Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 34 of 35

page 44

Sauri take yi sosai kamar wacce zata tashi sama koda ta isa falon ta matsu kai tsaye ta wuce bedroom É—in Alesha durk'ushe ta tarar da ita tana faman nishi mai haÉ—e da gurnani Noor na rungume da ita tana kuka da sauri ta isa wajen su ta janyo Noor dake kuka suka fito waje ta kaita falo ta zaunar da ita tace "Ta daina kuka ta jira su yanzu zasu fito" ta wuce ta koma, Noor ta sake fashewa da kuka

Mamma na zuwa ta cire hijab É—in ta tayi kan Alesha

Azaad yana fitowa masallaci ya ga mota bakin gate yabi motar da kallo nan take ya gano motar Mamma ce, da sauri ya wuce ciki zuciyarsa na har'bin uku uku, tun kafin ya ƙarasa shigowa falo yake jiyo sautin kukan Noor da sauri ya ƙara sa shigowa bai ko yi wajen Noor ba ya nufi ɗakin Alesha yana tura ƙofar Mamma tayi saurin cewa " Dakata Jira a waje" jikinsa a sanyaye ya koma, koda Mamma ta fito sai faman zarya yake yi a bakin ƙofa ganinta yasa da sauri ya nufo ta yace"Ta haihu ne?" Mamma ta girgiza kai tare da faɗin"Har yanzu " Mamma mu je asibiti"Nima nayi tunanin haka amman naga haihuwar tayi kusa mu ɗan jira kaɗan "Kina ganin ba matsala kuwa Mamma?" In Sha Allah ba wata matsala " Allah yasa wallahi ina tsoron na rasa ta"Ya faɗa idanunsa sun ciko da k'wallah yana tuna lokacin da mahaifiyar Noor ita ma ta rasu wajen haihuwa

"Idan na rasata bazan iya rayuwa ba nima mutuwa zan yi wallahi Alesha ita ce rayuwa ta ita ce komai nawa " Mamma tayi murmushin jin daÉ—i ganin tsantsan son da yake ma Alesha a cikin idanunsa tace"Kar ka damu in Sha Allah ba abunda zai sameta zata haihu lafiya ku ci gaba da rayuwa "Allah yasa Mamma"Kai dai kawai kaci gaba da yi mata addu'a bara na koma "ta faÉ—a tare da komawa É—akin

Cikin ƙank'anin lokaci Alesha duk ta fice hayyacinta har ta sadak'ar lokacin ta yayi mutuwa zata yi, nishi tayi da ƙarfi sai ga jaririya ta faɗo, cike da farin ciki da murna Mamma ta ɗauki jaririyar tana kuka daman tasan awon yadda ake yankar cibi ta auna ta yanke ta goge mata jikinta ta janyo zane ta sakata ciki tana ƙoƙarin miƙewa ta ga Alesha na wani irin nishi ko kafin kace me sai ga wata jaririyar ta faɗo murna da farin ciki duk suka mamaye Mamma ta aje jaririyar hannunta ta ɗauki wacce ta faɗo

'Bangaren Azaad kuwa yana cikin roƙon Allah yaji kukan jaririya, murna da farin ciki suka mamayesa amman duk wannan murnar da farin ciki sai tsoro da fargaba suka mamaye gurbin su tsoron kar a je ita ma ta rasu

Mamma ta gyara ma jarirran jikinsu ta ɗauki ɗaya ta nufo waje tana buɗe ƙofa Azaad yayo wajen ta yace "Zan iya shiga na ganta?"Saurin me ka ke yi ne zaka shiga ka ganta tana cikin ƙoshin lafiya "To" ya faɗa yana ƙoƙarin bi ta gefen Mamma ya wuce tayi saurin taresa tare da faɗin "Jira tukkunna sai an gyara mata jikinta amman yanzu ka fara ganin abunda ta haifa mana"Toh! Toh shikenan" ya faɗa tare da miƙa hannu ya kar'bi jaririyar duk ya dabulce da ka gansa zaka san a rud'e yake Mamma ta koma ciki don ɗauko ɗayar

Azaad yayi shuru yana kallan jaririyar, jajir da ita kamanninta kuwa duk na mahaifiyarta ne duk ita ta ɗauko gashin kanta har saman goshi ga yarinyar mulmul da ita ya kafeta da ido yana jin k'aunar yarinyar na ratsasa yana cikin mata wannan kallon Mamma ta fito da ɗayar ya kalleta ya kalli hannunsa cike da tsantsan farin ciki da wannan kyautar da Allah ya basu ya buɗe baki zai yi magana amman ya kasa sai ga hawayen farin ciki mamma na dariyar farin ciki tace "Yan biyu ta haifa duka mata"Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allah Nagode ma"ya faɗa tare da miƙa ma Mamma jaririyar hannunsa ya faɗi yayi sujjada ta nuna godiya a wajen mahalaccin sammai da ƙassai ya jima a sujjadar sannan ya taso ya kar'bi yaran, ku zo kuga zallar farin ciki a wajensa ya ma rasa abunda zai yi ya wuce falo da su ya fara kiran sunan Noor wacce daga kuka bacci ya ɗauke ta,

Ta buÉ—e idanunta ta tashi zaune Azaad yace "See! See your sisters "tayi shuru tana kallan jarirran tayi murmushi ganin sun buÉ—e idanunsu sun sa hannunsu a baki suna tsutsa tace "Papah namu ne?" Azaad ya gyad'a mata kai yana murmushi yace "Eh namu ne mommynki ta haifa muna su" Mommy?" Eh mommynki" Papah ina son su, kallah ka ga ta buÉ—e ido " ta faÉ—a tare da matsowa kusa da su

Mamma ta fito ta d'aura ruwa sai da suka tafasa ta juye takai toilet ta zuba cikin wata sabuwar babba roba, ita ta gasama Alesha jikinta sannan ta fito ta bata waje don ta ida wankan ita kuma ta ƙara gyara ɗakin ta feshe sa da turaruka nan take ɗakin ya ɗauki daddad'an k'amshi ta ɗan rage gudun AC

kayan haihuwar da ta saka a roba ta fito ta je can bayan gida wajen wasu fulawoyi ta wanke kayan tsaff ta shanya a wajen ta dawo ta shiga kitchen............
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.