Azaad Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: AZAAD.txt
Chapter 14 of 35
page 16 & 17
Dak'yar ta miƙe taci gaba da tafiya tana kuka ta nufi d'akin ta tana dafa bango ko da ta isa ɗakin kamar rayuwarta zata fita saboda azabar da take ji ta faɗa gado ta rushe da wani marayan kuka tana mai nadamar shiga d'akin sa da tayi, sai da taci kukanta ta k'oshi kanta har ya fara ciwo bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita
'Bangaren Azaad kuwa idanunsa sun yi jajirrr tana fita ya duk'a ya É—auki hoton ya aza saman mirror ya fice daga gidan baya jin daÉ—in komai
Noor da aka tada su school gidan Ammie aka wuce da ita, tun da Azaad ya je da ita gida rabonta da su Ammie, Lokacin da taje yan gidan sun yi farin cikin ganin ta sosai
Misalin ƙarfe uku Azaad ya koma gida, tun da ya shiga falo yaji gidan tsiff sa'banin yadda ya sake tarar da shi, ko ya iske su Noor na ta zuba mata surutu ko suna kallo ko ta goya Noor a bayanta suna zagaye falon, D'akin sa ya wuce har zai shiga ya tsaya kallan jinin da duk ya ɓata wajen har zuwa hanyar dakin ta jinin duk ya bushe, wani iri ya ji a zuciyarsa ya juya yayi hanyar dakin ta yana kai bakin k'ofa ya ja ya tsaya yana tunanin ya shiga ko yayi tafiyarsa wata zuciya na faɗa masa ya kamata ya shiga ko dan ya duba halin da take ji gashi ko motsinta bai ji ba tun da ya shigo, da haka dai ya tura k'ofar ya shiga sanyayyen k'amshi mai haɗe da k'amshin turare ya bugi hancinsa, sai da ya ƙara buɗe hancinsa ya shak'i k'amshin, hangota yayi kwance saman gado ya nufi wajen tun kafin ya ƙarasa ya hango k'aton glass ɗin da ya shigar mata tafin ƙafa jini duk ya lalata zanen gadon ƙafar har ta kumbura tafin hannun ta kuma tayi ƙasa da shi jini har ya bushe ga tayis
Duk sai yaji ta basa tausayi yaji yayi nadamar abunda yayi mata, zama yayi gefen gadon ya kai hannunsa tafin ƙafar wajen glass ɗin wata irin zabura tayi ta farka daga baccin da ya ɗauke ta ya sake kai hannunsa ta fashe da kuka tare da janye ƙafarta, kallanta yayi ba tare da ya ce komai ba ya tashi ya fito ya barta tana kuka
Wayarsa ya ciro ya kira likitar gidan su tare da tura mata address É—in gidansa, ba da jimawa ba yaji wayarsa na ringing ya duba yaga mai gadi ne ya É—aga kiran tun kafin mai gadi yayi magana ya basa umurni da a barta ta shigo yana gama faÉ—in haka ya cire wayar a kunnen sa ya je bakin k'ofa ya buÉ—e har ta iso suka gaisa ya wuce da ita d'akin Alesha
" Wai wai sannu ya aka yi haka? " Likitar ta faɗa tare da zama tana kallan ƙafar Alesha da ta kumbura tace "Tun yaushe wannan abun ya sameta?" Zai kai awa huɗu " What? Awa huɗu ba'a yi gaggawar cire mata wannan abun ba yanzu silar haka wata cutar zata iya shigar ta fa gaskiya kun yi sakaci ban ji daɗin wannan abun ba wallahi kunyi sakaci musamman ma kai Azaad da ilimin ka da hankali ba zaka ɗauke ta ka kai ta hospital ba zaka barta a gida da wannan k'aton glass cikin ƙafa duba ka ga yadda saman ƙafar yayi duk ya kumbura " Shi kansa ya ga yadda ƙafar ta kumbura, Alesha ko jin su bata yi azabar da take ji kaɗai ta ishe ta
