Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 5 of 35

page 5

Yaya Aminu ya saki baki yana kallansa ya kalli Ammie yace " Topah Ammie wa ya taɓa ɗan lelen ki naga ya ƙara haɗe rai" Ammie tayi murmushi tace "Shi da Mahaifin ku ne " Da alama an masa abunda ya taɓa zuciyarsa " Maganar dai ɗaya ce wacce ka sani" Aure?" Yaya Aminu ya faɗa, Ammie ta gyad'a masa kai"Allah ya shiryesa bara naje mu gaida da Dad " Okay" ya nufi dining wajen da Dad yake zaune yana ɗan wani aiki cikin wayarsa

Yaran suka dawo wajen Ammie, Azaad yana isa ɗaki banda zarya a ɗakin ba abunda yake yi kamar zai tashi sama zuciyarsa sai tafasa take akan 'bacin rai, yadda yake ji shi wallahi bazai iya tsayawa da wata mata ba da sunan soyayya bare kuma har ta kai su ga Aure bama soyayya ba ko tsayuwa da mace baya san yi, Amman shi ne Dad zai yanke wannan hukunci shi gaskiya bazai yi aure ba Noor kuma dan tana faɗin a kaita wajen Mommynta ba ga su Rukayya nan da husnah ba ai sun isheta d'ebe kewar mahaifiyarta, ya numfasa a zahiri yace " Zamuyi magana da Ammie nasan zata fahimce ni ita, toilet ya wuce ya sake wanka ya sauya kaya sai k'amshi yake zubawa kamar wanda a ka yima ɓarin turare a jikinsa

Koda ya sauko ƙasa ba kowa duk suna sama sai mai aikin su da ta fito daga kitchen wucewa yayi ya fice ya shiga motarsa ya bar gidan

Dad zaune a office ɗin sa sai faman aikin cike wasu takardu yake saboda yau za'a zo amsar su baya so azo amsa ba tare da ya kammala aikin ba knocked ƙofar aka yi yaɗan jima sannan ya bada izinin shigowa Daddy ne ya shigo hannunsa riƙe da wasu fayil yace "Sir angama aikin" Okay " Ya karɓi fayil ɗin ya duba yace " You can go " Thank you sir " Daddy ya juya har ya kai bakin ƙofa Dad ya kirasa ya dawo yace"Please sit " daddy ya zauna Dad ya dakatar da aikin da yake yi ya mayar da hankalinsa ga daddy yace " Two days bamu gaisa ba to ya gida ya iyalai" Daddy yayi murmushi yace " Wallahi alhamdulillah duk suna lafiya ya wajen ku?" Alhamdulillah " sai kuma duk suka yi shuru can Dad yace" Kana da 'yar mace Babba? " Daddy ya washe baki yace "Eh ina da dan a ƙallah tana da 20 years a duniya" Ahh ma sha Allah ya sunan ta ne?" Sunan mahaifiyata ne amman muna kiranta da Ummie" Allah sarki Allah ya albarkaci rayuwarta " Amin Sir " Bara na ci gaba da aikin nan kafin su iso " Okay Sir" Daddy ya miƙe Dad yace "Ohh na manta Please sanar da PK ya sanar after prayer akwai meeting so su ɗan jira kafin su je lunch break " Okay " daddy ya wuce ya fita Dad kuma yaci gaba da aikinsa

Bayan sun tashi daga aiki Daddy sai da ya koma gida ya riƙa tunanin tambayar da Shugabansu ya masa, bai dai sanar da kowa ba

Mommy zaune a falo tare da basmah Ummie ta yi wajen party tare da k'awayenta Alesha kuma na ɗaki, Sallamar da ake tayi ne yasa Mommy taja tsaki ba tare da ta amsa ba tace " Wai waye ne? " Duk da ta gane muryar matar "Amina ce"Matar ta faɗa Mommy tace "Basmah je ki buɗe ƙofa" Bubbuga ƙafa tayi tace " Ni Allah mommy bazan iya ba ina zaune ina kallo zaki wani ce naje na buɗe ƙofa ke ki tashi kije da kanki ki buɗe" Haba mai da wuk'ar yi hak'uri Alesha! Alesha!" Na'am" Alesha ta fito mommy tace taje ta buɗe ƙofa ta wuce taje ta buɗe matar da ta gani ne tsaye yasa ta saki murmushi tace "Mamma" ta faɗa jikinta ta rungumeta Mamma ta ɗago ta tana murmushi tace mu shiga daga ciki ta riƙe hannunta suka shiga sai tsakiyar falo ta saki hannunta ta samu waje ta zauna Alesha ta zauna ƙasa gefen ƙafafunta tana jin wani irin farin ciki na ganinta

