Best Hausa Novels

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt

Chapter 73 of 85

*200 kacal ya Isa ki samu cmplt littafin Nan ta hanyar turowa d ita ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻*
8/15/20, 8:09 PM - Ummi Tandama: "Shikenan ma wllhi, officer ka kawo shawara mekyau yanzu za'a gane karyar makaryata" Sageer yyi mgnr Yana karewa da dariyar mugunta domin shi ya Tabbatar wa kansa tabbas Dr. Omar karya suke, da sauri daddy ya dubi Abba daidai lkcn Abba yace, "shi gwajin jinin ya yake?" Dr. Omar ne yace, "Abba pls mu wuce" ya karasa mgnr Yana sake Jan hannun sa Wannan tozarci har Ina? Sadeeq ne da tun dazu ya Gama ganin kamannin su sosai tsakanin daddy da Mummy sai Kuma Omar yace, "ku Baku lura da physical Appearance bane? Gashi Nan tun daga kamannin su ai zai Tabbatar da cewa jinin su ne meye na zuwa hsplt?" Sageer ne ya riga tsoma da fadin, "kunji wani katon munafikin sbd Yana aminin ka ai dole kace Haka ba wata shegiya Kama dama can mutane Ana yin masu kamarsu koba Ahali guda bane" ran Sadeeq ne ya sake baci zai sake mgn daddy ya katse shi da sauri ta hanyar daga Masa hannu kafin ya dubi masu damarar yace, "I'm very sure Wannan da kuke gani jinina ne" ya nuna Dr. Omar dayake cikin takaicin hanashi tafiya da Abba yyi, yaci gaba da fadin, "but sbd kauda kokwanto yanzun Nan zamuje hsptl din" Nan kowa ya amince da hakan badan ran Omar yaso ba, Abinda yasashi saurin yadda ma da mgnr Abba shine yadda Saratu ta raineshi da yadda Abba ya kamu da Rashin lpyr Rashin mgn lkci guda shiyasama ya amince da Wannan Al'amarin bayaga Haka kuwa Sam Wannan tulin dukiyar Bata gabansa, a Haka duk suka shige mota mummy da Safna su Hajjaju sai salati ake a zuci da fatan Allah yasa Dr. Omar nasu ne. Acan bangaren saratu kuwa sunsha bulayi sosai har Rana tayi suna yawo a ciki, dakyar da sidin goshi suka samu fitowa a Wannan dokar daji da yake yiwa mutane gizo idan mutum ba yasan takan dajin bane yanzun Nan sai kansa ya juye ya Rasa hanyar fita bare su Nas da hankalin su yake a matukar tashe Kuma zuwansu na farko, a jigace suka karaso bakin titi suna numfarfashi, kallon juna sukayi bayan sun daidaita nutsuwar su Saratu Tace, "yanzu Nas Ina muka nufa?" Nas Tace, "ina kuwa muka nufa Banda muyi nesa da gari?" Zaro Ido Saratu tayi Tace, "muyi nesa da gari Ina zamu? Bayan Haka fa Sahabatu tana can Akan gwiwa haihuwa yau ko gobe bazan iya Barinta ba" tsaki Nas tayi Tace, "Toh mgnr gsky bazan koma a Kama ni ba" a rikice Saratu Tace, "suwaye zasu Kama mu?" Tsaki Nas ta sake ja Tace, "matsalata dake saratu kinada saurin mantuwa mutanen da akace musu ga Dansu na Asali kina tunanin zasu kyale mu ne?" Hankalin Saratu ne ya sake dugunzuma duk ta sake firgicewa baki na rawa Tace, "kinyi gsky Nas dole mubar garin Nan Amma fa saimun koma gida mun dauko Abubuwan amfani yadda idan muka gudu saimun Dade kafin a sake Jin duriyar mu" Nas Tace, "kinjiki da wata mgn, wanne irin mu koma gida? Mu tafi kawai duk Inda mukaje baza'a Rasa bayin