Best Hausa Novels

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt

Chapter 65 of 85

*MASHA ALLAH, SAI KUMA ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH INSHA ALLAHU ZAMU CI GABA, FATAN ALKHAIRI HAPPY SALLAH IN ADVANCE💰💷💶💶💴💴😜 Ina jiran Naman sallah😋*
8/15/20, 8:06 PM - Ummi Tandama: *YADDA ZAKI BIYA*
Zaki turo da 200 ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 Zaki iya turo da katin MTN ta waccar number👆🏻

*Kuyi hakuri da errors din ciki banyi editing ba👏🏻*

Lkcn da Meera ta dauko kular Abba tana shigowa parlo ta tarad da Dr. Omar zaune Kan kujera Yana latsa wayarsa, Dan Karasawa tayi wajensa a hankali tace Abba Yana dakin shi ne? Saida ya share wasu seconds kafin ya dago Kai ya dubeta Adan kaikaice sannan yace, muje, Yyi mgnr Yana tashi tsaye kafin ya fara tafiya, Bin bayansa Meera tayi tana karewa yanayin tafiyar tasa kallo har suka Isa kofar parlon da Abba yake, daidai zasu Shiga Dr. Omar ya gyara yanayin fuskar sa Yana duban Meera dake bayansa yyi Mata Alamar ta matso, matsowa tayi gefensa tana jiran taji mezai ce mata, Dan kallonta yyi a gefen nasa ya kawar da kansa Yana knocking din parlon Abba hade dayin sallama, Abba dake ciki yyi gyaran murya Alamar su shiga, Buda kofar Dr. Omar yyi Nan suka shiga parlon Abba Yana zaune Kan carpet Yana Jan carbi, dubansu yyi da fara'a yanajin Dadi har cikin ransa, Meera ce ta aje kular hannun ta hade da Dan bowl din da zata zubawa Abba tuwo ta aje tana fadin sannu Abba ya zaman shiru mun barka Kai kadai, tayi mgnr da murmushi, murmushi Abban yyi a ransa Fadi yake Allah sarki hafsatu ai indai zaman shiru ne na Saba da Wannan, Dr. Omar ne yace Abba da fatan hankalin ka ya kwanta da Nan din ko? Yyi mgnr Yana karewa yanayin parlon kallo, 'yar dariya Abba yyi Yana girgiza kansa Alamar eh, Meera na gaban Abba tana dibar Masa tuwo, Dr. Omar na juyowa yyi arba da tuwon samo din da Meera tayi da miyar Kubewa, Da mmki ya zuba mata Ido batare daya dauke ba, Meera na Dagowa kanta taga Ashe ita yake kallo, Dan firgita tayi da kallon nasa har tuwon da ta dauko na neman zubewa, dungurar shi Abba yyi Yana tsare shi da ido, da sauri Dr. Omar ya shafa kansa Yana tattaro fara'a sosai yace Kamar kinsan Abinda Abba yakeso kenan yyi mgnr Yana dauke kansa hade da duban Abban, Abba na murmushi kawai ba mgn, Meera ta sauke ajiyar zuciya ta dauka wani lefin tayi Nan ta tura Masa abincin gabansa sannan ta dauko robar ruwa ta aje Masa, Saida ta Gama jera Masa komai kafin tace Abba zandan fita tayi mgnr da ladabi, girgiza Kai Abba yyi Yana sa mata Albarka a zuciya, anan Meera ta Dan saci kallon Dr. Omar taga bama ita yake kallo ba a hankali Tace sai Anjima tayi mgnr tana ficewa, Koda taje daki ma kayanta ta cire don yin Wanka, bayan ta Gama wankan ne ta shirya ta nutsu kafin ta debo nata abincin taci a daki, lkcn data fito da plate din hannunta a lkcn Dr. Omar ya shigo parlon Ya dawo daga wajen Abba, Meera na ganin shi ta karasa a hankali Tace ban sani ba ko zakaci tuwon na kawo maka? Tayi mgnr kanta a kasa, Ji tayi ya dago Kan nata Yana bin kwayar idonta da kallo yace tuwo? Wazai ci maki tuwon? Yyi mgn cikin tsare gira, matsawa baya Meera tayi Tace kayi hakuri shiyasa na tmby, sake matsawa gabanta yyi yace sbd kinaso nayi katon tumbi irin naki Koh? Da sauri Meera ta dago tana girgiza Kai tace No ni ba nufina kenan ba Kuma dai ni Banda tumbi, tayi mgnr kamar me Shirin kuka, Sake matsowa yyi dab da ita yana kallon saitin cikin ta yace idan ba tumbi bane meye Wannan? Yyi mgnr Yana Fisge mata hijab dinta hade da dage mata rigar daidai saitin cikinta, da sauri Meera tayi kasa tana kokarin rufe jikinta taji ya tokare ta, zubawa shafaffen cikin nata kallo yyi da mugun mmki, Ramin cibiyar ta ya kurawa Ido kamar me nazarin wani Abu, Meera data kasa kaiwa kasa ta jawo rigarta daya dage da sauri ta mayar ta yanda take sai a lkcn Dr. Omar ya dago da sauri Yana sakin ta ya dafe goshin sa Dan tsaki Yaja batare daya sake bi ta kanta ba ya wuce sama da sauri. Bin bayansa tayi da kallo a tsorace tana dafe kirjinta daya fara harbawa da sauri da sauri dago Kan da zatayi kenan daidai lkcn Dr. Omar yadan juyo daga can sama idon su ne ya sarke da juna a tare dukkansu kowa ya janye idonsa da sauri ya wuce daki yyinda Meera itama jikinta na rawa ta wuce kitchen.