Best Hausa Novels

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt

Chapter 74 of 85

I'm sorry pls nasan kunata jira tun safe wani Abu yasani kawowa har Wannan lkcn domin typing nake Ina tashi a Haka dakyar na samu na hada wannan😬.

*200 kacal ya Isa ki samu cmplt littafin Nan ta hanyar turo da ita ta Wannan account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻*
8/16/20, 9:12 PM - Ummi Tandama: *********************
Ta Rasa meyasa takejin jikinta a mace saidai tana ganin kamar bccin data fara a jirgi ne be isheta ba shiyasa duk ta jita Kamar wacce Bata da laka, ganin hankalin ta baya garesu yasa shi Ahmad din fasa Yi mata mgnr dayaso Yi yaci gaba da Hira da dad har suka karasa gaban gate din gidan Inna fure, suna zuwa gateman ya bude musu Ahmad ya shige dakan motar, Meera data bude Ido sosai tana ganin yanayin garin Adamawa itama ta bude motar ta fito, karewa compound din gidan kallo take Ahmad yace, "muje Ameera" kallon sa tayi ta girgiza Kai batace komai ba, Nan suka shige cikin gidan suna shiga kuwa Inna fure na shigowa parlon da murnar ta ta Isa gaban Meera ta rungume ta Fadi take, "oyoyo Ameera mutanen kano barkanku da zuwa" murmushi Ameera tayi itama ta rungume ta tanajin wani irin Sanyi a ranta Wai yau itace a wajen Dangin Ummanta, dad ma fuskar sa cike da murmushi Yana kallon su Inna fure ta juyo kansa tace, "bakano sannun ku da zuwa" 'yar dariya dad yyi Yana zama kan kujera yace, "muna godiya Inna fure, da fatan mun sameku lpy" Inna fure na zama tare da Meera Tace, "lpy Lao Alhamdulillah ya ka baro mutanen naka" Dan murmushi Dad Yyi bece komai ba saidai ya tmbyi Alhji Kabir Tace,"dazun Nan ya fita yanataso yaga 'yar tashi aka kirashi Amma bada dadewa ba zaizo" dad yace, "Allah sarki" Ahmad ne ya tsoma baki da fadin, "inna Wai dama kanawa na halin Fulani?" Inna tace, "Toh aku wani Abu ka gani?" Ta Fadi hakan tana dariya, shima 'yar dariyar yyi Yana sosa keya yace, "ai Naga bakuwar Tamu Kamar bafulatana Sam Taki mgn sosai" Dagowa Meera tayi da mmki tana kallon sa, Inna fure Tace, "me kkeci na baka na zuba? daga haduwar farko sai Ayita zuba Kamar kanya" dariya suka sa har Ameera na Dan dukar da kanta, masu yiwa Inna fure hidima ne suka fara sauke kayan abin motsa baki gabansu Meera fitarsu keda wuya kuwa sukaji sallamar Alhji Kabir, wajen dad ya nufa da farinciki suka rungume juna suna musabaha, Dad yace, "soja marmari daga nesa" Alhji Kabir yyi murmushi yace, "engineer ka buya" Nan shima Alhji Kabir ya zauna Meera ta zamo kasan kujera a kunyace ta fara gaishe shi, Alhji Kabir yace, "matso Nan daughter ai kinzo gida" Meera dai duk badan ta sake ba ta Isa gareshi tana me dukawa da farinciki ya dafa hannun sa a kanta Yana fadin, "sannu da zuwa daughter Allah yyi maki Albarka ya jikan Aminatu" kowa na wajen amsawa yyi da Ameen Alhji Kabir yace, "ikon Allah kaga Kama sak Kamar Amina" Inna fure Tace, "Wlh kuwa ai Haka Allah ke ikonsa" Shidai Ahmad tun dazu binta yake da kallo kamar ya samu TV, Kiran Sallah ne ya sa Alhji da dad suka Mike suna