Best Hausa Novels

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt

Chapter 59 of 85

Zaki turo da 200 ta Wannan Account din 0030202448 saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻

Saida ya Gama dariyar muguntar sa kafin ya mike tsaye Yana duban Faisal yace, "Bari naje na watsa ruwa lkci ya gabato" "okay Nima Bari naje na shirya" Faisal ya furta hakan shima Yana tashi anan suka rabu. Acan wajen su Anty shafa kuwa har sun siyo duk wani snacks da suke bukata lkcn da suka dawo gida nan suka tarad da mom Ashe harta dawo, binsu da kallon mmki tayi tace, "tun dazu sai duba ko'ina nake a gidan Nan ban ganku ba Abinda ya dace ace kuna kitchen ko ya fasa zuwan ne?" Zama sukayi Kan kujera a gajiye kafin Anty Jamila tace, "fita mukayi" mom Tace, "kunsan da aiki a gaban ku kuka fita?" Anty shafa ce tace, "Mom Abinda zai amfane mu mukaje muka Nemo" tayi mgnr tana tura mata Ledar hannun ta, budawa mom tayi taji kamshin snacks ya bugi hancin ta, ta dago tana kallon su tace, "siyowa kukayi?" "Gashi Nan Kuma kin gani mom" Anty Jamila ta Furta hakan tana ci gaba da fadin, "kin sani Sarai dai Babu Abinda muka iya ta bangaren kitchen tun jiya muke fama mun gagara shiyasa muka yanke shawarar siya a waje" Girgiza Kai Mom tayi batare da wani damuwar Rashin iya girkin nasu ba tace, "dama ai bakuyi Kama da masu shiga kitchen ba idan aka samu nasarar janyo hankalin Sageer ma ai ku da kitchen saidai daga nesa" dariyar Jin Dadi sukayi kafin Anty shafa tace, "yauwa mom Ina mgnin?" Jawo jakar gefenta Mom tayi tana fadin, "tun safe da kuka ga na fice wajen bokan nawa naje dama yace yau na koma da sassafe sbd lakanin Yana jikin sanyin safiya Kuma an fiso a ranar da aka bada mgnin ayi amfani dashi shiyasa na koma" tayi mgnr tana dauko wasu kullin mgni kala biyu, bude dayar Ledar tayi tana shinshinawa kafin ta Mika musu, karba sukayi suna binta da kallo Dan Karin bayani, mom tayi murmushi tace, "Wannan shine turaren wanke tunani, a Haka zaku ganshi kamar turaren wutane Amma a zahiri akwai siddabarun da aka hada a ciki Dan Haka kunajin Sageer ya Kira yace gashi a gate daya daga cikin ku zata tafi ta turare parlon baki dashi sannan abar kaskon wutar da mgnin hayaki naci gaba da tashi Toh a daidai lkcn da Sageer ya shigo ya shaki Wannan kamshin turaren Ina me Tabbatar muku ya manta da asalin dalilin kawo shi gidan Nan, ya mance da duk wani zancen Meera dake kwanyar kansa, tunanin sa zai ta'allaka ne akan ki shafa" ta karasa mgnr tana kallon Anty shafa, murna ce ta Kamasu duka biyun Kamar su dira tsalle Dan Dadi, mom ta sake Miko musu dayar Ledar tace, "Wannan kuma shi ake Kira da cafke zuciyar Wanda kkeso, a cikin drink zaku barbada Masa bazai taba ganewa ba da zarar yasha mgnin Nan tofah aiki ya kammala domin kuwa zaiji soyayyar ki ta damqe Masa zuciya, zai koma yanzu kece a zuciyar shi ba wata can shegiya Meera ba, Ina Kara Tabbatar muku idan kukayi duk yadda nace batare da kuskure ba Toh kuwa kun Gama kame Sageer ya zama namu" ta karasa mgnr tana dariya, dariyar Suma sukayi cikin farinciki, kafin Jamila tace, "Toh Mom naji kinata Anty shafa ni Kuma Faisal din fa?" Mom tace, "ai gani nayi shi kedin yakeso ba wata a gaban shi" Jamila ta turbune fuska tace, "haba mom ko kanada kyau ai saika Kara da Wanka" dariya Mom tayi tace, "dawasa nake kema Zaki iya amfani dashi ai duk Wanda kayi nufi dashi Toh dashi mgnin zaiyi aiki Dan Haka Zaki iya Yi Masa kema" rungume mom sukayi cikin tsananin farinciki suna fadin, "Gsky mom keta dabance bamu da kamar ki" mom na dariya tace, "ai komai zan iya Yi akanku matukar Ina numfashi" Haka dai sukaci gaba da kulla tsiyarsu har suka Gama kafin suka Mike Dan zuwa yin wanka.
