Complete Hausa Novels

Azaad Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: AZAAD.txt

Chapter 27 of 35

page 34&35

Mommy zata wuce ta gaban ɗakin su Ummie taji wani irin numfashi da Ummie ke yi kamar shed'arta zata fita da sauri Mommy tayi cikin d'akin, koda ta shiga ta hangota ƙasa ta faɗo tana shure shure da ƙafa kanta yayi baya numfashinta kamar zai bar gangar jikinta a ruɗe mommy tayi wajenta tana jijjigata tana kiran sunanta, Ummie ko jinta bata yi " Mansur! Alhaji Alhaji? Mansur wayyooooooooooo Allah na shiga uku Ummie kada ki tafi ki barni dan Allah kar ki mutu" ta faɗa tare da miƙewa ta fito fuskarta duk hawaye ne tana kai falo sai ga Mansur ya shigo tace "Mansur zo" Mommy lafiya meya faru?" Ganin tashin hankali a kan fuskar mahaifiyarsa ga kuma hawaye tace" Ummie ce Ummie ce muje " Meya sameta Mommy?" Mu je Mansur " ta faɗa tare da juyawa tayi gaba Mansur na biye da ita suka yi d'akin

Turusssss ta ja ta tsaya ganin Ummie ta daina motsi Mansur ya nufi Ummie ya durk'usa yana jijjigata tare da kiran sunanta shima ya ruɗe ya ɗago ya kalli Mommy yace "Mommy bata motsi bata numfashi meya sameta?" Mommy tace " Aah aah wallahi! Wallahi Ummie baza ki mutu ba lokacin ki bai yi ba bazaki mutu ki barni ba wallahi"ta ƙarashe faɗa tare da fashewa da kuka tana jijjiga Ummie " Mu je asibiti" Mansur ya faɗa tare da miƙewa tsaye Mommy ta taimaka masa ya ɗora ta saman kafad'arsa suka fito suka nufi mota ya buɗe mazaunin baya ya sakata Mommy ta zagaya zata shiga Mansur yace "Mommy mayafin ki fa" Yi sauri je ka ɗauko min " ya wuce yaje ya ɗauko mata mayafinta suka wuce

Wata babbar asibiti suka tsaya suna shiga aka karɓe su aka yi emergency da ita Mommy ta kar'bi wayar Mansur ta kira Daddy ta shaida masa abunda yake faruwa ta sanar masa da asibitin da suke

Alesha kwance ita kaÉ—ai a falo Noor bata nan an kai ta gidan Ammie Azaad kuma ya fita, ga ciwon kan da yake damunta kusan kwana uku take fama da ciwon kai, yau ma kwance take ciwon kan ya dameta

Azaad ya shigo ya tarar da ita kwancen yace " Ba dai ciwon kan ne ba?" Ta ɗago ta kallesa tare da ƙoƙarin tashi yace "No yi kwancin ki kawai" ta koma ta kwanta tare da faɗin "Sannu da zuwa"Yawwa wai ko zamu je asibiti ne dear? Wannan ciwon kan yayi yawa " Yaya ban jima da shan magani ba" Amman ya kamata mu je a duba wannan yawan ciwon kan na mene ne " To Shikenan amman yaya mu bari zuwa anjima idan muka dawo sai mu biya mu ɗauko Noor "Okay" ya faɗa tare da zama ya ɗaura kanta saman cinyoyinsa ta ɗago ta kallesa shi ma kuma ita yake kallo tayi murmushi ta ƙara shigewa jikinsa ya tura hannunsa cikin rigarta yana matsa................... Alesha ta lumshe idanunta tana jin wani irin mugun daɗin abunda yake mata ita yanzu har mamakin kanta take duk yadda ya taɓa ta mugun daɗi take ji har Allah Allah take ya kai hannu a jikinta

Asibiti kuwa dak'yar suka samu numfashinta ya dawo suka bata taimakon gaggawa tare da binciken abunda yake damunta, Mommy sun kusa kai awa ɗaya tsaye hankalin su a tashe musamman Mommy, fitowa aka yi da ita kwance saman gado tana bacci sakamakon alluran da suka yi mata da sauri duk suka nufo ta Mommy tana kallan yar' ta ta cike da tausayi duk ta rame tayi baƙi wani ɗaki aka kai ta aka sa mata ruwa likita ya juyo ya kalli su Daddy yace "Please ku ɗan fita tana buƙatar hutu a halin yanzu " duk suka fito waje