*****A hankali ya gangara cikin B.U.K din Yana karewa yanayin ta kallo wani Abu na taso Masa a hankali, a Haka harya Isa wajen parking din motoci, Saida ya Gama parking dinsa Dr. Omar ya dauko wayarsa ya latsa Kiran Dr. Sadeeq, Bugu daya Dr. Sadeeq ya dauka hade da fadin yeah ka shigo. Yess Dr. Omar ya Furta hakan a takaice, Okay gani Nan zuwa, Dr. Sadeeq ya Furta hakan Yana yanke wayar, aje wayar hannun sa Dr. Omar yyi Yana me sa hannun sa a baki hade da karewa B.U.K din kallo Yana ganin yadda mata da maza ke harkokin gabansu, Yana zaune shiru Haka ya hango Dr. Sadeeq Yana karasowa, Knocking yyi Masa ya bude Masa gidan gaba ya shiga, zama Dr. Sadeeq yyi yace GM da kansa, yyi mgnr cikin tsokana, Dan cije lips Dr. Omar yyi yace ya ake ciki da Shirin mu? Yyi mgnr Yana duban Dr. Sadeeq, Jan ajiyar zuciya Dr. Sadeeq yyi da murmushi yace yanzu Haka yau za'a manne sunayen su a department sunan sa Yana daya daga cikin Wanda za'ayi musu canjin department ko yabar skul din ya karasa mgnr da murmushi, Girgiza Kai Dr. Omar yyi yace Ina fatan sabon H.O.D dinsu da aka sake yyi Abinda ya dace, Dr. Sageer yace ai karka damu Wannan karon Jan wuya ne Insha Allah bazai bada matsala ba is hardly yaci gaba da zama a department din Kai kaga yawan carryovers dinsa kuwa? Cikin takaici Dr. Omar yace shiyasa nake mmkin wanne irin Kan kifi gareshi 2years back ya kamata ace yyi graduation Amma har yau Yana school sbd tsabar Rashin ciwon Kai, Dr. Sadeeq yace Bari dai muga indai shi ba maloho bane yaji an Masa canjin department ko an cireshi a skul zai magantu Koda yake Yana takama da kudinsa maybe yace zaiyi amfani dasu, Dan murmushin gefen baki Dr. Omar yyi kafin ya hade Rai yace zuwa yanzu zai fahimci kudi ba komai bane domin ba'a ko'ina suke yiwa mutum amfani ba, Dr. Sadeeq yace kwarai kuwa haka mgnr ka take, karar wucewar motoci sukaji suna juyawa suka hango zugar motocin Sageer ne ke tafe a layi zuwa cikin makarantar, kallon juna sukayi kafin Dr. Omar ya fara Shirin tada motar sa, Dr. Sadeeq ya kalleshi da sauri yace Ina zamu? Dr. Omar na fitowa daga inda yyi parking yace can department dinsu zamu, Dr. Sadeeq yace haba Kai kuwa Kai da muke yin Abu cikin sirri Taya zamu fito karara tun yanzu? Dr. Omar nabin layin dasu Sageer sukayi be tankawa Sadeeq dinba saima dage glasses din motar sa da yyi ya zamana duhu ake gani daga waje Babu me ganin na ciki, Dr. Sadeeq ya dafe goshi Yana sake fadin please ko badan mu ba kayi tunani akan sabon H.O.D dinsu kada wani Abu ya sameshi, sai a lkcn Dr. Omar ya juyo Yana kallon Dr. Sadeeq yace tunda kace Jan wuya ne Ina kyautata zaton Babu Abinda zai sameshi, Dr. Sadeeq yace No sharrin mutanen Nan fa yawa gareshi Abinda zaka duba kenan, daidai lkcn Dr. Omar ya Karasa gaban Department dinsu Sageer becewa da Dr. Sadeeq komai ba yyi parking dinsa daga nesa dasu cikin wasu motoci tsilla-tsilla da aka jera aje a wajen, kallon Department din yyi Business Administration ya fadi hakan a ransa, kallon Sadeeq yyi a fili yace Business Admin yanada kyau sosai da ace ya maida hankali tabbas da yaji dadinsa especially da kace babansa babban mutum ne da kuwa Kota bangaren business ne Saiya taimaka Masa, Tunda ya fara mgnr Dr. Sadeeq tsura Masa ido yyi Yana tunanin ranar da Dr. Omar zai fahimci ai a company din baban Sageer din yake aiki, Amma a fili kuwa 'yar dariyar yake yyi kafin yace kasan wasu yaran masu kudin Basu cika bawa ilimi muhimmanci ba sbd sun taso cikin Gata Kuma suna ganin komai kudi zaiyi musu shiyasa Basu wani damu ba, girgiza Kai Dr. Omar yyi yace Allah ya kyauta, Ameen Dr. Sadeeq ya Furta hakan Yana hango taruwar wasu mutane bakin department Ana Dan hayaniya sama2 tabo Dr. Omar daya fara latsa wayarsa yyi, Dagowa yyi Yana Masa Alama da ido lpy? Dr. Sadeeq ya nuna Masa bakin department dinsu Sageer yace kamar fa har an manna Dan ga mutane can tsaye sun cure gu daya Ana hayaniya, kallon wajen Dr. Omar yyi daidai lkcn suka ga fitowar Sageer a fusace ashe Sageer tun Yana gida aka Kira aka tsegunta Masa cewar