Azaad Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: AZAAD.txt
Chapter 21 of 35
page 24&25
Ta sake 'balla masa harara har ta juya ta tuna da ta yaye mayafin kuma sun haɗa ido da mai gadi, wani uban ihu tayi tare da juyowa ta kalli mai gadi wanda ya ɗan matso kusa gareta tace "Wallahi ka cuceni ka cuce ni Allah ya isar min ban yafe ba" ta faɗa cikin kuka " Wallahi bazan yafe ma ba duk wannan baƙar wahalar da na sha Shikenan ta tafi a banza ka rusa min komai ina farin ciki komai yazo ƙarshe yanzu gashi............." Bata samu damar ƙara sawa ba saboda kukan da yazo mata ga wani baƙin ciki da haushin mai gadi da ya tsaya mata wallahi a yadda take ji kamar ta samesa tayi ta duka
Ta kama hanya tana tafiya tana kuka, Mai gadi ya biyo bayanta yana faÉ—in" Dan Allah ki daina kuka ki tsaya ki faÉ—a min me aka miki ki daina kuka wallahi jin nake nima kamar na kama miki kukan dan Allah ki daina kinji gimbiya " Ummie ko jinsa bata yi tasa gaba sai kuka take a haka har ta shige ciki mai gadi ya ja yayi tsaye yana faÉ—in"Gimbiya! Gimbiya! Gimbiyata ki tsaya" ya faÉ—a sai ga hawaye shi ma ya nemi waje ya zauna bakin k'ofa
Alesha tana fitowa wanka ta ja Noor ita ma tayi mata wanka ta shiryata cikin ƙananun kaya riga da wando ta bata waya ta ci gaba da game ita ma ta shirya ta haɗe cikin ƙananun kaya riga da wando ta saka hula kalar wando basu wani kama jikinta sosai ba duk da haka sun fito mata da surar jikinta, kayan sun ɗebota sosai sun mata kyau, sai k'amshi suke zubawa ita da Noor kamar inda aka yi ɓarin turare a jikinsu, Ta wuce ta ɗauki Noor tace "Washhhhhhhhhhhhhhhhh"Noor ta kalleta tace "Mommy kin gaji?" Alesha ta gyad'a kai tare da yatsina fuska tace " I'm very tired baby" Sorry Mommy I'll tell Daddy to buy you some sweets, you're tired. Okay " ta faɗa tare da gyad'a kai
Alesha tace"Really, my dear ? " Noor ta gyad'a kai ""Alright, let's go to the living room before dad returns."Okay mommy" Suka nufi falo sai ga Ummie tafe tana kuka "Subhanallah Ummie meya faru? Me aka miki ki ke kuka?" Alesha ta faɗa lokacin da Ummie ta ƙara so wajen su amman ko tsayawa bata yi ba ta wuce bedroom, hankalin Alesha ya tashi ganin yar' uwarta na kuka ta aje Noor tace ta jirata ta zo ita kuma ta bi Ummie a d'aki
Tsaye ta tarar da ita tana kuka sosai irin na ban tausayin nan wallahi ta bama Alesha tausayi sosai duk da bata san dalilin kukan nata ba, ta dafa kafad'ar Ummie cikin sanyayar murya ta kira sunan ta tare da faɗin "Ummie dan Allah ki daina kukan nan kinji ki faɗa min meya faru" Ta faɗa cikin raunanniyar murya, Ummie ta juyo ta kalleta da idanunta da suka yi ja saboda kuka ta wurga mata harara tare da ture hannunta daga saman jikinta cikin kuka tace "Ba ruwanki da abunda yake damuna ki je kawai kiyi sha'anin gabanki" Haba ke kuwa Ummie kar ki faɗi haka mana please ki faɗa min meya faru "Idan na faɗa miki abunda yake damuna zaki min magani ne? Eh " Wallahi muddin ina da maganin damuwarki Ummie zan baki idan kuma banada zan roƙi Allah da ya yaye miki dukkan abinda yake damunki ya kawo miki mafita "Alesha na roke ki dan girman Allah ki fita wallahi bana ko san jin muryar ki bare kuma na ganki" Alesha tayi shuru tana kallanta idanunta sun ciko da k'wallah zuciyarta tayi rauni sosai
Hawaye suka zubo mata ta goge ta kai hannu zata dafa Ummie,
Ummie ta wani ja baya da sauri tare da ɗaga hannu tace "Banaso! Banaso! Ki barni Alesha " Ta faɗa da ƙarfi, Alesha ta wani marairaice fuska Ummie ta janye daga nan ta koma wani gefe ta barta nan tsaye, Ta share hawaye ta juya ta fito ta ɗauki Noor tana tafiya tana tuna abunda Ummie ta gaya mata yanzu har ta iso falo
"Papah" Noor ta faɗa Alesha ta ɗaga kai ta gansa kwance shima ita yake kallo tun da yaji alamun tafiyarta ya mayar da dubansa wajen har suka ƙara so ga k'amshin su da ya mamaye falon kallanta yake tun daga sama har ƙasa ba ƙaramin kyau tayi masa ba sai dai fuskarta babu alamun annuri a tare da ita, Sauke Noor tayi hawaye suka zubo mata tayi saurin sa hannu ta ɗauke su Azaad na kalle da ita
Ta juya da sauri ta nufi kitchen saka makon wani kuka da yazo mata Noor ta wuce wajen daddynta ta na masa surutu Azaad wani abu yaji ya tsaya masa a zuci wannan damuwar da ya gani a tattare da Alesha yasan ba zata wuce silar Ummie ba ce yana jin ta lokacin da ta shigo tana kuka amman ko kallanta bai yi ba, ya tashi zaune ya miƙe tsaye ya kalli Noor yace " Zauna nan ina zuwa kinji?" Ta gyad'a masa kai ya bi bayan Alesha