yiwa Inna fure sallama zasu masallaci, bayan fitarsu ne Ahmad ya matso inda su Inna fure suke yace, "Meera tashi muje muma" Dagowa tayi da mmki tana kallon sa, Inna fure Tace, "Ina zaku?" Ahmad yace, "gida Mana su gaisa" Inna fure ta Kama haba Tace, "Ahmad daga zuwan nata ko hutawa batayi ba saita fita? Ina lefin zuwa Anjima ko gobe a gajiye ma take ya makata tayi Wanka ta huta* Ahmad yace, "ke kuwa Inna Wannan ai duk ba matsala bace zatayi idan taje gida nasan ma kila Asma'u tana hanyar dawowa daga islamiyya saita zauna dakinta" Inna fure Tace, "Toh naki wayon naka Ameera tashi na kaiki inda Zaki huta" ta karasa mgnr tana kamo hannun ta, zube hannayen sa a Aljihu Ahmad yyi Yana kare mata kallo kafin yace, "Shikenan Inna Ina Nan dawowa Anjima" Inna Tace, "saidai hakan" Nan ya fice ya Basu waje, suna Shiga daki Inna ta dubi Meera da take komai a sanyaye Tace, "Ameera akwai wani Abinda ke damunki ne?" Adan firgice ta kalli innar tana raba Ido Tace, "ba komai" tayi mgnr tana washe baki, Inna tayi shiru kafin Tace, "Toh shikenan Shiga kiyi wankan ko zakiji dadin jikin naki* Meera ta gyada kanta da murmushi kafin ta wuce toilet, tana Shiga toilet din kuwa ta hada ruwan dumi, a hankali ta cire kayanta kafin ta Shiga bahon wankan, lumshe ido tayi sannu a hankali fuskar Dr. Omar ta fara bayyana a gareta, bude idon tayi da sauri tana Dan Jan tsaki a hankali, da Haka ta Gama wankan nata ta fito trolley dinta da aka kawo Mata dakin ta bude ta samo wata rigar Atamfa riga da skirt ta saka dinkin ba karamin fito da shape dinta yyi ba har tana Kara ganin kanta a madubi, gashinta take gyarawa Yana warewa sbd tsantsi dakyar dai ta hade shi waje guda kafin ta kawo dankwali ta daura, tana cikin fesa turare Inna fure ta shigo da fara'ar ta tace, "Ashe har kin shirya ma" Meera ta juyo da murmushi sosai tana dubanta tace, "eh Inna" yanzun Kam taji kwarin jikinta sbd Shiga ruwan zafin da tayi, Inna Tace, "yauwa idan kinyi Salla ki sakko parlo Ina jiranki" Meera Tace, "Toh Inna" anan Inna fure ta fice ta barta a wajen, itama hijab tasa tayi Sallah bayan ta idar ne ta nufi parlo inda Inna fure take. Juya plate din gabansa yake tun dazu ya kasa Kai Koda spoon daya a bakinsa sbd tunani, Mummy da tun dazu take hankalce dashi Tace, "Ameer" Kiran nasa da Ameer ya jawo hankalin su daddy da aketa maida zance kowa na Fadar Abinda ke ransa Dan dazu dakyar suka samu nasarar kwacewa daga hannun jama'a anata tururuwar son Hira dasu yanzun ma dai akwai wasu jama'ar a kofar gida suna jiran fitowar wani ayi Hira dashi sunki fita Dan daddy Sam beso Wannan tonon sililin ba Amma daga baya daya fahimci Sageer ne yaso yiwa Omar Ramin mugunta sai abin ya daina bashi haushi sosai Dan shi daya Gina Ramin muguntar shiya rufta, kallon Omar kowa yake shi Kuma Yana kallon Mummy data kirashi, Dan murmushi kadan tayi Tace, "Kamar bakajin dadin zaman Nan kaje dakina zan kawo maka food din" Dadi sosai Omar yaji da Abinda mummy Tace Dan gaba1 a takure yake dama saidai Toh Ina zai nufa shi da besan Kan gidan ba? Kafin