*******Takowa yake tun daga can saman Beni cikin izza da Isa har izuwa kasa, Meera da tun dazu take mopping batasan da sakkowar tasa ba sai kamshin turaren sa daya mamaye wajen yasa ta dago da sauri, tsaye yake ya harde hannayen sa duka biyun Yana binta da wani irin kallon kaskanci yadda kasan cleaner Haka yake ganinta, wani tsohon dogon hijab dinta ne daya Gama jemewa sbd wahala tun acan gida dashi take aiki sbd Bata cika zama Haka ba musamman idan ta lura su Anty shafa da Mom suna yawan sa mata Ido a halittar ta da yadda take ganin hasadar su a fili yasa ta ware hijab din aikin gida, yawan aikin gidan da take dashi ne yasa ya jeme ya lalace domin ya kode sosai Bata hakura dashi ba ta taho da kayanta har gidan Omar sbd can gida sunce kada ta sake ta bar musu Koda Dan kwalinta ne basa bukata, ganin cewa Nan dinman sammakal ne da gida yasa ta dauko hijab din Dan ba wani hijabai ne da ita ba Dan Basu fi uku ba idan tana sake su duka tana aiki dasu Toh kuwa lalle zata Rasa na fita unguwa, gyara tsayuwarta tayi tana Dan since hijab dinta data daure ta baya sbd kada ya hanata aiki sosai murya na rawa Tace, "barka da safiya Ya Omar" "Mtwsssss.." Dr. Omar Yaja wani irin tsaki me sauti Yana matsawa gabanta, kallon gefen kumatun ta yyi take ya tuno da Marin data sharara Masa farkon haduwar su, Wannan tunani yasa zuciyar sa ta Kara tunzura da ita, ba tsammani Meera data kafe shi da ido taji ya kamo mata haba, kallon sa tayi da mmki zatayi mgn taji rikon bana Masa yyi mata ba, cikin kaushin murya yace, "Kece mace ta farko data taba breaking record a tarihin rayuwata" yyi mgnr Yana matse mata gefe da gefen habarta cikin mugunta Kamar Wanda za'ayiwa yaro durar mgni, jijjiga kanta Meera ta farayi taji kikam ta kasa kwacewa daga hannun sa, yyinda Kuma Dr. Omar yaci gaba da fadin, "bansan ke wacce irin mummunan kaddara bace a gareni dahar ace ranar farko da muka fara haduwa Kika samu zarrar wanka min mari a fuska" ya karasa mgnr Yana cije lips dinsa sbd zafin tuno da yadda ta marenshin, kwalla ce ta fara cika mata Ido tana kakarin mgn so take ta bashi hakuri Amma ya rike mata bakin, "da wayo na dai iyayena Basu taba marina ba saike kazama dake" yyi mgnr Yana bin jikinta da kallo na wulakanci kafin ya sakar mata bakin hade da dauketa da wani Marin bazata, dukawa Meera tayi kasa a gigice jikinta na rawa tana share hawayen dake sintiri Akan fuskar ta cikin Kuna da radadi, wani tsakin Dr. Omar ya sake ja yanajin Kamar ya dauketa yyita buga kwallo da ita har saita babbale zai huta yaji Dadi, ganin kamar Yana batawa kansa lkci ne ya saki wuci me zafi kafin yyi azamar barin gidan gaba1, Yana taku na daya Ana biyun yaji an kamo Masa kafa, juyowa yyi a tunzure yaga Meera ta hade hannayen ta biyu cikin roko tace, "Dan Allah ya Omar Dan Allah kayi hakuri Wlh duk Abinda nayi maka daga haduwar mu har kawo yanzu yanada dalili Kuma..." "Good point" Dr. Omar ya Furta hakan Yana Fisge kafarsa data rike