Kuka take sosai ya ja yayi tsaye bakin k'ofa yana kallanta sai da taci kukanta ta buɗe pampo ta wanke fuskarta ta juyo suka haɗa ido tayi ƙasa da kanta, takowa yayi yazo gabanta ya tsaya yasa hannu ya ɗago ha'barta idanunta a lumshe yace " Look at me " A hankali ta buɗe idanunta ta kallesa ta kuma janye idanun " Mene ne? Tell me " girgiza masa kai tayi yace "Ba komai ki ke kuka?" Wani sabon kuka yazo mata Azaad ya janyota jikinsa ya rungume, Alesha ta rungumesa sosai tana kuka ya shiga bubbuga bayanta cikin kuka take faɗin "Yaya meyasa su Ummie basa so na Mansur baya so na basmah bata so na Ummie bata so na Mommy bata so na ba wanda yake so na daddy ma...,................. Ta rushe da kuka Azaad na bubbuga bayanta alamun rarrashi kukan ya lafa ta ɗago tace "A rayuwata ban taɓa sanin na aikata musu wani laifi ba amman tunda iyayena suka rasu lokaci ɗaya duk suka juya min baya duk suka tsane ni bansan me na musu ba " Wallahi ta ba Azaad tausayi tace"Yaya ina jin zafi a nan" ta faɗa tare da nuna k'irjinta
Azaad ya buɗe fridge ya ɗauko mata ruwa ya kawo ya buɗe ya kafa mata robar ruwan a baki ta buɗe baki ta fara sha tana jin sanyin ruwan na ratsa zuciyarta taasha ruwan sosai sannan ya janye mata ya aje ya riƙo hannayenta ya kalleta yace "Wa ya gaya miki ba wanda yake son ki Yar' ki Noor tana son ki su Rukayya na son ki Mamma na son ki Ammie na son ki Daddy na son ki nima ina son ki"Ta ɗago ta kallesa yace "yes Alesha nima ina son ki so let they lose you if they think you're not enough if they don't see your value let them walk, people make time for who they care about and if they're not making time for you then believe them when they say they're too busy don't force it, if they wanted to be with you they would be if they choose something or someone else over you let them it hurts but you can't make someone feel what they don't you shouldn't have to beg for someone to care, to love you, to put in the effort, if they're okay with going weeks without talking to you or never seeing you, let them go focus on those who see your worth without you having to prove it, I always say one thing that I have stopped worrying about the thing's that I have lost , the people that I have lost, Things and people who are want to be with me are with me, So stop worry about mutanen da basu damu da ke ba basa son ki Okay we love you so much " Alesha ta faɗa jikinsa ta rungumesa tana jin wani irin sanyi da farin ciki yana ratsa gangar jikinta shima ya rungumeta sun kusa minti uku a haka sannan ta ɗago
Ya d'aura hannunsa saman fuskarta ya shafi gefen kumatun ta yace "Ki daina sama kan ki damuwa akan wannan abun ba'a san damuwa saboda ba ƙaramin illah takewa mutum ba ki daina kinji" ta gyad'a masa kai yace" Idan Allah ya kai mu gobe ku shirya zamu fita " Toh" ya ɗago ha'barta bakinsa kawai taji a nata ya shiga kissing bakin
"Papah! Papah!" Suka jiyo Noor na faɗi a bayan su Alesha tayi saurin ƙwace kanta daga gare shi tayi wajen Noor " Sweet mene ne?" Ana kiran Papah " ta faɗa tare da nuna mata waya Azaad ya zo ya karb'i wayar Alesha taja hannun Noor tace "Mu je" ya bi bayanta da kallo har suka fice ya sauke ajiyar zuciya wani kiran ya sake shigowa ya ɗaga shima ya nufi falon ya yi tsaye yana gama wayar ya aje zai zauna a ka k'wank'wasa k'ofa Alesha ta miƙa da zumma taje ta buɗe ya kalleta yace "A haka zaki je ki buɗe k'ofar idan masu aikin gidan nan suka zo wucewa suka ganki fa?" Ta koma ta zauna ya wuce yaje ya buɗe ƙofar
Mai gadi ya gani tsaye ya kallesa yace"Lafiya dai?" Uhmmm yalla'bai Alhaji uhmm daman naga hajiya ta shiga ne tana kuka wallahi duk na damu " Azaad kallansa yayi da mamaki to ina ruwansa ko me yaga tana yi harda su faÉ—in ya damu ko yayi tunanin wani abu ne ya faru, ya faÉ—a a zuci sai yace masa"Kar ka da mu ba wata matsala ba ce " To Shikenan " Azaad ya juya zai wuce" Dan Allah kace ina gaidata " mai gadi ya faÉ—a Azaad Ya juyo ya tsaya sai kuma ya juya ya rufe kofar ya koma falo................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo âœï¸( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.