yyi mgn ma mummy ta dubi Safna Tace, "tashi ki rakashi" Safna ta Mike da sauri Tace, "Toh Mummy" Nan ta zaga bangaren da Omar yake, tashi yyi a hankali ya dubi daddy yaga shi yake kallo da murmushi kallon Abba dayaketa washe baki yyi kafin yabi bayan Safna data riko hannun sa, Sadeeq tun a hospital ya wuce gidansu Meera Dan sake binciko Address a bisa rikon da Omar yyi Masa yaso ma yaje da kansa saidai ya lura bazasu barshi ya matsa ko'ina ba, suna tafe Safna na fadin, "ai ya Ameer kana Gama hutawa ma xan jaka mu zaga duka gidan Nan kaga yadda yake, zansa ma daddy ya Mana visa mubar kasar Nan dole kaje hutu kasar waje don ma ka manta da duk wani tension daya taba faruwa dakai" surutu take tayi Sam be Amsa Mata Koda daya daga ciki ba hakan yasa ta juyo tana kallon sa sai taga shi tafiya ma yake kansa a kasa da alama hankalin sa Yana wani wajen, sakin baki tayi tana mmkin Toh ko meke damunsa Kuma? Kamata yyi ace yafi kowa farinciki ai, da Haka suka Shiga dakin Mummy dayaji kayan Alatu Kai kace dakin wata budurwar ce sai daukar Ido yake ga kamshi me kwantar da zuciya, Shi kansa Dr. Omar besan lkcn daya lumshe ido ba, Zama yyi Kan kujerar daya gani doguwa daga can gefe Yana karewa dakin kallo, Safna Tace, "sai Anjima" gyada mata Kai yyi ita Kuma taja Masa kofa, a hanya suka hadu da Mummy rike da basket ta tahowa da Omar abincin sa, Yana kokarin kunna wayarsa Mummy tayi knocking amsawa yyi Mummy ta turo kofar a hankali hade da sallama, tashi Omar yyi da sauri ya Isa gabanta Yana amsar basket din hannun nata zuba Masa ido tayi cikin matukar kaunar gudan jinin nata, karon farko kenan data Amsa sunan uwa ga da namiji Dan batasan Wannan karramawar ba tun tasowar Sageer be taba karbar Abu daga gareta da nufin tausayawa ko karramawa ba, tura kofar tayi bayan ya karbi kayan itama ta iso inda yake tana me zama daga kasan carpet, ganin Haka shima Omar ya zamo daga kujerar ya zauna kansa a sunkuye duk kunyar Mummyn yake, Mummy ta Kare Masa kallo tsaff kafin Tace, "it seems like kana cikin damuwa Koh?" Da mmki ya dago da kansa Yana dubanta cikin wata irin soyayya ta 'Da da mahaifiya karon farko kenan a Rayuwar sa dayaga an damu da damuwar shi Abinda ya Dade Yanason gani kenan daga Saratu Ashe ba ba uwarsa bace, Dan murmushi yyi cikin son basarwa yace, "a'a Mummy ba Abinda ke damuna kawai Ina tunanin yadda Al'amuran duniya suke sauyawa ne lkci zuwa lkci" itama murmushin tayi sosai har hakwaran ta na bayyana Tace, "Ameer" amsawa yyi Yana dubanta, a hankali Tace, "I'm your mother right??" Gyada Kai Omar yyi yana murmushi Mummy Tace, "dukda baka taso akan Wannan hannayen nawa ba.." ta damke duka hannuwan nata tana kallo cikin Kuna da zafin Abinda Saratu ta mata kafin taci gaba da fadin, "zan iya fahimtar duk halin da kke ciki, damuwa, ko akasin haka" shiru Dr. Omar yyi Yana Sunkuyar da kansa kasa yaji tace, "What's happening between you and meera??" A razane Omar ya dago Yana duban Mummy bakinsa na rawa yace, "Mummy...Wani yace Miki wani Abu ne? Mummy Tace, "No kawai Ina hasashen