San d tayi ransa a hade yace, "Tun kafin ki furta hakan na fahimta tun bayan da Kika Kara Tabbatar min da dalilin d kike ikrari yanzu, yeah na sani, da dalili Mana, ai duk Abinda kikayi shiri ne Right?" Hankali tashe tace, "no ya Omar ba Abinda kke nufi bane fa? Pls ka fahimceni" Dan murmushin takaici Omar yyi Yana me hade fuska Kamar farko duban cikin kwayar idonta yyi sosai yace, "ki godewa Allah Kinyi nasara akan Omar a cikin Shirin ku na takun farko, but yanzu aka fara wasan Ina me Tabbatar Miki bazaki sake cin nasara Akaina ba ke da munafikin naki Sageer a sannu a hankali saina koya muku hankali dukan ku" yyi mgnr yana me barin wajen cikin takunsa na Isa ko waiwayen ta be karayi ba, dukawa a wajen Meera tayi tana me fashewa da kuka Fadi take, "ka cuceni Sageer, Insha Allahu Nima bazan barka ba zanci gaba da Kai kukana wajen Allah ya bimin hakkina agun duk Wanda ya zalunce ni" ta karasa tana ci gaba da kukan ta. Dr. Omar kuwa Koda ya fito a gida direct ya wuce AKTH Dan yau yasan su Dr. Sadeeq basuda Exam, saida ya shiga ciki ma Dr. Omar ya Kira Dr. Sadeeq a waya, Bayan sun gaisa ne Dr. Omar yake sanar Masa ai gashi Nan yazo ciki, Dr. Sadeeq yace, "Toh ka karaso mana" Dr. Omar yace, "no akwai wani uzuri daya kawoni ne" "okay Bari na fito" Dr. Sadeeq ya Furta hakan Yana kokarin kashe wayar yaji yace, "pls inaso ku taho da Dr. Amina" Da mmki Sadeeq yace, "Me kace?" Dr. Omar na tabe baki Kamar Yana gabansa yace, "nasan kaji" yyi mgnr Yana katse wayar, bin wayar da kallo Dr. Sadeeq yyi Yana fatan ace ba wani tuggun Dr. Omar yake Shirin Yi ba, ganin tsayuwar bazata kaishi ko'ina ba yasa ya Mike Dan Nemo inda Dr. Aminan tayi, Yana bude kofa kuwa sai Gata ta taho itama zata shigo, matsawa gefe Dr. Sadeeq yyi yace, "yauwa shikenan ma" binsa da kallo tayi tace, "kamar ya?" Dr. Sadeeq yace, "Omar ke neman ki" "Da gske?" Ta Furta hakan da karfi bakinta yaki rufuwa, Tsayawa kallonta Dr. Sadeeq yyi cikin mmki yace, "look Amina me kike shiryawa abokina ne Haka?" Dan daidaita nutsuwar ta tayi tana kawar da Kai gefe tace, "me zanyi Masa kuwa?" Girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi Dan ya kasa yadda da ita fatansa dai Allah yasa ba wani mugun abin taje ta shirya Kan Omar ba har yake nemanta Haka, Katse Masa tunanin tayi da fadin, "Yana Ina?" "Biyoni" Dr. Sadeeq ya furta hakan a takaice, binsa tayi da sauri kamar ma zata wuce shi duk Dadi ya kamata daman yau take Shirin taje har gida ta ciwa Saratu mutunci sbd Taki gaya mata komai akan Abinda ta Sata sai gashi cikin ruwan sanyi yazo, tun kafin su Isa wajen take baza ido taga ta inda zata ganshi Amma wayam take gani babu shi Babu Alamar sa, Dan batasan da motar sa ba shikuwa Dr. Sadeeq ya hango inda yake sbd motar tasa, har zata bude baki tayi mgn kenan Taga ya fito daga wata mota me matukar sheki da walwali, kasa cire idonta tayi a kansa Dan ba karamin tafiya da ruhinta yyi ba Wannan wankan daya dauka da motar daya