Best Hausa Novels

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt

Chapter 77 of 85

Idan na samu caji Anjima Insha Allahu zanyi wani Rashin enough charge yau yasa nayi kadan👏🏻

*Littafin na kudi ne 200 Zaki turo ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻*
8/20/20, 10:22 AM - Ummi Tandama: Kokarin cire bakinta daga nasa take Amma Ina Sam ta kasa sbd ba rikon wasa yyi mata ba, Riko ne da yake nuna yyi kewar ta he missed her a lot, Sadeeq ne ya dawo daga wajen bayan ya Amsa wayar Yana shigowa parlon yyi gamo take kuwa yyi turus Yana komawa baya bakinsa na furta, "Astagfirullah..." Yana fadin Haka ya juya da sauri, furucin sa ya dawo da Dr. Omar duniyar da yake neman zarmewa, sakin bakinta yyi Yana sauke numfashi a hankali, cikin matukar jajircewa Meera tayi ta maza ta banko Masa Harara tana Shirin mikewa taji ya riko mata qugu, fuska ta hade tana kallon kwayar idonsa da suka fara rinewa Tace, "mlm ka sakar min jiki" murya can kasan makoshi yace, "haramun ne Dan na taba matata?" Ya Kare mgnr Yana mata wani irin kallon daya bugi kirjinta a hanzarce kuwa ta dauke kallonta daga gareshi tana juya manyan idonta Tace, "kanada abin mmki" dage gira daya yyi Yana Mata Dan iskan kallon Nan yace, "kamar ya?" Hararar sa tayi kafin Tace, "be kamata ace kana wasting time dinka a wajen wacce tazo tai maka Aikatau ba, Matsayin ka da class dinka sunfi dacewa da yarinyar daka aura kwana biyu da suka wuce" Dan cije lips dinsa Omar yyi kafin yace, "Ki manta da komai domin ni na shaida kece Kika dace da class Dina Meera" ranta ne ya sosu kwarai tasan ba komai yasa yace hakan ba saidan kawai sbd jikinta, hakan yasa a Dan kausashe tace, "sbd jikina Koh?" Saurin girgiza Kansa yyi yace, "Sau nawa zance Miki ba Haka bane?" Samun nasarar ture shi tayi ranta na zafi tace, "idan bance Haka ba me kkeso nace maka ya Omar? Ka taba kula da damuwata ne tun bayan da mukayi aure? Ka taba tsayawa ka fahimci hakkin ma'aurata akan matan su? Kai bama Wannan ba aure anayin sa ne Dan so da kauna a zatona lkcn da kazo neman aurena zaka kasance me sharemin hawaye ne a lkcn Dana Rasa me sharemin, na zaci kaunace silar auren mu Ashe ni nayiwa abin Rashin fahimta, Ashe kaidin fansa kkeson dauka Kaina Akan Abinda Sam banida hakki a ciki, taurin ranka da nuna isarka ya Omar yasa kaki saurarata bare na fada maka dalilin amsar Dana bayar a kotu, kayi threatening Dina ta hanyoyi da dama marasa dadin ji da sauraro Wanda yake nuna tsantsar tsana da keta Babu Alamar tausayi Koh So na a ranka, koh zuwa yanzu banji da kunne na soyayya tace ta kawo ka ba sai anyi mgn kace ba Haka kke nufi ba a hakan kke tunanin zan aminta da cewar ba jikina kkeso ba...?" Ta karasa zancen nata lkcn da take share hawayen dake malala Kan kumatun kafin tayi Dan Murmushin takaici taci gaba da fadin, "tunda ka rusamin budurcina ya Omar ka fara son kasancewa Dani, baka so ni Ada yadda nake ba Saida ka samu rabo a jikina, Abinda bazan dauka ba kenan ya Omar ka sakeni kawai naje na auri Wanda zai Soni tsakani da Allah....." Ta Ida mgnr cikin fashewa da kuka sosai sbd cin karfinta da yyi kawai ta bude