Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt
Chapter 78 of 85
*Littafin na kudi ne, 200 Zaki turo account din Nan 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆ðŸÂ»*
8/22/20, 8:44 PM - Ummi Tandama: Nan parlon ya sake yin shiru Banda kukan Meera ba Abinda akeji, ba Kamar bangaren Omar daya daskare a wajen idonsa Akan Meera Yana mata wani irin kallo Wanda ya banbanta da duk wani irin kallo daya taba Yi mata a baya, Wannan kallon da yake mata kallo ne dayake haskowa daga can Fadar zuciyar sa, a take ya dinga Jin wasu irin kibiyar so da kaunar Meera na rige-rigen dira a hadaddiyar Fadar zuciyar sa, yanzu ne asalin zuciya da gangar jikinsa suke yiwa Meera kallon kauna badan ya kwashi Ni'ima a jikinta ba, jinta yake har cikin bargo da jijiya, tausayinta da Kuma zazzafar kaunar ta na safara a dukkanin magudanar jininsa, ya kasa daina kallon ta domin ya manta da wasu a wajen...Abban Ahmad ne yyi gyaran murya kafin yace, "tabbas mgnr Ibrahim Haka take akwai Rashin fahimta a tsakanin su duka biyun a kowanne bangare kowa yanada laifi mgnr gsky ko waye akace anyi sanadin barinsa karatu Yana matakin karshe na gamawa bazaiji Dadi ba especially medicine dinnan da a Nigeria ba karamin cin kwakwa suke ba yajin aiki da duk Abubuwan su Yana Jan su lkci me tsawo kafin ka kammala, Suna Shan gwagwarmayar rayuwa kafin su kawo Wannan stage din na matakin karshe, kaii dolene ma mutum yaji haushi Toh Amma inda matsalar take Dr. Omar beyi dogon bincike ba kafin ya yanke hukunci akan Ameera, Haka zalika Ameera shaidar data bayar tayi wauta kwarai dgske ba lalle saita Amsa hakan ba da ace tayi dogon tunani da tun a lkcn tayi hanzarin sanar dashi Koda ace yaki sauraranta ko Kuma take ta nuna mutumin dake rike da gun a Kotun gsky tayi kuruciya sosai" gyada Kai dukansu sukayi Banda Omar da har yanzu keta kallon Meera Sam besan ma me suke tattaunawa akai ba, dubansa Abba yyi yaga dai kamar baya tare dasu hakan yasa ya dubi dad, mgn sukayi kasa2 kafin Abba ya dubi Inna fure da duk tausayin yaran biyun ya kamata yace, "Mama tunda abin nasu yazo da Haka to sasanci Yana a tsakanin su saidai mu matsa dan Basu waje" kafin ma ya Ida mgnr Inna fure ta Mike zuciyar ta na fatan ace sun shirya, mikewa su dad sukayi suka fice Sadeeq dayaga Omar din har yanzu Yana wata duniyar yadan zungure shi, firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi Yana waigen Sadeeq bakinsa na rawa be Furta Masa komai ba yyi Kan Meera da take share hawaye, ganin hakan yasa shima Sadeeq din ya fice, Tashi Omar yyi ya matsa gaban Meera a hankali, Zama yyi dab da ita zuwa lkcn Meera Jan zuciyar d take ya ragu sai zuciyar ta dake harbawa da sauri duk tanajin motsin sa kusa da ita, dago hannu yyi zai jawota jikinsa ya kasa ya gwada hakan kusan sau uku Ana hudun ne ya samu kwarin gwiwar jawota jikinsa zuwa saman faffadan kirjinsa ya rungume ta tsam take kuwa suka sauke ajiyar zuciya a tare, habarsa na bisa Kan lallausan dogon gashinta sbd rolling din da tayi ya warware Yana shakar kamshin man kitson data saka sunyi kusan 5secs a Haka kafin a hankali yace, "i'm sorry Meeraaa.." ya Fadi sunan Yana Jan shi a hankali, har cikin ranta taji sunan nata Amma dai ta maze ta dago daga rungumar da yyi mata tana kallon kwayar idonsa da suke a lumshe