fito ba karamin dacewa dashi tayi ba, Mgnr da suka fara ne ta dawo da tunanin ta kansu, cikin rawar Kai tana ganin kamar yanzu yazo hannu tace, "Omar barka kwana biyu ya gida" ko kallon inda take ma beyi ba saima maida hankali da yyi kan Sadeeq suna mgnr exam, Sadeeq yace, "ai Omar mutanen Nan sun Karo wulakanci dakyar ma idan dukanmu zamu haye" da mmki Dr. Omar yace, "duk sbd me?" Dan tsaki Dr. Sadeeq yyi yace, "nake Gaya maka idan Ana neman mugayen malamai akazon Kan na medicine an gama, wani abun ma idan kaga Ana tmbyr ka Kai kasan ma ba'a taba nuna maka shi a aji ba, Amma sbd mugunta irin tasu ko kula da hakan basayi sunfi maida hankali Akan matan faculty din" Cije lips Dr. Omar yyi cikin Jin haushi yace, "Kuma a cikin ku a Rasa Wanda zaije yyi mgn akai?" Rike baki Dr. Sadeeq yyi yace, "waye ya Isa yyi mgn? Kasan mafi akasari da wuya da sidin goshi aka kawo final year dinnan Toh dayawan mutane musamman mazan faculty din kowa yyi shirune sbd kada ya jawowa kansa Kora Dan kowa Fadi yake tunda suka ki raga maka basuji kunyar korar ka ba Toh kuwa Babu Dan iskan da zasu ragar masa" Dan hucin takaici Dr. Omar yyi Yana Kara Jin tsanar duk wani shugaba da baya aikin sa tsakani da Allah abubuwa duk sun gurbace komai ya koma saida Hanya. Dr. Sadeeq ne ya dafa kafadar sa yace, "Ko zan iya Baku waje?" Yyi mgnr Yana nuna Masa Dr. Amina datayi tsaye ta kasa mgn Dan ta fara Shan jinin jikinta, Kallon sa Dr. Omar yyi Yana hade Rai yace, "ita din wa kenan?" Da mmki Dr. Sadeeq yace, "kace na taho da Dr. Amina" dafe goshin sa Dr. Omar yyi cikin yanayi na wulakanci yace, "na manta ne kwata2" yyi mgnr Yana jifan Dr. Aminan da mugun kallo, ja baya Dr. Sadeeq yyi bece komai ba yana jiran yaga Abinda Abinda zai faru, Dan taku kadan Dr. Omar yyi zuwa gabanta kafin yace, "Dr. Amina Koh?" Dr. Amina data fara tsurewa da lamarin sa tace, "eh" ta furka hakan bakinta na rawa, "Good" Dr. Omar ya furta hakan Yana me sake tsare gira sosai yace, "Da alama kin manta waye ni Koh?" Girgiza Kai Dr. Amina tayi ta kasa mgn, Dr. Omar Yaja tsaki yace, "Koda yake bansan wacce irin marar zuciya bace ke ko nace 'yar anace" zaro Ido Dr. Amina tayi tana kallon sa, "Yes kinma wuce Haka, but Bari Kiji last warning" yyi mgnr Yana kausasa muryar sa, "Matukar na sake Jin mahaifiyata ta karamin mgn a kanki you will be in trouble Zaki Sha mmkina I swear" ya furta hakan cikin kausasa murya sosai, ba karamin tsurewa Dr. Amina tayiba bakinta na rawa Tace, "Dan Allah kayi hakuri Dr. Omar bazan sake ba kaji?" Wara hannun sa Dr. Omar yyi irin be damu dinnan ba yace, "Wannan Kuma ruwanki" ya Furta hakan Yana juya Mata baya hannun sa yasa cikin Aljihu dayan hannun Yana shafa sumar kansa ya Dan jiyo a kaikaice yace, "tun kafin zuciyata tafi karfin controlling din da nake yanzu ki bace min da gani kafin na canja Miki kamanni" ya furta hakan da tsawa, ai kuwa Koh karasa mgnr da yake beyi ba Dr. Amina ta fece a wajen har tana tuntube.