kofar parlon ta fice da sauri. Sadeeq na waje yaga fitowar Meera tana kuka hakan ya bashi damar Shiga parlon da mmki, Dr. Omar kuwa yadda kasan ruwa ya cinyeshi Haka yakeji, tabbas Abinda Meera ta fada Masa gsky ne, Kuma ta fishi gsky shiyasa beyi nufin hanata mgn ba sbd kawai ya gano meye matsalar sa da ita domin ya gyara kuskuren sa Kuma tabbas yaji lalle ba karamin kuskure ya tabka ba, meyasa tun farko ya kasa tsayawa yaji dalilin bada amsar da tayi...? Girgiza shi Sadeeq yyi sbd yanata mgn yaji shiru be Amsa ba, firgigit ya dubi Sadeeq kamar Wanda ya tashi a bcci, har yanzu mmki ne bayyane fuskar Sadeeq yace, "Wai meke faruwa ne Omar?" Sauke ajiyar zuciya Omar yyi Yana me cusa hannayen sa cikin lallausan gashin sa Fadi yake, "akwai Kura Sadeeq" zama Sadeeq yyi yace, "wani Abu Kuma ka sake mata?" Girgiza Kai Omar yyi gaba1 ya Rasa ta inda zai Kama sbd tashin hankali dakyar dai ya samu ya sanar da Sadeeq Abinda zai iya fada Masa, gwauron Numfashi Sadeeq Yaja kafin yace, "mgnta ta zama gsky kenan Omar nasha fada maka ba sau daya ba ba sau biyu ba ka tsaya ka fuskanci matarka kuyi mgn ta fahimta Amma kayita botsarwa kana Dora mata laifi yanzu wa gari ya waya?" Nan fa Omar ya gyada Kai hankalin sa na sake tashi zumbur ya Mike yace, "Bari dai naje na fada mata bayin Kaina ba....." "Nuna min shi yanzun Nan naci kwal ubansa" Inna fure ta banko kofar parlon tana kumfar baki, mikewa dukansu Omar da Sadeeq din sukayi, Meera na gefen Inna fure tana Jan zuciya, Asma'u na kokarin Hana Inna furen fadan da take, "cikin ku waye gantalallen Nan Omar?" Kallon kallo sukayi da Sadeeq kafin a hankali suka duka har kasa Suna fadin, "Ina wuni baaba" "da ban wuni ba zaku ganni? Nace da ban wuni ba zaku ganni?" Shiru sukayi Suna dukar dakai, "Toh tunda Kun kasa fitar da waye umara a ciki nasan dai dole cikin dayan biyun, Dan Haka ku saurara dakyau Kai Omar tun kafin Raina ya Gama baci ka tattara naka ya naka da duk wani komatsan ka kabar Mana gida" saurin kallon ta sukai a tare Inna fure Tace, "eh na fada, kaje can ka nemi daidai Kai Amma ba Wannan Ameeran ba" Sadeeq ne yace, "kiyi hakuri baaba sulhu mukazo" "Toh naji me Ido a tsakar ka" Inna fure ta furta hakan tana Kama qugu, hakan yasa Sadeeq ya sunkuyar da kansa da sauri, Amina ce Tace, "Dan Allah Inna fure ki daina musu fada baki ne fah" "ke dallah ja can an Gaya Miki ko wanne bakone Dan arziki?" Tsuke bakinta Asma'un tayi Inna fure ta koma kan su Omar da gaba1 suka sake dulmiya cikin wani tashin hankalin Tace, "Wai ko an sassakaku da icce ne Naga bakwa motsi?" Tashi sukayi a sanyaye Suna jawo traveling bag dinsu Su Alhaji Kabir suka shigo gidan, tun da suka hango Inna fure suka taho da saurin su daidai lkcn su Omar din sun fito, Alhji Kabir ne yace, "lpy kuka fito bamu Gama mgn ba?" Inna fure Tace, "oh wato kune Nan kuka sauke su?" Alhji Kabir yace, "mijin Ameera ne fa da abokin sa" tafa hannu Inna fure tayi Tace, "Amma baka kyautawa yarinyar Nan ba kabiru" kallon mmki suka bita dashi Tace, "har shi umaran za'a kirashi da miji? Kasan kuwa lbrn aurensa da Ameeran kuwa? Ko Dan kwali fa be siya Mata ba