Tace, "nice ya dace na baka hakuri sbd nayi maka asarar Rasa karatun ka daka Dade kana fama akai Kuma..." "Shiiiii...." yasa yatsan sa daya akan tattausan lips dinta yace, "it's okay Meera mu manta baya kawai" riko yatsan nasa tayi hakan yasa ya zuba mata Ido sosai, Dan sauke numfashi tayi kafin Tace, "dole ne na baka hakuri ya Omar domin kaidin na daban ne I mean ba kowane zai iya daukar Wannan abun daya same ka ba ka godewa Allah kanada kwarin zuciya" Dan murmushi yyi kafin yace, "shiyasa nace mu manta baya Meera kisa a ranki tamkar Babu Abinda kikamin a baya Nima Ina neman afuwar ki plss" ya Ida mgnr Yana hade hannayen sa biyu, hannayen ta biyu tasa ta rike hannun nasa tana Dan dubanshi a hankali Tace, "ni wacece da bazan yafe maka Dan karamin Abinda kamin ba? Abinda nakeso tun wuri shine ka fahimci gskyr Kuma Alhamdulillah anzo wajen Ina fatan Allah ya yafe mana gaba1" "Ameen" Dr. Omar ya furta hakan da murmushi Meera Tace, "Toh tunda...tunda.." sai Kuma tayi shiru, Wara mata idonsa yyi yace, "tunda me?" Meera nayin kasa da kanta Tace, "tun..da dalilin dayasa ka aureni kenan har yanzu kana iya bani takarda na Allah ya hadaka da Zabin ranka Koda yake ma ai ka samu tunda tana gida...." Ta Ida mgnr a rarrabe, shiru taji yyi bece komai ba hakan yasa ta dago tana dubansa sai taga Ashe itan yake kallo, "Ya Omarr.." ta ambaci sunan sa tana Dan girgiza shi zaton ta beji me Tace ba dazun, Dan cije lips yyi kafin ya Kama duka kafafun ta biyu Yana duban kwayar idonta yace, "tunda...tunda..tunda.. me hakan yake nufi Meera?" Zaro idonta tayi a hankali Tace, "bafa Haka nace ba" ta Ida mgnr tana Dan tura baki, "Oh Toh wacce takarda kike nufi? Takardar tsire ko balangu?" Girgiza Kai tayi da sauri tace, "No ya Omar.." "yess Meera" shima ya katse ta d mgn kafin yaci gaba da fadin, "toh idan ma takardar tsiren ne ko balangu meye a ciki? Tunda nasan unborn ke bukata" ya karasa mgnr Yana kallon saitin marar ta kasa2 zaro idonta tayi a firgice tana kokarin matsawa baya ya rikota ta Fado jikinsa, dago Kanta tayi tana kallon sa dab da fuskar sa domin har hancin su ya hade Dana juna sunajin fitar Numfashi juna Tace, "Ka daina Wannan tunanin ya Omar ni Abinda nake nufi shine takardar sak...." Bata Ida mgnr ba kuwa ya manne bakinsu tare, anan ya Shiga tsote tattausan lips dinta zuwa cikin harshen ta, dakyar Meera ta kwace tana maida Numfashi Tace, "Ya Omar mgn muke ta fahimta Amma kana kawar da zancen meyasa Haka ne?" Dubanta yyi na tsanaki kafin a takaice yace, "Karen hauka ne ya cijeni dazan sake ki Ameera?" Zaro Ido tayi dan batayi tsammanin hakan daga gareshi ba, bakinta na rawa Tace, "Toh amma ya Omarr auren namu fa..." "Ya Isa Haka Ameera" ya Fadi hakan Yana Dan
Hade fuska, ja baya ta fara Yi yayi saurin tallafo fuskar ta Yana sassauta hade fuskar da yyi kafin yace, "look Meera Koda ace bansan gskyr ba bana tunanin zan sake ki bare yanzu Dana San gskyr Abinda ya faru" lumshe idonta tayi tanajin wani irin Abu na yawo a tsakankanin zuciyar ta, hakan yasa Dr. Omar yaci gaba da fadin, "mgnr gsky shine Raina na baci a duk lkcn da Kika ambaci sakin Nan Meeraaaa..." Bude idonta tayi ta zube shi a cikin nasa cikin wani irin yanayi sai yanzu ta fahimci Abinda ke yawo a tsakankanin zuciyar tata ba komai bane face kaunar Omar da tun