Best Hausa Novels

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt

Chapter 61 of 85

Ja baya Meera tayi a tsorace jikinta na rawa Tace, "Dan Allah kayi hakuri na dauka bakaji bane" Wani mugun tsaki Dr. Omar Yaja kamar ya maketa Haka yakeji Dan haushi juyawa yyi da nufin tafiya a hanzarce Meera Tace, "dama cewa zanyi Dan Allah ka Barni na koma school" cak Dr. Omar ya tsaya shi be juyo ba shi beyi mgn ba, Meera na ganin Haka tadan matso kusa dashi tace, "Wlh duk banajin Dadi zaman kadaici yamin yawa ne Kuma...." Bata karasa mgnr da take furtawa ba taji an debe ta da wani irin gigitaccen Mari, sbd zafin Marin daya shigeta Saida tayi wata irin katantanwa saura kadan ta zube kasa taji an cakumo hijab din nata, Dr. Omar ne ya riketa sosai jikinsa na Bari sbd tsabar dacin bacin ran da yake ciki a yanzu Ashe shirun d yyi tsuma kurum yake Yana kokarin controlling anger dinsa yaji taci gaba da mgn Wanda yakejin Kamar Ana dura Masa dalma ne a kunne, idonsa ne yyi jajir Yana fitar da hucin zafi ya fara mgn a kausashe yace, "kinaso ki koma school? Kadaici ya dameki?" Yyi mgnr Yana tsareta da Ido, Meera da tun dazu take ambaliyar hawaye ba damar ware baki sai Jan zuciya ta kasa ce Masa komai jikinta itama sai rawa yake Dan azabar da take ciki, Tsaki Dr. Omar Yaja Yana Kara tamke rikon da yyi mata yace, "kin Kara Tabbatar min da kedin kwata2 bakida hankali, wawiya ce ke, Bakida tunani, Oh na manta kinason haduwa da shedanin naki dake waje Koh? Ah no wonder zaman kadaici ya dameki domin kin kwana biyu Baku kebe ba" Meera dake Jan zuciya dakyar sbd mugun shakar da yyi Mata tahau girgiza Kai dakyar take fadin, "Wlh ba nufina kenan ba" buge mata lips dinta yyi d hannu Yana fadin, "Dallah yimin shiru, An Gaya muku ban gane Shirin ku bane? Kun dauka kowama irinku ne me Kwakwalwar kifi? Sbd ki Taya shi zubar min da mutunci Kika zabi ya tube Miki kaya a filin Allah Kuma..." da hanzari Meera ta katse shi da fadin, "haba ya Omar nifa ba Haka nake ba, ka daina zargina akan Abinda Babu tabbas" binta da kallo yyi Yana sake hade Rai sosai yace, "musu zakimin?" Girgiza Kai Meera tayi tana Jan zuciya, a zuciye ya sakar mata hijab din saura kadan ta Fadi sbd yanayin sakin na mugunta d yyi mata, hakan ya bawa Meera Daman matsawa can nesa dashi tana share hawaye, Cije lips dinsa yyi harya juya Kuma Saiya juyo Yana dubanta yace, "kee.." Meera data sunkuyar da kanta ta dago tana kallon sa duk idonta yyi ja, "Biyoni bazan barki a gidan Nan ba Dan ban yarda dake ba" yyi mgnr Yana wucewa gaba, binsa da kallo tayi Anya taji daidai kuwa? Wata zuciyar tata ce ta Kara Tabbatar Mata da zancen nasa hakan yasa ta bishi da sauri Dan har ya shige mota, Kokarin bude baya take Dr. Omar ya juyo tare da zube mata zakunan idonsa a kanta yace, "I'm ur driver?" Yyi mgnr Yana sake wara Mata idon nasa, juyowa tayi a rude ta dawo kofar gaba Kamar wacce aka shafe mata komai na Kai Haka tayi ta Kokarin bude kofar ta kasa sbd yadda hannunta yake rawa, "Mtwsss.." Dr. Omar Yaja tsaki me karfi yana me bankada kofar da gayya harta sameta a ciki, rike cikin nata Meera tayi cikin zugi taji yace, "Zaki shigo ne mu tafi ko saina fito wajen?" A firgice Meera ta fada motar tasa tana dafe cikinta da yake mata ciwo dakyar ta jawo murfin motar ma sbd yadda taga ya fisgi motar da sauri, Lumshe ido Meera tayi hade da kifa kanta cikin cinyarta tana share hawaye masu dumi da suke zubo Mata.
