Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt
Chapter 64 of 85
Fuska ya hade sosai yace, "ke a gidanku ba'a koya Miki sallama bane?" A firgice Meera Tace, "Yi hakuri" ta furta hakan bakinta na rawa tayi kokarin juyawa da sauri, Tsaki Dr. Omar yyi kawai shima ya shige toilet. Kallon kansa Sageer yyi a madubi wayewar yau yaga duk ta kumbura ransa ne ya baci sosai gashi Ayau dinnan za'a fara duk wani event da za'ayi na bikinsa, Yana tsayen ne yaji an fara Masa knocking ta waje kin mgn yyi Dan tun jiya daya fice sassafe be Kara waiwayar gidan ba sbd kamasa da Dr. Omar yyi, Koda yake har lkcn ma basu fahimci Dr. Omar dinne yyi musu hakan ba, ci gaba da buga Masa kofar akai a tunzure yaje ya bude Yana fadin, "Wai uban waye me nacin bugun Nan?" Ya karasa mgnr Yana bude kofar tasa, wani irin mugun tsaki Yaja ya harari na bakin kofar kafin ya juya, Saratu da tun jiya ta lura da Rashin shigowar sa gida shiyasa Sam ta kasa nutsuwa sai dubansa take tanaso tazo ta dubashi sbd a jiyan taji alamun shigowar sa gidan Babu damar hakan sai yanzu da Hajia Aisha ta nemi a tura wata ta Kira mata shi tace zataje da kanta, ganin yadda idonsa da bakinsa suka kumbura ne yasa hankalin ta ya tashi da sauri ta fada dakin bakinta na rawa tace, "sageeru waye ya maka Wannan mugun abin?" Ta Fadi hakan tana nuna fuskar sa da yatsa, ji tayi an buge yatsan nata Kamar zai lankwashe da sauri taja hannun nata Dan azaba, cikin Jin haushi yace, "ke wacece da Zaki dinga nuna ni da hannu? Bayan Haka ma wanne iya shege ne ya kawo ki dakina Banda bakar jaraba da Wannan safiyar ki isheni?" A rude Saratu Tace, "kayi hakuri dama Hajia ce Tace nazo na kiraka" tsaki me sauti Sageer yyi yace, "Dallah ni ficemin daga waje" a hanzarce kuwa Saratu ta juya da sauri tana waiwayen fuskar sa data kumbura sosai, kayansa daya dauko ya saka kafin ya wuce part din Mummy, suna zaune da Daddy yyi sallama ya shiga, Zama yyi kasa Yana dukar da kanshi Dukansu biyun kallon sa suke da mmki, Hajia Aisha ce Tace, "Sageer Wannan kumburin fuskar taka a Ina ka samo shi?" Sake dukar da kansa yyi kafin yace, "bugewa nayi" daddy yace, "bugewa kuma? Dame ka buge?" Sageer ya Rasa amsar dazai Basu kawai yyi shiru, ganin Haka yasa daddy yaci gaba da mgn Yana fadin, "Sageer tunda har auren ka ya matso a kalla befi saura kwana uku ba inason kafin lkcn ace ka tattaro min duk wani results dinka nacan school" a firgice Sageer ya dago Yana duban daddy kirjinsa na bugawa da karfi, daddy ya girgiza Kai yace, "inason na baka wani company din da zaka juyashi Dan kaima ka rike kanka but saina ga takardun ka" wata irin zufa ce ta fara karyo wa Sageer take ya fara zundumawa prof Aliyu zagi har cikin ransa yake Jin takaicin canjin department din da akai Masa yanzu ta Ina zai samarwa daddy Wannan takardu? Daddy ne ya katse Masa tunanin da fadin, "nasan irin karatun ka Sageer inaso Naga irin point din da kke ja a school anan ne zan San Matsayin dazan Dora ka" Dagowa Sageer yyi Yana Dan Bata Rai yace, "haba daddy wasu ma can daban ka Basu Matsayin me girma a manyan company dinka bare ni da nake jinin ka? Ai kamata yyi kawai kace nabar B.U.K dinnan nazo ka damka