fil'izal take Masa, ba ko shakka ta fara sonsa a lkcn da shi din baima San tanayi ba daga ranar daya nuna fushinsa akan Abinda Sageer yaso Yi Mata daga Wannan ranar ya samu gurbi a zuciyar ta, shirun nasu shiya bawa dukkanin zuciyoyin su damar da Isar da sako ta cikin idanun su da suka kafe da juna, wayar Omar ce tayi ringing hakan ya dawo dasu duniyar kallon kaunar da suke ma juna, firgigit kuwa suka farka Meera na Sunkuyar da kanta sbd kunya, shi Kuma Omar din na zaro wayar sa a pocket, ganin Mummy yasa shi daga wayar Yana amsawa da ladabi, Mummy Tace, "yauwa Ameer akwai wani Abu da za'a Kara ne bayan Abubuwan daka lissafa?" Dan kallon Meera yyi kafin yace, "no Mummy I think Abinda nace ma ya Isa saidai Kuma ki tmbyi Safna tunda kusan komai zaizo daya" Mummy Tace, "oh Toh da sauki ma Amma dai dukda Haka wa yafi wani?" Ya fahimci me tmbyr Mummy ke nufi hakan yasa shi sake duban Meera sosai, tana zaune ne kanta a kasa matsawa yyi gefenta ya mikar da ita Meera na Masa kallon mmki, Mummy na fadin, "hello, hello kanajina kuwa?" Omar daya Gama karewa Ameera kallo yace, "hello Mummy Kamar ntwrk mgnr yasa shi daukewa" Mummy Tace, "eh bani answer tmby na" Dan cije lips dinsa yyi Kamar Yana gabanta a hankali yace, "tafi" yyi mgnr a hankali, badan Allah yasa Mummy naji sosai bama bazata ji me yace ba, "Alright" ta Fadi hakan tana kashe wayar, dama hannun sa a bisa kuqun Meera yake ya mayar da wayar cikin Aljihun sa sai a lkcn Meera ta janye rikon da yyi Mata tace, "ni zan wuce ciki" "kina tare da mijin naki Zaki wuce ciki?" Ya mata mgnr Yana rungume hannu a kirji, Dan juya manyan idonta tayi kafin Tace, "Wai bakasan Nan parlon Abba bane?" "Oh! Really?" Dan hararar sa tayi tana sauke Kai, "It's okay yanzu ma saimu koma kano ai" kallon sa tayi da sauri Dr. Omar ya girgiza Kai yace, "yess". Acan bangaren su dad da Abban Ahmad kuwa Suna barin parlon Sadeeq na bayansu Inna fure kuwa tana fitowa ta dubi Sadeeq Tace, "Wai waye ne Wannan Dan iskan Sageer da Kuma waccar 'yar banzan Shafa?" Sosa Kai Sadeeq yyi yace, "ehto gsky sanin waye Sageer lbri ne me tsawo ita Kuma wacce ta Kira da Anty shafa tare nake ganinsu saidai bansan hadinsu ba" Inna fure Tace, "yanzu Haka cikin kawayenta ne masu bakin ciki sukai mata Wannan cin mutuncin Koh?" Dad ne yace, "Mama ba kawayenta bane" kallon sa sukai da mmki, Inna fure Tace, "ka sansu kenan?" Cikin takaicin zuciya dad yace, "yaran matar da nake aure ne da" Salati Inna fure taja ta dire tana tafa hannu tace, "yau Naga debabbun 'ya'ya Kai Wannan mata sadeeya Allah ya Isa tsakaninmu da ita, saidai kayi hakuri Ibrahim Amma Wlh sadiya ta cutar da jinin ameena" Dan Numfashi dad Yaja hakan yasa Abban Ahmad yace, "Mama muje can dayan parlon ayi mgnr a nutse" Nan suka Diba zuwa dayan parlon gidan, Shidai Sadeeq mmkin furucin Dad kawai yake a Haka suka Isa Bayan sun zauna ne dad yace, "Kamar yadda na fada Miki ne tun farko mama Abubuwan daya faru da Ameera tun tana Karama bayin Kaina bane lkcn da kikaje gidana na karshe banji dadin yadda muka rabu ba tun a lkcn naso zuwa baki hakuri har nake sanar da sadiya(Mom) ta nuna min a fuska ta bani goyon baya Amma Wlh bansan ya akai na manta d mgnr ba kwata2 har mancewa nake da Ameera Tanada Dangin mahaifiya...." Nan ya fara Basu lbrn kuncin