Azaad Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: AZAAD.txt
Chapter 12 of 35
page 14
Wani wulak'antaccen kallo yayi ma Ummie tun daga sama har ƙasa ya zubar ya ɗauki cup ɗin shayinsa yayi gaba Noor ta bi sa a baya, Ummie ta bi sa da kallo har sai da ta daina ganinsa, ta juyo ta kalli Alesha muryarta ta ɗan yi sanyi tace " Waye wannan?" Ta faɗa tare da kafeta da ido
"Abban Noor ne" ta bata amsa " Kina nufin shi ne wanda aka aura miki?" Ta faɗa k'irjinta na dukan uku uku " Eh shi ne meya faru?" Alesha na faɗin haka cikin Ummie ya wani irin murd'awa yayi ƙara har Alesha sai da taji ƙarar cikin ai ko nan take gudanawa ya kamata a wahalce tace " Ina ne d'aki ?" Alesha ta nuna mata da hannu a guje tayi bedroom tana shiga ta faɗa toilet jin ka ke fatattattattatttttttttt fattttttttttttttt hutttttttttt fattttttttttttttt
Alesha ta duk'a ta ɗauki kayan da ta shigo da su ta wuce bedroom, akan ƙarar zawon har Alesha sai da ta ji tace "Subhanallah to me yake damunta? Me taci ya 'bata mata ciki haka " Ta aje kayan tayi tsaye, sai ga Ummie ta fito a wahalce kamar zata yi kuka ta wuce gado ta zauna Alesha tace"Sannu bakya jin daɗi daman?" Ummie ta ɗago ta kalleta ta 'balla mata harara ta buɗe baki da zummar magana cikin ya sake murd'a mata ta miƙe ba shiri ta koma toilet, ko da ta fito kamar mai koyon tafiya a hankali take takawa ta zo ta zauna " Sannu kin san bakya jin daɗi ai da kinyi zaman ki" Dallah ni ki min shuru ki barni da abun da nake ji wannan wane irin bala'i ne da masifa abar mutum ma ya huta baza'a yi ba " Allah ya baki hak'uri" Alesha ta faɗa tare da kama bakinta tayi shuru sai ga Noor ta shigo tace " Mommy papah yace na kira ki" To zo kije ki zauna kusa da aunty bata jin daɗi " To Mommy" Kiyi mata hannu kinji?" Noor ta gyad'a mata kai
Alesha ta fita Noor taje kusa da Ummie tayi tsaye
Alesha taja tayi tsaye bakin k'ofar d'akin Azaad, duk tsawon lokacin nan bata taɓa saka ƙafarta a d'akin sa ba, kamar wacce za'a yi ma wani abu sai da ta runtse ido sosai sannan ta ɗago hannu ta k'wank'wasa k'ofar ta kusa minti uku sannan taji yace shigo, bakinta ɗauke da sallama ta shiga yana zaune gefen gado yana duba wayarsa da alama wanka ya fito saboda ya sauya kaya yanzu daga shi sai gajeren wando fari da vest fara ga alamun ruwa nan a jikinsa ta fara kallan d'akin yayi kyau sosai kamar ma yafi nata kyau ta kalli gadon ta gansa duk a hargitse d'akin ma yana buƙatar shara ta mayar da idanunta kansa, Alesha ta kafesa da ido tana kallan k'irar jikinsa ya ɗago kansa yaga yadda take kallansa ya ɗauke kansa yayi kamar bai ganta ba ya mayar da kansa ƙasa dagowarda zai yi suka haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta yayi murmushi yace " Ina abunda nasa ki dafa min?" Sorry wallahi na manta amman yanzu zan yi na kawo "Okay" ta wuce ta fita taje kitchen dan dafa masa tea ɗin da ya sakata
cikin yar' ƙaramar muryarta ta yara tace" Mommy ta ce na miki sannu bakya jin daɗi? " Ummie ta gyad'a mata kai" Uhm ni ma lokacin sai da papah ya bani magani na sha " Mtwwssssssssssssss naji dan Allah" Ummie ta faɗa cike da jin haushi dan gaba ɗaya haushin su take ji Noor tace " Aunty kema na je na ce ya baki" Ke!" Ta dakama Noor tsawa"dallah rufe min baki zabaya uwar surutu " ta faɗa tare da harararta, Noor sai da ta tsorata ta ja baya tana san yin kuka Ummie hankalinta na kan k'ofa tana Allah Allah Alesha ta dawo amman shuru shuru Noor ta juya ta kama hanya ta fita