bare wani Abu da ake Kira lefe" dafe goshinsa Alhji Kabir yyi Yana matsowa gun Inna fure yace, "haba Inna, habaa yanzu Akan lefen kike ta Wannan fadan?" Inna fure Tace, "Toh lefi nayi? Ka dubi yarinyar Nan ka gani.." ta nuna Meera dake matse kwalla a gefe Tace, "Gata Nan a bushe a kekashe Kai d gani horon yunwa yai mata" rintse idonsa Omar yyi gaba1 yanajin kansa Yana juyawa Kamar ya dare, Alhji Kabir kuwa yace, "duk Wannan be taso ba Inna yanzu dai kiyi hakuri zuwa gobe sai asan yadda za'a bullowa lamarin" Inna fure Tace, "Toh har sai ankai gobe? Ai karshen lamari yyi nesa da jikata ehe" dad ne ya matso a hankali yace, "kiyi hakuri Inna Kamar akwai Rashin fahimta tsakanin su" kwafa Inna tayi Dan tana kunyar dad din Dan Haka Tace, "shikenan Amma dai su San inda zasu kwana badai gidan Nan ba" Alhji Kabir zaiyi mgn kenan ta daga Masa hannu Alamar ta Gama mgn, kallon Meera tayi Tace, "daina zubar da hawayen ki a banza da gata dai Allah ne ya baki" ta Fadi hakan tana Jan hannun ta su tafi, goge kwallar data gangaro mata tayi kafin ta Dan dago a sace tana kallon Omar daya zuba mata Ido fuskar sa cike da dunbin damuwa, saurin kawar da idon nata tayi tabi Bayan Inna fure batare data sake waiwayen su ba, Alhji Kabir ne ya matso inda suke yace, "kuyi hakuri kunji" Dan murmushi sukai Masa Sadeeq yace, "Wlh ba komai Abba Bari muje gobe Insha Allah saimu dawo" Alhji Kabir yace, "naso ace anan kuka kwana sai ayi mgn ta fahimta a nutse" yanzu Kam Omar ne yyi mgn da fadin, "ba damuwa Tomorrow morning Insha Allah zamu dawo" Ba Haka Alhji Kabir Yaso ba Toh Amma ya ya'iya? Sallama suka ma Dad dake gefensu kafin suka wuce, Suna fita kuwa sunsha kwana kenan Ahmad Kuma ya shigo gidan sunyi sabani kenan.
Suna tafe ba Wanda yake mgn a cikinsu kowa na tunani a ransa especially Omar da gaba1 baya cikin nutsuwar sa ji yake kamar yabar wani bangare ne acan gidan, Suna fitowa bakin titi suka tsari abin hawan dazai kaisu hotel. Zama Omar yyi a bakin gado bayan ya fito Wanka shiru yyi kawai ya zurfafa a tunani, Sadeeq dake Kan sofa ma shirun yyi gaba1 tausayin frnd din nasa yake dukda Yana ganin lefin sa da ace tun wuri yabi Abinda yace da duk Haka Bata faruba, Toh Amma zaiyi kokari da kansa ya tmbyi Meera meyasa tayiwa frnd din nasa sharrin fyade a kotu? Wanda ya jawo zubewar mutuncinsa da Kuma karatun sa??, A bangaren Omar kuwa Dan kishingida yyi ransa duk a dagule besan Taya zai fassarawa Meera cewar shifa tun fil'izal ya kamu da matukar kaunar ta b, ya Dade da begenta a cikin ransa, idan akwai Wanda yake kauna Bayan iyayensa Toh kuwa itace, be gane hakan a kansa ba Saida aski yazo gaban goshi, Yanason structure dinta Toh Amma ai kauna da soyayya ba karya bane dole akwai shauki Akan Abinda kkeso, juyi yyi akan gadon sbd yadda yakejin Meera a cikin Fadar zuciyar sa sai yanzu ya fahimci ashe ya Dade Yana dakon soyayyar ta be sani ba girman Kai ya Hana shi gane hakan, dake wutar dakin ganin a kashe take hakan yasa Sadeeq yyi tunanin bcci yake Musamman da yyi lamo kamar me bccin, Sadeeq ma bccin ne ya sace Shi, shikuwa Omar kusan kwana yyi Yana sincewa da warwarewa.