Dr. Sadeeq dake kallon drama tun dazu ne ya matso Yana 'yar dariya ya dafa kafadar Dr. Omar yace, "meya hadaku ne da mutuniyar?" Dan tsaki Dr. Omar Yaja Yana me cire hannun Sadeeq din yace, "bar Wannan munafukar mana" Dr. Sadeeq yace, "tofah meya faru?" Yatsina fuska Dr. Omar yyi kafin ya gayawa Dr. Sadeeq komai Abinda ake ciki, Dr. Sadeeq yace, "Kai Amma Dr. Amina ta Bata wayonta banyi zaton zatayi Haka ba" tabe baki Omar yyi yace, "wasu matan ne bansan meyasa ba gaba1 basuda saiti" "Kwarai kuwa abindai sai du'ai" Dr. Sadeeq ya furta hakan Yana ci gaba da fadin, "ya madam?" Hararar sa Omar yyi Yana kokarin bude kofa yace, "bansan wacce kke mgn ba" da mmki Sadeeq yace, "kardai tsawon Wannan lkcn sati guda kenan baku daidaita ba?" Dr. Omar Yana zama cikin mota yace, "Sadeeq kenan wanne irin daidaito kke nufi?" Sadeeq yace, "Kai da Ameera Mana ya kamata ka sauke hayakin Kan Nan naka ku fuskanci juna na tabbata yarinyar Nan zatayi maka bayanin dalilin dayasa tayi maka Wannan shaidar" Yatsina fuska Dr. Omar yyi yace, "Banda lkcn dazan tsaya sauraron karerayin ta" Kama baki Dr. Sadeeq yyi yace, "Amma dai kaikam kanada taurin Kai Wlh" dage kafada Dr. Omar yyi kafin yace, "zan wuce wajen aiki sai mun hadu Anjima" ja baya Dr. Sadeeq yyi yace, "dama dai zuwan ba nawa bane Rashin mutunci kazo Yi" Dan murmushin gefen baki Dr. Omar yyi Yana juya steering motar sa batare da yace Masa komai ba ya dago Masa hannu, dago Masa hannun shima Dr. Sadeeq yyi a Haka dai Omar din ya fice daga hospital din yyinda shi Kuma Dr. Sadeeq ya koma zuwa ciki duk yanzu bayajin dadin zaman hospital din dama makarantar tasu gaba1 sbd Rashin abokin nasa a kusa, kusan hakan ne a wajen Dr. Omar Sam bayajin Dadi da basa tare da frnd dinsa yanzu shiyasa yakejin wani iri a wajen aiki saukinta ma dai idan Yana tare da daddy Yana tsintar kansa a cikin wani irin farinciki marar misaltuwa.