Direct company din da yake aiki ya wuce da ita, lkcn da suka Isa Meera kanta a duke yake batasan sun iso ba sai karar rufe kofarsa da taji yyi, Dagowa tayi da sauri tana binsa da kallon mmki be mata mgn ba yyi gaba abinsa, Ganin Haka yasa Meera ta fito da sauri itama Dan bataga amfanin zaman nata ba, fitowar ta keda wuya ta tsinci kanta da karewa yanayin company din kallo, ba karamin mmki tayi ba Dan tabbas tanajin sunan company din kenan anan Dr. Omar yake aiki? Bata da Wannan amsar tmbyr tata Dan Haka ta bi bayansa da sauri domin ya fara Yi mata nisa, kanta ne ya sake daurewa musamman da taga duk Wanda ya wuce zai duka ya gaishe shi sai kace shine me company din, Haka ta dinga binsa kamar jela yyinda Dr. Omar yake tafiyar sa cike da izza ransa a matukar hade duk Wannan gaisuwar da sauran ma'aikatan suke Masa baya kulasu, a Haka suka karasa har can sama ya bude kofar office dinsa ya shige, Meera na zuwa daidai kofar ta daga kanta sama tana karewa sunan office din kallo, General manager ta maimaita hakan a ranta, What? Me hakan ke nufi? Ya Omar Yana Dr. Ya koma General manager na company? Tayiwa kanta Wannan tmbyr da Babu me Amsa mata, tura kofar itama tayi da sauri ta hango shi Yana kokarin bude wata kofar dazai sadashi da ainahin office dinsa, PA dinsa Habib dake gyara takardu ya taso da sauri Yana tare Meera din yace, "ke wacece ke da Zaki wuce mutane ba mgn ko an Gaya Miki dandalin mabarata ne Nan?" Yyi mgnr cikin tsawa, bude kofar d Dr. Omar beyi ba kenan ya juyo a zuciye, d sauri Habib yace, "sorry sir yanzun Nan zan sata tabar Nan wajen mutanen ne da kulafuci sun fiye nacin roko..." "Enough Habib" Dr. Omar ya Furta hakan cikin karaji zuciyar sa na zafi, a tsorace Habib Yaja gefe jikinsa na rawa Dan zuwa yanzu shakkar Dr. Omar din yake, Kallon yanayin office din Dr. Omar yyi yaga Babu Alamar shara, ya tsaida kallon sa Kan Habib daya takure waje daya yace, "meyasa yau ba'a gyara wajen Nan ba?" Yyi mgnr Yana tsaresa da Ido, cikin kaduwa Habib yace, "har yanzu me aikin be iso bane" "Mtwssss.." Dr. Omar Yaja tsaki yace, "kaje yanzun Nan ka tattaro duk wani kayan aikin da za'a gyara office dinnan ka kawo" "Okay Sir" Habib ya furta hakan da sauri Yana barin office din, yyinda shi Kuma Dr. Omar ya shige nasa office din ko kallon bangaren inda Meera take beyi ba, Meera data Sha jinin jikinta ta takure waje guda ta kasa Koda daga kafa daya gaba1 hankalin tane ya sake tashi bisa ganin Isa da mulkin da taga Dr. Omar din yake nunawa a Wannan company din lalle ta dauro dala ba gammo domin Sha'anin Dr. Omar ya girmi tunanin ta, Kamar bazata bishi cikin ba taga cewa Babu amfanin tayi ta tsayuwa batare da tasan Matsayin zuwanta wajen ba yasa ta bishi har cikin office din, Yana zaune Kan doguwar kujerar dake cikin office dinsa wasu takardu yake dubawa da alama sunada muhimmanci yadda taga ya bada hankalin sa wajen sosai, daga gefen kofar ta rakube Bata karasa ciki ba, tana daidaita tsawurta kenan Habib ya shigo da sallama, Dagowa Dr. Omar yyi Yana kallonsa bece komai ba, Habib yace, "Sir kayan suna Nan waje duk na kawo" girgiza Kai Dr. Omar yyi kafin yace, "kaje can waje ka jira kafin a Gama" da mmki Habib ya kalleshi ya kalli Meera dake manne jikin bango kamar kadangare a takure ya bude baki zaiyi mgn Dr. Omar ya katse shi da tsawa yana fadin, "ko