something happens btw you and her" zuciyar Dr. Omar ce ta fara harbawa da sauri2 dan beyi zaton hasashen da take Masa yakai Haka ba shiyasa ma ya Rasa Abinda zai ce Mata Dan ta kamashi dumu2 akan Abinda yake boye mata, katse Masa Shirun tayi da fadin, "inaso ka kwantar da hankalin ka Ameee, ka manta da duk Abinda ya faru a baya ka maida yanzu Kamar mun dade da sanin juna a Matsayin Uwa da 'Danta ka fadamin gsky idan ka Fadi akasin hakan ma kasa a ranka zan gane" cikin tsoro Dr. Ya fara ja baya Dan gaba1 ya dauka ko Mummy nada Aljanu ne yaji Tace, "Bayan Haka ma nidin da ka gani psychologist ce
Dukda ba wani aiki nake ba saidai naji takaicin karatuna da beyi aiki akan Saratu ba coz na yarda da ita hundred percent sam-sam ban taba maida kula ga yanayin reaction dinta ba duk Wanda na yadda dashi bana negative thinking a kansa but daga lkcn Dana ji Abinda ya faru brain Dina ta Fara aiki akan kowa ma so ka gayamin mene ya faru" tsakanin Kai da Meera? Ya bude baki zaiyi mgn kenan wayarsa tahau ringing kallon wayar yyi yaga Sadeeq ne ke kiransa kasa dagawa yyi sbd Suna mgn da Mummy ganin Haka yasa Tace, "ba frnd dinnan naka bane?" Gyada Kai yyi Tace, "ka dauka Mana" Kamar Yana jira kuwa ya Kara a kunne ko Jiran Sadeeq beyi ba ya fara mgn Fadi yake yanzu me ake ciki Sadeeq? An samo Address din kuwa?" Duk yyi mgnr da sauri2 Yana fatan ace an dace, cikin sanyin murya Sadeeq yace, "sorry frnd Wlh har yanzu Wai be tuna ba har dakinsa na Shiga tayashi bincike Babu wata paper Babu Alamar ta" tsaki Omar Yaja cikin tsantsar takaici da alama ya fara mancewa Yana gaban Mummy Fadi yake, "Wannan wanne irin rikataccen mutum ne Wai? Dan Allah Sadeeq ka sake cajemin shi" Sadeeq yace, "don't worry duk yadda ake ciki zamuyi mgn" $Okay Thanks" Omar ya Fadi hakan Yana Jan tsaki, Mummy da batasan Kan zancen nasu ba Amma still ta tare shi da fadin, "Wai har yanzu Paper ce ba'a gani ba?" Tayi mgnr cikin damuwa tanason ya saki baki ya fada Mata Abinda suke boyewa, cikin damuwar shima yace, "Wlh kuwa Abu tun safe Kuma yauyau dinnan fa aka bashi takardar Amma harya manta" Mummy Tace, "ikon Allah kamata yyi ya caje Koda jikinsa ne Koh Kuma ka Kira Wanda ya bashi takardar" Cije lips yyi yace, "da ace zan samu number dad din Ameeran ma da sauki to ni Banda ita Mummy gashi sun tafi Adamawa tun safe na kasa sukuni Wlh." Shiru Mummy tayi tana kallon sa at last taji Abinda ke damunsa wato dai Ameera Bata Nan, shirun nata ne ya fargar dashi sakin bakin nasa da yyi tsabar ya Shiga tension ya Masa yawa da sauri yace, "am....Mummy dama Ameeran taje ganin gida ne" Jan zuciya Mummy tayi Tace, "taje ganin gida shine ka kasa sukuni?" Sunkuyar da kansa yyi kirjinsa na harbawa, mikewa Mummy tayi Tace, "kaci food dinka sosai ka koshi yanzun Nan zance nayi mgn da Daddyn ku" ta karasa mgnr tana ficewa, bin kofar yyi da kallo hankalin sa a tashe shikam yau da Alama littafin kundin kaddarar sa aka bude. Koda Mummy ta fito waje direct wajen daddy ta nufa domin harsun tashi a wajen an raka Abba inda zai zauna dukda