min Wannan katon company din naka na Nan" kallon sa sosai daddy yyi a takaice yace, "sai yanzu ka Kara Tabbatar min da ba karatun kke a school ba shiyasa Sam you don't know the meaning of company bare Abubuwan dake cikin at all" kawar da Kai gefe Sageer yyi Yana muzurai, daddy yaci gaba da fadin, "idan har kanason kaci gaba da rike matarka da mutunci da Kuma daraja tabbas saika kawo min takardun school dinka Naga a wanne matsayi kke ciki idan ba Haka ba..." Sai Kuma daddy yyi shiru, Dagowa Sageer yyi Yana kallon daddy Yana jiran yaji me zaice, daddy yace, "Abinda yafi maka sauki shine Naga Abinda kke a school" tashi Sageer yyi ko sallama be musu ba ya fice a tunzure gaba1 hankalin sa a tashe yake yanzu ta wacce hanyar zai bullowa lamarin Nan? Saratu dake labe daga can kofar kitchen taji nata hankalin itama ya tashi Ada tana burin Sageer din yyi aure ko za'a damka Masa wata dukiyar dazai juya sai Kuma taji wani sabon salo Wai takardu? Ashe dai su daddy da take kallo Haka da wayon su, Nan ta fara tunanin ya za'ai Wannan takardu su samu take a karon farko taji haushin Sageer din matuka da Rashin Kwakwalwar sa Dan tanaji dazu suna mgnr shekara biyu data wuce ya kamata ace ya Gama karatu Amma har yanzu jiya iyau ba lbri. Meera na Gama rufe jarkar ruwan data Gama yiwa Abba Addu'o'i ta dauka a hannu bayan ta gyara hijab dinta ta fito, yau kusan kwana biyar kenan Ana bashi mgnin Yana Amfani dashi, tun kafin Tasha kwana take jiyo kakarin Aman mlm sale da sauri ta kara saurin tafiyar ta tana daga nesa dashi ta hango ashe amai yake, da sauri ta Isa gareshi taga Yana wani irin amai na bakin Abu kamar ruwa Yana fita a bakinsa da sauri Meera ta juya wajen mlm habu me gadi da nufin sanar Masa sukaci Karo da Dr. Omar daya dawo gidan, binta da kallon mmki yyi d sauri Tace, "yauwa Dan Allah ya Omar taho muje Abba ba lpy" ta Fadi hakan a rikice, a rude dukansu suka Isa gaban Abba daya rike makogwaron sa dake Masa zafi sosai, riko shi Dr. Omar yyi Yana fadin, "sannu Abba Bari muje hospital" rike hannun sa Abba yyi ya girgiza Masa Kai Yana Nishi a hankali, daidai lkcin Meera ta Mika Masa ruwan data Debo danya wanke bakinsa, Wankewa Abba yyi kafin suka matsa a wajen, kallon shi Dr. Omar yyi yace, "Amma meyasa baza muje hospital ba?" Abba ya girgiza Masa Kai Yana bude baki domin jinsa yake Kamar zaiyi mgn sai yaji wani Abu ya tokare shi, shiyasa yake ta Wannan kakalen Aman sbd yanajin kamar abin zai fita, Miko Masa jarkar Meera tayi Tace, "Abba ga sauran mgnin sai kaci gaba da Amfani dashi" karba yyi da murna domin tabbas yanajin dadin mgnin, Meera Tace, "Da fatan kanajin dadin shi?" Girgiza Kai Abba yyi da fara'a sosai Yana washe baki, Dr. Omar ya taimaka Masa ya koma cikin daki Saida ya kwanta sbd makogwaron nasa dake zafi kafin suka futo, a tare suka Shiga parlon su Dr. Omar ya zaro wayarsa dake ringing tun dazu, dauka yyi sbd ya gane me Kiran zama yyi Kan kujera ya fara Amsa wayar Salma, Salma dake dayan barin Tace, "Dr. Omar kwana biyu na jika shiru Kuma idan nazo office PA dinka baya Bari na Shiga Wai hakan meke faruwa ne?" Dan kallon Meera da take Shirin tafiya dakinta yyi kafin ya maida