Best Hausa Novels

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt

Chapter 76 of 85

*200 kacal ya Isa ki samu cmplt littafin Nan ta hanyar turo da ita ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻*
8/19/20, 9:05 AM - Ummi Tandama: Wara Masa ido tayi tana Dan hade fuska Ahmad ya saki murmushi yace, "karya nayi?" Hararar sa tayi tazo giftawa yyi azamar kamo hannun ta da sauri kuwa ta goce tana dafe kirji hakan yasa Ahmad ya zuba mata idonsa, sake banko Masa Harara tayi tana Dan saita nutsuwar ta Tace, "Ya Ahmad don't try this again" "I'm sorry" ya Furta a hankali, kwafa tayi kawai ta fice itama harsu Inna fure sun Isa gaban motar sa, Yana biye da ita a baya isarsu wajen yasa su Inna furen Suka shige bayan mota itama Kama murfin kofar tayi zata wuce yace, "ki shigo Nan Mana Meera" tamkar bataji sa ba ta bude kofar Inna fure Tace, "ki shiga can din Ameera kinji?" Girgiza Kai tayi badan taso ba ta bude gaban ta shige, tana Shiga kuwa Ahmad ya tada motar sa suka fice daga gidan Suna Hawa Kan titi kuwa Meera tasa kanta gefen window tana karewa garin Adamawa kallo, Sun zaga ko'ina da ita kowa akace Masa 'yar Aminatu Jikar hadiza wato yayar inna fure sai yyita mmki, manyansu ne dai duk Basu manta ba saidai masu hankalin suke Jin kunyar wofintar da zumunci da akayi, sun gaji matuka, a hanyar su ta komawa ne ma Ahmad yace, "zan biya daku shopping Inna" Inna fure Tace, "Kai ba Dani za'ai Wannan gantalin ba na gaji" Abinda yakeson ji kenan Dan Haka yace, "Asma'u ku shirya Anjima bayan Kun huta zamu fita" yyi mgnr Yana dauke Kai Dan karma Meera ta Musa, Inna fure ce tace, "jikinku da kwari ku zaku iya zuwa Amma Banda ni" Asma'u Tace, "saiki fada Mana Abinda kikeso mu sayo Miki" Inna fure na tabe baki Tace, "ku kuka sani Amma dai a Tabbatar jikata ta zabi son ranta" 'yar dariya Ahmad yyi yace, "Kai Inna dukanmu ma ai jikoki ne" Inna Tace, "na sani Ita meeran dai banaso kunya ta hanata daukar komai" Meera sai a lkcn tayi murmushi hakan yasa Ahmad yace, "Kinga ma dariya take Miki" Inna Tace, "atho ai tasan gsky na fada." Su Omar na cikin jirgi Sadeeq ya dubeshi yadda yake ta duba agogon hannun nasa ne yaso bashi dariya gashi dai karshen gudu a jirgi suke Amma hakan da alama be wadatar dashi ba, Dan zungurin sa yyi hakan yasa Dr. Omar ya dubeshi, Sadeeq yace, "yanzu da kkeso mu Isa wajen Nan da wuri ka tanadar wa Meera kalaman da zaka Bata hakuri?" Dan shiru Omar yyi sai yanzu ya tuna fa akwai Kura a gaba, Amma cikin mazewa yace, "it's normal nasan ta yadda zan biyo mata" gyada Kai Sadeeq yyi yace, "that's good" Basu wani Jima sosai ba kuwa sai gasu a garin Adamawa, tunda Omar ya fara taka matattakalar jirgin Nan yakejin wani irin Sanyi na dukansa lalle yazo garin Adamawa garin Fulani da nono Dangin sahibar sa Meera, a hankali ya Gama saukowa hannun sa rike da traveling bag dinsa, Sadeeq na gefensa shima da Abinda yake kallo can, Suna fitowa daga airport din Omar ya duba pocket dinsa inda ya aje address din su Meera Yana dubawa kuwa ya karance tsab Toh dama harya haddace tun ganin farko da yyima takardar saidai sbd gudun Saba lamba ya dauko ya sake dubawa, taxi suka tare wacce zata kaisu har inda suke so, Koda Omar yyima driver bayanin inda suka nufa yace ya gane wajen, tafiya suke sannu a hankali har suka fara gangarawa unguwar Alhji Kabir Dan Anan ne ma Dad ya bada Address din tun daga hanya