Rayuwar da Meera ta taso da yadda yyi ta nuna halin ko in kula Kan Meera da fada musu asalin su waye Shafa'atu da Jamila ya dauki kauna d son duniya ya Dora musu kamar shi ya haife su ba Abinda suka nema suka Rasa daga wajen sa sai bayan bikin yaran hankalin sa ya dawo jikinsa, soyayyar Ameera ta dawo Masa, ya fahimci zaman cin Amana mom take dashi, daga karshe yace, "a ranar da abin ya kasance shine cikin bcci na nake mafarkin Aminatu tazo min tana tunatar Dani hakkin Ameera da akaci, sai Kuma fuskar Ameera Dana gani tana kuka sosai ba karamin girgiza nayi d Wannan mafarkin ba da Allah yaso Asirin zai karye Ina farkawa da salati a bakina Abinda ya biyo baya shine Ameera Dama a kwanakin Inajin canji a jikina shiyasa komai sadiya tamin nakejin haushin ta, Koda na fito a dakina ba Abinda nake Fadi sai Kiran sunan Ameera, Sadiya na fitowa a kitchen Jin na ambaci Ameera ta saki plate din dake hannun ta cikin firgici, na matso kusa da ita Ina fadin Ina kuka kaimin Ameera...? A takaice dai duk yadda naso ta bani Amsa kasawa tayi sai cemin take Bata sani ba. A zahirin gsky naji takaici kwarai a lkcn tunanin yadda Ameera tabar gidan ya dawo min, ba Bata lkci na rabu da Wannan annobar Sadiya nasa tabar min gidana ko kwana daya Bata Kara ba dukda taso na barta na rufe idona, tun daga Wannan lkcn na bazama neman Ameera Ina takaicin kalar auren da nayi mata ba bincike ba sanin inda take zaune, Toh da Allah ya taimake ni Ina fitowa ranar da safe muka hadu da ita bakin gate." Abban Ahmad da shi kansa Ahmad daya shigo parlon da Sadeeq ba Wanda be tausayawa Ameera ba, lalle Ameera taga rayuwa Sadeeq Kuma tunani ne ya shige shi kenan idan bazai manta bafa Wannan shafar itace ta auri Sageer? Tab lalle anyi gwarama ya Fadi hakan a ransa, Inna fure na goge hawayen takaici da tausayin Meera Tace, "Insha Allahu sai Allah ya saka wa yarinyar Nan, ace tun tana Karama ake cutar ta? Kai Allah ya Isa Wlh sai sun gani a kwaryar su matsiyata" Sadeeq yace, "ai Inna fure kusan Lbrn Ameera yaso yyi Kama Dana Omar" Nan suka zuba Masa ido da mmki, gyada Kai yyi Yana gyara Zama Nan ya fada musu sauyin da akayiwa Omar lalle sun firgita dajin Wannan lbri Inna fure jikinta har rawa yake sbd firgita cewa take, "duniya Ina Zaki damu? Yanzu wa gari ya waya? Kaii Hasbunallahi wani'imal wakil...." Abban Ahmad kuwa Fadi yake, "Allahu Akbar Lalle inda ranka kasha kallo Abu sai kace a film? Koda yake ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....." Dad kuwa tsabar tausayin Omar din ma kasa Furta komai yyi Ashe na Meera Nafila ne tunda tasan iyayenta shi kuwa dungurungun aka dauke shi daga wajen su tun besan kansa ba kaii duniya akwai macuta dayawa, duk Wanda ka jawo shi inuwa daga rana sai kaga wata Rana shike kokarin turaka ranar, shi kansa Ahmad ba karamin tausayi suka bashi dukansu ba hakan yasa a ransa lalle sun cancanci su mallaki junansu domin sun dace da juna kowa yaga rayuwa.