Gaisawa suka yi da Mommy, mommy sai wani shan k'amshi take yi Mamma ta jima zaune a falon kiran sallah da aka fara yasa tace ma Alesha ta taso suje É—akin ta tayi sallah

Sai da suka yi sallah, bayan sun gama Alesha ta fito ta je kitchen ta ɗauki filet ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa da lemo guda biyu ta fito tana fitowa sai ga mommy ta bita da wani mugun kallo Alesha ta sunna kanta ƙasa mommy tace " Duk wannan abun da kika ɗauko ubanwa zaki kai ma? Wallahi idan baki koma kika rage su ba zan wanka miki fari shashashar banza kawai" Mommy ta juya ta wuce Alesha ta koma ta mayar da lemo guda ta kaima Mamma

Tayi kwance saman jikin mamma tace " Mamma nayi kewarki sosai kullum ina san naje wajen ki" Ba wani nan ai baki yi kewana ba da kin isko ni, ni da na damu ai kinga na kawo ƙafafuna rabon da na ganki tun sallah fa da kika je idan na kira waya kuma ina san magana dake ba'a ɗaga wa wai meya samu wayan ki? " Ta lalace" Kuma ba'a gyara miki ba ko a siya miki wata ba?" Alesha tayi shuru dan abunda bazai yiwu ba ne Mamma ke faɗa

"Yanzu bama wannan ba me yake hanaki zuwa waje na " Mommy bata bari na ina zuwa ko ina daga makaranta sai gida sai kuma idan zanje cefa ne" Cefa ne fa?" Eh" Ke ke zuwa yin cefa ne ina ita mai aikin ku " Tare muke zuwa" Okay har yanzu kina karantarwar kenan?" Eh" Allah ya taimaka " Amin" Alesha " Na'am" ta amsa muryarta da alamun bacci take ji " Idan na tambeki zaki faɗa min gaskiya" Eh " Me yake damunki ?" Ba abunda ke damuna Mamma me kika gani ?" Alesha ni zaki ce ma ba abunda ke damunki ni fa mahaifiyar ki ce kuma ba haka na sanki ba duk wanda ya sanki yasan ba haka kike ba duba kiga yadda kika rame" Alesha ta kalli jikinta tace " Ni ba abunda ke damuna" Ki dai ce ba zaki sanar min ba Alesha kin sauya sosai ban san ki da zurfin ciki ba Aleshar da na sani da bata 'boye min komai amman yanzu" Mamma ta faɗa tare da yin shuru idanun alesha sun ciko da ƙwallah tace " Ni ba abunda nake 'boyewa" ta faɗa muryar ta kamar zata yi kuka

" Idan bakya 'boye komai ai da kin sanar min" Ko ida rufe baki bata yi ba Alesha ta fashe da kuka ta k'ank'ameta tana kuka mai ban tausayi, Mamma ta shiga rarrashinta tana Bubbuga bayanta har tayi shuru ta lumshe idanunta daga haka bacci yayi awon gaba da ita saman jikin mamma, Mamma ta gyara mata kwanciyarta tana shafa kanta ita ma baccin ya ɗan ɗauke ta huɗu da minti goma Mamma ta farka ta zabura Alesha baccinta take hankali kwance, Mamma ta shafi fuskarta tare da kiran sunanta a hankali ta buɗe idanunta da suka yi ja alamun bacci Mamma ta sakar mata murmushi tace " Tashi muyi sallah" ta turo baki ta miƙe Mamma ta shiga tayo alwala itama taje tayi suna gamawa Mamma ta shirya zata wuce Alesha ta sa mata kuka Mamma bata tsaya biye mata ba dan tasa idan ta biye mata zata kai kusan magrib kuɗi ta ciro dubu goma ta miƙa mata tace ta siye wani abu, Alesha na kuka ta fito yi mata rakiya Mommy na zaune a falo tana cin abinci ta ɗago tace " A she kina nan nazata kin wuce tun ɗazu" Aah yanzu zan wuce "Yayi kyau Allah yasa an tsuka abun kirki" Mamma tayi murmushi tace "Sai anjima"Mu jima da yawa " Mamma ta wuce

Kusan wata É—aya da sati biyu da maganar Dad da Azaad amman ba wani bayani a wajen Azaad, Dad ya zuba masa ido ne kawai shi kaÉ—ai yasan abunda yake shiryawa...........

🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943*

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.