Acan gidansu Meera kuwa Suna parlon mamy Inna fure nata surfa fada Ahmad ya shigo, mmki ne kwarai ya Kama shi yanzu Nan fa yadan fita waje Toh meya faru Haka yaga kowa fuska kadaran kadahan? Gyaran murya yyi Dan ya lura sallamar da yyi ba'a jishi ba, Inna fure ce ta waigo tace, "yauwa gara da Allah ya kawo ka Ahmad muje yanzun Nan ka maida mu gida" Ahmad yace, "gida Kuma Inna?" Inna fure Tace, "eh Haka nace ko anan zan kwana?" Kallon Mamy data sunkuyar da kanta yyi ya waiga ya hango Asma'u a rakube fuskarta na nuna Alamar damuwa kafin ya dubi Inna fure yace, "wani Abu ne ya faru?" Cikin fada2 Inna fure Tace, "Toh Menene ma be faru ba Ahmad? Wai yaron Nan umara Dan jaraba har Adamawa ya biyo Ameera bayan duk wulakancin da yai mata" a firgice Ahmad yace, "Inna waye Kuma Umara? Meye hadinta dashi? Meyasa ya biyota?" Tsaki Inna fure taja Tace, "idan Ina tuna matsayin sa Yana bani takaici" kirjin Ahmad ne ya buga da karfi Yana duban Ameera da kanta ke bisa cinyar Inna fure tana goge hawayen da suka ki tafiya yace, "Dan Allah Inna ki sanar Dani kin sani a duhu" tabe baki Inna tayi Tace, "Wai shi Nan mijinta ya kwaso kafafun sa Wai zai tafi da ita Kai wasu mutanen ma basuda kunya Sam" ko kadan Ahmad be fahimci duk sauran maganganun da Inna take ba sai kalmar "Wai shi Nan mijinta" ita take ta Masa yawo akai hakan ya jefashi cikin matukar tashin hankali, dakyar ya iya furta, "Inna dama Tanada aure?" Inna fure Tace, "kwarai kuwa Amma dab muke damu since Wannan aure Dan bamu gaji wulakanci ba" ko kadan yanzun ma be sake fahimtar sauran bayanan nata ba sai amsar ke Masa shawagi a Kwakwalwa "kwarai kuwa" tsam ya Mike beyi mata mgn ba yyi hanyar fita, Inna fure Tace, "Kai da nace kazo ka maida mu gida?" Ko sake waiwayen ta beyi ba yyi gaba da sauri jikinsa na rawa. Zaton Inna wani uzuri ne ya Kama shi saidai har wajen 10pm ba Ahmad ba lbrinsa idan anje part dinsa a kulle wayarsa a kashe hakan yasa badan taso ba ta kwana a gidan nasu, Ameera na dakin Asma'u tayi lamo tunanin duniya duk ya isheta, Asma'u tuni tayi bcci hakan yasa take ta tunanin Abinda ya faru batasan meyasa takejin Rashin Dadi a ranta ba saidai wata zuciyar tana Bata kwarin gwiwar gwara data fada Masa hakan domin ta fitar Abinda ke ranta, cije lips dinta tayi tana tuno yadda Inna fure ta kora su a wannan lkcn bazata banbance me taji a ranta ba Sam saidai tana ganin hakan shi ya dace dasu Abinda ya shuka shi yake girba, da Wannan tunanin nata bcci yyi awon gaba da ita. Washe garin ranar ma da wuri Omar da Sadeeq suka shirya har sunyi waya dasu Mummy ma sun sanar mata Abinda ake ciki saidai Suna nuna musu kamar cewa komai normal ne shiyasa suka gamsu kwarai, Suna hanyar su ta zuwa gidan Alhji Kabir Sadeeq ya dubi Omar daya zurfafa a tunani yadan zungure shi hakan yasa shi Juyowa Yana kallon sa, Dan murmushi ya Masa yace, "kana ganin zata saurare mu yau?" Sauke nannauyan ajiyar zuciya Omar yyi kafin yace, "ko Bata saurare mu ba bazan Yi kasa a gwiwa ba Sadeeq, nasan nayi wasa da damata amma yanzu Kam bazan yadda Meera tayi nesa Dani ba duk rintsi Ina Nan Kuma Abinda matar Nan ta fada gskyne inada lefi matuka Dan ko kyalle ban taba siyawa Meera ba bare nasan meye damuwar ta" Dan Jan Numfashi Sadeeq yyi kafin yace, "matsalar shine ka dauki abin da zafi sosai, ka yanke hukunci cikin fushi shiyasa duk Abubuwan ya kwabe maka" shafa lallausan gashin sa da yaji gyara yyi Yana lumshe Ido kuskure Kam an riga an yishi saidai kawai a fuskanci gaba, me taxi dinsu ne yyi parking Nan