Matsawa Meera tayi baya tana kada kanta Tace, "no ya Omar duka yaushe nazo garin? Ko sati fa banyi ba Kuma rabona da garin Nan tun Ina Karama" matsawa yyi dab da ita zai kamota ta zame tanayin hanyar kofa hakan ya sashi binta da sauri Dan yaga kamar zata gudu Aiko kafin ya karaso harta fece, dafe kansa yyi Yana takowa a hankali zuwa wajen daidai lkcn Sadeeq ya fito waje Yana Amsa Kira ya hango Omar din ya fito ita Kuma Meera tabi wata hanyar, Dan murmushi yyi Yana matsawo gun Omar din wayarsa a kunne zuwan sa wajen yyi daidai da Gama wayar tashi ya dubi Omar daya zube hannayen sa cikin Aljihun wando sa Yana bin hanyar da Meera tabi da kallo, ganin kamar baida niyar kulashi yasa shi Shan gabansa Yana tare inda yake kallon, dubansa Omar yyi Yana Dan yatsina fuska yace, "mlm lpy kke keta tsakanin mata da miji?" Gwalalo ido Sadeeq din yyi yace, "Amma Wlh Omar ka dinga Jin tsoron Allah" Omar na Dan hararar sa yace, "toh da Kai zanji tsoro? Haka kawai ka katse ni" "kuttt Amma Kai Dan iskane Wlh kaga ni duk ka maido da nutsuwar ka Nan muyi mgn" sai a lkcn Omar ya danyi murmushi yace, "Inajin ka" Sadeeq yace, "Kun daidaita ne?" Omar yace, "Eh Insha Allah" "Kai Alhamdulillah gsky naji Dadi" kallon sa Omar yyi yace, "tun dazu tare kke dasu ne?" Sadeeq yace, "hmmm kaidai Bari kawai frnd" Omar yace, "meya faru?" Sadeeq na sake sauke ajiyar zuciya yace, "Rayuwar Nan gaba dayanta cike take da Abubuwan tsoro" yanzu Kam da mmki yace, "wani Abu ne ya faru?" Dubansa Sadeeq yyi kafin yace, "ai ya Dade da faruwa ma saidai Allah ya kiyaye gaba yasa iyakar wahalar Taku kenan" Omar Adan tsorace yace, "kamin bayani yadda zan fahimta mana" Sadeeq ya Buda baki zayyi mgn kenan yaga fitowar su dad harda Ahmad dake bayansu hakan yasa ya hadiye Abinda yaso Fadi dukansu suka Isa garesu, Abban Ahmad ne yace, "toh Omar mu zamu fita saiku Kai kayanku can part din Ahmad ku zauna, gyada Kai yyi da murmushi yace, "Mun gode Allah ya saka da Alkhairi" "ba komai Omar mune da godiya" Nan sukayi masu sallama suka tafi, bayan tafiyar su ne Ahmad yace, "muje na nuna muku wajen" Amsa Masa sukai da Toh daidai zasu wuce inda Meera tabi Omar ya juya wajen yanata kallo kamar Wanda zai hango ta, kayansu suka kwashe Nan suka wuce dashi part din Ahmad da yanzu ya ware Yana musu Hira. Inna fure na saka hijab tace, "tafiya zamuyi can gidana" Asma'u dake rokon Inna fure Tace, "haba Inna duka fa kwana daya tayi Amma Zaki kwashe ta ku tafi" Inna fure Tace, "ke idan kinaso ki biyomu Amma nikam munyi gaba, maza karasa Shirin ki Ameera mu tafi" Ameera dake Sanya cikin Shirin nata tace, "Toh." Mami na parlo sai ganin fitowar su daga daki tayi tana dubansu da mmki wajen karfe 8pm kenan tace, "mama wani wajen zaku da Daren Nan?" Inna fure Tace, "gida zamu tafi" mami Tace, "Amma fa dare yyi da kin Bari sai gobe" Inna fure tace, "nayi harama nikam ke Asma'u Kira min Ahmad yazo ya kaimu" Asma'u badan taso ba Tace, "Toh" itadai Meera na gefe tana jinsu, wayarta Asma'u ta dauko kafin ta Danna Kiran Ahmad, yana tsakiyar su Omar anata Shan lbrin kwallo kowa na wasa gwaninsa Kiran Asma'un ya shigo, dagawa yyi Yana fadin, "yane?" Asma'u Ta sanar dashi sakon Inna fure, kallon Omar yyi sai Kuma yace, "toh Ina zuwa" ya karasa mgnr Yana kashe wayar, duban Omar ya sake Yi yace, "zankai su Inna gida" "harda Meera?" Omar ya Furta hakan da sauri, Dan murmushi Ahmad yyi yace, "shiyasa ma na fada maka nasan baka sani ba" dafe goshin sa Omar yyi shida yakeso zuwa Anjima yasa a Kira Masa meeran suyi mgn sai Kuma a dauke ta? Sadeeq ne yace, "Wannan Abu Dan sauki tunda kanason ku hadu a Daren Nan Kai saika karbi tukin" sai a lkcn Omar