Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 8 of 35

page 8 & 9

Kwatsam wata rana ya haɗu da wani mutume har suka fara hurd'a sosai abban Alesha ya aminta da mutumen sosai, mutumen yazo musu da wata hanya yadda zasu samu kuɗi sosai cikin k'ank'anin lokaci abban Alesha ya aminta da zancen sa hakan yasa ya basa rabin dukiyarsa ya basa rabi da sunan zasu yi kasuwanci, tun da mutumen ya tafi shuru kake ji har aka share watanni abban Alesha tun yana samunsa a waya har ya daina samunsa aka share watanni ba shi ba labarinsa abun ya damesa sosai, abu kamar wasa har aka yi shekara ɗaya mutumen bai dawo ba gashi Allah ya kawo ma abban Alesha wata jarabawa, ma'aikatarsa ta kama cikin shekara ɗaya arzikinsa ya ragu sosai har ya kai ga abincin da ake dafa ma mutane duk sati baya da wannan ƙarfin yanzu hakan yasa duk wani alkhairin da mutane suke yi masa suka daina saboda daman ba domin Allah suke yi ba

Wata safiyar juma'a da safe sun aje Alesha a makaranta za suyi final exam ta kammala SS 3 su kuma zusu wuce suje ƙauye dan ya ga gonarsa da ake masa noma har sunje sun dawo a hanyarsu ta dawowa suka samu accident gaba ɗaya motar ba wanda aka samu a raye su duka

Ko da Alesha ta dawo gida cike da farin ciki saboda exam ta musu daɗi sosai tun daga bakin gate taga mutane an taru wasu na alwala wasu kuma na zaune saman shimfid'a, gabanta ya faɗi sai da ta shiga ciki ta ƙara tsinkewa mutane sun cika sosai a harabar gidan su sai kallanta ake yi dauriya kawai tayi ta ƙara sa ciki turuss ta ja ta tsaya ganin mutum uku kwance ko motsi basa yi an lullu'be su da farin k'yalle ga jini ga mutane na kuka, yayar mahaifiyarta ce ta taso Mamma ita ma idanuwanta sun yi ja sosai alamun taci kuka ta riƙo Alesha tace " Kun ta so?" Alesha ta kalleta maimakon ta bata amsar tambayar da tayi mata sai tace " Mamma su waye waɗan nan? " Mamma tayi shuru ta kasa ce da ita komai Alesha tace " Ina mama na da abba Aminr! Aminr! " Ta riƙa kiran sunan k'anenta " Mamma ko basu dawo daga inda suka ce zasu je ne ba?" Duk dauriyar Mama akan kar tayi kuka ta kasa sai da ta fashe da kuka ta rungume Alesha tace" Kiyi hak'uri Alesha kiyi hak'uri " ta ja hannunta suka yi d'aki ta zaunar da ita sai da tayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta sanar mata abunda ke faruwa, Alesha tayi shuru Mamma ta ɗauko mata doguwar riga ta miƙa mata tace ta cire uniform ɗin ta tasaka rigar su fito falo, an shiryasu ana san a kai su makwancin su, tashi tayi ta sauya kayan suka fito falo ta tsaya wajen kanun su Daddy ya shigo tare da wasu yan uwansu aka ɗauki gawawwakin su Alesha ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi mai taɓa zuciya Mamma ta riƙo ta " Shikenan yanzu bana da kowa Mommy ta tafi ta barni abba ma haka yanzu babu wanda zamu riƙa faɗa da shi Amir ya tafiyarsa" Wallahi sai da ta ba ma duk mutanen da ke cikin falon tausayi " Shikenan bana da kowa" ta rushe da kuka mamma ta janyota jikinta tana bubbuga bayanta alamun rarrashi saboda ta kasa magana ita ma kukan na san cin k'arfinta

Koda akayi kwana uku da rasuwarsu Alesha ta rame sosai cikin yan kwanakin nan ko abinci bata ci sai aikin kuka, sati biyu da rasuwar su masu bin abba bashi suka zo aka biya su Mamma gidan ta tare da zama saboda ita ma shekara ɗaya da rasuwar mijinta yaranta maza ne kuma manya ne sauran sunyi aure biyu kuma karatu suke yi basa ma k'asar bayan wata ɗaya Mamma ta samu Daddy ta nemi alfarmar tana san ta ɗauki Alesha ta kasance a wajen ta Daddy yace bai san zancen ba shi zai riƙe ta a hannunsa Mommy ta taji shi zai riƙe Alesha baƙin ciki kamar ya kashe ta ganin ba wani abu kirki aka samu ga gadonta ba kuma zai d'auko musu wani nauyi ya ƙara musu Mamma ganin kamar Mommy bata san zama da Alesha yasa ta ƙara nacewa akan ita zata ɗauke ta ba yadda bata yi ba akan ya bata Alesha amman yaƙi amincewa dole ta hak'ura

Tun daga lokacin ta koma hannun Daddy gidan su aka rufesa, Bayan exam É—in su ta fito Daddy ya kai ta University tana University Ummie na SS 1 seconday school,

Ganin irin kulawar da Daddy yake yi mata yasa Mommy da yaranta suka fara kishi da Alesha, suka fara kai ma Daddy sukarta tun baya biye musu har ya fara biye musu, bai taɓa dukanta ba amman faɗa kam tana shan sa har sai tayi kuka, Mommy kuwa kamata take yi tayi ta jibga kamar Allah ya iko ta sannan muddin tana gida to duk wani aiki ita zata yi shi koda mai aiki su na nan kuwa, Wannan kenan

