Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt
Chapter 71 of 85
*Littafin kudi ne, domin Samun cmplt dinsa saiki turo da 200 ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆ðŸÂ»*
8/15/20, 8:08 PM - Ummi Tandama: Dr. Omar ke ta zabga sauri bayan dawowar da daga masallaci duk hankalin sa Yana Kan Meera yazo Shiga gate kenan yaji an kwala Masa Kira, a mugun firgice ya waiga Yanason tantance shin gsky kunnen sa yaji Muryar data kirashi ko kuwa gizo ne? Da mugun mmki yake kallon Abba dake saukowa daga napep fuskar sa cike da murmushi ganin Dr. Omar din ya zama kamar gunki yasa shi fadin, "nine Nan na kiraka" ya karasa mgnr Yana sallamar me napep, take Dr. Omar ya Isa gaban Abba da sauri murna fal ransa ya Kama hannun Abba yace, "Alhamdulillah, Alhamdulillah Ala kulli halin Abba ka samu lpy, bakinka ya dawo, Oh ya Rabbi Thank you" ya jera maganganun cikin tsananin farinciki, Shima Abba cikin murnar yace, "kayi hakuri nazo a Wannan lkcn Toh Amma dole ce ta sani hakan domin hausawa na cewa da zafi2 akan bugi karfe.." "haba Abba Kuma Dan kazo yanzu meye laifi a ciki? Mu Shiga daga ciki" girgiza Kai Abba yyi yace, "aa inason mu gaisa da Ameera nasan idan taga na warke zatayi farinciki sosai kiramin ita" Tsam da ransa Dr. Omar yyi hankalin sa a mugun tashe da kunya a fahimci halin da meeran take yasan ta wahala kwarai bayason tayi tafiya Dan zata Kara wahala Amma bazai iya yiwa Abba musu ba, a fili yace, "Toh" yyi mgnr Yana Shirin Shiga gida.., har ya Kama kofa zai shige take Abba ya tuna muhimmin Abinda ke tafe dashi, gani yake idan ya sake barin Wannan damar be sanar da Dr. Omar gsky ba za'a sake samun matsala musamman dayasan yanzu Haka Saratu tana can zata sake hada wata masifar, hakan yasa d sauri yace, "Omar dawo" Juyowa Omar yyi da mmki Abba Yana murmushi yace, "kila ta koma bcci Koh? Kada mu takura mata, dawo kaidin akwai wata muhimmiyar mgnr da zamuyi" a boye Dr. Omar ya saki ajiyar zuciya Dan bayason kowa yasan meye matsalar sa tsakanin sa da Meera har Saiya daidaita komai, Dawowa yyi gaban Abba yace, "gani" Abba yyi shiru Yana kallon sa gaba1 Fuskar sa ta canja zuwa yanayi na damuwa da Takaici, hakan yasa Dr. Omar yasha jinin jikinsa Haka kawai yaji zuciyar sa na harbawa da sauri, tunani Abba yake ya sanar Masa shi kadai ne ko kuwa yasashi gaba suje can gidan da Saratu ke Aikatau ya fada musu a tare? "Abba kayi shiru" Dr. Omar ya katse Masa tunanin da yake, sauke ajiyar zuciya Abba yyi kafin yace, "dauko motar ka akwai Inda zamu" A rude Dr. Omar yace, "Meera fah???" Ya Fadi hakan cikin subutar baki dan gaba1 hankalin sa fiye da rabi Yana wajenta, wara ido sosai Abba yyi da mmki yace, "kodai Bata da lpy ne Omar?" Girgiza Kai yyi da sauri bakinsa na rawa yace, "eh..aa lpyr ta kalau Bari na dauko motar" ya Furta hakan da sauri Yana shigewa cikin gidan, binsa da kallon mmki Abba yyi Yana ganin kamar akwai Abinda ya Sami meeran tun daga yanayin reaction dinsa na farko dayace a kirata zuwa yanzu, Dr. Omar na shiga gidan ya wuce wajen motar tasa sbd yaji akwai key a jikinsa Daman tunda yaje dakinsa da Asuba ya dauko akan idan ya dawo masallaci zai dauki Meera zuwa prvt hsplt ya gani