Tana fita sai ga Mommynta zata je d'akin Azaad tace "Mommy ni bazan zauna tare da ita ba kuma ni bana son ta" ta faɗa tare da shigewa jikin Alesha " Be careful princess tea ne a hannu na da zafi, Meyasa bazaki zauna da ita ba?" Bata bata amsa ba ganin haka yasa tace"To mu je a kai ma papah tea yana jira "Suka wuce ta kai masa " Ummie jin tayi kamar ta tashi tabi su taje taga me suke yi sai addu'a take "Allah yasa ba wani abun suke yi ba na shiga uku " Wani tunani ya faɗo mata a rai tayi ihu da ƙarfi tace "Wallahi bazai yiwu ba nasan ba abunda zai yi da ita" ta dafe kanta tana jin yana mugun sara mata, ta ciro wayarta daga jaka ta lalubo wata number ta fara kira
Har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba ta sake kira sai da ya kusa katsewa aka ɗaga tace "Rufi na shiga uku Shikenan" ta faɗa tare da fashewa da kuka ta cikin wayar rufi tace " Ummie lafiya meyake faruwa? Waye baya da lafiya? " Ta tsagaita kukan tace "Wallahi dama a ce wani ne baya da lafiya zai fiye min sauk'i akan wannan abun" Topah meyake faruwa naji harda kuka big girl dake haba kar ki bada mu mana " Rufi ba zaki gane halin da nake ciki ba ne shiyasa baza ki gane damuwar da nake ciki ba wallahi ina cikin tashin hankali " To naji daina kukan faɗa min meyake faruwa?" Ummie ta share hawayenta tace" Rufi kin san wannan saurayin nawa wanda muke nema dai?" Eh wanda kike mutuwar so ɗin nan ko wanda muke yawon nema? Yes yes shi Rufi wai a she shi ne ya auri Alesha " What" Rufi ta faɗa da ƙarfi "Oh my God, wace Alesha dan ni Alesha ɗaya na sani yar' uwar ki" Hmmmmm Rufi ita ce ita ce wallahi ta aure sa " Kutumar uba taya aka yi haka ? Alesha fa "Rufi kin san na faɗa miki auren da Daddy yaso ya min naƙi amincewa to shi ne ya tunkari Alesha da maganar ta amince a she ban sani ba mutumen da nake ta nema nake mugun so shi ne aka tashi aura min naƙi amincewa "Ta faɗa tare da fashewa da matsanancin kuka
Rufi ta lallasheta ta daina kuka tace "Ki kwantar da hankalin ki in sha Allah na miki alƙawarin sai kin auresa sai ya so ki fiye da yadda kike son sa"Taya kenan Rufi?" Ohhh daɗina dake rashin hak'uri ki jira ki ji me zan faɗa ba kin ce auren na haɗi ne ba?" Eh " Kenan basa san junan su?" Eh" Ai ta kwana gidan sauk'i to ke da kika zo gidan kinga alamun ba su damu da juna ba?" Ummie tayi shuru can tace " Ni dai banga alamun so ba kuma banga alamun ƙiba " Kina ina ne yanzu?" Ina cikin gidan " okay su suna ina" Tun d'azu ya aiko yar'sa kiranta suna can tare "Topah wata sabuwa kinsan shawarar da zan baki yanzu?" Aah sai kin faɗa " Yawwa Ki kasan ce mai zama inda zai riƙa ganin ki a koda yaushe idan ya juya sannan ki riƙa yi masa kalamai masu taushi da jan hankali ta tafiya mai ɗaukar hankali kina jan wanka kina ɗan saka kaya masu kama jiki sannan idan yasa matarsa aiki kiyi maza ki karɓe aikin kije kiyi komai wahalar sa sannan kada ki riƙa barin su su biyu kawai a waje ki je ki zama ta ukun su komai za'a yi ayi a gaban idon ki sannan sai kin ɗan tsaya kin lura da abunda yake so saboda ki riƙa yi masa shi to in sha Allah muddin kika yi haka da kaɗan kaɗan zaki fara shiga ransa har yaji yana son ki ki mamaye zuciyarsa wannan plan A ne idan bai yi aiki ba zamu sake gwada wani " Allah k'awata kina ko ganin plan A ɗin nan zai yi aiki? "Sosai ma ke dai kiyi abubuwan da na ce kawai zaki sha mamaki "Wallahi shiyasa nake son ki har kin kwantar min da hankali"Kar ki damu Allah yasa kawai mu dace Mrs Azaad " Amin har kinsan naji wani sanyi sunan nan da kika kira ni da shi" Wannan sunan ai naki ne da ke kaɗai ya dace " Allah ko rufi?" Eh mana....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.