Aka zo za'a cire glass ɗin taƙi tsayi kuka Himmhimmmhimm sai da Azaad ya riƙe ta aka samu aka cire glass ɗin aka yi treatment ɗin ƙafar da hannu ta rubuta maganin da za'a siyo ta riƙa sha wanda zai sa wajen yayi saurin haɗewa
Ya je ya raki likitar ya sallameta koda ya dawo wani nauyayyen bacci ya ɗauketa, ya kafeta da ido tayi bala'in basa tausayi tunawa yayi da marin da ya mata ya runtse idanunsa da sauri tare da girgiza kai ya buɗe ido ya ɗago hannunsa da ya mareta da shi yana kallo yana jin rashin kyautawar abun da yayi mata idanunsa na a kanta yana ƙaremata kallo bai taɓa yi mata irin wannan kallon ba in fact bai ma taɓa tsayawa ya mata irin wannan kallon ba yana san ya janye idanunsa a kanta amman ya kasa mai makon haka ma sai ƙarasawa da yayi wajen ta ya zauna kusa gareta, kan ta ba ɗankwali gashin ta duk ya bazu a wajen baƙi da shi ya sha gyara gaban goshinta gashi duk ya kwanta kamar abunda aka shafa jel ya kalli la'b'banta da suka ƙara yin pink saboda kukan da ta ci, ya kalli surar jikinta ta saman kayan da take sanye da su Wani abu zuciyarsa ta fara sak'a masa yana jin wani iri a jikinsa yayi saurin miƙewa tsaye ya fito daga d'akin ya wuce d'akinsa yayi alwala ya wuce masallaci lokacin ma har an kusa sallamewa
Bayan ya dawo ya lek'a ɗakinta ya ga har yanzu bacci take yi ya wuce d'akinsa ya ga d'akin duk ya hargitse ga jininta da ya zuba ga glass zube ya juyo ya fito ya koma falo ya zauna kamar yayi ihu haka yake ji ya rasa takamammen abunda zai yi, can wani tunani ya faɗo masa na ya kira ƙanwarsa Rukayya ta zo ko zata taimaka musu da wani abu, ya ɗauki wayarsa ya bincike kaff ba number Rukayya a ciki ya ja tsaki can ya yanke shawarar kiran Ammie sai ta haɗa sa da ita,haka kuwa a ka yi bayan ya kira Ammie suka gaisa ya nemi ta ba ma Rukayya wayar yana san magana da ita, Ammie na d'aki saboda haka sai ta kira wayar Rukayya ta faɗa mata ta kira Azaad zai yi magana da ita, Rukayya da taji haka sai da gabanta ya faɗi dan tayi zaton laifi tayi
Haka ta daure ta fara kiransa kusan kira uku sannan ya É—aga tayi sallama tace "Yaya ina wuni?" Aikin me ki ke yi yanzu?" Ya faÉ—a"Ba komai " Okay ki shirya ki zo nan yanzu"To "ta faÉ—a a sanyaye
"Ba fa to ba ki shirya ki zo kiyi sauri bata jin daÉ—i "yana gama faÉ—in haka ya kashe wayar
Tashi tayi ta je ta sanar ma Ammie ta dawo ta shirya ta gama shiryawa kenan sai ga Noor ta shigo tana kuka Rukayya ta tambeta waya taɓeta tace"Gun mommyna zan je" Noor manya yanzu gudun mu ma ake yi saboda kin ga Mommynki ko? zo na shirya ki muje " ta shiryata suka wuce
Azaad ko da ya koma d'akinta ya tarar da ta tashi ta goge jinin da ya zuba ƙasa ta cire zanen gado ta ɗauko wani sabo tana tsaye tana tunanin yadda zata shimfid'a zanen gadon da mamaki yake kallanta yace "Wa ya saki duk wannan aikin? Baki ga ciwon da yake jikin ki ba ne?" Alesha bata ce da shi komai ba sai ma zama da tayi saman drawer gadon sakamakon kanta da ya sara mata ganin yadda ta riƙe kai yasa ya isa wajen da take ya dafa ta yace "Ciwo yake miki ne?" Tana jin sa tayi banza da shi ya ƙara maimaitawa zai sake magana wayarsa tayi ƙara ya ciro ya duba yaga Rukayya ce ya ɗaga wayar ya kai kunnensa ba tare da yayi magana ba ya janye wayar ya juyo ya fito ya nufi k'ofa ya buɗe, Noor da ta matsu ta ga Mommynta tana ganin an buɗe ta shigo a guje tana faɗin "Mommy! Mommy! Mommy na dawo where are u " Noor ganin bata ganta ba yasa ta juya ta kalli Papah tace" Papah ina mommyna " D'akinta" ta juya tana murna tayi d'akin