anyi Masa canjin course, shine ya shigo makarantar a fusace badan Haka bama tunda ya fara harkokin bikinsa ya daina waiwayar B.U.K, Koda Sageer ya shige motar sa ma a guje suka bar makarantar bayan sun Gama bade Kura daga inda suka tashi, Saida suka tafi duka kafin Dr. Omar yyi kokarin fita, da sauri Dr. Sadeeq ya kamo hannun sa yace Dan Allah karka fita duk yadda akayi akwai masu sa Masa ido a skul dinnan kada ya fahimci kana bibiyar sa Bari ni naje yyi mgnr yana kokarin tashi, tsaki Dr. Omar yyi Yana Fisge hannun sa daga rikon da Dr. Sadeeq yyi Masa yace matsoraci baya zama gwani ka Barni Wannan fadan bana zaune bane Bayan Haka ma ni already sunana ya baci a skul dinnan banaso kaima sunan ka ya shiga ciki idan hakan ta faru Kuma bazan taba yafewa Kaina ba, yyi mgnr Yana dauko wata facing cap yasa Akan lallausan gashin kansa tare da wani mask dinsa daya dauko take ya badda Kama ya koma kamar ba Dr. Omar din ba, Kallon Dr. Sadeeq yyi yace ka jirani anan mota kada ka fito yanzu zan dawo, girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi Dan ya Rasa bakin mgn yanzu, Canja yanayin tafiyar sa yyi ya saki jiki Kamar Wanda zaije nasa department din, Kai tsaye office din H.O.D ya nufa, Yaje zai bude kofa kenan yaji Ana mgn sama2 cikin fada Dan dakatawa yyi har zai matsa gefe yaji ance Sageer din banza Sageer din wofi? Jin Wannan ambaton yasa Dr. Omar din ya matsa jikin kofar Dan Jin Abinda ake fada, ji yyi wani na mgn yace prof Aliyu Abinda zaka duba anan shine yaron Nan Dan babban mutum ne Kuma kasan yadda kasar tamu ta lalace kada Wannan canjin department din da akayi Masa ya jawo Mana tashin hankali a kujerar mu, tsaki Wanda aka Kira da prof Aliyu yyi yace su sauran yaran da suke samun carryover su ba mutane bane? Saishi me shafaffe da Mai shine za'a tsallakar dashi sbd ubansa wani ne? Toh Bari kaji koma Shidin Dan uban waye bazan barshi a Wannan department din ba yaje can Sashen Hausa inda na maida shi ya karanta, shiru dayan yyi kafin a hankali yace kaga nine exam officer na Wannan department din ba Haka muke da wancan H.O.D dinba sbd muna tattalin kujerar mu, yyi mgnr cikin Jin haushi sbd su biyun Nan a department su suke cin kudin Sageer shiyasa yake tsula tsiyarsa sbd ya Kama saman, Tsaki Prof Aliyu yyi yace look kabiru Ina aiki ne tsakani da Allah badan wasu can ba Dan Haka sabon tsarin department yazo duk Abinda nace hakan za'ayi, mikewa kabiru yyi cikin danne Jin haushin sa yace shikenan yyi mgnr Yana kokarin bude kofar da hanzarin sa Dr. Omar ya matsa gefe hade da sunkuyar da kansa kasa Yana jiran ya wuce shima ya shiga, lkcn da mlm Kabir ya fito Sam be lura da Dr. Omar din dake gefe ba sbd munafurci da son zuciya sun rufe Masa ido ya zaro waya Yana Danna Kiran Sageer, shi Dr. Omar jira yake yabar wajen gaba1 sai gani yyi yadan tsaya Yana mgn kasa2 yaji yace hello Sageer, daga dayan Bangaren yaji ance Faisal ne ya ake ciki da maganar mu? Cikin takaici yace Wlh Wannan taurin Kaine dashi kamar mutanen farko inaga saidai kuyi Masa Abinda kukace zakuyi na hanaku Ashe bazaiji lallami ba, Tsaki Faisal yyi yace Toh basai Yana raye zaiyi Abinda yakeson yin ba? Mlm Kabir yace tabbas, Faisal ya sake Jan tsaki yace ka saurari ambaton mutuwar sa yyi mgnr Yana datse wayar, saukar da wayar mlm kabir yyi da sauri ya Kama hanyar fita Yana fadin sai muga inda gskyr taka zata kaika Banda Kai wawane ai yanzu duniya ta koma yaki halak yaki haram da Haka yabar Sashen H.O.D gaba1, Dr. Omar dayayi niyyar zuwa gun H.O.D fasawa yyi sbd Abinda kunnen sa ya jiyo game da Wannan wayar da Kabir yyi da hanzari ya fito a department din direct motar sa ya shige, Yana shiga ya cire facing cap dinsa da mask Dr. Sadeeq da yake binsa da kallo a tsorace yace lpy dai Koh? Dr. Omar na kallon sa Kai tsaye yace karfe nawa H.O.D dinsu zai tashi? Da mmki yace nikuwa yashe nasan zai tashi? Kasan koyaushe ma yana iya tafiya, cije lips Dr. Omar yyi Yana me tsurawa steering din gabansa kallo, Dr. Sadeeq ne yace wani Abu ne ya faru? Cikin damuwa Dr. Omar yace banason a dalilina Wannan mutumin ya Rasa Rayuwar sa, a razane Sadeeq yace me suke Shirin Yi Kuma? Lumshe ido Dr. Omar yyi a