ya dago yace, "dake nasan gidan Koh?" Ahmad yace, "Wannan ba matsala bane Bari na fita da dayar motar gidan can bakin Hanya Kai Kuma saika zauna a mota na a Matsayin ni nasan Inna tana Shiga gida zata fita a motar tayi gaba a lkcn sai ku zanta kafin ta ankare" Dadi Omar yaji sosai Dan Haka yace, "Thank you" Ahmad na tashi yace, "haba ai Ana tare" Nan ya dauki key din motar sa ya bawa Omar kafin yyi hanyar waje yace ma Sadeeq, "idan na fita saika fito muje tare kaima" Sadeeq ya gyada kai, bayan fitar Ahmad ne Sadeeq ya dubi Omar yace, "Dan Allah karka bamu kunya garin zantawa a samu mishkila" hararar sa Omar yyi yace, "dake kowa irinka ne Dan iska" 'yar dariya Sadeeq yyi yace, "No tunatarwa ce" Saida Ahmad ya fitar da motar bakin layi kafin yyiwa Sadeeq waya dake sunyi exchanging numbers, mikewa yyi ya fita, shi Kuma Omar yasa kananun kaya da facing cap ya shige motar Ahmad, daidai lkcn ma kuwa su Inna suka fito Meera na tafe a sanyaye, Shiga Bayan taso Yi Inna fure Tace, "jeki gaban Nan kafata nakeso na Mike tsami take min" Meera Tace, "toh" Nan ta koma gaban motar zaton ta dai Ahmad ne, tana shiga kuwa ta juyar da kanta gefe tana kallon window hakan da tayi kuwa ba karamin birge Omar din tayi ba Ashe dai meeran tasa first class ce, a hankali ya fara driving harya Kai ga bakin layin nasu daga can nesa ya hango motar su Ahmad, hakan yasa ya fara binsu a hankali, Inna fure Tace, "oh Amadu wani lkcn kanada kirki yau tukin naka da alama irin na kwararru ne Babu jijjiga bare barin hanji" shiru motar tayi Omar be iya cewa komai ba saima dariya data bashi yyita a ciki, tabe baki tayi tace, "wani lkcn miskilancin ka ya tashi tsiyace dakai ai sai kayita Yi Mtwss" taja tsaki tana me Dan kishingida, juyawa baya Meera tayi Dan taji ba Dadi Akan shareta da yyi ta sake Juyowa da nufin kallon sa Daidai lkcn shima ya Dan jiyo da fuskar sa a hankali, a firgice Meera taso Wara baki tayi saurin rufewa da hannun ta sai dubansa take up and down Anya Omar dinne kuwa ko gizo yake mata? Toh Ina Ahmad din? Dan murmushi ya sakar mata Yana kashe mata Ido daya hade da dage gira kafin ya maida hankalin sa Kan tuki, mmike ne matuka ya Kama Meeran tanason yin mgn ba Hali sbd Inna shi kuwa Omar direct yake bin Ahmad har suka Kai ga layin da Inna fure take wayarsa tayi ringing Amma a silent take, ganin sunan Ahmad ne ya daga Kiran, "Yauwa Omar Wannan bakin gate din shi zaka Shiga" Omar na Gama ji ya katse wayar beyi mgn ba, Kai tsaye ya wuce gate din daya fada Masa me gadin gidan ya bude Yana musu barka da zuwa Inna fure ta leka ta window dake ta tashi tace, "sannu mlm Haruna" wucewa ciki Omar din yyi Yana tsaida motar kuwa Inna fure ta bude kofar baya Tace, "tunda miskilanci kkeji Saida safe ni na wuce Meera ku shigo Mana da kayan" Meera Tace, "Toh" itama tana kokarin bude kofa taji a rufe, kallon Omar din tayi da sauri taga ya zare hular kansa lallausan gashin sa suka Dan barbazu, murya can kasa Tace, "ka bude min na fita" kashe motar yyi Yana duban ta yace, "duk yadda na biyokin Nan saina barki ki tafi Haka kawai?" Meera Tace, "Toh ya Omar dare fa nayi, Kuma dai ni mezan maka" ta fada tana kawar dakai, juyo d fuskar tata yyi yace, "dgske baki San me Zaki min ba?" Meera ta girgiza kanta Tace, "eh" murmushi ya sakar mata yace, "gsky