Omar yake leken window kirjinsa na bugawa a hankali Dan besan da wacce fuska Ameera zata karbeshi ba bare Kuma ace Ahalin ta, Suna zuwa daidai katon gate din gidan Alhaji Kabir Suma daidai lkcn Ahmad ya danno tasa motar, su Omar biyan me taxi din sukayi harma ya haura kudin daya bukata ya karba kuwa da murnar sa Yana godiya, me gadinsu Ahmad ne ya bude musu gate suka wuce ciki yyinda Dr. Omar da Sadeeq suna Kara matsawa jikin gate kafin su wuce suka hango sojoji na shawagi a tsakankanin wajen, Dr. Omar da Sadeeq ne suka kalli juna a tare, shi Omar kallon mmki yake shikuwa Sadeeq kallon tsoro yake a hankali yace, "Shikenan ai Omar ka kawomu inda za'a harbe mu" Dan tsaki Omar Yaja Dan shi Bata Wannan yake ba hakan yasa ya Isa gaban soldiers din gadan2 ba tsoro ko kadan a tare dashi, gaban Wanda ya bude gate din gidan yaje Yana kokarin rufe gate din Omar yyi sallama, Dagowa yyi Yana Kare Masa kallo da gani ma kabila ne ya Amsa Masa da tasa hausar da Bata Gama isarsa ba, Bude baki Omar yyi zaiyi mgn ya hango bayan wata mace wani Namiji na bude kofa Dan already su Inna sun wuce ciki gabansa ne ya buga da karfi Yana kokarin kauda tunanin Abinda yake Dan yasan ba lalle hasashen sa ya zama gsky ba Kawai yaga Abinda idanun sa suke ta matukar son gani wato Meera na yiwa Wanda ya bude mata motar murmushi...., A rude Omar yayi hanyar Shiga ciki bakinsa na rawa yake fadin, "Meeeeraaaa...." Kamar saukar tsawa Haka Meera taji muryar da ko a mafarki taji bazata manta ba wato Omar hakan yasa ta kalli bakin gate din a firgice, soldiers din wajen ne suka taso da hanzarin su Suna tare shi Nan suka fara fadin, "Who are you?" Mika hannun sa Omar yyi Sam bebi ta kansu ba Amma Kuma sun rike shi gamgam fadi yake, "Meera pls kizo nan" Ahmad da ya Shiga mmkin Wannan Al'ajabi ya dubi Ameera da jikinta yaketa rawa yace, "waye Kuma wancan?" Kin bashi Amsa tayi kawai ta wuce cikin gidan da gudu tana kokarin danne hawayen daya taho mata, hakan yasa shima Ahmad din yabi bayanta da sauri, bangaje soldiers din Omar yyi Yana komawa baya duk sai suka zuba Masa ido, dafe kansa yyi Yana cije lips, Sadeeq ne ya kamo hannun sa a hankali yace, "haba Omar ai da saika Bari a Kira maka ita ko?" Fisge hannun sa Omar yyi ransa na zafi yace, "da aurena a kanta Naga tana yiwa wani katon murmushi ya kke tunanin zanji hakan a Raina?" Dan sauke ajiyar zuciya Sadeeq yyi Yana jansa gefe yace, "look Omar Nan ba kano bane kowa sarki ne a wajen zamansa mu bakine Omar bamu San komai Akan Wannan family din ba ya kamata ace mun biyowa abin ta sama" Tsaki Omar yyi Dan gsky har yanzu bawai ya huce bane kawai bayason ya zubar da mutuncin sa ne ya fada gidan mutane, Dan bubbuga kafadar sa Sadeeq yyi kafin yace, "Ina zuwa" wajen soldiers din ya nufa a nutse yace, "Dan Allah ko me gidan Nan yana Nan?" Daya daga cikinsu ne yace, "dazun Nan ya fita maybe Anjima ya dawo"