Allah da zasu taimake mu ba" Saratu Tace, "gsky bazan iya fadawa Shiga kuncin rayuwa irinta da ba ke baki San yadda ake Shan wuya bane idan mutum yaje garin da besan kowa ba Kuma baida 'yan canji saika kwana ka yini baka sa komai a bakinka ba sai ruwa Bayan Haka ma 'yata Sahabatu bazan barta a kamata ba Dan nasan idan aka nemeni aka Rasa to kuwa ita za'a Kama" cikin Jin haushi Nas Tace, "sai mu tafi yanzu tun kafin lkci ya kwace Mana" Nas Tace, "yanzu Kuma? Da tsakar ranar Nan ai sai aji dadin Kama mu" cike da masifa Nas Tace, "ke idan Kika isheni Wlh zanyi tafiyata na barki haba, ya za'ai anayin Abu da zafi2 ke kina sako Sanya a ciki? Ai da tsakar ranar ne ma zamuyi Abun mu a sirrrance batare da an ankare damu ba" shiru Saratu tayi tana hango kasadar da suke kokarin Yi, Nas tayi saurin katse Mata tunanin da fadin, "kin manta da halin Alhaji Abdullahi da Hajjaju ne? Ai ba kasafai suke yarda da mutane ba Kika sani ma ko a daure mlm sale din? Kinsan Wannan mgnr ba karamin mgn bane Babu yadda za'ai kana zaune Kai tsaye Azo ace Wanda kke tari dashi ba danka bane Bayan Kuma sun Dade dashi shekara fiye da talatin dole ko ayi bincike me zurfi ko Kuma a dauresu Dan za'a ga kamar rainin hankali ne" sai yanzu Saratu taji hankalin ta ya kwanta Tace, "shikenan ma yanzu Haka suna can Ana fafatawa mu Kuma sai muyi amfani da Wannan damar mu tsere" "kwarai kuwa" Nas ta Furta hakan itama da Wannan shawarar suka fara tare Napep din datazo wucewa.
Direct AKTH su daddy suka wuce su Omar ma da motar su suka tafi shi da Sadeeq Abba Kuma yabi su daddy, suna zuwa Hospital suka wuce wajen H.O.D na laboratory, Yana ganin su daddy ya Mike jikinsa na rawa Dan kowa yasan waye Alhaji Abdullahi, Yana washe baki yace, "Alhji da kanka? Sannun ku da zuwa" ya Basu waje cikin office nasa suka zauna, Dan murmushi daddy yyi Bayan sun gaisa ya zauna Akan kujera dake office din na dauke da wasu kujerun na zaman baki hakan yasa dukansu suka samu waje, officer ne yyi wa h.o.mgn cikin nutsuwa ya sanar dashi Abinda ya kawo su, ba karamin girgiza da Wannan lamarin h.o.d yyi ba, kallon Dr. Omar dake latsa waya yyi sosai ya kalli Sageer daya Dora daya Kan daya Yana jijjiga kafarsa jifa2 yake murmushi Yana tunano Tuggun daya hada dazu jira kawai yake a sanar da result yaga yadda wasan zai kaya musamman ya turawa Faisal txt message lkcn da suke hanya yace ya gayyato duk wasu 'yan jarida da masu tashe da Wanda basa tashe a tarkato su zuwa AKTH yau ya Sami Dami a akala zai sake watsar da mutuncin Dr. Omar, Faisal dake zaune parlon sa wata yarinya tana Masa tausa ya Mike da sauri reply yyi Masa da Meke faruwa? Sageer ya sake Masa reply da I will tell you later, kaidai kayi Abinda nace coz yau akwai show.., Wannan tunanin ya sashi sake sakin murmushin mugunta daidai lkcn h.o.d da kansa ya fara musu gwajin Dan daddy ne ya nemi hakan bayaso abun ya watsu har sai an Tabbatar da gsky, ba fata yake ba Koda ace Omar ba dansa bane Toh baya kaunar Abinda zai sake taba mutuncin sa.