Koda Dr. Omar yaje office Yana zama kan kujerar sa yaji an bude Masa kofa Koh izinin Shiga ba'a nema ba, juyowa yyi d mmki wanne Dan iskan ne yake d zarrar Yi Masa Haka? Ganinta yyi tsaye taci gayu ga kamshi me karfi na tashi a jikinta, "mrng dear" yarinyar datazo ranar ta Furta hakan cikin Jan hankali, tsare gira sosai Dr. Omar yyi Yana kallon ta sama da kasa kafin yace, "Salma?" Cikin mmki ta kalleshi bakinta yaki rufuwa tace, "oh Ashe kasan sunana?" Wani irin kallo yyi Mata ya watsar Yana me bude wata dirowa dake gefensa ya Ciro wata takarda yace, "karbi" karba Salma tayi a yangance cikin karya murya tace, "Wannan fah?" Kallon ta yyi sosai fuskar sa a daure yace, "idan kin fita kina iya budewa" dukda Salma ta tsorata da yanayin sa Amma saita dake tana sake kwantar da murya tace, "dukda bansan menene a ciki ba yau ranace ta farinciki a gareni sbd na karbi Abu a hannun mutumin da nafi so da kauna a Wannan duniyar idan aka debe iyayena" ta karasa mgnr tana Jan Numfashi hade da shinshinar takardar ta lumshe ido kafin ta sauke su Kan Dr. Omar daya maida hankalin sa Kan system din dake gabansa Yana kunnawa Dan yaga alama Kamar ita Wannan Kuma Bata da nutsuwa, Kallon sa take sosai tana hadiye yawu ji take kamar taje ta lashe shi har wani maiko take gani tattare dashi dama tasan tuntuni da alamun zaiyi Mai din ta karasa gaban Desk dinsa daidai lkcn ya dago Yana tsareta da Ido, ta saki murmushi tana me sumbatar takardar tace, "Thanks you" ta Furta hakan tana me juyawa cikin taku irin na bariki cikakkun hips dinnan na juyawa a slow tabar Masa office din, Binta da kallo Dr. Omar yyi batare daya tantance wanne irin kallon yanzu Kuma yyi mata ba.
Acan bangaren su Anty shafa kuwa kamar yadda Mom ta tsara musu hakan kuwa sukayi, wankan gayu suka dauka sosai suka Sha riga da wando daya zame musu kamar Al'ada gashin Kan Nan yasha Attachment abin dai gashi Nan dai, Gama Shirin su keda wuya wayar Sageer din ya shigo, dauka Anty shafa tayi tana me lankwasa murya tace, "harka iso?" Sageer na duba agogon hannun sa yace, "Kamar ma nayi late can't wait to see my princess" 'yar dariyar mugunta Anty shafa ta saki kafin tace, "karka damu ai yanzu ne Bari ma nazo" "yauwa frnd" Sageer ya furta hakan cikin Jin Dadi Yana me lumshe ido hade da hango luntsuma luntsuman breast din Meera dayaso kamawa Dan iskan Omar dinnan ya tare, kwankwasa Masa window yaji ake Dan Haka ya fito shi da Faisal da yake ta chatting da wata chicks din tasa a gefe, fitowa sukayi Anty shafa tace, "wow! duk wannan gayun na Meera ne?" Ta Furta hakan tana bin Sageer din da kallo sbd Shigar wasu arnan kaya da yyi Kai kace tacaccen Dan rawa ne, zube hannayen sa yyi a Aljihu Yana washe baki sbd an yabe shi yace, "pls muje daga ciki na Matsu fa" Dan satar kallon sa Anty shafa tayi tana 'yar dariya tace, "muje" Nan suka rankaya zuwa cikin gidan nasu Koda suka shiga parlon baki daidai lkcn Anty Jamila ta Gama turare dakin da turaren siddabaru, Sageer da Faisal suna shakar Wannan hayakin dayake tashi a hankali kuwa suka dafe kansu da sauri sbd juya musu da suka ga yanayi, Anty shafa ce ta riko hannun Sageer din tana kallon sa tace, "lpy dai?" Tayi