Sadeeq ya biya shi suka fito, Suna zuwa bakin gate din aka bude musu domin Alhji Kabir ya shaida musu idan sun dawo kawai a barsu su shiga, shigarsu gidan kuwa yyi daidai da fitowar Alhji Kabir Yana Amsa waya, hango su da yyi ne ya musu alama su matso, matsawa sukayi shi Kuma Yana kokarin yanke wayar da yake, Bayan sun Isa wajensa ne suka duka har kasa Suna diban gaisuwa, Alhji Kabir yace, "yanzun Nan nake mgnr ku nace jiya bamuyi exchanging numbers ba" Sadeeq yace, "hakane shiyasa ma mukayi sauri kafin ku fita" Alhji Kabir yace, "Shikenan ku biyo mu muje" Nan sukabi bayansa Yana gaba. Ahmad dake leke ta window ne ya zame a hankali zuciyar sa na harbawa da sauri2, jiya kusan kwana yyi Yana juyi Sam ya kasa yadda da Wai Ameera Tanada aure, yarinyar data sace Masa zuciya tun a karon farko daya ganta gsky batayi Masa Kama dame aure ba Sam, ya Dade Yana wannan tunanin Yana sane ya kulle parlon sa hade da kashe wutar dakinsa jiya kawai Dan kada a dameshi, yanzun ma damuwar ce ta sashi tsayuwa gaban window Yana leke tunda ya hango su Omar kirjinsa ya buga da karfi especially daya gane Omar din lkcn dayake Kiran Meera jiya, rintse idonsa yyi ya koma bakin gado ya zauna hade da dafe kansa. Zamansu keda wuya aka fara kawo musu abin Kari, Alhji Kabir ya dubesu bayan an gama aje musu komai yace, "kuyi breakfast zanje na shirya kafin muzo ayi mgn" gyada Masa Kai sukayi shikuma ya fice waje, Yana fita kuwa Omar ya maida bayansa Yana lumshe Ido, zamowa Sadeeq yyi ya hada tea cup biyu ya dubi Omar da idonsa ke rufe yace, "ya kamata ka rage Wannan damuwar Omar kasan Abinda hakan ke haifarwa ga lpyr mutum" bude idonsa Omar yyi yace, "sadeeq kenan Kaima kasan a tsakankanin kwanakin Nan Ina haduwa da Abubuwane kala2 da farko Rashin sanin Asalina, ga Kuma bacewar Meera ya kke tunanin zan dau lamarin? Na tabbata da wani ne Wlh sai zuciyar sa ta buga sbd dawanne zaiji? Zafi bisa zafi lkci guda?" Sauke numfashi Sadeeq yyi sai yanzu ya lura Ashe har wata 'yar rama Omar din yyi lalle abun ba sauki danma omar din jarumi ne ya iya dauke duk wannan kaddarar data Fado Masa lokaci guda, cikin matukar tausayin sa yace, "Kayi hakuri komai zai zama normal Insha Allah" Dan guntun murmushi yyi kafin yace, "Haka nake fata" Mika Masa cup din yyi yace, "karbi ko kadan ne kasha tunda kaki Bari muyi breakfast acan" karba Omar din yyi ya fara Sha a hankali, ko Rabin cup din beyi ba yaji tea din ya gundure shi hakan yasa shi ajiyewa, shima Sadeeq din be wani Sha sosai ba ya aje Dan shimafa kusan acikin damuwar yake, Suna zaune Haka dad da Alhji Kabir suka shigo, gaishe da dad sukayi har kasa ya Amsa musu da sakin fuska hakan yasa Sukaji Dadi matuka, zaman su dad keda wuya Inna fure d Meera suka shigo, Dagowa Omar yyi da sauri Yana karewa Meera kallo yadda take ta dukar da kanta tana rabewa Bayan Inna fure, ita kuwa Inna fure fuskar Tace a hade dakyar ma su dad suka lallabata tazo akan kawai anaso aji ta bakin yaran kowa yasan Matsayin sa, zama tayi su Omar suka sake zamowa har kasa Suna kwasar gaisuwa kamar bazata Amsa musu ba sai Kuma ta juyo ta Amsa gaisuwar tasu, zamansu kawai sukai a kasa Basu koma kan kujerar ba, Alhji Kabir yace, "toh madallah, dama Abinda yasa nace kowa yazo Nan shine inaso naji dalilin dayasa shi Omar din ya nemi auren Ameera Alhalin baya sonta" shiru Omar yyi Yana dukar da kansa Sam bayason yaji ance baya sonta, Sadeeq ne yyi gyaran murya kafin yace, "idan ban Shiga tsakani ba ko za'a bani Wannan damar na Amsa tmbyr da aka Masa?" Alhji Kabir