ko ya mata rauni ne, me gadi ne ya bude Masa gate din Yana daga ciki besan da zuwan Abba ba harya kulle gate din, Yana fita kuwa Abba ya shige motar Nan ya jata suka tafi, shiru motar tayi kowa da tunanin da yake, Abba na tunani da tausayin Yadda Dr. Omar zai dau abin shikuwa Dr. Omar na fatan ace ba wani daukan lkci zasuyi ba Dan Yana bukatar ganin Meera shiyasa ma yake ta tuki da sauri, Saida sukazo main road Dr. Omar yace, "Ina muka nufa Abba?" Abba yyi Masa bayanin unguwar da zasuje, girgiza Kai Dr. Omar yyi kafin ya maida hankalin sa Kan tuki, dukda safiya ce hakan be hanasu samun goslow ba hakan ya jawo musu delay kafin su samu Karasawa unguwar har 9am tayi, kallon unguwar Dukkansu suke yyinda Dr. Omar yake mmkin me Kuma zasuyi a Wannan unguwar? Dan daga yanayin unguwar kasan ta manyan mutane ce duba da yanayin gidajen Wannan Yana wane Wannan, har lkcn Abba beyi Masa mgn ba Saida sukazo saitin gidan dayafi kowanne girma da daukar hankali sbd kyawunsa yace, "dakata anan" tsayawa Dr. Omar yyi yace Masa su fita, Shidai Dr. Omar bin umarnin Abba kawai yake batare daya fahimci komai ba, bayan ya gyara parking dinsa ne suka nufi gate din dake gabansu, wasu security ne suka taso suna binsu da kallo kafin suce, "Kai suwaye ku?" Abba yace, "Dan Allah ko Alhaji Yana ciki?" Wani daga cikine yace, "da sassafen Nan Dan jaraba kabar mutum da iyalin sa man..." Kafin ya Gama rufe bakin nasa kuwa yaji an kwashe shi da Mari, a gigice kuwa ya rike Kumatu hankali tashe Yana kallon Dr. Omar dake tsaye cikin zafin zuciya, sauran security din ne suka taso hade da pointing Dr. Omar da guns dinsu, a rude Abba yace, "Dan Allah kuyi hakuri karkuyi Masa komai" yyi mgnr Yana kokarin hade hannayen sa da nufin roko Dr. Omar yyi saurin rikewa Rai bace yace, "Ina wajen kke kokarin Basu hakuri Abba? Allah ya sauwake Wai mema zamuyi anan inda ba'asan darajar mutane ba? Dan Allah mu tafi" ya Ida mgnr Yana Jan hannun Abba, kin motsi Abba yyi Yana kallon Dr. Omar cikin damuwa yace, "kayi hakuri Omar Amma ganin megidan Nan yanada matukar muhimmancin a garemu" baki sake Dr. Omar yake kallon Abba, yyinda sauran security din suka fara musu isgilanci suna fadin da gani rokar maka jari zaiyi idan hakane kuwa sai ku jira Nan da karfe daya tunda weekend ne Saiya fito Sallah, ran Dr. Omar ne ya Kara baci zaiyi mgn Abba ya dakatar dashi da fadin, "Dan Allah karkace komai da sannu zasu gane mutum daraja gareshi ko a Yaya yake" dariya suka fara musu sbd gani suke Kamar talauci yasa Abba ya nace su tsaya Dan a Basu taimako, shi kuwa Dr. Omar ji yake kamar ya bubbuge su ba damar hakan sbd Abba ya Hana, Abba Yaja hannun sa yace, "muje gefe mu jirashi" cikin matukar takaici Dr. Omar yace, "I don't know why Abba ka nace saimun tsaya a inda ake cin zarafin mu Kuma kace muyi hakuri bayan inada damar na saita musu hankali" girgiza Kai Abba yyi yace, "dama ai Manzon Allah S.a.w. yace muyi hakuri a inda muke da karfin ramawa shiyasa nakeso kayi hakurin" cije lips dinsa Dr. Omar yyi Yana shafa sumar kansa hade da lumshe ido Meera ce ta bayyana a idon nasa take ya bude idon da sauri hankalin sa a mugun tashe gsky zai tafi idan mutumin ya fito