tmbyr Kamar gske Haka itama Anty Jamilan tayi, Zuwa yanzu sun dawo cikin nutsuwar su Dan Haka Sageer yace, "ah nothing mu zauna Mana Shafna" yyi mgnr Kamar yadda yaji su Afra na fada Mata, shima Faisal din hakan yyi kallon juna sukayi da Anty Jamila da Anty shafa suka kyastawa junan su Ido suna dariyar mugunta kasa2 kafin kowacce ta tsiyayo lemon da aka Gama watsa Masa garin cafke zuciya suka bawa bakin nasu cikin yanga, karba Sageer yyi sbd yadda yaji kamar makogwaron sa ya bushe musamman daya shaki hayakin Nan, haka ma Faisal, tofah tsafi gskyr meshi take dai Shirin da akayiwa samarin Nan biyu yahau kansu, kafin wani lkci hirar ta canja ta koma irin ta masoyan Nan ta Asali, Sageer tsabar yadda yakejin Anty shafa a ransa ma cewa yyi daya koma gida zaisa daddy yazo ya nema Masa Aurenta, shima Faisal din kusan hakan ne Dan yyiwa Anty Jamila Alqawarin turo nasa magabatan suzo ayi mgnr auren su, duk Dadi da murna ta Kama su sai Nan Nan suke da junan su, a kalla dai Saida akayi Dan tabe-taben da aka Saba kafin aka rabu da juna cikin shauki Bayan sunyi musu barin naira especially ma Sageer din, kudin d akaso zubewa Meera su aka zubewa Anty shafa, Bayan tafiyar su da gudun su suka Antaya cikin gida, a daki suka tarad d mom tana shirya wasu kaya, fadawa jikinta sukayi suna dariya, mom ta dubesu tana gyara zamanta sosai tace, "Kai lpy Naga kunata dariya kamar sabon kamu?" Anty shafa ce ta zube mata kudin wajenta bakinta yaki rufuwa tace, "Mom aikin mu ya Kama su" dariya Mom tayi tana kallon kudin da Anty Jamila itama ta zube tace, "Kai yau babbar ranace a gareni yarana kun Gama min komai Wlh" Suma cikin murna sukace, "ai mom mun yadda d bokan Nan naki aikinsa Kamar cin wuta Haka yake dandanan har Abu ya juye?" Mom na dariya tace, "an Gaya muku nidin ta wasa ce? Ai Dana nace kusha kurumin ku kamar anyi an gam" Anty Jamila tace, "gsky na jinjina Miki mom ai matukar munada ke bamuda wata matsala a gidan auren mu" mom tace, "yoh ba Dole ayi babban shiri ba? Ai aure ya wuce wasa, yanzu ma so nake ace sun turo manyan su sai musan Ina mukasa gaba" Anty shafa tace, "ai zance ya Kare Dan dukansu a gigice suka tafi zasu sanar da manya" ta karasa mgnr Yana dariya, dariyar itama mom tayi tace, "kaii Amma fa nagai da aikin boka" Nan suka sa dariya gaba dayansu.
Kamar mahaukaciya Haka Saratu tahau dukan Sahabatu tana sambatu Fadi take, "Shegiya marar wayo Banda Rashin wayo yaushe Zaki Bari kazamin Dan Tasha ya turmushe ki?" Dakyar Sahabatu ta kwace daga rikon saratun tace, "ni Umma ki daina dukana Haka Nan ko ni nace a daura min tallar?" Saratu a tunzure tace, "au sai yanzu zakiyi korafin na Dora Miki tallah?" Zumburo baki Sahabatu tayi tace, "Toh koma dai meye ai a dalilin tallar ne Kuma Dan tsabar Rashin tausayi kihau Kaina kina duka kinsan Abinda nake dauke dashi ko so kike ki kasheni?" Ciza yatsa Saratu tayi tana huci ta gallara mata harara tace, "Shikenan Amma Wlh baki Isa ki fita Koda kofar gida bane bare ki jawomin zagi" tabe baki Sahabatu tayi tace, "ni fitar me zanyi? Idan na fita ma Ina zanje?" Saratu taja tsaki tace, "oho maki" tayi mgnr tana shigewa daki, Koda ta shiga dakin ma kasa nutsuwa tayi