"Okay" Sadeeq ya Furta hakan Yana koma gun Omar dake ta faman cika Yana batsewa, dafa kafadar sa yyi sannan yace, "Kayi hakuri har me gidan ya dawo Omar tanan ne zamu San ydda zamu Kama bakin zaren" cije lips dinsa Omar yyi har yanzu murmushin da Meera ta sakarma saurayin Nan be daina sukar sa a zuciya ba, Suna tsaye kuwa saiga motar Alhaji Kabir ta shawo kwana shi da dad ne a ciki, inda Allah ya taimake su ma ba ciki Suka shige da motar ba, dad ne ya fara fitowa take kirjin Omar ya fara harbawa yanzu da wacce kalma zai tari mutumin Nan daya bashi 'yarsa ya mata rikon sakainar Kashi? Sam dad be lura da su ba saima Hira da suke da Alhaji Kabir dake zuge glass Yana Shirin fitowa, Saida ya fito dad ya juyo domin su tafi idonsa ya sauka kansu, kallon su yake saidai ya kasa tuna inda ya sansu Sadeeq Kam duk kunyace ta ishe shi saikace shine Omar din, Alhaji Kabir dake be gane su waye ba Yana ganin su ya dauke kai dake Suna jikin gate din wani gidan makocinsa be kawo cewar bakinsu bane, Dan zungurin sa Omar yyi ganin Suna kokarin wucewa Dan shima dad din ya daina kallon su Sadeeq ya dubeshi mgn kasa2 yace, "ka musu mgn man" Omar ya dubeshi da sauri Yana Masa mgn da Ido, Dan sauke ajiyar zuciya yyi kafin yyi ta maza ya Isa gaban su dad ya musu sallama, Juyowa sukai Suna Amsa Masa har Omar din dake ta Bayan Sadeeq, gaishe su sukayi a mutunce Suma suka Amsa musu a mutunce Alhaji Kabir yace, "saidai ban gane ku ba 'yan samari" Dan yake Sadeeq yyi yace, "dama baki ne daga kano" sai yanzu dad ya sake Juyowa Yana Kare musu kallo, Alhj Kabir yace, "ikon Allah Kuma wajena kukazo?" Dan sosa keyarsa Sadeeq yyi yace, "ehto dama dai...." Sai Kuma yyi shiru Yana Jin nauyin furucin da zaiyi, Omar kuwa tunda Sadeeq ya fara mgn kansa a duke yake zuciyar sa na harbawa da sauri2 besan me zaije ya dawo ba da alama dad din Ameeran ma ya manta su tunda yake musu kallon Rashin sani, "Continue...Inajin ka" Alhji Kabir ya katse shirun, bakin Sadeeq na rawa yace, "uhum...dama..ni da mijin Ameera ne mukazo" Sai yanzu hasashen da dad yake ya zama gsky hakan yasa shi daure fuska, Alhaji Kabir kuwa kallon mmki yake musu yace, "wancan din ne mijin nata?" Dad kuwa cewa yyi, "akwai wani sauran alaka da suke dashi ne bayan sakin wulakancin da yyi Mata?" A razane Omar ya dago hankalin sa a mugun tashe Yace, "i'm Very sorry dad Amma ni Wlh ban saketa ba" Jin Wannan furucin na Omar yasa Alhaji Kabir yace, "toh Wannan mgnr Bata tsaye bace ku biyomu ciki a tattauna" gaba dad yyi be sake sauraron su ba, su Omar kuwa sunji Dadi kwarai da Alhaji Kabir ya bukaci da su shiga ciki. Inna fure na shirun tube hijab dinta a parlon mamy mahaifiyar Ahmad taga fadowar Ameera da gudu tana kuka, saurin rikota tayi ta zauna kan kujerar hankali tashe tace, "meya faru Ameera?" Shiru Ameera ba mgn sai Jan zuciya, Nan Ahmad ya Fado dakin shima Inna fure Tace, "Kai lpy kuwa kuke ta guje2?" Sauke numfashi Ahmad yyi Yana zama kan kujera yace, "Dan Allah Inna ki tmbyeta Nima bansan Abinda ya faru ba" "Kamar ya baka sani ba bayan tare kuke?" Mamy dake shigowa tayi Wannan furucin, dafe goshinsa yyi kafin yace, "muna Shirin shigowa ciki wani daga bakin gate ya dinga kwala mata Kira Yana Mika mata hannu tazo badan Allah yasa masu gadin Nan sun tare shi b Toh kuwa ba shakka Saiya shigo ciki" "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" inna fure ta furta hakan tana dora hannu akai Tace, "Wanne irin mutum ne Haka daga zuwanta ko Gama sanin garin batayi ba za'ace an biyota?" "Nima Abinda ya bani mmki kenan" Ahmad ya Furta hakan, ita dai Meera Bata dago Tace musu kala ba Dan gaba1 jikinta rawa yake, hakan yasa Inna fure Tace, "jeka Ahmad ka dubo Mana waye mutumin? A yadda ta firgice dinna Ina kyautata zaton ko ba mutum bane" 'yar dariya Ahmad yyi Yana mikewa tsaye yace, "haba mutum ne sak Kamar kowa Bari dai naji wanene" Mamy Tace, "Wannan Abu