Saiya dawo bazai iya jurewa ba da Wannan tunanin ya dubi Abba zaiyi mgn kenan Sukaji an bude gate, da murna Abba yace, "Alhamdulillah kaga ma ya fito muje" yyi mgnr Yana nuna bayan Omar dake ya juyawa gate din baya Juyawa Dr. Omar yyi Yanason ganin Wanda Abba Ke nuna Masa yyi Arba da Alhaji Abdullahi, da mugun mmki Dr. Omar yace, "Abba ka sanshi ne? Meye hadinku dashi?" Ya karasa mgnr Yana sake waigawa daidai lkcn Alhaji Abdullahi ya dubesu shima take ya cika da mmkin ganin Dr. Omar kofar gidansa, nufar su yyi da sauri fuskar sa a sake yace, "Omar Kaine? Meyasa baka kirani na fito ba?" Ya karasa mgnr Yana Ida zuwa wajensu, yanzu Kuma mmki ne ya Kama Abba sosai Saiya koma kallon Alhji Abdullahi da Dr. Omar, kawar da nasa mmkin Dr. Omar yyi Yana shafa sumar kansa yace, "I'm sorry daddy" daddy ya Mika Masa hannu sukayi musabaha zuciyar sa fari Tass yace, "gsky kamin zuwan bazata Kuma naji Dadi ainun dama kullum burina kenan naga kazo" Sunkuyar da kansa Dr. Omar yyi duk kunya ta Kama shi ya tuna yadda Alhji ke Masa tayin zuwa shikuma yyita zamewa sbd bayason Abinda zai sashi rikici da masu kudi, sai a lkcn Abba da daddy sukayi musabaha daddy yace, "Masha Allah ku shigo ciki" Abba ya gyada Kai tamkar kadangare duk mmkin sanayyar su yake, Sam Alhji Abdullahi be kawo komai a ransa ba Shidai kawai ya amshe su a Matsayin baki Kuma masu muhimmancin Nan yyi gaba suka bishi a baya, direct parlon baki yyi dasu, suna shiga kuwa motar Sageer ta sharo gidan a guje har Yana tada Kura. Bayan sun zauna ne daddy yace, "abin mmki Taya ka samu Address din gidana?" Shiru Dr. Omar yyi Yana Sunkuyar dakai Abba yyi saurin saka baki da fadin, "mgnr gsky Alhaji nine Nan na kawo shi bawai Dan yasan gidanka bane" kallon sa daddy yyi d mmki yanaso yasan Toh Ina ya sanshi? Saidai duk tunanin sa ya manta, Abba yaci gaba da fadin, "wata muhimmiyar mgn ce ta kawo ni Nan, saidai inaso duk kuyiwa zancen nawa kyakkyawar fahimta" yanzu Kam harda Dr. Omar yake kallon Abba duk ya Matsu yaji wacce irin mgn ce Wannan? "Ikon Allah bawan Allah wacce irin mgnce Haka daka zabi ka hadamu waje guda muyi?" Murmushin takaici Abba yyi yanajin zuciyar sa na rawa yace, "Bayan ku biyun ma idan da son samu ne ace duka Ahalin gidan Nan suna Nan" yanzu Kam gaba1 kansu ne ya kulle Dr. Omar yace, "Abba tun da Allah ya baka lpy naji Kanata min mgnr da Sam ban fahimta ba, dama kasan shi ne? Meye dalilin Wannan taramun da kke? Meyasa ka zabi muzo Nan? Bayan tun d can bamu taba zuwa ba?" Girgiza Kai Abba yyi cikin yanayin tausayawa yace, "dama ya za'ayi ka samu zuwa Nan Omar? Nima bansan zan kawo ka Nan din ba Saida dalili me girma ya jawo hakan" daddy ne Yaja ajiyar zuciya yace, "shikenan Bari na Kira su" Nan ya Mike ya fice a parlon, Kallon sa Dr. Omar yyi yace, "Abba Dan Allah ka fahimtar Dani Abinda ke faruwa Wlh gaba1 Kaina ya kulle duk kasa na Shiga fargaba" kokarin mayar da kwallar sa Abba yyi yace, "ni Kaina Omar a cikin fargabar nake, dolece ta sani hakan kayi hakuri kaji?" Cije lips dinsa Dr. Omar yyi Yana matse yatsunsa, daidai lkcn daddy yyi sallama, Amsa Masa sukayi daga Nan Kuma sai ga Hajia Aisha ta iso itama bakinta dauke da sallama, wani