hankali ya fara tsarawa Dr. Sadeeq Abinda ake ciki, Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un Dr. Sadeeq ya furta hakan hankali tashe yace Anya Sageer Yana fatan Rahamar Allah a gareshi kuwa? Shiru Dr. Omar yyi bece komai ba, Dr. Sadeeq yace lalle ya kamata muyi wani Abu akai, kallon sa Dr. Omar yyi sai kuma ya tada motar sa suna barin wajen gaba1 dake su Sadeeq din sun Gama exam yasa yabar school din itama gaba1, hanyar company dinsa ya nufa dasu, Koda suka Isa office ma duk hankalin Dr. Sadeeq din ya kasa kwanciya, Dr. Omar ya dubeshi yace ya akai duk Naga ka birkice? Dr. Sadeeq yace ai dole na birkice sbd nasan illar sharrin mutanen can, Dan murmushin takaici Dr. Omar yyi a ransa yace baka kaini sanin illar su ba, Amma a fili kuwa yace kada ka wani damu I'm very sure Babu Abinda zasuyi Masa yau, Dr. Sadeeq yace meyasa kace Haka? Dr. Omar na gyara wasu takardu yace sbd nasan bazasuyi Abinda zai zama zargi a kansu ba, zasu Dan bada lkci yadda zasu batar da shaidar su Dan suci galaba a Kan mlmin, Tagumi Dr. Sadeeq yyi yace Ina fatan kada Allah ya Basu nasara a kansa, Ameen Dr. Omar ya furta hakan Yana duba system dinsa, Dr. Sadeeq ne yace ya lbrn madam? Share shi Dr. Omar yyi beyi mgn ba, Dr. Sadeeq yace oh abin ba mgn kenan, Dan hararar sa Dr. Omar yyi Yana yatsina fuska yace Kai kasan da wata madam ni mantawa nake da nayi ajiya a gidan Nan, da mmki Sadeeq yace Omar? Dagowa Omar yyi Yana kallonsa yace naji ka Kira sunana zunubi nayi? Rufe bakinsa Dr. Sadeeq yyi yace Al'amuran ka suna bani mmki ne Wlh, Dan murmushi Dr. Omar yyi yace Kai very soon zanyi aure, Au me??? Dr. Sadeeq ya Furta hakan da mugun mmki, Dan hade fuska Dr. Omar yyi Babu Alamar wasa yace Abinda kaji, daidai lkcn Salma ta turo kofar office din hade da sallama, Zuba mata Ido sukayi ita Kuma batasan da zaman Sadeeq din ba cikin karairaya Tace I'm sorry honey nayi late yau tayi mgnr tana fadada murmushin ta, Dan kawar da Kai Dr. Omar yyi daidai lkcn suka hada Ido d Dr. Sadeeq Ashe tuntuni ya maido da kallon sa kansa, fuskar sa a hade Dan be taba tunanin zancen da suke yanzu gsky bane, dage Masa gira Dr. Omar yyi hade da furta Sadeeq ga Salma Nan ku gaisa yyi mgnr Yana Dan dage Masa gira, sai a lkcn ta juya tana kallon Sadeeq din da fuskar sa take a hade tace hallo Sadeeq a tunzure Sadeeq ya Mike Yana hararar Dr. Omar din ya daga Mata hannu batare daya sake waiwayar su ba ya fice a office din, juyo da kallon ta gun Omar tayi lkcn shima kansa a kasa yake yana Yana latsa system taji yace ga waje Nan ki zauna yyi mgnr yana Dan Dagowa ya kalleta idonsa ne ya dire shi Kan manyan hips dinta dake Masa gizo da sauri yyi kokarin janye idon nasa ya hango cikinta daya matse cikin rigar data saka dake riga da skirt ne sai Dan gyale data yafa da hanzari ya kawar da kansa hade da fadawa duniyar tunani Yana hango Ramin cibiyar daya gani a shafaffen cikinta na jiya, lumshe ido yyi yaji Salma ta katse shi da fadin ya aiki, Bude idonsa yyi da sauri fuskar sa Gata Nan dai ba yabo ba fallasa yace Alhamdulillah, shiru Salma tayi tana jiran Abinda zaice, yyinda shi Kuma Dr. Omar yaci gaba da harkar gabansa Dan shi ba gwanin Hira bane besan ma ya ake hirar ba, Salma ce Tace am..nace ba? Dr. Omar na cike wasu takardu ya girgiza kansa batare daya dago ya kalleta ba, a hankali tace kanada aure ne? Tsayawa yyi tsak be ci gaba da rubutun ba ya dago Yana kallon ta cikin tsarewar gira yace meyasa kike tmby? Shan jinin jikinta Salma tayi bakinta na rawa Tace ah..ba komi dama na tmby ne, kawar da Kai Dr. Omar yyi yaci gaba da rubutun sa zuwa can Anjima taji yace inada shi ya furta hakan a takaice, kirjin Salma ne ya buga daramm wani irin zafin kishi na taso mata ta danne zuciyar ta kafin tace Allah sarki, tayi mgnr Kamar abin tausayi, bazaki auri me Mata bane? Yyi mgnr kansa na kasa har yanzu, da mmki Salma tace me kke nufi? Dr. Omar yace Abinda kike nufi, Dan matse hannun ta Salma tayi kafin tace ah.. why not? Ai ba haramun bane, Good Dr. Omar ya Furta hakan Yana duba agogon hannun sa lkcn sallar azahar ya taho yace zan wuce mosque, Kallon shi tayi tana hadiye yawunta musamman data zubawa pink lips dinsa