A bangaren Dr. Omar kuwa latsa wayar yake Amma gaba1 hankalin sa Yana wajen Meera Albarkacin Abba kawai yasashi zaman dole bayan Haka da tuni Yana can Yana tunanin Mafita. Saida akaje yin gwajin H.o.d ya dawo Yana duban daddy yace, "Alhji Ina matar da akace itace mahaifiyar Sageer?" Daddy yace, "Bata Nan" h.o.d yace, "ai kuwa itama muna bukatar ta" kirjin Abba ne ya buga Yana tunanin ya za'ai a samo Saratu? Mummy kuwa hannun ta na rawa Tace, "Bari na kirata muji" saurin dakatar da ita daddy yyi yace, "Bari na Kira mutanen Dana tura unguwar su muji ko ta dawo Dan tun dazu suka Tabbatar min da Bata Nan" Yana Gama fadin Haka ya zaro wayarsa kafin ya Kira yaga Kiran security dinsa daya tura unguwar na kiransa, karawa yyi a kunne hade da sallama, security din ne yace, "Alhji Kuna Ina ne munzo gida aka sanar Mana Kun fita" daddy yace, "Kai Dana saka jiran Wannan 'yar aikin meya dawo dakai gida?" Security din yace, "ka gafarceni Alhji Wlh sai yanzun Nan muka samu nasarar damko ta" fuska sake daddy yace, "yanzu tana Ina?" Security din yace, "tana cikin mota har Wannan nurse din da aka Mana kwatance" "Alhamdulillah kuzo Nan AKTH ku samemu a office din H.O.D na laboratory" "okay Sir." Security din ya Furta hakan Yana kashe wayar, duban sauran securities din yyi yace, "muje hospital" Nan suka sake shigewa wata motar yyinda Saratu da Nas suke bayan mota an daure musu hannuwa da kafa bakinsu a toshe duk sunyi shabe2 da hawaye hankalin su a mugun tashe. Shikuwa daddy dubansu yyi da murmushi yace, "Mun gode Allah sun kamata ita da nurse din suna tafe" take dukansu suka hau hamdala hankalin su ya kwanta, Haka kawai Dr. Omar yaji Dan tashin hankali kadan ya ziyarce shi what if aka Tabbatar ba shine Dan nasu ba Kamar yadda ake tunani? Ko kuwa idan aka gane gsky shine Dan Alhaji Abdullahi ya zai dauki lamarin? Take Wannan tunanin ya rinjayeshi kirjinsa na bugawa da sauri karon farko kenan da yaji case din ya shige shi, shi kuwa Sadeeq kasa zaman office din yyi yaki yadda ko kadan yyi nesa da h.o.d abinka da anzo gidansu wato inda yake aiki yasan kusan duk mutanen wajen, tunda ya lura da murmushin da Sageer yake yaki aminta dashi, shiyasa tun daga farkon diban jinin su daddy har zuwa cikin lab Yana biye da h.o.d, h.o.d beyi mgn ba sbd yasan Sadeeq din Yana aiki anan shima, Koda aka tuna Ana bukatar jinin Saratu h.o.d damkawa wani ma'aikacin cikin lab din jinin yyi Akan zai je ya sanar da daddy, still Dr. Sadeeq be matsa ko Ina ba ya kasa ya tsare, Dan baya bukatar a samu mistake Kona miskali zarratan, suna cikin office aka hankada Saratu da Nas zuwa lkcn an cire musu daurin da akai musu sbd kada suja hankalin mutane a Fara fuskantar Abinda ke faruwa, suna Shiga ciki kuwa jikinsu ya dinga kakkarwa especially da sukayi Ido hudu da daddy bare Mummy data hade girar sama data kasa jira kawai take a Tabbatar da gsky ta fitar Abinda ke ranta, Hajjaju kuwa na ganin su ta kasa shiru cikin bakin ciki take fadin, "shegiya algunguma ni dama tun farkon zuwanki gidan Nan naji Sam baki kwanta min arai ba Ashe akwai mugun nufi a ranki" ta karasa mgnr tana kaiwa Saratu duka a baya da iya karfin ta, cije baki Saratu tayi cikin