irin bugawar zuciya ce ta kasance tsakanin ta da Dr. Omar a lkcn da sukayi Ido biyu da juna cikin azama tayi saurin kawar da idon nata zuciyar ta na harbawa da sauri2 bayanta Safna ce da Katon hijab tana kumbura fuska Dan bcci take aka tasota, tana ganin Dr. Omar ta washe fuska sosai da murna ta Isa gareshi Fadi take, "ya Omar? Yau Kaine a gidan namu? OMG! Mummy shine fa GM na company da muke baki lbri Koh daddy?" ta karashe mgnr da sigar tmby gaba1 ta karade falon da surutu sai kace aku, yyinda mummy da Dr. Omar suka cika da tsananin mmkin juna, shikuwa Abba kawai kallon ikon Allah yake idan ya kalli daddy, Saiya kalli Mummy ya dawo ya dire kallon nasa Kan Dr. Omar, Daddy ne ya katse surutun Safna da fadin ta zauna kafin ya dubi Abba yace, "gashi mun taru saidai ba duka b Hajjaju tana bangaren ta kasan Sha'anin tsoffi tafiya tana wahala, babban Dana Kuma Yana zuwa" girgiza Kai Abba yyi kafin yace, "Toh Masha Allah, godiya ga Allah subhanahu wata'ala daya bani Aron Rai har izuwa kawo Wannan lkcn da nake tare daku." Shiru parlon ya dauka Ana sauraron Abba dake mgn kowa mmki ne dankare a ransa daidai lkcn Sageer ya fado parlon ba ko sallama, zuruf Dr. Omar ya Mike Yana kallon Sageer, Sageer shima da mugun mmki ya kafe Dr. Omar da kallo, daddy ne yace, "lpy dai Omar?" Dr. Omar na kallon daddy Yana kokarin danne zuciyar sa yace, "yaron ka ne?" Girgiza Kai daddy yyi, cije lips Dr. Omar yyi wasu irin zafafan takaici na safara a ransa ya maida kallon sa Kan Abba da yake kallon sa da mmki shima yace, "Abba tashi mu tafi" Abba yace, "meyasa kace Haka Bayan ban sanar daku dalilin taraku da nayi ba?" Shafa sumar kansa Dr. Omar yyi cikin Jin haushi yace, "Abba ni zan wuce idan kun Gama zan dawo mu tafi ko Menene zamu hadu ka fadamin" yyi mgnr Yana Shirin tafiya, saurin rikosa Daddy yyi Yana fadin, "duk me ya jawo bacin Rai Haka lkci guda? Ka sanshi ne? Koh wani Abu ya taba hadaku?" Dan cije lips Dr. Omar yyi kafin yace, "I'm sorry daddy but Ina tunanin lkcn barin aikina ne yazo yau" hankali tashe daddy yace, "Omar?" Lumshe Ido Dr. Omar yyi yanajin wani irin zafi a ransa harga Allah da yasan a karkashin mahaifin Sageer yake aiki da ko kadan beyi marmarin karbar aikin ba, yadda akai yyi sanadiyar barin karatun sa ne ya dawo Masa sabo sai yakejin haushi da bacin Rai na barazanar tarwatsa ransa sbd Kuna, Muryar Abba ce ta katse su da fadin, "Wai Omar meye matsalar?" Sai a lkcn Dr. Omar ya bude idonsa da suka fara rinewa daga fari zuwa ja ya dubi Sageer dake bakin kofa hankalin sa a mugun tashe Yana tsoron kada Dr. Omar ya sanar da daddy Abinda ya Masa a skul shiyasa duk ya gagara tsayuwa Yana fatan Omar din ya tafi, zuba Masa ido Dr. Omar yyi na wasu seconds kafin yace, "Abba ka tuna dalilin barina skul?" Abba ya gyada Kai Dr. Omar ya cije lips dinsa Yana kallon su duka yace, "ba kowa bane face Wannan mutumin" ya karasa mgnr Yana pointing Sageer cikin tsantsar takaici, "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" duka suka hau salati Mummy gaba1 ji tayi ranta ya mugun baci bare daddy dayake Jin Kamar yahau Sageer din da suka shikuwa Abba kwallar bakin ciki ne ta Kama shi sbd Jin yadda akai Dan