Ido kamar taje ta Kama ta tsotse duk Bata gaji da zama dashi ba tace sai yaushe kenan? Dr. Omar yace sai Bayan wani lkci yyi mgnr Yana kokarin yin hanyar toilet dinsa, tashi Salma tayi Tace Toh Dan Allah ka bani number ka man, tayi mgnr Kamar zatayi kuka, Kamar bazai tsaya ba Kuma Saiya juyo yace okay Nan ya karanto mata number da hanzari take sawa har ta Gama kafin ta dubeshi da murmushi sosai tace Thank you tayi mgnr tana juyawa a hankali tabe baki yyi batare daya ci gaba da kallon mazaunan ta da take juyawa ba ya wuce toilet din. ~~~~Acan bangaren Meera kuwa tunda safe da take mopping mamakin ficewar Dr. Omar tayi da wuri mutumin da sai wajen goma yake tafiya Amma 8am yabar gidan koda yaje gurin Abba ma a gurguje yyi Masa sallama ya tafi, Ganin baya Nan tayi breakfast din su kadai har me gadi bayan ta kaiwa Abba sun gaisa ta koma ta dauko na me gadin ma takai Masa, dawowa parlo tayi ta zauna kan carpet tanaci tana kallon Sunnah TV data canja, a hankali take breakfast din tana sauraron wa'azin malamin da yakeyi, ba karamin Shigarta wa'azin yyi ba harya gangaro Kan kissar Sihirin da aka yiwa Manzon Allah S.A.W, kwarai ta shagaltu dajin Wannan wa'azin Kuma ta karu ainun Saida mlmin ya kusa tashi aka fara karanta tambayoyi, anan taji an fara karanto tmbyr data Kara Jan hankalin ta, take ta fara waige2 tana neman abin rubutu Dan dazu da zatayi gyaran parlon ta canja musu waje inda Dr. Omar ya Bari jiya da dare, da hanzarin ta ta Isa wajen sbd ta hango inda ta aje Masa su, daidai lkcn aka Kara maimaita Fadar tmbyr da fadin Allah ya gafarta malam yanzu idan mutum akayi Masa Sihiri ta wanne hanyoyi za'a bi domin a warware shi? Mlmin yyi gyaran murya kafin yace Toh Alhamdulillah ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta:117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta: 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta: 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba ganyen magarya guda bakwai, sannan a yi wanka da shi, Insha Allahu aka jimanci Wannan mgnin da izinin Allah za'a samu waraka, Me tmbyr yace Toh Masha Allah duka-duka Anan muka kawo karshen Amsa tambayoyin mu sai Kuma me kowa me komai ya Kara nuna Mana wani lkcn, cikin tsananin farinciki Meera ta sake karanta Abinda ta rubuce kaf akan takardar kafin ta zari katon hijab dinta ta saka batare da tunanin komai ba tayi waje duk murna ta Kama ta, bangaren da Abba yake taje Nan ta tarad baya daki Nan ta fara dubansa can ta hango shi tare da mlm habu a bakin gate, da sauri ta Isa wajen bakinta a washe, Abba na ganin ta ya fara fara'a Kamar koyaushe, mlm habu yace sannu Hajia kina bukatar wani Abu ne? Meera data karaso yanzu tace Abba Insha Allahu ciwon ka yazo karshe, da mmki suka zuba mata Ido mlm habu yace kin samo mgnin ne? Shi Kuma Abba ba bakin mgn bare yace wani Abu sai kallon ta yake d takarda a hannu, bakin Meera yaki rufuwa ta fara nunawa Abba rubutun da tayi kamar Wanda Shidin zai fahimcin Abinda aka rubuta tace kalli Abba yanzun Nan na Gama rubuta Ayoyin da ake amfani dasu wajen karya Sihiri, kallon ta Abba yyi da sauri Meera Tace eh Abba anan sunnah TV naji wani mlmi na wa'azi ta Fadi wa'annan Ayoyin tayi mgnr tana karanta Abinda mlmin yace Tace Insha Allahu zamu gwada maka shi Abba da izinin Allah zaka samu bakin mgn ta karasa mgnr bakinta na rawa sbd mugun tausayin Abban da take gaba1 idonta cikowa yake da ruwa, mlm habu yace Kai Masha Allah gsky hajiya Allah ya saka Miki da Alkhairi Allah Kuma ya dafa Miki bisa kokarin aikin Nan da Kika dauko, kallon sa Meera tayi tana kokarin maida kwallar data taho Mata Tace saidai mlm habu bansan inda zan samu ganyen magaryar ba sonsamu ma na samu danyen ba Wanda ya bushe ba wato ba irin na kasuwa ba, mlm habu yace Abu me sauki? Nan Nan kauyen mu idan naje zan tsinko miki shi dayawa gashi Nan a hanyar garinmu Kamar banza, Da fara'a Meera Tace Toh Amma har sai yaushe za'a samu? Inason Abba ya samu lpy d wuri, Mlm habu yace karki damu Hajia zansa yarona yau dinnan ya kawo ganyen Nan domin ki fara aikin ki da wuri, da murna Tace Nagode mlm habu, mlm habu yace haba ai yiwa kaine Alllah ya bashi lpy, Ameen Meera ta