Dan Haka ta zaro wayarta ta Kira Nas, bugu biyu Nas ta dauka tace, "idan an jiki matsala ce" Saratu tace, "Dan Allah kibar Wannan mgnr akwai mgnr da nakeso muyi" Nas na dariya tace, "mgnr me?" Saratu tace, "so nake na kawo Miki Sahabatu ki rikemin ita harta haihu a wajenki" Nas Tace, "yaushe kikayi Aurenta da har ta samu cikin?" Saratu tace, "shiyasa na tunkare ki d mgnr sbd ke kadai ce Zaki rufamin Asiri" Nas tace, "Amma ke meyasa bazaki rike 'yarki ba?" Saratu cikin damuwa tace, "banason abin kunya ne tun kafin mutanen unguwar Nan Susan da zaman cikin Nan nakeso tayi kaura damu" dariya sosai Nas tayi tace, "Wai gudun abun kunya kike Saratu? Amma fa kinada abin mmki Wlh" ta karasa mgnr tana dariya, "nidai Dan Allah ki Amsa min bukata ta" Nas tace, "Shikenan Amma fa da sharadi" Saratu tace, "name?" Nas tace, "Zaki dinga biyana dubu goma duk wata" a razane Saratu tace, "haba Nas kin manta yadda muke dake ne?" Nas tace, "yadda muke kamar ya? Haduwar barikice fah? Atho Dan ba haduwar Alkhairi bace ta hadamu Dan Haka Koh gwamnati Bata aikin banza" Jan Numfashi Saratu tayi tace, "Shikenan naji Ina lefin na baki dubu biyar?" Nas tace, "Ashe ba so kike na rike Miki itan ba saiki nemi wata" tayi mgnr tana kokarin rufe wayar, da sauri Saratu tace, "Toh Shikenan naji zan biyaki" Nas na washe baki Kamar tana gabanta tace, "yauwa 'yar gari Ashe kin gane," nan suka yanke wayar Nas na dariya sosai a fili tace, "Haka kurum zanyi ta Miki wahala ba lada? Gashi bana sana'ar komai bare na samu Dan Haka a jikin ki zan tatsa Nima." Ita kuwa Saratu tashin hankalin tane ya karu yanzu kenan duk wata saita zare dubu goma cikin kudin Albashin ta? Wannan ai ta bada kusan duka kudin nata kenan Amma Yata iya? Haka ta fito da niyyar sanarwa Sahabatu yadda ta yanke.
~~~Tun yana office yaga labulayen office dinsa suka fara kadawa a hankali, wata sassanyar iskace take shigowa a hankali daga karshe ma iskar ce take kadawa sosai, tashi yyi zai kulle window dinsa ya hango gabas ta hadu sosai tayi baki Kamar za'a kece da ruwa, tsayawa yyi kawai ya zubawa gabas din Ido, knocking akayi be juya ba Amma ya bada damar shigowa, PA Dinsa ne ya shigo a gurguje yace, "Dr. Omar ni zan wuce gida kafin ruwan Nan ya kece tunda lkcn tashi yyi" kallon sa yyi yaga harya rungumi jakar aikinsa Dan Haka ya girgiza Masa Kai batare d yyi furucin komai ba, juyawa Habib yyi Yana tabe baki yace, "wata Rana dai dakai da kurma bakuda banbanci mutum Allah ya tsaga Masa baki Amma mgn ta gagare shi ba kurma ko bebe ba" da Wannan tunanin yabar office din gaba1, Shiko Dr. Omar maida hankalin sa gabas yyi Yana hango wasu fararen balbelu sunata gudu a jere gwanin sha'awa sbd yadda saman tayi baki sai farin nasu ya Kara kawata wajen, Dan murmushi yyi yanaji kamar ya Kama su, kafin yyi aune yaji an kece da ruwa kamar da bakin kwarya ruwa Kuma me irin feshin Nan, hakan yasa har cikin office dinsa ta window ruwan na shigowa, be rufe window dinba saima Jan Numfashi da yyi ya lumshe idonsa Yana shakar sanyin ruwa da Kuma feshin dake taba Masa jiki da fuska.
8/15/20, 8:05 PM - Ummi Tandama: *YADDA ZAKI BIYA*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.