A guje ta isa wajenta tana murna suka rungume juna suna farin cikin ganin juna, ta É—auketa ta aza saman cinyoyinta tace "Wa ya kawo ki?" Aunty " Tare da aunty ki ke?" Ta gyad'a mata kai, "Mommy miye wannan?" Noor ta faÉ—a tare da nuna kad'ar da ke hannun Alesha"Na ji ciwo ne a hannu " Aww sorry Mommy"ta faÉ—a tare da yin wani abu da baki, Rukayya ta shigo ta gaidata tare da yi mata ya jiki, kasancewar Azaad ya faÉ—a mata abunda zata yi yasa ta wuce kitchen ta É—ora girki ganin marece yayi yasa ta dafa taliya ta gama ta je d'akin sa d'akin a gyare yake glass É—in da ya fashe kawai ta tattara ta kwashe ta goge jinin da ya zuba ta dawo d'akin Alesha ta zauna suka fara fira sama sama har aka yi kiran magrib Rukayya ta fara zuwa tayi alwala sannan Alesha ta tashi Noor ta bi ta suka yi alwala suka fito a zaune tayi sallah, Bayan ta sallame ta É—auko Alkur'ani mai girma tana biya ma Noor tana amsawa Rukayya ta sa su gaba kamar mai kallan tv sunanan suna karatu har aka ta da isha'i sannan suka yi sallah suka fito falo gaba É—aya
Suna zama Azaad na shigowa ɗauke da ledodi bai tsaya ko ina ba sai gaban Alesha ya aje ledodin Noor da Rukayya suka yi masa sannu da zuwa, Alesha idanunta na kan tv tayi kamar bata san da tsayuwar mutum a wajen ba, ya kalli Rukayya yace "Kin kammala girkin?" Eh " Okay je ki kawo muna"To " Ta faɗa tare da miƙewa Noor ta taso ta faɗa jikin Alesha kanta ya bugi hannunta mai ciwo tace "Washhhhhhhhhhh"Ta faɗa tare da runtse ido "Sorry mommy yana miki zafi?" Eh "Sorryyy" ta faɗa kamar zata yi kuka tace "Papah ka ba Mommy magani hannunta na zafi"Ga maganin nan na siyo mata " To Mommy zaki sha?" Alesha ta gyad'a mata kai Noor ta sake cewa "Ba zaki yi kuka ba ko?" Wallahi sai da ta sa Alesha dariya hatta Azaad sai da ya murmusa, tace"Princess bazan yi ba " Okay mommy "
Rukayya ta kawo abincin nan tsakar falo ta zubama Azaad nasa ta aje gabansa ta kalli Alesha tace"Aunty na haɗe muna waje ɗaya?" Eh" ta saka musu waje ɗaya su duka, Azaad yace ta duba cikin ledodin nan akwai nama ta miƙa ma kowa ta duba ta miƙa ma kowa gasasshen nama ne kowa da nasa ɗauri ta zauna suka fara cin abinci, Alesha bata ci naman ba Noor da Rukayya ɗauri ɗaya suka buɗe suna ci Azaad kam ya tashi da filet ɗin taliyar duniya taliya tana cikin favorite food nasa yana mutuwar son ta shi ma bai wani ci naman sosai ba ya tashi ya miƙa mata magani ya ce ma rukayya" ga fruit nan ta yanka saura kuma tasa a fridge" ya wuce d'akinsa
Bayan sun gama cin abinci ta sha magani Rukayya kuwa ta wuce kitchen da kayan ta É—ibi waÉ—an da zata yanka saura kuma tasa a fridge...............
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.