furta hakan tana kallon Abba, Abba tun dazu share kwallar murna yake ya rasa bakin mgnr da zaiyiwa Meera godiya, Allah ya amsa Addu'ar sa tun ranar da Saratu ta juyar da tunanin su Dr. Omar akan neman mgnin Abba yake rokon Allah ya bashi lpy, ya kawo wata silar dazai wargaza Alqadarin Saratu, Kallon sa take da tausayi tace Dan Allah Abba ka daina zubar da hawayen ka Insha Allahu zaka sami lpy, kallon ta yake da murmushi Yana girgiza kansa so yake ya fada mata kukan Dadi yake bana bakin ciki ba, Saida ya share hawayen nasa Tass kafin tabar wajen tanaji a ranta Insha Allahu Nan da wani lkci Abban zai warke shima ya fara mgn. Yamma liss Dr. Omar ya dawo gidan a bakin gate ya tarad da Abba tare da mlm habu, be karasa da motar sa gun parking ba ya tsayar ta kafin ya fito daga ciki, wajensu ya nufa suka tarbe shi da fara'a, Dr. Omar da murmushi yace Abba hutawa ake Anan? Abba ya girgiza kansa bakinsa a washe yanaso ya bawa Omar lbrn Abinda ya faru dazu Babu damar mgn, mlm habu ne yace ai yallabai dazun Nan hajiya tazo Nan da fara'ar ta, da sauri Dr. Omar ya dubeshi bece komai ba Yana jiran Karin bayani, Mlm habu yaci gaba da mgn yace Da murnar ta tazo nan Tace ta samo Ayoyin da ake amfani dasu Dan karya Sihiri, wani irin sarawa Kan Dr. Omar yyi ya dafe goshin sa da sauri ba komai ya sashi Jin hakan ba sai tunowa da Kamar yyi irin kaman cacceniyar mgnr Nan a baya take Kuma ya manta, Batare da mlm habu ya fahimci halin daya shiga ba Nan ya fara feso Masa bayani, kallon Abba Dr. Omar yyi yaga fara'ar sa ta karu, shima samun kansa yyi dajin dadin abinda za'ayiwa Abban, suna Nan sukaji sallama daga waje, lekawa mlm habu yyi yaga Ashe yaron sa ne yace shigowa Mana Musa, shigowa Dan samarin yaron yyi ya gaishe su kafin ya Mika Ledar hannun sa yace ga sakon baba, karba mlm habu yyi yace yauwa Musa Allah yyi Albarka Ameen Musa ya Amsa da murmushi, kallon su mlm habu yyi Yana mikawa Dr. Omar Ledar dake cike da ganyen magarya yace ga Wannan dashi Hajia zatayi amfani saika Bata idan ka Shiga ciki, karba Omar yyi Yana juya Ledar hannun nasa, mlm habu yace ganyen magarya ne, Dan murmushi Dr. Omar yyi yasa hannu ya debo kudi ya mikawa Musa, kin karba Musa yyi Saida Abba yyi Masa Alamar daya karba kafin ya karba din sannan yyi musu sallama ya tafi, Dr. Omar ma sallamar yyi musu ya nufi cikin gidan bayan ya gyara parking din motar sa, Yana Shiga ciki kuwa Meera na zaune a parlo tayi shiru ta fada tunani ba komai take tunawa ba sai Dad dinta, Tabbas a yadda taji wa'azin mlmin Nan ya Fadi Abubuwa da yawa na alamomin Wanda aka yiwa Sihiri da tayi dogon nazari ta fahimci tabbas Dad dinta Yana daya daga cikin Wanda aka lissafo shima, tunani take Taya zata taima Masa? Yanzu me yakamata tayi Dan ceto Dad dinta daga hannun mugaye da yake ciki? Ji tayi an bugi kujerar da take zaune a firgice ta dawo daga duniyar tunanin data Lula idonta ne ya sauka Kan Dr. Omar da tun dazu yake tsaye kanta duk mmkin Wannan dogon tunanin data tafi yake, Meera ce tayi azamar janye nata idanun tana kawar da kanta da sauri bakinta na rawa Tace Ashe ka dawo sannu, tayi mgnr tana gyara zaman ta, Shiru taji yyi beyi mgn ba hakan yasa ta juyo ta kalleshi, ga mmkinta taga still itan yake kallo, wara ido tayi Tace Ya Omar? Gani tayi ya tabe baki Yana zagayowa Kan kujerar ya tsareta da Ido sosai yace kalleki duka2 baki wuce 18yrs da wani Abu ba yarinya dake Sharaf wacce Ba'a Dade da Gama goyonta ba kila ko kirgen dangi baki Gama ba Kika zauna Anan harda fadawa tunani kamar wata babbar mace me Yara Ashirin, dubansa tayi d mmki tace Ya Omar? Cikin tsare gira yace fadamin tunanin me kike? Girgiza Kai Meera tayi Tace ba komai, yatsina fuska yyi Yana aje Ledar hannun sa yace ga sakon ki inji mlm habu, karba tayi da sauri tana Buda Ledar Tace Alhamdulillah Insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe tayi mgnr da fara'a sosai Kan fuskar ta, kallon ta yyi yace me Zaki dashi? Nan Meera ta fada Masa komai akan Ayoyin balla Sihiri, Girgiza Kai yyi yace Good Allah ya taimaka, Ameen Meera ta furta da fara'a tana kokarin tashi daga wajen kafin ta wuce dakinta, tashi shima yyi ya wuce can sama Dan rage kaya.