Ammie taci kwalliya ta haÉ—e cikin wani leshi mai masifar kyau ta zuba wata kafurar sarka mai tsada ta yafa babban mayafinta fuskarta É—auke da murmushi tana sauko wa su Rukayya dake zaune a falo suna d'aurin takeaway da Ammie ta sa ka su husnah ta É—ago tana kallan Ammie dake saukowa har ta iso wajen su

" Wai har yanzu baku ida ba?" Saura kaɗan ammie " Rukayya ta faɗa"Okay kuyi maza " To Ammie wai na miye wa ake haɗa ma wannan! ?" Na baƙi ne ku kama jiki sun kusa fara zuwa " Baƙi za muyi? " Yau ake auren yayan ku koma na ce an ɗaura " Rukayya da husnah suka kalli juna cikin mamaki da jin furucin ammie Rukayya zata yi magana Dad ya shigo ya ja wankan farar shadda kamar shi ne angon, su husnah suka gaishe shi yace ma Ammie " Tare muke da yan d'aurin aure suna waje yanzu zanje na du'be musu ƙofar baya dan Allah ayi k'ok'ari a aiko musu abun taɓawa " In Sha Allah yanzu kuwa" Daddy ya wuce ammie ta kama hanya zata yi kitchen Rukayya tace " Ammie wai wa ne yayan na mu yayi aure ba mu sani ba?" AZAAD " Ta faɗa tare da shigewa kitchen

Rukayya da husnah suka buÉ—e baki suna kallan juna

Mamma ta ɗauki sadakin tayi ɗakin Alesha koda ta sameta idanunta sun yi jajirrr alamun taci kuka har ta k'oshi tana ganin Mamma ta fashe da wani sabon kuka, Mamma ta zauna saman gado kusa gareta ta janyota tana bubbuga bayanta tace " Mammaaa" Naam " Kai na ciwo yake min" Alesha ba dole kan ki yayi ciwo ba kin yi zaune sai kuka kike kinga yadda idanunki suka yi kuwa Please ki daina kukan nan kinji ya isa haka kinji! baban ku ya min bayanin komai nayi farin ciki sosai duk da ba ta haka naso auren ki ya kasance ba amman ba yadda zamuyi saboda Ubangiji ya riga da ya tsara lamarinsa ba wanda ya isa ya sauya sa Wallahi tayi farin ciki sosai da Ubangiji ya nuna min auren ki Alesha na jima ina san naga kinyi aure ke ma kin kama naki gida ki duba kiga duk fa yan sa'an ki sunyi aure harda yara idan ina miki magana sai ki mayar da maganata banza yanzu gashi nan da Allah ya tashi yin lamarinsa lokaci ɗaya ya kawo miki miji har gida Allah abun godiya ne sannan gidan miji sun ce basa buk'atar komai har kayan ɗakin ki duk su zasu yi komai nan da zuwa sati uku sai ki tare a gidan ki naji babanku ya ce ya taɓa aure matarsa ta rasu ta bar yarinya Alesha ina san ki natsu ki kwantar da hankalin ki kin dai ga yadda auren ki ya kasance ba sanin juna kuka yi ba keda shi bare ace har kun shak'u kin san abunda yake so da wanda baya so dan haka dole sai kinyi hak'uri kin jire kin kai zuciyarki nesa aure ma ana son ka ya aka ƙarasa bare kuma wannan nasan ki da hak'uri da juriya to ki ƙara akan wanda na sanki da shi kin san abunda yasa ake yawan gayama ma'aurata su yi hak'uri?" Alesha ta girgiza mata kai" Saboda hak'urin cikinsa yafi yawa akan jin daɗin da ke cikin sa Alesha zan iya ce wa duk matar duniya ba za'a rasa wata damuwa a tare da ita ba dangance da zamantakewarta da mijinta ba hak'urin nan da kika sani shi ne take yi dan haka Alesha ki kasance mai hak'uri da kau da kai ki gani kiyi kamar baki gani ba ki ji kiyi kamar baki ji ba kiyi masa biyyayya gwargwadon iyawarki ki kula da yarsa tamkar ke kika haifeta hakan ma zai sa ya ƙara ganin kimar ki da girmanki Ina san ki zamo gimbiya a gidan auren ki da wajen mijin ki in Sha Allah tunda har yanzu akwai sauran lokaci zan zaunar da ke na koya miki abubuwa sosai ta yadda zaki saye zuciyar mijin ki cikin ruwan sanyi, an gyara wayar ki? " Aah" ta faɗa tare da girgiza mata kai

"Okay kar ki damu shekaran jiya yayan ki ya kira yace idan ya kira layin ki baya samu na sanar masa wayar ta lalace shi ne ya turo kuÉ—i yace a siya miki sabuwa yanzu ma haka na bayar a siyo ina tsammanin anjima ko gobe za'a kawo min wayar sai na kawo miki " Nagode sosai Ubangiji Allah ya saka masa da alkhairi Allah ya basa sa'ar karatun sa"Amin "

Mamma ta ɗaura mata sadakin a hannunta tace " Ga sadakin ki" Alesha ta kalli kuɗin tayi shuru can tace "Ni bana so ba abunda zan yi da su"Alesha kin taɓa jin an ce babu abunda za'a yi da kuɗi? Ki kar'ba ki aje zanyi tunanin abunda za'a yi da su "To Mamma amman ki aje a wajen ki zai fi"Shikenan "

Azaad tun da ya shigo abun ke basa mamaki duk da wannan ba abun mamaki bane a wajen sa dan inda sabo kusan haka gidan su yake al'umma na taruwa sosai musamman idan Dad na gari amman yanzu abunda ya fara basa mamaki na murnar da mutane ke masa suna faÉ—in Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya kansa duk ya d'aure ya kasa fahimtar abunda ke faruwa...............

🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943*

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.