Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt
Chapter 9 of 85
duka Saratu ta kawowa Nas tace,
"banson wulakanci abin harda bakar mgn?"
dariya Nas tayi sannan tace,
"babban farincikina shine na hango danki shine a gidan suke rike dashi a zaton nasu ne Alhalin ba hakan bane, gefe guda Dan nasu Yana karkashin bakar rayuwa a gidan"
Nan ta karasa mgnr tana kallon tsarin yanayin kodadden gidan da Saratu take ciki, Saratu tasa dariyar itama tace,
"Tabbas zanyi Masa riko na Allah ya tsine, domin Saiya gwammace bezo duniya ba Zan wulakanta shi a idon duniya, Zan kaskantar dashi, Zan zame Masa tamkar bakin kumurci Dan bazai taba samun farinciki daga gareni ba yyinda Dana Yana can cikin daula Ana Yi Masa rikon Gata rarrafen kafet."
Nas ta Mika hannu suka tafa tace,
"kamar kin shiga Raina kenan sai gashi kin rigani furtawa Abinda zance Miki kenan karki ragawa Dan kokadan, Dan nafiso Naga jinin Aisha na wulakanta a ido na"
Saratu tace,
"Sha kurumin ki kawata"
Nas tace,
"Tabbas mun zama kawaye sbd Wannan babban sirrin dake tsakanin mu"
Ana sukaci gaba da tattauna mugun nufin su akan Hajia Aisha.
****
Allah sarki, kana naka Allah na nashi Hajia Aisha batasan wainar da ake toyawa ba harta kayan baby's Saida ta siyawa jaririn Saratu ita kanta saratun Saida tayi Mata sutura ta fitar suna, Saratu dai murna ta isheta duk ta kosa ma ta haihu yaron cikinta ya samu Gata da daula Dan yadda taga Ana ririta cikin Hajian Nan ba karamin Gata zaisha ba, a kwana a tashi Babu wuya a wajen Allah, kamar hadin baki kuwa saiga Hajia Aisha na labour tare da Saratu, yyinda Habiba Nurse tayi ka'in da na'in akan su Duk Wanda ya ganta Kai kace har cikin zuciyar ta take tausayin Hajia Aisha yanda tabi ta kanainaye wajen, Sosai take ta zirga2 a tsakanin su biyun wasu nurses din na Taya ta wato na kasan ta, cikin hukuncin ubangiji saiga Hajia Aisha ta haifo yaronta namiji tubarkallah da sauri Habiba ta karbi jaririn tasa sauran Nurses din su gyara Hajian, saiga Saratu itama ta sullubo nata yaron a gurguje Habiba ta sake karban jaririn ya zamana Yara biyu ne a hannun ta, wata Nurse tazo karba Habiba tace,
"barsu Zan wanke su"
nurse tace,
"kar aje a hade su ne a kasa gane na kowa a ciki"
Habiba ta wurga Mata Harara tace,
"Zaki koyamin aikina ne?"
Da sauri yarinyar ta Girgiza Kai kafin ta kauce a hanya, Babu Wanda ya kawo komai a ransa sbd kowa ya sani dama Habiba Nurse itace me kula da iyayen yaran, cikin sassarfa ta gyarasu tsaf tana wani irin mugun murmushi, lkcn data Gama an wuce da iyayen dakin hutu Dan haka itama din can ta wuce, a gurguje ta Isa bakin gadon yaran kowa ta aje Mata nata wato dai yaron Hajia Aisha an sashi a gefen Saratu shi Kuma na Saratu an sashi a gefen Hajia Aisha, Ajewar ta keda wuya Hajjaju ta shigo dakin da Sallama, adan tsorace Habiba ta Amsa sallamar tana matsawa gefe, Hajjaju tace,
"Yadai na ganki duk bakida da nutsuwa kodai da matsala ne?"
Hajjaju ta tmby sbd yadda taga habiban ta firgice, Dariyar dole Nas tahau Yi tace,
"Haba Hajjaju ba wani Abu"
tayi mgnr tana nufar gadon jaririn Hajia Aisha ta dauko shi da sauri tana me mikawa Hajjaju shi tace,
"Ina tayaku murna Hajjaju ga jikan ki ya iso cikin koshin lpy"
Fadar hakan yasa Hajjaju ta manta da tuhumar da take yiwa Nas din ta rungume jaririn cikin tsananin murna tana sumbatar sa hade da mikawa Allah godiya, Fadi take,
"Ashe Rai kanga Rai me gidana? Yiiiii...."