ma yaso tafiya suka rikeshi, Yana Shirin Shiga Wanka ta shigo dakin fuskar ta cike da damuwa, rikota yyi Yana shafa bayanta Nan suka zauna gefen gadonsa, a nutse yace meke faruwa Na ganki, "cikin damuwa mu daya kamata ace an hada liyafar farinciki" Mummy ta danyi murmushi kadan kafin Tace, "Ameer ne" gyara zamansa sosai daddy yyi yace, "meya samu Ameer din?" Nan Mummy ta fada Masa komai akan Rashin Ameera, sosai hankalin daddy ya tashi dukda Basu taba ganin Ameerar ba Amma a yanda Abba keta Basu lbrnta yasa Sukaji kaunar yarinyar ta Shiga ransu, Dan Haka yace, "Bari yyi Wanka asan abin yi" Dadine ya Kama Mummy Dan Haka itama tabi bayansa Suka shige toilet. Omar da tunda Mummy ta barshi yake ta faman tunani abincin ma spoon biyu yyi yaji ya cika Masa ciki Dan Haka ya Mike da sauri Yana kwasar key din motar sa yyi waje, Yana fitowa kuwa yyi sa'a Babu kowa a parlon hakan ya bashi damar zare jiki zai gudu yaje can gun Ayuba ya caje shi, Yana dab da fita kuwa yaji an Kira sunan sa, a tsorace ya waiga yaga Ashe Abba ne dake tsaye can kasan wata bishiya, juyawa yyi ya nufi inda yake, Yana zuwa kuwa Abba yace, "Ina zaka ne kketa sauri?" Shiru Omar yyi Dan besan mezai fadawa Abban ba, a bisa mmkin nasa yaji Abba yace, "ta gaji da Halinka ne ta tafi?" A mugun firgice yake bin Abban da kallo, Abba ya danyin murmushi irin na Manya kafin yace, "haba Omar ko kwana daya mutum yyi a gidanku ai Saiya fahimci Rashin jituwar ku bare ni da nayi fiye da wata a gidan" kunyace ta Kama Omar ya Rasa inda zai dura kansa yaji Dadi hannayen sa kurum yasa cikin lallausan gashin sa Yana hargitsa shi, Abba yaci gaba da fadin, "a lkcn daka Zo min da zancen Meera Tace ka Kara aure a Wannan ranar na Kara Tabbatar da Rashin zaman lpyr ku Omar, Babu yadda za'ayi a Wannan zamanin kaji mace tana neman kishiya da kanta saidai ko Bata da lpy" bakin Omar ne ya fara rawa yanaso yyi mgn ya kasa, Dan sauke numfashi Abba yyi kafin yaci gaba da fadin, "lkcn daka roki Sadeeq ya koma gidansu Meera a lkcn nasan bakwa tare" "Kayi hakuri Abba" Omar ya furta hakan ransa a dagule, tabe baki Abba yyi kafin yace, "toh ita salmar tana Ina bakazo da ita ba?" Oh Ya Salam! Question again, Omar ya Fadi hakan a ransa Amma Toh ya zaiyi? Haka dai yyi ta maza ya sanar da Abba ya saketa, "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un..." Abba ya furta hakan a rude Fadi yake, "Omar yaushe ka zama Haka? Wanne irin haline ka tsiro dashi Wanda ni ban sanka dashi ba?? Daga aure Rana daya sai saki???" Lumshe idon sa yyi Yana Sunkuyar da kansa kasa, sosai Abba hankalin sa ya Tashi yace, "kaifa da kanka kaje ka auro musu yarinya meyasa kke nema ka maida mu kananan mutane?" Omar na cije lips dinsa yace, "Kayi hakuri Abba" "Banason ka kasance cikin maza masu auri saki ne Omar, tashi guda Kamar Wanda aka maka baki ba Uwargida ba Amarya??" Still Omar ya Rasa bakin mgn, Jan Numfashi Abba yyi yace, "kaje can gidansu Meeran ka sake jiyo Mana lbrn ta banaso kakai dare baka samota ba" ya karasa mgnr cikin fada2, girgiza kansa yyi