Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 25 of 35

page 32

Tafiya take ko ganin gabanta bata yi sauran kaɗan ta buge da bangon ƙofa ta tsaya ta share hawaye ta buɗe ƙofar ta fice

Tana fitowa mai gadi ya rugo a guje ya nufo fa yana faɗin "Gimbiya fita za'a yi da kayan ne ai da kin kira ni nazo na ɗaukar miki kin san bana son naga kin wahala"Wata uwar harara Ummie ta watsa masa sai da ya tsorata saboda idanunta sun yi ja sosai amman duk da haka sai yayi murmushi ya kai hannu zai kar'bi akwatin tare da faɗin "Allah ya huci zuciyarki gimbiyar mata"Tak'i miƙa masa akwatin ya sake kai hannu zai kar'ba ta daka masa tsawa tare da faɗin " Shin na ce bana so ko ana dole ne? Musa ka fita idona na rufe wallahi kaji na rantse wallahi! Wallahi na rantse da wanda ya busa min rayuwa idan ka sake min magana sai na shararamaka mari ai ka ji ni dai banza kawai saboda tsabagen rainin wayo ni sa'ar ka ce ko tsararka ce iskancin banza kawai mtssssssssssssssssssasa" ta faɗa tare da jan akwatin ta tayi gaba da sauri mai gadi ya biyo bayan ta yace" Hajiya gimbiya kiyi hak'uri abun bai..................... " Ai ko ida faɗa bai yi ba Ummie ta juyo da ɗauke shi da wani gigitaccen mari sai da ya ja baya tare da dafe kuncensa saboda iya ƙarfin ta haɗi da ɓacin ran da take ciki ta sauke masa a fuska tare da yi masa warning da hannu ta juya taci gaba da tafiya ta buɗe ƙofar gate ta fita mai gadi bai daddara ya sake biyota yana" Hajiya dan Allah kar ki tafi ki barni ki tausaya min" Ummie cike da mamaki ta juyo ta kallesa duk marin da ta masa amman sai da ya sake biyota ganin yana neman cimmata yasa ta riƙa sauri sai ga taxi ta biyo ta tare tayi sauri ta shige suka wuce

Mai gadi kamar wani ƙaramin yaro ya fashe da kuka yana kiran sunan ta ya juya ya koma ciki yayi zaune kuka kawai yake yi a haka Azaad ya dawo ya tarar da shi bayan ya buɗe masa gate ya shigo yayi parking ya kirasa ganin yana kuka a tunanin sa ko Rashi aka masa Azaad yace "Musa lafiya meya faru?da girmanka kana kuka haka kamar yaro" Mai gadi ya ƙara fashewa da kuka yace "Ta tafi yalla'bai ta tafi ta barni"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un musa hak'uri zaka yi duk mai rai baya wuce lokacin sa Ubangiji Allah ya gafarta mata Allah ya raya abun da ta bari " Azaad ya faɗa a tunaninsa matarsa ce ta rasu musamman da yaji yace ta tafi ta barsa" Mai gadi ya ɗago ya kallesa jin yana faɗin Allah ya gafarta mata yace "Yalla'bai ba rasuwa aka min ba"Ikon Allah to meya faru?" Hajiya ce ta tafi" Hajiya ta tafi?" Ya faɗa cike da mamaki yace" Wace hajiyar?" Hajiya Ummie yanzun nan ta wuce ba yadda ban yi ba dan ta tsaya kar ta tafi amman sai da ta tafiyarta " ya faɗa wani sabon kuka na taso masa

Azaad ya gyara tsayuwarsa yana kallan mai gadi cike da mamakinsa saboda Ummie ta tafi shi ne yake wannan kukan kamar wanda aka aiko ma uwarsa ko matarsa ta rasu yace "Musa saboda Ummie ta tafi ka ke wannan kukan? To miye matsalarka da tafiyarta ne?" Wallahi yalla'bai bazan 'boye maka ba ina mutuwar bala'in son hajiya Ummie idan ban sameta ba zan iya rasa rayuwata dan Allah yalla'bai ka taimaka min na aureta "ya faÉ—a tare da gurfanawa ya haÉ—e hannayesa yana rok'on sa

Azaad rasa abunda zai ce masa yayi can yace ya taso ya miƙe tsaye Azaad yace "Ya aka yi haka?" Wallahi ban sani ba lokaci ɗaya Allah ya ɗora min son ta" Shikenan nan ka daina kuka zamuyi magana "To yalla'bai zaka mata magana ne ta aure ni"Azaad yayi murmushi yace "Kai dai kawai zamu yi magana"To yalla'bai Nagode sosai "Yanzu ka daina kukan nan ka je kaci gaba da aikin ka"To " ya faɗa tare da goge fuskarsa Azaad ya wuce

Koda ya shiga cikin gida ya tarar da Alesha goye da Noor tayi bacci tana tsaye yayi sallama kusan sau uku amman hankalin ta baya nan tana can duniyar tunani sai da ya taɓata ta firgita ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya yace "Tunanin me kike haka?" Yaya Ummie ta tafi " Okay wani abu ne ya faru?" Aah " ta faɗa tare da girgiza masa kai"Okay sauketa " Bacci take yi" Ki kwantar da ita mana ta fa wuce goyo ki daina goyonta " Yaya yarinya ce fa"Yarinya ce amman ta wuce goyo ta girma"Ni gaskiya bana ganin girmanta bata wuce goyo a guna ba" To shikenan zamu gani idan cikin ci ya girma zaki goya ta " Ciki! Wane ciki?" Wanda na baki ajiya jiya " Ya faɗa tare da ɗaga mata gira ta turo baki tace "Ni ba abunda ka bani" To shikenan idan ma ban baki jiya ba yau zan tabbatar na baki " Ni dai wallahi bana so" ta faɗa tare da wucewa tayi ɗaki ya biyo bayanta

Ta shimfid'e Noor zata wuce ya janyota ya mannata da bango hannunsa kawai taji ya damk'i na shanunta yana matsa zata yi magana ya haɗe bakin su waje ɗaya duk ya kashe mata jiki ƙafafunta suna neman gagarar ɗaukar ta bakin su na haɗe ya ɗauke ta suka fito ɗakin suka yi nasa ɗakin ya kwantar da ita saman gado abubuwan da yake mata yasa jikinta ya mutu tana son ta hanasa amman ta kasa tana ji tana gani ya raba ta da kayan jikinta bata fargaba sai da taji wani azababben zafi ya kai mata ta fashe da kuka tare da sa hannu ta turasa bata san ta makaro ba don ko gezo bai yi ba, taci kuka sosai kamar me kiran sallah da ake ne ya faɗo kunnen sa da sauri ya sauka a kanta ya ɗauke ta suka yi toilet ya haɗa mata ruwan zafi ya sakata ta wahala sosai taci kuka, bayan sun yi wanka harda na tsarki tare da dauro alwala ya sake ɗauko ta suka fito ya ajeta gefen gado ya fita yaje ɗakin ta ya ɗauko mata wata riga da hijab ya saka mata ya zura mata hijab ya shimfid'a musu sallaya ya ja su sallah a zaune tayi tata sallah ko da ta gama sallah jikinta har ya fara zafi Azaad ya juyo yace" Sannu" ta ɗauke kanta wallahi Allah ya gani haushi take ji, ta tuna da Noor dake bacci gashi an yi sallah ta miƙe dakyar ta yi hanyar fita Azaad yace "Ina zaki je?" Ɗaki " ta faɗa ba tare da ta juyo ba ta wuce.................

🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.