Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA cmpl-2.txt
Chapter 10 of 85
Wannan kokarin da Allah ya bawa Omar Yana matukar konawa Saratu Rai, musamman idan ta kalli yadda danta baida kokari ko kadan dukda Yana makaranta me Tsadar gske dake Garin kano ba kowa ke shigar skul din ba sai Dan wane da wane, Ada tayi matukar farinciki sbd danta zaiyi karatu mekyau sai gashi taga sabanin haka, shiyasa duk lkcn da Omar ya nuna Mata jarabawar sa atake take kushe Masa, Omar a lkcn tun baya damuwa harya zo ya fara damuwa domin baya manta wata Rana ya zana placement dinsa yaci yazo da murnar sa da tsalle Yana kwalawa Saratu Kira ummah..., Saratu dake daki ta fito da sauri Sahabatu 'yarta mace na binta a baya tace,
"Kai lpy meya faru?"
Bakinsa a washe yace,
"Kinga takardar shaidar shigata secondary naci dama bana Gaya Miki wani mutum ya biyamin prvt skul ba matukar na samu takardar?"
Cikin kunar zuciya ta warce takardar tace,
"kana nufin makarantar masu kudi zakaje?"
Omar ya Amsa Mata da murna yace,
"eh Umma badan komai yasa nakeson zuwa can ba saidan principal dinmu yace matukar inason na zama Dr. Saina samu ingantaccen ilimi yace hakan bazai samu ba idan ba private din na shiga ba sbd can anfi samun isassun malamai"
Wani kululun bakin ciki ne ya Kama Saratu tace,
"toh bazakaje can din ba"
tayi mgnr tana keta takardar hannun ta, sandarewa Omar yyi a wajen Yana kallon yadda mahaifiyar tasa take yayyaga takardar hannun ta, a daidai lkcn mlm sale ya shigo gidan da Sallama da mmki ya karasa garesu yace,
"lpy kike yaga takarda?"
Saratu na huci tace,
"sbd yaron Nan ya Raina Mana Arziki shine yaje yyi roko a sashi a makarantar masu kudi? Duka nawa yake Yana Dan takala futuk?"
Mlm sale yace,
"sbd Allah meye lefin yaron Nan da kullum kike zuga Masa fada tamkar bake Kika haifesa ba? Na lura duk wani cigaban sa fa bakyaso bansan meyasa ba Sam"
a harzuqe Saratu ta taso dama duk takaici ya cika Mata ciki tace,
"eh naji tunda Kai ka Haifa min shi ko? Kai kasan zafin haihuwa kuwa da kke cewa kamar bani na haifesa ba? Toh idan be aminta Dani mahaifiyar sa bace ga kofa Nan ya fita daga rayuwata fakat..."
da sauri Omar ya sunkuya Zuciyar sa na zafi abubuwa biyu sun dirar Masa na farko irin tsanar da mahaifiyar sa keyi Masa Yana damunsa kwarai, na biyu bayajin dadin sabanin da suke samu tsakanin su da Abban sa, gashi abin ya sake gaba har tana ikirarin yabar gidan, Cikin danne zuciyar sa yace,
"Dan Allah ummah kiyi hakuri abin bekai har haka ba ni Wlh yadda kike zato ba haka bane da taimakon Allah da kokarina yasa na samu gurbin karatu a Wannan makarantar"
wani kululun bakin ciki ne ya sake Kama Saratu ta warce kafarta da Omar ya Kama tana Jan mugun tsaki sbd ambato kokarin da yyi Abinda bataso shine Sam bataso taji Omar din yanada kokari batason Abinda zaisa Rayuwar sa farinciki, so take Rayuwar sa ta dishashe ya zama irin jahilan Nan marasa aikin Yi cikin zafin Rai tace,
"karka Kara tabamin kafa banza marar amfani da haihuwar ka gwara barin ka Mtwsss"
ta fada tana barin wajen da sauri, Barinta wajen keda wuya mlm sale Yaja Omar dakinsa suka zauna Nan ya kwantar da Omar kan cinyar sa Yana shafa bayansa, yyinda Omar yake Jan zuciya da sauri da sauri idonsa duk yyi ja ransa na Masa suya kwarai, tunowa da yyi takardar daya Bata photocopy ce sai hankalin sa ya kwanta, anan mlm sale ya fara bashi hakuri da ban baki kamar kullum.