hankalin sa Kan Salma Yana Dan daga murya yadda Meera zata ji yyi Dan guntun murmushi yace, "karki damu tomorrow zanyi Masa mgn yadda zai fahimci su waye ya dace su Shiga office dina" ya karasa mgnr Yana satar kallon Meera data kasa tafiya saima Juyowa da tayi a tunzure ta rike qugunta duka biyun tanajin wani irin kishi na taso mata hakan yasa ya maida hankalin sa Kan wayar Yana sauraron Salma, da murna Salma Tace, "shikenan zanzo goben" Nan suka ci gaba da wayar Yana biye Maya badan komai ba sai domin Meera taji haushi, Saida ya gaji da Jin shirmen ta kafin ya kashe, Meera da tun dazu ta daskare a tsaye tana sauraron sa ta matso inda take ranta a bace tace, "Ya Omar" kallon ta yyi up and down yace, "Ya akai?" Dan kawar da kanta Meera tayi tana kokarin zama nesa dashi tace, "inason muyi mgn ne" aje wayar hannun sa yyi Yana me Bata attention dinsa yace, "meya matsalar?" Meera tadan ja Numfashi sosai tace, "kusan watanni kenan da auren mu Amma haryau bansan meye asalin matsayina a gidan Nan ba, auren da Kai da kanka ka nemi ayi shi, ko badan NI da nake mace yarinya ba ya kamata ace ka dubi girma da Matsayin aure ka saurareni ta wani Bangaren" Hade fuska Dr. Omar yyi yace, "yaushe Kika fara zama me saurin mantuwa ne?" Meera Tace, "Kamar ya?" Dr. Omar yace, "Kin manta tun lkcn da Kika shigo gidan Nan nace kada ki kuskura ki dauki kanki a Matsayin mata domin kedin baki da banbanci da wacce tazo Aikatau?" Meera na share hawayen da suke gangaro mata tace, "yanzu tsawon lkcn Nan ban cancanci ace ka manta da Abinda ya faru a baya ka rungumi auren ka ba?" 'yar dariyar takaici Omar yyi yace, "Na manta?" Sai Kuma yyi shiru Yana Kare mata kallo yace, "a jaririya na dauke ki wacce batasan me ake Kira da aure ba but Naga kamar kedin kin zaqe da yawa alamu ya nuna kinsan meye aure wato kina bukatar Namijin dazai debe Miki kewa" cikin mugun tashin hankali Meera Tace, "Ya Omar?" Dr. Omar cikin tsare gira yace, "ba hakan bane? A zaton ki nidin kowacce kucakar ce zata birgeni har naji Ina sha'awar daukar ta a Matsayin Mata? Look Meera idan ma ni kike tunanin zai zame Miki wani bangare na Rayuwar ki kinyiwa kanki gurguwar fahimta, domin kedin bakya cikin tsarin irin matar da nakeso, bakida class din daya dace na jera hanya dake a Matsayin Mata, bakida Kirar jikin da zan kalla ki birgeni a Matsayin Mata, Ban taba Jin Inajin sha'awar kasancewa dake ba Meera, Da zarar Abba ya koma gida zanyi kokari naga na baki sallama kin tafi gidanku domin amfanin ki ma ya kusa karewa a gidan Nan" a razane Meera Tace, "bayan cin mutunci da wa'annan mugayen kalaman daka furta a Kaina zaka tozartani da saki?" Kawar da kansa yyi yanajin wani irin Abu na tokare Masa kirji yace, "hakan dai nake tunani Kuma idan hakan zaisa Kiji Kamar na tozarta ki to kuwa ba shakka daukar fansar da nayi yazo akan gaba kenan, matukar Abba ya koma gida Toh a satin Zaki bar gidan Nan domin ci gaba da zama dake baida amfani" yyi mgnr Yana zube mata idonsa a nata, rintse ido Meera tayi jikinta sai rawa yake sbd tashin hankali tace, "akan lefin da ba nawa ba kke fatan kaga tozarci na Ya Omar?" Ta karasa mgnr tana bude idonta a kansa, taci gaba da fadin,