azaba tana dukar dakai, wani dukan ta kaiwa Nas tana fadin, "marar Imani da tausayi iliminki be amfanar dake komai ba Wlh jahilin Kare ma yafiki" ta karasa mgnr tana bugunta a baya, officer ne ya riko Hajjaju data fara haukace musu sai dimar su take a baya Kamar ta samu jakkai yace, "kiyi hakuri Hajia a Gama Abinda ya kawo mu daga Nan sai adau hukuncin daya dace" Hajjaju na huci tace, "daka Barni na huce takaicina Akan wa'annan mugayen" hakuri ya sake Bata badan taso ba kuwa ta koma ta zauna, zamanta keda wuya H.o.d ya shigo Yana tmbyr wacece matar a ciki? Nan aka sake nuna Masa Saratu, gabanta ya Isa dakyar ya samu nasarar diban jininta Dan gaba1 jikin Saratu ba Abinda yake sai rawa ko kadan ta kasa hada Ido dasu sai kyarma take, Hajjaju Tace, "ahaff ai daga yadda take Wannan kyarmar kowa yasan cewa Wannan bakin Dan nata ta aje Mana a Matsayin namu saikace Aljana masu musayar Dan ruwa" Sageer da yake bin Saratu da wani matsiyacin kallo cikin tsawa yace, "ke dallah mlm ki daina yiwa mutane Wannan kyarmar jikin Nasan Wannan duk acikin tsarin kune nason hada baki a cuceni Kuma Wlh..." "Shut up...Sageer" daddy ya Fadi hakan da Dan tsawa take Sageer ya tsuke bakinsa Yana Harare Harare, Saida aka dauki lkci me tsawo kafin h.o.d ya nufo office dinsa shi da Dr. Sadeeq dake manne dashi har yanzu yaki barin sa Dan Yana tsaye akai komai akan idonsa yyinda can cikin zuciyar sa yake Addu'a da fatan zancen Abba ya tabbata, suna shiga kuwa daddy ya Mike kirjinsa na harbawa, shi kuwa Abba murna ce ta Kama shi yanzu dai za'ayi me kankat, bangaren su mummy kuwa Suma kirjinsu be daina harbawa ba sai zabga Addu'o'i suke, Safna Kamar tayi kuka sbd shiga rudani. Kallon takardar hannun sa h.o.d Bala yyi Yana Kara gyarasu, Dr. Omar dayaga Haka shima mikewa yyi Yana me harde hannayen sa ta baya yyinda Sageer ya shiga ci gaba da kada kafa Yana 'yar dariya Dan yasan shine a sama, Saida h.o.d Bala ya Gama gyarasu kafin ya dubi babban cikin officer din yace,"ni zan fada musu result ko Kaine?" Officer yace, "no Kai keda Alhakin hakan muna jinka" sake gyara tsayuwar sa h.o.d yyi Yana bin duka Ahalin da kallo kafin ya dire shi Kan Sageer dayake ta girgiza kafa cikin gadara Dan sauke numfashi yyi kadan kafin ya dubi Alhaji Abdullahi cike da girmamawa yace, "Alhaji saidai kuyi hakuri" Alhji Abdullahi yace, "hakuri kamar Yaya?" H.o.d yace, "a bisa Wannan binciken Dana gano gsky kafin nace komai Ina me bawa dukkanin ku hakuri ciki harda Kai Omar" a rude Abba yace, "Kai Likita me kke nufi?" Alhji Abdullahi kuwa kasa motsi yyi, Mummy kuwa cewa take, "meyasa zakace shi? Me kke nufi?" Ta Fadi hakan itama bakinta na rawa, Omar da yaji zancen kuwa tuni yaji wata irin zufa ta ketso Masa ta goshi hakan yasa shi nufin ficewa a office din da sauri...shima h.o.d da sauri ya damko hannun sa, kafin yyi mgn Sageer ya fashe da wata irin dariyar keta Fadi yake haba, "waya Gaya maka barno gabas take? Ai Wlh duk makircinka Omar a bayana kke karyane da Raina kazo kace daddy ubanka ne hhhh....Amma dai anji kunya" ya Fadi hakan Yana Kara wayarsa a kunne bugu daya Faisal ya dauka Sageer yace, "ku futo daga inda kuka boye Dan yanzun Nan za'a