daya Haifa ma halin uwarsa ya biyo wajen mugunta ga kamarta Nan a fuskar sa Banda mugun Asiri ma ai kowa ya ganshi yasan ba Dan gidan bane Dan kuwa su Dukansu farare ne tastas Kamar jinin larabawa, Fuska Sageer yyi ya juyar da kansa gefe saidai acan cikin ckinsa hanjinsa kadawa yake sosai, daddy ne ya kalli Dr. Omar yace, "I'm very sorry for...." "Bakai kamin lefin ba daddy meyasa zaka ban hakuri?" Dr. Omar ya katse Masa mgnr, daddy yace, "dole a baka hakuri sbd Abinda yyi maka Babu Adalci a ciki tun a lkcn da kace kabar skul naso sanin dalili ka rokeni da kada na tmbyeka da duk ba'a kawo Wannan lkcn ba Amma yanzun lkci be kure ba zan dauki mummunan mataki a kansa dashi da duk Wanda yyi sanadin barinka skul din" Cije lips Dr. Omar yyi Abba ya kamo hannun sa yace, "ka zauna tun kafin na Rasa bakin dazan sanar muku" Nan dukansu suka bishi da kallo a mugun firgice, take gun yyi tsit Ana son Jin tabakin sa, Abba yyi gyaran murya kafin yaci gaba da fadin, "bansan ya zaku dauki lamarin ba Amma dai duk Abinda kukaji nace tofah tabbas gskyne" har yanzu shi suke kallo, shima Dagowa yyi ya dubesu daya bayan daya kafin ya dire kallon sa Kan daddy yace, "Alhaji ko ka tuna da 'yar aikin ku Saratu?" "Saratu..?" Mummy ta fadi hakan da mugun mmki, "Anty Sara..?" Safna ta furta hakan itama da mmki, shima Dr. Omar da mmki yace, "Ummah..?" daddy yace, "Eh wani Abu ne ya faru?" Abba yace, "ehto Amma dai idan zan iya tunawa ta Dade a gidan Nan tana aiki sama da shekara talatin" "confirm" daddy ya furta hakan, sauke ajiyar zuciya yyi zuciyar sa na tarabbabin yadda zai sanar dasu Wannan kulli kafin can yyi ta maza yace, "a zahirin gsky matatace saidai Kai tsaye zan iya kiranta da muguwa marar tsoron Allah" Dr. Omar ne yace, "Abba Ummah kke mgn akai?" Kallon sa Abba yyi yace, "kwarai kuwa, domin ita din Azzaluma ce me raba iyaye da yaransu, Kai idan akwai Wanda yafi cutuwa a Wannan Rashin tausayin nata ma ya biyo bayanka" wara ido sosai Dr. Omar yyi yanzu Kam ya fara tunanin kodai Abba ya kunce ne? Abba kuwa yaci gaba da fadin, "Kuna tare da itane batare da kunsan kullun data Dade tana muku ba domin tun farkon zamanku da ita take muku zagon kasa" daddy ne yace, "bawan Allah tun dazu kke Mana mgn me Kama da surkulle kasa kanmu ya daure me kke nufi da duk Abubuwan da kace?" Abba yace, "a takaice dai Wannan yaron da kke gani" ya dafa Dr. Omar yace, "shine jininka Ina nufin shine Dan da matarka ta Haifa shi kuwa wancan.." ya nuna Sageer daya dago kansa a firgice yace, "shine danta data Haifa lkci guda tayi Wannan canjin tun suna jarirai" Qalu innalillahi wa'inna ilaihin raji'un gaba1 parlon ya dauka da salati kowa ya rude ya firgice, kafin wani yyi mgn sukaji an kwada sallama hade da shigowa parlon Hajjaju ce ta shigo tana fadin, "naje bangaren ku duk bakwa Nan me ake tattauna anan...??" Bakinta ne ya makale lkcn datayi Arba da fuskar Dr. Omar, karasowa tayi da sauri tana nufar inda yake bakinta na fadin, "yau Naga ikon Allah Kai baban Safna kaga me kamar ka kuwa? billahil Azeem kamar an tsaga Kara kodai idona ne?" Ta Ida mgnr tana shafa fuskar Dr. Omar da gaba1 ya zama kamar gunki sbd fadawa tashin hankali, a firgice