"Ko halin da Abba yake ciki baka gani kaidai tunanin ka kaga zubewar mutuncina akan auren da ko shekara beyi ba?" Dr. Omar na Shirin tashi yace, "idan ta Abba ne ki rubuta duk wani kudin aikin da kikayi Masa na samun sauki da zarar ya fara mgn ni Kuma zan biyaki shi dama nasan tun da Kika fara rawar jiki a kansa nasan cewa badan Allah kike ba kinayi ne Dan ki samu kusanci a gareni Wanda hakan Kuma bazai taba yiyuwa ba Dan kar nake kallon komai, lkci kawai nake jira na samo matar data dace Dani" ya karasa mgnr Yana tafiya kafin ya fara taka stairs ko waiwayen ta ba yyi, Bin bayansa tayi da kallo harya kule ya shige daki Bata daina kallon hanyar stairs din ba, zuwa yanzu gaba1 kukan da take ya daina zubowa samun kanta tayi da tashi ta wuce dakinta tana Shiga ta fara jawo tsohuwar Trolley dinta da tazo da ita, sai yanzu ta fara tunanin irin auren cin mutunci da Dr. Omar din yyi da ita, auren da Babu sutura bare kayan kwalliya, zuciyar ta ce take zugata akan kawai ta tafi, gwara tabar Masa gidan yaje ya auri wacce yake so din, zuciyar ta Banda zafi ba Abinda take, harta fara zuba kaya a Trolley dinta tunanin Abba ya fado Mata, wani irin tausayin sane ya sake Kama ta harga Allah take tausayin bawan Allah Nan Amma tsabar wulakanci Dr. Omar ya dubi kwayar idonta yace Wai Dan neman kusanci take Yi, ranta ya baci sosai saidai tana so taga samun saukin Abba domin ta fara ganin Alamar hakan, a hankali ta sulale kasa wasu irin zafafan hawaye na kwarara a Kan kumatun ta, ta Rasa wacce irin rayuwa take ciki, gidan ubanta bataji Dadi ba yanzun ma gidan mijin Bata more ba a maimakon aga tayi kyau tayi haske saima sake ramewa da tayi da baki danma jikinta ba me nuna Rama bane shiyasa ake ganin ta Kamar a cike, sbd yadda take kwana da tashi cikin razana da firgici. Rana Bata karya saidai uwar Diya taji kunya Yau ta kasance Saturday inda dubban manyan kusoshin masu kudin Nigeria da wasu na mutanen ketare suka halarci daurin auren Sageer Abdullahi Omar me fata da Amaryar sa Shafa'atu Ibrahim Usman dake sun boye sunan mahaifin su na Asali shiyasa sukayi amfani da sunan dad bikin da ko Dangin ubansu Basu San dashi ba mom tayi hakan ne sbd tana tsoron kada a samu cikas a auren itadai burinta kawai ayi a daura, fadin irin watsewa da shagulgulan da akayi a Wannan bikin ba'a mgn domin a Wannan ranar ma Faisal ya angwance da Amaryar sa Jamila. Saratu ce ta fito daga bangaren da take zaune na masu aiki taci ado za'aje mother's Eve kalar lace din da su mom suka fitar me mugun tsada da kudi kusan dubu 100k shine a jikinta itama ta saka, tun daga wajen masu aikin ake binta da kallon mmki, zata shiga part din Hajia Aisha kenan Hajjaju ta jawota da sauri Tace, "Saratu, ko ba Saratu bace?" Tayi mgnr tana kallon kayan dake jikinta Saratu na washe baki Tace, "nice Hajjaju wani Abu kike bukata?" Ja baya Hajjaju tayi tana tafa hannu tace, "ke kuwa Saratu a Ina Kika samu uban kudin da Kika dinka kayan da iyayen yaro zasu saka?" Fara'ar Saratu ce ta fara raguwa zuwa bacin Rai waigawa baya tayi taga har an fara taruwa a wajen abinka da Taron biki, Saratu tace, "haba Hajjaju yanzu Dan nayi ankon iyaye