Bayan doctor ya fito ya kalli Daddy yace"Kai ne mahaifita ko?" Eh ni ne" Daddy ya faÉ—a tare da gyad'a kai " Okay muje office ina san ganin ka" Okay " Ko na zo mu je ne" Mommy ta faÉ—a Daddy yace " Aah ki tsaya a nan kawai kar ki damu in sha Allah zata samu lafiya " Ya faÉ—a suka wuce office É—in likitan

Bayan sun shiga suka zauna likitan ya kalli Daddy yace" Yalla'bai wane irin sakaci ne haka kuka bar yar' ku da damuwa har tayi mata yawa irin haka " Wallahi likita ni bansan tana da wata damuwa ba idan ba kwanaki ba da mahaifiyarta take sanar min cewar bata da lafiya aka je aka siyo mata maganukka wallahi ban sani ba "To a gaskiya bazan ɓoye muku ba kun yi sakaci sosai saboda yar' ku tana cikin damuwa matuƙa akwai abunda take ɓoye muku wanda bata sanar muku ba ban sani ba ko bata so ku sani ne wanda sana diyar haka ya haifar mata da ciwon zuciya" Ciwon zuciya?" Daddy ya faɗa tare da miƙewa tsaye ya dafe k'irji " Kwantar da hankalinka yalla'bai "Likita taya hankalina zai kwanta kana sanar min yar'ta ta kamu da ciwon zuciya " Hak'uri zaku yi sannan muddin aka bi matakan da zamu ɗora ta a kai in sha Allah za'a ga haske " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Daddy ya faɗa tare da komawa ya zauna, likita ya basa shawara akan su lalla'bata ta sanar musu abunda yake damunta idan kuma taƙi faɗa yayi masa bayanin yadda za'a riƙa kula da ita da bata kulawa sannan a riƙa zama kusa da ita da hana mata tunanin komai ta hanyar bata labarai masu daɗi har Allah yasa ta mance da damuwar da ke damunta, Daddy yayi masa godiya sosai likitan ya rubuta maganin da za'a siyo wanda zata riƙa sha kafin su sallameta aka kuma maganin da za'a bata,
Daddy ya fito ya sanar ma Mommy duk abunda suka tattauna da likita

Ƙarfe huɗu ta farka ta buɗe idanunta tana kallan d'akin, Mommy ta lek'o kenan taga ta farka ta shiga da sauri ta yi wajenta tana faɗin " Ummie sannu kin farka sannu! Sannu mamana" ta faɗa tare da zama gefen gadon ta riƙo ɗaya hannun ta Ummie tace " Mommy ki kira min aunty" Ummie wace aunty?" Aunty Alesha dan Allah ki kira min ita" Me zata miki ke da ki ke cikin wannan condition " Mommy ki kira ta ki kirata" Ta faɗa numfashinta yana wani iri ganin haka yasa Mommy tace "Shikenan! Shikenan kwantar da hankalin ki zan kira ta Shikenan" Ki ce ta zo yanzu" To bara na kar'bo wayar Mansur " ta faɗa tare da tashi ta fita tayi tsaye tana dubin inda zata gansa saboda sun yi masallaci hanyar masallacin ta nufa sai gasu shi da Daddy tace " Kana da number Alesha ne?" Mansur yayi shuru can yace "Eh ina da" Okay kira min ita ka bani " To" ya faɗa tare da ciro wayar daga aljihu ya binciko number ya fara dialing number
Alesha sun gama sallah kenan tana kwance saman jikin Azaad wayarta ta fara ringing, Azaad yace bara na É—auko miki ya mayar da ita gefe ya tashi yaje ya É—auko mata wayar ya kawo da mugun sauri ta tashi zaune sunan da taga yana yawo akan screen É—in ne yasa gabanta ya faÉ—i saboda tun da take maganar kirki ma ba haÉ—a su take yi ba bare har ya kira ta sai dai idan wani abu ne ya faru ganin yadda tayi Azaad yace "Lafiya kuwa" Yaya Mansur ne ke kira na anya lafiya kuwa " Mansur wane Mansur?" Yaya Mansur dai " Ohh Mansur yayan Ummie?" Eh shi " Shi ma sai da yayi shuru can yace"To ki É—aga ki ji Allah yasa lafiya " Amin" ta faÉ—a tare da É—aukar kiran da ya sake shigowa a karo na uku