Koh da mmki yake" Inna fure ta sauke ajiyar zuciya tana shafa Bayan Meera tace, "Allah shi kyauta." A bangaren su Omar kuwa parlon baki Alhji Kabir ya sauke su Bayan sun zauna ne shi Kuma ya fita Dan a kawo musu abin tabi, Yana shiga gidan ya Kira mamy ya sanar da ita ta kaiwa bakinsa abinci Tace, "Toh" Nan tasa masu aiki suka fara kaiwa su Omar kayan motsa baki da abinci, Sauke ajiyar zuciya Sadeeq yyi bayan masu kawo musu abincin sun Gama ya dubi Omar daya cusa hannayen sa cikin lallausan gashin sa Yana hargitsa shi, Dan gyaran murya yyi kafin yace, "da alama abun zaizo Mana da sauki" Omar ya dube shi cikin damuwa yace, "sauki? Kana gani fah kiranta nake tayi banza Dani Sadeeq" ya Kare mgnr kamar yyi kuka Dan takaici, sauke numfashi Sadeeq yyi kafin yace, "komai a sannu ake binsa Insha Allahu zaku daidaita da wuri" Dan cije lips dinsa Omar yyi kafin yace, "Haka nake fata" dubansa Sadeeq din yyi sannan yace, "gashi duk ka hargitsa gashin naka a Haka kkeso ka birge ta?" Shiru Omar yyi kafin yace, "yeah ko a Yaya nake Ina birgeta" "Haka Tace maka?" Sadeeq ya Fadi hakan d mmki, Omar na tabe baki yace, "Haka nake tunani" Sadeeq yace, "Dan Allah Shiga Koda toilet ne ka duba gashinka a madubi idan ba so kke Dan saurayin can yyi maka kafa ba" wata irin muguwar hararar Omar ya sakar Masa Kamar ya doke shi hakan yasa Sadeeq Yaja bakinsa ya tsuke, dakyar dai suka cusa Abinda ya samu a cikin Abubuwan da aka kawo musu, Alhaji Kabir kuwa na can yana tmbyr dad meyasa ya share su dad ya Gaya masa dalilin sa, Shiru Alhaji Kabir yyi shima ransa ya baci Amma dai dole Abi abun a hankali Dan Haka yace, "toh ita yarinyar ta fada maka saki nawa yyi mata?" Girgiza Kai dad yyi yace, "duk lkcn da aka tmbyeta akan hakan saidai ta fashe da kuka shiyasa nake tunanin sakin wulakanci yyi mata" sauke ajiyar zuciya Alhaji Kabir yyi kafin yace, "kuma gashi yaron yace Bai saketa ba" shiru dad yyi beyi mgn ba, hakan yasa Alhji Kabir yaci gaba da fadin, "inaga kamata yyi a Kira Ameeran sai muji daga gareta tunda Yana wajen idan har ya saketan yanzun Nan zansa subarmin gidana, idan be saketa ba sai musan abin yi" cikin gamsuwa da shawarar Alhji Kabir yace, "ya amince";mamy Alhji Kabir ya Kira yasan tunda dad ya sanar Masa yadda sukayi da Inna fure za'a iya samun matsala idan tasan Omar din yazo Dan Haka yasa mamy ta turo Masa Ameera, Ameera data daina jan zuciya yanzu mamy ta shigo da fara'ar ta Tace, "kije Abban su Ahmad na Kiran ki" mikewa Meera tayi Tace, "Toh,?";Inna fure Tace, "Suna gidan ne dama?" Mamy Tace, "a'a yanzu dai suka shigo" shigowar Ahmad ce ta katse musu mgnr yace, "inaga dai sojojin Nan sun kora su Dan Banga kowa ba" Inna fure na murmushi Tace, "Sun kyauta" Meera Kam tsam tayi da ranta tana tunanin Kuma Ina ya tafi? Mamy ce ta katse mata tunanin da fadin, "Suna jiranki fah" tashi tsaye tayi hakan yasa mamy ta kamo hannun ta Dan ta rakata parlon Abban su Ahmad, Ahmad ne yace, "mamy wani wajen zaku ne?" Mamy Tace, "Abbanku ke kiranta" "okay" Ahmad ya Furta hakan Yana zama hade da kwalawa Asma'u Kira, kafin suje parlon Alhji Kabir ya kirata a waya yace ta sameshi a parlon baki, hakan yasa mamy ta canja direction dinta zuwa can, ita dai Meera Kamar jela Haka take binta zuciyar ta nadan harbawa kadan, acan kuwa dad da Alhji Kabir ne a parlon bakin tare dasu Omar Bayan sun sake sabuwar gaisuwa Alhji Kabir na Amsa musu