shine abin aibi a ciki?" Daidai lkcn su Mummy da frnds dinta suka fito hajiyoyi dasu Wanda Suma ake damawa dasu a duniyar naira wata daga cikinsu tace, "Hajjaju wacece Wannan din?" Hajjaju tace, "wacece kuwa idan ba 'yar aiki ba?" Fuska a hade wata kosasshiyar Hajia a ciki tace, "Kan uban Nan ankon dake jikin mu shine Wannan jemammiyar me aikin tasa itama a jikinta?" A rude Saratu ta dubesu tace, "Dan Allah kuyi hakuri Nima Sageer Kamar da ne a guna Koh Hajia?" Ta Kare zancen nata Kan Hajia Aisha da ranta yyi mugun baci sbd kunyar data Bata gaban frnds dinta wasu ma matan Alhazai ne abokan daddy dake Hulda dasu, a tunzure Hajia Aisha Tace, "sbd Yana Kamar da a wajen ki sai akace danki ne? Meyasa Kika fiye Shiga sabgar da ba'a saki a ciki ba?" Sakin baki Saratu tayi tana kallon Hajia Aisha data rufe Ido ta fara zabga mata fada, a tsorace tace, "Dan Allah kiyi hakuri hajiya ni duk bansan hakan zai Bata muku Rai ba" Rai bace Hajia Aisha tace, "yanzun Nan basai Anjima ba nakeson kiyi maza ki cire kayan dake jikin ki idan ba so kike ki fuskanci mummunan hukunci daga gareni ba" gaba1 Saratu ta rude Bata taba zaton Hajia Aisha ta iya fada bare masifa ba sbd rikicewa tun daga wajen ta fara cire dankwalin kanta da taci gwaggwaro tana tafiya da sauri takalmin data sa Medan tudu shima ta gurde garin sauri saura kadan ta Fadi zanin dake jikinta duk ya harde ta hakan yasa ta figse zanin ya rage Mata daga ita sai fatari tana tafe tsingil-tsingil cikin Taron biki, ai kuwa me mutane zasuyi mata idan ba dariya ba sai gulmar ta ake wata na cewa ni da farko ma Dana Zo bikin na dauka itace uwar ango yanda Naga duk Abinda akace Ina uwar da indai Hajia Aisha Bata wajen zaka ga tayi tsugul Tace Gata Ashe 'yar aiki ce gsky ta zaqe dayawa, Nan mutanen wajen suka Amsa da cewa tabbas hakane anan dai akaci gaba da mgnr Saratu masu dariya nayi, Hajjaju ma tuni ta koma part dinta tun bayan data Gama Shan dariyar tafiyar Saratu, Hajia Aisha dai a kunyace ta bawa frnds din nata hakuri kafin suka fara shigewa manyan motocin da zai kaisu hall din da aka Kama na Iyaye, Saratu na komawa inda 'yan aiki ke zama taci sa'a ba kowa a dakin da suke, cire kayan tayi tana share kwallar takaici data fito Mata, kallon kayan tayi tana tunano yadda akai ta samu kudin data dinka su, duk kudin da take karbewa a wajen Omar dana aikinta da Wannan bikin da aka fara ta zama itace Kan gaba wajen siyo abubuwa anan ta samu damar Tara kudi me yawan gske, da munafurci da gulma Haka ta samu damar sanin kalar ankon dasu Hajia Aisha zasuyi, ta girgiza dajin kudin lace din Amma data tuna auren danta ne bana uban kowa ba sai taji itama dole tayi ankon tunda itace uwarsa ta Asali, wani irin hucin takaici tayi tana Muzurai, gaba1 ba Wanda tafi Jin haushi irin Hajjaju duk ta Bata mata shirinta Dan Ada niyyar ta tayi sauri ta saje cikin manyan Mata batare da an fahimci tana wajen ba, Tsaki ta Kara ja a Karo na Babu adadi tanajin Kamar taje ta shake Hajjaju ta huta. Bangaren su Anty shafa ma abin ba'a mgn domin wani irin uban bashi Mom taci Dan ganin kawai sun fita kunya a idon surukai, dukda Dad ya Basu kudi hakan be ishesu ba domin komai karya