daddy ya dubeta Yanason ganin Abinda take nuna Masa, tabbas sai yanzu yake hango tsagwaron kamarsa da Dr. Omar yyinda a fusge yake Kama da Hajia Aisha "Hasbunallahi wani'imal wakil...." daddy ya samu bakinsa da Furta hakan a kidime, Mummy kuwa wani irin kuka ne ya kwace mata take ta fashe dashi jikinta na rawa, sai a lkcn Hajjaju ta dubi yanayin su Tace, "Wai meke faruwa Anan?" Abba ne ya samu kwarin gwiwar sanar da ita Abinda ake tattaunawa akai, da mmki suka ga Hajjaju tayi sujjadar godiya ga Allah kafin ta dago bakinta a washe tace, "billahillazi mgnr bawan Allah Nan gsky ce, ni dama tun tuni nake jin zuciya tana kokwantan Anya ja'irin Sageer dinnan jinin mu ne?" Tashi Dr. Omar yyi domin ya kasa gaskatawa da hakan sbd rudani yyi nufin ficewa daga parlon daddy yyi saurin riko shi yace, "ai tunda kazo Nan Babu inda zakaje kazo gidanku" yyi mgnr Yana bin Dr. Omar da kallo sosai yadda yake Abubuwan sa ne suka fara dawo Masa musamman a company idan yyi wani abun sai yaji tamkar jininsa ne sbd ra'ayinsu da izzar su da Kuma Rashin tsoron su dake zuwa kusan daya domin shi Dr. Omar harya take daddy a wa'annan halayen dayake shi yanzu yake cin duniyar tasa daddy Kuma an kwana biyu, Mummy ma mikewa tayi da sauri ta kamo dayan hannun sa hawaye na zuba a kumatun ta sosai bakinta na rawa tace, "laifina ne Ameer" da sauri Dr. Omar ya juyo Yana kallonta da mmkin sunan da yaji ta kirashi dashi, Mummy kuwa ta sakaye sunan ne sbd sunan mahaifin daddy gareshi wato uban mijinta, girgiza Kai tayi tana ci gaba da fadin, "sakacina ne dayasa na aminta da matar da ban santa ba harna jawota jikina da tun farko naji mgnr Hajjaju duk hakan bazai faru ba Dan Allah kar ka tafi" rintse ido Dr. Omar yyi kafin ya juyo garesu gaba1 take kuwa yaji zuciyar sa ta kamu da tsananin son mahaifan nasa na gsky, yanajin feelings irin na Iyaye da Dansu, Safna ce ta rungume shi ta baya hawaye duk ya wanke Fuskar ta Tace, "Dan Allah ya Ameer karka tafi Wlh muna son ka" itama ta sake kiransa da sunan daya Kara Jan hankalin sa, besan meyasa yaji tashin farko lakabin *Ameer* ya shiga zuciyar sa sosai Haka ba, Hajjaju ma matse kwallar ta take tace, "Amma Wannan mata kin cucemu Saratu Allah ya Isa tsakaninmu dake" Daddy yace, "dole ne Ayau dinnan a kamo ta domin ta fuskanci hukuncin daya dace da ita" Cije lips dinsa Dr. Omar yyi yana tuno irin zaman da yyi da Saratu Ashe duk lkcn dayake tunanin kodai ba ita ta haifeshi ba gskyne, Ashe itadin ba mahaifiyar sa bace, Abba ne yace, "ai bama ita kadai ba harda Wannan Nas din da suka kulla abin tare za'a Kama su" kallon sa Hajjaju tayi Tace, "Dan Allah yi Mana bayani daya bayan daya yadda akai ta dauke Mana jinin mu tasa nata" Nan Abba ya fara sanar dasu tun daga farkon yadda yaji hirar su har kawo lkcn datayi Masa Asiri ya daina mgn kwata2, gaba1 wajen Ba Wanda be girgiza da lbrn Abinda Saratu tayi ba, take suka fara Allah wadai da halinta mikewa daddy yyi yace, "muje a dauko ta basai mun jira tazo ba" Nan Abba ya sanar musu shirinta na zuwa gun boka jiya, "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" suka sake sakin salati gaba1 hankalin su ya sake tashi ba Kamar ma Mummy da gani