Ta saki kuka tana matse hawaye tace,
"Ashe da rabon Zan ganka kafin kasa ta rufe min ido"
ta Kara mgnr tana zuba Masa ido sosai, kirjin Habiba Nas ne ya bada dam a ranta tace karfa tsohuwar Nan ta gano wani Abu ga jaririn Nan? Batare da Bata lkci ba tayi azamar barin dakin da sauri Dan karma Hajjaju ta tsareta da tmby Kuma a yadda take da Kama mutum tsaf saita kamo ta musamman da yanzu Bata da nutsuwa SBD faduwar gaba, Tana fita kuwa Alhaji Abdullahi na shigowa dakin shima da murna ya karbi yaron sai sumbatu yake a takaice ma har sujjada yyi ta godiyar Allah daya bashi Da, Toh Ashe duk wainar da ake toyawa Saratu tanajin su kawai dai idonta a rufe yake farinciki ne sosai ya mamaye ranta tasan danta ake ta rububi haka, yanzu ma kenan bare an koma gida Nan Dadi ya sake Kama ta a kalla dai yaronta zai taso cikin daula.
Fadin irin bidirin da aka Sha ranar sunan abin ba'ace komai, Hajia Aisha taso a hada sunan yaronta Dana Saratu tace a'a gida zata tafi sbd makota da Wanda aka Saba za'a zo ganin jariri, Hajia Aisha tace toh shikenan Nan ta hadata da goma ta arziki tace gashi Nan asha bidirin suna Albarkacin Ni'imar da Allah yyi Mana, Saratu ta karba da murna suka wuce gida, A Wannan Rana ta suna Alhaji Abdullahi Omar Mai fata ya sawa dansa suna *SAGEER* yyinda a bangaren Saratu kuwa mlm Sale ya radawa dansa suna *OMAR* Aiko takaicin sunan ya Kama Saratu kamar ta hambare mlm sale sbd sanin da tayi yyi daidai da sunan kakan yaron na Asali kenan wato baban Babansa Abdullahi, Gashi ba damar ta nuna Jin haushin ta mlm zai iya son yaji dalili to ita me zatace Masa? Shiyasa ma a takaice take kiransa da *MARU*
~~~~~~~
Bayan shekara 18, abubuwa da dama sun faru a Rayuwar gidan Saratu da gidan Hajia Aisha ciki harda sake haifar Yara Mata da sukayi saidai Wannan karon Hajia Aisha ta riga Saratu haihuwa da kusan 3mthns kafin itama saratun ta haihu, A bangaren Reno kuwa idan muka fada gidan Alhaji Abdullahi Omar zamu hango tsantsar so da kauna da ake nunawa Sageer, Sageer ya taso cikin Gata da soyayyar Ahalin sa hade da daula me dunbin yawa hakan shi yake Kara Masa girman Kai da jiji da Kai, tun Yana yaro ya taso da bakin hali da mugunta mutum ne da yake da son kansa kwarai da gske, dayawa Ansha kawo karar sa saidai a bawa mutanen hakuri su kansu iyayen basajin dadin halin na Sageer shiyasa dayawan lokuta Hajjaju kance Masa Sam Albasa batayi halin ruwa ba, shiyasa ko kadan basa shiri da shi tafi shiri da kanwar sa Safna, gashi tun Yana primary irin marasa ja dinnan ne Sam bayacin exam Kuma hakan baya damunsa sbd shi Yana Tara Yara ne irinsa tsageru suyita Wasa suna shashanci ba karatun bane a gaban sa shiyasa ake ta Masa repeating sbd Alhaji Abdullahi yace baza'a wuce dashi ba saidai yaci da kokarin sa Dan haka besa harkar kudi akai ba,
A Wannan repeating din nasa yasa Omar dake hannun Saratu yyi masa fintinkau a karatu Dan ya kasance ZAKARAN gwajin dafi a makarantar su dukda ta gwabnati ce Amma yanada kokari sosai Dan koyaushe shine ke zuwa na daya a class dinsu, sbd kokarin sa ya samu damar zuwa wata private skul dake cikin garin kanon da taimakon wani wakilin ilimi daya kaiwa primary dinsu ziyara ya fahimci kwanya da Allah ya bawa Omar din sai ya biya Masa prvt skul din gaba1 harya Gama sanadin daya hadu da abokin sa Sadeeq kenan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.