bakaji Abinda nace bane?" A rude Habib yace, "i'm sorry Sir" yyi mgnr Yana juyawa da sauri Dan barin office din, shiru office din ya dauka Kamar ba mutane sai karar takardun da Dr. Omar yake dubawa a hankali, Meera Kam kallon ikon Allah kawai take agun miskilancin Dr. Omar, kamar daga sama taji yace, "kije ki dauki kayan aikin da Habib ya kawo ki fara gyara wajen kafin ki shigo Nan shima ki gyara" wara ido sosai Meera tayi da mugun mmki batasan lkcn da tace, "nidin?" Dago dara-daran idanunsa yyi Yana kafeta dasu yace, "a'a ni" yyi mgnr Yana binta da mugun kallo, Kame bakinta Meera tayi batace dashi komai ba Kawai ta juya cikin tsananin tausayin kanta tabar Masa office din, tana fitowa ta tarad da kayan inda Habib ya ajiye, kallon su tayi tana Dan goge kwallar data ziraro mata ta Wutsiyar Ido, Bata da zabin daya wuce tayi Abinda yace din, Dan Haka ta zage sosai ta gyara inda PA dinsa ke zama, bayan ta Gama ne ta shiga ciki inda yake har yanzu Yana Kan kujera, batayi Masa mgn ba ta fara aikinta shima be dago ya kalleta ba harta Gama gyara wajen ta shige cikin toilet dinsa, Shigarta toilet din keda wuya aka turo kofar office din, Dr. Omar na zama kenen shima akan kujerar aikinsa yaji turowar kofar harda sallama cikin siririyar murya tajan hankali, zamansa ya gyara Kan kujera kafin ya dago kansa a tunzure yace, "Wai ke wacce irin mayyace ban sani ba?" Salma data Sha kwalliya sosai fuskar ta cike da Annuri ta matso gabansa cikin takun yanga tana juya cikakkun hips dinta tace, "haba Mana Dr. Calm down meye abin zafi Kuma?" Ran Omar ne ya sake baci zaiyi mgn kenan Salma ta tare shi da fadin, "ai Naga sakon ka na korar da kayimin shiyasa nazo Yi maka godiya" tsaki me sauti Dr. Omar yyi yace, "ko ki ficemin a office ko na sa a Kira cleaners din company Dinna su fitar min dake" 'yar dariya Salma tayi tana Dan rankwafowa Kan table din gabansa tace, "Dr. Omar kenan naji da farko Kamar kace mayya, Yes mayya ce Amma mayyar da take kwana da tashi da kwadayin samun ka" ta karasa mgnr tana kyasta Masa ido daya, a tunzure Dr. Omar ya tashi Yana fadin "cleaners" da karfi duk ya mance ma ba lalle su jishi ba, saidai Kash daidai lkcn Meera ta fito daga toilet din nasa tana gyara zaman hijab dinta, dukansu juyawa sukayi suna kallon ta, itama dagowar da zatai ta gansu a tare, Salma ce ta kwashe da dariya tana nuna Meera Tace, "Wai dama irin Wannan cleaner dinne zasu fitar Dani?" Tayi mgnr tana nuna Meera, wani irin shocked ne ya Kama Meera din Ranta a mugun bace ta dubu Dr. Omar da Shidin ma yake tantance sunan da aka kirata dashi mmki ne sosai ya Kama shi dayaga bacin Rai karara Akan fuskar Meera sbd sunan da Salma ta kirata dashi duk irin cin zarafin da yake mata be taba ganin bacin ranta Haka ba, hakan yasa take yaji wani Dan guntun tunani ya shige shi, komawa mazaunin sa yyi ya zauna Yana Dan murmushin gefen baki, da alama zaiyi amfani da Salma wajen muzanta Meera din, hakan yasa ya dago da kansa fuskar sa kadaran kadahan Yana duban Salma yace, "Alright mubar Wannan mgnr ki sameni gobe around 11am sai mu tattauna akai" yyi mgnr cikin kulawa, dubansa Salma take da mmki Anya kunnen ta yaji sosai? Karkada hannunsa gaban idon Salma yyi yace, "Yadai?" Yyi mgnr Yana kallon ta a nutse, Salma da murna ta Kama ta Tace, "I..I'm.really surp...." "Shiiiii..." Dr. Omar ya