take duk silarta Abubuwan ke faruwa shiyasa duk ta kidime Kamar tayi hauka, ganin Haka yasa daddy yace, su wuce a fara Kai report kafin su dawo tunda ba'asan inda suka nufa ba sannan yace kowa ya rike Addu'a Insha Allahu Babu Abinda zai samu dayansu. a bangaren Sageer kuwa Ai tunda Abba ya Gama bada lbrn kullin da Saratu tayi a hankali ya sulale yabar parlon batare da an ankare dashi ba, Dukda Dr. Omar Yana cikin tashin hankalin Abinda Rayuwar sa take ciki hakan besa ya manta da batun Meera ba, Dan Haka Yana ganin daddy zai sake turashi suje wajen Kai report ya dafe kansa da sauri kamar Wanda ya Sara Masa, kasa yyi da sauri Yana dafa kujera, cikin azama daddy ya rikoshi Yana dubansa yace, "Omar kana lpy?" Dan yatsina fuska yyi Yanason pretending kawai sbd yaje gurin Meera yace, "my head" ya furta hakan Yana Dan cije lips dinsa, cikin damuwa yace, "muje cikin gidan kasha mgni" shiru Dr. Omar yyi yana Sunkuyar da kansa, Daddy yace, "idan kasha saika huta kaji?" Still Dr. Omar be dago ba Dan ba Haka yakeson ji ba, sai yanzu Mummy tayi murmushi tace, "Kasan be fara sakewa damu ba Inaga a barshi ya tafi gida Saiya dawo Anjima" wata irin boyayyar ajiyar zuciya ya saki har ma taso yasa a gane yyi saurin yin fuska, Safna ce Tace, "tho Bari na bishi tunda bayajin Dadi" a rude Dr. Omar ya kallota shikenan zata Bata Masa plan dinsa, Mummy Tace, "No Wannan surutun naki ma Kara Masa ciwon zaiyi" lumshe ido yyi yanajin kaunar Mummy na ratsa Masa zuciya, ba yadda suka iya Haka dai suka barshi ya tafi yyinda suka rike Abba a gidan hakan yasa sai shi kadai ne ya tafi. Tunda yahau titi yake sharara gudu burinsa ya Isa ga Meera gefe guda tunanin Rayuwar sa ne fal ransa, mmkin yadda akai yyi rayuwa batare da iyayensa na Asali ba yake, lbrn tamkar a film kk Novel? Wannan wacce irin matace Saratu? Yanajin Kamar yafi kowa shiga damuwa da tashin hankali akan Abinda yaji, Haka zalika yafi kowa son daukar mummunan mataki Kan Saratu datayi sanadin rabashi da Ahalin sa, saidai yanzu Meera ce a ransa shiyasa ya kasa maida hankali akan Abinda ke faruwa, tunanin yadda zai fuskanci Meera ne ya sake Fado Masa yanzu Kuma mezai ce mata?. Koda ya Isa gida ma ko parking beyi d kyau ba ya wuce can parlon sa, da Dan saurin sa ya bude kofar Yana shiga yaji Kara sosai ta saman sa anata buga kofar dafe kansa yyi domin ya manta da wanzuwar Salma a gidan, tsaki Yaja kawai ya wuce dakin Meera direct, kallon Kan gadon yyi yaga Alamar tudun bargo hakan sai yasashi tunanin Koh har yanzu bcci take? Dan guntun murmushi yyi Yana lumshe Ido Daren su na jiya yake tunawa Yana hango yadda take ta Masa rigima, kasa tsayuwar kofar dakin yyi yanajin wani Abu na taso Masa acan kasan ransa game da ita gefe daya Kuma cije lips dinsa yake Yana tuno gardi da dadin daya kwasa a gareta, cikin sanda ya lallaba Yanason Jin Koda duminta ne kadata farka harya fara Hawa gadon beji Alamar motsi ba, hakan yasashi Jin Dadi yasan Sarai zata wanke Masa duk wata damuwa da yake cikinta a yanzu, Saida ya daidaita Kan gadon ya fara janye katon bargon da yyi tudu a wajen, Yana fara ja bega Alamun ta ba be kawo komai a ransa ba yaci gaba da budewa, a mugun firgice yyi