da fara'a be tmbyesu komai ba Dan jira kawai yake meeran tazo, Suna cikin Haka kuwa su Meera suka Isa gaban kofar Mamy Tace, "ki shiga ciki ni zan juya" Ameera ta gyada kanta mamy ta juya ita Kuma ta tura kofar da sallama, muryar Tace ta makale lkcn da tayi tozali da idon Omar dama bakin kofa yake kallo hakan yasa idanun su ya sarke da juna, Sam Bata lura dasu dad dinba tana Shirin juyawa kenan taji muryar Alhji Kabir na Fadin, "ina Kuma zakije Meera?" Juyowa tayi jikinta na rawa Nan ta karewa mutanen wajen kallo, ,
"karaso ki zauna kinji" Alhji Kabir ya sake Furta hakan, a hankali ta fara takowa Kamar Wanda kwai ya fashe mata a ciki ta raba can gefen su Alhji Kabir din ta zauna a dofane, still idon Omar a kanta Yana kallon ta akaikaice ji yake kamar ya jawota ta fada a kirjinsa Dan kawai ya shaida mata yyi missing dinta sosai, Alhji Kabir ne ya dubi Ameera dake ta ta raba Ido ta kasa sukuni yace, "kin gane wa'annan?" Ya Mata nuni dasu Omar, kanta ta dukar kasa batace komai ba, Alhji Kabir yace, "mgn nake Miki Ameera, Ameera jikinta na Bari ta daga kanta a hankali Alamar eh, Toh Masha Allah tunda kin gane su "shi Wannan waye dinki?" Ya nuna mata Omar dake kallon ta, ko Bata gani ba tasan Omar yake nufi Hannayen ta tafara murzawa a hankali ta kasa furta komai, hakan yasa dad yace, "Meera ki fada Mana a kawo karshen matsalar" Meera bakinta na rawa Tace, "mi....mi..mijina ne Ada." "mijinki Ada Kuma?" Alhji Kabir ya maimata Abinda Tace shi kuwa Omar a rikice yaso Yin mgn Alhji Kabir ya dakatar dashi da hannu, hakan ya sashi hadiye Abinda yaso Furtawa badan yaso ba, Meera da taji Abinda Alhji Kabir yace ta daga kanta Alamar eh, Alhji Kabir yace, "idan nayiwa abun kyakkyawar fahimta kenan bakwa tare yanzu?" Zuwa yanzu kukan da take dannewa ne ya taso mata hannun ta a baki take fadin, "muna tare Amma so nake mu rabu ya sakeni..." Ta Furta hakan tana rushewa da kuka, shiru dakin ya dauka Banda Omar daya Shiga rudani matuka, Bayan shirun na wani lkci Alhji Kabir yyi gyaran murya Yana duban Omar daya Gama rudewa matuka yace, "Kai kaji Abinda Tace Koh?" Bakin Omar na rawa yace, "pls Ameera kar muyi Haka dake man ni Wlh ban shirya rabuwa dake ba" yyi mgnr da sauri2 hankalin sa na Kara tashi, kallon dad daya sunkuyar da kansa Alhji Kabir yyi kafin yace Masa komai harya Mike ya fice fuskar sa bazakace Yana farinciki ko akasin hka ba, hakan yasa shima Alhji Kabir din yabi bayan Dad Dan ya lura akwai kuriciya sosai akan Ameera, wayar Sadeeq ce tayi ringing hakan ya sashi fita Dan answer call, Kamar Wanda Omar ke jira dake Ameera duk batasan ficewar su ba kanta na Duke sai ji kawai tayi an jawota, a firgice ta dago kanta Nan taga Ashe ba kowa sai Omar da yake kokarin cusata a kirjinsa, cike da Takaici ta dinga zamewa daga jikinsa Fadi take "sbd bakason cigaba na shiyasa kkeson ka sake komar Dani? Wlh bazan yadda ba auren ka a Kaina ya Kare" "Meera pls ki saurareni ni yanzu Wlh nafi bukatar ki bazan iya zama Babu ke ba" Omar ya Fadi hakan Yana sake riketa sosai a jikinsa Dan hanata tashi, kokarin tirjewa taci gaba dayi Tace, "sbd kanason jikina Koh?" Ta Fadi hakan tana zubar da hawaye masu zafi, "No Meera ba Haka bane" Meera tace, "ba gsky bane bana sonka Omar ka sake...." Difff kkeji sakamakon hade bakinsu da yyi Dan kawai ya hanata Furta kalmar sakin nan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.