Toh dake duk Abinda Allah ya rubuta Saiya faru hakan ya kasance, Dan Omar ya samu gurbin karatu na secondary a wata prvt dake cikin garin kano Kuma babban farinikin sa ma boarding ce sai ransa yyi fari tas harma yaji zaman boarding din yafiye Masa Dadi fiye da gida Dan Yana sawa ya mance kunci da takaicin da yake kwasa a cikin gidansu, Ana haka cikin Rayuwar sa ta boarding ya hadu d Sadeeq, A farkon haduwar su basa shiri Sam kowa Dan Shan kamshi ne, Saida Sadeeq ya lura Omar ya fishi Shan kamshi nesa ba kusa ba sannan yadan risina sbd shima krtn yazo ba shashanci ba Kuma dama burinsa ya hadu dame ilimi sai gashi Allah ya hadashi da Omar, a zaton sa ya dauka Omar Dan wani babban me mukamin ne sai a hankali ya fahimci Ashe Shidin ba kowa bane saima ta hanyar Alfarma dayazo makaranta, abin ya bawa Sadeeq mmki sbd kafin Omar ya amince dashi Saida shi Sadeeq din ya yada makaman yakin sa kafin suka kasance abokai daga Nan abotar tasu ta daure har izuwa Yanzu da suke matakin karshe a university dinsu.
Mlm sale Yana Shiga damuwa sbd muguwar tsanar da Saratu takeyiwa Omar ya rasa meyasa hakan ke faruwa sai wanna lkcn Allah ya nufe shi dajin sirrin su tana waya ita da kawarta Habiba Nas da suka zama kawayen gaske. Dalilin kenan daya jawo kwanciyar Mlm sale a hospital kenan.
Taikaitaccen bayanin waye Omar kenan hade da sanin Asalin Sageer Hadi da sanayyar abotar Omar da Sadeeq.
*WACECE MEERA?*
Hafsat Ibrahim kenan 'ya daya tilo wajen Alhaji Ibrahim Usman (Dad) kenan da matar sa Hajia Amina, yarinya hafsat wadda suke kiranta da Ameera sbd sunan maman Dad da taci yarinya ta taso cikin Gata da soyayyar iyayen ta, tana primary 4 mahaifiyar ta Hajia Amina ta rasu sanadin haihuwa yaron ma bezo da Rai ba, dad ya Shiga damuwa kwarai dgske gashi kullum Ameera kuka take itadai mamanta, haka Dad zaice zata zo, toh abin yaci tura sbd hafsat har Rashin lpy tayi sbd kukan Rashin mahaifiya, Ana haka abokin dad ya bashi shawara ya Kara aure kodan ita ameeran tunda mace ce sai a samu me kula da ita, sosai Dad ya gamsu da Wannan shawarar harya Shiga sahun zawarawa Dan neman aure,
Ana haka Allah ya hadashi da Sadiya(Mom) Sadiya bazawara ce Dan tayi aure harta haihu Yara Mata biyu Shafa'atu da Jamila, Karshe auren ya mutu ta dawo gida zawarci, Cikin ikon Allah dad ya nemi auren Sadiya batare da Bata lkci ba ta amince musamman data ganshi da maiko, kafin auren ya shaida Mata yanada yarinya me suna Ameera Sadiya tace ai kar yaji komai da na kowa ne zata rike Ameera da Amana, dad yaji Dadi kwarai da Wannan kalaman nata batare da Bata lkci ba aka daura aurensu cikin aminci, a kwana a tashi Sadiya tayi renon Ameera na marmari da ganin ido Bayan wata guda kuwa ta fara yunkurin fadar qudurin ta wajen Dad,
Wata Rana suna tare ta nemi Alfarmar dad akan tanaso ta dawo yaranta gabanta sbd Yara Mata ne rikesu Dole sai uwa sbd tarbiya, Dad ya amince Mata sbd yaga yadda take nuna kulawa akan Ameeran sa, a takaice dai yaranta sun dawo sannu a hankali Ameera ta fara ganin banbanci a gidan, kafin wani lkci har an fara janye hankalin Dad akanta Saiya kasance Shafa'atu da Jamila sun fita nuna Isa da gidan ubanta akanta, Saiya kasance zuwa yanzu Ameera itace meyi musu duk wata wahala ta gida Dad Yana kallo bazaice komai ba saima hantarar ta da yake idan tayi lefi Ameera dai sai gani tayi kamar Wanda aka canja Mata Dad dinta me tsananin sonta zuwa wani can daban kamar besan wacece itadin agareshi ba. A kwana a tashi Babu wuya a wajen Allah sai gashi Ameera dakinta ya koma shine nasu Aunty Shafa haka wardrobe dinta shine nasu kayanta ya zama nasu sbd da kadan suka fita a shekara a surar jiki kuwa ta fisu shape saima ragewa da sukayi, ita Kuma me daki kayanta ya koma Ghana masgo me cike da kodaddun kaya, Kuma wajen kwanciyar ta shine dandanin kasa komai Sanyi kuwa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.