suke zubawa a ciki Suna ganin kamar sun kusa kamowa su Sageer komai da komai, Adan kwanakin Nan ne ma Dad yake Dan rike Aljihun sa idan Mom tayi Masa mgn Saiya Musa mata yace su Ina nasu uban da bazaiyi musu ba? Ranar daya fara Furta mata hakan hankalin ta ba karamin tashi yyi ba domin tasan baya Mata mgnr ubnsu kwata2 sbd tasa an kawar Masa da Wannan tunanin, sannu a hankali ta fara fahimtar canjawar Dad Abu kadan zai zugeta da fada batare da abun yakai ayi fadan a kansa ba, Wannan sabon canjin na dad ba karamin sake hargitsa tunanin Mom yyi ba ga biki ya shigo gadan2 hakan yasa take lallabawa a samu a Gama bikin duka kafin tasan bakin inda zata Kama bakin zaren
Fitowar dad daga Wanka kenan Mom ta shigo dakin nasa, kallon ta yyi ya watsar Mom tace, "Haba Alhaji kwana biyun Nan sai Naga kamar kana fushi damu" be kulata ba yaci gaba da shafa man da yake, matsowa tayi tana cire wani ganye daya makale Masa a baya daidai lkcn ya jiyo da sauri zaiyi mgn ta aje Masa ganyen Kan mirror dake gabansa Tace, ,"cire maka nayi gashi Nan" ta furta hakan tana nuna Masa ganyen, kallon ganyen yyi ya fahimci na miye Saiya dauka yaje can windows sa ya jefar, Yana dawowa ya fara saka kayansa Saida ya Gama still Mom na bakin gado tayi tagumi tana jiransa ya Gama, Yana gamawa kuwa yayi hanyar fita batare da yyi mata mgn ba, da sauri Mom ta Mike cikin kasa da murya Tace, "Alhaji tun dazu fa Kai nake jira?" A tunzure yace, "meye Wai?" Ya karasa mgnr Yana kallon ta Haka kawai 2days dinnan yakejin haushin duk mutanen gidan gaba1 mom ta Dan risinar da kanta kasa Tace, "Dan Allah idan ma lefi nayi maka kayi hakuri dama yaran Nan ne zasu Zo kuyi sallama ka tsaya ka saurare su kamar yadda ka Saba a baya Dan Allah" tsaki Yaja Yana Kama handle din kofa yace, "idan har sai sunyi min sallama ne zasu bar gidan Nan Toh karsu tafi suyita zama" yyi mgnr Yana bangaje rikon da tayi Masa kafin ya fice daga dakin, dukda Ana Taron biki hakan be Hana dad zuwa parking space ya dauki motar sa hade da barin gidan gaba1 ba, Mom ba karamin rudewa tayi da Wannan abun daya auki tsakanin ta da dad ba, Tasowa tayi hankalin ta a mugun tashe har zata fito daga parlon nasa ta tuna jama'a nacan suna jiranta akai Masa su Anty shafa, da hanzari ta dakata tana me rike kirjinta dakyar ta samu ta danne duk wani tashin hankalin da take ciki kafin ta fito a parlon, tana zuwa gun su Anty shafa suka Mike Anty shafa na fadin, "Mom Sageer yace masu daukar suna hanya muje muyiwa dad sallama kafin su iso" kallon su Mom tayi tana murmushin yake tace, "yanzun Nan daga wajen sa nake ina shiga Naga ya fito da key a hannun sa Wai anyi Masa Kiran gaggawa ne acan ma'aikatar su" Jamila ce Tace, "kasshh Amma dai Mom kinsan dai Babu kudi ajikin mu da baki Bari ya tafi ba sbd munaso ya sallame mu da wani abun" ja baya Mom tayi Tace, "Kiran yanada muhimmancin ne saidai kuyi amfani da sadakin ku" Anty shafa tace, "Mom Wai har kin manta ne?" Mom Tace, "me kenan?" a hankali Anty shafa tace, "kudin cikon boka ne fa muka Kai Masa gaba daya sadakin mu 200k akan samun mallakar mazajen mu bita zaizai Nan fa kudin namu ya tafi" dafe goshi Mom tayi gaba1 ta manta