wurgi da bargon Yana kallon wajen da yake wayam ba Alamar Meera, cikin hanzari ya diro akan gadon Yana nufar toilet tunanin sa ko can tayi, Nan ma Yana budewa yaga wayam, Toh kardai kitchen ta nufa Nan ya fito daga dakin ya nufi kitchen Nan ma shiru, take hankalin sa ya fara tashi duk Inda yake tunanin zai ganta Bata wajen Nan ya haura saman sa Yana tunanin ko dakinsa taje, Yana shiga dakin nasa ma Babu Alamar mutum ya Shiga saima bugun kofar da Salma take tayi tun dazu ya cika Masa kunne cikin takaici ya fito yazo wucewa ya cire key din jikin kofar kafin yaci gaba da tafiya Yana son komawa dakinta duk hankalin sa ya fara tashi, Yana shiga dakin nata take hankalin sa yakai wajen data aje trolley jiya yaga wayam besan lkcn daya Furta "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" ba, a mugun firgice ya fito Yana bin hanyar waje direct wajen me gadi ya nufa bakinsa na rawa tun daga nesa ya fara kwalawa mlm habu kira, mlm habu dake daki ya fito da sauri daidai lkcn Dr. Omar ya iso yace, "Mlm habu ko kaga ficewar Ameera?" Mlm habu yace, "kwarai kuwa tun bayan tafiyar ka masallaci tabar gidan Nan Ina mata mgn ma Bata kulani ba" cikin karaji Dr. Omar yace, "Whyyyyy....???? Meyasa ka barta ta tafi....???" Ya karasa mgnr Yana dunkule hannun sa daya hade da kaiwa dayan hannun nasa naushi take mlm habu ya girgiza da yanayin reaction din Omar, jikinsa na rawa yace, "kayi hakuri yallabai nayi zaton da saninka ta tafi" wata irin doguwar tsuka Dr. Omar yyi yanajin badan darajar shekaru ba Babu Abinda zai Hanashi wankawa mlm habu Mari, tsayuwarsa a wajen Bata da Amfani Dan Haka a zuciye yyi hanyar fita Yana Ciro wayarsa Dan Kiran Dr. Sadeeq, saura kadan ya buge mlm habu ma Allah yaso yyi azamar matsawa gefe, kafin ya Shiga motar tasa yyi dialing number Dr. Sadeeq yanajin ta fara ringing ya bude motar ya shige, Yana driving yaji ringing din har ya katse Dr. Sadeeq be dauka ba, tsaki Dr. Omar yyi ya sake bin number still Dr. Sadeeq be dauka ba, cikin kunar Rai ya fara mgn shi kadai Yana sake dialing number Fadi yake, "ka dauki Kiran Mana Sadeeq" be Ida rufe bakinsa ba kuwa yaji alamun ya dauka, Dr. Omar najin Haka ya fara mgn da sauri2 Yana fadin, "haba Sadeeq Wai Ina ka shigane Ayita kiranka baka picking call" Cikin yanayin bcci Dr. Sadeeq yace, "haba Ango irin Wannan ihu Haka ai saika fadamin dodon kunne" tsaki Omar Yaja yace, "Dan Allah ka tashi ganin Nan zuwa inda kke I need your help" wata irin dariyace ta kwacewa Sadeeq har Yana rike ciki yace, "Kai Mijin Ameera Angon salamatu kace jiya kayi babban aiki harka manta da asalin waye Kai wato Doctor kana neman Dr. Sadeeq ya duba ku, ah lalle Salma tayi kokari" wani mugun tsaki Dr. Omar Yaja me daci-daci yace, "Wai meyasa Ana zancen serious kana sa wasa a ciki?" still Dr. Sadeeq na dariya yace, _Toh Angon salame saika iso" wani irin takaici ne ya sake makure Omar ji yake kamar ya fasa ta wayar ya naushi Sadeeq koya huce da takaicin hadashi da Salma dayake, Kai tsaye ya kashe wayar Yana karawa motar gudu Yana fatan daga can Sadeeq ya rakashi gidansu Meera Dan bazai iya jure rashinta a kusa dashi ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.