cikin ladabi kafin ya juya a hankali ya nufi parking space Yana tada motar sa ya fice a gidan Bayan ya dage glasses dinsa bayaso a ganeshi Dan yasan yanzu Haka hotunan su da labaran su ya Gama game ko'ina, direct gidan su Meera ya nufa. Meera data sauko parlo tana Shirin zama kenan taji Anyi sallama tana juyawa taga wata budurwar wacce Bata wuce tsarar ta bane ta shigo, da murnar ta budurwar Tace, "oyoyo Ameera welcome to Adamawa state" ta Fadi hakan tana rungume Meera, Meera ma rungume ta tayi cikin fara'a sosai tace, "Thanks you very much" sakinta tayi suka zauna tare budurwar Tace, "sunana Asma'u kanwar Ahmad ce ai da tare zamu Zo daukar ku sai Kuma naje islamiyya" Ameera Tace, "Allah sarki Mlm Asma'u ya karatu" Asma'u na murmushi tace, "Alhamdulillah Wai Ina Inna furen ne?" "Gani Nan akwatin radio" Inna fure ta Fadi hakan tana kawo kular abinci inda suke zaune Tace, "Naga alama bakwason zaman wancan kujerun" dariya Asma'u tayi Tace, "haba sai kace ke Inna, mu ai da kwarin mu Koh Ameera?" Ameera na dariya tace, "gaky Kam" Inna tana dariyar itama Tace, "kwaji dashi Banda iyayi meye na tashi sama aci abinci saikace tsuntsaye" Nan suka sa Mata dariya dukansu
Suna cikin cin Abincin kuwa Ahmad ya shigo da tasa sallamar, Inna fure ce ta dubeshi da mmki tace, "Ashe kuwa dgske kke" Ahmad yace, "meya faru?" Inna fure Tace, "gashi kuwa ka dawo banyi zaton hakan ba" 'yar dariya yyi yace, "ke kuwa munada bakuwa guda ai dole na dawo mu gaisa" "ikon Allah gaisuwar ta dazu Bata Kare ba?" Ahmad yace, "kedai Inna akwai tmby Kamar 'yar jarida" Meera ce tasa murmushi hakan yasa shi zuba mata Ido tana dago Ido kuwa taga Yana kallon ta hakan yasa ta fara rage dariyar ta, Asma'u ce Tace, "Ya Ahmad yau Babu kallon kwallon ne?" Hararar ta yyi yace, "ban sani ba" 'yar dariya tayi kawai batace komai ba, hakan yasa yace, "Ameera da fatan dai garin Adamawa kinajin dadinsa?" Dan bushashen murmushi ta Masa tana gyada Kai, Inna fure Tace, "haba ita da garin Ummanta? Ai Allah ya kaimu gobe Dan liti ya zaga damu dangi kowa yaga 'yar Aminatu" Ahmad yace, "haba Inna wanne Dan liti Kuma?" Inna Tace, "toh inada wani driver ne daya wuce shi?" Ahmad yace, "ki fada min lkci da Kaina zan zaga daku" Kama haba Inna tayi Tace, "oh su Ahmad an fara mutunci" dariyace ta kwacewa Asma'u da take ta dannewa tun dazu, Bata Rai Ahmad yyi cikin tsawa yace, "ke wanne Dan iskan kike ma dariya?" Tsuke bakinta Asma'u tayi Bata Kara cewa komai ba hakan yasa Meera tayi murmushi ba komai ya Sata hakan ba sai tunowa da Dr. Omar itama yadda yake mata tsawa Yana Bata Rai. Ayuba na zaune yaga fitowar Omar da sauri cikin mota, mikewa yyi tsaye hankalin sa a tashe yace, "yau na Shiga uku nikam ko kisa nayi karshen zarya kenan..." kafin ya rufe bakinsa kuwa Omar ya karaso inda yake fuskar sa a hade yace, "kaga Paper?" Jikin mlm Ayuba ne ya fara rawa yace, "Dan Allah kayi hakuri Wlh na caje ko'ina Banga komai ba dazu2 Nan ma saida muka Gama birkice ko'ina bamuga takardar Nan ba" Omar na matsowa gabansa yace, "ka duba jikin