da sunyi Wannan Shirin sbd yadda kanta yadau zafi ji take kamar ya rabe biyu ga tashin hankalin da canjin dad yake kunno mata ga Rashin ishashe kudin dake wajen su, Anty Jamila ce Tace, "ba matsala idan ya dawo saiki karba Mana kisa Lami takai Mana" (sabuwar me aikinsu sbd lalaci sun kasa yin komai a gidan Saida aka Nemo me tayasu) Mom na murmushin yake tace, "Toh Shikenan" suna tsaye Haka akace Wai Ina amare ne har an gama kwashe masu rakiya? Anan Mom ta rungume yaran nata tana hawaye su kuwa ko a jikinsu, saima dariya da suke sbd sunsan daular da zasu Shiga, a Haka aka rabata dasu har suka fice a gidan Suma ba dadewa aka kwashe su sai gidan mazajen su. Tun ranar da Dr. Omar ya gayawa Meera matsayinta a gunsa da yadda ya dauketa ta dauke Masa wuta, Sam yanzu Bata bi ta kansa itama sai idan suna tare da Abba suyi drama kamar Ana zaman Dadi hakan yasa Abba Sam be fahimci Rashin jituwar dake tsakanin su ba, Kuma dukda Haka Meera Bata fasa sauke hakkin duk wani Abu daya rataya a kanta ba so take kafin tabar gidan saita Tabbatar Bata da hakkin Omar a kanta, daga Nan tasan cewa Allah zaiyi Mata sakayya ta inda Bata zato domin Yanason masu hakuri.
Yauma kamar kullum Meera tana dakin ta Dan yanzu Bata cika zama parlo ba tunda Omar yace komai tanayi ne Dan ta samu kusanci dashi shiyasa ta koma zaman daki dukda tanajin soyayyar sa a zuciya hakan be hanata danne wa ba Dan gani take Son maso wani take wato koshin wahala, Gama cire kayanta kenan ta samu Dan karamin kwalinta ta daura Bata da towel din Wanka Dan Haka da dankwalin take daurawa idan zata Shiga, Dan kwalin ko hips dinta be Gama rufewa ba ta Isa gaban mirror, karon farko dai yau ta tsaya tana yiwa kanta duba na tsanaki, a hankali take karewa surar jikin nata kallo, Doguwace daidai misali ba irin sosai dinnan ba, Haka zalika kirjinta a cike yake fam Kamar Wanda aka hurasu da iska, cikinta a shafe yake kamar an kifa faranti yyinda Ramin cibiyar ta yake fari Tass Babu Alamar dauda a ciki idan aka gangara Kan duma-duman hips dinta kuwa abin ba'ace komai domin a dunkule idan aka hada zai baka asalin me ake Kira da figure 8, dogon gashin kanta na daure dukda Haka ya sauko baya ta cije lips dinta a hankali tana tunano munanan kalaman da Omar ya jefeta dasu ranar, tana tsaye a bakin mirror taji iska na kadawa sosai ashe hadari ne ya taso kafin wani lkci har an kece da ruwa kamar da bakin kwarya, Meera dake jikin madubi tabar wajen ta Isa jikin window take ta tsuwara ruwan dake sauka da karfi Ido, washe baki tayi tanaji Kamar Ana janta ta fada ruwan tayi Wanka a inda takeyi duk lkcn da ruwan sama yazo, ata wajen lungu yadan Shiga ba lalle ma a ganka ba sbd ta saman da ruwa yake zuwa ta wajen anan Meera ke tsayawa tayi Wanka, Mika hannun ta tayi ta window take ruwan ya fara jika mata shi sai juya hannun take tana wasa dashi,
Ganin hakan bazai Mata ba Kawai ta fito da Wannan daurin kirjin nata tayi waje da Dan gudun ta gashin kanta na warwarewa da kansa ta zaga baya, daidai lkcn Dr. Omar dake dakinsa ya Gama zuge labulen dakinsa dake can sama Yana kurawa ruwan dake zuba da karfi Ido.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.