Washe garin ranar Meera na parlo da azahar lkcn ta Gama girkin Rana taga shigowar Dr. Omar da saurin sa ya wuce sama, bin sa da kallon mmki tayi ta leka can kofar waje taga be shigo da motar sa ba, Abba ma baya bakin gate da alama da yyi Sallah dakinsa ya wuce, Meera na tsaye tsakiyar parlon tana nazarin Abinda ya dawo da Dr. Omar da Rana Haka ta hango shi daga can sama Yana taku da hanzarin sa ya canja kaya zuwa wasu bakaken kananan kaya d facing cap hade da mask daidai zai wuce ta gabanta da sauri ta Isa wajen sa tace ya Omar, ko kallon ta beyi ba yyi haramar fita da sauri Yana duba agogon hannun sa, da mugun mmki ta sake bin bayansa daidai zai bude kofa ya juyo Yana kallon ta ransa a hade yace kada ki soma sanar da Abba nazo na fita kin gane? Girgiza Kai Meera tayi a tsorace ta kasa mgn, Juya fuskar sa yyi yaci gaba da tafiya Yana Isa gaban gate mlm habu ya bude Masa kofa ya fita Yana Masa fatan nasara, fitar sa keda wuya Ashe a kofar gida yyi parking motar sa kawai ya shige cikinta ya Bata wuta a tamanin kafin wani lkci harya bace a unguwar Kamar walkiya, Sosai ya dinga ratsar shortcut harya cimma layin da yake kokarin Hawa, a hankali yake bin bayansu a fisge Kamar ba Dan su din yake tafiya ba, Motar su Sageer ne sbd haushi ma Sageer yace da kansa yakeson Harbin prof Aliyu sbd ya bashi gardama a department, prof Aliyu dake tafiya a nutse Sam besan da Ana binsa ba dake hanyar da zata kaishi gida tana Dan wajen gari yasa su Sageer suka samu damar binsa suna jiran ya Shiga lungun da zasu kashe shi batare da an fahimce su ba, Sageer shine me driving din sai Faisal a gefensa, wasu yaransa biyu a Bayan motar a takaice dai su hudu ne a ciki Daidai wani Shan kwana Sageer ya zaro Bindigar dake ajiye gefensa ya rike dayan hannun sa da steering dayan Kuma ya fiddo dashi waje cikin salo na mugunta ya saita gun din Kan tayar motar prof ta gaba Yana Shirin harbin wajen yaji harbi ya daki hannunsa, cikin wata irin kururuwar azaba Sageer ya saki gun din hannun nasa Yana me sakin Kan motar gaba1 sai ihu yake azaba ta isheshi besan a wanne Hali yake ciki ba, karar ihun Sageer ita ta fargar da prof dake driving a gaba, rage gudun motar sa yyi Yana duban bayansa a hankali, take ya hango motar bayansa na layi Akan titi ita kadai, besan meke faruwa ba hakan yasa yyi kokarin dakatawa, Daidai lkcn Dr. Omar dake can nesa dasu ya Kara wayarsa a kunne Yana fadin hello Sadeeq turo su, Sadeeq dake dayan Bangaren yace okay, Nan ya bawa wasu 'yan sanda umarnin su fito daga inda suka lafe, daidai lkcn Faisal ya rike Kan motar Yara biyun dake baya da suka shiga rudani Ada ganin motar ta tsaya yasa suka zaro guns dinsu a take suka fara harba wuta Kota Ina, Prof Aliyu daya ga hakan sai hankalin sa ya tashi Yana kokarin juyawa kenan yaga wani harbi ya wuce ta saitin kirjin sa kadan ya rage ya taba Masa jiki, kaucewa yyi cikin azama yaga sun Kara harbo Masa wani anan ya shige mota da sauri Yana kallon su ta mirror sai a lkcn ya fahimci ashe yaran Sageer ne, hankalin sa ne yyi mummunan tashi ya dauko wayarsa Yana kokarin Kira yaga motar 'yan sanda ta iso, a lkcn yaran Sageer din suka daina harbi, da hanzarin su 'yan sandan suka fito daga mota suna furta You're under arrest, Faisal ne ya fito a motar Yana nufar 'yan sandan yace Kunga bama bukatar ku Bata Mana lkci nawa kuke so mu Baku ki tafi? Da mmki 'yan sandan sukace Kai me kke nufi? Faisal yace kudi Mana nasan shine toshiyar ku, Wani daga cikinsu yace Amma kaikam baka da hankali wato so kke muci amanar kasar mu? Faisal yace Kai kunsan waye a cikin motar can kuwa? Sageer ne fa babban yaron me kudin Nan da kowa yasan dashi a fadin Nigeria gwara ku rufawa kanku Asiri ku Fadi Abinda kukeso ku bamu waje ko Kuma muje can gun manyan naku ai su sunsan harkar da alama kukam baku Dade da fitowa daga training ba, Dan Ayau dinnan mukeson kawo karshen wancan munafikin ya nuna prof Aliyu da yyi mutuwar zaune Yana kallon su da mmki, wani irin gigitaccen Mari Faisal yaji an dauke shi dashi besan daga Ina Marin yake ba Kawai dai ya bude idonsa ya ganshi tsaye gaban wani mutum da yyi Shigar bakaken kananan kaya da facing cap hade da mask, Cikin mugun takaici faisal ya bude baki zaiyi mgn yaji an sake wanke shi da Mari take yyi shiru Yana muzurai, Dr. Omar dake kallon su Sadeeq da shima ya badda Kama cikin kayan 'yan sanda yyi Masa Alama da ido akan a debe su, Nan kuwa aka kwashe su Bayan an gama Shaka musu hodar bcci aka nufi can wata unguwar dasu, Dr. Omar kuwa gaban prof Aliyu ya Isa, Lkcn dayaje prof Aliyu ya fito Yana fadin Gsky ban taba haduwa da babban Dan sanda Kuma Dan Nigeria dayasan Kan aikin sa ba sama dakai yallabai, dan murmushi Dr. Omar yyi har yanzu be cire mask dinsa ba yace Abinda nakeso dakai shine ka saki jikinka ka manta da komai kamar Babu Abinda ya faru dakai anan zanji da komai a hannun na, prof Aliyu yace Dan Allah ko zan iya sanin sunan ka? Girgiza Kai Dr. Omar yyi