katse ta da sauri Yana sa Dan yatsan sa a baki, shiru Salma tayi tana murmushi tace, "okay Bye" tayi mgnr tana juyawa a hankali hips dinta na cewa bye2 sbd irin juyasun d take, Dan satar kallon Meera Dr. Omar yyi yaga ta cika tayi fam, hakan yasa ya dada maida hankalin sa sosai Kan Salma da niyyar cusawa Meera takaici sbd taga ya bita da kallo, saidai kashhh Irin juya hips din da Salma take Saida tasa mazantakar sa ta motsa har wani Dan girgiza tayi abinka da dama can be Gama warwarewa daga takurar da lollipop din tasa ta Masa jiya ba, d sauri ya kawar da kansa Yana dukar dashi tare dayin Istigfari, Fitar Salma keda wuya ya bawa Meera kwarin gwiwar matsowa inda Dr. Omar din yake ranta a bace tace, "yanzu duk Abinda kkemin be wadatar dakai ba har saika kawoni wajen aikinka ka zubar min kima da mutuncina a idon duniya??" Tayi mgnr Kamar ta fashe Dan haushi gaba1 wani irin makakin kishin Salman ne ya taso mata, Dagowa Dr. Omar yyi zuwa yanzu fuskar sa a daure take sosai yace, "Au Ashe kinsan me ake Kira da kima da mutunci? Shine Kika watsar min nawa?" Ya karasa mgnr da Dan daga murya, Sunkuyar dakai Meera tayi tana Dan share zafafan hawayen da suka zubo mata a hankali Sam Bata da bakin mgn Kuma yanzu itakam Yaya zatayi ta goge Wannan bakin tabon da tayi Masa ne? Zaton ta Abinda tayi shine zai kawo maslaha ga Rayuwar sa Ashe rusa Masa rayuwa tayi, ta kashe shi da ransa Bata sani ba, Tsaki me sauti Dr. Omar Yaja be Kara bi ta kanta ba yaci gaba da aikin dake gabansa, A Wannan Rana dai Haka Meera da Omar suka kwashe awanni a office Babu me cewa da Dan uwansa ci kanka Koh lunch basuyi ba Koda yake Bata sani ba ko Shidin yyi domin ya fita na wani lkci dazu itan ce dai kamar wata me azumi saidai tayita share kwalla lkci bayan lkci, har lkcn tashi yyi, koda yazo tafiya ma Saida yaje har jikin kofa ya waiwayo tana rakube daga gefe a zaune yace, "Zaki taso mu tafi ne Koh kuwa anan Zaki kwana?" Yyi mgnr Yana binta da Harara, Tasowa tayi da hanzarin ta domin ta gaji dama d Wannan zaman a Haka suka sauko har izuwa can inda yyi parking motar sa.
Direct unguwar su Abba ya nufa dama tun jiya be leka yaga yadda Abba yake ba, Meera d kanta ke duke saijin tsayuwar mota taji Ashe har sunzo, shiru yyi Yana tunanin Shiga da Meera gidan wajen Abba, Yasan idan Abba ya kalleta a Wannan yanayin zai iya tuhumar sa dukda bazaiyi mgn ba yasan zai nuna alama, Kallon gorar ruwan gefensa yyi ya Ciro a hankali Yana dubanta Yace, "kee" Meera da har yanzu hawayen Basu daina zuba ba ta dago da kanta a hankali tana kallon sa duk idonta yyi ja, kawar dakai yyi Yana Mika mata gorar ruwan dake hannun sa yace, "karbi Wannan ki wanke Wannan hawayen munafurcin da kikeyi banason ganin sa" yyi mgnr Yana cilla mata robar jikinta, dauka Meera tayi har yanzu Jan zuciya take batace Masa komai ba ta bude motar kadan ta fara wanke idonta, Saida ta Gama ta rufe murfin muryar ta a dashe Tace, "na Gama" juyowa Dr. Omar yyi yaga har yanzu kwalla Bata bar idonta ba yace, "sauran munafukar kwallar da Kika Bari fah?" Yyi mgnr Yana tsareta da Ido, Dukar da kanta tayi kasa tace, "kayi hakuri hawayen yaki tafiya ne" "Mtwsss.." Dr. Omar Yaja tsaki yace, "look banason gulma duk yadda za'ayi kiyi domin Wannan shegun hawayen naki su bace daga fuskar ki Dan bazamu Shiga gida a Haka ba" Kallon sa tayi da