yace, "eh Babu damuwa ai Amsa mukeso" Sadeeq yace, "Nagode" Nan ya gyara zaman sa yace, "harga Allah a farkon auren da frnd Dina yyi da Ameera ba komai bane a ciki Banda daukar fansa" "fansa??" Duka suka Furta hakan da mmki, shi kuwa Omar kansa na kasa be dago ba, Sadeeq yace, "kwarai kuwa, dalilin Wannan fansar kuwa shine...." Tiryan-tiryan ya fara Basu lbrn yadda abubuwa suka faru tun daga lkcn da Omar yazo ceton Meera da Sageer yaso Yi mata fyade da Kuma son kwatar mata 'yan dayaso Yi a kotu....karshe ya karkare mgnr da fadin..."a maimakon Ameera ta bada shaidar gsky ta Fadi Wanda yaso rusa mata mutuncin ta shine ta maida mgnr akan Omar inda ya jawo Masa zubewar mutuncinsa a idon jama'a dama dukkan 'yan skul dinmu, Cikakken Likita ne shi me Jiran license dinsa a satin zamu Fara zana final exam dinmu Amma sanadiyar shaidar da Meera ta bayar hakan ya jawo Kora daga faculty dinmu shima duk a cikin plan din Sageer ne a takaice dai komai ya lalace game da Omar duk a sanadin furucin Meera shiyasa yyi auren fansa a kanta a ganinsa hakan shi zai rage Masa radadin Abinda tayi Masa....." shiru parlon ya dauka har Ahmad dake jikin window a labe Saida ya girgiza da Wannan lbrin, Inna fure kuwa Kamar wacce ruwa ya cinye ta Tama kasa Dagowa ta kalli Omar din, dad Kam kunyace ta Kama shi kwarai Haka zalika Alhji Kabir duk sunyi tsumu2, Meera kuwa a hankali ta rabe can gefen kujera jikinta na Bari duk Kuma Omar na kallon ta ta Wutsiyar Ido shima kansa a duke, gwauron Numfashi Alhji Kabir Yaja kafin ya dubi bangaren Ameera yace, "duk Abinda ya fada hakane?" A tsorace Meera Tace, "eh Abba" _Hasbunallahi wani'imal wakil_ Suka Furta hakan a ransu shikenan Kuma me zasu ce da Omar? Cikin fada dad yaso Yi mata mgn Alhji Kabir ya dakatar dashi, kafin a kunyace yace, "Omar shine dalilin aurenka da Meera?" Omar ya girgiza Kai be dago ba, Numfashi Alhji Kabir Yaja toh duk idea ta kwance Meera ai ta kunce musu zani a kasuwa, saidai a hankali ya dubi meeran da jikinta keta rawa Yana Dan kausasa muryar sa yace, "Ameera mutumin dayaso kwatar Miki 'yancin ki irin sakayyar da Zaki Masa kenan?" Girgiza Kai Meera tayi hawaye na cika mata Ido, a tsawace dad yace, "Amma meyasa Kika bada Wannan shaidar?" A rude Meera ta fashe da kuka hade da fadin, "kashe shi zaiyi dad, Wlh kashe shi zasuyi da idona Naga Bindigar" ta karasa mgnr hade da kifa kanta jikin hannun kujera dama a kasan carpet take, wani shirun ne ya sake game parlon yyinda Dr. Omar ya dago a firgice Yana binta da kallo, a nutse Alhji Kabir yace, "bamu gane kashe shi zasuyi ba, su waye? ki Mana bayanin yadda zamu fahimta." Bakin Meera na rawa Tace, "Sa...Sageer da su Anty shafa" Nan ta fara Basu lbrn yadda suka tsoratar da ita Akan matukar Bata bada Wannan shaidar ba saisun kashe shi,...ta karkare zancen da fadin, "ni Kuma Banda wata idea dazan ceci ya Omar daga hannu azzaluman Nan, Banda number sa Kuma lkcn da muka hadu kafin a Shiga kotu idan zai tuna Saida nace Masa inada mgn ya dakatar Dani da fadin dole sai an fito daga shari'a kafin nace komai, be Barni nayi mgn ba shiyasa tunani na ya sake kwancewa a cikin Kotun ma Saida na hango Bindigar a satin bayan Omar mutumin daya zauna a bayansa dauke yake da ita hakan ya Tabbatar min d lalle zasu iya Abinda sukace, bani da wani zabi ne domin tseratar da Rayuwar sa na zabi kare shi ta Wannan shedar bansan Abinda zai juye ba kenan w....l...h...." Ta Ida mgnr a rarrabe sbd yadda kuka yaci karfin ta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.