yace I'm sorry But na maka Alqawari wata rana zaka sani, girgiza Kai Prof yyi yace Alright, I wish you all the best, Thanks Dr. Omar ya furta kafin yyi Masa sallama. Farkawa Sageer yyi ya ganshi a wani dakin shi kadai ba kowa an rufe ga hannun sa anyi dressing wajen har an cire bullet din da aka harbe shi, cikin tsananin takaici ya ware murya sosai yace Wai uban waye ya kawo ni Nan? Ko rufe bakinsa beyi ba yaga mutane sun shigo da abin duka a hannun su, Sageer yace Kai uban me nake anan? Suwaye ku? Yyi mgnr ransa a bace, basuyi masa mgn ba Kawai suka hau dukansa Kota ita, kururuwa Sageer ya fara Yana zaginsu da dura musu ashar yace indai akan Wannan prof Aliyu ne saina kashe shi bazan fasa kuduri na ba, Basu fasa fasa Masa jiki ba Saida yyi laushi, Saida yyi shiru kafin daya daga cikinsu yace zaka Kara bibiyar Rayuwar Prof Aliyu ko kuwa kanaso mu dauki duk wani record naka mu kaiwa mahaifin ka? Da sauri Sageer ya dago kansa a mugun tsorace yasan duk Wannan mugayen halin da yake daddy be sani ba yanzu idan aka sanar Masa Abinda yake a skul yasan ba karamin hukunci zai fuskanta ba Dan Haka ya girgiza Kai yace lalle ma prof dinnan wato tsabar bakin Hali daga zuwan nasa har ya San ya tattara duk wani record da zai iya kaiwa mahaifina? Wanda yyi mgnr ne yace Toh kana mmkine? Ko ka dauka boyayyen gidan ka da kke masha'a ba'asan dashi ba? Kasan kuwa ba karamin sani yyi maka ba, kallon su Sageer yake yace shikenan naji ya Furta hakan cikin takaici, okay Bari mu sanar da ogan mu yadda akayi suka Fadi hakan suna kokarin rufe shi yace waye ogan naku? Ku hadani dashi Mana, Lekowa dayan yyi yace sbd kana takamar kanada kudin da zaka siye shi dashi Koh? Toh gwara ma ka yadda makaman yakin ka Dan wannnan na musamman ne ba kowa ke ganin sa b yafi karfin tunanin ka ya karasa mgnr Yana jawo kofar da sauri, fitowa parlo sukayi Nan suka tarad da Dr. Omar ya Dora daya Kan daya a parlo Yana sauraron zuwan su, yyinda Sadeeq ke gefe Yana waya cikin risinawa sukace yallabai duk Abinda ka samu muyi munyi shi daga karshe ya amince da bazai Kara bibiyar Rayuwar Prof ba, cije lips Dr. Omar yyi Yana kallon Sadeeq daya Gama Waya yanzu ya Mika masa hannu Alamar ya bashi paper gabansa, Miko Masa Sadeeq yyi shi Kuma Omar din ya Mika musu yace ku bashi yyi signing a kasa shine zai tabbatar da Abinda yace, karba sukayi cikin girmamawa suka koma wajen Sageer, lkcn da sukaje sai cika yake Yana batsewa suka Mika Masa takardar hannun su sukace gashi Nan yace kayi signing anan Dan Tabbatar da Abinda kace, karba Sageer yyi yahau dubawa kafin yyi signing din da murmushi yace Wai ku nufinku Nan Akan Wannan takardar sai ya hanani Abinda nayi niyya? Wani daga cikinsu ne shima yyi murmushin yace ai tunda kasa hannu zance ya Kare Wannan da kke gani itace takardar da za'a mikawa mahaifin ka ita Kuma ka sani a duk lkcn da kukayi yunkurin bibiyar Rayuwar prof a lkcn idon mu na kanku, a maimakon ka ganmu a wajen saidai kaga idon mahaifin ka a wajen ya ganewa kansa irin mugayen lefikan da dansa yake Yi, Ko kadan Sageer beyi zaton rufta shi sukai ba take hankalin sa yyi mugun tashi cikin tsananin takaici ya kaiwa dayan hannun sa naushi Yana muzurai sudai anan suka barshi suka nufi wajen Dr. Omar, kallon takardar Dr. Omar yyi Yana juyata kfin yace Suma yaran a aje a fito dasu, Nan aka tiso keyar su Faisal da aka kulle a wani daki, Haka shima Sageer din aka tiso keyar sa lkcn har dare yyi Bayan sallar Isha duhu ya Shiga sosai hakan yasa Basu gane yanayin gidan ba har suka Gama fitowa, Koda suka fito ma rufe musu Ido akai da kyalle da Kuma hannayen su da aka daure Babu damar su fahimci inda suke har suka bar unguwar gaba1, Saida aka shigo gari dasu kafin aka watsar su can wata gefen wata unguwar Bayan an bude musu Ido sannan wa'annan 'yan sanda suka bawa tasu motar wuta Dan barin wajen. Meera na parlo har yanzu sai duba agogo take Bata ga Alamar zuwan Dr. Omar ba gaba1 hankalin ta ya tashi gashi batasan me zata cewa Abba ba Dan tun dazu yake zuba idon ganin Omar din be gansa ba, daga yanayin yadda yake kallon ta idan ta leko waje yanason Jin Karin bayani ne ita Kuma Taki Karasawa wajen sbd batasan me zata ce ba, a Haka harya shige dakinsa sbd yadda duhun dare yyi, tana cikin safa da marwa kenan taji Alamar budewar kofa a hankali, juyowa tayi a razane sai Kuma taga Ashe Omar ne, da mmki ya bita da kallo saidai beyi Mata mgn ba ya wuce sama da sauri, kallon kofar tayi taje ta datse da sauri kafin ta bishi saman itama, gaba1 ta manta da wani Abu waishi knocking tana zuwa ta tura kofar a rude tanason Jin lpyr sa, Daidai lkcn Dr. Omar ya cire rigar jikinsa ya rage daga shi sai gajeran wando dama tuni ya zare dogon wandon dake jikinsa, take faffadan kirjin sa ya bayyana kirarrar sa ta mazan taka ta fito, Wani irin mutuwar tsaye Meera tayi bakinta a hangame ita Bata karasa cikin ba ita Kuma Bata koma waje ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.