ka?" Mlm Ayuba yace, "sbd Allah kaikuwa me takarda zatayi a jikina?" Bata Rai sosai Omar yyi yace, "inason yanzun Nan ka caje min duk wata maboya a jikin ka" badan Ayuba ya so ba Haka yasa hannun sa a duka Aljihun jikinsa Yana cajewa, duk fitowa yyi da Aljihun ba komai, idon Omar akansa Yana Shirin maida kudin daya fito dasu ya hango farin Abu da sauri ya dakatar dashi yace, "caje Wannan kudin hannun naka" dawo da hannun sa Ayuba yyi Yana warawa kuwa saiga takardar a ninke salati ya dire cikin murna yace, "Alhamdulillah Wlh itace ai Wannan kudin ya bani da safe kafin su wuce tare dasu na ninke na aje...." Karbe takardar Omar yyi hannun sa na rawa ya warware ta wani irin farinciki ne ya Kama shi besan lkcn daya saki lallausan murmushi ba har hakwaran sa na bayyana, cikin Jin Dadi yace, "na gode mlm Allah ya saka" Mlm Ayuba yace, "ai kuwa Nima na gode Allah Wlh, Wannan Aba tun safe a kanta na kasa samun sukuni" hannu Omar yasa a Aljihun sa Nan ya zaro kudin da besan yawansu ba tsabar farinciki ya damkawa mlm Ayuba yace, "gashi Nan tukwici" Yana Gama fadin Haka ya juya da hanzarin sa, Kallon kudin mlm Ayuba yyi da murna Yana washe baki yace, "Allah sarki Ashe Alheri ke bibiyata tun safe ban sani ba."
Dr. Omar kuwa daga Nan gidansa ya nufa ransa fari tas, Kiran Sadeeq yyi bugu daya ya dauka cikin Jin Dadi yace, "Sadeeq an samu" da murna Sadeeq yace, "dgske?" Omar yace, "yesso Dan Haka ka fara hada kaya zamu Adamawa" mikewa daga zaunen dayake Sadeeq yyi ya tashi tsaye d mmki yace, "Omar kana ganin lkci kuwa?" Omar yace, "Dan Allah ka daina duba lkci I just want to see my wife kawai" "dare fa ya kusa Omar har yaushe mukaje Adamawa bafa Nan da jigawa bane?" Omar yace, "an so? Son samu ma ace Daren yau tare mukayi shi..." "Dan iskaa..." Sadeeq ya katse sa d fadin Hakan Dan yaga kamar ya fara Saba lamba, 'yar dariya Omar yyi yace, "pls kazo Nima gida zan wuce na hada kayana daga Nan muje muyi masu sallama saimu tafi" Sadeeq yace, "Wai yaushe ka zama me naci ne Omar?" "Idan akan sugar babe ne u don't see anything..." "Sugar babe?" Sadeeq maimaita hakan Yana sakin baki kamar Yana kallon sa, "ehnn...watin?" Omar ya Fadi hakan shima, rufe bakin nasa Sadeeq yyi Dan yaga alama Rashin kunya Omar din yakeji Dan Haka yace, "saimun Hadu" "Alright." Omar ya Fadi hakan shima Yana katse wayar, Yana Isa gidansa kuwa da saurin sa ya wuce samansa kayansa ya zuba a traveling bag dinsa ya fito a gurguje, Mlm habu na ganin sa ya Mike da sauri Yana zare Ido yace, "yallabai lpy kuwa Naga kuke ta zari daidai?" Murmushin da be taba ganin ya Masa ba ya sakar Masa yace, "mlm habu abubuwa ne suka faru dayawa a safiyar yau ciki ma harda samun warakar Abba Yana mgn yanzu" cikin matukar murna mlm habu yace, "Allahu Akbar kaji Allah babban sarki, Alhamdulillah Allah sarki Koh can zakane Nima na bika nayi Masa murna?" Dr. Omar yace, "a'a ai baya gida zancen da tsayi gashi Kuma Ina Kan hanya" da mmki mlm habu yace, "wani wajen ka nufa yanzu?" Dr. Omar yace, "eh Insha Allahu Adamawa zan tafi" mlm habu