fara show..." Gaba1 mutanen office din hankalin su a tashe yake hardai Abba daya kasa nutsuwa, a zuciye Sadeeq ya cakumo wuyan H.o.d cikin matukar bacin Rai yace, "kada ka rainawa mutane hankali ka sanar damu direct Abinda ake ciki bawai ka tsaya Mana indirectly ba," hannun h.o.d na bisa hannun Omar daya damke gefe guda na kokawa da rikon da Sadeeq ya Masa yace, "Dan Allah kuyi hakuri nifa har yanzu bakuji nace ga Abinda Yake a rubuce ba hakuri fa kawai nace kuyi" officer ne yazo ya janye Sadeeq din Yana duban h.o.d yace, "kasan Wannan case din babbane Amma kana ja musu Rai ka fada Mana me result ya nuna idan yaso daga baya ka bawa Wanda kaso hakuri..." Gyara kwalar labcoat dinsa h.o.d yyi kafin yace, "ku gafarceni" Nan ya dubi takardar hannun sa zai fara mgn kenan masu daukar rahoto na gidan radio da TV har sun hallara a wajen kowa da abun daukar sa sai fadowa office din ake, Sam hankalin su daddy bekai kansu ba shi kansa h.o.d be kula dasu ba Dan ya tsorata da reaction din Ahalin Dan Haka a gurguje ya fara fadin, "a bisa duba da kwayoyin halittar ku da mukayi a duka bangarori biyun cikin hukuncin Allah ya Tabbatar Mana da cewar Dr. Omar Wanda aka Fi sani da Dr. Omar salees shine Nan asalin jinin Alhaji Abdullahi Omar Mai fata, yyinda shi Kuma Sageer Wanda Ada ake ganin shine Sageer Abdullahi Omar mai fata asalin iyayensa sune Saratu 'yar aikin gidan Alhaji Abdullahi da mlm sale......" murnace ta karade mutanen office din, sai hamdala suke shi kansa Omar besan meyasa yaji zuciyar sa tayi Sanyi ba, oga Sageer fa? Tun daga ambaton Omar na farko ya Shiga shock, yyi suman zaune bakinsa a hangame gaba1 baya iya fahimtar Abinda ke faruwa Kuma, Faisal da yaji Abinda ya girgiza Masa tunani kokarin dakatar da 'yan jaridar da suke ta dauka suke Amma Ina sun samu new topic of discussion kowa Allah Allah yake ya zanta da daya daga cikin mutanen wajen, sai a lkcn hankalin daddy ya koma kansu da mmki yake tunanin waya turosu Kuma? Sadeeq kuwa rungume Omar yyi bakinsa yaki rufuwa sbd murna Fadi yake, "Alhamdulillah" Dan murmushi Omar yyi shima ya rungume shi ta baya, kowa fara'ace fal a fuskar sa duk 'yan jaridun sun cikasu da tmby Hajjaju da murna ta isheta tayi gaba tana Basu Amsa wani Dan jarida yace, "baaba koh Zaki iya fada Mana yadda abinnan ya faru?" Hajjaju bakinta a washe tana goge busassun hawayenta Tace, "kaidai Bari dannan Wlh duniya ta lalace kaga waccar munafukar matar?" Ta nuna Saratu da kanta ke kasa jikinta ya jike jalab da gumi, Nan kuwa aka hasko ta ita da Nas, Hajjaju taci gaba da fadin, "itace Nan 'yar aikin gidan Dana, munafukar mata muna tare da ita shekara fiye da talatin Ashe cin dunduniyar mu take tana Mana zagon kasa Allah ya Isa bamu yafe Mata ba" ta karasa mgnr tana matse kwallar takaici Tace, "yaron Nan umaru ta reneshi cikin azabar rayuwa da kunci har gaba da abadan abada bazamu taba yafe mata ba muguwa marar tausayi" Nan fa dayawan mutanen wajen suka cika da Alhini anaci gaba da daukar su, masu damarar wajen ne suka tiso keyar Saratu da Nas gaba, daidai lkcn Sageer yyi firgigit daga dogon suman zaunen da yyi dalilin girgizashi da Faisal yyi, a zabure ya Mike Sam be lura