sauri kirjinta na bugawa da karfi kodai gidan ubanta ya maida ta? Tayi mgnr a ranta tana kokarin karewa yanayin unguwar kallo, sai yanzu ta fara ganin wata unguwar ce ba tasu ba a hankali ta sauke boyayyar ajiyar zuciya jawo Dan kwalinta tayi da niyyar goge kwallar Dan ta tafi gaba1 taji ta taho da dogon gashinta harya fito waje, a rude ta Dan saci kallon Dr. Omar taga Ashe ba itan yake kallo ba Nan ma ajiyar zuciya ta saki tana kokarin nannade dogon gashin nata ta cikin hijab, bayan ta Gama ne tasa Dan kwalin nata ta goge sauran kwallar da Bata Gama tafiya ba, Saida fuskar ta tayi wasai kafin ta maida dankwalin nata tana gyara hijab taji yace, "muje" fitowa sukayi daga motar tana daga gefensa suna tafiya a hankali saidai shi yadan zartata sbd yanayin tafiyar tasa da yakeyi cikin Isa da takama Wanda ya kasance nature dinsa ne amma a fili sai aga Kamar da sanin sa yake hakan, itadai nata shine ta bishi a Haka har suka karasa kofar gidan nasu, batayi mmkin ganin yanayin gidan nasu ba Dan tun tuni taji su Aunty Shafa na lbrn asalin Dr. Omar din sai kallon yanayin gidan nasu take har suka Shiga ciki, Shiru Kamar ba mutane a gidan Dr. Omar ya sake Yin sallama sai sukaji alamun tahowar Abba daga dakinsa, Meera dake gefensa ganin Abba ya iso da fara'ar sa ya tarbesu Yana binsu da kallo yasa ta saki ranta sosai hade da Isa wajensa ta tsugunna Tace, "sannu Abba barka da yamma" tayi mgnr cikin tsantsar ladabi, kallon ta Abba yyi da murmushi ya juya ya kalli Dr. Omar kallo na tuhuma Dan yyi mmkin ace matar daya aura tsawon Wannan lkcn ace batasan baya mgn ba? Wanne irin zama sukeyi Wannan?? ganin irin kallon da Abba yake masa ne yyi hanzarin matsawa gaban Meera cikin taushin lafazi kamar gske yace, "Oh! Meeeraaa kin manta na fada Miki Abba baida lpy baya iya mgn ai" yyi mgnr kamar gske, Dagowa Meera tayi a hankali ta zube Masa manyan idanunta da suke kyalli gaba1 mmkinsa ne ya kamata kanta Kuma ya daure tamau, yaushe sukayi Wannan mgnr dashi? Ganin zata jika Masa aiki ne yyi mata mgnr Ido Yana dage mata gira, hakan da yyi da Kiran sunan ta da yyi besan cewa Yana tafiya da dukkan Imani ta bane domin gani take kamar b Dr. Omar din daya Gama ci Mata zarafi bane yanzu, Amma dake itama tasan kalar irin Wannan abun ta juyo da sauri harga Allah dukda batasan mafarin meye matsalar Abba ba taji a ranta tana tausayin sa sosai cikin yanayin tausayawa tace, "eyya sannu Abba Wlh na sha'afa ne" tayi mgnr tana matsawa gefe ta zauna kan kujerar tsungunno data gani, taci gaba da fadin, "Allah ubangiji ya baka lpy" girgiza Kai Abba yyi cikin murmushi Yana nuna alamun Jin dadinsa, zama shima Dr. Omar yyi yana gaishe da Abba, Nan Abba ya girgiza Masa Kai, Bayan sun Gama gaisuwar ne Dr. Omar ya dubi gidan kaca2 Alamar dai Babu shara da mmki yace, "Sahabatu Bata Nan ne?" Yyi mgnr Yana tsare Abba da Ido, Dan Jim Abba yyi be nuna Alamar komai ba, Dr. Omar ya Kama hannun sa yace, "ta samu saukin ne harta samu damar fita?" Girgiza Kai Abba yyi yanayin sa na canjawa, Gaban Dr. Omar ne ya Fadi Toh meke faruwa ne? Ciro wayarsa yyi da nufin Danna Kiran Saratu, Meera na gefe tayi shiru duk tausayin Rashin mgnr Abban ya dameta, Dr. Omar kuwa Saida ya gwada Kiran Saratu har sau uku ya kasa, Ana hudun ne dai yyi nasarar danne zuciyar sa ya Danna Kiran, bugu biyu yaji ta dauka muryar ta