yace, "dare fa ya kusa magriba ta gabato?" Dan murmushi Omar yyi Yana sa hannun sa a Aljihu ya debo kudi masu kauri ya Mika Masa yace, "bansani ba ko zanyi sati ko akasin haka sai yadda Abin dai ya kasance" karba mlm habu yyi da murna sosai yace, "Toh shikenan Allah ya tsare Hanya Allah ya kiyaye" "Ameen Insha Allah zan sanar da Abba sai yazo Koda d safe ne ku gaisa" "Toh madallah a sauka lpy" "Ameen" Omar ya furta hakan kafin ya fice a gidan dama be shigo da motar sa ba Dan Yanason Barinta a gidan daddy Dan Haka Yana fita ya Bata wuta. Suna tsaye a compound sbd Abba ya sanar musu inda omar din ya tafi Dan da farko da suka duba Basu ganshi ba zaton su an sace musu shi ne shiyasa hankalin su ya fara tashi, tun daga gate ya hango su a tsaye mmki ne ya Kama shi hakan yasa be karasa parking space ba ya fito, Hajjaju ce Tace, "Jikana ka samu tashin hankali" isowar sa kenan ya dubeta da 'yar dariyar sa yace, "me nayi d zaisa hankalin ku ya tashi?" Hajjaju Tace, "duk mun laluma lungu da sako na gidan Nan baka Nan sai muke tunanin ko sace min Dan kyakkyawan ango akai" dariyace ta Kama Omar hakan yasa duk suka zuba Masa ido da mugun mmki Dan tunda yazo gidan dazu Basu ganshi cikin fara'a ba sama da yanzu, hakan yasa Abba yace, "an dace?" Da fara'a yace, "eh Abba yanzu ma Shirin tafiya nayi zan jira Sadeeq yazo saimu wuce" kallon mmki suka Kara Yi Masa Daddy yace, "Adamawan Ayau?" Mummy Tace, "ai na dauka Shirin dawowa gida kayi" Sunkuyar da kansa yyi Yana murmushi, Safna tace, "ai kuwa zan bishi Nima inaso muje" Dagowa yyi Yana kallon ta, daddy yyi 'yar dariya yace, "lalle surukar tamu she's special" kunyace ta Kama Omar hakan yasa shi juya kansa Yana wani basarwa, daddy yace, "shikenan Amma sai zuwa gobe" da sauri Omar ya juyo Yana kallon daddy cikin damuwa, daddy yace, "yes yanzu dare yyi Omar gashi yau duk baka zauna ka nutsu ba tunda kaji good news ai yakamata ace kaje ka huta ne idan ta ganta Haka wujiga2 ai saita dauka Dan dambe ka koma" dariyace ta Kama mutanen wajen shikuwa Omar ya juya keya Yana tura baki shifa gsky ba Haka yaso ba Amma Kuma bazai iya yiwa daddy musu ba, Suna tsayen kuwa saiga Sadeeq ya shigo da tasa traveling bag din, Hajjaju tace, "hoo ashe duk kun Gama Shirin ku" Sadeeq Yana dariya yace, "Wlh nace ya Bari da safe Amma duk ya matsa Wai yanzu" daddy yace, "ai zancen ka Haka yake da safen zaku tafi Insha Allahu" "Toh Allah ya nuna Mana safiyar da Alkhairi ni Bari na koma" Sadeeq ya Fadi hakan, Omar ya riko shi Yana fadin, "ba inda zakaje" Mummy Tace, "Sadeeq ai Nan ma gida ne Safna rakasu inda aka Gama gyarawa Ameer dazu" Safna Tace, "Toh" Nan suka bi bayanta tana gabansu yyinda Sadeeq ke yiwa Omar dariya kasa2 so yake su kebe ya Masa Iskanci iya son ransa dama tun safe yake tarashi Akan Meera yadda ya gigicen Nan yasan dole da walakin goro a Miya bazai Bari yasha lami ba Saiya tsokane shi, shi Kuma Omar Banda turo baki ba Abinda Yake, Dan jinsa yake tamkar yyi tsuntsuwa ya ganshi gaban Meera.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.