daki jin an buɗe k'ofar yasa ya fito ya lek'a yaga ita ce ya juyo sai ga daddy ya fito ya gaida sa ya buɗe masa gate ya fice, Tafiya take a ƙafa sai sauri take yi ta buɗe jakarta taga Naira 60 saba'in ce gareta kuma ba zasu kaita school ba dan haka ta ƙara sauri tana cikin tafiya motar Daddy ta biyo ta wuce ko alamun tsayi bai yi ba bare ya kalli gefenta ita kam ba abunda ya dameta dan ta saba gata ga su zata fita suma zasu fita amman ba mai rage mata hanya ko ya bama kuɗi yace ta hau abun hawa

Tayi tafiya mai ɗan nisa, sannan ta tsaya wani shago ta shiga ta siyo biscuit na hamsin sweet guda ɗaya na Ten Naira ya rage mata saura naira goma, ta fito taci gaba da tafiya bata ƙara wata tafiya mai nisa ba ta iso Wata private school, cikin mutumci suka gaida da baba mai gadi ta wuce tana shiga ana tashi breakfast, kai tsaye office ɗin shugabar makaranta ta wuce dan sa hannu koda ta je shugaba baya nan ɗan aikensa ne kawai tasa hannu ta fito ta wuce staff ɗin su na malamai

Tana shiga yan uwanta malamai suka sanar mata Noor tayi ta zuwa bata nan tace "Allah sarki princess nima ina can gida amman tunanin ta ya dameni " Zata zauna sai ga Noor ta shigo da gudu sai wajen ta tana dariya ta É—auke ta sama tana juyawa suna ci gaba da dariya, Noor yarinya ce yar' kimanin shekaru shida tunda aka kawota makaranta kullum cikin kuka take bata zama school amman zuwan Alesha ya sauya komai Jinin Noor da Alesha ya haÉ—u waje É—aya daman Allah yayi ma Alesha san yara bare kuma da taji ance mahaifiyar Noor ta rasu tana haihuwarta idan ka ga abunda suke zaka iya rantsuwa kace uwa da yar' ne saboda shak'uwarsu sauran malamai ma farko sun zata Ita ce mahaifiyar Noor waÉ—an da basu sani ba, sometimes idan aka tashi school sai anyi drama tsakaninsu Noor tace sai ta bita gida, dak'yar ta ke lalla'bata driver ya wuce da ita, wannan kenan

Sai da suka gama juyin su sannan ta sauke ta ta zauna ta ɗaura ta saman ƙafafunta Noor tace "Mommy tun d'azu nake ta neman ki" ta faɗa cikin muryarta ta yara Alesha tace "Ohh Sorry princess yau Mommy ta makara sosai ko amman bazata sake ba kinji?" Noor ta gyad'a kai tana murmushi
"Kin ci abinci?" Alesha ta tambeta ta girgiza mata kai alamun aah tace"Ina abincin?" In bag " Alesha ta shiga cire jakar da ke bayan ta ta ciro wata had'ad'd'iyar ƙaramar kula ta yan makaranta ta buɗe ta riƙa bata a baki har sai da ta k'oshi ta bata ruwa ta sha, ta ciro biscuit ɗin da ta siyo mata ta buɗe ta bata ta ɗauke ta suka yi class ɗin su saboda an gama break har an koma class ajinsu ma take da yanzu

Bayan an tashi Noor harda kuka sai ta bita ga driver tsaye ya na jiran su yana kallan su yana murmushi dan rigimar su na burgeshi dak'yar ta hak'ura Alesha ta sata mota suka wuce ta kama hanya ita kaɗai tana tafiya ga zafi ga kuma zafin rana koda ta isa gida kamar zata kama da wuta, tayi wanka ta yi sallah sannan ta fito duk da a gajiye take tana buƙatar ta kwanta ta huta amman tasan hakan ba mai samuwa ba ne
, gidan yayi shuru da alama yaran duk basa nan Mommy kaÉ—ai ce a falo daga kallo bacci ya É—auke ta a zaune sallamar Alesha ta tayar da ita

Mommy tace "Sai yanzu kika dawo?" Eh" ta faɗa kanta a ƙasa Mommy taja tsaki tace" Kije kitchen kaji na nan guda shida cikin fridge ki ɗauke su a gyara sannan gida biyu za'a raba rabi ayi farfesu rabi a soya irin jar suyan nan sannan da kin soya sai ki barbad'a yaji a kai ai kingane yadda nake nufi ko?" Eh" Okay maza wuce ki fara saboda bana san babanku ya dawo ba tare da an gama ba tun d'azu ya aiko su uwani kuma bazata iya yin yadda nake so ba idan kin gama gugar kayan Basmah na nan "To" ta wuce kitchen taje ta fara aiki tana cikin aiki su Ummie suka dawo kowa nen su riƙe da leda sun siyo kayan mak'ulashe

Ita kaÉ—ai tayi ta bulek'en aikin kajin har ta gama, zuwa lokacin har biyar tayi, har ta gama ko tsinke É—aya bata sa a baki ba ta É—auke sa gaba É—aya ta kaima Mommy

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Wani katafaren gida ne mai masifar kyau, gidan ya haɗu sosai ga shi da girma kai da ganin gidan kasan na masu shegunan ne ( Kuɗi kenan 😅) buɗe gate aka yi motarsa ta danno kai ciki ya nufi wajen aje motoci yayi parking ya fito, kyakkyawa ne ajin farko fatarsa baƙa ce sai dai ba irin baƙin nan ba dan ba zaka ce masa fari ba kuma ba zaka kirasa baƙi ba irin dai tsaka tsakar nan ne gashi da hanci sa Allah ya basa gira kamar mace idanuwansa basa da wani girma amman farare ne tasss bakinsa shi ba ƙarami ba kuma shi ba babba ba yana da ɗan gashin gemunsa ɗan daidai yana sanye cikin ƙananun kaya riga da wando, fuskar nan tasa a haɗe take kamar ko yaushe ko alamun murmushi babu a kanta, Ɗaya ɗaya yake takawa irin cikin izzar nan, Ma'aikatan dake gaidasa ko kallo basu ishesa ba bare ya samu damar amsa musu har ya isa bakin falo ya tura k'ofar ya shiga, sallamar da yayi ko wanda yake kusa da shi sai idan ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya a bakinsa sannan zai ga alamun yayi sallama dan ko sautin maganar baza ka ji ba bakinsa kawai da yayi motsi shi zai nuna ma alamun yayi sallama

Matar da take zaune a falo tare da baƙi kallo ɗaya zaka mata ka gane ita ce mahaifiyarsa saboda suna da kama sosai amman sai dai ita fara ce, juyowar da zata yi ta gansa tafe saboda ko sautin tafiyarsa baka ji tayi murmushi har ya ƙaraso yana ƙoƙarin wuce su tace "AZAAD.....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943*

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.