kinada saurin mantuwa" Meera Tace, "Kamar me?" Omar yace, kamata yyi ki bani goodnight ai" cikin Rashin fahimta Tace, "like how?" Omar yace, "let me show you" ya karasa mgnr Yana Rikota ta fada jikinsa shikuma yyi baya Dan ya kwantar da kujerar kokarin tashi Meera tayi Tace, "ya Omar nifa na kasa tuna Abinda kke Shirin Yi" tayi mgnr da Niyar basarwa Dan ya barta ta tafi, yace, "zan tunatar dake yanzu" yyi mgnr Yana cire hijab dinta har Dan kwalin, a tsorace Meera Tace, "ya Omar idan wani...." katse mata mgnr yyi ta hanyar rufe bakinsu, cikin shauki ya fara kissing dinta Yana me sa hannayen sa cikin lallausan gashin ta, Meera duk ta rikice yyinda Omar Kuma ya rikice da sauke numfashi dumin jikinta na rudashi gsky yyi missing dinta sosai, duk yadda taso ta kwace kasawa tayi hakan yasa jikinta yyi laushi tana amsar sakonnin da yake aika mata, a hankali ya gangaro da hannayen sa dake cikin gshi zuwa cikin rigarta yana shafata slowly, tsikar jikinta ne ya tashi matuka duk yasa tayi laushi sosai shiyasa ta Rasa karfi Dan sakonnin da yake isar mata ba kanana bane na manyan gwarzaye ne, sannu a hankali ya maida kissing din da yake zuwa wuyanta Haka zalika ya gangaro izuwa na fulanin ta daya Gama bude rigar bakinsa ya Sanya ya fara sucking breast dinta..., wayarsa ce tayi Kara sbd ya cireta a silent sai a lkcn ya dawo hayyacin sa da yake neman kaucewa, matsawa gefe Meera tayi tana gyara rigarta, hade da hararar sa, Shafa kansa yyi yace, "sorry" "bude min kofa zan wuce" ta Fadi hakan a takaice, Kallon ta yyi yace, "Meera...." Dagowa tayi tana kallon sa cije lips dinsa yyi Yana Dan matse kafafu a hankali yace, "you're so sweet I LOVE YOU" Kamar a mafarki taji wa'annan kalaman, kalaman da take fatan ace ya furta sama da sauran kalamai, kunya ce ta kamata tayi saurin rufe Ido tana kokarin tura kofar taji ya bude aikuwa da sauri ta fice tana murmushi, binta da kallon kauna yyi yanaji Kamar ya fisgota, fitowa yyi ya kawo musu kayan bakin kofa kafin ya koma mota Yana kunna motar kuwa Kiran Sadeeq ya sake shigowa, dagawa yyi yace, "Kai Wannan Kira Haka" Sadeeq yace, "Dan Allah mlm ka taho Haka nan haba" Omar yace, "Toh sa'idawa anan zan kwana" "kutt...." Sadeeq ya Furta hakan kafin ya Furta wata kalmar Omar ya katse wayar, daidai lkcn ya fito daga gate din gidan Yana hango motar su, Ahmad yace, "sai ka daina Masa tsiya gashi can ya fito" Sadeeq na dariya yace, "Barni dashi Dan iska" dariya Ahmad din yyi shima yace, "mutum da matar sa?" Sadeeq yace, "ai Ana barin halak Dan kunya Saiya hakura sai ankai Masa ita" daidai lkcn Omar ya karaso wajen su Yana Danna horn, fitowa sukayi Suna Isa wajen sa shima ya fito, Sadeeq yace, "Yauwa Asirin mu a rufe Wlh" Omar yace, "kaifa Wlh baka da mutunci" Ahmad yace, "shiyasa nace ya daina maka iya shege" Omar yace, "kyaleshi Nima zan Rama" Sadeeq yace, "oho dai nidai kaga Ahmad ka zaga damu garin Nan muga me duniyar take ciki" Ahmad yace, "da Daren Nan?" Sadeeq yace, "Bari kawai ai bamu samu nutsuwa bane da farkon shiyasa" Omar yace, "kaga Ahmad karmu biyeshi Haka kawai ba'a tashi yawo ba sai dare? A Bari zuwa gobe pls" hararar sa Sadeeq yyi zaiyi mgn Kuma ya fasa sbd ganin Ahmad wajen, Haka kuwa suka Kama hanyar komawa gida.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.