Tayi sallama da siririyar muryarta, muryar Mommy taji ta amsa sallamar, Mommy tace " Alesha ce?" Eh ni ce Mommy " Okay Alesha muna asibiti Ummie ba lafiya"Subhanallah Mommy meya ke damunta " Uhm Alesha bari kawai yanzun ma ta farka ne take ta kiran sunan ki tace na kira ki dan Allah ki zo" In sha Allah Mommy gani nan tafe Allah ya bata lafiya kuna wace asibitin?" Mommy ta sanar mata asibitin ta kashe wayar

"Yaya Ummie ce ba lafiya suna asibiti ta farka yanzu tana son gani na" Allah sarki Allah ya bata lafiya "Amin" Zaki iya zuwa yanzu ne?" Eh" Okay shirya sai na kai ki " ta tashi ta sauya tufafi saboda kayan da ke jikinta ba na fita ba ne Azaad kuma jallabiya ya zuba Alesha ta zura hijab ɗin ta har ƙasa suka fito, Saman hanya suka sayi Fruit ya'yan itãcen marmari

Tare suka shigo asibitin suna isa ta kira Mansur shi yazo ya kai su wajen da suke Azaad suka tsaya shi da Daddy suna gaisawa ita kuma tana gaidasa ta wuce cikin d'akin, Mommy na zaune kusa gareta basmah Kuma na gefe zaune saman kujerar dake d'akin
Koda abun ya faru bata nan tana school dawowarta ta samu labarin suna asibiti

Sallama tayi duk suka juyo suka kalleta har da Ummie, Mommy tace " Har kin iso" Eh " ta faɗa tare da nufar gadon ta aje ledar hannunta ta kalli Ummie tace"Sannu Ummie ya jikin?" Da sauƙi " Allah ya ƙara sauƙi " Mommy tace "Amin Alesha Mommy sai kallan Alesha take tun da ta shigo taga ta ƙara kyau ta cika ga wani yanayi da ta gani a tare da ita wanda ta kasa fahimtar mene ne

Alesha ta tausayama Ummie ganin duk ta rame tayi baƙi

Ummie ta kalli Mommy tace " Mommy dan Allah ku bamu waje ina son muyi magana da ita"Ummie Mu fita fa kika ce? har da ni mahaifiyarki na fita " Please Mommy magana zamu yi" To Shikenan zamu fita kinji karki damu basmah mu je waje ko " Ta faÉ—a tare da tashi suka fito ganin su yasa Daddy yace" Lafiya?" Cewa tayi mu basu waje zasu yi magana"Okay "

Alesha ta zauna inda Mommy ta tashi tace "Ummie wace irin magana ce ki ke son mu yi da baza ki yi a gaban Mommy ba "Aunty Alesha wallahi ina cikin matsanan cin damuwa da takaici wanda ni na ja ma kai na aunty Alesha duniyar nan zaune ne kawai nake a cikinta amman wallahi ban jin daɗin ta duniya ta daina min daɗi aunty Alesha duk wannan damuwar tawa ke kaɗai ce ke da maganinta " Ummie ni kuma? Taya nake da maganin damuwar da take damun ki?" Yanzu zan sanar miki amman sai kin min alƙawarin zaki amince da abunda zan faɗa miki 'Ummie taya zan ɗau alƙawarin abunda ban sani ba "Aunty Alesha kin taɓa cewa muddin kina da maganin damuwata zaki yi min don Allah ki ɗaukar min alƙawari zaki yi min maganin damuwata wallahi ke kaɗai ce zaki iya yi min maganinta don Allah aunty ki taimaka min wallahi zan iya rasa rayuwata " Kar ki sake faɗin haka Ummie in sha Allah baza ki rasa rayuwarki ba ki faɗi kawai in sha Allahu muddin ina da maganin matsalar ki zan miki" Aunty Alesha ina matuƙar son yaya Azaad Alesha ta buɗe ido tana kallanta.................

🌸🌸 AZAAD 🌸🌸

Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)

*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

*Bismillahi Rahmanin Rahim*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.