raurau tace, "Alo" Dan cije lips dinsa Dr. Omar yyi yace, "Ummah" Jin muryar Maru ce yasa Saratu ta Mike da sauri domin a parlon hajiya Aisha take ana shirye-shiryen bikin Sageer, Saida ta matsa can bayan fulawa kafin tace, "ya akai?" Danne zuciyar sa yyi yace, "dama Nazo gidan ne sai naga Sahabatu Bata Nan shine nace ko ta samu saukin ne?" Saratu dake can barin tace, "au so kke kazo ka ganta kwance ita kadai gwalam a gida?" Girgiza Kai Dr. Omar yyi kamar Yana gabanta yace, "ba Haka bane Ummah" Saratu taja tsaki tace, " 'yata na kaita inda za'a kularmin da ita bazan barta a gidan Nan ba domin mahaifinta ma baida amfanin dazai iya tmbyr ta Abinda takeso" rintse ido Dr. Omar yyi kamar ya kwada wayar a kasa Haka yakeji, can yaji Saratu Tace, "Kai gwara ma daka Zo kasan yadda zakayi da wannan tsohon marar amfani domin Nan inda nake aiki zamuyi bikin babban Danmu, bikin da ba'a taba yin irinsa ba, biki na Dan masu dashi ba irinka da kayo gadon talauci ba" Sauke wayar Dr. Omar yyi Yana me kawar da kansa gefe Dan baya son daga Abba har Meera su fahimci irin mugun bacin ran da yake ciki, Abba ne ya riko hannun sa Yana matsawa a hankali, hakan yasa Dr. Omar yaji zuciyar sa tadan rage zafi a hankali ya juyo Yana kallon Abba da murmushin yake yace, "Zamu tafi dakai Abba kafin ta dawo" yyi mgnr Yana dukar da kansa, dago kansa Abba yyi Yana girgiza Masa Kai Alamar bayaso, Dr. Omar yace, "Dole muje tare sbd Nan din waye zai kula dakai? Tunda ba yanzu tace zata dawo ba" shiru Abba yyi yanajin takaicin Saratu kwarai, tunowa da jiya da safe yyi har gabansa tazo tace, "duk wani me bakinciki daci gabana dai saidai ya mutu domin yau dinnan Shirin Nan daka ga nayi na bikin Dana ne Sageer Nan da sati biyu za'a daura shiyasa ma xan tare a gidan tun yau domin bikine za'ayi irin na masu shi, Dan ita kanta amaryar ubanta ba baya bane wajen naira burina Yana gab da cika suna Gama damka Masa komai zan fara zartar da hukuncin Dana dauka a kansu" ta karasa mgnr tana sakin dari hade da ci gaba da fadin, "su dunkum sai Ayita zaman shiru baki na wari Babu damar Fadar gsky kaji waliyyi" tayi mgnr cikin isgilanci tana dariyar keta a Haka ta kada bujenta tabar Masa gidan, Mlm sale yyi kunkan bakin ciki Daren jiya haryau da takaicin Saratu ya tashi a ransa..., Girgiza shi Dr. Omar yyi yace, "Dan Allah Abba" kallon Meera da tayi tagumi Abba yyi itama da sauri Tace, "Eh Abba Dan Allah ka taho muje" tayi mgnr Kamar zatayi kuka ita duk tausayin sa take, Girgiza Kai Abba yyi Alamar ya amince Dan Haka suka Mike da murnar su suna hada Masa kaya, kallon su Abba yake cikin birgewa yanajin dadin yadda Yaga Omar din nasa ya samu mace ta gari, a Haka suka Gama diban kayan nasa kamar wasu masu shiri har suka Kai Masa mota, Bayan sun Gama ne Dr. Omar ya kamo hannun Abba suka fito, Saida ya rufe gidan nasu yaga yaron mlm Shamsu zai Shiga gida yyi masa Alamar yazo, yaron ne ya matso Yana kallon Dr. Omar yace, "gani" Dr. Omar yace, "Abbanku na gida?" Girgiza Kai yyi yace, "yaje kasuwa" Dr. Omar yace, "idan ya dawo ka sanar Masa Abba ya danyi tafiya" "Toh zaiji Insha Allah" yaron ya fada dake yanada hankali. tun kafin su iso Meera ta bude Masa gaban mota anan Abba ya zauna ita Kuma ta koma baya yyinda Dr. Omar Kuma ya shige matukin driver.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.