da 'yan jaridar ba ya nufi gaban h.o.d Bala zai cakumar Masa wuya officer ya riko shi, sai kwacewa yake Yana tirjewa Fadi yake, "kur'ani ban yadda ba, idan na yadda da Wannan batun shege nake, Kai karyane ma Wlh biyansa sukayi" officer daya rike shi yace, kana gani fa a gabanka aka Debi jini kowa Yana Nan har result ya fito Toh Kuma wanne irin shaida kkeso bayan Wannan?" Sageer yace, "dalla sakeni kaima biyanka akai" baki hangame officer yabi Sageer da kallo yace, "tsakanin Kai da Omar waye yaje har ma'aikatar mu ya kawo mu Nan?" Sageer da ya zama kamar zararre sbd dunbin takaici yace, "dama can Kun shirya hakan shiyasa ma kuka biyoni Dan Haka wallhi bazan lamunta ba saina hada musu jini da majina" ya Fadi hakan yanayin wajen h.o.d, da sauri officer yasa sauran mutanen nasa suka Kama Sageer take suka maka Masa ankwa shima suna turoshi waje, Abba dake can gefe ba Abinda fuskar sa take sai ambaliyar hawaye, idonsa na dama na kwararar da hawayen farincikin shahadar da yyi ya bayyanar da gsky, yyinda dayan idon nasa na hagu ke malalar zafafan hawayen bakincikin halin dayaga gudan jininsa ya Shiga a dalilin bakar ashana Saratu, dukansu tasa keyarsu akayi gaba har izuwa waje Nan suka tarad da mutane jingim gaba1 hospital din ya rude dajin Al'ajabi shiyasa Kota Ina bullowa ake Ana ganewa Ido hatta majinyatan da sukejin kwarin jikinsu ba'a barsu a baya ba Nan aka fara cincirindon ganewa ido, har daga waje ma shigowa ake lbri harya fara bazawa ko'ina especially gidan TV da suke watsa abin a daidai lkcin, Kan Saratu na kasa Amma sbd zungurinta da ake Saida yasa ta dago kowa Nan ya shaida fuskar Azzalumar matar datayi Wannan danyen aikin da ita kanta nurse, Sageer kuwa Banda harbe2 ba Abinda yake sai dura ashar yake Yana surfa zagi hatta daddy ma cewa yyi biyansa akai lol# Abu dai ya baci yyinda a bangaren su Omar ya kasance duhu ya yaye haske ya bayyana, camera kuwa tayi aiki domin duk Inda ka juya flash kke gani hatta masu manyan wayoyi ba'a barsu a baya ba take wasu suka fara uploading Ana dorawa a kafafen sada zumunta labari da dumi-duminsa.
Acan bangaren Meera kuwa tun bayan da suka Gama mgn d dad ta lumshe Ido take bcci yyi awon gaba da ita abinka da dama tun Daren jiya batayi bcci ba, Koda suka Isa Adamawa lkcn la'asar tayi suna sauka dad ya hango Ahmad wato jikan inna fure kanwar kakar Meera kenan ta wajen ummah, da fara'ar sa dad yayi nuni da Ahmad din da ko kadan be hango su ba yace, "Yauwa Ameera Kinga Ahmad can ya Zo daukar mu" kallon inda dad yake nuna mata tayi daidai lkcn kuwa Ahmad ya dago kansa, Yana ganin dad ya taho da sauri da murnar sa shima, musabaha sukayi da dad cikin fara'a Ahmad ya kalli Meera yace, "sister barka da zuwa Adamawa" Dan murmushi Meera tayi kafin Tace, "Ina wuni" "lpy Alhamdulillah" Ahmad ya furta hakan Yana karbar trolley din wajenta, sun Fara tafiya kenan Ahmad yaci gaba da fadin, "Amma dai dad Bata taba zuwa Adamawa ba Koh?" Dad Yana Dan murmushi yace, "tazo Mana Amma lkcn tana Karama" Ahmad yace, "yauwa Koda naji Dan ban taba ganinta ba, ya Kare mgnr Yana sake waigawa gefen da Meera dake tafiya a slow kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.